Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

diri.

Zama Baba ya gyara kusa da Amana,tare da riko hannunta,kwace hannunta Amana tayi tare da cewa Baba ni ka daina rikeni kar nima ka mai dani irin watsatsun matan da kake Harka dasu,haba Amanata nifa Babanki ne duk abinda zanyi bazanyi da yarana ba,to naji Baba mene ne,yawwa Amanata so nake kema na turaki Lagos Neman kudi,kije Cirani kiyi Sana'a ki dinga samomana kudi,watakil ma Allah ya baki miji me kudin gaske a can ko? Dariya Amana tayi cike da jin dadi zata bar jarabar gidansu,tace Allah barmin Baba,wlh sai Baba,shi yasa watarana kake birgeni idan kayi tsiya ta wani wajen sai kayi dadi ta nan,Allah dai ya biya.
Dadi Baba yaji yanda zai dinga tsula tsiyarsa Amana bata gidan bare ta dameshi da wa'azi.

Kallonta yayi yace yawwa ta wajena,kudi zan baki masu yawa Wanda zasu isheki amfani a can Lagos kafin ki fara Sana'a.
Sa'a dai sa'adai Baba cewar Amana tana murmushi.

Nan da sati biyu zaki tafi Amana,akwai abokina zan masa waya shi zai kaiki wajen kwana,amma Baba ba irinka bane ko ?ai shi Amana daban yake yawwa yanzu naji batu Allah kaimu sati biyun cewar Amana, Baba yace kinga duk manyan maza na suna jahohin kudi cirani,amma basa tsinana min komai sai lalacewa da suka kara yi,

Duk cikinsu babu Wanda yaje lagos suna cross river wasu suna Abuja,wasu Enugu,jibi Hamaza na turashi nassarawa lafiya amma jibi da yazo gida doya kawai ya kawo min,sai 3qurtr da ya zo dasu,dariya Amana tayi tace Baba rannan saura kadan na masge Hamza bashi da mutunci har ni zai zaga,shi din banza,Baba ne yayi dan turancinsa daya koya a garin Tafa kusa da Abuja,yace control control Amanata,

Cike da farin ciki Baba ya fito,
Amana shirin Makaranta tayi ta fito tare da yin ball da wani pow da ta gani a kofar dakinsu,tayi gaba zuwa schl.
Sabon Malami ta tarar a jinsu har an shiga,cike da gadara tana budawa ta shiga class din,Malamin ta gani a kan wata kujera da ba Wanda yake hawanta a ajin sai ita,
Wajen malamin ta karasa tare da cewa daga wannan kujerar,mamaki ne ya kama sabon malamin,yace ke dan uwarki ni zaki fadawa haka,sa'an ki ne ni? Kujerar daga gidan ubanka kazo da ita,ko ta ubanka ce cewar Amana,bude baki malam yayi,yan class kowa yayi luf,
Ke wlh sai na koreki daga schl din nan bari na fadawa p.c hannu Amana ta tura a aljihu tace uwar principal zaka fadawa,p.c yaci uwarsa ka fada masa ni Amana na fada uban p.c yaci Uban sa,

Kujerar ta janye malamin na kai ta zame kujerar da karfi ya fadi kasa ta matsa gefe ta zauna tare da harde kafa daya kan daya.malamin mikewa yayi tare da karkade rigarsa ya fice fuuu wajen p.c,
Wajen principal yaje ya fada masa komai,principal dai ya gaji da halin Amana,nan take aka karkada kararrawa aka tara Assembly duka makarantar,

Guri yayi tsit PC yace ina Amana Suleiman Harka?da sauri tace yes gani nan,nasan a kaina akayi taro, ko bakace ba zan fito gani,
Ta fito ta tsaya gaban dandazon mutane hannayenta biyu cikin Aljihu tana kallon kowa dai dai,PC yace kinwa sabon malami rashin tarbiya da cin mutunci gaban aji?yes nayi masa kuma ko gobe ya kara zan sakeyi masa komai naga dama,
PC ne ya daka mata tsawa ke yar matsiyata,yar gidan Sule tantiri me Neman mata bafa tsoronki akeyi ba,wlh yau sai kowa ya zaneki a malaman schl din nan cewar pc,

