Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

4,sai Alhaji Ishaq shima kanin Abban Alim shi tare suke zama da Babarsu wato kakar Alim da yaransa Maza samari manya su 4 mata 2 yara sune suka taru a gidan.
Shuru Amana tayi tabi Kaka suka tafi sashenta Aabid sai kuka yakeyi shi Anty Amana zai bi.

Kaka sai tsokanar Amana takeyi tun Amana bata saki jiki ba har ta saba da kaka, ita kaka dai haka kawai taji tana son Amana,wanka Amana tayi taci abinci ta haura gadon kaka sai bacci,Alhaji Ishaq sai fada yakewa Alim ya wahalar masa da jika tun daga Lagos har kano a mota, ka tabbata sai dai securities su koma da motocin kai da Aabid kubi flight.
Kowanne cikin Wanda sukazo baccin gajiya suke ta kwasa tun safe har 5 sannan suka tashi sukayi wanka da Sallah,Banda Amana domin hutun sallah takeyi,kuma Ita kadaice batayi bacci ba har sukazo kano,Aabid tuni yar Haj Sameera Ikram tayi masa wanka ta shiryashi,Alim ma ya gwangwaje cikin shiga ta alfarma.sunyi sallar isha an hallara ana jiran kaka da Amana amma shuru Alim sai baza ido yakeyi ina sa ran ganin Amana.




AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳



60-65


By
AsmaBaffa






Amana ta fito daga wanka a toilet din Kaka ta gama shafe shafenta sannan ta dauko Riga da wando zata sa abinda harda pcap,Kakace ta karbe kayan tare da cewa haba jikata gidan nan maza ne da yawa samari,bai dace kiyi wannan shigar ba kinji,
Babu kyau,kuma daga yau jikata idan kinga manya ki gaishesu sosai ba irin gaisuwar da kikayi dazu ba kinji,ki rusuna ki gaishesu a ladabce,nan Kaka ta zage ta dinga koyawa Amana abubuwa sosai,
Kuma Amana ta gamsu ta yarda maganar Kaka gaskiyace,ita kuwa Kaka ta tabbatar Amana tana bukatar tarbiya,da alama bata samu kulawar iyaye ba,a hankali Amana tace to Na gode kaka kuma zanyi yanda kikace,ki zama mace ta gaske me aji kinji? nan ma jiki a mace Amana tace to kaka domin tunda take arayuwarta babu Wanda ya taba cewa ta gyara halinta sai kaka,nan taji ta kara kaunar tsohuwar,
To dauko atamfa kisa a kayanki muje cin abinci,ba musu Amana ta dauko wata Riga da skert Na atamfa me kyau da tsada red ta saka ta shafa powder harda jambaki red,ba karamin kyau tayiba kamar yar India ga diri da shape ga fadin hips da tudu sosai,komai cib,
Kaka tace masha'allah,to saura daurin Dan kwali,kaka ban iyaba cewar Amana tare da dakko red gyale ta yana Dan siriri,tasa flat shoe red,suka fito tare da kaka gwanin sha'awa.

Palo suka fito karo Na farko kenan da Amana taji kunyar mutane,kowa ya zubo mata ido,Baren ma Alim da yake kallonta kamar me,karasowa tayi a nutse ta tsuguna har kasa gaban Abba Ishaq da matarsa da Haj Sameera tare da cewa Ina yini Abba,kuna lfy?fuska sake ya amsa mata,haka tayiwa su Sameera ma,mazan samari da suke ta faman binta da kallo tace sannunku Ina yini,suma sun amsa da fara'a,ganin yan matan tayi ai sa'anninta ne koma ta girmesu,ga wani kallo da suke mata Na banza kawai sai ta sharesu ta mike tsaye,daya daga ciki wato Ikram tace mu baza ki gaishe mu ba?

