Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwan snow ake duk da babu yawa...".
Fiddo rigar yayi wacce take mai nauyi ya saka mata bottom dinta, ya zaro scarf ya daura mata a wuya sai kuma ya kalli dogon gashinta ya tattarashi ya saka a cikin rigar saying,
"Arfaat ke matar aure ce, gashi kuma mijin naki kishi ne dashi...".
Arfaat ta rumtse idanu yayinda hotonsa ya dawo mata a kai yana kwance akan wata yana making love yana kiran sunanta, ya daura mata scarf ya rufe mata har saman fuskarta dashi, ya rufe mata kai da hular sanyi sannan shima ya saka rigar sanyi ya rufe wuyanshi, ya kama hannunta suka fita, security ne tsaitsaye a bakin ward din, sukayi escorting dinsu to the elevator, guda daya ya shiga tare dasu yayinda sauran suka bi daya elevator, suka k'arasa parking lot, zungureriyar mota ce new and expensive, ya bude mata backseat ta shiga yayinda one of the security ya bude mashi daya bangaren ya shiga, direba yaja motar heading to the villa yayinda suke tare da daya daga cikin security din, sauran suna biye dasu ta gaba da baya domin tabbatar da tsaronsu....
Arfaat kallon komai take cike da mamaki akwai tarin tambayoyi a bakinta but there's is no one to ask, a wata katuwar villa sukayi parking, aka b'alle murfin motar ya fita yayinda ya zagaya daya bangaren ya bude bangaren da take ya mik'a mata hannunsa ta kama ta fito....
(Tayi still tana mai tambayar, yace villa dinsa, yaushe yayi kudin da har zai mallaki wannan villa)


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[28/03, 19:25] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 20

Lamido yana gaba tana biye dashi har suka shiga ciki, gini ne babba wanda yake dauke da upstairs har guda ukku, tana biye dashi ya bude wani katon bedroom suka shiga ya juyo yana mata murmurshi yace,
"A nan zamu rink'a kwana, bazan iya barinki ki kwana ke daya ba, akwai wanda yake girki a nan amma na bashi hutu dukkanin abun da kike so zan girka maki da kaina, I'm all yours, sauran wadanda suke kula da tsaftace gidan zasu rink'a zuwa tun da safe suna ayyukansu tun kafin mu fita...".
Sukayi alwalla suka rama sallolin dake a saman kansu....
Gani tayi ya kama hannunta tareda janta har zuwa gaban mirror yayi hugging dinta daga baya saying,
"Arfaat ina son in kaiki gida saidai kinga wahalar da muka sha duk mun rame kuma nayi wa Ummy alk'awarin zan kai mata ke a cikin koshin lafiya... Zamu zauna a kasar nan har ki murmure sai mu koma gida... Uhmm, Matar Lamido...".
Arfaat ta gyad'a mashi kai kawai, ya saketa saying,
"Ki kwanta akan gadon, ki huta, zan rink'a kwanciya akan sofa...".
Arfaat tayi walking ta haye saman gadon ta kwanta tareda jan blanket ta lumshe idanu babu b'ata lokaci bacci yayi awon gaba da ita....
Gab da sallar Magrib ta farka ta hangeshi zaune akan sofa ya daura kafa daya akan daya yana operating system dake a saman cinyarsa, smile yayi mata saying,
"Angel...".
Arfaat ta kirkiro murmurshi ta duro daga saman gadon ta wuce bathroom jim kadan ta fito ta zauna a gefen gado, yace,
"Kina bacci aka kawo shopping da nayi maki, let go, ki gansu...".
Tayi jim sai kuma ta mike yana gaba tana biye dashi, ya bude wata kofa yayinda closet ta bayyana kaya ne na mata birjik kuma size dinta, da mamaki take kallon wajen tana mamakin yadda aka shirya kayan nan duk tana bacci, kalli yawan kayan mi wannan mutanen yake nufi da ita ne wadannan kayan kamar wadanda zasu dauwama a nan, yana nuna mata kayan tana gyad'a head, har da shoes, bag and jewelry, suka fito, lokacin sallar Magrib sukayi alwalla ya jasu sallah...
"Dinner is ready...".