karya kake Saminu PC,gaka nan bakin kwarto dan iska,wlh akan ka zagi iyayena ko ku dakeni gwara na bar makarantar,babu Wanda ya isa ya taba iyayena ya kwana lfy,makarantar ku din banza shegu gaba dayanku,PC ne ya cakumo Amana da niyar dukanta nan Amana ta riko makwallaton wuyan PC kamar zata zareshi daga wuyan,ba shiri PC ya saketa,amma Amana zagi takeyi iri iri sai da ta gaji ta kada kai ta kalli PC tare da cewar Wanda ya kirkiro boko ma yaci uwatas,uban uban uwar Bokon an daina bokon dan uwarsa.ta kada kai ta bar schl din,tazo bakin gate zata fita ta tsaya ta zubawa me gadi rankwashi kwas,sannan tayi gaba,

bagazan bagazan ta shiga gidansu,ba Wanda ta kula ta cire uniform dinta ta tattarosu waje ta hada da jakar schl din da littafan a tsakar gida ta zuba musu kananzir ta cinna musu wuta,bal bal suna ci har suka kone kurmus,sannan ta kwashe tokar ta watsar a waje tana bin iska tace bye bye Boko ni da zan tafi Cirani Lagos garin turancin da Bokon gaba daya,
Wani Nishadi taji ya mamayeta da ta tuna zata tafi lagos,

Wanka tayi ta sa wani wandon jean kato Tsoho tukuf gwiwar duk ta yage,tasa rigar Atamfa katuwa ta kai cinyarta,p cap ta sa wata kalar tsohuwa tukuf da ita,ta fita,wani Namijine ya ce sai Amana ya garin ne,kallonsa tayi easy T.j easy dai,ya kk?lfy Amana ,kwana 2,wlh tj wai schl ne zasuyi min iya shege tuni na kwancewa PC number 8 dinsa,dariya tj yayi yace bakya farke shege ko ki kiramu muzo da yaranmu a yi maganinsa haba Amana ya kike masu sauki ne,kyalesu nayi kawai sabo da Lagos zan je Baba,
Iyye kice kin kusa fasowa gari gaskiya Dad dinku yana birgeni,murmushi me kyau Amana tayi ina zuwa tj ku zama cikin shiri zan muku hanya kuma kuzo, sai Amana cewar tj ya zaro 200 ya bawa Amana ga wannan kya danyi eh yane,godiya nake tj,haba share kawai aike tamuce,jiyafa Majalisa ta cika ana ta jiranki baki zo,ai ina nan zuwa yau,sai mun ganki.

Rabuwa sukayi da tj,wasu yan matane sukazo wucewa sunci kwalliya yan makarantar k.u.t wudil ne,sai yanga sukeyi suna yiwa Amana kallon banza,bata kula su ba.har wani turanci sukeyi su a dole yan University suna degree,tafiya Amana tayi tana kwobarewa tare da takama tana wani budawa,

Shekewa sukayi da dariya suka tafa,wata a ciki tace oh budurwa har budurwa kyau iya kyau amma jibi ta kashe kanta,
Amana dai bata kulasu ba,sai wata tace inye kaga maza fa,wannan da gani shaye shaye takeyi,ko ciwon hauka ya kamata,
A fusace Amana taci birki tare da juyowa,ganin yanda amana ta canja lokaci daya yasa yan matan nan suka tsorata,zasu yi gudu gashi sun sa takalmi me tsini da damammen skert,

Daya Amana ta cakumo ta hau dukanta sai da ta karya mata hannu daya,sauran su biyun sun fara gudu Amana ta damkosu saida ta sumar dasu sannan tayi gaba abinta ko juyowa batayi ba,

Ran Amana ya baci ta fasa zuwa inda tayi niyya ta koma gida,Ummanta ta gani tana yin Alalar siyarwa ta Rana,can gefe Amarya tana Awarar siyarwa,Goggo shinkafa da miya,Hajiya shinkafa da wake duk na siyarwa.
Ko wacce ranar girkinta ita zata ci da Sulemanu Harka da sana'ar da takeyi.kowacce tana ci da kanta da yaranta,Amana kuwa ummanta bata bata sai dai ta siya,sabo da bata da saurayi.

Wajen Amarya Amana ta nufa tare da mika mata kudi Bani ta Naira Dari nama biyu zakisa min kuma Manya,harara Amarya ta watsa mata,ubanki ne ya bani kudin?ko bashi ya baki ba wlh in bakisa 2meat ba sai na tankadar da tukunyar miyar baki dayanta,ba shiri Amarya ta zuba mata shinkafa da Nama biyu manya harda gyaran guda,karba tayi tare da cewa cire gyaranki,na fada muku ku daina yi min mutunci a kan na siyi abunku,bana son a dinga taimaka min,
Gyaran da Amarya ta sa mata ta cire tace jeki yar Iskar banza.

