Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

part dinsa ki dauki kayanki da Aabid can zaki zauna,munafuka saura ayi dan hali muna nan muna zuba ido kwanan nan za a koreki,kar kice zaki mike kafa matsiyaciya.

Amana ta dau Aniyar cin uban su saude sai nan da yan kwanaki,
Aabid ta nade cikin towel sosai fuskarsa kadai ake gani,goyashi tayi ta kinkimi akwatinta ta tafi part din Alim zuciyarta cike da tsoro,
Ta rasa dalilin da yasa take jin tsoron Alim,a palon kasa ta sameshi yana kallon News,sallama dauke a bakinta ta shiga,taga bakinsa ya motsa amma Sam bata ji muryarsa ba.
Aabid ta sauke cikin towel yayi fresh dashi,ba tare da Alim yayi magana ba ya mika mata uniform dinta,karba tayi tana budawa taga skert, a ranta tace yaufa akeyinta,a fili kuwa cike da tsoro tace master....master ban iya sa skert ba pls ka bani uniform me wando,
Ko kallon inda take baiyi ba kuma baice komai ba,shuru Amana tayi can tace to Master a bani kayan Aabid zan sa masa,sannan ka nuna min dakina zan je Na kwanta.
Sai da ya dauki 15mnt sannan ya mike yace biyoni ki karbi kayansa,a hankali ta bishi har bedroom dinsa ya nuna mata Sip wani part shake da kayan Aabid,akwati ta cika guda da kayan sawar Aabid har uniform din schl dinsa sanannan Alim ya gwada mata address din dakinta,godiya sannan ta sauka kasa dakin da ta fara shiga da farko me kofa biyu,daya kofar wacce zata kaita kitchen,bedroom din ya gaji da haduwa kamar Na Amarya,
Aabid ta shirya cikin kayan bacci itama tasa nata ta sukayi Addua suka kwanta tare,Aabid ya makalkaleta ya rungumeta sai kamshi sukeyi bacci me dadi ya kwashesu.

Washe gari da asubar fari Amana ta tashi Aabid sukayi sallah abinda Aabid bai taba yi ba sallar Asuba amma yau Amana ta sa yayi har azkhar ta fara koya masa,ita Amana fa yanzu bata da burin da ya wuce taga yaro me tarbiya,tana sha'awan hakan saboda gidansu kaf babu me tarbiya,shi yasa ma ta ke son koyawa yaro tarbiya duk da cewa ita bata da ita,ta sani amma tana so ta koyawa wani,shi yasa take koyawa Alim tofa kaji su Amana.
Wanka da brush tayiwa Alim sannan ta shiryashi cikin uniform din schl dinsa,ta yi wanka itama tare da tsaftace lungu da sako Na jikinta sannan ta fara shiri,uniform din Ma'aikata da Alim ya bata Riga da skert su ta ebo,tana kunkuni tasa pant da wani tight iya gwiwa,sannan tasa skert din,Amana kwai diri da sura,kamar an gwada ta skert din das a jikinta,sannan tasa rigar,gyalenta ba fari Alim ya bata ba kalar skert ne dark blue,Amana gaba daya ji take a takure take ta dabaibaye,ita da wando ta saba,
Gyalen maimakon ta yafa sai ta daura kawai a kanta ta gyaran room din tas,sannan ta fesa turarenta ta fesawa Aabid ma,7am ta riko hannun Aabid suka haura saman Alim,

Aabid da gudu ya shige bedroom Alim yana cikin bacci yaji Aabid Na tashinsa Daddy ina kwana Anty ce tace Na dinga Ce maka ina kwana,
Alim a hankali ya mike tare da shafa kan Alim yana morning son har kayi shirin schl,ae Daddy Anty tana jirana zanci abinci ta kaini schl,maza to jeka kace tazo ina nemanta,

Da gudu Aabid ya koma wajen Amana yace Anty Daddy yace kizo,gabanta ne yayi mugun faduwa kamar kwai ya fashe mata a ciki haka ta shiga dakin tana tafiya bata saba da sa skert ba,kawai garin tafiyar niggoginta skert ya hardeta ji kake rim ta fadi a kasan tiles Na dakin Alim,Alim dake kwance nade cikin bargo yana kallonta,ko sannu bai mata ba,haka ta mike tana Sosa kanta,tunda Alim yake bai taba sanin uniform din ma'aikatansa Na da kyau ba sai a jikin Amana,a ransa sai ayyana irin kyanta da kyan diri irin Na Amana amma take cutar kanta kullum abubuwan maza takeyi.

