Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin Amana taci Amanarsa ta zalinceshi gashi yana sonta Amma dole ya hakura da ita,maybe ma ta manta dashi tana ta rayuwarta cikin Jin dadi,a hankali ya furta Allah sarki ni..a fili .

To Alim dai yana ta baza idanu Ba Amana ba labarinta,tunowa yayi da Badriyya mutuniyarsa me handling case dinsa,
Komawa yayi wajensu ita da Huzaifa yace sorry frnd zanyi magana da kanwata for some few minutes,

Sun kebe waje daya shi da Badriyya Alim yace Sis wannan yarinyar fa? Badriyya tace wa kenan a hankali yace Aman...kasa karasawa yayi saboda yanda zuciyarsa ta kare,takaici yake son taso masa haka ya daure,
Badriyya ta lura da hakan sai tace oh...Amana ai sun bar gidan na....kafin ta karasa Alim yace Badai aure tayi kan aure na ba?Badriyya tayi dariya kamar bata San komai ba tace haba aure ba aure ba kawai Ummanta ce ta takura mata sai sun tafi Yola garinsu tayi mata talla.
Talla?Alim ya kwala da karfi yace to wlh bazai yiwu ba Sam,nan ya fara fada ni nake da iko da abata,
Badriyya batace komai ba sai tace ai na tausaya mata in ka ganta baza ka ganeta ba ta rame sosai kullum cikin kuka take tace wai sharri akayi mata aka rabaku gashi tana da ciki har ya fara girma,kasan me Baka ga bakar wahalar da take Sha da cikin nan ba,yanzu Amana ko maganar kirki ta daina sai da dalili,
Fiya fiya fiya Alim ya kama fyalla sauri kamar zai tashi sama,mota ya bude tare da fadawa ciki ya dinga bakin ciki da share kwalla na tausayin Amana har ya gaji yace ko mene ke kika jawo,ke kika jefa mu cikin masifa...nan take zazzabi ya rufeshi da ciwon kai mai tsanani cikin motar ya kudundune saida Huzaifa ya kaishi asibiti sannan suka koma gidansu Kano kenan.

Amana sun sauka lfy,wani gida suka shiga da Alama nan ne gidan su Umma,gidan Bulo ne ko siminti babu,daki biyu ne rak,ba mace a gidan iya Baban Umma ne kawai wato kakan Amana kenan,shi kadai yake rayuwa saboda tsabar masifar tsohon,masifaffe ne number daya,sabo da haka mata basa Zama da shi,haka Umma ta masa bayanin Amana da ita,zasuyi Sana'a,
Malam Nuhu yace to gwara da kukace zakuyi Sana'a ni dai kwandalata bazan kashe muku ba,gida dai gashi nan Ku zauna a waccen dakin baya Ga wannan ba zan yi muku abun sisi ba,

Amana dai tunda ta gaisheshi kala batace ba,tana rakube a bango kamar marainiya,tana tunanin Umma Babanta ta gado, Umma ce ta dan sai musu abinci har Malam Nuhu sukaci dan kadan dashi baifi mutum daya ba,
Amana kuwa bata cin shinkafa da miya amai takeyi da tashin zuciya amma Umma tace iskancine wlh baza ta sai mata komai ba,ga yunwa tana ji gashi bata da ko sisi,haka taci abincin tana ci ta fara Amai sosai Ai kuwa Malam Nuhu ya fara sauke Bala'i wannan iskanci ne wannan?yanzu haka ma cikin shege ne kuka gudo min nan za a cuceni, Umman Amana tace Haba Baffa da kai fa aka daura mata aure.

Amana ta ebu ruwa zata kuskure baki ta wanke hannu datt
ijon yace karki bata min gida kimin asarar ruwa ubanki ne ya sai min?kai gaskiya ubanku ya Sha wahala daku to wlh baza a zo a hanani walawa ba a gidana,

Amana kwalla ta share tare da tsugunawa tace kayi hakuri,kallonta yayi tsab yace iyye ke baiwar Allah yaushe kika daina harkar niganci da jagaliyar ne?Allah da iko yaushe haka ta faru?amma wanda ya aureki kamata yayi a bashi kyautar sarkin hakuri,yo ni da nine yausheeeeee tabbb,badan halin ki ba ebi ruwan kadan amma ki shiga bayi ki wanke hannu da baki ba a tsakar gidana ba bar ganin gidan ba siminti ba a lalata min gida,hakan Amana tayi ba tare da tacewa Malam kala ba,saboda tasan ma idan tayi magana to bakar magana zatayi domin ta kai wuya saboda halin da take ciki ga duniya ta bata darasi shi yasa bata cewa komai,kun San shi karatun duniya dole sai ka jishi,kuma ba iya kunne ne ke ji ba duk gangar jiki ce ke karba sosai.Amana sarkin zuciya ji take kamar tayi ta dukan Malam har ya suma,dan darajar Umma ta kyaleshi amma da sai ta nuna masa ita wace