Amana ce ta juyo a fusace tace hey mind ur tongue bana daukan nonsense,ta juya wajen Alim abinta sauran kuwa da mamaki suka bude baki lallai yarinyar nan masifaffiyace daga magana,su kuwa mazan birgesu Amana tayi ma,

Huzaifa dan gidan Abba Ishaq dake wajen yace bakuwace fa maybe ma ta girmeku Ku Baku kulata ba, tazo gidanku sai ita zata gaisheku,Kaka da Abba Ishaq sukace kyaleshu shashashai.
Amana kusa da Alim ta koma ta zauna a hankali tace ina Aabid,A hankali shima yace Aabid yayi fushi da ke,ni baza ki gaisheni ba?

Dariya tayi tace Daddy Kakace ta koya min fa,Kallonta Alim yayi yana jin wani farin ciki da ya rasa Na mene,ga kamshinta da kyan da tayi yana wani fusgarshi,
Alim da Amana hirarsu kawai sukeyi a palon an zuba musu ido kowa da abinda yake sakawa a ransa,

Abinci aka shirya kowa ya hau dining banda Amana da Kaka su basa zama a kujera,suna ci suna hirarsu,Huzaifa ma wajen Amana ya koma ya like musu,sai hira suke sha,Dan danan Amana ta saba da mazan gidan gaba daya banda matan,

Suna gama cin abincin Alim ya cillawa Amana Key din mota muje ki kaini gidan su khaleed Frnd dina ne.cafe key din Amana tayi tace wlh ni bacci nake ji ka nemi wani driver din, tun daga Lagos ko bacci banyi ba har kano kuma kace mu kara fita,

Palon gaba daya aka cika da mamaki mace ta tuko mota tun daga lagos har kano ansha mamaki tare da jinjina mata,Haj Sameera tace ke yan mata ya sunanki ma, sunana Amana, great name,Huzaifa yace lallai sunanki Na daban ne Baby Allah sa ki zama me Amana

Kaka tace ke kyaleshi muje kiyi baccinki,shi kanshi Alim fasa zuwa yayi yaje ya kwanta shi da Aabid,cikin dare Aabid ya dinga tsala ihu shi A kaishi wajen Antynsa,
Daukoshi Alim yayi har part din Kaka ya buga mata kofa ta fito,yace Aabid ke Neman waccen yarinyar,sai kaje ka kai mata tana waccen dakin,nan Kaka ta koma dakinta Alim ya shiga dakin Amana,

Da sauri ya runtse idonsa ganinta sanye da short wando da kadan ya rufe duwawunta,sai wata half vest a jikinta ta tale kafafu tana ta bacci,
da sauri Alim ya daura Aabid a bed din ya fice da sauri tare da rufo dakin.
Da kyar Alim ya iya runtsawa a ranar,washe gari da safe Amana ta hada kayanta Dana kaka ta fito can bayan gidan jikin wani panfo daga ita sai wata doguwar Riga me hannun vest,wankin kayanta dana Kaka take faman yi,

Mutanen gidan sai dadi sukeji tana girmamasu tsohuwa,Aabid yana kusa da ita,Alim yana sama yana kare mata kallo ta window,

Kwanansu Amana uku a kano,Alim yace tashirya zasuje ya kaita gidansu,Ta gama shirinta Na tafiya Garinsu wudil sai murna takeyi,
Motocin Alim gaba daya da escort suka jera zuwa gidan su Amana cikin yan tafiyar harda Huzaifa.

Amana tana ta driving dinta sanye take cikin wani rantsatsen lace Golden Colo tayi matukar kyau,Alim yasha arniyar shadda light blue fitted,Aabid kam English wear ne,Huzaifa ma ya chakare,jerawa sukayi har garin su Amana tun a hanya Alim ya fara sa ido yana dariya kasa kasa,zasu sha kallo yau.
Ana zuwa wata majalisa Amana ta tsaya da motar tare da sauke glass kasa tace hi guys Baaabaa Baabaa kuna sha'aninku,kallonta sukayi sosai da kyar suka iya ganewa Amana ce,Alim Huzaifa sai kallon ikon Allah sukeyi,ganin gungun samari sun yanyame motar ana ta kawowa Amana gaisuwa,haka Amana ta dinga tsayawa majalisa majalisa suna gaisawa,tace sai Na nutsu Baabaa akwai labari fa.