Lamido yana gaba Arfaat tana biye dashi suka wuce dinning table, warmers ne birjik, yace,
"Angel... Guess what?".
Sai kuma ya bude daya daga cikin warmers din saying,
"Ta da...".
Ya lumshe idanu yana mai shakar kamshinsa, yayi serving dinta sannan yayi serving kansa, bayan sun gama ta mike ta wuce upstairs to the bedroom, ya tattara kayan da suka b'ata ya wuce dasu kitchen ya wanke yana shiga ya tarar da ita akan sofa tayi relaxing tareda lumshe idanu, ya jasu sallar Isha'i suna gamawa ya mike heading to the closet ya dauko mata wata half night gown ya ajiye mata saying,
"Ki saka ki kwanta idan kuma kallo kika son kiyi sai in kunna maki...".
Arfaat tace, "Bacci...".
Lamido yace, "Okay then, good night and sweet dreams... Sleeping cute...".
Heading to the balcony, Arfaat ta d'aga kayan da ya fiddo mata tana kallonsu, duk da rigar ba zata wuce gwuwa ba amma tana da kauri, ta dauka ta wuce bathroom saida ta gama shiryawa sannan ta fito ta haye saman gado taja blanket ta rufa dashi, tayi kamar tana bacci tana jin yana kaiwa da komowa, tayi lamo kamar tana bacci har bacci yayi awon gaba da ita....
Early in the morning, mafarkin dajin ta soma yana rik'e da hannunta suna gudu yayinda wasu halittu mararsa kyan gani suke biye dasu zasu kwaceta daga hannunsa, a firgice ta farka saying,
"Ka ceceni kadda su cutar dani...".
A firgice take idanunta a waje tana dube-dube yayinda baki da jikinta yake rawa, Lamido ya k'araso da sauri ya kama hannunta, saying,
"Calm down... Ki nutsu... I'm here... You are safe with me...".
Hugging dinta yayi, tayi lamo a jikinsa tana maida lumfashi sun jima a haka sannan ya saketa ya kama hannunta saying,
"Mi ya faru?".
Arfaat muryarta tana cracking tace,
"Mafarki nayi akan dajin can muna gudu zasu kwaceni daga wajenka...".
Lamido yace, "Arfaat ki kwantar da hankalinki... They are all gone... They are no more... Babu abun da zai faru dake In shaa Allah...".
Tana kuka tace,
"I'm afraid... A tsorace nike...".
Yace, "Okay let do that... Did you want to be in therapy session... Therapy session...".
Arfaat tayi baya da sauri sai kuma ta girgiza kai, Lamido ya zauna a gefen gadon saying,
"Angel ya kike so ayi?".
Tace, "Ina son waya sannan ka tura min complete Qur'an a ciki...".
Yace, "Sure... Ki tashi kiyi wanka zan dauko maki kayan da zaki saka... Breakfast is ready and it's your favorite breakfast...".
Arfaat ta gyad'a kai ta mike ta wuce bathroom, ta jima sannan ta fito ta samu ba ya nan saidai kaya dake akan gado, doguwar riga ce daidai gwuwa, ribbon, saida tayi applying cream, tareda janyo hand dryer ta busar da dogon gashinta wanda ta wanke, ta saka kayan tayi zuru tana kallon kanta tana mamakin sauyawar da tayi a tsayin shakarun nan wadanda har yanzu bata tantance yawansu ba....
Lamido ne ya shigo daga balcony ya amshi ribbon dake hannunta ya tattara gashinta ya saka mata sannan ya zaro wata sarkar diamond ya tattara gashinta ya saka mata yana mai kallonta ta cikin mirror, under his breath yace,
"Gorgeous... Kece kadai a zuciyata...".
Ya kama hannunta ya janyo wata siririn bracelet mai stone a jikinsa ya saka mata saying,
"Angel, promise me ba zaki tab'a rabuwa dashi ba, ya kasance a koda yaushe yana tare dake, koda wanka zakiyi kadda ki cireshi...".