Washe gari Umman Amana ta siyo gero ta fara kunun siyarwa ba na markade ba na daka su surfa ita da Amana su daka ayi Amana ta dauki katon botikin paint a kanta ta fita can wata majalisa,bata so gudun fushin Umma ta hakura, Amana kar A manta fa,dama can ta Saba da sana'a talla ne kawai bata taba yi ba amma duk aikin wahala tayishi kuma gata da zafin nama ba bata lokaci tunda tasan dole tayi ko dan abinda zasu sa a bakin salati bare ma ta San Umma ba kyaleta za tayi ba kuma bata son yi mata musu heeeee su Amana anji jiki fa da dane na tabbata Umma baza ta iya juya Amana ba,sai gashi yau Amana har mamakin wai ita Amana akewa abinda aka ga dama,da ace da dane har Baban Umma Malam Nuhu zata ci Ubansa. duniya kenan.

Amana kam yau satinsu Biyu da zuwa Yola,suna zuwa har gidajen sauran yan Uwan su Umma suna zumunci,
Amana tana zaune da waya a hannunta zata kira Hamza Umma ta kwace wayar kawo siyarta zanyi na kara jari,Amana shuru tayi ta zare sim dinta ta mikawa Umma dalleliyar wayarta sannan ta fashe da kuka sabo da wayar taka rage zafi da ita wajen kallon hotunansu tare da Alim sai taji sanyi a ranta ta samu nishadi to yau Umma ta kwace wayar ma amma duk da haka ba iya sim ta cire ba komai na wayar ta mayar kan Memory ta zare Memorynta ta hade ta daure a Leda tasa a bag dinta,
A banza Umma ta siyar da wayar Amana duk tsadarta,yayi dai dai da Alim wanda ya kasa hakura da Amana,ya shiga matsanancin Hali kullum sai ya Sha maganin bacci yake iya bacci kawai ya yanke shawarar kiran Amana ko muryarta zaiji ya rage zafi,canja new Sim yayi tare da dan nawa Amana kira amma ya makara wayar bata shiga,Badriyya ya kira itama ta gwada bata zuwa,yace Badriyya pls bani Address din inda suke a Adamawa,Badriyya tace wlh duk gidan basu sani ba amma dai gwaggo tasan sunan local government da suke a can da unguwar amma bata San wanne gida bane,tsaki Alim yaja yace kinga Illar rashin Zumunci wannan ba zumunci bane yanzu idan wani abu ya sameta kuma baza Ku sani ba، ya kamata ace ko kishiyoyi a dinga zumunci ana sanin asalin inda kowanne ke zaune Sabo da irin wannan. yanzu wannan me yake nufi kenan kuna Uba daya baku san inda yar uwarku take ba ku bakwa shiga harkar kowa gashi abin har yan Uwa na jini ma wannan ba dai dai bane,
Haka Alim ya dage ya dinga bala'in da masifa ya dinga saukewa Badriyya kwando kwando yana ta nuna mata illar rashin zumunci wasu kuma zumuncinsu ma sai suna Uwa daya Uba daya da iya su suke zumunci.Sai da ya gama yana huci kana yace hadani da gwaggo ta fada min Unguwar da lg din,
Bayan an fadawa Alim komai sai kuma ya fara jin dadi da nishadi kamar wanda akace masa ga Amana a gabansa,

Amana ce suke ta daka geron kunu,sanye take cikin kayan da ta saba dasu wata falkekiyar riga tshirt saboda cikinta ya dan fito sai jean trouser fari tayi kyau ba laifi Sabo da yanzu yawan addua yasa ta dan rage damuwa duk da cewar kullum sai tayi Kukan rashin Alim,amma yanzu ta danyi kiba kadan Sabo da cikin ya sata yar kiba da kyau yanzu,