Ko gaisuwa Amana bata yi ba kawai sallama takeyi ita bata saba da gaida mutane ba,shima Alim bai damu ba yace kije kitchen ki hadawa Aabid abinci, kece kullum zaki Na dafa masa abinci,ki kaishi schl ki daukoshi ke da driver,
To kawai Amana ta furta tare da fadawa tunanin family dinta,jibi gata da son karatu, amma su iyayensu Sam ba ruwansu da ilimin yaransu,gashi suna son karatu ba dama,a fili kuwa cewa tayi master dan Allah ka sani a makarantar Aabid kaga ni a ss2 Na tsaya sai mu dinga zuwa muna dawowa tare,

Bazan saki ba cewar Alim,kafin ya rufe baki Amana tace master lada zaka samu Ina fada ma taimakon irinmu zai iya jefaka a aljanna,Fice min da gani cewar Alim, baki ta zumbura tare da ficewa tana kunkuni.Alim a ransa yace lallai yarinyar nan bata da kunya karshe,zan gyarata very soon.
Kitchen Amana ta shiga Wanda ke part din Alim,Dattijuwa Saude ta iske a ciki tana shiryawa Alim girki,ko sallama Amana batayi ba ta fara shiryawa Aabid da kanta abinci, minti kadan ta soya chips, da egg,sai tea me kauri,ta damawa Aabid oats da madara.

Saude sai kallon Amana takeyi tana dama haka take da kyau,lallai karfa yarinyar nan ta karbe gidan nan watarana, a fili Saude ta ce insha'allahu hakan ma baza ta faru ba,

Amana tana aikinta sai ji tayi Saude ta bangajeta, a zuciye Amana ta shaki wuyan Saude tare da makata jikin bango sannan ta dinga zagin Saude tare da kara makure Saude ta kwala mata ludayin miya a goshi kafin kace me goshin Saude ya kumbura ya fashe yayi wani sumtum,Amana kuwa ta gama aikinta ta jera komai a tire ta dauka ta haura saman Alim,

Ganin haka yasa Saude tace wlh baza ta kyale Amana ta mata illa ta tafi a banza ba,Saude Ce ta suri mubirgin miya tabi Amana a guje har Saman Alim,tunaninsu Alim bacci yakeyi,turus suka ja birki ganin Alim zaune cikin shiri da Alama fita zaiyi,Saude uwar makirci nan take ta fashe da kuka tace Alhaji kalli yanda wannan yarinyar tayi min duka a kitchen,ta fasa min kai akan kawai nayi mata nasihar gishirin zaman duniya,yar daba ta fara dukana harda cewa itace ajalina ta kara fashewa da kuka,Alim sarai yasan karyar Saude, Saude kuwa ganin Alim bashi da niyyar magana yasa ta kara bude baki zatayi magana,ji kake fafff Amana ta make mata baki tare da cewa ki kyale mana master dallah haka karki sa masa headache,

Bakin ciki yasa Saude shako wuyan Amana,Amana kuwa me karfin maaza Hannu tasa ta mirdewa Saude hannu, wayyooooo cewar Saude tana ta kara,Amana tace ina daga miki kafa Iya ke babbace kija girmanki kafin Na fara taka ki,wannan abin ba komai nayi miki ba wlh ki kiyayeni ko a garinmu Na kano bani da mutunci ki tambayi tarihina kiji,

Saude da kyar ta kwaci kanta ta arce da gudun tsiya,Alim Na kallonsu a ransa yace naga Alama yarinyar da ta ja da yan fashi ta fansheni ai ta kai karshe a duniyanci.
A fili kuwa tsaki yaja sannan a hankali yace idan Aabid yayi late a schl sai kin karbi punishment,da sauri ta zauna ta bawa Aabid yaci ya koshi itama taci sannan ta daukeshi ta wanke masa baki neat ita kuma ta dauko aswaki zurere Na itace ta sa abakinta sukayiwa Alim sallama driver ya daukesu a rantsatsiyar mota ta kai Aabid schl sannan suka dawo tare da driver,tana ta dirzar bakinta da itacen aswaki,Amana idan tayi brush da asuba to duk cin abinci ko sallah sai tayi aswaki haka tsarinta yake,har palon ta shigo tana aswakinta,
Alim taci karo dashi zai fita ba Wanda ya kula wani ta wuce dakinta ta kuskure bakinta ta kwanta sai bacci.