Har kofar gidansu ta tsaya sauran motocinma suka tsaya,Ko wa kallon irin rubewar da gidan yayi sukeyi,su Baban Amana suna waje sun zata shugaban kasane yazo wucewa,shi kanshi Baba kasa gane Amana Yayi su Alim gaba daya fitowa sukayi daga motar,mutane sun yanyamesu ana kallon turawa sunzo,wasu suce turawane zasuyi Titin kwalta,wasu suce ai makaranta zasu Gina,wasu sunce ruwan tuka tuka za ayi ko pampo,

Amana tace Allah taimaki Baba, Baba Amana ce fa,ai Baba kamar ya suma, Da karfi yace Amana yaushe kika zama haka ko takarar Gomnan Lagos kika fito kika ci bamu sani ba,ai Alim da Huzaifa Dariya suka kamayi,can sai ga Haladu da gudu yana haki yana zuwa ya dakumi Amana yace arniyar kasa wlh itace Dan ubanki ina wayata?

Matan gari sai leke sukeyi ta Katanga suna gulma gidan Baki sunyi kudi,Amana ta dawo da arziki harda sojoji masu take musu baya,Amana kafin ta shiga cikin gidan yan gidan kaf maza da mata yara da manya sun fito gaba daya kamar yaki,
Hamza babban yaya yazo wajen Amana yace shegiyar ban biyar Amana ta bashi hannu suka tafa tace How far man,Hamza a Abuja yake Cirani kawai sai ya juya harshe suka fara broken English pigeon shi da Amana,
Huzaifa da Alim dariya kamar su mutu,duk shuru shurun Alim kasa dannewa yayi.

Badariya yar kwalisa ita ta matso tace Banza yar kauye to ki shiga cikin gidan mana,kinzo da mutane kin barsu a waje,wajen Aabid Badariya taje tace kaga Bature amma wannan baya jin hausa,Fatar Aabid ta latsa da Sauri ta kalli Alim tace laushi wlh,dariya Alim yayi tare da cewa Badariya ko?tace laaaa dama kuna jin Hausa?a ina kasanni? Huzaifa ta kalla tace kuzo Na Baku wajen zama Ku kyale shashasha Amana,dariya Huzaifa yayi yace antynki cefa ko? Ae yayata ce amma Allah Amana bata da mutunci kaf garin nan an sani,yanzu ta balla mutum,
Amma fa tafi kowa hankali a gidan har Baba dasu Umma cewar Badariya, dauko mana tabarma mu zauna a waje kinga muna da yawa cewar Huzaifa

Wai wanne ne cikinku saurayin Amana?cewar Badariya,Huzaifa bai San me zai ce ba kawai sai ya nuna Alim yace gashi,harara Alim ya makawa Huzaifa,
Cikin gida Badariya ta koma dakin Babansu ta dauko manyan tabarmi sababbi dal dal guda uku musamman Baba ya siya sabo da bakinsa.

Inuwar mangoro me sanyi dake kofar gidan ta shindidawa Alim da Huzaifa,suka ce ta mayar da sauran saboda guards basa bukata suna can jikin motoci,
Baba ne ya karaso wajen Su Alim a mutunce suka gaisa aka kawo musu ruwa pure water leda uku me sanyi,
Amana kuwa tana cikin gidan ana ta labarin duniya,dan ma Amana bata fiye surutu ba,Badariya duk ta fesa cewar Alim ne saurayin Amana sai kallonsa akeyu.

