Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dasu ta fashe da kuka saying,
"Sun kassara min diya, ashe fatalwa suka mayar da ita, my poor girl...".
Lamido ya girgiza kai saying,
"Ummy wacce kika gani ba Arfaat bace... Aljana ce, kuma musulma ce, sunanta Maryam, tana zuwa ne a siffar Arfaat...".
Shima ya kwashe dukkanin abun da ya faru a wancen ranar ya sanar dasu....

Safnah tace, "Tabbas biri yayi kama da mutum domin shekaru biyar da suka wuce a lokacin hidimomin bikin sai Arfaat ta rink'a razana tana cewa tana ganin wata mai KAMANNI da ita, har a football day take sanar dani cewa ta bayyana a gareta ta kuma hanata buga kwallon domin a cewarta idan ta buga kwallon zata lula ne zuwa sararin samaniya wanda kuma zai zama kamar tarwatsa bikinta ne har ta nuna mata samfuri ta hanyar buga kwallon kuma a take kwallon tayi sama ta lula a sararin samaniya, shiyasa a lokacin ta shafi kwallon kawai da kafarta, itama kuma maryam tace sunanta...".
Lamido yace, "Ummy na b'oye maku wannan al'amari ne saboda bana son in tayar maku da hankali... Abbi wannan shine dalilin da yasa na nuna bana son auren nan saboda matata tana a raye, Arfaat tana a raye, amma tunda yanzu gaskiya ta bayyana... Please ka janye maganar auren Baraka...".
Abba yace, "A'a... Lamido, babanka ya fika gaskiya, dole kayi aure, ba zamu zuba maka idanu jiran wacce bamu san ranar bayyanarta ba... Idan ta dawo sai ta zauna da abokiyar zamanta kamar yadda wayancin mata suke tunda ba'a kanta aka soma ba, kuma ba haramun bane...".
Lamido ya kama hannun Ummy yana girgiza kai saying,
"Ummy ki saka baki kiyi masu magana kadda suyi min auren da bana so, kadda su saka inyi wa matata kishiya, kadda su saka inyi wa Arfaat kishiya...".
Ummy ta girgiza kai saying,
"Lamido sun fika gaskiya, ya kamata kayi aure....".
Lamido ya kwantar da kanshi a saman gadon saying,
"Arfaat... Bana son inyi mata kishiya...".
Ummy ta soma bubbuga bayanshi saying,
"Kaifa mijin mace hudu ne... Halak ne... Ka ganni nan tare dani za'ayi hidimar bikin nan, babu ruwana... Nice babbar uwar ango...".
Dukkanin wanda yake dakin saida yayi dariya...
Lamido ya amshi little Arfaat dake kuka, ya nuna mata Ummy saying,
"She's also your granny, your mother's mom...".
Little Arfaat tace, "My mom...".
Lamido ya nuna mata hoton Arfaat, yace,
"She's your mom... Tayi tafiya amma zata dawo wata rana...".
Little Arfaat ta soma wangale baki tana dariya, yayi kissing kumatunta....
Two hours later aka yi discharging Ummy suka wuce gida....
*************
Ammi tace, "Lamido, furniture da kayan Arfaat dake waccen gidan zuwa yanzu ya kamata ace ka bari an kwashesu...".
Lamido kamar zaiyi kuka yace,
"Amma Ammi idan na gansu ina tunawa da ita ne...".
Ammi tace, "Amma bazai yiyu suyi ta zama a gidan nan ba, koda ta dawo ba amfani zatayi dasu ba, ka bari a kwashesu tun yanzu da suke da sauran moriya...".
Lamido yace, "Mallakinta ne, bani da ta cewa a nan...".
Ammi tace, "Then...".
Ta janyo wayarta ta dannawa Ummy call, bayan sunyi exchanging greetings tace,
"Dama akan kayan Arfaat ne dake a wancen gidan, nike ganin ya kamata ace an kwashesu tun da koda ta dawo ba amfani zatayi dasu ba...".
Daga daya bangaren Ummy tace,
"Idan akan wannan ne ai ba sai kin kirani ba, bani da iko a kansu, Lamido shine mijinta shine yake da cikakken iko a kansu, kome yayi bamu da ja a kai...".
