Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shirya cikin shadda dark brown tayi kyau kamar itace Amaryar Aabid kuwa ya tafi weekend wajen Mum Alim,

Wani gigitaccen kamshi Amana taji ya daketa,Alim ya sakko cikin hadaddiyar shigar wata tsadaddar shadda yar gaske fara kwal,yayi Kyan da bai taba yi ba a duniya,ita kanta Amana gigicewa tayi,
Da Sauri ta mike tsaye tana wani kyafta ido sannan ta fara magana,dan Allah Dan Annabi dan Darajar Allah dan girman Allah kaje dani daurin auren naka kaji,

Pls Daddy kaje dani sosai ta damu Alim sai yaje da ita,je kiyi shiri kwana yini daya zamuyi tunda ma hakane sai Na tsaya mu taho da Amaryata.cikin tawagar angwaye dake flight harda Amana,

Amana burinta idan sunje kano taje gidansu su gaisa da yan uwanta.
Gidan Amarya kuwa an cika makil ana jiran angwaye,Abba da yan uwansa duk Suna can,Mum ma ta tura Aminiyarta Haj Talatuwa da Haj sameera kanwar Abba da matar Alhj Ishaq Aisha. Duk suna gidan Amarya ana jira a daura aure.

Angwaye sun sauka a kano sun kara haduwa a manyan motoci Na alfarma tare da frnds na kano an tafi gidan Amarya daurin aure,Amana tana kusa da Alim,sai tsokanarsu akeyi cewar tayiwa Amarya wayo,Amana dai tayi shuru ita da Alim a bayan mota Khaleed ne driver,ana ta zankada tafiya,zuciyar Amana cike da kunci,shi kam Alim ya rasa dalili jin wannan auren yakeyi daban da sauran da Mum tayi masa,baya jin wani kunci,ya danganta hakan da sabo.
Amana bata kaunar ganin garin Amaryar ma sabo da haka ta kwantar da kanta a jikin kujera tare da lumshe ido,khaleed kuwa sai tsokanar ango yakeyi yaki yin shuru,sauran motocin abokan ango suna binsu a baya,

Garin Amarya aka shigo har unguwarsu da layin gidan su amarya wani dandasheshe gida da duk unguwar babu kamarsa shi aka tsaya da motoci,mutane damkam cikin masallaci da wajensa,dangin ango duk gasu nan,har su Huzaifa, Amana bude lumsassun idanuwanta tayi don kallon unguwar Amarya,ai da sauri ta kara damke idonta ganin wani tsantsararren gida me kyau,gida Na fita kunya,ga mutane sunsha wanka,kamshi Na tashi kowanne cikin shigar alfarma,

Amana sai zare ido takeyi da mamaki tana kara bude idonta sai kallon dangin Amarya takeyi cikin suturu Na gaske,da gani sun samu harka,mamaki cike da zuciyar Amana,sai murza ido Amana takeyi.
Kallo Amana take tayi tana murje ido,ga kwalla ta cika idonta har hawaye ya fara zubar mata ta rasa meke mata yawo a zuciyarta.




AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳



70-75





By
AsmaBaffa





Amana bata gama shan mamaki ba sai da taga Babanta ya fito daga gida dauke da Alawa goro da chewgum Na daurin aure domin a kauyen haka akeyi,
Hangame baki Amana tayi domin ganin su Haladu da Hamza tare da sauran yayyenta duk sunzo daga garin da suke Cirani,mamakin Amana shine ganinsu cikin shiga me Kyan gaske,gaba daya sun canja,kyansu ya fito,sunyi fresh,to me ya faru haka,amma ai suna waya dasu Baba me yasa basu bata labarin komai ba,cikin motar da take ta kalla kawai sai taga wayam ba kowa Ashe angwaye duk sun fice an barta a ciki,su Alim ta hango sai hada hada sukeyi,musamman yanda taga Alim da danginta sai wasa da dariya sukeyi,mutumin da ba ya magana shine yake ta wasa da dariya haka.

Ana haka aka fara hudubar daurin aure,Amana sauke glass din window motar tayi dai dai da lokacin da taji ance an daura auren ALIM USMAN MUSA da AMANA SULEMAN HARKA kan sadaki naira million daya.

