Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinyi kyau da tuni kin cuceni banga shigar da kikayi ba,
Muji nan ya fara shafa dukiyar fulaninta, ai Amana sai gashi ta fara layi tare da lumshe Ido kamar me bacci suna a tsaye,yake romancing dinta tana mayar da martani,Rada masa tayi Baby idan kace na tsaye zakayi bazan iya jurewa ba sai dai ka daureni da igiya, ai Alim Bai San sanda dariya ta kwace masa ba,

I love my Amana amma dole kiyi kokari kiyi domin duk style din duniya sai munyi,kullum ke kike bada style most of the time amma yau nawa zan kawo,Amana tace Bazan iya ba amma idan kaga na fadi ai ka fada musu,Alim yace ai to rikeki zanyi,hmm Baby kenan kai har wani karfi ne da kai,na tabbata idan ka fara to ko ni sai na iya zaneka bare kace idan an fara zaka iya tsayawa abinda karfi guduwa yakeyi,

Shuru Alim yayi tare da daukanta cik ya maidata bed nan suka fara baje koli,Amana yau kam tasha wahala hanun sa domin Har kuka tayi dan ba saurarawa kamar yau ne na farkonsa,
Ya bata wahala sosai amma itama taji sweet wanda yafi na baya ma cewar Amana.

Alim sai albarka yake sa mata kamar me sannan yace Abishirinki Amana tace kudi yan Dubu Dubu ba goro ba,murmushi Alim yayi,yace na biya mana aikin Hajji,suma su Ummanki duk na biya musu,next yr kuma su Hamza,Badriyya da Sakeena da mijinta duk zamu tafi na biya harda su.

Key din mota ya miko mata sabuwa dal me matukar tsada da kyau ya siyawa Amana,takaddu ya mika mata gashi wannan gidane na sai miki a cikin kano idan munje kano ciki zamu dinga Zama,
Amana ta rasa me zata ce ma addua ta fara rakarkatowa Alim baji ba gani kamar ta zare,
Alim yace to mene hakan kikeyi kayana nakine fa ki daina min godiya,
Amana tace kai da na iya rawa yau da har rawar Michael Jackson zanyi,
Me kake so na baka a duniya? Da murmushi Alim yace kin bani komai,kina min komai,bani da matsala,kawai kiyi ta sona,ki zauna Dani har a bada sannan kuma ki bani dadi ya karasa tare da kashe mata Ido daya.

An gama Dear sai abinda kake so na Amana bada kanka a sare,Alim ya karasa mata da Naje wajen Abba nace ya fadi wlh ya furta wlh da muryar Yan daba yanda Amana takeyin magana da kafin yanzu,
Dariya tayi tare da furta Kana yawa fa.

Soyayya su Amana suke Sha kullum cikin kwanciyar hankali,har suka tafi Saudiya,kuzo kuga Badriyya na addua a jikin kaabah a fili takeyi uban kowa naji, Huzaifa yace to idan kinyi a hankali ma ai Allah zaiji sweety, dukansa Badriyya tayi kadan da wasa taci gaba da adduarta,Amana da Alim suna can gefe tayiwa kanta,tayiwa Babanta,Ummanta,uwa uba mijinta, yan uwa,da Sauran Alumma, Saida ta gama adduoi masu muhimmanci, a karshe ta dawo ta fara ta soyayyarta da mallake miji,tace Ya Allah mijina Alim kasa yayi ta sona,ubangiji Allah Allah yaaa Rab Alim ni kadai nawa,Allah ka mallaka minshi,haka Amana ta dinga adduar mallake Alim,Alim ya dinga ta sonta ita kadai,bata ma San a fili takeyi ba Alim na jinta,yana ta Jin dadi ga dariyar Adduar Badriyya ma da take cewa ya Allah dan nan dake cikina kasa ya gaji halin Ubansa na kwarai,Allah kayiwa dan Huzaifana Albarka yana kyautata min...Huzaifana mijina ka tsundumashi a Aljanna.