Suna zaune Amana ta fito tana kuyi hakuri Na barku kuzo muje ciki Ku gaisa dasu Umma,Aabid yana makale jikin Alim suka shiga suka gaisa dasu Umma,Alim a hankali ya cewa Amana wace Ummanki? Nan Amana ta nunana musu Ummanta wata fara kwal kamar kwara,suna kama da Amana,gashi yan gidan gaba daya ba laifi suna da kyau sosai Amana ce ta fisu gaba daya,
Alim zai tafi matan manya kowacce dubu hamsim,Umman Amana dubu Dari,Baba ma dubu Dari,sai kayan tsarabarsu yace Na Amana ne ta siyo musu,su doya,manja,dankali,etc harda wayar Haladu,Apple,banana da lemo,su guava, duk abinda suke fada a waya Alim ya siyawa Amana ta basu,gida da makwafta an rude,

Alim sunyi Sallama da Amana cewar jibi za a zo a dauketa zasu koma lagos,Amana tace to ka tafi ni idan nayi 3wks sai Na dawo lagos din,Aabid dinfa? Alim ya furta,baki ta turo gaba to shike nan ka turo jibin a daukeni, Kudi ya bata yace ga salary dinki,

Kin karba tayi to wannan kyautar da kayi a gidanmu ai yafi karfin salary kawai ka barshi,ban son iyayi karba malama kina bata mana lokaci,Karba tayi tare da godiya,baku ci komai ba,tabe baki Alim yayi mungode zamuci a gida, Aabid tayiwa bye bye tare da cewa dama nasan ba ci zakuyi ba Ku yan gayune,Huzaifa yace no ba haka bane Baby Amana, wuce gida tayi aka ci gaba da labarin duniya. Alim sai wurin dare suka koma can gidan su Kaka.

Amana kuwa bata basu labarin halin da ta Shiga a lagos ba,bata fada musu irin rayuwar da tayi a lagos ba,kawai labarin duniya ta basu,haka frnds dinta maza ta ba wasu Dari biyar,wasu 1k,tunda Amana taje take yiwa yan gidansu hudubar Ilmi,cikin kwana daya duk kannenta saida ta sa su a makaranta,
Har alkwari tayi musu indai sunyi karatu to zata sai musu motar hawa,sai murna sukeyi suka sami kwarin gwiwar zuwa Islamiyya da boko,suma yayyen nata sun shiga islamiyyar Matan aure suna jira Amana ta sai musu motoci,mazan kuwa Amana tayi musu alkawarin jari,suma har sun fara nutsuwa,
Iyayensu kuwa tace Makkah zata kaisu suma wannan dalilin yasa ba shiri suka shige islamiyyar matan aure,sunga fa lallai Amana da gaske take,
Baba halinsa yana nan Na banza sai Wanda ya karu a kai,har matan aure bi yakeyi,shi yasa kudin da Alim ya bashi Amana tayi masa wayo ta kwashe kudin ta bar masa iya 20k,sauran kuwa duk ta biya family schl,

Baba yaso yayiwa Amana dukan tsiya kan ta karbi kudinsa amma sai ya tuna alkawarirrikan da tayi masa sai yayi shuru da bakinsa, yaune ranar da Amana zata bar garinsu,kananan kayanta duk ta rabawa su Badariya,su Umma ma sun samu T-shirt dai dai,Aabid ya dami Alim rigimar a kaishi wajen Antynsa ba shiri Alim ya turo driver guda daya da mota da safe da wuri yazo daukan Amana,sai kumburi Amana takeyi sai wajen 5pm sannan ta dauko akwatinta tabi driver suka taho cikin kano city.karfe takwas Na dare suka karaso gidan.
Aabid yana jin sallamar Amana ya fanfaro da gudun tsiya ya dafalfaleta,mutan gidan duk suna Palo banda Alim Wanda sun fita gari da Frnd dinsa khaleed,
Gaishesu Amana tayi ta tafi wajen Kaka can ta ya da zango sai hira sukeyi da Kaka,har tayi wanka Kaka ta kawo mata abinci sukaci tare da Aabid,
Alim kuwa tun safe yake jiran dawowar su Amana amma shuru har khaleed yazo suka fita.Amana har tsarabar Goro ta kawowa Kaka,sai murna Kaka takeyi Goro lafiyayye me yawan gaske,Matar Abba Ishaq kuwa da Haj Sameera kayan miya irinsu su kuka,kubewa bushashiya,gyada danya etc duk Amana ta kawo musu da yawa.




AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳


65-70



By
AsmaBaffa






Tunda Alim ya dawo yaga ba Aabid yasan Amana ta dawo,washe gari da safe ma Amana bata fito ba a dakin Kaka taci abincinta,
Har yamma lis Huzaifa yaje yasa Amana tayi shiri sosai cikin wata arniyar shadda sky blue,suka fito sai kyalli sukeyi,khaleed da Alim suka gani a compound,
Da fara'a tace Daddy barka da yamma,ta kalli khaleed kadan tace ina yini tayi gaba abinta ba tare da ta jira amsarsu ba, Alim a ransa yace lallai ma yarinyar nan,
Khaleed yace wannan kyakyawarfa?yar uwarku ce? A Ina ka zama Daddy dinta?

Tabe baki Alim yayi tare da cewa Nanny din Aabid ce fa,Aabid yana ce min Daddy shine itama take fadamin,lallai ka iya zaben Nanny cewar khaleed,sai wurin 9pm Amana ta shigo ita da Huzaifa,yayi mata siyayya sosai,Alim suka gani shi kadai a Palo,ko me yake jira oho,
Yana ganin Amana ya sauke Ajiyar zuciya me karfi hade da mikewa ya bar palon,washe gari 6am escorts dinsa suka kwashi motoci suka dauki hanyar lagos, da Aabid jirgin karfe 5na yamma suka bi,Amana sai murna akeyi ana zare ido an hau jirgi,

Mintuna kadan suka sauka a Lagos wani Frnd din Alim Kamal yazo ya daukesu a airport,ya kaisu har gidan Alim ya wuce abinsa.
Gidan neat kal kal suka samu ko ina kasancewar yan aiki sunayin gyaransu,
Tunda Amana ta dawo ta shige dakinta suka sha bacci da Aabid washe gari ma haka Alim bai ganinsu Sam,

Kwanansu Uku da dawowa amma Amana bata kara sa wani atamfa ko lace ba damunta sukeyi,kayanta ta koma sawa,yau shirin wanka sukayi Amana sanye da Wando legins tight iya gwiwa da rigar ta tshirt armless irin doguwar nan ta kai Rabin cinyarta
Aabid kuwa dan pant ta sa masa ta jashi sukayi bangaren sweeming pool din gidan,
Alim suka gani zaune a kujera daga shi sai short ko Riga babu,yana karanta jarida yana kora lemo,towel dinsu Amana ta ajiye gefe,da fruits salad da ta hada musu,Aabid ta Goya ta shige cikin ruwan nan ba tare da suncewa Alim ci kanka ba,

Tunanin Alim Amana bata iya ruwa ba kawai sai ya hangota ta Goya Aabid tana iyo a ruwa kamar wata kifi,a ransa yace ita wannan komai ta iya kenan.
Aabid kuwa dariya yake ta bangalawa yau ya shiga ruwa,dama bai taba shiga ba,sun Dade ciki sannan ta fito zasu huta su koma,gaba daya bata sa bra ba rigarta duk ta manne a jikinta.
Alim gaba daya ya rude ya shiga wani yanayi ganinta a haka,kafe kirjinta yayi da kallo,yanda ko ya tayi motsi kadawa sukeyi,ji yake kamar ya cafkosu ya shafa,gasu shape dinsu gwanin birgewa,Amana fruits dinsu suke sha bata San me Alim yakeyi ba,Alim gani yayi Amana zata koma cikin ruwa kallonsa zai kare,kiranta yayi da sauri,
Amana! Wani iri Amana taji a jikinta babu abinda ke birgeta a rayuwarta irin taji Alim ya kira sunanta,sai taji kamar ta shide,cikin tafiyarta ta gadara da zafin nama ta karasa wajen Alim,shi kuwa Alim kallonsa yake ta sha yanda Na shanunta suke juyawa,

