Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aabid room dinta sallah sukayi da wanka suka canja kaya marasa nauyi,sannan ta riko hannun Aabid suka kwaso kayan gaba daya har part din Alim,lokacin 8:30pm suka sami Alim a Palo yana zaman jiransu da tunanin ina suka tafi haka tun 5pm,

Ganinsu yayi da kaya niki Niki,a gabansa suka ajiye komai,a hankali yace dama kun Dade da dawowa?Aabid yace Daddy wanka mukayi da sallah,

Kayan Amana ta fara budewa ta nunawa Alim kayan Aabid gaskiya shi kanshi sun birgeshi ta iya zaben kaya,jawo wata ledar tayi ta nuna masa nata,sai yayi mamaki nata ko kayan make up din ma ba masu tsada bane,ba wani abu special da ta siyawa kanta,daya ledar kuwa mika wa Alim tayi Master kalli naka,Alim yaso gwasaleta amma yayi tunanin hakan ba dadi ayi ma abin kirki kaki yabawa,karba yayi ya duba,komai size dinsa kuma ta siyi masu tsada,
Gasu best Color nasa komai white,

Thnx ya furta a hankali,ledarta ya kalla yace amma wannan shirme kika kwasowa kanki kika dawo,next time ki kiyaye in ba haka ba baza ki kara zuwa ba,ok master cewar Amana.
Alim yace aransa jibeta kamar ta kirki yanzu kaji ana dambe da ita,kayan zakinsu ta diba tace Aabid baka shan wannan yau sai watarana watarana,idan ana shan zaki hakora mutuwa sukeyi su fara ciwo,mata iyaye a kiyaye za kuga yanzu yaro zaije schl sai a sa masa lemon kwali da biscuit a jaka kayan break,ba kudi bane,ba birgewa bace,ba kuma gata da tarbiya bace,saboda illa zai masa hakoransa su mutu da wuri,ko ya fara ciwon hakori tun yana yaro,gwara ki bashi ashirin ya siyi aya,ko taura,tsamiyar biri etc yanda akeyi da,ko ki dafa musu abinci me kyau yafi wannan kayan zakin.a kiyaye pls.

Kwashe kayan tayi ta boye icecream biyu da nama da drinks kawai ta bari,kitchen ta koma ta dauko su plate etc ta bude ta ebi nata Dana Aabid ta zubawa Alim shima

Alim a ransa yace to yau abincinmu kenan,ci yayi sosai yana kora drink yasha icecream kadan ya mika musu abinsu yana kallonsu suna ta cin nasu suma.

News Alim ke ta kalla Amana ta matsu a canja tashar ball amma shuru gajiya tayi tacewa Aabid tashi muje muyi baccinmu,ko kallonsu Alim baiyi ba har suka sauka suka bacewa ganinsa,
Washe gari Sunday da 9pm Alim ya kira Amana ya mika mata schl Uniform irin Na makarantar su Aabid green and white,ba hijab sai hula da mata ke sawa,Riga da skert,skert din irin da kadan ya wuce gwiwa abinka da lagos,
Kayan har kala biyar,sandal dasu canvas,schl bags,littafai komai ya mika mata,yace kuma Ss1 suka baki ba ss2 ba,
Murna wajen Amana ba a magana hakan ma Na gode master,Allah ya biya bukatunka ya kara buda maka,
Gobe sai kiyi shiri idan kinje office din pc zakije,wani card ya mika mata yace ki bashi wannan cewar Alim,karba Amana tayi tana ta murna.

Washe gari kuwa da sassafe ta shirya ta shirya Aabid cikin uniform ba karamin kyau Amana tayi ba, already ta hada breakfast,cin nasu sukayi suka barwa Alim nasa, brush suka karayi suka gyara sannan suka je wajen Alim dake zaune a palonsa,

Gaisar dashi sukayi sai kallon Amana yakeyi yanda ta hade a uniform,key din mota ya mika mata gashi kin iya driving ai no need driver ya tukaku,ki kiyaye ban son ayi tukin ganganci da Aabid dina.
Murmushi kawai Amana tayi ta rike hannun Aabid suka fito compound,ba motar jiya da ta tuka bace,wata motarce har tafi ta jiya kyau da tsada,
Ma'aikata kamar idonsu zai fado ganin Amana a uniform wato matsayinta har oga ya sata a schl,kuma a schl dinma me tsadar gaske irin ta dansa,ga motoci ko wacce hawa takeyi,mazan gaba daya murna suke taya Amana,matan kuwa bakin ciki kamar su kasheta haka sukaji,