Ammi tace, "Torh shikenan, na gode, a gaida gida...".
Ta ajiye wayar saying,
"Tace duk yadda kace haka za'ayi...".
Lamido yace, "Da lefen da furnitures din a dauka a bayar dasu a inda ba zanci karo dasu ba amma zanje inyi parking abubuwan da zan ajiye mata...".
Ammi tace, "Alright...".
Lamido ya mike tareda little Arfaat a kirjinsa, direct ya wuce gidan, ya rink'a bin gidan da kallo da damuwa kwance akan fuskarsa, shine gidan da suka shirya rayuwa a ciki amma gashi zai kyautar dashi ba tareda sun samu memory ko daya a ciki ba....
Saida ya saka little Arfaat bacci sannan ya soma parking abubuwan da zai ajiye mata wadanda suka had'a da hotunanta da sauransu, bayan ya gama ya sakasu a backseat ya wuce dasu sabon gidansa ya bude part dinsa wanda yake gari guda, ya sakasu a wani empty room....
Sai bayan sallar Isha'i sannan ya koma gida yana dauke da little Arfaat wacce tayi bacci abunta, direct bedroom din Ammi ya wuce ya tarar tana bathroom, ya ajiye Little Arfaat akan gado sannan yayi relaxing akan sofa tareda lumshe idanu....
Jim kadan Ammi ta fito saying,
"Lamido yanzu na gama jajen Little Arfaat nace ko Ina kuka makale...".
Lamido ya bude idanunsa saying,
"Muna gidana, ta samu kayan wasa tayi zamanta...".
Sai kuma ya mik'a mata makullin wancen gidan saying,
"Na dauke abubuwan da zan ajiye mata, Ammi har gidan na bada...".
Ammi tace, "Allah ya amfana... Zan saka a duba wanda yake cikin buk'atar gida sai a bashi...".


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 8

*Nace Ba, Mub'Ash Tace Ita Take Son Setin Akwatun Da Gidan, Hajeer Beauty Tace Ita Take Son Gida, Torh Ku Zama Shaida Na Rigasu Kamun Gidan, Ita Mub'Ash ta hakura Da Akwatuna kawai, Ita Kuma Hajeer Sai Tayi Manage Da Furniture... Zahra Ki Isar Mamu Da Sako Wajen Mai Girma Lamido Idan Yaso Sai Hajeer Ta Hakura Ta Baki Kayan Kitchen...* 😂😂😂
*Nace Ba, Team Arfaat R, Ya Da Haka, Bikin Sunan Little Arfaat Kun Shiga Hidima Amma Munje Bikin Baraka Kun Barmu A Gantale Muna Kallon Dajaja Tana Kallonmu Amma Babu Wanda Zai Bamu... Ku Rage Kishi, atorh, Naga Dai Hudu Aka Ce, Suyi...* 😂😂😂

Lamido yace, "Abbi yana kirana zanje idan na dawo sai in dauketa, tayi dinner already...".
Ammi tace, "Alright...".
Lamido ya fita heading to Abbi's part....
*************
Abeed shine tsaye akan bikin, Lamido's busy taking care of his business and his beloved daughter Little Arfaat, tun bayan da free weeding pictures suka fita akan the young billionaire Lamido zaiyi aure maganar take trending, mata da yawa suna kishi da Baraka ne ganin zatayi wuff da dream husband dinsu, there crush, wasu suna ganin tayi sa'a sosai, wasu kuwa gani sukeyi bata kai nan ba domin kuwa sun fita kyau da komai...
Maganar cewa matarshi ce ta biyu shine ya k'ara hawar da farashin zance, mutane suna mamaki ashe dama yana wata matar, wasu suka ari zance aka rink'a maida yadda aka yi akan matarshi ta farko wacce har tayi sakaci da diamond dinta za'a mata wuff, yadda maganar take yawo har hira aka yi dashi abun da bayyana kawai shine yana da wata matar sannan kuma Baraka zata zo ne a matarshi biyu....
Masu son ganin kwaf sun kasa sun tsare domin ganin wacece matarshi ta farko wacce tayi sakaci har zai k'ara aure, wasu har habaici suke mata saying ta rako mata ne, saidai babu hotunanta babu wanda yasan a inda za'a sameta....