Sakeena kuwa ba ruwanta a hankali takeyin tata.,su Umma ma suna nasu bangaren abinsu.
Saida suka koma Hotel masaukinsu Alim yake ta tsokanar Amana da cewa aure zai kara Addua bata karbu ba,
Sun gama aikin Hajji lafiya sundawo banda Alim da Amana domin sun wuce London sati Uku sukayi sannan suka dawo gida,Amana tsaraba ba a magana,

Sun dawo da sati daya Alim yace ta shirya zatayi waec da Neco,murna sosai Amana harda tsalle,
Mum tana can a kasarsu ta rame tayi baki ta fige ta yage,danma Alim na kiranta kullum ya lallasheta,kuma yana tura mata kudi su Nura kuwa kawai a sati sau daya suke kiranta ma,Abba kuwa ko zancen Mum bayayi ba yaso yaji zancenta,

Amana tana zaune a kujera Alim ya shugo ya fada kujerar yana sauke gajiya juyawa yayi tare da kwantawa a cinyar Amana,Ta fara wasa da botin rigar sa tana masa sannu da zuwa,
Sai shagwaba yake mata,kamar karamin yaro tana ta lallabashi,wayar Amana ce tayi kara,dubawa tayi taga Ya Kb dauka tayi suka gaisa suna wasa da dariya sannan yace wani tsoho tukuf yazo har gidafa yana nemanki,

Ya bamu labarin abinda ke tafe dashi kaf dangi munji komai harsu Badriyya da Sakeena Amma yanzu ya za ayi?gwara kiji abinda yazo dashi da kanki,Amana tace bari nama transfer kudi ka sakoshi a jirgi yazo zan sa a daukoshi daga airport,

Nan Amana take fadawa Alim yace ba matsala,haka kuwa akayi Alim ya tura kudi tsoho yazo lagos aka daukoshi har gidan Su Amana,sai kalle kalle yakeyi,
Abinci me aiki ta kai masa yaci ya koshi yayi Sallah,Sannan Amana tare da Alim suka fito wajen tsohon,suna ta masa kallon sani kamar sun sanshi.
Gaisawa sukayi da tsoho,Alim yace make tafe dakai? Kamar na taba ganinka,
Tsoho ya karkace yana goge hawaye tare da furta ba kama bace Dannan,yaro ba kama bace kun sanni idan zaku iya tuna Baba tsoho dake haskaku da fitila a lungun duhu,har na maka ihun kwarto aka biyoku,
Amana tace yes mun tuna mun ganeka amma lafiya Baba? Tsoho yace labarin me tsawo ne,sanda muke haduwa kece baki sanni ba amma ni na sanki nasan komai na rayuwarki,kuma nasan kuna da aure tun tuni,zuwa nayi na roki gafara Ku yafemin na yi muku babban laifi,zuciya da shedan suka sa na kasa hakuri,
Labari ya fara basu,watarana ke Amana tun kina budurwa kina kauye sannan kina fama da kuruciya kuma bakya barin ko ta kwana.
Ni na kasance tunda nake ban taba haihuwa ba a duniya har na tsufa,ina cikin bukatar haihuwa Allah yasa na auri wata kwatsam ta samu ciki ta haifamin Namiji,
Bani da kamar yaron nan na dauki son duniya na dora masa,ko zaginsa bana bari ayi,watarana ya tsokaneki kika biyoshi har gida kika lakada masa duka tare da farfasa masa jiki,readers idan baza Ku manta ba farkon novel din nan Amana yaro ya tsokaneta ta bishi har gaban uwarsa ta hada masa jini da majina,to wannan yaron Baba tsoho ke magana shine dansa.

Bana gida na dawo na tarar da yarona ance ke kika masa haka,raina ya baci nayi niyyar shiga malamai domin naga bayanki sai na fasa na shiga bibiyarki har Allah yasa naji labarin kin dawo garinku da zama ke da mijinki,
Ina sani nake muku magana har na gano gidan da kuke Zama dalilin ihun kwarto da nayi muku,
Muka biki har gida dan naga gidanku,hakan yasa na tafi Adamawa nayo hayar yaro na biyashi kudi yazo har gidan ya shige dakinki ya fito ya kulla miki sharri don naga na cusa miki bakin ciki sabo da naga duk duniya kin fi son mijinki da komai,

Yaron yana Adamawa yanzu ya shiryu sanadiyar wata yarinya da yake so,
Sai laifina na biyu wata baiwar Allah tazo garin neman gidan Babanki cewar Sulemanu yayiwa Yarta fyade ni na mata jagora ta ga gidanku,da dare ta dawo da matasa yan daba tasa sukayi wa Sulemanu duka suka karairayashi.