Ya kwashi wajen 10mnt baice mata komai ba,ita kuwa sabo da tasan yanayinsa baya magana a kan lokaci sai bata damu ba ta tsaya tana juransa,shi kuwa ba haka bane kallon kirjinta yakeyi a hankali saboda ya daga jarida nufinsa ita yake karantawa Ashe wayo ya hada kawai idonsa Na kan Amana ta saman jaridar.

Mikewa yayi daf da Amana kamar zai shige jikinta a zuwan shi tafiya zaiyi,Amana ganin kyaykyawar surar Alim yana kyalli yasa ta jin wani dummmmmm a kwakwalwarta,ta rasa gane mene domin bata taba jin hakan ba,

Alim yana sani yayi luuuu ya tafi zai fadi tare da dafe kansa yace ouch...da sauri Amana ta taroshi ya fado jikinta ragwajaf tare da sakar mata nauyinsa ai kuwa yafi karfin Amana nan take suka fada cikin ruwan gaba daya,
Sai lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa sai ya fara tamke fuska yana cin magani tare da tsaki ya fice daga pool din,yana ta faman masifa,aikin banza daga kiranki sai ki jefani cikin ruwa,komai bakyayi A hankali kamar wata sakarai yaja tsaki tare da barin wajen cike da kunya.

Amana kuwa bata kawo komai ba tace masifaffan mutum,shuru shuru dashi sai masifa,Aabid ne yace Antyna Daddy baya masifa fa,to naji muje muyi wankanmu,komawa ruwan sukayi suna ta wankansu har suka gama,
Yau sati biyu kenan hutun makarantar su Amana ya kare sun koma schl,Mum Alim tun safe take damun Alim kan yazo fa akan maganarsu,haka ya hakura yaje har dakin Abbansa,

Bayan sun gaisa Abba yace Alim wata magana nake jin cewar wai ka tsayar da mata za a je Neman aure,kallon Mum Alim yayi,Mum kuwa ta daka masa harara ba shiri yace yeah Abba,amma a kano take shike nan Alim ka turo min driver ka jibi za muje nemo maka aurenta,cike da takaici Alim yace to Abba ya musu sallama ya bar gidan kamar ya kashe kansa tsabar bakin ciki,

Kwana tsakani Abba ya shirya tare da Amininsa da Mum Alim,sai driver dan rakiya,flight suka bi har kano suka dauki Alhaji Ishaq sukaje can garin da za a nemowa Alim aure,

Suka nemowa Alim aure kuma an basu yarinya tare da sa ranar aure nan da 1mnth domin Mum tace bata so a day lokaci sabo da shedan,
Mum Alim koda sukaje Neman auren mutuniyar kirki ta zama tare da kaunar talaka haka ta nuna,gidan Amarya sai yabon halinta sukeyi,basu San Mum tana da dalilinta,akwai abinda ta boye a kasa.su kuwa Allah sarki sai murna sukeyi gida ya rude sabo da jin dadi zasu shiga gidan Naira.

Bayan sun dawo Abba ya sanarwa Alim komai tare da yabon dangin Amarya,Abba yace son sai watarana kafin biki ka kawo min sirikata Na ganta,domin Mum dinka tace kana sonta sosai,Asiya kanwarku ma naji yanda take yabon halinta,haka Nura da Auta Sadiq ma naji sunce sun Santa yarinyar kirkice.
Alim dai cike da mamakin makircin uwarsu yace Hmm kawai,shi kuwa Abba ya zata kunya Ce kawai.