Netizen suka rink'a maida yadda aka yi, maganar ce tayi ta trending throughout the week, Baraka ta zama cele...
Lamido yace babu wani party da za'ayi saida aka matsa mashi sannan ya yarda za'ayi Dinner ranar Friday, itama Baraka friends evening kawai zatayi a ranar Thursday, lefe akwatuna ashirin aka kai wanda sosai yaja hankalin mutane aka soma magana ana maida yadda aka yi, tuni both gidajen suka zama busy with the wedding preparations, kai lefe, ganin daki, jere, and the rest....
Part guda ya ware mata aka saka kayanta yayinda shi kuma a part dinsa bedroom din little Arfaat yake....
On Thursday Baraka tayi friends evening....
The following day evening,
Tuni motoci suka fara jerangiyar zuwa katon hall da za'ayi dinner din, gate pass kanshi wahala yake, guest ne sosai har da abokan kasuwancinsa na kasashe daban-daban, mutane ne sosai har da wadanda ba'a gayyata ba saidai suci birki domin masu gate pass ne kawai suke shiga, haska komai ake wa duniya domin aure ne na attajiri wanda yayi fice a duniya baki daya (Ni da Soffi muka sha kwalliya amma aka hanamu wucewa 😭 saboda Arfaat da zata bamu gate pass bata nan, gashi a book 1 munce babu mu a Team Baraka 😉🤔🙄🤣 haka muka kwasho kafafu muka koma gida 😭 saura kuyi mamu dariya ,😒😒😒😏)....
The groom is nowhere to be found...
Lamido ne kwance akan bed yayinda little Arfaat take tsalle a kanshi tana wangale baki suna dariya...
Abeed ne ya shigo fuskarsa a murtuke, yana sanye da wata expensive shadda brown, dinkin babbar riga, looking as abokin ango as he is, yace,
"Ashe a nan ka b'uya...".
Little Arfaat ta juyo tareda wangale baki tace,
"Uncle...".
Abeed yayi mata waving hand, yace,
"Lamido I'm talking to you, kowa ya shirya kai kadai ake jira...".
Lamido ya lumshe idanu saying,
"I'm tired...".
Abeed ya murtuke fuska saying,
"Ko ka tashi ka shirya ko kuma in kira Ummy in sanar da ita komai...".
Lamido ya bude idanu da sauri saying,
"Please mana, yanzu kuma so kake ka hadani da Ummy...".
Abeed yace, "Then ka tashi ka shirya mu wuce...".
Lamido ya b'ata fuska, ganin da gaske Abeed yake zai kira Ummy, ya mike ya mik'a mashi little Arfaat saying,
"Kace wa Maimoon tayi mata wanka ta shiryata akwai kayanta suna a saman gado...".
Abeed ya amsheta ya fice yayinda Lamido ya wuce bathroom, ya b'ata lokaci sosai sannan ya fito ya shirya cikin experience shadda fara wacce tasha aiki, ya murza hula tangaram kafafunsa rufe da cover shoes, ya daura expensive wrist watch akan tsintsiyar hannunsa, looking handsome and breathtaking, a parlor ya tarar da Abeed ya mike suka fice yana tsokanarshi, Lamido yayi mashi banza, a stairs suka hadu da Maimoon ta mik'a mashi little Arfaat wacce tasha kyau, Maimoon ta kafta masu selfie sannan ta matsa suka wuce....
Motar da suka shiga kanta abun kallo ce, Lamido dake a backseat yace,
"Abeed mu wuce kawai, mu hade dasu a can...".
Abeed yace, "No... Dole muje mu dauko amarya...".
Lamido yayi mashi banza, direct gidansu Baraka suka wuce, aka fito da ita tana sanye experience gown brown, with head, ta zuba jewelry, kafarta sanye da heels shoes, tana tafiya da murmurshi akan fuskarta, Abeed ya bude mata backseat yayinda wani kamshi mai sanyi ya doki hancinta, ta lumshe idanu ta bude tareda zuba mashi idanu ganin matuk'ar kyau da yayi, ji tayi yace,
"Ba zaki gaidani ba...".
Baraka ta kawar da kanta da sauri tana kallon henna dake akan palm dinta tace,
"Ina wuni?".