Nayi hakane sabo da son dana son kai da son zuciya,yanzu kuma nayi nadama naga banyi dai dai ba nazo Ku yafe min,domin yanzu dan nawa ya kangare yaro karami yanzu ya fada shaye shaye dalilin son dana ke nuna masa bana masa fada sai gata danake nuna masa,

Amana ce tayi ta maza tace sanda kace anyi maka haihuwa fa?har mijina ya baka kudin rago,tsohon yace yarinya mace aka haifar min,yanzu kuma duk wanda muka aikata muku ba a Dade ba sun rokeni idan na ganki na fada musu zasu zo neman gafara,dan Allah yarinya ki yafe min,Alim zuciya ta cika da takaici ji yake kamar ya masa mugun duka,
Sai dai ka karbi hukunci a koti domin baka ma da hujjar yi mana haka,ka zaluncemu kasa na zargi matata,da ace na saketa fa,kuma bayan yaron shi ya tsokaneta wannan hujja ce?kawai bakar zuciyarka dama can mugun halinka ne,kasa mun zargi mutane da yawa wanda Ashe basu suka aikata ba sai wanda kai bamu sanka ba,bamu damu da kai ba,mun manta dakai Ashe kai sharri kake kulla mana to baza mu yafe ba itama baza ta yafe ba kuma sai kasha dauri tsohon banza,bakaji dadin halinkaba cewar Alim....tsoho yaci gaba da magana.










AsmaBaffa


Godiya nake readers.
✳CIRANIN AMANA✳



190-195


Official




By
AsmaBaffa

Ku yafe min sharrin shedan ne,Amana nayi hakan ne a nufina dan na koyawa zuriarku hankali saboda abinda kukeyi a gari baku kyale kowa ba a garin nan mutanen gari,yan uwanku ma gudunku sukeyi domin da Sulemanu ya rasu da kyar suka zo gaisuwa saboda su Kansu baku kyalesu ba,sai gashi hukuncin Allah ya canja muku rayuwa,

Ku yafe min gafararku nazo nema domin idan ma a kotu an yanke min hukunci kwana nawa zan kara a duniya,
Nasan banyi dai dai ba,Alim cike da takaici yace pls ka kyalemu haka ni na zata mutumin kirki ne kai har nayi asarar kudina aka kawoka gidana,bana kaunar ganinka,kuma dole ka karbi hukunci dai dai da abinda ka aikata,Amana dai tana jinsu ta kasa magana sabo da mamaki daya lullubeta,Alim sai faman masifa yake saukewa tsoho,

Amana ce tayi magana ba komai Baba kanka ka cuta ka ganni dai baka rageni da komai ba domin mijina Bai sakeni ba Kuma Bai jira ya tsaya dogon bincike ba saboda ya yarda Dani muka ci gaba da zaman aurenmu,
Ka bani mamaki tsoho wlh da ace dane da nake Amanar Sulemanu Harka da a nan wajen saina bajeka,duk tsufanka saina barar da kai,a kan son yayanku Ku dinga mugun abu,wato na wani banza naka dukiya ko,Danka kuma ko yanzu ya min rashin kunya kaji da kyau saina ballashi ni matar Alim yar Sulaiman ba a ja Dani,murmushi Alim yayi yanda Amana take zabga kuri,
Ita kuma wacce ta yi sanadin Babana ina jiranta ka kawota,da yaron daka tura yamin sharri harda kwasheni da mari ina matar aure,ya gyara kumatunsa domin Idona idonsa sai mijina ya rama min Marin daya min.

Kaikuma sanadin tsufanka kaje halinka ya isheka amma ni na yafema har Abada,
Alim da sauri yace ke mene haka wa yace ki yafe,karka damu gashi munci riba tunda kaga na yafe kawai ka kyale maganar,ai na gaba yayi gaba na baya sai labari Allah yanason me yafiya kyaleshi kawai,
Alim yace to shike nan Baba an yafe ma ka kiyayi gaba,ba haka akeyi ba daga anyi ma abu ka rike mutum a zuciya har sai ka yi masa mummunan sharri.

Baba tsoho godiya ya dinga yi sannan ya danna waya tare da kiran Matar da ta ragar gaza Sulemanu Harka,da yaron da yaje gidan su Amana,adress ya basu na gidan Alim yace Suzo yana gidan ma.
Tashi Amana tayi tare da komawa sama cike da mamakin tsoho a fuska kamar mutumin kirki.