Arfaat ta gyad'a kai, suka sauko kasa yana rike da hannunta, lokacin da ya bude warmers din saida ta lumshe idanu, yayi serving dinta sannan yayi serving kanshi, spoon daya tayi ta dago tana kallonshi cike da mamaki, yaushe ya iya girki haka, a saninta ko ruwan zafi bai iya dafawa ba amma koda yake komai zai iya faruwa a tsayin shekarun da ta dauka bata nan wadanda ita kanta bata san adadinsu ba, tana gamawa ta mike ta wuce sama ta fita balcony tayi tsaye tana kallon waje....
Three hours later, Lamido ya sauka kasa ya kawo mata sabuwar waya fil tareda system, ta kunna karatun Alk'ur'ani tareda hadeshi da abun dake a kunnanta ta janyo system din, ta duba date, ta ware idanu cikin ranta tace,
"What? Six Years... Twenty four...".
She's curious about something and she wants to look into it, akwai internet connection a system din, tayi searching sunan Lamido, ta ware idanu tana karanta newspaper da magazine da sukayi magana a kanshi, is he that rich now, ganin sunanshi a cikin jerin masu kudi sanannu, ta kashe ta kwanta tayi lamo bacci ne yayi awon gaba da ita har ya fita ya dawo bata sani ba, suna gama lunch ta koma bacci a sanadin magungunan da take sha har da na saka bacci....
The following day, a hankali ta bude idanunta daga baccin da ta koma bayan sallar subh, ta mike zaune tareda durowa daga saman gadon, ba ya nan, walking heading to the balcony, tayi tsaye tana kallon waje....
Lamido dake zaune akan kujera yana karanta newspaper yace,
"Angel...".
Arfaat ta juya saying,
"Yaa Lamido...".
"Good morning...".
"Ina kwana...".
Lamido yace, "Lafiya lau...".
Arfaat zata juya taji yace,
"Hold on for some minutes...".
Arfaat tayi still tana kallonshi cike da mamaki, ganin yana dagowa yana kallonta yayinda yake zana wani abu akan farar takarda, mikewa yayi ya k'arasa inda take har tana juyo sautin lumfashinsa, ya mik'a mata farar takardar dake a hannunsa, ta amsa, yace,
"Ki duba...".
Arfaat ta warware tana kallo, da sauri ta d'ago ta kalleshi, ganin itace ya zana kuma zanen ya fita sosai, professional, da mamaki take kallonshi cikin ranta tace,
"Shi kuma yaushe ya iya zane?".
Sai kuma tayi mashi murmurshi shima ya maida mata martani da murmurshi, ta mik'a mashi saying,
"Zanyi wanka...".
Yace, "Okay then... Yau zamu fita in zaga dake kiga gari... Ki saki jikinki ki maida jikinki ta yadda idan Ummy ta ganki hankalinta bazai tashi ba... Ta damu sosai da b'atanki...".
Arfaat tace, "In shaa Allah...".
Juyawa tayi ta wuce ciki heading to the bathroom ta jima sannan ta fito ta tarar da riga da wando akan gado, ta shirya cikinsu, ta rufe kanta da hula, ta zauna a gefen gado tayi tagumi duk idan ta rufe idanunta abun da take hangowa kenan...
Bayan sun gama breakfast, ya saka mata jewelry, daukar veil yai yayi rolling kanta dashi, shima ya shirya cikin wando tareda riga, ya daura rigar sanyi ta saki a sama, ya zaro bakin glass ya saka, ta dauki handbag da ya ajiye mata, ya kama hannunta suka fita, security ne zagaye da gidan, wasu sukayi escorting dinsu yayinda wasu suka tsaya guard din gidan, a saman titi aka saukesu ya kama hannunta suna tafiya yana murmurshi tareda motsi da lips dinsa yayinda yake nuna mata wajaje...
Security dinsa daya ne yake biye dasu from a distance, a waje sukayi lunch, ya kaita museum da kuma art gallery suka shiga super market yayi mata shopping, suka hau dogon gini yana nuna mata kasa yana murmurshi, tayi baya da sauri ya kama hannunta yana murmurshi, a waje sukayi both sallar zuhr da Asr...
Bayan sun dawo ta barshi da Sa'ud a parlor ta wuce sama, ta fad'a bathroom ta jima sannan ta fito tayi applying cream ta juya tana kallon kofar closet din sai kuma ta mike ta wuce ciki tayi still tana kallon kayan, wata doguwar gown ta zaro ta saka, ta fito ta zauna a gefen gado tayi zuru...
