Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kaka ce shi yasa baya Jin kunyarsa

Alim yace sai na ballaki kika kara yi min magana,Amana tace na gaba yayi gaba na baya sai labari,gobe i yanzu na tafi gida ina zaka ganni kuma kafin na tafi sai na tabbatar dana yi maganinka.

Ina ma da ne yaro da kagane shayi ruwane,Alim yace kanki ake ji,
Har aka je cece kuce akeyi,amma Kaka tasan da wata a kasa idan sun koma gida zata hadasu taji me laifi acikinsu,

Amana da Alim ba wanda ya kula wani har akayi party suka dawo gida,Kaka tace kuzo muje dakina zanji dalilin wannan shirmen da kukeyi a matsayin fada.

Suna dakin Kaka zaune a kasa Kaka tana saman Bed tace ke fada min jikata mene matsalar ke da mijinki? Amana tace ki tambayeshi,Alim yace ke dai ki fada,k a fada dai kai da akayiwa laifi,Alim yace in zakiyi bayani kiyi,bazanyi ba nan suka fara cacar baki,ita Amana mamakin Alim takeyi har yaushe yake da baki haka yanzu,

Alim ne ya gyara zama tun farkon haduwarsu da Amana da halin Mum da abinda Sulemanu yayi musu da sanadin rabuwarsu duk Alim ya kwashe ya fadawa Kaka yace Amma kaka sirri pls kinji iya mu dake,Kaka tace kaine da laifi baka kyauta ba,kasan da halin Mum Dinka dana Saude amma ka zargi matarka ba tunani ba komai,kayi kuruciya Alim ga matarka ta gari,kuma yanzu gashi kasan kayi laifi ba bincike ba komai maimakon ka fara bata hakuri da lallashi sai ka dinga fada da tsokana da yakushi,

Ke kuma jikata nasan yayi laifi bai kyauta ba kiyi hakuri ki dauka kaddarace,nan Kaka tayi musu nasiha sosai tayi musu fada sannan tace kar na kara ji da gani ya wuce daga yau,Amana a ranta tace tab yaci banza ma kenan wlh Bai isa ba,a fili Amana tace ya wuce Kaka insha'allah bazai kara faduwa ba,

Alim wani sanyi yaji da dadi a ransa marar misaltuwa,Amana ma taji dadi da sanyi sosai zuciyarta wasai saboda Alim baya zarginta yayi tunani ya San ta gari ce ita,

Alim ne ya kalleta tare da cewa Kaka kice ta biyani cikina,Kunne kaka ta toshe tace kai ban son shashanci,to wlh ta fadi inda ta kaimin ciki cewar Alim,Amana tace ciki ya zube ka auri wata ta haifarma ta Mike tare da ficewa,Kaka tace sai kayi aiki da lallashi fa,
Kaka yarinyar nan taurin kai gareta,nasan baza ta taba kulani ba shi yasa kika ga ina tsokanarta da fada,nasan tana da saurin zuciya shi yasa nake mata abinda zatayi magana in ba haka ba nine zan Sha wahala,
Koma me ta maka kai ka jawo ba tunani ba komai ka yanke hukunci cikin fushi,Kaka kishine wlh da shedan amma nasan Amana ba yar iska bace a virgin na samu abata cikin kwali a like,kaka tace tashi ka tafi marar kunya,

Fita Alim yayi tare da tunanin ta yanda zai bullowa Amana ta hakura,washe gari da rana Mum Alim ta sauka tana gadara da takama,

Amana ce ta shigo palon Mama tana neman Aabid,
Mum Alim ta gani zaune tana latsa waya,har gabanta Amana taje tare da tsugunawa har kasa ta gaisheta cikin ladabi,lfy kawai tace ta dauke kanta cike da mamaki dama jarabar yarinyar nan tana makale da Alim lallai aiki Bai kare ba,dole ta aikata lahira kowa ya huta.

Amana dama tasan abinda Mum zata mata kenan kawai sai ta Mike,Alim ta gani a bayanta ya harde hannaye yana ta murmushin Jin dadi an girmama uwarsa.