Amana tana kallonsu suna shiga motar tayi wani tuki Na yan tasha ta fice daga gidan,Alim yana kallonta ta window,bai San sanda ya saki murmushi ba,tare da furta yarinyar nan bata ji ko Kadan

Tunda Amana ta cinna hancin motar schl ake ta faman kallonsu,an zata yar gidan wani shegen me kudice tazo da kaninta,kowa driver ke kawo su amma Amana ita ke tukin gasu daga Amana har Aabid masu kyau ne,kalar naira da Hutu,saida takai Aabid har class sannan ta wuce office din PC ta bashi card, ya kaita har ss1A tafiyar da Amana takeyi cike da gadara da takama tana cin magani an dauka Naira ce ta hudata,basu San Amana tun tana kauye haka take ba.
Kafin kace me duk mazan Ajin sun saba da Amana,matan kuwa ko kallonsu bata yi,break aka kada anje restaurant Na schl cin abinci,Amana duk yan aji maza da mata sai da ta raba musu maltina kowa daya daya,nan da nan schl ta dauka wata yar gidan wani kusace Amana

Har class din su Aabid taje ta daukoshi ta bashi abinci da kanta Amana tana mugun kaunar Aabid bata son abinda zai bata masa rai,Aabid kuwa yanzu ya daina tsokana da ciwa mutane mutunci ya nutsu sosai,gashi Aabid yafi ma Alim haske ka rantse baturene,shi yasa yake da farin jini.
Amana har malamai take kaiwa drinks kyauta,kwananta 3 da fara schl amma har ta zama popular, kuma ba laifi tana da kokarinta,amma Amana tafi iya mathts duk wani abu Na calculation to Amana ta sanshi ta iya gifted ce,

Matan schl din tsinewa Amana sukeyi bata da mutunci bata kula kowa sai maza,guda dayace yar ajin su Amana wata Rufaida ita kadai ce suke magana da Amana sabo da Rufaida tana son Amana haka kawai,shi yasa ta nacewa Amana tun bata kulata har ta fara kulata.

Shi kanshi Alim dadi yakeji yanda yaga Amana Na kula da Aabid,ga Aabid sai kiba yakeyi yanzu kuma yayi hankali sosai.dan haka Amana ta kara daraja da kima a idonsa,Amana kuwa a schl kullum sai anyi fada da ita a schl,gashi ba a daukan mataki a kanta sabo da ta siye kowa da kyaututtukanta.

Kamar kullum Amana ta fito da mota ita da Aabid zasu je schl ta ware mota tana fella gudu,wata rantsantsiyar mota ta gani ta parker wata kyakyawar dattijuwa ajin farko ta fito daga bayan motar tana yanga da takama tazo zata tsallaka titi tana ganin mota amma sabo da takama irin ta wannan dattijuwa kawai ta hau titi tana tsaida wata mata,Amana ta Riga ta kawo da mota da kyar ta iya take birki amma duk da haka sai da ta bigi dattijuwar nan kadan a kafa,matar ta fadi wanwar,Amana da sauri ta gangare tazo tana yiwa matar sannu tana bata hakuri,matar ta rigada ta rude sosai bata gane wace kawai murya takeji,
Masifa ta fara yiwa Amana dalla matsa dabba yar talakawa matsiyata,sai faman ashar matar nan takeyi Amana Na bata hakuri amma matar nan cewa take wlh iyayenki ma sai sunyi nadamar haihuwar ki,sai Na batar dasu.

Amana haushi taji kawai ta take motar ta suka tafi schl,ta bar matar nata masifa da zage zage,da kyar driver da wannan kawar tata da take kokarin zuwa wajenta suka sata a mota suka kaita asibiti aka dan duba lfyrta suka dawo gida,matar kawai tunani takeyi a ina zata ga yarin yar nan da ta kadeta taci ubanta har iyayenta,gashi ko ta ganta baza ta gane ta ba tana rude bata ga fuskar yarinyar ba,amma zata gane muryar,motar ta tuna sai taga kamar tasan motar,kamar motar Alim danta,amma me zai kawo wata ta hau kai ba ta Alim bace amma taci alwashin nemo Amana dan ubanta,wannan dattijuwa ba kowa bace face Mum din Alim.
Amana kuwa mamakin irin masifar matar takeyi,bayan sun tashi daga schl saloon ta wuce aka gyara mata gashinta wannan karan kasan gashin tasa aka canjawa kala y koma yellow fari fari,sama kuma baki,kaji turawa an waye a lagos.

