Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefen wandonsa ya gyara mata zama, kamar jira suke a lokaci guda suka yanyameshi, ya rink'a harbensu da kafa yana kai masu naushi a fuska tareda cakar wuyansu da wukar dake hannunsa, suka rink'a faduwa kasa warwas basa lumfashi amma sosai suka ji mashi ciwo domin babu b'ata lokaci suka galabaitar dashi, fuskar Arfaat ce ta dawo mashi a brain, yayi tsalle tareda bayyana a ysakiyarsu yana masu munanan raunika a wuya, ya addabesu yana nakasasu tareda kashesu, bayan mintina goma suka soma ja da baya baiyi yunkurin binsu, suka arta da gudu zuwa inda suka fito....
Lamido ya zube a kasa yana maida lumfashi, ya jima sannan yayi treating ciwukan da suka ji mashi, ya wanke jini dake a jikinsa, yayi alwalla yayi sallar zuhr, ya mike ya cigaba da tafiya daga nan bai k'ara haduwa da wani abu ba har lokacin sallar Magrib, ya yada zango tareda kafa tanti ya had'a woods ya kunna wuta, koda ya gama sallar Magrib yana zaune akan praying mat har yayi sallar Isha'i, yasha fruit da ya tsinka da safe ya kwanta, baccin two hours yayi ya tashi ya cigaba da jera nafila saida yayi sallar subh sannan ya kwanta bacci ne yayi awon gaba dashi har ya makara tashi da safe, ya mike zaune tareda yin mik'a ya wanke fuskarsa ya bazama cikin dajin ya farauto dabba ya dawo ya gasa yaci ya kora da ruwa ya mike ya tattara kayansa, ya goya jikkarsa ya cigaba da tafiya, tafiya kadan yayi ya hango wata katuwar macijiya tayi kwantan bauna tana jiranshi, cak ya tsaya, ta sulalo ta tsaya a gabanshi ta mike tareda wangame bakinta zata hadeshi yayi tsalle ya koma gefe ta cafki iska, ta juyo tareda k'ara kawo mashi sara ya sunkuya ya sulale ta kasanta, tareda zaro wuka ya kai mata sara ta kasa har yaji mata ciwo, wannan ne ya fusatata ta juyo tareda kawo mashi cafka yayi tsalle ya da ki wata bishiya ya dura a kasa, ta rink'a kawo mashi cafka yana tsallaketa kamar string, har mamakin yadda yake tsalle yake, duk yadda zata kawo mashi farmaki amma ta kasa koda lakutar jikinsa yayinda shi kuma ya addaba mata yaji mata naucika manya-manya, fusata tayi taja gefe tana kallonshi shima yayi cak yana kallonta, da dukkanin karfinta ta wangame baki tareda kawo mashi cafka, ya zuba mata idanu yayi tsaye kamar bazai kauce ba saida ta kawo kusa dashi sannan yayi tsalle yayi rolling a sama ya dura a samanta ya zaro takobinsa ya caka mata ya cigaba da ja har saida ya tsargata gida biyu, ta zube a mace, ya ja gefe yana maida lumfashi, ya zube a kasa yana maida lumfashi....
Saida ya huta sannan ya mike ya cigaba da tafiya wadda ta daukeshi wunin ranar sannan ya soma fita daga dajin, sanyi ya soma ji har cikin bargon jikinsa, ya dakata tareda yada zango ya kunna wuta....
Washegari da safe ya koma da baya ya tsinko fruit tareda farauto dabba ya gasa ya saka a jikkarsa sannan ya sauya kayanshi da kayan sanyi masu tudu sosai, ya saka takalman shiga snow, ya rufe ko'ina na jikinsa har fuskarsa, ya rufe idanunsa da wani farin glass mai madauri, ya rataya jikarsa ya nausa a cikin filin wanda yake dauke da snow, k'ank'ara ne ta ko'ina yayinda ruwan k'ank'ara yake sauka, yana tafiya yana fesar da iska mai tafowa da sanyi, yana dogara wani stick yana tafiya a cikin dussar k'ank'arar, dakyar yake d'aga kafafunsa saboda yadda suke nutsewa a cikin snow, ya hanga iya hangowarsa amma ba ya hango komai sai zallar k'ank'ara a fili wanda yake dauke da duwatsu babu alamar wata hallitta da ta wanku a wajen, saida ya daukeshi wuni yana tafiya sannan ya yada zango, ya kafa tanti ya kunna heater ya shige ciki, bayan ya gama sallar Isha'i ya kwanta bacci tareda dukunkunewa a waje guda, duk da heater da ya kunna da kuma barguna da yayi rufa dasu amma sanyi yake ji har cikin b'argonsa, a haka ya kwana ba tareda yaji dadin kwanciyar ba....