AsmaBaffa

[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳



45-50



By
AsmaBaffa




Amana duk baccin nan da takeyi a kasa ta kwanta,jiya da ta hau bed jikinta damunta yayi saura kadan ta makara a sallar asuba,shi yasa ta sauka kasa,sabo da Aabid ta kwanta a kan bed,
12:30 pm Amana ta farka,sallah kawai tayi ta fada kitchen ta shirya lafiyayyen abinci sannan tayi wanka ta shirya cikin uniform dinta,sai kamshi take zubawa saboda uniform kala biyar Alim ke bawa ma'aikatansa kuma duk shekara sai an sake musu new,a hankali Amana take tafiya saboda skert dinta bata iya tafiya da shi ba mantawa tayi ta taka kayam kayam da sauri,shi yasa a kullum sai ta fadi wajen sau biyu ko uku,

Wucewa tayi wajen driver zuwa dauko Aabid saboda 1:30pm ake tashinsu,Amana yan gayu har takama takeyi tana kamewa a bayan mota,
Tana zuwa schl din har an tashi Aabid da gudu ya shigo motar yana rungume Amana,schl bag dinsa ta karba suka karaso gida,
A palon sama suka iske Alim zaune cikin 3qtr brown da Riga coffee color,sai kamshi yakeyi part din dama yan aiki sun gyarashi neat ko ina kyalli yakeyi, Suna shigowa suka rafkawa Alim sallama tare da cewa Daddy mun dawo cewar Amana kaji shishigi wajen Amana,
Daya room din opposite Na Alim ta kai Aabid ta cire masa uniform tare da jefa kayan a washing machine,ta hau yiwa Aabid wanka,a towel ta nadoshi ta fito dashi Palo yana bayanta ta zaunar dashi a kujera,komawa tayi ta shanya kayan da ta cire masa,sannan ta fito da sauri tana ta fiyarta zata dakkowa Aabid kaya ji kake timmm skert ya harde ta fadi,wannan karan sai da taji ciwo a kafarta,Alim ko a bai ce ba Aabid ne kadai yayi mata sannu,
Abinci ta dauko musu suka ci abinsu a Palo,Alim sai satar kallonsu yakeyi yanda suke wasa da cokula,
Bayan ta shirya Aabid cikin uniform din islamiyya nan kuwa ba nisa a kusa da gidan Alim Islamiyyar take,a kafa ta kai Aabid ta dawo ta gyara wajen da suka bata kana ta wuce room dinta.

Mum Alim zaune a bakin makeken bed dinta da Alama nazari takeyi a ranta tana ta tunanin yanda zata bullowa Abban Alim domin so takeyi tayiwa Alim aure tana jin tsoron karfa Alim ya hadu da wacce yake so,
Bari zanje gidan Alim da kaina next Wk zamuyi magana dashi dole ya karbi zabina haka ta gama sake sakenta sannan ta fita kitchen wajen masu girki tana zunduma musu ashar basu gama girki a kan lokaci ba,

Gidan baki kuwa yana nan inda yake sai abinda ya karu domin lalacewar tayi yawa,yayyen Amana mata guda biyu an sako su daga gidan miji suna nan an hadu ana sheka tsiya,Baba kuwa wato sulemanu Harka ya shagala wajen wata bakuwar bazawara da ta zo wajen matarsa wato umma Babar Amana kenan sun bude harka a boye suke fasikancinsu a gidan liman abokinsa,wani dakinsa da yake harkar bokanci anan suke kwashewa tare da wannan bazawara me suna Salamatu, har yau matan gidan basu gano ba,har Babar Amana bata sani ba sabo da Salamatu ta kware wajen rike sirri,bata wasa da sirri.

5pm Aabid ya dawo daga islamiyya, 8pm Amana ta dauko abincin Aabid ta zo sama part din Alim,Aabid yana can yana wasansa Alim yana cike wasu takaddu Amana tayi sallama ta shigo dauke da tire,ta kalli Alim Wanda ya ke cikin jallabiya fitted fara tas sai sheki yakeyi,yayi kyau matuka kamar aljani cewar Amana,sai kuma tace barka master asha aiki Lfy master,
Ko kallonta Alim baiyi ba yana jinta,TV Amana ta kalla taga ana nuna wasan Barcelona da Chelsea, da sauri ta ajiye abincin gefe,wata uwar sufa tayi a kasan center carpet kamar zata fada cikin TV din,ta tsura ido tana kallo,
Can Messi ya fara yanke yan wasan Chelsea Ya wuce zai kaita raga Amana da karfi ta fara uhum....uhummm...yawwa....yanke shege....sai Messi.....a....goal.......sai tafi ta fara raf raf tana murna kamar an mata bushara da gidan Aljanna,Alim dake aiki cak ya tsaya yana kallon abinda Amana takeyi,
Can kuma Iniester ya dakko ball Amana tace ehem..good idea mikawa Suares mana ai kuwa Iniester kamar yaji ya mikawa Suares,