Yanzu ma tana dakan geron ta tuno Alim sai hawaye tana yi Hawaye na bin kuncin ta,Malam Nuhu dake gefe yana jin radio ya mike yau ga kwarzababbiyar yarinya yar iska ke zan koreki fa daga gidana kullum cikin kunci da kuka ko uwarki aka yimiki iyeeee nace Ubanki aka miki? Ke kenan a gidana kullum cikin shigar yan iska kike kina nuna tsaraici,shi yasa ma ga badayanki zubin karuwa shaddar kasuwa ce dake wannan anya jikata tace ba musaya akayi ba,Umma dake wajen Murhu haushin Babanta taji yana zagin yarta sai taji tausayin Amana kuma,mikewa tayi tace ajiye dakan muje ciki muyi magana ba musu Amana ta shige daki tsoho ya dauki Salati yace Hauleeeee Hauleeeee yau ni Ubanki zaki nunawa kin haihu niiiiiiiiii....sai ya saki kuka.

Umma daki ta samu Amana kwance bisa tabarma tana sharbar Kukan takaici tayi rashin Uba da miji yanzu da Ubansu ya na raye duk Lalacewarsa ai gidansa zata zauna,a da suna ganin Baba bai musu rana ba bashi da amfani a garesu sai gashi tun ba a je ko ina ba mutuwarsa tasa sun ga rashin Uba babban wani abune a rayuwa,

Da da Mahaifa sai Allah Umma ce ke lallashin Amana tace kiyi hakuri kinji tashi ki siyo abunda kike so yau kici kinji,Amana bata ce komai ba,Umma ta rasa abinda zata cewa Amana ta sata nishadi Umma gani take yau kudi zata kashewa Amana sai tace Amanan Baba ko za kici mitimis?saida Amana tayi murmushi,Umma taci gaba zan kashe miki kudi ko mene fadi kinji,shuru Amana tayi tare da goge hawaye,Umma tace Aya fa? Dan tamatsitsi?dabino?awara?gurasa?ko dan silif zaki siyo flour kiyi? Amana tace ni kaza nake sha'awa dan Allah Umma ki sai min a ribar da muka samu,Hangame baki Umma tayi tace yo ina kudin kaza yake ke Amana wannan ai zalincine da mugunta har Kaza fa?

So kike ki karya jari canja wani kinji yar Baba,Amana kuma a duniya kazar take son ci,haka tasan Umma ba siya mata zata yi ba,sai ta hakura tace Umma to ki siya min kasar calabar da Aya.
Umma tace ko kefa zauna da kaina zan siyo miki ma,A mana insha'allah sai mijinki Alim ya dawo da kafarsa ya nemeki har ki ja masa aji da yanga ko?kyalkyal Amana ta kyalkyale da dariyar Jin dadi tare da furta ai Sai Umma,Amana sai nishadi Umma bata taba birgeta ba irin yau,tunda Umma ta ambaci Alim ta gamawa Amana komai a duniya.
Umma kuwa mamakin Yarta takeyi yanda take matukar son Alim haka,

Umma tace tab Amana ni kuwa me Alim yake miki ne kike sonsa haka?ko kanki bakya so haka,Amana cike da fara'ar da ta Dade rabonta da yin irin ta ta fara magana Umma baza ki gane ba komai Alim yi min yake Umma komai da kika sani,Umma tace komai? Amana tace komai Umma bazai fadu ba ina fada miki Umma Mijina karshene a komai da kika sani wasu suka rab....sai kuka wiwi Amana ta fara,sannan tana murmushi sosai ga hawaye tace Umma Allah uban giji ya daidaita ni da mijina,Umma Alim mutum ne,Mijina yayi Umma nayi dace,hawaye ya kwararo mata taci gaba da sambatu Umma Alim abin so ne dan ina Jin kunya ne da kullum sai na dinga baki labarinsa abubuwan da yake min.

Umma harda kwalla tace kullum zan dinga tayaki da addua yata.
Fita tayi da kanta ta siyowa Amana Aya da calabar harda Rabin kaza gashashiya sai da Umma ta siyo mata,Amana bata zata ba Allah sarki Uwa me tausayin yayanta.

Nan Amana ta zauna a tabarma ta dinga Garza,
Umma na kallon ta da tausayi.

Kusa da gidan da Amana suke makwaftansu akwai wani Deeni kwaro tantirin dan iskan gari ne,tunda yaga Amana ta fita tallan kunu yaji a duniya Bai taba sha'awar mace ba irin Amana,a ransa yace ko hannun Amana ya shafa sosai to ko ranar ma dan ta shi ya mutu,
Sabo da haka duk unguwar ake ce masa na me Kunu ko hannunta ka shafa sai ya karasa musu da ko yau namutu.

