Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Complete 500
6. Ba Ni Da Laifi Complete 300
7. Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion complete 600

9169472057
Aisha
Opay Digital Service

Sai a tura shaida via WhatsApp 09169472057 Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel)


💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)


Page 3

*Alhamdulillah... I'm back...*


Arfaat tace, "Shine kika sato...".
Aljanar ta bushe da dariya sannan tace,
"Na dauko dai domin in ciyar da diyarta sannan kuma shugabarmu...".
Arfaat ta fasa k'ara saying,
"Ni ba shugabarku bace, Ni ba mallakinku bace, I have nothing to do with you...".
Aljanar ta fashe da dariya saying,
"Kodai kici abincin nan ko kuma mu dandanawa dabbobin dake cikin garken can yunwa tareda azaba wadda zata zama aljalinsu....".
Arfaat tayi mata wani mugun kallo sannan ta kalli garken, ta dauki abincin ta soma ci, a koda yaushe suna mata barazana ne dasu suna sakawa taci abinci dole...
Aljanar ta fashe da wata mahaukaciyar dariya sannan ta b'ace while saying,
"Hutawarki lafiya ya ke shugabarmu....".
Arfaat tana cin abinci tana hawaye tana tuna halin da ahalinta da masoyanta tareda Lamido zasu shiga a sanadin rashinta na tsayin shekaru hudu, tana mai tambayar kanta, shin yaushe ne zata kubuta, ta wace hanya, shin waye zai kub'utar da ita....
***********
Lamido ya shirya cikin experience shadda dinkin kaptain ya murza hula tangaram, ya zura takalma slippers tareda b'alle cufflinks, ya saka wristwatch, ya feshe jikinsa da expensive perfumes, ya fice yana taking steps to parlor yaba Ammi side hug, saying,
"Na gama shiri, inyi breakfast din...".
Ammi tace, "No... Idan kaje gidansu Arfaat sai kayi, mahaifiyarta zataji dadi...".
Lamido ya mike saying,
"Alright then...".
Ammi tace, "Allah ya kiyaye hanya... When zaka dawo?".
"Not sure because wani abun zai iya tasowa, I'm leaving, take care...".
Ya fice yana mata waving hand, direba ya bude mashi backseat, Lamido yayi jim sai kuma yace,
"Bani makullin idan na gama zan kiraka ka dauki motar a airport...".
Direba ya rusuna tareda mik'a mashi makullin, ya bude mashi frontseat ya shiga tareda danna horn mai guard ya wangame mashi get, ya danna motar waje, yana driving a nutse heading to gidansu Arfaat....
Ummy tana zaune a balcony tayi zuru fuskarta dauke da damuwa, yayi parking mota ya fito yana k'arewa gidan kallo yayinda abubuwa masu yawa suka dawo a kwanyarsa akan Arfaat da kuma soyayyarsu har zuwa ranar aurensu wadda ta juye ta zama ranar bakin ciki a garesu, ya k'arasa inda Ummy, kanshi a kasa, yace,
"Ummy Ina kwana... Barka da warhaka...".
Ummy ta goge hawayen da suka gangaro daga idanunta tace,
"Lamido idonka kenan, rabonka da gidan nan kusan shekara guda kenan...".
Lamido yace, "I'm sorry ma...".
Ummy tace, "Idan akan abun da ya faru da Arfaat ne kadda ka saka komai a ranka, idan na kalleki na kanji farin ciki ne a raina tunawa da akwai aurenka a saman kanta, you are the perfect son in-law da kowanne iyaye suka fatarwa y'ay'ansu... Kai kenan saidai dukkanin bayan wani lokaci muga alert da sakon ni, ba a hakan kawai ake neman albarka ba, zuwanka yana da muhimmanci...".