2weeks ta cika Amana ta gama shirin tafiya Lagos,fitowa tayi sanye da wani 3qtr jean Wanda wandon kaninta ne Yusuf ta yanke da Almakashi ya dawo gajere,wata falkekiyar t-shirt din Hamza ta sa ja ta gama kodewa da jemewa,siririn gyale ta daura a kanta,da wata kwarababbiyar Jakarta karama tasa yan tsummokin kayanta ciki,

Umman Amana sai murna takeyi zasuyi kudi,yarta ta tafi Lagos,yan gidan suma dadi sukeji masifaffiya zata tafi su Shana,Babane ya kalli Amana sai da dariya ta kusa kwace masa irin wankan lagos da tayi,Babane yace Amanata ki canja kaya jibarki kamar inyamura haka zaki je lagos?Yo Baba so kake nayi yawa,Lagos ce fa gwara na saje dasu.

Har tasha Baba ya kaita ya biya mata kudin mota sannan ya bata dubu Hamsin saboda kafin ta fara aiki,sosai Amana ta Adana kudinta,gashi irin katuwar mota ta hau lexs,
Amana anyi kicin kicin cikin Arna,motarsu ta tashi sai washe baki takeyi tana yin guntun turancinta,sun kwashe tafiya me nisa cikin duhun dare,har sun wuce rabi sun kusa zuwa,kitttt driver ya gangare kasa yana ihu yan fashi,ai kuwa sai karar bindiga ce ke tashi,Amana ko a jikinta,nan yan fashi suka fito da kowa waje,motoci suka gani birjik an taresu,ga wasu motoci daban na Alfarma sun kai wajen 10 a Jere,daga gani na wani me kudin ne,Amana motocin me kudin kawai take kallo ta manta a gaban yan fashi take,

Wani daga cikinsu ne ya bugawa Amana tsawa amma ko tsoro baiga taji ba,su Kansu yan fashi dariyar shigar Amana sukeyi,wani azababben gaye me tsananin kyau da kowa yake tunanin Bature,kyau kamar Aljani,da ganin yanda yake tafiya Naira ta ratsashi,sai kallonsa akeyi kowa,yan fashi ne suka nuna shi da bindiga tare da nuna masa wata tsohuwa sukace kayi sex da wannan maza ko yanzu mu aikaka lahira,
Wani takaici da bakin ciki ya mamayeshi,sai hawaye a idon wannan hadadden saurayi suke zuba sharrrrr,tsohuwa da kamar kakarsa ce,gata Arniyace,kuma shi da bai taba zina ba ko da budurwa sai wannan tsohuwar,cikin matsanancin tashin hankali ya riska,tare da dana sanin zuwa Kano a mota,bai bi flight ba,

Amana ita kanta sai taji saurayin ya bata tausayi,taya zata iya cetoshi,sai kallo take kare masa,gashi kamar Aljani sabo da kyau,a ranta tace wannan da gani bature ne Allah sarki ko Hausa ma naga Alama baya ji.

A ranta tace dole na taimaki me kyan nan,Amana ce ta buda tare da kwobarewa da 3qutr tanta,tace easy sir easy dai,wa yace daku ba ku ba,ai wlh ba mazaje sai ku,duk wajen nan Matane,Allah dai ya biya ogoginmu,sai Mazaje,irinku kuna birgeni Allah wlh ba a shiga dawa dan karya, haka Amana taci gaba da yi musu kirari sosai,murmushi ogan yayi na jin dadin yanda Amana take kodasu,

wani yace Yan mata ina kudi,dubu hamsim din da Baba ya bata ta mika musu ai Mazaje ko Baku tambaya ba dole na Baku,ai nakune dama,ko wiwi kwa danyi eh yane,murmushi Oga yayi tare da cewa sai yan mata me kikeso yanzu ayi miki sabo da ke ta wajen mu ce.Amana taga ma kallai yan fashin nan masu saukin kai ne,kuma basu fiye zalinci ba.nan ta fara magana
Allah taimaki Oga waccan me kyan nake so a bani shi ya kaini har lagos a motocinsa,Allah bar mana oga kar ya taba tsohuwar can,kawai ni a barni dashi,yarinya mun baki shi,kema kina son ki dan dandanashi ko,ai Oganmu tunda na ganshi nake kwadayinsa a dan bani shi nayi masa Eh yane ka gane,

Oganne ya dakawa handsome tsawa kai mike tsaye, Allah ya taimakeka ka godewa wannan yarinyar,ka kuma tabbatar ka kaita inda take so.shi kam wannan me kyau ya cika da mamakin wannan yarinya marar tarbiyya me 3qtr.abin ya bashi matukar mamaki,lallai tafiya mabudin Ilmi ce.