Amana kuwa harkar gabanta takeyi kawai daga schl sai karatu,zama da kawarta Rufaida yar gayu yasa Amana ta fara dan canja halinta ba laifi,
Mum tace baza ayi biki ba kawai aure za a daura amarya ta tare,

Biki ya matso Amana a bakin yan aiki taji ogafa zaiyi aure, wannan matar yana sonta ba zabin Mum dinsa bace,nan Amana taji tarihin Alim har auri saki da Mum ke sashi yi saboda bata so wata ta ci arzikinsa sai ita uwarsa da ta haifi abinta,
Ko yan uwansa Na jini bata kauna Alim ya musu kyauta sai ta dinga nuna kyashi da bakin ciki,

Bare Abbansa bata so ko hira taga sunayi da Alim saboda kar ya bashi wani abu,Abban Alim kuwa shima me arzikine, hassada ce tayiwa Mum yawa,shi yasa bata taba yarda Alim ya auri wacce yake so,shi yasa duk wacce tasan Alim bazai taba kauna ba har a bada to ita zata nemo ta aura masa.

Amana tana gama jin labarin taji wani bakin ciki da bata San Na mene ba ya taru ya cushe mata a zuciya,hankalinta ya tashi ta nemi farin cikinta ta rasa,a ranta saida ta tsinewa Mum Alim yafi dubu kan wanne dalili zatayiwa Daddy aure, bakin cikin Amana kenan.

Amana tana shiga Palo bata kula da Alim ba ta jefar da Jakarta a palon ta cire takalminta ta watsar cike da tsananin bakin ciki ta ja tsaki,nan ta fara zagaya Palon,da karfi tace a'a...wai mene haka ne eh....ina ruwana ma aikin banza aikin wofi,
Minti kadan ta buga kafafu tare da miko hannu kamar damisa zata damki nama tace saina ehhhhhhhhhh......shake tsohuwar nan.....can wani lokaci ta dakko ruwa ta kafa kai kwat...kwat...ta shanye tare da jefar da robar tace sai naci uwar tsohuwa wlh...tambadaddiya.....kodaddiyya.....sokayayya....me suffar hanjin ligidi.... Tayi dakinta da sauri ta fada bed dinta,Aabid ne ya shigo daga baya shi kam yaga Daddynsa wajensa ya nufa.

Ihun Amana su Alim sukaji sai karaji takeyi a dakinta,da sauri Alim ya bude dakin nata a kan bed ya ganta kawai wutsil wutsil takeyi tana karajinta tare da tsine tsine,Allah ya baki lfy cewar Alim yayi waje abinsa.Aabid yana a kafadarsa,
Ranar Amana da kyar ta iya yin wanka haka ta kwana ba bacci,sai asuba ta samu bacci,Aabid sai driver ne ya kaishi schl,amma Amana tace Sam ita bata da lfy.haka Amana ta yini da zazzabi,ga period tanayi,harda su amai tsabar bacin ran za a yiwa Daddynsu aure.

Alim kuwa tun yana damuwa har ma ya gaji gudun kar ciwo ya shigeshi a banza,frnds dinsa ma sun jajanta masa, sun tabbatar auren babu inda zaije.
Yau daurin aure saura 1wk Amana duk ta rame ita kanta bata San dalili ba,Alim kuwa ko a kwalar rigarsa indai irin wannan aure ne ya rigada ya saba dashi.
Mum kuwa burinta ya kusa cika,

Kwanaki fa suna ta ja gobe Saturday gobe daurin Auren Alim,dole ya gayyaci abokansa sosai,Amana kuwa tana Palo tana jira taga wankan auren Alim,itama

Please Login or Register in order to submit comment