Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu kama ba,

Alim ne ya shigo palon da Sallama yagansu suna ta ciye ciye ana ta labari,
Dan Zama yayi suka gaisa yana musu sannu da zuwa Amma idonsa yana ga Amana yana aika mata da kallo tare da harara wai bata je ta tarbeshi ba,
Kunya taji tare da dauke kai,ina zuwa Alim ya shige bedroom, Amana tana so taje wajensa tana dan Jin kunya wai zata yi musu wayo tace Asiya Amarya bari na dauko miki wani abu ko zai miki,zuruf ta shige dakin Alim,
Tana tafiya suka kama dariya wannan yarinyar da abin dariya take cewar matar Nura,Nura yace ina ruwanki yan sa Ido,

Alim daga shi sai towel iya kugu zai shiga wanka,yaji Amana ta rungumeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa,
Sai yanzu zaki wani zo,murmushi tayi yi hakuri kunya nakeji ta ya Nura,
To ya Nura tsaya ki gani shi a gabanki zaiyi abinda yaga dama da matarsa.

Muje kayi wankan kawai,suna shiga toilet yace sai ta shigo sunyi kuma ba iya wanka zaiyi ba ta gane nufinshi kin yarda tayi tace ni bana son kara wanka ga baki munyi kuma dadewa zamuyi fa,
Jeki to karki Dameni da Surutu kuma karki kara cemin kina son Aabid tafi, Amana magana tayi bata fito ba kamar kunkuni,Alim yace me kikace,Amana tace a'a cewa fa nayi Allah zai kawo ai,oh Allah ya taimakeki kuma idan banyi ba baza ki samu Aabid ba yarinya,
Dole ma kayi min na samu,toilet Alim ya shiga,Amana ta bishi ciki,to mene zaki kalle min tsaraici kuma? Dariya tayi ba kallonka zanyi ba kayi wankanka,a toilet din ta nemi waje gefen Bowl din wankan tayi zaman ta,Alim ya fara wankansa,tace haka akeyin wankan,shuru ya mata,can baka sabulunba fa,
Sabulun ya mika mata ungo karasa,hannu tasa zata karba ya jawota tana ihu ya tsundumata ciki tare da danna shower ruwa shaaa ya jikata gaba daya,

Ruwan na zubowa ya tubeta gaba daya ya sake mata sabon wanka,sai kukan shagwaba takeyi masa,
Sai da ya gama murzata son ransa da kyar ya hakura towel daya ya daura musu tana cikin jikinsa kamar masu koyon tafiya suka fito ko mai bata shafa ba tasa doguwar Riga brown color ta dan gyara fuskarta sosai sannan ta zurma hijab har kasa wai kar su Asiya su gane anyi wani abu gashi har ta sake wanka ta canja kaya.tana fitowa suna kallonta suka San anyi wani abu domin rigarta ana hangowa ba kayan dazu bane,

Auta a ransa yace kut Amma ya Alim jaraba ne daga dawowa shi yasa yake ta kallonta,muma dai mayi auren nan,Alim da 3qtr da T-shirt ya fito suka fara hira,Amana ta kawo masa abincinsa ta jera a gabansa ta cika gabansa tab,har yafi na bakin domin na Alim na musamman,abin mamaki hattana kalar spoon din Alim daban ne ba irin na kowa bane,
Alim ne ya kifta Ido Amana ta kau da kai,ya kara kashe mata Ido ta juya gefen Asiya,
Nufin Alim wai tazo ta bashi yaci abinci da kanta,ita kuma tayi kamar bata gani ba,

Su Nura suna kallon abinda Alim keyi,magrib na gabatowa suka ce zasu tafi har mota suka rakasu,Auta da Asiya motarsu daya,Nura da matarsa ma haka,
Suna tafiya a hanya Alim ya dagata sama tare da sabata a kafada har cikin Palo,

Amana ta fara waec a cikin jerin motocin Alim ake kaita tare da securities sai ta gama suna jiranta a dawo da ita gida,
Har ta gama waec suka fara Neco,
Tana gamawa ta shirya cikin tsadajjiyar motarta taje har kofar gidan Dan Uzuri,
Mutane da wanda suka Santa sun gaisa suna mamakin canjawarta domin basu gane Amana bace sam, saboda da kyau da haduwa da tayi ana kallonta an San Naira ta ratsata,
Tambaya tayi ko dan Uzuri na nan,suka ce ai Dan Uzuri ya Dade a prison da kyar aka sakeshi amma yanzu ya koma kauyensu da rayuwa,gida ta koma tana shiga Alim ta hango a Palo yana kallon News tana zuwa ta kwantar da kanta a cinyarsa tare da mikar da kafafunta a doguwar kujera yana mata sannu da gajiya har bacci ya dauketa.