Sauran mutane kowa kallon Amana yake har Wanda basa jin Hausa ma.


AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳


10-15


by
AsmaBaffa




Wannan saurayi tunda Amana ta fara magana yake kallonta yanda take acting kamar a film,gashi a kankanin time ta canja musu ra'ayi,wani farin ciki ne ya mamayeshi,yarinyar nan ta taimakeshi a rayuwa babu abinda zai mata sai addua,
Kudinta ogan yan fashin ya mika mata karbi yan mata kuje,haba Oga ai nakune idan na karba nayi fariya,nifa sabo daku na taho dasu,an gaisheki yan mata kuje abinku,daya ne a ciki ya bugawa handsome tsawa maza kuje a kaita inda take so,Amana ce tace wa me kyau hey guy basu rabonsu su samu suma,nan take kuwa ya rubuta musu check na 5 hundred thousand,sukace tayi kadan ya kara musu 1million,sukace tayi kadan,Amana ce tayi magana ai sai Oga ayi masa afwa haka,angama yar Oga kuje kawai cewar wani daga cikin yan fashin,

Wannan jerin motocin suka nufa da handsome da Amana wata dalleliya da tafi ko wacce kyau a tsakiya ita wani guard ya budewa Amana ta shiga,saurayin bai so kazama ta shigar masa mota ba amma ganin Yan fashin zasu iya canja ra'ayi yasa yayi shuru ya shiga shima,su biyu a bayan motar,shi da Amana,kana yawa master wlh kayi sauri ka bawa guards dinka dama suja motocin muyi gaba,zasu iya canja mind yan fashi basu da tabbas,ya kana abu kamar baka son lafiyarka Baba cewar Amana,harara ya watsa mata,easy man ya kake yawane eh,sabo da kai fa na taimakawa wlh ganin za a hadaka da tsohuwa,nasan duk da Allah bazai kama ka da laifi ba amma tsohuwa tukuf haka,gata Christian,
Harara ya kuma watsawa Amana,ka Adana Harararka malam kar nayi fushi wlh zan iya ma dukan tsiya na jefarka a hanya,banda mutunci,dankwalin kanta ta cire ta zaro pcap dinta tsohuwa ta saka,
Kamar Handsome yayi dariya ya maze,aswakinta ta dakko a jaka sabo ta fara dirzar bakinta,yayinda motocin suka dau hanyar lagos gaba daya guda 10 a Jere suke tafiya,sai satar kallon Amana yakeyi yanda take dirzar hakoranta da aswaki,sanda ta zaro harshenta ta fara yi har can ciki har kakarin Amai takeyi,ita kadai nan ma yaso yin dariya,

Amana dai akwai tsafta sai dai kayan jikinta sun ji jiki da yawa,sai da ta kusa kwashe 1hr tana aswaki,sannan ta gama,tace Baaba dan miko min ruwa kuma ka sauke glass,ko kulata baiyi ba,turancinta tayi am talking to u Mr Man,guard dinsa dake gaban motane ya mika mata ruwan roba, tare da sauke mata Glass,ta kuskure bakinta tare da shan ruwan ta jefar da robar cike da takama,
Mudubi ta dakko karami ta dinga duba hakoran nata sai da ta gama tace perfect,itafa turancin lagos ta fara tun yanzu,kasa kasa me kyau yake kallonta,sanyin ac ne ya fara gigitata, Jakarta ta duba ta dakko wani dan towel light blue sabone Baba ya siya mata shi,har turare ta fesa masa na tafiya lagos,
Ware towel din tayi tare da rufe jikinta da kafafunta da sanyi ya ratsasu,kamshi kawai me kyau yaji,ya dan bigeshi ba laifi kuma turaren da dadin kamshi,minti 2 ta fara bacci baji ba gani,a nutse takeyin baccinta,