Lamido yace, "In shaa Allah hakan bazai sake faruwa ba...".
Ummy tace, "I hope so, ka shiga ciki akwai abinci akan dinning table na girka favorite din Arfaat...".
Lamido yace, "Sure...".
Ya shiga parlor, Ummy ta bishi da kallo yayinda hawaye suka zubo mata tunawa da diyarta Arfaat wacce aka rabata da ita tsayin shekaru hudu har yanzu babu ita babu alamarta, tana raye ko ta mutu basu sani ba....
Maid ne sukayi serving dinsa yana ci yana tuna matarshi Arfaat, bayan ya kammala ya mike ya wuce upstairs to her bedroom, ya murda handle ya shiga, dakin yana nan kamar yadda yake shekaru hudu da suka wuce, babu abun da ya sauya, ya dauki hotonta dake akan bedside drawer yana kallo yayinda hawaye suka gangaro a saman fuskarsa, ya ajiye heading to the balcony ya fice ta backdoor, ya koma inda Ummy take, inda ya sameta tana hawaye, fuskarsa dauke da damuwa yace,
"Ummy bana son ganinki a cikin damuwa, ki kwantar da hankalinki, ki rage sakawa kanki damuwa, In shaa Allah Arfaat tana a raye kuma zata dawo garemu a cikin koshin lafiya, nayi maki alkawari idan har muka san inda take a ko'ina ne a fad'in duniyar nan, kome hatsarin dake tattare da wajen zanje da kaina in buk'atar da ita sannan in dawo maki da ita... Gashi babu yawa a saka mamu albarka...".
Ummy ta kalli damin kudin da ajiye mata tace,
"Na gode, Allah ya albarkaci kasuwancinka... Allah ya bayyana d'iyata sannan kuma matarka Arfaat...".
Lamido yace, "Ameen...".
Horn ya danna mai guard ya wangame mashi get ya danna motar waje heading to gidanshi wanda mahaifinsa ya gina mashi 4years back domin ya zauna tareda Arfaat....
A bakin get yayi parking ya fito ya k'arasa a kafa, ya danna pin kofar dake a gefen get ta bude ya shiga yana bin gidan da kallo fuskarsa dauke da damuwa, ya shiga parlor furnitures da aka yi mata tun a wancen lokacin suna nan, babu abun da ya sauya, ya k'arasa upstairs to her bedroom wanda yake dauke da expensive bed, akwatunan lefenta and her belongings da aka kawo, shine ya hana a dauke komai saboda suna tuna mashi da ita ne...
Maryam ce ta bayyana a gareshi da KAMMANIN Arfaat, yace,
"Arfaat...".
Maryam ta girgiza kai saying,
"Ni ba Arfaat bace, Ni ba mutum bace, Ni alj*na ce, tun bayan b'acewar Arfaat nike bibiyarka domin in sanar da kai inda take saidai alj*nnun da suka saceta sunyi min katanga daga bayyana a gareka shiyasa wani lokacin nike maka gizau, na zabi in bayyana a KAMANNIN Arfaat ne saboda kadda kayi burus dani...".
Lamido ya k'arasa inda take da sauri saying,
"Ina Arfaat take... Ina matata take...".
Maryam tace, "Arfaat tana can a wani bangare na duniyar nan, tana a raye... Arfaat tana a raye... Zan taimaka maka domin ka kubutar da ita daga garesu...".
Kafin ta k'ara magana, wasu bakaken Alj*nnu suka bayyana suka daureta da sarkoki sukayi waje da ita, ta b'ace b'at, ya daina ganinta....