Washegari bayan yayi sallar subh yaci kadan daga fruit da ya tsinka ya kora da ruwa ya tattara kayansa ya goya jikkarsa ya cigaba da tafiya yana saka stick yana rawar sanyi, tsintar kansa yayi a saman wani dutse and is either ya koma baya wanda ba ya da tabbacin samun wata hanyar ko kuma ya sauka daga kasa, ya leka, daga inda yake zuwa kasa zurfi ne sosai, iya kallonsa, ya rik'e kugu yana tunani, ya zaro igiya ya saka a kugunsa ya fiddo adduna guda biyu na sauka daga tsauni, yana cakasu yana sauka idan ya gaji ya tsaya ya huta ya kora da ruwa ya cigaba da sauka saida ya shafe rabin wunin bai kai kasa ba ya yada zango a wani k'aramin kogo dake a dutsen, ya kafa tantinsa ya kunna heater, bayan yayi sallar Isha'i ya kwanta, bayan ya gama sallar subh ya zaro dabbar da ya gasa yaci kadan ya kora da ruwa ya mike tareda tattara kayansa, ya goya jikkarsa, juyowa da zaiyi yaci karo da wata wasu kartuwar dabba tana kallonshi, tayi wani sauti babu b'ata lokaci gungun danginta masu yawa suka bayyana, sukayo kanshi, ya juya ya falfala da gudu tareda sunkuyo kasa ya soma reto a cikin iska, yana kokarin cakar dutsen amma ya kasa, saida ya kusa kaiwa kasa sannan ya samu nasarar caka addar a dutsen, ya bugu dashi tareda sakin k'ara, ya sulale kasa a sume, sanyin dake shiga jikinsa ne ya farkar dashi ya mike zaune yana maida lumfashi saida ya huta sannan ya cigaba da tafiya, da daddare ya yada zango ya kwana, washegari ya dasa, zuwa wannan lokacin ya soma galabaita domin kuwa abincin da yayi guzuri da ruwansa ya soma kawowa karshe, komai nashi ya k'are, dakyar yake d'aga kafafunsa yana tafiya, wasu ruwa ya tarar wadanda k'ankara tayi blocking samansu, ya saka katuwar k'ankara ya fasa ciki ya zura sulkar ruwansa ya cika ya kwankwada sannan ya k'ara cikawa, ya had'a strap na kama kifi, ya zura a ciki, cikin ikon Allah ya rink'a kamo kifi yana tarawa har ya samu enough ya koma gefe ya had'a wood da wasu kananan itace da ya samu ya kunna wuta ya gasa yaci yayi gyatsa tareda godewa Allah madaukakin Sarki sannan ya mike ya cigaba da tafiya, gab da sallar zuhr yazo wani waje da ya kasa fahimtar yadda yake, a hankali yake taka kafafunsa yana kallon kasa abun da bai sani ba shine abun da yake zargi gaskiya ne domin kuwa a saman ruwa yake tafiya wadanda k'ankara ta rufe upper layer dinsu, kuma k'ankarar bata da karfi, kafin ya farga saidai ji yayi k'ankarar tana zaftarewa tana komawa ciki, cike da zafin nama ya soma falfala gudu saidai ya riga ya makara domin tuni inda yake ya zaftare saidai cintar kansa yayi a tsakiyar ruwan, ya dauke lumfashi tareda soma tasowa zuwa sama saidai kafin ya ankara wani katon kifi ya wurgar dashi gefe tareda kai mashi farmaki, Lamido ya ware idanu tareda iyo cike da kwarewa domin ceton ransa amma tuni ya k'ure mashi, ya kawo mashi cafka da baki ya goce tareda dira a samanshi, suka soma artabu yana jujjuyawa dashi har zuwa kasan ruwan, tun Lamido yana rik'e lumfashi har ya sare ya sakeshi, cike da zafin nama yayi tsalle sama ya cigaba da taka k'ankarar yana gudu yayinda kifin yake biye dashi yana fasa k'ankarar, Lamido yayi tsalle tareda durewa a nesa da ruwan ya zube a kasa yana maida lumfashi tareda tari wanda yake tafowa da ruwan da ya tuttula a ciki....