Ya shigo yayi still yana kallonta saying,
"Wow... You looks beautiful...".
Arfaat tayi murmurshi kawai, Lamido ya shiga bathroom, ya jima sannan ya fito yana daure da towel a kugu, kallo daya mashi bata k'ara dagowa ba har ya gama shiri...
Suna gama sallar Isha'i tayi bacci, ta barshi zaune yana aiki akan system...
Washegari bayan sun gama sallar subh ta koma bacci, a hankali ta bude idanunta wadanda suka sauka akan wani k'aramin flame dake a gefen gadon, ta mike zaune tareda duro kafafunta a kasa, ta dauki hoton tana gani, yarinyar ce...
Takonsa ta jiyo daga bayanta ya k'araso tareda zama a kusa da ita yana kallon flame din yace,
"She is your daughter... Little Arfaat... Sunnanku daya... Ni kuma kamarmu daya... Kin ganta kin ganni kamar kobo da kobo...".
Arfaat kallonshi take da mamaki ganin hankalinsa a kwance yake dangantata da yarinyar da ya haifa da wata mace daban out of wedlock, yarinyar da ya haifa ba tareda aure ba (that's according to her base on karyar da Aljannun sukayi mata), shiyasa taga sunanta akan kamfaninsa, ashe diyarsa yake nufi...
Lamido yace, "Kije kiyi wanka zamu fita... Yau beach zamuje... Zaki hau yacht ki zagaya a teku...".
Arfaat ta mike yayinda tafiyarsu akan wannan ruwan ta fad'o mata a rai, tana fitowa ta tarar ya zaro mata doguwar riga, veil with hat, saida ta shirya tsaf sannan ta fita ta sameshi zaune a parlor yana kallon News, ta zauna a daya daga cikin kujerun ya mike saying,
"Muje...".
Yaja mata kujera ta zauna sannan yayi serving dinta, yayi serving kansa sannan yaja kujera ya zauna, suka gama ta mike ta wuce parlor ta zauna akan kujera tana kallon television din yayinda shi kuma ya tattara abubuwan da suka b'ata ya wuce dasu kitchen ya wanke ya fito ya wuce sama jim kadan ya sauko yana sanye da wando wanda ya wuce gwuwa kadan tareda t-shirt marar kauri, ya mik'a mata hannunsa ta kama ya mik'ar da ita suka fita....
Yawo sukayi sosai a gab'ar ruwa yana nuna mata abubuwa suna murmurshi, suka sha kankana, suka hau yacht yana yawo dasu a cikin ruwan yayinda da kanshi yake tuka yacht din....
Arfaat tayi tsaye a wajen karfe tana kallon cikin ruwan yayinda abubuwa da yawa suke dawo mata a kwanya....
Lamido ya k'araso inda take da glass cup akan hannunsa ya tsaya a bayanta yana mata magana yana murmurshi....
Saida dare sannan suka koma gida, sukayi sallar Isha'i sannan suka kwanta....
Washegari da safe, can cikin barci ta soma jiyo nishi tareda kakarin amai, ta mike zaune sai kuma ta duro daga saman gadon ta wuce bathroom....
Lamido ne a durkushe yana kwarara amai, ta duka tana mashi sannu, ya gama ya mike ya fice yana tafiya yana tangadi, ta gyara bathroom din ta fito ta sameshi kwance akan gado yana rawar sanyi, ta dauko bargo ta lullub'a mashi, duk ta rude ta rasa yadda zatayi dashi, ta soma hawaye tana kallon yadda yake rawar sanyi, ta janyo wayarsa sai kuma taga lock, ta k'arasa inda yake tace,
"A garkame wayar take...".
Lamido ya bude baki dakyar yace,
"Kece...".
Arfaat tayi jim sai kuma ta rubuta sunanta akai, gani tayi wayar ta bude, ta shiga contact tayi searching Sa'ud sunan da taji yana kiransa dashi, ta danna mashi call, yayi picking saying,
"Salaam alaikum... Good morning sir...".
Arfaat ta fashe da kuka saying,
"Bashi da lafiya sai amai yake yi... I'm scared... He's sick...".