Lamido ya soma waige-waige yana nemanta saidai ta riga ta b'acewa ganinsa sun dauketa zuwa wani bangare na duniya, ya durkushe tareda fasa k'ara saying,
"Maryam... Kina ina? Kizo ki sanar dani a inda Arfaat take, zanje in kubutar da ita komai hatsarin dake tattare da hakan....".
Sulalewa yayi a kasa ba ya lumfashi, ta hanyar motarsa Abeed ya bi diddigi ya gano inda yake, yana zuwa ya sameshi a cikin wannan mawuyacin hali, hankalinsa ya tashi sosai, da gaggawa aka wuce dashi asibiti inda likitoci suka soma bashi taimakon gaggawa, babu abun da yake ambata sai....
"Maryam... Ina Arfaat take? Ina suka kaita? Ina suka kai matata?".
Bacci ne yayi awon gaba dashi, cikin kankanin lokaci Ammi da Abbi, Ummy da Abba suka iso asibitin, hankalin kowannensu a tashe, Ummy tace,
"Bawan Allah dazun nan yazo gida har nace mashi ya shiga ciki na dafa abun da Arfaat tafi so, ya shiga yaci har ya shiga bedroom dinta...".
Ammi tace, "Hakane, he suppose to be in Shanghai but never show up for his flight and he's nowhere to be found shine Abeed yabi diddigin motarshi ashe gidanshi yaje...".
Ummy tace, "Allah ya tashi kafadunsa...".
Ammi tace, "Amin...".
Lokacin da ya fardado babu abun da ya yake ambata sai sunanta....
"Arfaat... Arfaat... Arfaat...".
Ammi ta rike hannunsa saying,
"Son kayi hakuri, in sha Allah zata dawo garemu cikin koshin lafiya...".
Lamido yace, "Arfaat... Mariam...".
Ammi tace, "Wacece Mariam kuma?".
Lamido ya juya ganin Ummy a gefensa sai ya fasa furta abun da yayi niyya a maimakon hakan sai ya sauya jimlarshi saying,
"Ammi I'm confused... Ummy...".
Ummy tace, "Allah ya k'ara sauki... Allah ya bayyana matarka Arfaat...".
Lamido yace, "Amin... Ummy In sha Allah zan kawo maki diyarki Arfaat har gida a cikin koshin lafiya, in a good shape...".
Ummy tayi murmurshi tana mai gyad'a mashi kai, ta jima saida Abba ya dawo ya dauketa suka wuce gida....
Da daddare around eight Ummy ta koma ta kai masu abinci ta jima sannan ta juyo da yake a motarta ta tafi, fitarta asibitin yayi daidai da shigowar motar Mom, tana parking ta fito da gyalenta akan shoulder tana sanye da tbubu, direct ta wuce Vvip to the ward da akayi admitting dinsa, tayi salaam ciki-ciki sannan ta shiga....
Suka amsa, tace,
"Yaya Ina wuni... Ya mukaji da wannan abun, Allah ya bashi lafiya... Allah ya tashi kafadunsa... Banji labari sai yanzu da Aseeyerh ta kirana ta fad'a min har tace bata jima da tafiya ba...".
Abbi yace, "Amin... Hakane... Abeed bai jima da zuwa ya dauketa ba, zai sauketa a can gidanmu ne, yayi shirye-shiryen da zaiyi da yake shi zaiyi jinyarsa...".
Mom tace, "Ohhh ni murjanatu, Lamido ne ya koma haka, sannu kaji, Allah ya k'ara sauki...".
Lamido yace, "Amin Mom...".
Mom tana ganin Ammi amma tayi kamar bata ganta ba, Ammi tace,
"Hajiya Murja, sannu da zuwa...".