An fara Zafi sosai a Adamawa nan su Amana suka dawo suna kwana a tsakar gida,Amana tana can karshen gidan kan tabarma ta shige cikin net dinta sabo da sauro
Umman Amana ma tana tsakar gidan farkon gidan cikin Net,haka Malam kuwa yana can cikin daki,

Cikin tsakar dare Deeni kwaro ya taka katangar gidan ya dane tare da lekowa a hankali,sai yaga mata biyu saboda duhu gashi baya so Amana ta farka tayi ihu ya kasa shafa jikinta,haka ya shiga gidan ta saman Katanga sadab sadab ya shige cikin Net din Umman Amana ya zata Amana ce, kawai ya ya kara shigewa jikin Umma sosai ya fara shafa jikinta,Umma cikin bacci taji ana shafata ta manta Sulemanu Harka ya rasu cikin magagin bacci tace uhhmmm......Sulemanu....Sulemanu a'a....a'a mene haka Sulemanu,kaji jarabar taka ko,Da gudu Deeni kwaro ya fito fit kamar walkiyya Umma ta dawo hayyacinta ta jawo rigarsa baya ai kuwa Deeni kwaro ya cire rigar cikin zafin Nama ya barwa Umma a hannunta ya tsallake ta Katanga ya fece,

Umma ta fara kuka da kurruwa Sulemanu ya jawo mana yayiwa matan wasu wlh dole ayiwa nasa wani tsohon zan samu na aura kafin wani ya min Illa ohhh yau na gane da saurana Ashe saurayi haka na bi na ai sai aure,
Tashin Amana tayi tace tashi dan Ubanki mushe kina can wani zaimin fyade,bazan iya zaman nan ba wani satin zamu koma gidan Babanki gwara gidan Mirgayi wlh ina gama takaba zan samu sakarkarin dattijo na aura domin ubanku ya jawo mana sai mun tsare mutuncinmu.

Amana sabo da murna harda tsalle da kyar ta iya bacci sabo da murna zata koma wajen yan uwanta,murnar Amana dayace tasan dole bikin Huzaifa da Badriyya Alim zai zo ko don Huzaifa to dole ta ganshi ko taji sanyi.
Malam Nuhu kuwa dadi yaji zasu bar masa gidansa wani satin.

Alim duk abin duniya ya masa Zafi shirye shiryen bikin Huzaifa sukeyi kuma shine kan gaba shi ya tsaida dashi zuwa Adamawa neman Amana.
Washe gari Amana ta tashi fes cikin tsananin murna,karin Jin dadi n Amana Umma tace ta daina talla kudin da suke dashi ya ishesu har su koma gidan Baba Mirgayi.
Yau Amana ta fita siyo kayan miya a hanya garin tsallaka kwalabati kafarta ta goce ta fada katon Kwalabati marar ruwa cikinta ya bugu sosai nan take cikin ya juya sai jini ya yanke mata sosai yake ambaliyar fita daga kasanta,Amana ihu takeyi tana wayyo Allah dana dana zai mutu na shiga uku dana wayyoooo dana kar ka tafi me kama da ubansa,kai nake sa rai zan haifa na dinga ganinka kamar babanka 'yata ko dana me kama da Alim dina,
Gudan jinin Alim,zarota mutane sukayi da kyar ta kara dafe cikin taci gaba wayyo dan Halak dan Alim,wlh Alim ne yayi cikinka mijina Alim a gidan aurenmu,Ka tallafamin kaine shedata da zan wanke kaina wajen babanka,
Deeni kwaro ne ya taho da gudun tsiya masoyiyarsa ta samu matsala yace mahaukata kun tsaya my love tana gabanku shinfide cikin wani Hali kun kasa kaita asibiti sai kallonta kukeyi kuna kallon daga inda jinin ke fitowa kuna Jin dadi kuna kissima surart a zuciyoyinku,to gurin yafi karfinku,daga wanda yayi mata cikin sai nine kadai zan San wajen nan,

Amana dai ta fara fita daga hayyacinta sai nishi takeyi tana Dan Alim...shedata...dan Alim
Habawa ai tuni Deeni kwaro ya Sureta tare da tare napep sai asibiti.