Ba tareda ya kalleta ba yace,
"Lafiya lau and please kallon ya isa haka, ina tare da diyata...".


Baraka ta dubeshi da sauri saidai bata ce komai ba, motar tayi parking, abokan ango ne da k'awayen amarya, a tsaye, kowanne sanye da anko, Lamido ya fito yana dauke da little Arfaat yana mata wasa suna dariya, ya manna mata kiss a kumatu da murmurshi akan fuskarsa, Baraka ta fito daga daya bangaren aka tattare jelar gown dinta suka jera suka shiga ciki yayinda abokansu suka mara masu baya, kida mai sanyi yana tashi tareda waka wadda aka rera domin wannan ranar....
Guest suka mike yayinda amarya da ango suka nufi hightable suka zauna aka soma gudanar da abubuwan da suka tarasu, Lamido's busy yana gaisawa da mutanensa ana daukar hotona, KAMANNI da yake yi da little Arfaat ya saka mutane ayyanawa a ransu cewa itace diyar uwar gida sarautar mata....
Aseeyerh da Maimoon with sauran siblings dinsa anko daban sukayi, k'awayen amarya suma ankonsu daban, Safnah, Naja'atu, Rufaida, Nabila da sauran Arfaat's relative suma anko daban sukayi....
Lamido da Baraka suka fito filin rawa yayinda aka saki sauti, k'awayen amarya suka fito suka cashe, abokan ango suka fito suka cashe, Lamido baiyi rawa ba amma Baraka tayi rawa sosai, Aseeyerh tareda sauran siblings dinsa suka fito suka cashe....
Safnah, Naja'atu, Rufaida, Nabila tareda sauran dangin Arfaat da suka zo suka fito sukayi liki suna takawa....
"Yanzu mahaifiyar uwar gida sannan kuma babbar uwar ango zata fito domin tayi masu liki...".
Ummy ta fito tareda k'awayenta suka masu liki, suma sun taka, can na hango Ummy tana rawa irin tasu ta manyan mata....
Tun ana maganar uwar gida ta fito tayi liki har aka gaji aka yi shiru, mutane sun zuba idanu domin ganin uwar gida sarautar mata saidai babu ita babu alamarta, netizen sun ci burin ganin wacece uwar gida (Kai muje yankan cake, ehe 🤣🤣🤣)....
Baraka ta yanko kadan ta saka mashi a baki, shima ya yanka ya saka mata, ya yanko kadan ya sakawa little Arfaat, ta amsa daga hannunsa ta saka mashi a baki, yayi kissing kumatunta da murmurshi akan fuskarsa yayinda aka shiga kashe masu picture (en gulma suna daga gefe suna yi da uwar gida saying shegen kishi ya hanata zuwa, ta son tana son mijin mi yasa tayi sakaci har aka yi mata wuff dashi)....
Komai cike tsari aka gabatar dashi har aka gangara serve yourself, (can na hango su o'e suna wawaso akan kaji wanda ba zasu iya k'arar dasu ba, nikam nace babu ruwan Angel, na kanfato na zuba a handbag idan na koma gida na had'a har da bones ehe, torh idan a can ne au da kunya aga Angel tana tauna bones 😏🤣🤣🤣).....
Saida suka sauke Baraka a gida sannan suka wuce, Maimoon ta amshi little Arfaat yayinda suka juya kan motar zuwa inda ya sauke bakinsa da suka zo daga kasashe daban-daban....
***********
Abba ya mik'awa Ummy wayar dake hannunsa saying,
"Miye wannan?".
Ummy tace, "Wajen dinner da zanyi masu liki...".
Abba ranshi a b'ace yace,
"Shine kuma aka ce da girmanki with shekarunki kije kina rawa...".
Ummy tace, "Alhaji, naga Lamido ba ya son auren nan ne shiyasa nayi haka domin in nuna mashi ina farin ciki da auren...".
Abba yace, "Shikenan kuma sai aka ce kiyi gyara da b'arna...".
Ummy tace, "Kayi hakuri, In shaa Allah hakan bazai sake faruwa...".
Abba yace, "Better...".
Ummy tace, "Gobe zan leka gidan bikin tareda su Hajiya Rahama...".