Mom tace, "Sannun dai, duk da ba'a gayyaceni ba, a gayyar sodi nazo wato gayyar nagayyaro, ace d'an brothernah bashi da lafiya amma ba za'a kirani a sanar dani ba har sai da Aseeyerh ta kira, da bata yi hankalin cewa ta kirani ba da shikenan sai mutan gari su rink'a z*gina suna cewa na yar da zumunci... Ina ce uwayen waccen Alj*nar yarinyar tunda abun ya faru suka zo har yanzu mahaifiyarta ta dawo tunda naga fitar motarta da zan shigo... A dai rink'a jin tsoron Allah...".
Ammi tace, "Ayi hakuri, I was carried away...".
Mom tace, "You most be carried away tunda a kaina ne, amma kinga su you are not carried away, dama an jima ana nuna min wariyar launin fata, thou dai a mahaifa daya muka zauna da ni da mahaifinsu, ni dolensu ce....".
Abbi ya fita already bayan da suka gaisa....
Mom taja kujera ta zauna saying,
"Sannu kaji Lamido, Allah ya k'ara sauki babana... Dukkanin abun da yake faruwa da kai iyayenka *SUNE SUKA JANYO MAKA...* suka had'aka aure da dangin m*tsafa, yarinyar nan dama nace alj*na ce amma aka k'*ryatani aka watsa min kasa a idanu ana ganin domin ina son ka auri diyata ne shiyasa, amma kaga daga karshe gaskiya tayi halinta tunda gashi alj*nun sunzo sun dauketa sun wuce da abarsu, thou wacce take sauya *KAMANNI...* (my previous novel duk wacce take son complete 400 ne kacal...) ai an riga an cuceka, yadda kake kullum da fara'a amma ka koma miskilin karfi da yaji...".
Lamido ya b'ata fuska tareda juya fuskarsa ta daya bangaren, Mom ta tab'e baki saying,
"Domin na fad'i gaskiya shine zaka b'ata fuska, ai dama har da kai aka had'a kai aka cuceka, ka mannewa waccen alj*nar diyar, ni dai gaskiya ce bazan gaji da fad'a ba...".
Abbi ne ya shigo ya zauna daga gefe yana kallonsa cike da tausayi, Mom tace,
"Yaya, ina ga kawai kuje sai in zauna a tare dashi har Abeed yazo tunda dama ban jima da zuwa ba...".
Abbi yace, "Alright then, Hajiya Bilkisu muje... Lamido, Allah ya k'ara sauki...".
Mom tace, "Amin...".
Abbi da Ammi suka fice, fitarsu yayi daidai da shigowar motar Abeed, yayi parking ya fito ya shige ciki yana dauke da k'aramar trolley, direct ya wuce ward din ya shiga da salaam akan bakinsa ya gaida Mom sannan yaja kujera ya zauna....
Mom tace, "Abeed, ya mai jikin?".
Abeed yace, "Da sauki...".
Mom tace, "Allah ya k'ara sauki...".
Abeed yace, "Amin...".
Mom tace, "Ya wajen d'iyata Aseeyerh?".
Abeed yace, "Lafiya lau...".
Mom tace, "Allah ya sauketa lafiya... Kuma zan fad'a maka gaskiya ka rink'a fad'awa abokinka gaskiya, tunda ya riga ya cuci kansa ya auri er m*tsafa ga kuma abun da ya faru, ka bashi shawara yazo yayi aure ya manta da wacce babu tabbacin zata dawo, amma saidai kuyi rufa-rufa domin iyaye kadan ne zasu yarda a had'a diyarsu kishi da Arfaat duk da kuwa bata nan, thou kadda ta dawo ta saka alj*nnu en uwanta su kassarawa mutane d'iya...".
Abeed yace, "Mom ai shekarar da ta wuce saida muka matsa shi and dakyar muka samu ya yarda zai auri Baraka amma kika hana, kuma tana sonsa...".