AsmaBaffa

Tnx alot readers.
CIRANIN AMANA


160-165



Official




By
AsmaBaffa






Dukkan yan AsmaBaffa fans club godiya gareku da jinjina.love u all






Da sauri Deeni ya shiga da Amana cikin wani private hospital nan danan akayi emergency da ita likitoci suka rufa a kanta,komawa Deeni yayi tare da sanarwa Umman Amana da Malam Nuhu,a sukwane suka rufta asibitin,Umma sai kuka takeyi tana ohhh na jawo miki,na jawo miki masifa Amana Ashe kaddarace ta kawoni na daukoki nan Adamawa,
Deeni ne ya biya kudin asibiti da komai da aka bukata domin Deeni kwaro akwai neman kudi baya talauci..

Duk iya kokarin da likitoci sukayi dan ganin Cikin Bai fita ba amma abu yaci tura domin tun kafin ma a kara so asibiti ciki ya zube,dan haka suka mata wankin ciki,sai allurai da magunguna na Karin jini da sauran abubuwa,Deeni Kwaro kuwa maltina carton 3 ya kai da madara peak ta ruwa kwali biyu,sai kuma kullum da kalar naman da yake kaiwa asibiti wajen Amana.
Amana kuwa bata magana sai yanda akace da ita,da ance yi zata yi bari zata bari,kai ko gabas kace kalla zatayi,arewa,kudu,
Sai hawayen da basa tsaya a idonta,tasan yanzu ita da Alim sai a darul salam dama da cikin ta dogara idan ta haifa dole zaiyi ko kama da Alim sai ya San da gaske shine Ubansa to gashi ya zube.
Umma kuwa ko a asibitin gasa Amana takeyi sosai tana gyara ta cike da tausayi,
Satinsu guda aka sallamesu,Deeni kam yayi Namijin kokari,sai yanzu ya gane lallai son Amana yakeyi,kuma yaji labarin tana da aure,hakan yasa ya tattara soyayyarsa da kwadayinsa ya kara gaba dan karma ya dinga ganin Amana yana Jin wani abu ya koma daga gida sai wajen aiki,sanadin hakan Deeni kwaro ya daina halayen banza ya samu shiriya Sanadiyyar Amana me Kunu,Amana ma batasan yana yi ba,sunje dai har gidan su Deeni sunyi Godiya sosai,sai lokacin Maman Deeni ta basu labarin Deeni da komai har shiryuwarsa sanadin Amana,ai nan take ya birge Amana ta dinga yi masa fatan alkhairi,Amana ta bashi Address dinsu na gidan Baba.Deeni dai ya karba kawai amma bazai je ba tunda Amana Nada aure, kuma ga kunyar shiga net din Umman Amana da yaya satin Amana biyu cif da yin Bari yanzu kam Umma gyarata tayi sosai a saboda Shan madarar rakumi da sauran Abubuwa yasa Amana ta maida jikinta tayi sumul sumul tayi kyau na ban mamaki sabo da kayan da Umma ke bata tana ci da Sha na gyara,

Itama Amana saboda kullum cikin sa rai take zata hadu da Alim dinta yasa take yarda da gyaran sosai,kai ba kace Amana ta taba aure a duniya ba yanda ta kara komawa kuma gashi kullum dai sai tayi kukan rashin Alim amma a hakan ba laifi ramarta kadan ce ta rashin mijin ta.
Saura kwana Uku su koma gidan Baba Sulemanu Umma ta samu Amana tace na dauki Number Hamza dake littafi jiya na ari wayar Malam na kira shi mun gaisa sosai duk sunce a gaisheki,bikin Sakina da Badriyya Saura kwana 5 biyar a fara kinga zamuje a dai dai,Badriyya tace na fada miki ta kai miki dinkunanki cikin Kano za a yo miki,wai ya cikinki na basu Labari ya zube da abinda ya faru,sunyi jaje sosai,
Murmushi Amana tayi tace Umma bari naje gidan su Nusaiba ayi min dilka da halawa,Malam Nuhu shi ya bawa Amana kudin,Amana kuwa gaba daya kwana Ukun nan a gidan gyaran jiki take yini,ko ina ta gifta kamshi take bari me dadin gaske,skin dinta tayi smooth sai sheki da kyalli takeyi,duk wannan Alim takewa tanaji wai ko zai ganta ya ganta bata lalace ba ya ganta har yanzu fa za a je da ita,yaga bata ci baya ba,kuma duk sabo da tsaro bata San ya ta Allah zata kasance ba ko Alim zai yi tunani ya daina zarginta ya maida ta wajensa kunga kenan a shirye take,dama kuma kun San Amana bata son raini akwai son har kar wanka da gyara hade da tsabta.