Washe gari da wuri sai ga matar ta shigo gidan Alim harda sanda tana dogarawa kayan jikinta duk sun yage,
Itama an bata abinci da ruwa taci ta koshi,da karfe biyu saiga Saurayin nan da yaje gidan su Amana,shima an masa saukar mutunci,har yau su Amana basu leko ba kuma gaba dayan bakin nasu suna bangaren masu aikin gidan nan aka basu masauki,
Shuru suna jiran su Amana shuru suna can suna soyewa sun manta da baki,har wurin 3pm sannan Suka fito makale da juna tare da bada Umarnin a kawo musu baki part dinsu,

Baki dai sai kalle kalle sukeyi sunga gidan da basu taba gani ba,Amana ta fara magana sannunku da zuwa,nan baki suka gaishesu kai a kasa,
Jin muryar ta yasa Saurayin nan ya dago tare da kallon wace wannan me muryar masoyiyarsa matar aure,
Ai kuwa karaf suka hada Ido da Amana ba wani bane face Deeni kwaro dan Adamawa wanda ya kai Amana asibiti,to wai ma ya Akayi Amana bata ganeshi ba time din da suna Adamawa,
Deeni Kwaro cewar Amana dama kaine ya Akayi ban ganeka ba? Mamaki da zufa ta ketowa Deeni,yana ina...Ina fara magana,lokacin kin shiga cikin tashin hankali ba tani kike ba ta mijinki kikeyi shi yasa ba ki Kula ba har nazo na kwada miki Marin daya gigita ki na fita da sauri,ni kaina wlh ban taba yin irin wannan aikin ba saida Baba tsoho ya rokeni sosai ina yin aiki kala kala a biyani kudi amma ban taba yin irin wannan ba,shi yasa ni kaina a tsorace nayi aikin,
Amana tace shi yasa nake ma kallon sani a Adamawa,Alim abin ya daina bashi mamaki magana yayi yace ni kam ina ganinsa na ganeshi,ko a ina na ganshi wlh sai na ganeshi amma ba komai rayuwa ce,Deeni har kasa yana bada hakuri,tare da furta na Dade da tuba kuma kin Sani a sanadiyarki na tuba wlh na daina komai sanda nake ganinki a garinmu,
Lokacin ban San ke matar wani bace kuma harga Allah ban gane kece ba sai yanzu,ki yafe min dan Allah Ku yafe min,
Amana murmushi tayi tare da furta ai ka cancanci na yafe maka,na yafe maka Deeni,Alim yace wai ke meke damunki ne yanzu ni gaskiya Amanata ta farko nake so bata yanzu ba,gwara Amana me Zafi da masifa ta,ke wannan Amanar ta yanzu ban gane miki ba,Dariya Amana sukayi gaba daya harda su tsoho

Matar ce tace gani nima dan Allah a yafe min,ni kun Sanni farin sani Saude ce,duniya ta dawo Dani haka,Amana tace na Dade da ganewa kece Saude,ko dan dukan da kikaci a hannuna na yafe miki,Alim ne ya kwalawa Amana Biro a kanta na gaji da wannan abin naki komai kice na yafe,

Amana tace idan bamu yafe ba mene ribar mu kawai ka kyalesu,Allah ma yana yafiya bare wasu mu,duniyar nawa take kowa yaje da halinsa,Halinka jarinka babu abinda dan Adam zai hanaka ko yi ma a rayuwa face da Sanin Allah,
Deeni kuwa shi ya taimaka min da tuni na mutu ya kaini asibiti ya biya kudin magani lokacin da bani da kowa bani da ko sisi lokacin da cikina ya zube,
Ka kusa aure kuwa?Amana ta tambayi Deeni,Alim ina ruwanki dashi kuma,Amana cikin rada suruntunta ya kaita tacewa Alim da fa sanda Ina Adamawa so na yakeyi sosai,sunansa Na me Kunu,bai San ni matar Aure bace,amma da na fada masa ya hakura,har address dinmu na bashi,niyya ta na bashi kanwata Salam tunda ta girma,

Kafin kace me Alim mood dinsa ya canja gaba daya ya bata rai sai muzurai yakeyi hannu yasa ya gyarawa Amana hijab dinta sosai sannan yace to Alhmdllh duk mun yafe muku,ke kuma Saude kin makara Baba da kika sa aka sassara ya rasu shariarku sai a lahira sai dai kiyi tuba Allah ya yafe miki nasa laifin, Allah kiyaye gaba,kuje driver ya kaiku wajen shiga mota Ku koma gida Allah kiyaye gaba,