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰


💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)
*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 4

Kuyi joining, anan ne kawai zan rink'a tura books dina
https://chat.whatsapp.com/EeRiaTz6whEA7XHeWIVho6


Mom ta mike saying,
"Ba za'ayi haka dani ba, bazan had'a Baraka kishi da waccen yarinyar ba, tun usulin farko saida na fad'a masu gaskiya sukayi burus da ita, nace ya auri Baraka amma ya nuna waccen yarinyar yake so, sai kuma yanzu da abun da nike gudu ya faru sannan a dawo ace nima in jefa gudan jinina a tasko, ya dai je can wani gidan ya nemi aure muyi rufa-rufa ayi... Na wuce saida safenku...".
Abeed yace, "Hajiya Mom... Da girman kujerarki...".
Mom ta janyo handbag dinta ta fice saying,
"Babu wani dadin baki da zakayi min...".
Abeed ya matsa kusa da Lamido, yace,
"Lamido, mi ya faru?".
Lamido ya rufe idanu ya bude sannan yace,
"Abeed zan sanar da kai abun da ya faru saboda kai aminina ne, kuma abokina, d'an uwana na jini... Amma na rokeka da girman Allah kadda ka fad'awa kowa...".
Abeed ya gyara zama saying,
"In shaa Allah... I'm hearing you...".
Lamido yayi jim sannan yace,
"Wata alj*na ce tazo min a KAMANNIN Arfaat, ta sanar dani ita musulma ce sunanta Mariam, tun bayan b'acewar Arfaat take bibiyata tana son ta sanar dani inda take amma bak*ken alj*nnun da suka sac*ta sunyi mata katanga daga bayyana a gareni shiyasa bana ganinta amma tana tare dani, take min gizau most of the time... Arfaat tana a raye, sun b'oyeta ne a wani daji mai tattare abubuwan f*rgitarwa da h*tsarin gaske, saidai kafin ta sanar dani inda Arfaat take sai ta b'*ce b'*t na nemeta na rasa, ina kyautata zaton cewa sune suka dauketa domin kadda ta sanar dani a inda Arfaat take, daga nan ban k'ara sanin inda nike ba saidai ganina nayi akan gadon asibiti...".
Abeed ya jinjina kai sannan yace,
"Ka kwantar da hankalinka wannan alama ce ta nasara tunda mun san cewa tana a raye, in shaa Allah da sannu zamu san a inda take... Amma Lamido ya kamata kayi aure kamar yadda Mom tace...".
Lamido ya lumshe idanu ba tareda ya bashi amsa ba, Abeed yace,
"Da kai nike...".
Lamido ya bude idanu saying,
"What did you want me to say, last year kuka addabawa rayuwata kuka hanani sakat har saida na yarda zan auri Baraka amma daga karshe Mom tace bata san da zancen ba... Baraka ce kawai macen da zan iya aura saboda ta nuna tana sona tun a wancen lokacin, amma yanzu zaiyi wahala in gane wacce take sona saboda Allah, dukkanin en matan daka gani suna bibiyata suna yi ne saboda dukiyar dake gareni... And yanzu babu maganar aure a tsarina saboda na samu tabbaci akan matata Arfaat tana a raye kuma in shaa Allah zan san inda take, inje in kubutar da ita daga garesu... Good Night...".
Yaja blanket ya lullube, Abeed yayi murmurshi saying,
"Good night, duk da dai na avoiding maganata ne...".
Lamido ya rufe idanunsa saying,
"Whatever, kuma ka tabbata likita ya sameni gobe...".