Umma tace kinga gobe zamu tafi ko zakiyo lallen bikin?Amana tace a'a Umma salon ya goge ma da wuri kenan ai sai naje can zanje har cikin Kano city ayi min na kece raini,
Duk sabo da Alim Amana ake wannan cakarewa.

Ta wani bangaren Amana tana Jin haushin Alim sosai yanda ya manta da ita duk zaman da sukayi,ya kasa tunani akan abinda ya gani,ya zargeta,har ya yarda zata iya cin Amanarsa,
Uhmmmmm Amana ta furta a fili tace Namiji kenan me manta alkhairi,ka shekara kana aikin me kyau rana daya ta baci ba mutunci...wai ni Alim zai yarda Ina bin maza,wai Alim ya gujeni ya manta Dani,lallai a duniya anything is possible shuru tayi tana ta tunani,
Maybe idan Alim ya ganta ma ko kallonta bazai yi ba ya manta da rayuwarta,wani Hawayene ya zubo mata masu Zafi,ganin Umma na kallonta yasa tayi sauri ta fada daki ta kwanta tana ta shesheka har bacci ya kwasheta.

Alim kam bangarensa sai duai domin yafi Amana shiga kunci yaje Har Adamawa ya gama bulayi baiga Amana ba ya dawo ya dage da addua sosai na tabbata da Alim Bai rungumi addua ba shima da tuni ya haukace ya zare.amma a haka idan ka ganshi sai ka dauka bashi da matsala haka Addua take da yawan karatun Qurani yan uwa mu dage da Addua karatun Qurani shine magani.Alim gaba daya sun rankaya sun taho Kano bikin Huzaifa aboki kuma dan uwa.

Baban su Huzaifa part guda ya warewa Amare da kawayensu haka angwaye da abokai nasu daban duk cikin gidansa sabo da Amare Sakina da Badriyya ba a cikin Kano suke ba su kuma angwaye a cikin birni suke saboda dinner kala uku da angwaye suka shirya yasa Abba yace Amare da kawayensu su taho gidansa angwaye ma haka har mijin Sakina sabo da shima sanadin zuwa zance suke haduwa da Huzaifa har zumunci ya kullu tsakaninsu tare suke shirye shiryen komai,Alim kuma shi ya shirya musu party har kala biyu,Abban mijin Sakina ma ya shirya musu daya.don haka duk shagalin biki gidan su Huzaifa za ayi shi,daurin aure ne kawai za aje gidan Amare a dauro,su kuma iyaye mata suna can zasu Kula da jamaarsu ta gari.
Alim sabo da zaman mutuncin da sukayi da Amana da kuma sonta da yakeyi yasa kaf mazan da matan gidan da yara yayi musu dunkuna na alfarma manyan mazan kala Uku uku yaran kala biyu biyu,har iyaye har Umman Amana ya bayar da nata a Dinka a ajiye mata,Amana kuwa ya Dinka mata har kala Goma da takalma da jakankuna da mayafai tsakaninsa da Badriyya sukayi sirri yace tace wai Huzaifa ne ya Dinka mata itama kar ta fada shine,Badriyya tace to bakina kanin kafata,a halin yanzu Huzaifa yasan Alim da Amana basa tare amma duk ya tambayi dalili ba wanda ya fada masa har Badriyya kawai sai ya kyaleta.
Kayan abincin biki kaf Alim ne ya saukewa su Hamza shi da kudin kayan dakin Amare,amma Sam Angwaye sukace kar a kawo Amare da cokali sunyi komai nasu.
Alim ya karbi kudin ya siyawa Hamza da Kabiru kb fili kato guda biyi a Na'ibawa Kano,sun Hamza harda kukan dadi za a koma City,
Yacewa su Haladu ma za a basu nasu suyi aure shi kuma Huzaifa yace zaiyi tallafin Gina gidajen nasu,Ishaq Saurayin Sakina yace shi kuma zai zuba musu furniture,wannan murna kawai sukeyi suna cewa duk A sanadin Amana suka hadu da wannan alkhairi,Ciranin Amana ciranin alkhairi,ta yo musu hanyar arziki gaba daya gidan,domin ta hanyar su Alim kadai Alkhairi ke fado musu,

Allah

Please Login or Register in order to submit comment