Amana poster tayi ta kame waje daya tare da hangame baki,shi kuwa Alim ya rasa me yake ji a ransa sai congrat akeyi masa da fatan alkhairi,
Baban Amana baki har kunne sai rabon alawa da goro yakeyi ana masa Allah sanya Alkhairi,Amana kuwa ta matsu mazan su watse ta shiga cikin gidansu taji wannan wanne irin abune,za a min aure ban sani ba,
Wani bangaren kuma wani nishadin dadi ta tsinci kanta ciki,tana ta tunanin duniya bata sani ba har mutane sun waste,angwaye kadai suka rage a kofar gidan su Amana,

A rude Amana ta gyara gyalenta siriri shara shara da ta yana a kanta bata daura dankwaliba sai acuci da tayi,gashi shaddar da tasha kowa ya ganta zaice Amarya ce,
Fitowa tayi daga motar kamar zata tashi sama ta wuce cikin gida ko bangaren angwaye bata kalla ba,Amana doluwa ta zama data shiga hadadden gidansu,kamar a birni,ko ina yasha tiles kofofi da windows masu kyau,cikin dakuna sun sha furniture masu kyau,
Komai Na gidan Na yan gayu,dakuna ta duba bedrooms gasu nan na maza Dana mata,Dana baki,da Na Babansu Palo da bedroom,
Dakin iyayensu ma Palo da bedroom ko wacce,kakarsu ma haka.gida ya kai gida ba jin kunya,mamakinta waye yayi gidan haka,
Yan biki mata sai kallon Amana yar gayu akeyi,ana guda,shewa,tare da tsokanar Amarya,Amana sabo da tsabar gulma dan kar ace tana so sai ta fashe da kuka tare da kallon Badariya tace ke dan uwarki ina dakin Umma,nuna mata badariya tayi ta fada ciki da kuka,

Babane ya shigo dakin shima,Amana cikin kuka tace Baba ya zaka yi min haka,ayi min aure ban sani ba,ko a waya ai ka fada min,Baba yace haba Amana ta ki yafewa Babanki kinji,uwar mijinki ce tace kar Na fada maki sabo da tana kaunarki tafi so tayi abinda zai saki nishadi,kinga gidan nan mijinki shi ya Gina min,kinga kowa Na gidan nan ya basu jari me tsoka,kannenki duk ya biya musu kudin makaranta,kudi da abinci da sutura duk shi ya aiko mana sosai har yayyenki da suke Abuja da cross river yayi musu komai,ta dalilinsa gidan nan an ci gaba,ga ilmi ana samu,
Ga shi kowa yana da aikinyi,yanzu duk iskancin da jahilcin da ake tafkawa a gidan nan Nawa ya fara raguwa, Iyayenku sun fara daina zage zage sabo da islamiyyar da kika ce su shiga,haka duk maza da mata masu shaye shaye da sata da matan ma masu mugun hali ta sanadiyyar makaranta da aikinyi da suka samu duk sun daina sai abinda ba a rasa ba,
Ki duba da kanki ki gani su Hamza duk sunyi hankali,nima yanzu alhmdllh Ina ciyar da iyalaina,to Baba kaifa ka daina daya halin naka?cewar Amana,

Jan numfashi Baba yayi yace kuci gaba da min addua Amana Na kusa dainawa,kuka Amana tasa haba Baba yanzu so kake yayanmu su gajeka,mu gaskiya kana jawo mana abin kunya,
To Amanata sai hakuri ai inji Baba,shi yasa alherin da mutanen nan sukayi mana dole Amana nayi musu abinda suka bukata,amma gaskiya uwar yaron nan mijinki da Babansa mutanen kirki ne,kinyi dace,yanda suka nuna mana kauna gamu talakawa amma suka iya hada zuriya damu ai sai dai Allah ya saka,Allah sa Albarka cewar Umman Amana dake zaune bakin gado,Amana tace nidai kawai ba a kyauta min ba,
Kudin sadakinta Baba ya mika mata dubu dari shida ta dauka haladu yaje banki ya sa mata a accnt dinta Dari hudu kuma ta rabawa iyayenta da danginta,

Gidan su Amana suna da tsafta sosai saboda shi Baba Allah yayoshi me tsamtsami,shi yasa dole kowacce ta zama me tsafta a ko ina,saboda yana ganin kazanta zai iya sakin mace.
Badariya ce ta kawowa Amana wainar fulawa da yaji me dadin gaske,ta kawo mata waina da miya ta bikinta,tuwon shinkafa miyar ganye,ummanta kuma ta kawo mata danwake me zafi,

Tun anan Amana taga canji,da Dane yaushe Badariya zata wani girmamata haka,gashi abin farin ciki Badariya ta daina zuka hayakin sigari,Umma ma da ace da ce yaushe ma zata wani saurareta idan ba kudi Amana ta bayar ba gaskiya Alim da iyayensa sun taimaka musu,ko sabo da wannan dalilin ta yiwa mijinta biyayya.