Magazine yake dubawa sanye da wani glass fari kal siriri a fuskarsa ko kallon Amana bai kara yi ba,yana duba jaridarsa yana kora ruwan juice,tafiya sukeyi tare da sheka gudu,Driver me kyau ne ya kauce hanya tare da kasa control din motar,nan suka kafa tangal tangal a titi,kafin kace me ya daki motar gabansa ta baya ma ta dakeshi,Allah yasa duk motocin tawagar me kyau ne,nan take Amana ta farka firgigit,amma ko a jikinta bare ta razana,me kyau ya gama firgita amma yaga Amana tsaki taja tare da cewa kai malam parker mortar nan ka bani tukin,ba shiri driver ya gangare kasa suma sauran motocin haka sukayi,saida suka duba lafiyar motocin me kyau sannan driver cike da girmamawa yace Sir a bata key din,

Me kyau kuwa dan ya kure Amana yace a bata ta tukashi,yasan bata iya mota ba,inda take talaka haka ina suka ga motar da zata koyi mota,da gani ma bata da iyaye karuwan tasha ce,
Karbar key tayi tare da fita da karfi ta zauna a mazaunin Driver tacewa driver koma wata motar kar hanjinka yayo waje bana saurarawa a hanya nikam,ai kuwa a cikin motocin ya shiga daya,guard daya dake gaba ya gama tsurewa karfa yarinya bata iya mota ba ta kashesu a hanya.

Key Amana tayiwa motar tare da bata wuta sosai,har wani jiny jiny tayi sannan ta take motar tare da hawa titi,ta fara tafiya a nutse da mitar a cikin nutsuwa na gaba tayiwa Alama su tsaya a baya itace a gaba coz gudu zata sharara,
Ai kuwa ta fara tuki gashi gudu take tsulawa me uban yawa sosai tare da over taking da takewa motoci,amma kai baka is a kace gudu takeyi,irin tuki ne na kwararru,manyan drivers ba kowa ya iya irin tukin Amana ba sai babban kwaro,kamar ka hau jirgi ba wani gargada a titi haka take tuki suuuuuuuuu kawai kake ji,haka takeyin tukin,kafin kace me tayiwa sauran motocin tazara sosai basa hango motarsa duk da suma gudun sukeyi kamar zasu tashi sama,
Amana wucewa takeyi yuuuut yuuut,vol ta karo na kida ta cika motar har stiyari take duka idan kida yayi dadi,kadan Kadan take kallon me kyau ta mudubi,

Ga shegiyar pcap dinta kamar zata rufe mata ido,kara kallon mudubi tayi ai kuwa carab suka hada ido da me kyau,Wanda yake cike da mamakin wannan Aljanar yarinya kamar namiji har ma tafi mazan,
A cikin motocin tayiwa daya Alama da ta shiga gabansu ta nuna mata hanya,saboda sun kusa shiga garin Lagos,me kyau ya gama cika da mamakin Amana,suna shiga lagos Amana ta ciro wata yar wayarta Nokia 1110 da Baba ya siya mata second sabo da kira,number abokin Baba ta kira bugu daya ya dauka ta sanar masa ta iso,
Yace to ki shiga taxi kice ta kaiki mytwelve,parker motar tayi tacewa me kyau na kawoka iya nan zan wuce ni ka gane?
Wani driver ne ya karbi tukin,shi kuma me kyau Wanda tunda suka hadu sai yanzu ya kara kare mata kallon ba tare da yayi magana ba ya Mika bundles na 1k guda biyu

Ganin bata da kudi yasa tace sabo da bani da kudi zan karba amma ka kiyaye ko dan gaba bana son taimako,bana son a dinga taimakamin ni ka gane ko,harda zare masa ido,kai man ko kurmane?idan baka jin Hausa ka fada min na iya English dina,har ta gama surutunta bai yi magana ba,kawai da hannu yayiwa driver alama dasu tafi,kudinta ta boye a jaka zata tafi ta hango ana fada a gefen titi,da Sauri ta karasa wajen su,Wanda suke fadan kawai Amana ta fesawa ko wanne cikinsu mari daya tace Wanda yaji zafi ya rama dan Ubansa,
Ai kuwa yarabawa bata sani ba duk basa jin Hausa nan take suka rufeta da duka,sai da sukayiwa Amana jina jina,da kyar wasu suka taimaka mata suka janyeta gefe,amma saboda da taurin rai irin na Amana ko hawaye batayi ba,Jakarta ta duba ta tare da zaro yar kudigar wayarta ta kira wayar abokin Baba tare da fada masa inda take yazo ya dauketa wai an mata duka.