Amana ta fara ihu cikin siririyar muryarta tana tafi Suares ya buga sai ta daki pose ta dawo ai Amana tace Oh.....God..tayi kararrawa...shege yayi kararrawa, dakiki Suares ya zakayimana haka dabba shashasha dolo,common ka buga ta ka wani makata sama,

Ana ta ball tayi zafi Chelsea suka farke 1-1 Amana tayi lakwas tana zage zage,Alim kuwa tsayawa yayi yana kallon abinda Amana takeyi kamar tv, ana ball fa can wani lokaci Suares yaci daya,minti kadan messi ya karawa Chelsea,sai ga Amana ta mike tsaye tana ta tafi da tsallen murna,kuma gashi an tashi 3-1 Barcelona sun cinye Chelsea.

Juyowa tayi taga Alim ya kafe ta da ido a tunaninta shima ball din yake kallo shi kuwa Alim tunaninsa anya Amana kalau take kuwa.
Abinci ta jawo tare da cewa Aabid my Boy zo maza muci abincinmu sai wasa kakeyi kana gani munci ball ko murna baza ka taya ni ba,shi dai Aabid dariyarsa yayi ya zauna,
Abincin ta bude wata hadaddiyarr jallop din taliya da doya tasha kifi,ga wani lemon dabino da kwakwa da ta hada me sanyi da dadi,ga wani flask dan karami ta hada coffee lafiyayye,wani plate kuma kankana ce da yawa ta yanka da pork ciki,gefe guda kuma wani farfesun kazane sai kamshin dadi,

Kallon Aabid tayi tace boy da wanne zamu fara?Alim tun a ido yasan girkin zaiyi dadi da ace zasu bashi to da ba shakka zai ci,amma yaga Amana kwatakwata bata iya tayi ba a rayuwarta,idan zata ci mene a gaban mutum baza tace gashi ba,kuji Alim din nan da kwadayi,to Amana a gidansu basawa juna tayi haka suka taso,

Yau kamar Amana tasan Alim me yake sakawa a ransa,taga yanda yake kallonsu,kawai sai tace uhm mutum da yake siyo kayan abinci a cinye a dinga hanashi,ban taba yi masa tayi ba,yau dai bari Na gwada ko zaici,
A plate ta zuba girki ruwa ruwa malam yana tiriri da kamshi ta je har gabansa ta ajiye masa gashi ko zaka iya ci,dawowa tayi ta zauna,a ransa yace to iya taliyar zata bani jibi fa abubuwa,bai gama tunani ba yaganta taje kasa ta dawo dauke da wani glass jug da karamin glass cup,lemon kwakwa ne ciki ta ajiye masa,ta ebo farfesu nan ma ta ajiye,kankana ma ta zuba masa tasa ta ajiye masa,sannan suka cin nasu da Aabid,kafin kace me Amana da Aabid sun cinye girkin su tas komai coffee kawai basu sha ba,

Alim yana gani yagansu sun fara exercise suna motsa jiki sai tsalle sukeyi,suna faman sheka dariya kamar tababbu,can Aabid ya kwanta yayi flat Amana ta danne masa kafafu yana tasowa a hankali yana komawa,sosai sukeyin gym dinsu,shi Alim mamaki yakeyi har yaushe Aabid dinsa ya koyi irin abubuwan nan?lallai in hakane yarinyar nan ta cika shedaniya,su kuwa kala kala suke gym dinsu idan ta kwanta tayi Sai ayiwa Aabid ma,wurin 30mnt sunayi sannan suka gama,bayan sun huta suka fara shan coffee dinsu,

Alim kuwa sai abincin Amana yakeci yana lumshe ido bai taba cin abinci me dadin Na Amana ba a duniya,saida ya cinye komai ya shanye komai,

Aikinsa yaci gaba da yi sai da ya kwashe 1hr lokacin Amana harta kwashe komai ta gyara wajen,coffee ta hado masa shima a cup ta ajiye masa sannan ta fara koyawa Aabid assignment suna gamawa suka tafi dakinsu tare da cewa Alim Good night Daddy Amana ita a dole Aabid take koyawa tarbiya.