Ta fara cin danwakenta kenan Badariya ta kara shigowa Anty Amana kinga booth din motar angwaye kuwa abincine irin Na hotel da kaji,da ruwan jarka ke harda lemuka sun bude a irin abin take away suna ta ci in fada miki gaskiya yan gayu ne,amma angonki bai ci ba shi,Badariya tace kinga wannan Huzaifan ya bani da yawa Na kawowa su umma,

Anty Amana wai dan Allah nima ina da kyau?kinji wannan Huzaifan sai yace ni me kyauce,nace ai kin fimu kyau yace bai yarda ba Badriya ke ta faman surutu,Amana cike da masifa tace karki dameni dallah,

Sallamar Alim sukaji Umma dake waje tace shiga mana tana ciki ai an zama daya,tana cin danwakenta Alim ya shigo ya zauna a daya daga cikin kujerun palon.

Kwanikan gaban Amana ya shiga Budawa wainar fulawa ya gani tana ta tiriri,dama shi yana son wainar fulawa,gabansa yaja kawai ya fara ci,saida yaci ya koshi ya mike yace ki gama ki fito mu tafi ina jiranki,OK kawai tace da kyar,

Saida ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da shakar kamshinsa,
Saida taci ta koshi sannan ta mike tace Umma zamu tafi, hhhh dariya akayi sosai amarya da ango sunzo daurin aurensu tare sun koma tare,ba a taba ganin irin wannan aure ba,Amarya kamar bata da gatan dangi,

Umma wata katuwar Leda ta mikawa Amana tare da fadin Badriya ta rubuta komai a jiki,wajen Baba Amana taje sukayi sallama,Baba yace to Amana in kayi da kyau kaga da kyau,kibi Allah kibi mijinki Idan kika tsaya wuru wuru ki gani a allonki, muna kallo za a watsaki a jahannama,gidana ba a yaji,idan miji ya sakoki to ki nemi wani gidan ba gidana ba,Amana dai aranta tace wannan ai ba nasiha bace ta kirki,kai Allah shiryi su Baba,a hakanma gwara Baba ya kamanta,Umma ba wata nasiha sai wasu kwalabe manya ta wani bani a Leda,ko mene oho,

A fili kuwa kallon Baba tayi tace ai billahillazi ya sakoni ko nayi yaji dole gidanmu zan taho, ina kakeso naje,Baba ma yace aikuwa kinyi karya in kina wasa ki gwada ki gani,Baba no...zanci Ubanki Amana karki ga ina lallabaki Na fiki iya shege,Amana tace Baba Allah baka hakuri,yawwa tashi maza kuje Allah bada zaman lafiya,

Baba yanzu baza a kaini a matsayin Amarya ba?ke ya isheki Amana tafi gashi duk angwaye sun tafi mijinki ne kadai ya rage a garin nan.
Amana tana cin magani tare da kukan gulma wai dan kar ace batayi kuka ba ta fito har jikin motarsu taje Har khaleed driver yabi wata motar sun tafi cikin kano city,

Alim ne kwal a wajen,key din mota ya mikawa Amana me kuka,a ranta tace wato baima daukeni Amarya ba kenan, karbar key din tayi Alim ya Shiga gaba,ta zauna mazaunin driver ta fara tuki har suka bar garin Amana tukinta takeyi Hawayen karya nata sharara a fuskarta harda shesheka,
Har sukazo airport Amana bata daina kuka ba,Alim yana ta satar kallonta,ga driving ga kuka,frnds tuni suna jirgi ango da Amarya ma shiga jirgi sukayi khaleed ya juya gida da motar,
Amana ana lungu a kujerar jirgi har yau kuka takeyi tare da cewa Ashe tana kaunata,me sonace,Ashe kaunace zunzurutu Na dinga zaginta a banza,Ashe uwata ce nima,
Nima ina kaunarki ta kara fashewa da kuka,Alim bai gane kan zancen Amana ba,

Ashe Amana duk kukan takaici takeyi rannan da taji Mum zatayiwa Alim aure ta kwana tana zaginta kala kala,ashe ma itace amaryar,ashe Mum din Alim tana matukar kaunar Amana tunda har ta iya hada jininta da Na Amana.