Aabid ma anma masa wani kala ya kalli sama ka rantse bature ne,dama Aabid gashin turawa gareshi yellow ba black ba,
Amana har islamiyya Saturday Sunday tana zuwa yanzu,Alim tunda yaga gyaran gashin Amana yake mamakinta kamar wata baturiya wayewar tayi yawa,na Aabid kuwa ai kasa magana ma yayi ya rabu dasu kawai,.
Suna zaune a palon kasa, Baban Amana ya kirata a waya,dagawa tayi da sauri tare da cewa Allah bar mana me gida sai Baba,ya kowa da kowa,alhmdlh cewar Baban Amana sannan yaci gaba bakya nemanmu ko, haba Baba ka daina irin wannan kasan ina ji dai kai fa cewar Amana, Baba a gaishe da Umma kace gobe zan kirata pls,Baba hope dai ka daina abin nan da kakeyi ?Allah Baba shi yasa naki zuwa Na ganku ga kudi ina samu.

Baban Amana yaji Amana tace tayi kudi sai murna ta kamashi bai damu da abinda Amana tace ba kawai ya fara haba yar Amanata yaushe zakizo Na ganki yanzu Allah ya kusa shiryata ai Amanata,zan hadaki da Ummanki,Umman Amana dake gefe taji ance Amana tayi kudi caraf ta kwace tace Amana yata yaushe zan ganki dan Allah kizo mu ganki,ki siyo min doya da manja,ki taho min da garin kwaki dan lagos,ki tahowa da kannenki kwakwar manja,da ashobe Na yarabawa zan dinga zuwa biki,
Baba ne ya kwace wayar daga hannu Umma yana harararta tare da cewa matsa banza kwadayayya,yace Amanata Nima ki siyo min leshi dinkin buba zanyi Na yarabawa maza,ki siyo wa Haladu 3qutr Na maza,ga kannenki su Badariya ko T-shirt ki siyo musu kinji,

Matan gidan da yara duk sun rude kowa yana Anty Amana ki kawo min ayaba da lemo,wasu suce naman kaza,wasu suce yohourt,Badariya yan mata kanwar Amana me ji da kanta da tashen fitsara ita ta fisge wayar daga hannun Baba tace ke Amana ni Apple zaki siyo min kin San ni ba kalar kauye bace,amma Baba yana wani wai ki kawo min T-shirt yo Allah Na tuba T-shirt ko ta su Badaru ai Na sa,kin San Baba dan kauye ne wlh,

Zanci Uwarki Badariya Jakar banza dan Ubanki Babane dan kauyen?mahaifinkine fa Allah ya kamaki shegu marasa tarbiya cewar Amana,Badariya ma ta cikin waya tace Badai ni ba kece shegiya wlh,su iyayen namu da kike tarewa Ubanme suka tsinana ma,komai mu mukewa kanmu,ba makaranta hattana sabulun wanki mu ke siya,sannan kuma muyi musu biyayya,Amana tace ke Iyayenmune fa dole mu duba darajarsu garemu,kuma dole mu bisu ko me sukayi mana,iyaye iyayene wlh amma Badariya kodai kina Jan hayakine?
Tun yaushe kuma Amana ai har wiwi ja nakeyi cewar Badariya,shuru Amana tayi.

Badariya tace ke Amana anfa kama Isa yana police station ya saci akuyar gidan shehu me alewa,Zahrau kuma ta cirewa wani yatsa daya ana ta rigima,Goggo uwar gida ita ta karbi wayar tace Amana ni ayabar da ake soyawa zaki kawo min,Amana tace oh Goggo plantain? Eh yawwa inji goggo.to shike nan sai mun kara magana kitt Amana ta kashe waya tare da dafe kai tana maida numfashi.

Sun dameta da surutu kowa nata shirme,tsaki taja a fili tace gidanmu gidanmu baza su taba canjawa ba,hannu ta daga sama tace ya Rab gamu gareka,
Kyalkyalkyal taji dariyar Alim da Aabid har sun tuntsuro kasa sabo da dariyar kauyancin yan gidan su Amana,juyowa Amana tayi taga yanda Alim yake sheka dariya sosai dimple dinshi sun lotsa yayi mugun kyau,
Sakin baki tayi tana kallonsu,ita ta manta Alim yana wajen gashi wayar a handsfree ta sata,
Tsayawa tayi ta shagala tana ta faman kallon dan bakin Alim da hakoransa yar yar ga dariyar tayi masa mugun kyau,