Abba yace, "Okay amma kadda in k'ara ganin abun da na gani yau...".
Ummy tace, "In sha Allah...".
The following day gari ya dauki harama, ya cika da mutane en daurin aure kasancewar Lamido mutum ne sananne sannan kuma mutum ne na mutane, manyan motoci ne ta ko'ina, ga private jets da suketa shawagi....
Karfe sha biyu da rabi aka daura auren Abdurrahman Munner (Lamido) tareda Amaryarsa Baraka Ahmad, daurin auren da ya samu halarta dumbin jama'a wadanda babu wanda yasan adadinsu....
Lamido yana sanye ne da farar shadda dinkin babbar riga yana gaisawa da mutanensa ana daukar hotona, reception aka yi immediately, daga nan Lamido ya sulale ya wuce daya daga cikin gidajensa ya kira Maimoon ta kai mashi little Arfaat tareda abinci....
Karfe hudu daidai aka kawo amarya gidansu Lamido har da Ummy cikin en karbar amarya daga nan aka wuce da ita gidan da ya gina wanda yake katon mansion gari guda, iya kallon mai kallo, iya hasashen mai hasashe....
Team Arfaat R, suna ta tab'e baki anyi wa Arfaat bukulun zama ita daya a gidanta...
Bacci ne yayi awon gaba da Lamido da Little Arfaat, da daddare ya girka masu abinci suka ci suka kwanta....
Aka bar Abeed da hidimar k'awayen amarya wadanda zasu kwana a gidan...
Washegari a gidansu Lamido aka yi walima, inda aka gwangwaje dangin ango da kaya na alfarma su kuma suka bada tukwuci, aka watse tareda shirya amarya aka mayar da ita, tun besties dinta suna jiran zuwan ango har suka gaji kowacce ta kama gabanta....
Baraka tayi zuru tana jiran tsammani, babu Lamido babu alamarsa, ji tayi kuka ya tafo mata, ga abubuwan da aka rink'a dura mata, ta rasa yadda zatayi da kanta....
********
Lamido ne kwance ya daura little Arfaat a saman cikinsa tana wasa, wayarsa ya janyo ya kunnata kamar jira ake kira ya shigo, Abeed ne, sai a lokacin ya tuna da Baraka, har ga Allah ya manta da ita, yayi picking tareda kangawa a kunne, yayi jim sannan yace,
"Ina gidana dake kofar marusa with little Arfaat... Ina son hutawa ne... Naji zanje yanzu... Bye...".
Yayi hanging call din tareda duba lokaci wanda ya nuna karfe goma da rabi na dare har ya gota...

WhatsApp 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)
*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 9

Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion, Complete 600, 9169472057, Aisha, Opay Digital Service

Lamido ya mike ya dauki little Arfaat suka wuce sama, saida yayi shower yayi mata wanka sannan ya shirya cikin wani expensive yard fari ya murza hula, tareda zura expensive takalma slippers, ya feshe jikinsa da designer perfumes, ya shirya little cikin riga da wando, saida ya ajiyeta a daya bangaren sannan ya zagaya bangaren direba ya danna horn mai guard ya wangame mashi get ya danna motar waje, a nutse yake tuki, yayi tafiya kadan yayi parking a bakin wani get, ya zaro wayarshi yayi dialing call yayi jim sannan yace,
"Gani a bakin get... Ban san mita, or else in tafi babu shi... Alright...".
Babu jimawa Abeed ya fito yana dauke da manya-manyan leathers guda biyu, ya bude backseat ya saka mashi sannan ya zuro kai saying,
"Ango...".
Lamido yace, "Whatever...".
Little Arfaat ta washe baki saying,
"Uncle...".
Abeed yayi mata waving hand saying,
"Little...".
Lamido yace, "I'm leaving...".
Abeed yace, "Good Night... Ka gaida amarya...".
Lamido yayi mashi banza yaja motar ya dauki hanyar sabon gidansa, yayi horn mai guard ya wangame mashi get ya danna motar ciki, ya wuce get na farko, ya wuce get na biyu sannan ya shiga farfajiyar gidan, yayi parking motar a jerin motocinsa dake a parker, ya dauki little Arfaat da daya hannunsa yayinda yake dauke da leathers guda biyu da daya hannun....