Satin Amana Biyu da fara aiki a gidan Alim yanzu sun shaku da Aabid sosai,shi kanshi Alim ya saba da hayaniyarsu a part dinsa,dama Alim indai ya dauki me kula da Aabid yafi so su dinga yawan zama a part dinsa ta yanda zai dinga ganin meke faruwa da dan nasa,shi yasa baya hana me kula da Aabid zama a part dinsa,ganin yanda yan aikin Alim ma Kansu yan gayu ne yasa Amana ta kara wayewa,amma harkar jagaliyancinta yana nan,bata ragawa kowa sai Alim,uniform dinma sai taga dama take sawa,kayanta take sawa,bata mutunci da matan masu aiki,amma duk ma'aikatan Alim maza natane mutunci sukeyi sosai,tafi yin muamula dasu,mata kuwa tsakaninta dasu sai harara,har girki take shiryawa me dadi ta rabawa mazan,watarana har kaji take soya wa ta basu kowanne me yawa,
Shi yasa idan ka dauke Alim to Amana ce ta biyu da suke girmamawa,

Amana kuma duk kula mazanta ko yatsa bata bari ko da wasa wani ya ce zai rike mata,ita duk harkar iakancin nan bata sanshi ba,ba ruwanta da shi,dan yanzu ko american film da finanan soyayya bata kaunarsu,tafi son film din yaki ko Na sojoji,tafi so taga film din tashin hankali,bata son taga film ana zaman lafiya,tafiso taga Wanda ake kashe kashe ana harbe harbe ana Sara suka,ana harba bum.to fa ka gama birge Amana

Yau Aabid tazo dauka a bangaren Alim sai taga ana film din yaki american film wani Na sojoji me taron mutane,kawai wuta ake ba daga kafa,
Kawai sai ta samu waje ta zauna,Alim kuwa da Aabid suna bedroom har 11pm tayi har Aabid yayi bacci a wajen Alim ba Susan Amana tana Palo tana kallon ba,11-30pm aka gama film din akasa 2 dinsa,duk Amana tana zaune a wajen,har bacci ya saceta ta bingire a wajen,ta wani baje skeet din uniform din nata ya tartare ya dawo Rabin cinyarta Allah yasa tana da wando tight gajere shima Rabin cinya amma da ansha kallo,
Alim yaji karar tv ya fito zai kashe sai yaga Amana ta baje a kasa tana ta bacci skert ya kara tattarewa ya kusa komawa kugu,dankwali ya kwance gashi yayi yalala a kasa,juyi ta karayi tana Sosa cinyarta tare da sa hannu ta zuge zip din skert dinta ta zareshi ta jefar,Alim ya saki baki yana kallon inda zallar baiwar kyau da kyan sura yake,cikin jikinta har yafi fuskarta fari ma kal dashi luwai luwai ko gashin jiki bata dasu,

Can ta kara juyowa ta zuge zip din rigarta ta jefar da ita daga ita sai vest da tight dinta,tana ta baccinta,Alim duk ya diririce,maimakon ya kashe tv sai ya kashe ac ya juya dakinsa kamar munafuki ya kwanta yayi lakwas yana ta nazari,tare da tunanin surar Amana,
Da kyar ya samu yayi bacci,Amana kuwa bata farka ba sai da asuba,ganin inda take yasa ta kwashe kayanta ta arce da gudu dakinta tare da banko kofa tana mamakin yaushe ta cire kayanta,

Sallah tayi ta koma baccinta kasancewar yau Saturday ba kai Aabid schl,ba ita ta farka ba sai 11am,da sauri ta fada kitchen ta hadu da Saude ,Saude tace aikin banza dama zuwa nayi Na fada miki Alhaji ya canja min wajen aiki ya mai dani bangaren gyaran swimming pool yace daga yau ke zaki dinga yi masa abinci,munafuka abinda kike so dama kenan,an manne masa ana tsafi mayya.

Tana gama fadi ta sheka da gudu ta bar kitchen din domin tasan Amana ba mutunci gareta ba,ita Saude dadi taji yanzu ta huta da girke girke,
Amana kuwa ko ajikinta tana hada breakfast ta hada harda Alim,sannan tayi wanka,tasa uniform dinta yasha guga sai kamshi takeyi,har part din ta shirya abinci wannan lokacin sabo da Alim ta shirya masu a dining table.