Ta gefen sa Amana zata wuce ya rukota tare da hadata da jikinta,wani so da shauki hade da shock sukaji gaba dayansu,Amana Hawaye ya cika idonta Alim ya kai bakinsa a kunnenta tare da cewa am so sorry ki yafe min kinji,missed u kwace jikinta tayi tare da ficewa daga dakin,Mum ta kalleshi tace kayi asarar halinka jibi yanda take tureka kana manne mata,Alim ficewarsa yayi baice komai ba,

Amana kuwa room ta koma tana share hawaye sosai ga wani sabon son Alim da yake azalzalarta,
Alim ma kasa Zama yayi ya rasa inda zaisa kansa matarsa yake so,kuma taki hakura
A ranar duk yanda Alim yaso suyi magana da Amana abin yaci tura,sam Amana taki ma yasan inda take,
Last party ma da zata je babu yanda baiyi ba ta kulashi ko ta saurareshi suyi magana ta kirki amma taki yarda
Duk hanyar dayabi ta tosheta, kukane kawai Alim baiyi ba,
Haka aka gama biki sannan suka dawo garinsu har Amare washe gari aka daura Aure tare da kai Amare abinsu shar komai yayi a gidansu.

Amana ta dawo gida washe gari da safe wanka tayi ta shirya tare da komawa baccin gajiya,Alim yazo gidan gaba daya sai da yabi dangin Amana da iyayenta wai su bata hakuri ta saurareshi,su kuwa kaf Alim nasu ne musamman yanda yake kyautata musu ba musu suka kwantar masa da hankali harsu Umma.

Gaba daya manya da yara tare da iyaye suka dungumo dakin Amana tana bacci suka tasheta,Amana gabanta ya fadi da ta gansu gaba daya,nan fa suka zauna zasu fara magana.




AsmaBaffa


Happy sallah to u all
✳CIRANIN AMANA ✳



175-180



Official


By
AsmaBaffa





Maza da mata iyaye harda yara ne suka sa Amana a tsakiya suka fara caccake ta, me fada nayi me masifa nayi me nasiha nayi da masu lallashinta yan yara kenan,
Amana tana jinsu a ranta tace lallai Alim ya gama siye dangina da kudi amma ai nafi sonsa daku ina son abina kuma nafi Ku farin cikin dawowar mijina wajena,a fili kuwa sai Amana ta fashe musu da kuka, Gwaggo ta hangame baki tace yau naji shashashar yarinya ana nema miki gata kina shirme, Umma ta hayayyako yo dan ubanta ma laifinsane ki duba sharrin da aka kulla miki har yau gaskiyar abin Bai fito ba amma ya dawo wajenki a haka zai mai dake amma kin tsaya shirme,

Hamza yace akwai me kaunarta irin wannan bawan Allah idan wani ne a take a wajen zai sakeki,yana da kudi ga mata nan ke kadai ce mace,
Kb ya fara ai ni wlh tana kin komawa wata rangadediya zan Nemo masa ya aura,Amana ce ta dago tare da gallawa Kb harara,Isa yace ga kannenta da yawa ai ya halarta ya rabu da ya mu bashi kanwa, Amana ta sigar wasa ta daki Isa a kirji,Haladu yace munafunfun ana so ana kaiwa kasuwa wai ke jan aji ko?

Wayar Hamza ce ta dau ruri Badriyya ce ta kira tana fada masa yanda Alim ke kiranta a waya ita da Sakeena akan su tayashi lallashin Amana.
Umma ce tace duk kuyi shuru zan yanke hukunci yanzu Amana dolene ki koma wajen mijinki jibi nace ya dawo jibi ya tafi dake kuma Umarni ne na baki a matsayina na mahaifiyarki,yanzu ma yana palo ki tashi ki shirya kije ko yanzu na turoshi nan,
Amana kamar zatayi kuka tace haba Umma wai mene haka.
Gwaggo tace kai kuzo mu fita karki koma idan kinga dama,mazan ma sai da suka tsaya tare da yiwa Amana nasiha sosai sannan suka fita,

Suna fita Amana ta Mike tsaye tare da daka tsalle ta fada kan Bed ta jawo pilo ta kanka me tana ta dariyar Jin dadi tare da furta Alhmdllh,ta kara mikewa tsaye ta daka tsalle tare da furta jibi sai lagos ko da kafar katako ne Allah kaimu,towel ta daura ta fada toilet,

Umma kuwa ganin Amana shuru taki fitowa taje wajen Alim kawai sai ta sa Kb ya rakoshi har dakin Amana,daga bakin kofa Kb ya juya,Alim daya shiga ciki karar ruwa yaji a toilet yasan itace take wanka,jikin kofar toilet din ya karasa tare da cewa na shigo? Amana tana jin muryarsa tace ya salam kai Umma,ji tayi ya kara magana nazo muyi wankan?Amana tayi banza dashi da wasa ya murda handle Amana cikin fada tayi magana basai ka shigo ba pls.
Murmushi Alim yayi tare da komawa kan bed ya kwanta yana shakar kamshin Amana.