Saida ya huta sannan ya kafa tanti yayi alwalla yayi sallah yaci kadan daga cikin kifin da ya gasa sannan ya mike ya cigaba da nausawa a cikin tafiyarsa, sai gab da sallar Magrib sannan ya yada zango, washegari da safe ya dasa zuwa yanzu ya soma tarar da itace a cikin k'ankarar, ya zaro takobinsa yana tafiya yana observing around him, cak ya tsaya ya kasa kunne, wata katuwar dabba ta bayyana a gabanshi, and it seem like it's not alone, probably they hunt in group, kafin tayi wani yunkuri ya zaro wata k'aramar bindiga ya harba mata allurar barci ya juya ya soma falfala gudu saida ya fahimci he's safe sannan ya tsaya yaci abinci and then continue with the journey...
Saida duhu yayi sannan ya yada zango, gefin Magrib a cikin baccinsa ya soma jiyo wata k'ara, da sauri ya fito ya hango guguwa daga nesa, cike da zafin nama ya tattara kayansa ya goya jikkarsa ya soma falfala gudu babu ji babu gani, guguwa ce wacce take tafe da k'ankara tana shafe dukkanin abun da ya tarar a gabanta, duk da yadda yake falfala gudu da dukkanin karfinsa amma saura kadan k'ank'arar ta cin masa, cike da zafin nama ya janyo wani icce ya zauna ciki yana sulalewa dashi yayinda guguwar k'ankarar take dab dashi har iskan ya cimmashi amma yana nesa ne kadan da k'ank'arar wacce take rufe dukkanin abun da ta tarar, daga nan bai k'ara sanin abun da ya faru ba saidai farkawa yayi ya tsinci kanshi a tsakanin wasu itace duk da akwai sanyi a wajen amma babu snow....
Lamido ya mike zaune tareda dafe kanshi ya d'aga kanshi domin fahimtar lokaci, yayi alwalla yayi sallar zuhr and then Asr, yaci cikin kifin da ya kama ya kora da ruwa sannan ya bazama a cikin dajin wanda daga nan yana hango k'ankara ya yanki enough fruit, ya kama dabba ya gasa yaci ya cike sulkenshi da wasu ruwa ya saka masu abun da zai saka su kwanta kuma su tace and then continue with the journey, gab da sallar Magrib sanyin da yake ji ya soma raguwa yayinda ya gangaro kusa da sahara, a nan ya yada zango ya kwana....
Washegari ya nausa a cikin sahara, ya daura rawani a saman kansa yana mai rufe hancinsa yayinda iska ta tafo da yashi, a haka ya rink'a tafiya cikin sahara yana takawa a cikin yashi mai zafi yayinda rana take dukansa, sosai yake gabalaita sannan babu mafaka, saidai ya zaro fruit yaci ya kora da little drop na ruwa domin idan yayi sakaci suka k'are akwai issue domin duk iya hangensa bai hango wata halitta ta dabba ko shuka a wajen ba haka nan babu alamar ruwa a kusa, saida ya daukeshi kwanaki ukku yana ratsawa ta cikin sahara, baki daya guzurinsa ya k'are, ruwan da yayi tanadi suma saura kadan tun yana tafiya sannu a hankali har ya soma layi, ya zube a kasa yana rarrafe, cikin wani yashi mai nitsewa ya fad'a yayinda yashin yayi kasa dashi tun yana moving da hannuwansa yana k'ok'arin fitowa daga ciki har ya saduda yayinda yayi kasa ya nutse a cikin yashin har ba'a iya hangoshi....


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 15


Kamar fitar kibiya Lamido yayi tsalle ya fito daga cikin yashin tareda durowa a gefe yayinda wata katuwar halitta mai suffar kunama ta mara mashi baya, sukayi cirko-cirko suna kallon-kallo, addar dake a gefen kugunsa ya fiddo tareda gyara mata zama a hannunsa yana jiran kota kwana, wannan halitta tayo kanshi suka kacame da fad'a, yana sararta tana kawo mashi hari yana gocewa amma duk da haka sosai taji mashi ciwuka masu zurfi da jelarta saida ya daukesu mintina talatin suna artabu amma ta kasa kaishi kasa saidai ciwuka da taji mashi, ya galabaita sosai dama kuma babu karfi sosai a jikinsa saboda matsananciyar yunwa da kishirwa dake addabarsa, ja tayi da baya ta soma kawo mashi hari da jelolinta tana makashi da kasa saida ta had'a mashi jini da majina har yakai kasa warwas ba ya iya motsin kirki, ta tako inda yake ta wangame baki zata hadiyeshi, da sauri ya goce tareda zaro k'aramar wuka ya caki saitin zuciyarta tayi baya da sauri wanda ya bashi damar daka tsalle yayi rolling a sama tareda dura a saman kanta ya cake both idanunta, wata k'ara ta soma yayinda tayi kasa warwas a daidai wajen yashin ta nutse ba'a hangota....