Direct ya wuce bangarenta, da salaam ya shiga parlor ya haura sama ya tarar da ita a bedroom dinta tayi kuka har ta gode Allah, tana zaune a tsakiyar gado, ya zauna gefen gadon saying,
"Amarya...".
Sai kuma ya zare veil dake a saman kanta saying,
"Welcome to Lamido's house...".
Ya ajiye mata leather guda daya saying,
"Here you go, kaji ne da yoghurt with ohh na manta, cox bani na siya ba... Kici kafin ki kwanta, ga namu nan ni da little Arfaat...".
Ya mike heading out while saying,
"Good night and sweet dreams...".
Ya fita tareda ja mata kofa ya wuce sashensa, ya zaunar da little Arfaat, ya zaro leather, kaji ne guda biyu tareda yoghurt sai kuma fried rice wacce tasha vegetables, yana feeding dinta tana gocewa tana saka mashi a baki, har suka koshi, ya zuba mata yoghurt tasha ya wuce da ita bathroom yayi mata wanka da brush, ya kwantar da ita tana mashi rigima yana biye mata suna dariya, bacci ne yayi awon gaba da ita, ya wuce bathroom yayi wanka sannan ya kwanta.....
A bangaren Baraka, ture leather din tayi ta kwanta hawaye takaici suna bin idanunta har baccin wahala yayi awon gaba da ita....
***********
Arfaat ce takure a waje guda, ta k'ara ramewa daga ganinta tana cikin damuwa, suna tsatsaiye a gabanta, a tare suka fashe da dariya, daya daga cikinsu yace,
"Gwara ki daina b'ata ranki akan bil'adama wanda yana can ya dade da mantawa dake... Yayi aurensa ya manta dake...".
Arfaat ta dubeshi da sauri, yayi mata nuni zuwa wani kutse, a take hoton Lamido ya fito a wajen dinner da kuma daurin aure, tace,
"What... Baraka?".
Yace, "Dan haka ki manta dashi kiyi amfani damu ki shayar damu b****d domin mune kawai muke sanki a duniyar nan...".
Da sauri ta toshe kunnuwanta saying,
"No... No... No...".
Ji tayi an cire mata hannun daga kunne ba tareda taga wanda ya cire ba, ya fashe da dariya sannan yace,
"Dukkanin danginki da k'awayenki, da familynki suna murna ne da wannan auren kuma zamu nuna maki zahiri...".
A take wajen dinner ya bayyana aka nuno Aseeyerh tana rawa with smile on her face, aka nuno Safnah, Naja'atu, Rufaida, Nabila, suna zagaye ango da amarya suna rawa, ta kalli Lamido taga murmurshi ne akan fuskarsa, Sultan yana masu like....
Ta fashe da kuka saying,
"K'arya ne...".
Bata rufe baki ba aka nuno Ummy tana rawa a wajen dinner, ta fasa k'ara, Ummy wacce bata rawa itace take rawa a wajen bikin mata kishiya, it can't be, aka nuno Abba a wajen daurin aure a matsayin wakilin Ango...
Ta mike tareda fasa k'ara, suka fashe da wata mahaukaciyar dariya, saida sukayi mai isarsu sannan suka tsagaita, wata murya mai amo tace,
"Tun daga familynki, k'awayenki, relative dinki, da masoyinki wanda kika kwallafa rai a kanshi duk sun manta dake koda kin koma ba zasu amsheki ba domin sun gama yarda da cewa ke aljana ce, mune kadai gatanki a yanzu don haka kiyi kamar yadda muke so ki rayu a cikin daula...".
Arfaat ta fasa k'ara saying,
"K'arya kuke...".
Tayi luu saidai gani sukayi ta zube kasa a sume....
************
Kiran sallar subh ne ya farkar da Lamido, kasancewar little Arfaat bata cika tashi fitsarin dare ba, ya gyara mata kwanciya....
Arfaat duplicate ce ta soma gizau ta bayanshi saidai bai lura da ita, ya duro daga saman gado ya zura takalma slippers heading to the bathroom saida ya sakarwa kanshi shower sannan ya dauro alwalla ya zura farar jallabiya, ya wuce sashen Baraka ya samu tana kwance, ya k'arasa tareda buga pillow....