Saida suka gaji da dariyar suka tsaya Alim yace no wonder kike haka,Ashe a hakan kamar ma kece wayayya nutsatsiya a gidanku,wlh Na kusa zuwa kano kece driver komai za a siya musu kar ki damu,nan ya kara sakin dariya,

Amana takaici ya kamata za a raina mata dangi da iyaye a masifance tace don't go there pls dan billahillazi ka zagi iyayena sai nayi butar malam da kai,kai akan iyayena zan iya karyaka,ka San me zaka fada min bana daukan wulakanci gwara ka koreni,dan kana da kudi muma haka Allah yaso ganinmu ehe,
Aabid ne ya matso kusa da ita zai riketa da sauri ta hankadashi baya ya fadi tim,ta zare masa ido kai ni zaka yiwa dariya a haife Na haifeka takalminta ta cire ta Zane duwawun Aabid dashi,

Sai kuka yakeyi yana bata hakuri,Alim yana gefe yana kallonsu yace kinji kunya your Boy kike duka yau,da sauri ta jefar da takalmin ta rungume Aabid tana lallashi,Mum Alim wacce ke labe jikin kofa tana kallon komai akan idonta,banko kofar dakin tayi da karfin gaske.


AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳



55-60




By
AsmaBaffa





Mum Alim tana muzurai zata fara masifa tare da bin Amana da wani mugun kallon tsana,amma shigar Amana ta bata mamaki,domin Amana bata sa uniform din yan aikin Alim ba,kayan sawarta ne Na swagg a jikinta,Wani tunanin mugunta ne ya darsu a zuciyar Mum Alim nan take ta saki fuska da fara'a tace Alim wannan yarinyar fa? Alim yace Mum me kula da Aabid ce,ya ban ganta da uniform ba? Yanzu ta cire Mum,Aabid kuma me yayi mata take dukansa?tsokanarta yayi Mum,hmm ba a haka yarinya me raino da hakuri akasanshi,
Alim ne ya kyaftawa Amana ido wai ta gaisar da Mum,da sauri Amana tace Mum An yini lfy?hmm haka ake gaisar da manya a garinku?Baki da tarbiya ne? Amana tana zumburo baki tace sorry fa Ina kwana,
Mum ce tace hmm yanzu ai yamma ce,to ina yini?lfy cewar Mum tare da tabe baki,

Amana kuwa sarai ta gane masifaffiyar matar da ta kade ce a titi,itama Mum ta gane Amanace ta kade ta,shi yasa ta kulla mugunta a ranta,
A fili tace ke yarinya ya sunanki,sunana Amana,wanne gari? Kano state a garin wudil.murmushi Mum tayi tace good tare da cewa Alim dama Aabid nazo gani ni Na tafi gida,
Haba Mum ki zauna mana,murmushin mugunta tayi tace abinda nazo wajenka zan nemo Na samu cikin sauki shiken nan bye ta yi waje cike da shirya mugunta,

Mum murna take taga yarinyar da tafi tsana a duniya,ga laifin ta dukar mata jikanta,gata a gidan danta tana cin arzikinsa,lallai Amana zata ci Ubanta.
Ita kuwa Amana bata kawo komai ba a ranta,Hannun Aabid ta kama take ta faman lallashinsa tare da cewa master pls ka tayani lallashi,tabe baki Alim yayi yace kunfi kusa Amana keda ur Boy.
Bacci Aabid yayi a jikin Amana,kallon Alim tayi dake latsa waya tare da cewa Daddyn Alim wannan dama Mum dinka ce? Itace wacce nake fada maka Na kusa bigeta a mota tana ta fada,Kinyi sa'a da ta iya kyaleki haka ki godewa Allah,shuru Amana tayi tana tunani.bayan sati daya Alim ya samu kiran gaggawa daga wajen Mum, 5pm ya dawo gida cikin tsananin kunci da bacin rai ba a San wacce Magana sukayi da Mum dinsa ba

Amana suna palonsa ita da Aabid sunga lallai Alim yana cikin damuwa,shi kanshi Alim so yake ya samu abin nishadi abinda zai sanyaya masa rai,wayar sa ya dauko tare da mikawa Amana wayar take this kira Daddynki kuyi hira da su Ummanki,da sauran yan gidanku,
Amana cike da mamaki ta kalli Alim tace rannan fa munyi waya dasu kuma,Na sani ai ki kirasu kawai kuyi hira ungo karbi cewar Alim,shi Alim so yake yaji shirmen gidan su Amana ya sha dariya ko zai samu saukin zuciyarsa.
Amana kuwa karba tayi amma sai ta kasa amfani da wayar,karba yayi ta karanta masa number Baba yasa tare da dialing,bugu daya Baba ya dauki wayar tare da cewa Alo...Alo ..da sauri Alim ya mikawa Amana wayar ta kara a kunne tare da cewa Hello Baba Amana ce.