Tana sani taki fitowa daga wankan ya dade yana jiranta har bacci ya daukeshi sosai sannan ta fito, saida ta leka fuskar sa taga bacci yakeyi sosai,ta fara kare masa kallo sanye yake cikin farar shadda dinkin Maza fitted domin Maza ma yanzu dai dai su suke dinki sai ya dan damesu,
Harda sa hula domin shi ba sosai yake sa hula ba Amma yau harda hula dai dai shi ya wani coko ta gaban goshi sawar yan gayu na zamani duk gashinsa me uban yawa gasu nan waje,yayi kyau sosai komai fari dama shi akwai sa farin kaya,

Murmushi tayi a fili tace dan duniya kenan harda bacci a hankali ta cire masa hular tare da ajiyeta gefe,kafarsa ta kalla duk rabi a kasa karfinta tasa a hankali gudun kar ya tashi ta gyara masa kwanciyar saida ta hau dashi bed din sosai,Amana da karfinta to, Amma duk da haka tasha wahala dama tasan Alim din nata idan ya fara bacci to sai ka saceshi bai farka ba,

A nutse ta shirya tsab cikin riga da skert na material black tayi kyau matuka nan ta fara Barin turaruka a jikinta harga Allah a zuciyarta dan Alim tayi kwalliyar Amma a fili wai sai tace badan shi nayi ba dama nayi niyyar kwalliyata,idan zuciyarta ta tabbatar mata dan Alim tayi sai ta karyata,tunani Amana tayi ta shiga kitchen ta dafa masa abinci amma kuma idan ta shiga kitchen kwalliyarta zata baci duk da cewar da Gas suke amfani amma ai aiki zaisa kwalliyar ta lalace tun Alim bai gani ba,

Fasa shiga kitchen tayi tace idan ya tashi na hada masa,wata zuciyar tace idan yaki tashi da wuri fa har sai kwalliyar ta baje,tace kai bari na tasheshi na masa wayo ya gani sai ya koma baccinsa,

Toilet ta shiga tare da ebo ruwa a hannunta ta yarfa masa a fuska zumbur ya bude ido tare da mikewa ya zauna,
Kallon Amana yayi gaba daya kwalliyar Amana ta tafi da hankalin sa sai kallonta yakeyi bai ce komai ba,
Amana ta kara tamke fuska irin ba wasa ta kara gyarawa tayi tsaiwar daukan hoto ta gama Zuko da matso kyau tare da kallon saitin Alim,tunowa tayi baiga bayanta ba sai ta juya tare da kallon mudubi tana neman wani abu a kan Mirror dan Alim ya ga bayan,Alim kuwa ai tuni ta gama kashe masa jiki da kwalliyarta sha'awarta ce ta taso masa,
Sai da ta tabbatar ya kalli bayan ma sannan ta juyo tare da tamke fuska ta furta malam lafiya ka sani a gaba,nayi maka kara,na maka tauna,nayi maka hadiya ina jira naji me kazo yi a gidanmu harda shigo min daki ka kama bacci?

Shuru Alim yayi baice komai ba,Amana ta kara magana jibeka simi simi kamar mutumin kwarai,Alim dai baice komai ba,Amana tayi mamaki shi da yake tsokanarta ma,