Sai kuma ta cire wayar daga kunnanta ta durkushe a gabanshi tana hawaye, jin motsi a parlor ta mike ta wuce closet ta saka doguwar gown ta yane kanta da veil, ta fito, knocking taji tace,
"Yes... Come in...".
Sa'ud ya shigo cike da girmamawa yace,
"Good morning Ma...".
Arfaat ta gyad'a mashi kai, ya k'arasa wajen Lamido ya sunkuya yana mashi magana sai kuma ya mike ya fita, jim kadan ya dawo tareda doctor ya dubashi tareda saka mashi drip, bacci ne yayi awon gaba dashi....
Throughout the day yana bacci, tana zaune kusa dashi, Sa'ud ne ya kawo mata both breakfast and lunch, kadan taci ta ajiye sauran, ta damu sosai akan halin da yake ciki....
Gab da sallar Magrib ya farka aka cire mashi drip yayi wanka ya rama sallolin dake a saman kanshi....
Bayan sallar Isha'i Sa'ud ya wuce, Arfaat ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata half gown ta fito ta dubeshi taga yana kwance ne a daya bangaren, ta zagaya daya bangaren ta kwanta, ta takure a waje daya tana jinta uncomfortable, bacci ne yayi awon gaba da ita, bacci yayi mata dadi ta haura inda yake ta haye samanshi tareda rukunkumeshi, a hankali ya bude idanunsa yayinda baki daya jikinsa ya soma rawa, ya burkitata tareda soma mata wasu abubuwa, cikin bacci ta soma jin ana yamutsata ta bude idanu da sauri tana k'ok'arin kwacewa amma ta kasa, ta bude baki zata fasa ihu, ya rufe bakin, ta ware idanu tana wiki-wiki dasu, abun ne ya soma b'ata tsoro ganin yana niyyar yayi mai gaba daya, ta fizge bakinta ta fasa k'ara, da sauri ya saketa ya koma gefe, ta takure waje daya tana kuka...
Lamido ya kunna wuta saying,
"Arfaat stop crying, babu abun da zanyi maki... I'm sorry...".
Arfaat ta fasa k'ara tareda juya baya ganin a yadda yake, da sauri ya janyo bargo ya rufe jikinsa....
Arfaat ta kasa had'a idanu dashi, ya mike ya wuce bathroom jim kadan ya fito ya kwanta akan sofa, ta mike ta wuce bathroom ta jima sannan ta fito ta haye saman gado tareda lumshe idanu....
Washegari, an tashi ne da labarin bayyanar hotunan Lamido tareda Arfaat, sanannan mai kudi wanda yayi b'atan damo aka rasa inda ya shiga yayinda na kusa dashi basu bada wani kwakwkwaren bayani ba, sai gashi an wayi gari da hotunansa tareda wata mace a kasar waje, hotunansu guda ukku ne suke yawo, daya an daukeshi ne a lokacin da suke yawo akan titi, daya a gab'ar ruwa yana rik'e da hannunta, daya kuma suna tsaye a yacht yayinda yake a bayanta yana rik'e da glass cup, cikin k'ank'anin lokaci hotunan suke yaduwa yayinda aka saka alamar tambaya akan wacece wadda suke a tare....
Nan da nan maganar ta soma trending, en nema suka soma maida yadda a kai yayinda mata suke ganin wautar matarshi har tayi sake wata tayi mata wuff da miji, aka rink'a maganganu a kai, wasu gani suke ai dama Baraka bata kai ba koda sune shi da gudu zasu zabi waccen, maganganu iri daban-daban...
Arfaat tana zaune akan sofa ta lumshe idanu, ji tayi Lamido yace,
"What, how's that possible?".
Sai kuma ya janyo wayarsa ya kira numbar Sa'ud, yace,
"Sa'ud... What is this? How is that possible?".
Arfaat ta zuba mashi idanu, saida ya gama dogon turanci yana bin ba'asin abun da ya faru sannan yace,
"Send me Abeed's phone number now...".
Hanging call din yayi....




Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[28/03, 19:25] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 21 to 22

Lamido yayi dialing numbar Abeed, tana soma ringing yayi picking saying,
"Hello... Who's on the phone?".