Amana tunanin halin Mum ta shigayi yanda take sa Alim yana auri saki,kawai sai Alim ya kara jin kukanta tace shikenan bazanyi lasting ba,bazanyi inganci ba,
Shi dai baya gane me Amana take nufi,masu kula da cikin jirgi sai lallashin Amana sukeyi tunaninsu ko bata da lafiya,

Har suka zo lagos bata sani ba,motocin Alim Jere sun kai bakwai su suka kwashe tawagar ango,har gida wajen Mum dinsa aka rakasu,Har Amana sai wani rufe fuska takeyi saboda kunya
Mum cike da nuna murna da farin ciki Na karya ta tarbi Amana,

Yata kiyi hakuri kinji anyi aure ba tare da amince warkiba Na yaba da halayenki matuka shi yasa naji kwadayin hadaki da Dana,kuma shima Alim ya fada min yana sonki,haka Mum Alim ta dinga shiryawa Amana zancen karya iri iri,har sai da Amana taji ta yarda da Mum,

Su hajiya Talatuwa kawar Mum sun dawo suma,Talatuwa ita kadai tasan dalilin da yasa Mum tasa Alim ya auri Amana,Aabid yana makale a jikin amarya Amana, Mum ce ta sa ma'aikata suka fito da lefen Amana Na gani Na fada har akwati 9 babu abinda babu,wasu ma a Holland Mum ta hadosu,har mota aka shigar da akwatuna,Mum ta kalli Amana tare da kallon ledar da Amana tazo da ita,da wasa da dariya Mum tace wannan kayan fa daughter,Amana murmushi ta saki tare da cewa Umma Na ce ta bani nima ban San mene ba, Mum ce ta karba tare da dubawa kayan gyara Na mata ta gani,ingatattun magunguna,fakar idon Amana tayi ta dalla mata wata uwar harara tare da maka mata banzan kallo,a ranta Mum tace za a mallakemin yarona tsinanniya zaki ga yanda zan mai da rayuwarki,a fili kuwa cewa tayi yata wannan ai sunyi araha da yawa sai su lalata miki mahaifa,ki bari ki zauna yanda Allah yayiki sai mijinki yafi sonki,Amana baiwar Allah to Mum kawai tace,

Bayan sunyi sallar isha Abban Alim ya nemi Alim da Amana yayi nasiha ta gaske sannan yayiwa Alim tasu ta sirri,Asiya ma sai yabon irin kyan Amarya takeyi har sai da Mum ta maketa,

Aabid Alim da Amana haka aka rakasu har mota suka tafi gidan Alim,kowa yana murna da fatan alkhairi banda Mum da kullum cikin kulla sharri take,
Ma'aikatan gidan Alim kaf sun sa ido suga an kawo amarya su ga kalarta su sami abin gulma,sai sukaji shuru kawai Amana suka gani da Aabid da Alim,sai suke tunanin ba yau za a kawo Amarya ba,amma wasu maza daga ma'aikata sunzo da gulmar cewar sunji ance Amana itace matar da Alim ya aura,amma aka karyatasu ba a yarda ba ganin babu wata alama data nuna Amana Amaryace,kuma sunga da safe da ita Alim ya tafi gidan biki,

Amana kuwa suna shiga Palo Alim yace ina ledar hannunki da aka baki a garinku? Mum ce tace Na bata basu da inganci Amana ta fadi,mene a ciki?Alim ya tambaya,hmm nima ban sani ba amma naji Mum tace wai kayan gyaran matane,nan take Alim ya gano wato Mum kwacewa tayi dan kar ma ko ya kusanci Amana yaji wani dadi,

Baki ya tabe tare da cewa ke kuma sai kika tsaya sototo ta karbe ko?gaki da wayo amma kuma baki dashi,sai kiyi tayi ai.ga Aabid karbeshi yayi bacci zanje Na huta

Wanka sukayi gaba daya suka kwanta baccin gajiya Kowanne a dakinsa yake,washe gari dukkansu babu Wanda ya fita,haka sai ga yan aiki sun shugo da lefen Amana gaba daya,Suna zaune sai ga Mum da sassafe tayi sallama a gidan,da sauri Alim yacewa Amana dauki Aabid ki koma dakinki,saida ya tabbatar Amana ta shiga dakinta sannan ya budewa Mum kofa ta shigo tana faman baza ido,ko gaisawa basuyi ba tace ina Amarya,yatsina fuska Alim yayi tare da tabe baki yace Mum pls ki daina hadani da wannan yarinyar bana kaunarta,