Abeed ya ware idanu saying,
"Sati biyu zakayi...".
Lamido yace, "I see...".
****************
Mom tana komawa gida ta zube akan kujera tareda dropping veil da handbag dinta, maid ce ta kawo mata bottle water tareda glass cup ta tsiyaya ta mik'a mata, ta amsa tareda d'aga mata hannu, maid ta juya ta fita....
Baraka ta sauko daga stairs wearing black arebian gown, ta zauna akan kujera saying,
"Mom Ina bedroom na fito ban ganki ba, one of those maid tace min kin fita...".
Mom tace, "Ehhh na je asibiti ne...".
Baraka tace, "Waye babu lafiya?".
Mom ta taso mata saying,
"Ban sani ba, kin isheni da tambaya kamar wata er jarida, torh Lamido ne ba shi da lafiya kuma na san shegen nacinki shiyasa na wuce ban fad'a maki ba...".
Baraka ta dafe kirji idanunta a waje, tace,
"Na boni... Mi ya samu Yaa Lamido?".
Mom tace, "Oho, idan kinje ganinshi sun fad'a maki domin nidai bazan hanaki zuwa dubashi ba domin kadda ace na raba zumunci...".
Baraka tace, "Okay bara in tashi inje yanzu...".
Mom ta daka mata tsawa saying,
"Da daren ne, lallai na yarda baki san inda yake maki ciwo ba, torh Idan ke baki da hankali ni ina dashi... Karfen goman daren zaki saka kafa ki fita, baki isa ba... Kuma kiyi gaggawar cire sonshi daga cikin zuciyarki domin bazan tab'a yarda ki aureshi ba, kema ki gantale kamar yadda ya gantale, bazan cuci kaina da kaina ba...".
Baraka tace, "I can't stop loving him, zan aureshi koda hakan zai kasance sanadin aj*lina...".
Mom tayi mata wani mugun kallo sannan tace,
"Torh ni ba haka nike ba, tunda kin gama masters dinki ki gabatar da wanda zaki aura ko kuma in aurar dake ga dukkanin wanda naga ya dace koda kuwa baki sonshi...".
Baraka ta fashe da kuka tareda durkushewa kasa, saying,
"Please Mom... Don't do this to me...".
Mom ta murtuke fuska saying,
"Then ki gabatar min da wanda zaki aura, and Lamido's is excluded... Ki tashi ki b'ace min daga gani, kuma na baki sati ukku ki yanke shawara ko kuma in zab'a maki da kaina, ana fad'a maki gaskiya kina kaucewa... Ki b'ace min daga gani...".
Baraka ta mike ta wuce sama da gudu tana kuka, Mom ta bita da kallo saying,
"Aikin b*nza da wofi, ana fad'a mata gaskiya tana kaucewa...".
Washegari tunda safe, Baraka ta shiga kitchen ta soma had'a breakfast da zata kai asibiti duba Lamido, ta jima kafin ta gama, ta zuba komai a mazubi, ta saka a basket sannan ta koma bedroom dinta, ta fad'a bathroom ta jima sannan ta fito jikinta yana dropping ruwa, ta zauna a gaban mirror ta jima tana cancara makeup akan fuskarta wacce tayi suiting dinta looking good, ta shirya cikin experience leshe dinkin tbubu, ta zuba sarka da awarwaro, ta daura kallabi samfurin ture kiga tsiya, ta yafa veil, ta feshe jikinta da perfumes ta fice tana takonta a nutse, a parlor ta tarar da Mom tana kallon News, tace,
"Mom zan wuce asibitin...".
Mom ba tareda ta kalleta ba tace,
"Tun yanzu, torh ni dai bazan ce komai, babu dalili ki b'ata min rai da sanyin safiyar nan, kije... Allah ya kiyaye hanya...".