Alim a hankali ya furta am so sorry abinda na miki kiyi hakuri kinji,Amana wani tausayinsa taji kamar tace ta hakura amma sai ta daure tace ka daina bani hakuri haka ya isheni me zaka ce Dani yanzu na yarda,kai harni zaka Zarga,da masifa Alim yace taya bazan zargekiba ko kece kika shigo kika sameni wata tayi min haka exactly abinda na gani ya zakiyi? Dole ki shiga kokonto,ni waye da bazanyi laifi ba?Sufi neni?dan Adam ajizine Kuma na fada miki na baki hakuri uncountable ya kikeso nayi kashe kaina zanyi?na biki na biki ok to zo ki cinyeni ko ki yankani,ko sati biyu bamuyi ba da rabuwa sai da na nemeki,ranar da Baba ya rasu zuwana nawa?ance miki da bana sonki zanzo inda gidanku yake ne?abinda yasa ban ce a kira min ke ba nasan kina cikin wani Hali kuma banson ganin damuwarki tunda Baba ya rasu,ki tambaya zuwana nawa gidanku bakya garin nan,kafin ma ki tafi Adamawa, ni fa ko a waya kin nemeni? Ko text kin taba yi min na tunanin wanke kanki ko kimin bayani ko kiji halin da nake ciki,ko namiji shine marar aji?shi ba mutun bane? Gidanku nazo ki fada min abinda kika ga dama kuma dole ki koma gidana yarinya amma kisan me zaki fada min banson raini ya karashe fadan da kinyi kyau dai badon halinki ba,

Amana dake tsaye sannan ta fara nata itama ka dakeni ka hanani kuka,daga yin abu Baka tsaya ka saurareni ba kayi tafiyarka,harda zazzagina kuji sharrin Amana,
Alim yace kiji tsoron Allah yaushe na zageki?Amana ta gwada muryar Alim tace haka fa kace ke din banza ni nafi karfinki talaka,wawiya,doluwa,bahuwa,kuchaka kuma saina ballaki idan na kara ganinki sai na karya miki wuya,
Salati Alim ya saki sannan yace kiji tsoron Allah,Amana ta kara hade rai tana Hawaye Alim yace to mene na Kukan kuma?,Amana tace ai kaci mutuncina da yawa dole idan na tuna nayi kuka,Alim dai sharrin Amana ya isheshi yace to yi hakuri kinji.

Ni Bazan hakura ba yanzu cewar Amana,Alim yace to sai yaushe? yayi maganar cikin sigar lallashi,Amana tace sai an gano wanda ya kulla min sharri,tsaki Alim yaja ke ban son shirme fa dole ki hakura kinji na fada miki, Bazan hakura ba to dolene,mikewa Alim yayi tare da furta bari na mike kika tsawona,tunkarota yayi sosai da gudu ta fice tare da cewa ka jira na sanmaka abinci amma ban hakura ba

Kwanciya Alim yayi bacci ya kara dauke shi,ya dinga yi har Amana ta gama hada masa jullop din taliya tasha hadi sosai,tana zuwa ta ciji yatsansa ya tashi firgit tare da rike wajen,
Kallonta yayi kana yace bashi kike ci,
Toilet din ya shiga tare da dauro Alwala sannan ya zauna yace to zuba min abincin tace ka zuba da kanka mana ai ban hakura ba bare na fara yima hidima,kyaleta yayi ya zuba abinsa tare da hada tea yaci yasha,
Amana ta kalleshi tace kwadayi anzo ana cinye mana shinkafarmu da taliya bai san sanda dariya ta kamashi ba sosai,Alim yace yimin kudi na biya mana,banza ta masa tana danna wayarta yace me kikeyi a waya Ba tare da ta dago ba tace Charting,idan da namiji ne wanda ba muharraminki bane bada yawu na ba, tashi ka tafi gidanku gaskiya ka takura min, basai kin koreni ba ya furta tare da mikewa tsaye
Kudi ya zaro Bundle biyu na yan dari biyar biyar yace dauki daya kallon kudin tayi dama bata da ko sisi sun kare a biki,hannu tasa ta kwace duka bundle biyun duka nake so kuma ka biyani kudin da ci da kaina da nayi yunda da aurena a kanka ka barni nasha wahala kasan hakkinka ne ka biyani duk kudin dana kashe,kudin sabulu da omo,kamo hannunta Alim yayi suka zauna gefen bed sannan yana murmushi yace sai ki fada min dalilin kenan na fushinki tuntuni na biyaki ashe da dalili to fada min komai na biya,Amana sai yanzu tayi dariya sannan tace dan kadan ne ma fa,banda wannan kudin da ka bani saboda wannan kyauta ka min,Alim yace ina Jinki,Amana ta gyara zama tace kudin Kukan dana sha da wahalar da ka bani na bacin rai,Alim yace daya,tace kudin ci da kai,kudin rainon ciki kafin ya zube,kudin kayan kwalliya dana siya nayi amfani dasu baka nan,kudin zirga zirga ta zuwa unguwa kasan dole zan kashe kudin Mota, sauran na yafe maka basai ka biya ba,
Dariya Alim yayi cikin jin dadi yace to ki jira zaki ga Alert ya mike zai tafi,Amana tace na manta kudin mintsini da Yakushi,sai kudin gyaran jiki kafin na bika mu koma lagos.