Tana can dakinta nifa Mum duk cikin matan da kike aura mun babu wacce Na tsana kamar wannan yarinyar,bana kaunar ganinta Sam,da nasan zakisa Na aureta da bazan taba daukanta aiki a gidana ba,yanzu wlh kin jawo mata masifa da bala'i aiki zata sha ta zama baiwata kawai,.
Wani sanyi da dadi ne ya ziyarci zuciyar Mum,nan take tayiwa Alim sallama driver ya maidata gida,

Wata ajiyar zuciya Alim ya saki tare da kwankwasa dakin Amana ta fito tana fitowa ya sakar mata kayataccen murmushi tare da cewa Amarya yau bazaki hada mana break ba ko hutun Amarcinne,Amana dai kunya ce ta lullubeta,harda nunawa Alim Aabid karfa yajika tare da fadawa kitchen sai Murna takeyi




AsmaBaffa


Ina godiya kwarai readers luv u all,ina ganin sakonninku ta ko ina tnx.
[6/27, 9:25 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✳CIRANIN AMANA✳



75-80



By
AsmaBaffa



Alim suna ta game da Aabid har Amarya Amana ta gama shirya girke girkenta a dining sannan ta koma dakinta ta shige toilet ta feso wanka tare da cancada kwalliya cikin shigarta ta yau da kullum amma yau ta dabance wani burmemen wando 3qtr red da wata Riga T-shirt karama ko dankwali bata daura ba ta fito,su Alim ta hango a dining tun kafin ta karaso wajen Alim ya mata alama da hannu cewar ta juya ta canja kaya,

Tasan kayan da yake nufi dan haka ta cuno dan bakinta ta juya tana kunkuni ta canja shigar atamfa wata lemon green dinkin Riga da skert sosai tayi mugun kyau ta fito a Amaryarta,yau Amana cewa tayi sai ta daura dankwalinta nan ta fara kici ciki ta kasa kawai sai ta Dora dankwalin kawai a kanta kamar gyale ta fito haka,
Tana zuwa Alim yace ko kefa,zo...zo..da sauri taje wajensa,dankwalin ya zame a kanta,habawa nan yaga zallar baiwar gashi baki sidik yana kamshi da kyalli,
Amana kuwa gabanta sai faduwa yakeyi kasancewar namiji bai taba yi mata haka ba,

Shi kuwa Alim daurin dankwali ya shiga tsantsarawa Amana harda rera wakar barmani choge ....sakarai... bata da wayo,ai Amana dariya ta fara kyalkyalawa,Alim bai taba ganin dariyarta haka ba domin Amana ba komai ne ke bata dariya ba,
Tsayawa yayi har ta gama dariyar sannan ya daura mata daurin zamani kamar ta daura goggoro haka Alim ya Nada mata dauri,da sauri ta shiga bedroom din Alim ta kalli kanta yanda ta zama kamar sarauniya,

Fitowa tayi tare da cewa dan Allah a ina ka koyi dauri haka,ko a mata ban taba ganin wannan kalar ba,ba kin maida kanki namiji ba ta ya zaki San da wannan sakara kawai cewar Alim.tun daga wannan rana Amana ita ba abinda ke birgeta irin ta zauna taga Alim yana nannada mata dauri abin birgeta yakeyi yana bata sha'awa.sabi da haka yasa Amana kullum burinta tasa atamfa ko lace ko shadda ko material tazo wajen Alim tace Daddy ayi min dauri,shiko Alim ya zauna ya tsantsara mata dauri,kuma tayi tayi ya fada mata a ina ya koyi dauri yaki fada mata,

Amana tare da Aabid zaune a kujera tana taje masa gashi,Aabid ne yace Anty ki siyo min icecream gobe idan munje schl,Amana ce ta bige masa baki kar ka sake Na kara ji kace min Anty as from today Na zama your Momy, kunji fa Amana,Aabid kuwa ya rike gam Momy yake ce mata
Yau Amana sauri tayi kafin Alim ya fita Office tayi wanka tasha wani dakakken lace a cikin kayan lefenta ta fito main Palo Alim ma ya sakko cikin shirin sa zai wuce office da sauri tasha gabansa Daddy...Daddyn Aabid pls ayi min dauri,me zakiyi da dauri yanzu ke da Mum ke nemanki,kiyi sauri ki je wlh kafin ki shiga Matsala,cike da shagwabar da bata San ta iya ba tace to Daddy nifa kana gani ko schl banje ba yau saboda Mum tana nemana,kuma nace kamin daurin Na je kaki,kuma ma Allah ni bazan iya Driving ba yau muje ka saukeni a gidan,