Baraka ta mike zaune tana kallonshi da idanunta da sukayi luhu-luhu, da mamaki yake kallonta yace,
"You look... Did you cry? Anyway ki tashi kiyi sallah, we will talk later...".
Ya juya heading to the door, Baraka ta bi bayanshi da kallo, ta mike ta wuce bathroom....


Lamido ya fita compound ya shiga daya daga cikin motocinsa yayi mata key heading to the first gate, mai guard ya wangame mashi get ya danna motar waje, to the nearest Masjid dake akan road din, ya jima zaune yana azkar sannan ya fito ya shiga motarsa heading to the mansion, yayi parking ya wuce sashensa, little Arfaat tana kwance kamar yadda ya barta, yana duba abu a system bacci yayi awon gaba dashi....
Baraka tayi wanka tareda shiryawa cikin wasu riga da skirt en kanti, na yane kanta da veil, ta zauna a falonta tayi zuru tana jinta kamar ba amarya ba (Ni kuwa nace ai saida ya fad'a maki gaskiya amma kikayi burus da hakan saying you can take it and it appears that you can't, wetin concern me tukun, na gudu tun kafin team baraka suyi ball dani, atorh aww na manta ashe ni da Hajeer mun koma team Baraka, kuma idan Baraka ta haihu zamuje ranar soye😏🙄🤔)....
Maimoon one of his sibling ce tayi parking motarta ta fito tana dauke da basket, tbubu ce a jikinta tayi rolling veil, tana taking steps tana duba wristwatch, ta danna bell...
Baraka ta mike tareda duba wani k'aramin screen dake akan bango, Maimoon ta gani, daga nan ta bude lock din....
Maimoon ta shigo tana k'arewa falon kallo, ta ajiye basket din tareda zama akan kujera tana duba wristwatch, call ne tayi parking, tace,
"Besty ku jirani da motata na fito sai in biyo in daukeku mu wuce... Alright... Bye...".
Baraka ce ta sauko da smile akan fuskarta saying,
"Maimoon...".
Maimoon ta d'ago saying,
"Morning, Aunty Baraka...".
Baraka tace, "Morning Maimoon kin tashi lafiya, how's Ammi and everyone?".
Maimoon tace, "They're all fine... Alhamdullilah... Breakfast ne Ammi ce in kawo maku...".
Baraka tace, "Mun gode...".
Maimoon ta mike saying,
"Sauri nike ina da lectures, kulle venue yake... Bye... Yaa Lamido fa?".
Baraka tayi jim sai kuma tace,
"Ya koma bacci...".
Maimoon tace, "Okay, ina gaidashi, send my regard to Little...".
Ta juya ta fice ta fad'a motarta ta danna mata key....
Baraka ta dauki basket din tareda dropping akan dinning table wanda yake a dinning room, ta fita heading to his part, ta danna bell babu respond, and she didn't have access to his pin, tayi dialing numbarsa ba ya picking, ta juya ta koma sashenta....
_9:00AM_
Little Arfaat ta farka ta soma mintsinin idanu, tsallenta takeyi akan gadon saying,
"Abbana... Wake up... Haske yayi...".
Lamido ya bude idanu tareda janyota yayi hugging, ya manna mata kiss a kumatu saying,
"Good morning, Angel...".
Little Arfaat tace, "Good morning, Ab bana...".
Text message yayi sending wa Baraka na passcode dinsa, ya dauki little Arfaat ya wuce bathroom...
Sai bayan mintina sha biyar sannan Baraka ta lura da text message dinsa ta mike heading to his part, yunwa takeji sosai, ta d'aure ne kawai domin ta jirashi, ta danna passcode ta shiga tana k'arewa sashen kallo, babba ne sosai, gari guda, ta wuce sama to the bedroom da take jiyo gwarancin little Arfaat, tayi salaam tareda knocking....
Little Arfaat tana zaune akan sofa tana sirfing tea da bread....
Lamido dake aiki akan system yana sirfing coffee yace,
"Wa alaikissalaam... Yes, come in...".
Baraka ta shiga, ta kalleshi yana sanye ne da dogon trouser with riga mai wani

Please Login or Register in order to submit comment