jagira (eye liner) baka da ja sun kare ka siyo,ko kuma kaga fuska ba kwalliya, jambakina sun zama tsohon yayi a siyo wasu, sannan sai ka sake min lefe zan koma kuma duk ka bayar dinki a dinka da kana nan kaya ka bani 2wks sannan kazo mu tafi,Alim yace an gama indai zaki koma ai shike nan,Amana tace kuma ka Aiko min da Mota ko na dinga hawa mashin dan acaba kasan kauye har yau ana hawa machine cinyata ta gogi ta dan achaba ba ruwana ni,
To karki hau dan Allah Huzaifa zai kawo miki Mota,Amana tace kuma aikin hajji da za aje bana sai ka biya min na sauke farali,Alim yace wannan me sauki ne, yawwa nima nasan me kudine mijina Amma kazo sai cutata kakeyi kana jin dadinka kai kadai cewar Amana
dariya Alim yayi sosai yace to zamuje,
Amana tace na karasa yafe maka sauran laifinka to,dariya Alim yayi sosai sannan ya jawo Amana jikinsa tare da rungumeta kam kam,
Baby so kike ki karar min da kudi ko?,Amana cikin shagwaba tace me teku tasan anyi dan an ebeta da cokali? Murmushi yayi tare da yi mata rada Baby danyi min kiss kinji,Amana tace naki din Ai dane muka dafawa jaka shayi ,Alim yana sheka dariya yace ina kika samo karin magana haka ni ban taba ji ba,

Amana tace ae mana kalli dai jaka wato donkey Amma a dafa mata shayi ai an bata dadi kuma gatan yayi yawa shine nima nace ai dane muka dafawa jaka shayi,
Murmushi Alim yayi tare da furta i love Amanata tare da kankameta i missed u,a hankali Alim ya hade bakinsu waje daya yana faman tsotsa kudin dake hannun Amana ta watsar daga hannunta tare da kara kankame mijinta,sosai suka shiga mirzar juna kamar zasu cinye kansu, kan bed suka fada Alim ya shiga zare mata kayan jikinta one by one,da kyar Amana tace ka bari na koma lagos dan Allah,Alim yace ina so ni dai ki kyaleni,zan fasa yin hakurin to naki yafe ma cewar Amana,Alim yace bakya tausayina dama na sani,to ka bari mana na kara warkewa har yaushe nayi Barin cikin ma da za ka kara min wani,ka bari idan na koma lagos sai kayi,na hakura to ai tunda bakya so nasan ko bari naji dadi Baza kiyi ba Allah kaimu ki koma zaki fada,

Gyara kayansa yayi itama ya mayar mata da zip dinta sannan ya mike tace to karka manta da motar kuma kudin gyaran jiki kwandalata Baza tayi ciwon kai ba don bani nace ka koreni daga gidanka ba sannan lefe Sabo in ba haka ba bazan ma kwalliya da masu kyau ba ehe,

Alim yayi murmushi tare da cewa Amma a Adamawa kika koyo rashin Imani ko?haushi ka bani da har ka iya zargina shi yasa Sabo da na huce zan ci ma kudi nima,zance kayi aka baka ni?a sadaka ka aureni tsabar gata ranar da aka daura aure ranar na bika muka tafi ba wani tarzoma,

Alim yace to naji fadi kudin gyaran jikin Amana tace salon na fadi kadan saboda da zan iya tausaya maka,kawai ka bayar da abinda kaga dama,au na tuna ribbom dina ma suna bukatar canji,

Check Alim ya zaro tare da rubuta mata check na million biyar ya Mika mata karba Amana tayi ta duba,sannan tace laaaa ashe da gaske kake zaka bani,ungo abinka ni wasa nake maka to,
Alim yace bazai karba ba,Hh dama tsokanarka nakeyi ai sai dai nace Allah kara budi ubangiji ya biya ma bukatunka nan gaba ka bani 20million kace Amanata gashi a siyawa Yara a
Icecream, murmushi sukayi gaba dayansu,har Mota ta rakashi ya tafi cike da jin dadin samun nasara.