Lallai yarinya baki San nufin Mum akanki ba,to ko driving karkiyi ta ganki a motata kinji Na fada miki,muje Jan hannunta yayi har dakinta,tsofaffin kayanta ya duba ya dakko wata doguwar rigar atamfa wacce take karama kuma ta kode ta jeme,yace sa wannan maza,ba musu ta yi hanyar toilet da sauri Alim ya jawota baya yace kut amma kinma raina ni dalla malama sa kayanki anan me zan gani,

Kunya sosai taji haka ta daura zani cikin dabara ta canja kayan,sannan ya dauko wani dark powder sosai ya shafa mata saiga Amana ta dawo baka baka tayi kalar wahala,kowa ya ganta zai rantse a cikin talauci take, oya yi kalar tausayi Na gani Alim ya furta,ai kuwa Amana ta wani langabe kamar Almajira, good ki yi acting ina zaluntarki,ina baki wahala a gaban Mum,karki bari Abba ya ganki a hakan,kuma zamu tafi amma zan saukeki ki hau taxi ta kaiki,duk abinda Mum zatace ki nuna wahala kike sha a hannuna,

Amana to kawai tace tana tausayin kanta haka ta sa hijab har kasa sabo da yan aiki kar su ganta haka,cikin jerin motocin Alim suka fita sun kusa da gidan su Alim aka tsaya,Amana ta cire hijab dinta tare da yafa wani yankwanannen gyale Tsoho kalar talauci,ta fito tare da shiga taxi ta bashi Address din da Alim ya bata,me taxi ya kaita har gidan,

Sunkuyar da kai tayi har sashen Mum,tana shiga palon tayi ido hudu da Mum Alim ana mata tausa,kamar gaske Mum ta mike tsaye tare da rafka salati Yata kece kuwa, haka kika dawo?me ya faru,Alim ne ko?Amana kuwa kawai sai ta fara Kuka wiwi kamar gaske
Tace Mum baya sona,bakiga azabar da yake gana min ba,har marina yakeyi,kuma ko dakina bai taba shiga ba,yanzu kusan aikin gidan kaf ni nakeyinsa,

Ya tsaneni baya kaunata,bauta kawai nakeyi,kayan sawata gaba daya ya kwace har Na lefe,ni dai kice ya sawwake min wlh na gaji,wani dadi da sanyi ne ya lullube Mum Alim,a fili tace ki bari yata zanyi masa magana,wannan ai shirmene,ya zai watsa min kasa a ido,ina zuwa,da sauri Amana ta riko kafafun Mum tana kuka dan Allah Mum karki fada masa, ki rufa min asiri,idan kika fada masa na shiga Uku na lalace,

Mum a ranta tace baki shiga uku ba sai nan gaba,a fili kuwa kan Amana ta shafa tace ina zuwa wani daki ta shiga,Amana ta bita a hankali ta labe a jikin kofar,Mum taji ta fara waya da kawarta tana ta shewa da murna tare da bayyana irin makircin da ta hadawa Amana,da Wanda zata hada mata nan gaba,

Amana ce ta fashe da kukan gaske tana tunanin bala'in daya tunkarota da halin da zata shiga nan gaba,Mum ce taji motsi taji ajikinta Amana ce,da sauri ta katse wayar ta kira Alim tare da sawa a handsfree ta matso jikin kofa wai sabo da Amana taji bakin ciki a ranta tace Son wannan yarinyar me kayi mata haka,gaskiya kaci Amana baka kyauta ba,
Alim kuwa yasan makircin uwarsa kuma ya tabbata wannan nasihar ba tsakani da Allah tayita ba,sabo da haka Alim yace Mum na tsani yarinyar nan,bana kaunarta,bantaba tsanar wani dan Adam a duniyaba kamarta ,kema Mum kin San bazan taba son wannan ballagazar yarinyar ba,kawai biyayya nayi miki,

Amana taji komai da Alim ya fada dama kuma

Please Login or Register in order to submit comment