Hhhhh Baba ya kyalkyale da dariya tare da cewa 'yata Amanatullah wannan lambar fa ta waye? Kallon Alim tayi ya yayi mata nuni kawai tace ta saurayinta ce ,Baba number Saurayina ce,wata kara Baba ya saki Amanata yanzu a lagos kinyi farin jini kin samu masoyi,Ashe zanga aurenki a duniya,Amanata duk bakin jininki a lagos kika samu miji,murmushi Amana tayi tace Baba sai ma ka ganshi kamar bature,me kudin gaske,yeeeeeeee ahayye yan gidan su Amana suka dauki shewa da guda tuni yan gidan kaf suka yanyame Baba,Umman Amana ce ta fashe da kuka tace Allahu Akabar kabira,yanzu Yar nan duk bakin jininki kinyi saurayi,Ki gaishe mana dashi idan zaki zo ki taho da shi mu ganshi,Goggo ma ta fisge wayar tare da cewa ice ko yana bada kudi me kyauta ne?Amana tace dubu Dari Dari yake rabawa sai yan gida suka dau tafi da ihu,Haladu ne ya matso ya wafce wayar Amana dan ubanki wayar tarho zai siyo min ki fada masa, wlh kika zo babu wayar sai Na karyaki,kaji Haladu kaifa jarabane karma ka dameni cewar Amana,Badariya daga gefe tace kai Amana shegiyar gari ce,yanzu tana can tana Shanawa.
Jamila tace Amana ki kula mazan lagos HIV ce garesu karki bari ya sa miki ita,gwara ta kama Baba,Baba dake gefe samu yayi ya kwadawa Jamila mari tare da fisge wayar ,nan take matan gidan suka fara fada ana zage zagen juna,kafin kace me gidan ya hargitse ana ta cakaki,gajiya Amana tayi ta kashe wayar cike da bacin rai,
Ga kunya ta lullubeta domin Alim yasa wayar a hands free.
Kallonsa Amana tayi taga shi sai dariya da murmushi yakeyi abinsa.tare da fadin why zaki kashewa Baba waya ana hira yaci gaba da murmushinsa.

Kwanaki kadan akayiwa su Amana hutun makaranta Alim yace su shirya zasu je kano wajen danginsa for 1wk zai kai musu Aabid,su. Dameshi da son ganin Aabid,murna wajen Amana ba a magana zata ga danginta,yauce ranar tafiya Alim yace kuma a motocinsa zai tafi bazai bi flight ba,Amana ce me driving Alim da Aabid, escort suna sauran motocin,
Fitowa sukayi Amana cikin shigarta ta yau da kullum,Alim ne ya Ce ina kayan Dana siya miki aka kai dinki gaba daya Riga da skert ne kala 10 harda dogayen riguna readymade wajen 5,takalma da bags,gyale komai dai me tsada akwati guda Alim yayi mata duk wani kayan tsaraba kuma an jibge a mota basu da matsala
In dai baki canja kaya ba wlh baza ki je ba,ko kunya bakyaji yanda kika zo lagos ki koma haka,

Akwatinta dake mota ta zuge ta dauko wani lace me tsadar gaske milk and brown,cikin gidan ta koma ta shirya sosai ta fito a yan mata,ba karamin kyau tayi ba kamar a saceta,takalmi gyale da jaka duk brown,bata iya daura dankwali ba acuci maza kawai tayi ta yafa siririn gyalen a kanta ta fito cike da takun gadara,wai ai Alim ya kusa suma yanda yaga Amana yar india,ta hadu sosai,shi kuwa wani milk wandon jean ne pencil a jikinsa sai wata T-shirt pupple, takalmi ma milk color yasha kyau,Amana fa an waye sosai key ta karba ta shige mazaunin driver Alim Na gaba ya daura kafa daya kan daya can saman gaban mortar, Aabid a bayan mota,Amana a nutse ta fara sarrafa kan mota sannan suka dauke hanya,tafiya Amana take shararawa ta gaske tun Alim yana tunanin zaiji tace ta gaji amma sai yaji shuru kida kawai takesha tana murza kan mota,Aabid yayi bacci wurin kai Uku,Alim ma sai bacci yakeyi,
Sai da sukayi Rabin tafiya har dare ya kusa yi sannan Amana ta kalli Alim tace Master yunwa mukeji ga my Boy ma sai bacci yakeyi aci abinci ayi sallah, ok kawai Alim yace tare da gwadawa Amana garin da zata tsaya restaurant din,