Lamido yace, "Abeed...".
Abeed yace, "Lamido... Yau tunda safe nike samun kira babu kakkautawa saidai kashe wayata nayi...".
Lamido yace, "Abeed mun sha wahala ne sosai kafin mu kub'uta, Arfaat bata cikin hayyacinta kuma duk ta rame idan suka ganta a haka hankalinsu zai tashi ne shiyasa na tsaya da ita a nan ta k'ara murmurewa...".
Abeed yace, "How's is she?".
Lamido yace, "She's fine...".
Abeed yace, "Alhamdullilah... Congratulations...".
Lamido yace, "Thanks... About hotunan kayi masu bayani akan itace matata ta farko sannan ka basu hotunan bikinmu...".
Abeed yace, "Sure... Ango... Ango...".
Lamido yace, "Huh... Ammi sun sani kuwa?".
Abeed yace, "Babu wanda bai sani ba...".
Lamido yace, "Okay bara in kira Maimoon ta hadamu video call... Ka turo min numbarta...".
Sun jima suna magana sannan yayi hanging call din....
Lamido yayi dialing numbar Maimoon, tayi picking saying,
"Salaam alaikum...".
Lamido yace, "Wa alaikissalaam...".
Maimoon ta fasa k'ara saying,
"Ammi... Yaa Lamido ne... Yaa Lamido ya kira...".
Lamido ya dafe kai saying,
"Maimoon ki nutsu, kije sashen Abbi zanyi maku video call...".
Hanging call din yayi, ya juyo facing Arfaat yace,
"Kije kiyi wanka ki sauya kaya zamuyi waya da gida...".
Arfaat ta gyad'a kai tareda mikewa ta shiga bathroom ta jima sannan ta fito ba ya bedroom din sai kayan da ya ajiye mata akan gado, tayi applying cream tareda gyara fuskarta ta shirya cikin doguwar rigar da ya ajiye mata, ta taje dogon gashinta ta tattarashi ta saka ribbon, ya shigo yana sanye da farar riga da trouser yana saka cufflinks mai adon diamond, looking handsome and breathtaking, ya k'araso inda take tareda sunkuyawa ya saka mata sarkar diamond, dan kunne and bracelet, ya hade gefen fuskarsa da fuskarta da murmurshi akan fuskarsa yace,
"Perfect match... Made For Each Other...".
Yaja hannunta suka wuce balcony, ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita, ya ajiye wayar akan table dake a gabansu sannan ya danna masu video call, Ammi da Abbi tareda Maimoon ne suka bayyana....
Maimoon ta fasa k'ara saying,
"Arfaat... Alhamdullilah...".
Lamido yace, "Ke miye haka zaki fasawa mutane kunne... Ammi barka da warhaka... Abbi Ina wuni?".
Ammi tace, "Barkanmu...".
Abbi yace, "Lafiya lau...".
Arfaat tace, "Ammi... Abbi... Ina kwananku... Maimuna... Hi...".
Maimoon tace, "Hi...".
Ammi tace, "Lafiya lau... Sannu kinji... Allah ya kiyaye gaba... Allah ya tsare... Alhamdullilah kin kub'uta...".
Abbi yace, "Allah ya k'ara tsarewa...".
Arfaat tace, "Amin, Na gode... Allah ya k'ara girma...".
"Amin...".
Abbi yace, "Lamido mi yasa baka sanar damu ba bayan kasan tun tafiyarka muke a cikin zullumi, shekara daya ake magana, watanni goma sha biyu...".
Lamido yace, "Bamuyi sati da samun kanmu ba, mun sha wahala ne sosai duk ta rame shiyasa na tsaya da ita a nan idan ta k'ara murmurewa sai in tafo da ita...".
Ammi tace, "Kadda ka manta ka kira gidansu ku gaisa, hankalinsu a tashe yake...".
Lamido yace, "In shaa Allah... Little Arfaat?".
Maimoon tace, "She's sleeping...".
Ammi tace, "D'azun ta gama rigima ta kwanta...".
Lamido yace, "Little Arfaat... My other half...".
Abbi yace, "Ta k'ara wayo da girma idan ka ganta zakayi mamaki...".
Lamido yace, "Maimoon ki tura min hotunanta ta what'sApp...".