Bikin Asiya yana ta gabatowa kuma Mum zata zo bikin Yarta sannan gidan Alim zata sauka,Alim ya kira Mum suna hira,Mum tace bawa matarka waya mu gaisa,Alim dai a tsorace ya mikawa Amana,Amana cike da ladabi kamar tana gabanta ta gaisheta,Mum cike da fara'a suka gaisa harda Jan Amana da hira.

Alhaji Shehu da sauran kannen Sulemanu ne suka yo waya zasuzo gidan Amana suga yarsu.
Murna wajen Amana ba a magana suma yanzu danginsu suna kulasu.Alim ta sanarwa shima yaji dadi ko ba komai dangin matarsa ne.





Korafi ya karbu Maman Minat,godiya da tunatarwa.





AsmaBaffa.
✳CIRANIN AMANA✳



195-200



Official




By
AsmaBaffa







Kwana biyu tsakani su Baba Shehu da Ahj Sani tare da kannen Sulemanu,sai su Anty Maimuna,Anty Sajida,Maryam da Sauran yayyen Su Amana mata,duk suka sauka a Lagos,kwanansu daya suka tafi tare da sha tara ta arzikin da me gidan na Amana ya musu,su Hamza kuwa da su Umman Amana sai bikin Asiya zasu tattaro suzo suma Asha biki dasu.

Alim ne ya dawo daga Office 5pm,Amana ta fito cikin hadewarta data saba me rikita Alim,rungume abinta tayi kam tare da masa sannu da zuwa tana sakin murmushin dake kara mata kyau,wani Apple Juice da ta hada da kanta ta dakko me zanyi a glass cup ta bawa Alim dinta yasha yana santi,

kashe murya tayi tare da kara kasa da ita can kasan makoshi tace muje ayi wanka ko? shagwaba ya fara mata ni nayi wanka da kaina fa? Sai kace marar gata,ni dai ki min da kanki wani wanka na iya me kyau,

Dariya suka saki gaba daya Amana tana dariya ta dan tureshi shagwaba kullum ko? Alim yaci gaba da shagwabarsa pls......mana ni ban iya wanka ba,yanda yake Abin Amana sai faman dariya take tace muje to,da sauri yace ok ko kefa,
Tsayawa yayi kamar jariri ta cire masa kaya,ta kaishi toilet ta fara masa wanka,aka zo wanke wuya Alim ma bai son a taba masa wuya sai ya dinga dariya kamar yaro, Amana tasan halinsa tace daga wuyan na wanke, Yana dagawa tasa sabulu ai kuwa dama ta sani sai ya kyalkyale da dariya tare da makale wuyansa,

Halinka kenan kara dagawa yayi ya kyalkyale da dariya tun kafin ta taba wuyan yake makale abinsa,yana sorry to na tsaya,da kyar ya bari aka gama wankan.

Tazo ta fara shafa masa mai,Amana ta dan dakeshi a kafada cikin wasa,tsaya mana joo....aka zo sa kaya yace shi Baza a sa masa kaya yau ba sai gobe,to da me zaka zauna? Ki barni da towel dina nayi sallah fa saura magrib da Isha idan zanyi nasa kayan,
Kyaleshi tayi suka koma dining suna cin abinci,brush ta masa itama haka,

Chewgum ya zaro zai tauna a baki,Amana tace ina nawa?ka sanmin kaji ta fada kamar zata yi kuka,a kan Mirror na gani na dauko,to nawa ne fa tun yaushe nake ce ma ka siyo min ko sweet duk sun kare sai kace to ka manta,
Alim sai da ya gama taunewa da tsotse zakin ya dora chewgum din a harshensa tare da miko mata harshen ungo to karbi abinki,
Miko bakin tayi kuwa kamar tsintsaye ta karbo ta kama ci ta kara hade bakinsu ta maida masa chewgum dinsa, murmushi tayi tace yawwa yi min taunar yan gayu,Alim kuwa ya gyara ya fara taunawa da kyar yana yanga harda yin kwai kalar na yan gayu kamar wata mace,Amana kuwa tana dariya tace to ayi na yan kauye Alim ya koma cakal cakal yana tauna chewgum,Amana tace na karuwai fa? Ya koma kas kas kas yana taunawa,Amana tace wink me,ya juyo side to side din idonsa yana kashe daya tare da mintsinawa,
Yanda yake yi abin dariya Amana sai dariya takeyi.