Tunawa tayi da Aabid ko wanka ba tayi masa ba.dakin Alim ta kwankwasa shuru,kofar ta tura a hankali ta shiga ciki,ba kowa a room din karar ruwa taji alama wanka akeyi,kallonta ta mayar kofar toilet a bude taga kofar tare da hango Alim daure da towel iya kugu yana yiwa Aabid wanka,
Gyaran murya tayi daga can nesa tace Daddyn Aabid zanyiwa Aabid wanka,da sauri Alim ya juyo tare da zubawa Amana ido ba tare da yayi magana ba ya yafitota da hannu wai tazo,ai kuwa da sauri ta shiga kamar bazai yi magana ba sai kuma yace gashi nan Na gama masa wankan kiyi sauran aikinki,kallon Aabid tayi taga kunnensa duk kumfa,dariya ta kyalkyale dashi tare da cewa sorry Baabaaa haka akeyin wankan?kai haka kayiwa kanka,pls ka dinga karfafa jikinka kana koyon abin duniya
Komai ka wani langwabe baka iya ba,harara Alim ya watsa mata tare da ficewa daga toilet din,

Yaga alama yarinyar zata rainashi,bayan ta Shirya Aabid dinning suka fito Alim yaja sit ya zauna,Aabid ma haka serving dinsu tayi komai sannan ta kwashi nata ta koma wajen tv kasa ta zauna tare da kamo sport Chanel tana kallon wrestling.
Alim kuwa ya mai da kai sai shan kunun gyada yakeyi,ga wasu girki da ta hada wajen kala 4 bai ma San sunansu ba, dadi kawai yake kwasa,
5pm Amana ta dau wanka cikin kalar kayanta masu kama da Na wizzy ta fito,da yake Amana me kyauce shigar kyau take mata,a palon kasa ta hanyar kitchen wajen sweeming pool ta iske Alim yana hutawa,yana karanta news paper ga lemo yana korawa,
Tana zuwa tace Daddyn my boy?shuru ba amsa,Master kana yawa a kasar nan,key din mota za a bani pls muje yawo da My Boy,Alim sai yanzu ya tuna Amana ta iya tuka mota,ba tare da yayi magana ba ya cilla mata key abin mamaki yaga ta cafe kamar namiji,tace nagode saura ka bamu kudi,ice cream zamu sha da my Boy,
Baice kala ba ya ebo kudu a aljihu bai San adadinsu ba ya mika mata,tace sai master Allah dai ya saka, tayi waje abinta ta dauki Aabid sannan ta dauki motar da ya bata key wata arniyar mota,ta bata wuta tare da fisgar motar irin Na yan tasha ta kotseta tayi gaba,yan aikin gidan sai kallonta sukeyi da mamaki,matan kuwa kamar su kashe Kansu da alama Amana ta samu fada har motar oga ta fara hawa.



Godiya me tarin yawa gareku fans dina.



AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳


50-55



By
AsmaBaffa





Wurin wani hadadden park Amana ta kai Aabid wuraren wasan yara,sosai Aabid yaji dadi sai murna yakeyi tare da zubawa Anty Amana surutu, hadadden resturant ta kaisu sukayi ciye ciyensu,ko ina Amana ta gifta sai an kalli motar,
Ga wani hadadden tuki da takeyi,shopping mall ta shiga Aabid ta kwasarwa kayan zaki,da wasu kayan sport,schl bag new design,dasu canvas da tarkacen dai makaranta,wasu panties Na maza 3qtrs da riguna duk ta siyawa Aabid, Wasu singlet ta gani na maza latest masu tsadar gaske da boxers,Kudin ta ebo dungurugun ta siyawa Alim boxers guda biyar singlet biyar,ita kuwa kayan make up ta siya da turaruka masu saukin kudi,

Sai takalmi guda biyu da ta siya,da wasu sabuwar pcap guda biyu, ice cream ta jidar musu sannan ta je can wurin da Alim ke siyo nama,wato wajen manager inda ta taba yin aiki,sai mamaki sukeyi yanda suka ga Amana ta kara gogewa ta kara haske da kiba,ga wata shegiyar mota da tazo da ita,sun zata Amana ce tayi kudi,nama ta siya ta wuce gida,8pm suka shigo gidan,ko kayan basu ebo ba ta ja

Please Login or Register in order to submit comment