Baraka tace, "Amin...".
Mom tace, "Kinyi breakfast...".
Baraka tayi jim sannan tace,
"Idan naje asibitin zanyi...".
Mom ta tab'e baki ba tareda tace da ita komai ba, Baraka ta dauki basket ta fita, Mom ta tab'e baki a karo na biyu saying,
"Iska yana wahalar da mai kayan kara, wannan soyayya ko kuma wahalar da kai...".
**************
Around seven in the morning, Ammi da Abbi suka isa asibitin wanda yayi daidai da zuwan Ummy da Abba, kowannensu yana dauke da breakfast (both Ummy da Ammi), a tare suka shiga, Abeed ya mike tsaye yana mai gaidasu, suka amsa suna tambayarsa mai jiki....
Lamido ya bude idanu saying,
"Ammi... Ummy... Ina kwananku? Abba... Abbi... Ina kwana?".
A tare suka ce,
"Lafiya lau... Ya jiki?".
"Da sauki...".
"Allah ya k'ara sauki...".
"Amin...".
Bayan mintina ukku Abba da Abbi suka wuce suka bar Ummy da Ammi, Ammi ta zauna akan gado dake gefe, yayinda Ummy taja kujera a kusa dashi ta zauna, Lamido yace,
"Ammi, Aseeyerh fa?".
Ammi tace, "Zata zo ba da jimawa ba...".
Ummy ta dubeshi da damuwa sannan tace,
"Abdurrahman...".
Lamido ya maida hankalinsa a kanta jin ta kira aihinin sunanshi, yace,
"Na'am Ummy...".
Ummy ta lumfasa sannan tace,
"Lamido zuwa wannan lokacin ya kamata kayi aure, zamanka a haka ya isa...".
Lamido yace, "In sha Allah Arfaat tana raye...".
Ummy tace, "Fatanmu kenan amma bazai yiyu kayi ta zama babu aure ba, ya kamata kayi aure...".
Lamido ya rufe idanu ya bude yana tuna matarshi Arfaat, yace,
"Amma Arfaat fa?".
Ummy tace, "Idan Allah ya bayyanata sai ku zauna tare, ai halak ne, kuma bata isa tace bata zama da kishiya...".
Lamido yace, "Amma Ummy...".
Ummy ta katseshi saying,
"Ka nutsu sannan kayi tunani sosai akan maganar da nayi maka...".
Kafin ya bata amsa wayarta ta soma ringing ta janyo wayar tayi picking,
"Wa alaikissalaam... Hajjo... A gidana?... Lamido ne babu lafiya nazo ganinshi... A nan asibitin dake kusa da gidan Hajiya Rahama... Sure... Zan taho yanzu...".
Sai kuma tayi hanging call din, tace,
"Lamido, Hajjo tana maka ya jiki, tace zata shigo...".
Lamido yace, "Na gode...".
Ta mike saying,
"Torh, Lamido zan wuce tana jirana, Allah ya k'ara sauki...".
Lamido yace, "Amin...".
The more yake kallonta the more yake tunawa da matarshi Arfaat kasancewar suna shigen KAMANNI duk da Arfaat ta fita kyau nesa ba kusa ba, Ummy tace,
"Hajiya Bilkisu na wuce, Hajjo ce tazo tana jirana a gida...".
Ammi tace, "Mun gode, Allah ya saka da alkhairi, ki gaida gida...".
Ummy tace, "Amin... Ai babu komai, yi wa kai ne...".
Abeed ya dauko basket na jiya, Ammi tace,
"Ka juye na yau ka had'a dashi...".
Ummy tace, "A barshi, idan Sultan da Nabila sun zo anjima sai su tafi dashi...".
Ammi tace, "To shikenan, Ki gaida gida...".
Har mota Abeed ya kaiwa Ummy basket ta amsa ta saka backseat tana mai saka mashi albarka, ta shige mota saida ta share hawayen da suka zubo mata sannan taja motar ta dauki hanyar gida....
Ammi ta girgiza kai saying,
"Allah sarki... Hajiya Aysher tana cikin damuwa, daurewa kawai take tana nuna kamar babu komai, b'acewar d'iya kuma ace mace a wannan zamanin, tashin hankali ne babba...".
Abeed yace, "Musamman da ya kasance a ranar daurin aure abun ya faru, tana murnar zata aurar da diyarta, mintina biyar bayan daurin aure suka gudu da ita, ranar farin ciki ta juya ta koma ranar bakin ciki...".
Lamido yana jinsu amma baice komai ba....
Baraka tayi parking motarta ta fito tana gyara veil dake akan shoulder dinta ta zaro basket daga backseat tayi pressing makullin motar sannan ta wuce ciki, direct ta wuce ward da aka yi admitting dinsa kasancewar ta kira Aseeyerh ta sanar da ita numbar ward din, ta shiga da salaam akan bakinta, Abeed da Ammi suka amsa yayinda Lamido yayi mata kallo daya ya lumshe idanu....
Da murmurshi akan fuskarta tace,
"Ammi Ina kwana...".
Ammi tace, "Lafiya lau... Kin tashi lafiya...".
Baraka tace, "Lafiya lau... Ya mai jiki?".
"Jiki yayi sauki...".
"Allah ya k'ara sauki...".
"Amin...".
"Mom tana gaisheshi da jiki...".
"Yana amsawa...".
Baraka taja kujera a kusa dashi ta zauna saying,
"Morning Yaa Abeed...".
Abeed yace, "Morning Baraka...".
Baraka ganin idanun Lamido a rufe, tace,
"Is he sleeping? Yana bacci ne?".
Abeed yace, "A'a idanunsa biyu...".
Lamido ya bude idanu tareda galla mashi harara sai kuma yayi murmurshi saying,
"Sis baraka...".