Magrib nayi ya zura jallabiya sukayi Sallah,suna idarwa ya zare kayan ya daura towel dinsa,Amana tace ikon Allah muje to muci abinci,nan ma ya kama shagwaba sai da bashi da kanta,dama dazu kasa ci yayi da kansa,suna gamawa

Daukanta yayi har kan Bed ya kwanta a jikinta tare da rada mata wannan ne dalilin zama da towel kinga ba sai na sha wahalar cire kaya ba,

Kissing dinta ya fara hannunta ta dago a hankali tare da sakaloshi ta wuyan Alim suna ta kissing din juna,daga nan ya zare mata kaya ya fara wasa da sassan jikinta sun fita a tunaninsu,wayar Alim ta shiga kara tsayawa yayi da niyyar jawo wayar tasa, Amana ta jawoshi tare da makalkaleshi sannan ta furta wannan lokacinane fa,Alim kuwa yanda tayi maganar shi ya kara rikitashi ya fasa daukan waya,suka ci gaba da farantawa juna rai,
Waya dai tana ta kara basu san ma me takeyi ba sunyi nisa,

Bikin Asiya saura 2 days lokacin Mum tazo,da wuri Alim yasa driver ya daukota,gaskiya ko waye ya kalli Mum sai ya tausaya mata,ta kwanjale dama kuma ba wata kiba ce da ita ba,.
Ta fige sosai,Alim har kwalla ya goge da yaga Mum,Amana ma ta tausaya mata,ta tarbeta cikin mutunci,Mum kuwa anyi laushi kamar yarta haka ta dauki Amana,
Amana tana kusa da ita Mum tana basu hakuri ita da Alim,Amana tace mune zamu baki hakuri Mum munyi miki laifi ni da kanwata ki yafe mana,Mum tace haba a daina tuna baya ai laifina ne ba matsala,Alim dai bai san kan zancen ba, sai abinda Mum ke so Amana take mata,haka su Nura ma duk Kullum sai sunzo gaisheta,k ullum Mum asa albarka take da Kukan rashin Aabid ta sularta,ana haka har aka fara bikin Asiya,
Amana anci kwalliyar dinner party,Alim ya shigo yace ba wani dinner da zakije fa,Amana ta fara kuka taje wajen Mum dake shiri ta fada mata,Mum tace rabu dashi tare zamu tafi daga dinner ma kije can cikin yan mata Asha biki dake idan an gama kya dawo.

Alim yana wajen dinner sai yaga Amana da Mum sunzo,da sauri yaje wajensu yace wa yace kizo so kike Maza suyi ta kallonki jiba da Allah gyalen ma rikeshi kikayi,cike da shagwaba Amana tace kai kuma fa ai kallon matan kakeyi kuma Mum ce tace nazo,Mum tace ke muje ki rabu dashi,haka aka gama Dinner,Amana ta zirare tabi motar su Badriyya suka tafi cikin kawaye can gidan Abban Alim suna ta shagali da yan mata tare da yan Uwa,

Alim ya koma gida ba Amana ba labarinta har 2 na tsakar dare,dakin Mum ya shiga,Mum tana bacci yace Mum wai ina Honey,Mum tace tana jikin bishiya tana sakar zuma.
Babyfa nake nufi Mum tace tana bayan Uwarta,
Alim yace Mum Matata fa nake nufi kin kaita wajen dinner to tana ina,Mum tace ka kiyayeni kai kadai ne me mata wai ka hana yarinya sakewa a cikin kawaye,tana can wajen su Asiya,a ransa yace wai Mum ce zata nuna tafi son Amana a kaina,ikon Allah kenan,watarana me Sonka shine makiyinka,makiyinka ya koma me Sonka.