Tun daga ranar Amana gyaran jiki takeyi kawai da sauran shirye shirye sai zumudi da jindadi takeyi,bangaren ogan ma haka yana can sai da ya canja komai na gidansa,kayan sawa kuwa na Amana da Rabin nasa duk ya bayar dasu ya canja mata sababbi kamar sabuwar Amarya,Yanda Mum taga Alim ya wani rude gaba daya kullum cikin farin ciki yake har yayi kiba ya kara fresh ta zata sabon aure zaiyi har murna takeyi ta zata Zainab din da ta bashi ya aura ita zai kawo,Abba da sauran yan uwansa duk sun san Amana ce zata dawo,

Asiya ma Abba ya tsai da ranar bikinsu ita da Ahmad yayan Huzaifa,murna wajensu ba a magana,Mum kuwa bata murna dan kawai Abba yafi karfinta ne,

Bangaren Amare su Badriyya ana can ana cin soyayya da angwayensu,
Sati biyu kenan yaune Alim yawa Amana waya ta shirya gobe zasu tafi,
Amana sai murna akeyi a boye, Umma tace Allah yasa dai uwar miji ta barki lafiya,kar kiji komai Umma kawai addua ce taku,
Musamman Amana ta figi mota taje lalle tare da tsantsaro saloon,dama tuni Huzaifa ya kawo mata motar hawa a cikin nasa ya bata daya Sabo da Alim ne ya bashi Umarni ya kai mata.

Amana ta kashe kudi sosai haka su gwaggo dasu Umma duk sunyi mata nasu suma,
Washe gari da sassafe sai ga Alim Sabo da tsabar zumudi,Amana lokacin ma ko bacci bata tashi ba,bayan sun gaisa da mutan gida,Umma tace shiga tana ciki,harda ledar take away a hannunsa,yana shigewa Umma tace gwaggo yau naga rashin kunya zumudin yayi yawa kamar wata Amarya.

Gwaggo tace kema kya fada wannan uban sammako haka ko kasar waje zaije ai sai haka,kamar zai tashi sama kai irin Sulemanu harka suna da yawa a kasar nan cewar Inna dayar kishiyar, Amana tana cikin bacci tajita a sama an daga tare da direta a kasa,da kyar ta bude ido tana kallon yanda yayi mugun kyau,

Kije pls kiyi wanka ba kallona zakiyi ba sauri zamuyi muje gida,flight zan canja mana Baza mubi na 5pm ba yayi dare da yawa,
to naji ka zauna banfa ci komai ba ma,to nidin naci ne? kiyi sauri dan Allah mu tafi gida, janta yayi har toilet ya Suri brush tare da zaunarta a wata kujera tana layin bacci idonta a rufe yace bude bakin mana ai kuwa ta bude yayi ta yi mata brush a hankali ya gama,

Ki bude idonki mana haka sai wani bacci kike,a hankali Amana tace zaka bata kayanka da ruwa fa,kamota yayi suka fito taki bude idonta wai bacci takeyi ita,fresh milk ya dura mata a bakin tare da bata chips da egg,ina ka samo abinci?da abina nazo nasan zaki bata min lokacine,haka ya dinga tura mata tana cinyewa shima yaci,suna gamawa yace wanka je ki shirya ko na miki,kuma ki bude idon haka mana kiyi sauri,

Wanka ta shiga tayi sannan ta fito tana goge jikinta,ta fara sha mai duk jikinta,tazo kafafu Alim ya fisge man kamar wani engine ya karasa shafa mata,kayan ta dauko ya kwace ya dauko pant yace to dafani kisa, Amana ta dafa shi ya sa mata da towel dinta a daure,
Cire towel din asa bra,haba a'a ni dai ka sa min akan towel din sai na zame towel din haka akeyi,kamota yayi yanda tace haka ya sa mata ita kuma ta zame towel din ta gyara sosai ta kara daura abinta,



Please Login or Register in order to submit comment