Jansa gefe Amana tayi tace haba honey jirgi zaka biya musu,harara ya balla mata,pls kaji da kudin nan fa mene amfaninsu,to bari ni na biya musu a nawa kudin,Alim yace gwara da kikace ke ni dai bazan yi asarar kudina ba bare waccen munafukin yaron wlh karya kara zuwa gidana,kuma baza a bashi kanwarki ba salon a dinga zumunci dashi yana kallonki yana jin dadi,ko ya zauna da Salma ya dinga tunanin kamar kece.
Suyi sauri su bar min gida.

Amana kuwa Bedroom dinsu ta koma tare da jawo wardrobe wajen da Alim ke ajiyar kudi da yawa ta ebo tare da dubawa a hand bag, Alim yana Palo a kwance ta wuce da sauri ya jawota ina zakije ya kuma ganinki ya dinga sonki,yana sha'awar min ke, zuwa zanyi na sallamesu,kudina kika ebo? Yeah cewar Amana kudinmu dai,zauna to naje ni na sallamesu idan akan jirgine zan biya amma ki zauna baza ki kara lekawa Palo ba sai sun tafi,
Ai dai mayi Sallama ko da Deeni ne cewar Amana,Alim ne ya fita tare da banko kofa,yana zuwa yasa driver ya kaisu airport sannan yace tace ku gai da gida,Deeni kuwa yasan Alim ne ya hana ta fitowa sabo dashi,kawai sai yace ni dama Abuja zan wuce ba sai ka bani komai ba na gode ina da returning ticket dina,Alim yace Good tare da tabe baki,haka suka tattara driver ya kaisu suka ware,Deeni dama da kudinsa shi yana da sana'a.
Alim kuwa masu aiki ya kira yace su kara share masa Palo su goge shi tas su sa air freshener da yawa da turaren wuta,wai dan karma Amana taji kamshin kalar turaren Deeni kwaro domin Deeni kwaro dan gayune sosai kuma kyakyawane ba laifi,

Deeni kwaro kuwa Bai zarce ko ina ba sai kano har gidan su Amana,yaje cikin gidan ya gaishe da Umman Amana yana ta zura Ido ko zaiga kanwar Amana ya so ta ya aureta,yana zaune da Umma suna hira sai ga Salma ta shigo kuwa daga makaranta Salma yan Ss3,ai kuwa Deeni yaga Salma kyakyawa itama yar caras da ita,
Umma ya tambaya Umma wannan yarkice? Umma tace yar gidan Inna ce kishiyata, nan ya shiga ina..Ina...da kyar yace Umma zata bani ita,Umma kuwa taga Deeni ya shiryu sosai gashi dan garinsu tasan asalinsa tace me zai hana idan tana sonka,ka nemi soyayyarta.

Salma ce ta shigo dakin Umma tare da cewa Umma ina su Inna da sauran yara? Umma tace sun tafi gaishe da yayan Babanki Alhaji Shehu,zasu biya gidan sauran yan Uwa ma sabo da kulla Zumunci,
Shagwaba Salma ta fara wai Umma amma basu jirani ba nace zanje gidan Anty Maimuna fa,Maimuna itama yayar su Amanace me aure da yaranta.
Deeni a ransa yace naga waje irin wannan shagwaba haka me birgewa,
Salma gaishe da Deeni tayi sannan ta fita tana fushi,
Mikewa Deeni yayi tare da yiwa Umma Sallama zai tafi Adamawa,har kudi ya bawa Umma,

Umma ta kwalawa Salma kira,Salma na zuwa Umma tace kinga wannan Saurayin daya fita? Salma tace eh,to Sonki yakeyi kuma mutumin kirki ne,Antynki Amana ma ta sanshi sosai,maza kije Ku gaisa ki rakashi zai tafi gida a garinmu Adamawa yake.

Salma murmushi kawai tayi tare da zurma hijab ta fita wajen Deeni,jikin kofa ta samu Deeni yana jiranta,cike da kunya taje wajensa suka gaisa,Deeni da idonsa yake a tangare tuni ya tsara Salma saiga Salma kamar ta Dade da saninsa Suna ta hira,duk yaron da ya shigo in dai kanin Salma ne ko kanwa sai Deeni ya bashi Dari biyar sabuwa kar,
Haka suka gama Hira ya tafi tare da karbar Number Salma.