Alim takaici ya lullubeshi da haushin Amana,fita yayi kawai yawa mota key wurin 2:30 na dare,su Asiya Amarya suna bacci wayarta tayi kara,da kyar ta daga, fada ya fara ki turo min Matata ina waje kice wlh ta fito mu tafi,ta wani kashe waya,

Asiya tace haba yaya da daren nan kuma Mum ce tace ta zauna sai an gama biki,what zan Mareki wlh ki turo min ita yanzu cewar Alim kamar zai tashi sama,

Asiya tace jaraba ta mike ta Isa dakin da Amana suke kwance tare da Sakeena da Badriyya,
Duka ta bugawa Amana a baya tashi ki tafi mijinki yana kofar gida zai tashi gari akan zaki kwana,kin San Bai yarda ba kika zo? Tsakaninmu da gidan naku ai ba nisa gaskiya ya hanani bacci da masifa cewar Asiya Amarya.

Amana da bacci a idonta tace rabu dashi ni Bazan je ba,Sakeena tace Anty ki tashi kawai,Badriyya ma ta mike tace kin san dai mazan nan akwai son kai kar yayi fushi ki tafi, ni da Huzaifa ne da tuni na tafi,
To a tsohon daren nan fadin Amana ....wayar Asiyace ta kara daukan ruri Alim ne again,Amana tace ita kam sai gobe zata koma,
Minti 5 saiga Alim ya shigo har cikin gidan Asiya ya gani ta fito zata koma dakinta yace tana wanne room?tace tana wannan room din,ai kuwa fuu ya bubbuga kofar,Amana ta zata yan biki ne ta bude ya figota waje da karfi,Amana ta zille tana hakki tace sai gobe fa zan dawo,kizo nan nace miki ko,Amana tace naki din,zagayowa yayi ta jikin kujera zai kamata,ta gudu jikin dayar kujerar,ya kara biyota,
Suka fara zagaye kujerun palon,ko wanne dake gidan nan yan biki kasa bacci sukayi suka tashi zaune Sabo da yanda ake ta guje guje da ture ture a palon wasu ma sun zata aljanune suka kara buya a room,

Alim ya kama Amana da kyar duk haki sukeyi,ya safa ta a kafada, kara bubbuga kofar room din da Amana ta fito yayi, Badriyya ta leko tana dariya,yace Sis miko min hand bag dinta da komai da tazo dasu,Ai kuwa Badrriya ta miko masa ya rike gyalen da Hand Bag suka bar gidan yasata a mota har gidansu yana masifa.

Suna zuwa ya kaita har Bedroom sannan yace nayi niyyar kyaleki kije Amma ni zaki raina ki tafi ba tare da Umarnina ba kan Mum tace kije,kin ma rainani ko? Shi yasa naje na dawo dake ta karfi naga kuma ta tsiya,ya karasa yana hucin masifa.

Amana taga ransa ya baci sosai tace to kayi hakuri shike nan ta juya ta kwanta shima haka can dai ya matsa jikinta tare da manneta tsam a jikinsa,Amana tana kwance ta kifa cikinta ta dago gwiwar hannunta tawa Alim elbow daya,da sauri ya matsa tare da rike wajen kirjinsa,harda Elbow ma akan kina Jin haushi na,Amana dai bata ce komai ba,taci gaba da kwanciyar ta,bai hakura ba ya kara daura hannunsa a saman bayanta,ba bata lokaci ta jawo hannun ta cikinta tare da ganya masa cizo,ba shiri ya dauke hannunsa,
Jira yayi aka dan dauki lokaci tunaninsa tayi bacci ya koma ya kara rugunmeta,kafarta ta buga masa a kansa kamar me magagin bacci,
Ba shiri Alim ya koma karshen bed ya kwanta yana murmushi a ransa yace masifaffiya akan na hanata kwana gidan biki,

Washe gari da safe Mum ta fara salati ganin Amana tana jera abinci a dining,amma bata ce komai ba har Amana ta duka ta gaisheta, Alim ya fito sanye cikin tsadajjiyar shadda kamar a saceshi sai kamshi yakeyi yana ta kallon Amana yanda take cika tana batsewa shi kuwa dariyar mugunta yake mata kasa kasa, tana kallonsa ta kara cika fam.