Abinci da sallah sukayi Amana da escort suka take kan mota har dare yayi har wurin 2am Na dare suka zo Kaduna Alim yace suyi bacci a kd gobe su karasa kano saboda kafafunsa har sun kumbura,Amana tace a'a wlh baza mu tsayaba sai munkai kano,ke engine ce wai bakya gajiya ko namiji ba kowa ne zai iya abinda kike ba,
Ae naji amma ba wani kwana a kd sai munje kano.haka suka dinga sharara gudu 4:50am suka isa kano,wajen ciromawa suka tsaya sukayi sallar asuba Amana harda yin brush a gefen titi,haka tacewa sauran ma duk saida kowa yayi brush har Aabid,Alim ma,sannan suka tsaya zasu dan huta,kafin wani lokaci Masu shayi sun fara yi,Amana har teburin me shayi taje ta zauna aka yi mata hadin kauri da indomie da kwai a wajen taci ta koshi ta shanye tea dinta Allah yasa ma mutane basu fara fitowa ba,haka tayiwa Alim da Aabid take away har mota,su kuma sauran escort sukaje duk suka sha suka ci abinda suke so Alim ya biya kudin,shi kam Alim sabo da yunwa shima cinye nasa yayi,Aabid ma Amana tayi feeding dinsa,Amana harda wanke fuska da sabulu tayi fresh,ta shafa powder da lipglow,Alim ya kalleta tare da tabe baki tare da cewa bafa saurayi zakiyi ba,dama bakin jini gareki,kar muje gidanku wlh kice ni saurayinki ne ba ruwana,
Amana murmushi tayi tace za a gani ai.ni nace kace Na fadawa Baba hakan.

Ci gaba sukayi da ta tafiya a nutse har kano cikin Tudun yola GRA,wani tsantsararren gida suka nufa nan take aka wangale musu gate suka kutsa ciki,matan gidan da sauran wasu mutanen yan uwan Abban Alim,duk suna waje sunzo tarbar Alim da Aabid,abinda ya basu mamaki mace ce driver dinsu,

Basu ce komai ba Amana ta fara budewa ta fito tare da gantsarewa tayi mika tana Hamma da salati,duk an zuba mata ido ganin ta fito ba dankwali gyalen na ta ma a hannunta yake,
Zagawa tayi ta dauko Aabid Alim kuwa daya daga cikin guards shi yazo ya bude masa kofa sannan ya fito a gajiye,danginsa yan mata da samari kowa rungumeshi yakeyi ana masa sannu da zuwa,haka manyan iyaye ma,sannan suka koma kan Aabid,gaba daya securities din Alim sun kwashi gaisu wajen dangin Alim sannan aka basu part guda masaukinsu da masu basu abinci etc,Amana kuwa duk cikin manya samari da yan mata ba Wanda ta kalla da idon rahma,babu Wanda ta gaisar kawai gefe taja ta tsaya tana binsu da kallo,har suka gama rungume rungumensu,
Daya kanin Abban Alim ne yace Alim wannan fa?

Sai lokacin Alim ya yafito Amana da hannu ta karaso wajen,tunawa tayi yace in sun hadu da manya ta dinga gaisar dasu da wannan dalilin tace barkanku da gida tayi shuru Abinta,Alim yace Kawu wannan me kula da Aabid ce,madalla cewar Kawu,kakar Alim ce ta jawo Amana zo muje wannan ta wajena ce da kyar Amana ta danyi murmushin yake,ita gidansu can wudil take so ta tafi,
Alim ta kalla kurrr tace Daddy gidanmu zanje ni dai,nan take Alim ya watsa mata hararar data firgitata, a hankali yace haka ake gaishe da manya gidanku,zan fasa barinki kije gida wlh in kikara irin wannan,kuma kibi kaka kuje can ki zama me tarbiya kina koyawa Aabid why ke baza kiyi ba.
Haj Sameera kanwar Abban Alim itama tazo daga Nassarawa G.R.A gidan mijinta sabo da tarbar Alim,tare da iyalanta yan mata su

Please Login or Register in order to submit comment