What's App 09169472057
(Justice For Arfaat 🤣🤣🤣 Ummy tana son ta saka ayi mamu Kishiya 😱😱😱, kuyi hakuri mu tsaya a nan, bana jin dadi ne yau...).

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 5

*This Page Is Dedicated to you team Arfaat's R, FatimaZahra (Zahra Graphics), Hajeer Beauty, Sofiyya, Doctor Fateema, Ramsy Rahmat, sharhinku yana matuk'ar sakani farin ciki... Love you all...* 🥰😘😍


Baraka tayi murmushi sannan tace,
"Ya Lamido... Ya jiki... Allah ya k'ara sauki...".
Lamido yace, "Amin... Na gode...".
Baraka ta juya zuwa bangaren da Abeed yake, tace,
"Yayi breakfast kuwa?".
Abeed dake sirfing coffee yace,
"No... Coffee kawai yasha...".
Ta juya tareda janyo basket wanda ta shigo dashi tace,
"Here you go, zanyi serving dinka breakfast da na kawo maka...".
Tayi pressing bottom gadon da yake a samanshi ya soma tasowa ta wajen kanshi, ta soma bude foodflask saying,
"Da kaina na girka maka, kunun gero without sugar, chifs, farfesun kayan ciki, jelof couscous and wainar kwai...".
Lamido yana kallonta ne kawai amma idanunsa suna akan basket da Ummy ta kawo, Baraka ta juya tana kallon abun da yake kallo, ji tayi yace,
"Okay, kiyi serving dina wanda Ummy ta kawo...".
Ya k'arasa maganar yana mata pointing flask din, saida tayi jim sannan ta mike walking toward the basket, Abeed ya girgiza kai domin akan kunnanshi komai ya faru....
Baraka ji take kamar ta saki basket din a kasa komai ya tarwatse amma ta karfafa zuciyarta, ta zauna tareda serving mashi, chifs ne, farfesun kaji, wainar kwai sai kuma kunun gyad'a, sai kuma tea wamda yasha kayan kamshi, tana serving tana kallonshi saida ta zuba da yawa sannan ya dakatar da ita, ta janyo abun ta daura mashi plate tareda bowls tareda cups din a kai, yace,
"Thank you...".
Tace, "You are welcome...".
Ta yunkura zata mike yace,
"Ki zauna har in gama...".
Saida tayi jim sannan ta koma ta zauna ba tareda tabi ta kanshi ba ta janyo handbag dinta ta zaro wayarta ta zama busy tana pressing dinta....
Lamido yayi 1bite ya lumshe idanu yayinda smile yayi escaping akan lips dinsa yace,
"Delicious... Arfaat most like this...".
Har a kunnanta taji komai....
Abeed yace, "Sis Baraka nima ban yi breakfast ba, kiyi serving dina wanda kika kawo...".
Ba tareda Baraka tace komai ta janyo basket wanda tazo dashi tayi serving komai ta mik'a mashi, ya

Please Login or Register in order to submit comment