Gwaggo dasu Inna kuwa kaf yan uwan Sulemanu sai da suka je suka basu hakuri suka ce kuma za a ci gaba da zumunci,sosai sunji dadi,Alhaji Shehu yace zasu je har gidan su Amana da Badriyya da sauran yaran Sulemanu inda zasu ga mazauninsu a kara karfafa Zumunci.

Amana tana zaune Alim ya shirya zai fita office,Amana tace dan Allah Baby kaje Dani kaji gidan so boring idan baka nan,
Lallashinta ya fara tare da rungumeta yana goga fuskarsa a wuyanta tare da magana a hankali,ba dadewa zanyi ba,kinga anjima su Asiya zasu zo da Autan Mum,idan mun tafi kinga ba kowa gidan ko,kai ta girgiza shike nan to bari na jirasu,
Zagayowa yayi da ita gabansa tare da fara kissing dinta,ya naga kamar kina fushi,murmushi tayi ba fushi nayi ba kawai dai banjin dadi ko period dina ne zaizo I think,har yau bamu samo Aabid ba?na zata ma mun samu dana ga kina wani kiba da kyau,

To da alama bamu samu bafa dan Allah kayi sauri ka dawo a kara nemowa ko zamu dace kafin period yazo kasan yanzu mahaifa ta bude,na matsu a samu Aabid dina,dariya Alim yayi tare da cewa ai kece idan nace a kwana ana yi sai kice waye waye ai gashi nan anji samowa, shagwaba ta fara masa da badan ya daure ba bazai iya fita ba,
Yana fita ta zauna tare da kiran Badriyya suna ta Shan hira,bayan sun gama ta kira Sakeena ma,ta koma su Hamza da su Anty Maimuna,Sadiya da sauran yan Uwa.

Tana gamawa ta fada kitchen tare da shirya lafiyayyen girkinta,ta kara gyara gidan ko ina neat,Alim minti kadan zai kirata yaji wai ko period yazo sabo da sauri yakeyi kar yazo baiyi komai ba,
Wanka Amana ta fito tare da yin Sallar sa'asar ta shirya cikin Atamfa fara me zanen baki Riga da skert dai dai ita Dinkin zamani tayi matukar kyau Sosai duk wanda ya kalleta sai ya kara,tana fesa turare taji door bell,takawa tayi har kasa ta bude kofa Asiya ce da Autan Mum suka kwada Sallama tare da shigowa,
Amana da fara'a mutunci hade da karramawa ta tarbesu har palon Sama ta kaisu,suna ta hira ta cika musu gaba da lemuka da ruwa hade da dambun naman kaza,
Asiya tace na girmeki nesa ba kusa ba ni Antynki ce amma ya zanyi matar yaya dole nace miki Anty,dariya sukayi Amana tace ya Zama dole kuwa ko na fada masa ya zaneki.
Asiya tace rufa min asiri da masifar ya Alim akanki.
Yanzu dai ankon biki na kawo miki fa gashi kuma zan fada miki shirye shiryenmu sai kiji ko zaki kawo idea,
Auta yace hmm Anty Asiya zumudi sai mijin ma ya rainaki wlh danma ya Ahmad ne me hakuri,kin fiye zumudi,Amana tace jinji yaro da'allah rufe mana baki manya na magana.
Dariya sukayi duka,domin Autan Mum ya girmi Amana sosai.

Suna ta hira da tsare tsaren bikin Asiya sai ga Matar Ya Nura ta zo itama tare da mijinta Nura babban yaya,nan suka kacame da hira da nishadi,Amana da Asiya suka jera abincin da Amana ta dafa kala wajen uku,Asiya ta dauko wani mugun azababben foodflask guda hudu ta kawo,Amana da Sauri tace ke yan mata wannan na me aiki me gayya ne,na Oga kwata kwata ne,ko a Ido kin San na me girma Alim ne angon....kasa karasawa tayi saboda hada ido da sukayi da ya Nura,wayancewa tayi da murmushi tana sosa wuya,Asiya ta sheke da Dariya tare da matar Nura suna tsokanar Amana su Na Ogan zasu ci,
Amana ta kwashe flasks dinta ta mayar kitchen,ta bar musu nasu suma masu kyau amma ko kafar na Alim

Please Login or Register in order to submit comment