Maimoon tace, "Okay...".
Abbi yace, "Yaushe ne dawowarku?".
Lamido yace, "Akwai abun da zanyi attending a Shanghai... Italy... India... Daga can zamuzo...".
Arfaat mamakinsu take ganin yadda suke magana cike da farin ciki akan yarinyar nan, sun jima sannan yayi hanging call din, yayi video call gidansu Arfaat....
Ummy da Abba ne zaune akan kujera tareda Nabila....
Arfaat ta fashe da kuka saying,
"Ummy... Abba... Nabila...".
Nabila ta fashe da kuka saying,
"Angel...".
Ummy ta share hawayen da suka zubo mata tace,
"Arfaat... Kece... Alhamdullilah... Lamido na gode sosai... Allah ya saka maka da alkhairi...".
Lamido yace, "Amin... Ummy ki daina kuka bana son ganin hawayenki...".
Ummy tace, "Son... Kukan farin ciki ne...".
Lamido yace, "Abba Ina wuni... Barka da warhaka...".
Abba yace, "Barkanmu... Sannu kaji... Mun gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi... Arfaat sannu kinji... Allah ya kiyaye gaba... Finally you are back...".
Arfaat ta goge hawayen da suke a fuskarta tace,
"Ummy... Abba... Nabila...".
Sai kuma kuka yaci karfinta, Lamido ya juya yana mata magana a kunne saying,
"Ki daina kukan ko kuma in datse kiran...".
Arfaat ta goge hawayen dake a fuskarta saying,
"Na daina... Nabila kece kika koma en mata... Ina Sultan?".
Nabila tace, "Sultan yana London karatu... Nima wannan shekarar nike gama sekondire...".
Arfaat ta ware idanu saying,
"Are you serious? Koda yake shekaru shidda kenan...".
Ummy tace, "D'azun kuwa Safnah tazo gidan nan tana ganin hotunan tazo...".
Arfaat tace, "Safnah... My other half...".
Sun jima sannan yayi hanging call din, yace,
"In shaa Allah... Gobe zamu wuce Shanghai...".
Arfaat ta gyad'a kai....
**********
Tun bayan da Abeed yayi bayani akan abun tareda sakin hotunan auren Arfaat da Lamido, tun daga nan labarin ya sauya salo, ya soma trending fiye da before, Arfaat da Baraka the difference is clear, banbancin a bayyane yake, koda makaho ya laluba zaiji, da yawa mamaki suke ta yadda Lamido yana da zureriyar mata kamar Arfaat amma har ya k'are da mata ta biyu kuma mai KAMMANin Baraka, wasu suce watakila bata mashi abun da yake so ne, da yawa suna ganin wautar Arfaat da kyanta da komai tana da miji kamar Lamido har ta yadda yayi mata kishiya, hotunan bikinsu ne suka rink'a yawo tareda hotunanta wadanda aka dauka shekaru shidda da suka wuce, hotonta da na little Arfaat ya rink'a yawo ana cewa itace uwarta....
*******
Da daddare, Arfaat ce zaune akan gado tana bincike akan system sai a lokacin take ganin abun da ya faru, ta rink'a cin karo da hotunanta tareda hotunan bikinsu, wasu suna sukarta cewa tayi sakaci anyi mata wuff da miji, saying tayi rakiyar mata ce da har ta bari mace mai kamannni irin Baraka ta aure mata miji, ta girgiza kai kawai mutane basu san yadda abu yake ba amma sai su zage suyi ta maida yadda aka yi, tayi still tana kallon hotonta da na Little Arfaat sai kuma ta tab'e baki ta kashe system din ta ajiye akan bedside table ta kwanta tareda jan blanket, wato wannan shine dalilin kiran gida da yayi da kuma maganar komawarsu....
Washegari bayan sun gama breakfast suka shirya, halcofter ne ya daukesu daga villa din zuwa airport daga nan suka hau private jet dinsa zuwa Shanghai...
Lamido yana zaune akan kujera ya daura kafa daya akan daya yana sirfing abu a glass cup, yayinda yake duba system, lokaci zuwa lokaci yana picking call....
Arfaat kallonshi take

Please Login or Register in order to submit comment