Masifa ya farayi tare da cewar bazai zo ba idan bazaki hau taxi ba ki shekara a wajen,nan lagos ce fa ditt ya kashe wayarsa,ba shiri ta mike da kyar ta fada taxi tare da fada masa unguwar da mutumin yace mata.
Har mytwelve ya kai Amana basu san Layin ba sai da ta kara kiran wayar sa sannan ya ce Aisha 12 street,sai da suka isa can sannan ta biya driver kudinsa ta dauki jakarta da kyar.
A bakin wani shago taga tsohon mutumin abokin Babanta,
Har gidan da yake ya kaita amma da alama gidan karuwai ne saboda ko ina dakuna ne gashi duk mata arna da musulmai,

A tsakar gidan yace ke yan mata lagos ba a aikin banza kawo kudin dakinki,murmushi Amana tayi tare da yin wani yar jijjiga tana doro,ta zura hannaye a Aljihu tace Tsoho kenan da Alama baka sanni ba,amma ni da ka ganni bana Neman sauki da rangwame a wajen mutum,sannan bana son a dinga taimakamin,da kudina nake harkata,ka Bini a hankali ka gane ko,tsohon bariki na fika iya shege,mamaki ne ya kama dattijon nan dan ko a karuwai bai taba saukar irin Amana ba,

Kaga tsohon banza yi min kudin dakina naji,dubu Dari a shekara kudin dakinki,dattijon banza harda dariyar mugunta irin ya San Amana bata da kudi,nan take yaga ta karkace ta Ciro bundle daya na 1k sababbi kar kar ta mika masa,tace oya karba iya kudina iya shagalina,
Na biya na shekara guda kar kuma ka dawo ka takura min zan iya ballaka a gidan nan.

Key din dakinta ya bata ta shiga harda toilet,ko ciwon raunin da yarabawa suka ji mata bata ji,wanka tayi a toilet din room dinta,ta sa wata rigar atamfa da wani falkeken jean blue,ta fito har wajen tsohon nan,tace Man tashi maza ka rakani kasuwa,yanda yaga Amana a dire gata komai da jikinta takeyi ba wani lako lako,tsorata yayi ya sata a gaba har kasuwa,ta siyo tabarma,da risho da kayan girki,Tsoho yace ke da zaki siyo katifa yan mata,
Tsoho kenan ka gane Neman kudi nazo ba jin dadi ba,shi kuwa Tsoho sai kallon Amana yake yana lashe baki,a ransa yace dole na dandana wannan yar chamai mai din.

Har tukunya Amana ta siyo guda biyu,komai biyu ko daya take siya har ta gama suka koma gida,yau baza ta fara girki ba,a kasuwar ta samu wata me saida doya da miya,nan ta siya taci a wajen,ta siyawa tsohon ma,harda shan lemon kwalba,
Wani me shayi da kwai ta gani tace ayi min hadin kauri,ta manta yanda zata fada da turanci sai tace thick thick tare da gwadawa da hannu 2 cups harda Tsoho,saida suka koshi sannan ta ga wani bahaushe me gashin kaza taje ta siyo biyu manya ta dauki tata ta bawa tsoho tasa,sannan suka Shiga Taxi har gida,
Tsoho dai sai mamaki yakeyi,tare da jin dadi ya samu budurwa me kudi,zai like mata ta zama kawarsa.

Dakinta ta shirya tsab sannan ta fara zaga gidan sannan ta dan leka waje ta kai 1hr a waje amma kafin kace duk ta fara sabawa da mazan layin nasu,ganin kudin da me kyau ya bata suna da yawa har wasu ta siya abinci suka ci,wasu lemo ta siya musu,duk majalisar data je ko shago sai ta raba musu lemuka sunsha hira,kullum haka takeyi har ta kwashe 2wks a lagos,duk ta saba da mutane amma iya maza,dan bata saurarar mata ita,
Yanzu da kaje Layin kace Amana kowa ya Santa,gata dama da karambani,ko mai ta gani sai ta koya kuma ta iyashi,har yau bata samu aikin yi ba,yayin da kudin me kyau daya bata suka kusa karewa,abin na damunta gashi tsohon nan yaki nemo mata aikin,
Amana tana ganin rayuwa kala kala a lagos gasu da Neman mata kamar yan akuya,ita kanta duk abin ya isheta,ko wanne yace zai kawo mata hari,baren ma tsohon daya bata masauki ya dameta da zuwar mata cikin dare wai sai ta yarda sunyi xxx ita kuma baya tsarinta tana tsoron Allah,

Amana zuwanta lagos ta kara wayewa da gogewa fatarta ta kara haske sosai ta kara yin smooth,ta zubar da kayan da tazo dasu daga kano ta siyi wasu wajen 10 amma fa duk ba skert

Please Login or Register in order to submit comment