Mum kuwa abincinta ta Eba ta koma room dinta,Alim yana ganin ba Mum yace shirya na kaiki masifaffiya karki cinyeni akan biki,Amana cikin fushi tace bana so kuyi bukinku bazan je ba ka daina nuna mun ba yan Uwa na bane akan naje bikin gidanku duk duniya sai ta sani ka je ka daukoni cikin talatainin dare.

Alim yana kallonta har ta gama masifarta yace tooo Allah ya baki hakuri ni ba fada nake nema ba,shirya mu tafi,yatsina fuska Amana tayi Alim yace kinga kyan da kike min kuwa idan kina yatsina fuskar nan taki me kyau,
Fuska Amana ta hade tare da fashewa da kuka, wai tunda Alim yace tana kyau da yatsina fuska,shine ta koma kuka,Alim yace kaiiiii kinga kyan da kukan nan,ai ban San haka kike kyau da kuka ba kullum zaki dinga yi min?
Amana najin haka ta kama dariya,Alim yace kash kin cuceni mene zakiyi dariya ni nafi son kukan kinfi kyau dan yi min,ai Amana sai ta dinga murmushi me kyau wai dan kar Alim yaji dadi yaganta tayi kyau.

Alim baiji dadi ba ganin Amanansa na fushi dashi sai yayi dana Sanin daukota jiya,suna gama break yace je ki shirya mu tafi Amana ta makale kafada,bata rai yayi ban son musu jeki shirya na kaiki,
Amana da sauri taje ta shirya ta fito suka tafi,suna zuwa zata fita Alim ya riketa ki tsaya muyi Sallama mana,shuru tayi tana kallonsa,kiss ya manna mata a goshi tare da tambaya anan zaki kwana? Amana tace eh,kiyi hakuri kinji nazo da dare na daukeki kinji? Make kafada Amana tayi wai ita kwana zatayi,kin San bana iya kwana ba ke,kunkuni Amana ta kama masa cike da shagwaba,ni bana gane wannen kunkunin naki wa ya sani ko zagina kikeyi,kallonsa Amana take baki bude cikin shagwaba tace ya zanyi na zageka,naji to dan Allah nazo na daukeki? Alim ya fada cikin shagwaba tare da yin kalar tausayi,
Amana tace a'a ni gaskiya kwana nake so,
Alim ya kara magana nine fa Babynki ni din? Amana ta make kafada,kwafa yayi tare da cewa to fita ki tafi sai da safe,Amana ta fice,Dear Alim ya kira ta har zata shige gidan ta juyo daga nesa yace nine fa? Amana ta kama sheshekar kuka,ajiyar zuciya ya sauke yace to jeki jeki daina kuka,nine?ta daga kai wai eh,yace to bazan dawo na daukeki ba sai gobe jeki...yana kallonta ta shige gidan.

Alim kuwa driver ya tura airport ya dauko su Umman Amana da kishiyoyinta dasu Hamza harda zaliha da Salma.

Direct gidan Abba aka wuce dasu nan su Amana suka dinga murna aka basu masauki,sunci sun Sha sun huta sannan aka kaisu wajen Abba suka gaisa cikin girmamawa,su Nura da sauran dangi duk sun gaisa an San juna,
Mum ma gidan ta taho suka hadu da sauran dangi ana ta shagali,sannan ta bawa dangin mijinta hakurin abinda tayi musu wai su yafe mata,

Washe gari su Umma gidan Amana suka dunguma suka Sha kallon aljannar duniya,kwana biyu Alim baiga Amana ba,har gidan yaje sau nawa bata nan wai sun fita shirya wajen dinner,anjima kuma ace sun wuce gyaran jiki da lalle,

Haka aka gama biki lafiya aka kai Amarya Asiya kano a jirgi,su Umman Amana da sauran dangi kaf Amare suka bi a jirgi suka koma kano,

Kowa ya shirya ya koma gidansa,Mum kuwa idan suka hadu da Abba ma harara yake Dalla mata,ba fuska bare ta sa rai zai maidata dakinta,har hakuri taje ta bashi amma Abba ya kara ci mata mutuncin da ba shiri ta hada nata ya nata tace zata tafi kasarsu,Alim yace ta zauna dasu Nura ko a bata gidanta daban ta zauna su kai mata yar aiki da kyar Mum ta yarda,

Ai kuwa gida karami flat me kyau Alim ya bata tare da me gadi da kuma yar aiki mace,Mum ta koma ciki suna zamansu lafiya,
Amana kuwa ranar da aka tafi kai Amarya ranar ta dawo gida da kanta,

Tunaninta Alim zaiyi fushi da ita amma sai taganshi sai murna yakeyi da dawowarta,
Rungumeshi tayi ta fara bashi hakuri me kikayi?ai ni naga dama na barki kema kin San da ace banyi niyyar ba ko yini daya bazan bari kiyi ba,
Na kyaleki sabo da ki samu nishadi da yan uwanki da iyayenmu shi yasa,ki daina bani hakuri ma,

Cike da murna ta fara kissing dinsa,bai direta ko ina ba sai saman Bed,
Tun daga yanda Alim ya fara murzata Amana ta raina kanta، tun daga yanda ya shigeta Amana ta fara bada hakuri ta gane mugunta ya shirya mata ba hakura yayi ba,
Saida tayi kuka sosai,ranar kusan kwana yayi,Amana cikin kuka tace da ka min irin wannan hukuncin ai gwara ka zaneni wlh,
Murmushi Alim yayi bana fada miki ba bana son musu,na barki kiyi kwana daya kwana nawa kikayi? Amana tace Uku,da naje kullum ina kike zuwa ba izinina kike bin yan mata kuna yawo,su Badriyya duk suna gida sabo da suna daraja aurensu,missed calls nawa na miki kinki dagawa dan kar nace ki dawo,atleast kin San kullum zan barki kije amma kin tafi kinma manta da aurenki,

Duk wannan Bai isheki ba da kukaje dinner kin zage har da rabon take away maza na kallonki duk abinda kikayi ina zuwa na ganki na tafi,bai kamata na kyaleki haka bama kin bata min rai da yawa,kara fisgota yayi tare da furta bari na kara goge miki rainin da kike min,Amana kuka ta fasa sosai tana bashi hakuri,
Wlh bazan kara ba na tuba,dan Allah mutuwa zanyi idan ka kara yi,
Ko tafiya da kyar zan iya,ke kika jawo ban so na miki horon nan ba Amma ba kya ji duk ranar dana ce kaza kika min musu saina miki wanda yafi wannan,
Da sauri Amana tace Bazan ma kara ba wlh na daina,dama tsautsayine.

Daukanta yayi tare da mata wanka ya gasata sosai sannan ya shiryata ya kawo mata abinci taci ya bata magani tasha ya kwanta tare da makalkaleta a jikinsa yana ta faman bata hakuri,

Washe gari da safe warkai Amana ta tashi ras da ita,Alim ta duba baya gidan,short note ya bar mata kan mirror,

Sweet heart dina na tashi kina bacci ban son tashinki, naje office ina da meeting,yanzu zan dawo,ki kular min da kanki, love u.

Murmushi ta tayi a hankali ta furta honey kenan jiya ya gama min muguntarsa amma na tsorata ni yanzu ma lallabashi zan dinga yi tunda idan ya fara mugunta Bai San ya bari ba.

Sati Uku da biki Alim ya samowa Amana private university me tsadar gaske take karanta microbiology,
Amana ta kara Zama classic girl tayi wata irin wayewa,murjewa hade da gogewa,
Yau watanta Uku tana zuwa schl bata da wata matsala burinta kawai ta ji ta dauke da ciki,ta haifo Aabid dinta amma har yau shuru kakeji.

Alim yanda yake gwadawa Amana so da kauna ga tattali,baya son bacin ranta,itama haka,Amman duk da haka idan tayi masa laifi sosai yake mata fada.
Itama Amana ba sanya idan ya mata tana hakuri sosai ta kyale watarana kuma yasha masifarta dole ya lallasheta,
Dama zaman tare watarana hakane dole a samu sabani amma an fi so farin cikin ya ninnika bakin cikin,sai da hakuri dole,

Mum kuwa sosai take nunawa Amana so,matar Nura ma haka,dan Auta ma tace ya nemi wacce yake so ya aura.
Amana ce a cikin toilet ta siyo pt na gwada fitsari ko tana da ciki,

Samu tayi ta dauki murfin robar ruwa ta tsula fitsari a ciki ta bare a bin tasa sai taga ya nuna bata da wani ciki ba komai,kuka ta fara yi tare da yin ball da murfin,ta jefa abin a dustbin,
Alim ne yaji kamar kukanta ya shiga toilet

Please Login or Register in order to submit comment