Lamido ya mike dakyar yana tafiya yana faduwa yana tashi har yayi tafiya bai ankara ya soma gangarewa yana rolling a kasa, saidai ji yayi yayo kasa daga nan ya suma bai k'ara sanin inda kansa yake ba saida ya kwana ya wuni unconscious sannan ya farka yayinda ya tsinci kansa a kwance a gabar ruwa, yayinda iska yake kad'awa da ruwan suna tafiya tareda dawowa suna haifar da 🌊 wave, ya yunkura zai mike da sauri ya koma baya a sanadin zafi da yaji a kafarsa ya duba yaga ciwuka ne a jikinta yayinda tayi kunburi, ciwoka ne sosai a kafarsa, da rarrafe ya k'arasa ya kwankwadi ruwa tareda collection small dabbobin ruwa dake a gabar ya gasa yaci, ya rarrafa ya hado itace ya soma baiwa kanshi first aid, saida ya gyara ciwukan dake jikinsa sannan ya kama kafarsa tareda murd'ata ya gyara gocewar da tayi, ya saka itace tareda igiya da yayi da ganyen icce ya tamke kafar, a zaune waje guda ya kwana....
Saida ya daukeshi kwanaki biyu ba ya iya takawa sannan ya had'a stick da icce ya soma dogarawa, yana dogarawa dasu a both hannuwansa yana shiga cikin dajin dake kusa da ruwan yana tsinko abubuwan da zaici sannan ya dawo yaci yasha ruwa, yayi alwalla yayi sallah, wasu lokuttan kuma yana collection k'ananan dabbobin ruwa dake a gabar ruwan ne, ya gasa yaci, saida ya daukeshi kwanaki goma sha biyar yana jinya sannan ya murmure ya soma takawa da kafarsa....
Washegari ya nausa cikin dajin ya tsinko fruit sosai tareda farauto dabba, ya saro itace ya kawo ya ajiye yayinda yake amfani da itacen da igiya yana had'a kwale-kwale, tun daga wannan rana a kowacce rana zai shiga cikin dajin ya saro itace ya tsinko fruits da yawa sannan ya farauto dabba ya dawo ya adana domin wannan doguwar tafiyar dake jiransa don duk iya hangensa ba ya iya hango karshen ruwan, sosai ya tadani fruit, dabbobin dawa tareda k'ananan dabbobin dake a gabar ruwan, ya had'a guzuri sosai, a kowace rana yana cigaba da had'a kwale-kwale wanda zaiyi amfani dashi, saida ya daukeshi kwanaki biyar sannan ya kammala komai, ya loda kayansa tareda guzurinsa a ciki sannan ya wanke kayanshi ya kwanta....
Washegari da safe yayi wanka tareda sauya kaya yayi shirin cigaba da tafiya yayinda ya juya yana kallon dajin yana jin kewa a zuciyarsa, ya tura jirgin a cikin ruwan ya haye yayinda wave yajashi zuwa cikin ruwan, wave ne yake kad'awa da kwale-kwalen yayinda yake amfani da sandunan icce yana controlling direction da yake nufa....
Ya dauki tsayin kwanaki yana tafiya a cikin ruwan, idan yaji yunwa yaci abinci yasha ruwa, idan lokacin sallah yayi yayi alwalla yayi, tun yana da enough guzuri har ya k'are baki daya, saida ya saka abu yayi kamun kifi ko kuma ya cire kayansa yayi linkaya a cikin ruwan ya nemo kananan kifaye ya koma ya kunna wuta a kwano sannan ya gasa yaci, ya kwankwadi ruwa, ya galabaita sosai, yazo bangaren da koda yayi linkaya babu abun da yake samu saidai bakar wuya da yake sha, tun yana da karfin takuba wani abu har ya sare, yunwa ce take addabarsa kamar yaci babu, tun yana d'aurewa har ya sume....
A hankali ya bude idanunsa yayinda ya tsinci kansa a bakin wani tsibiri yayinda wave yake dauko ruwa yana dukanshi dashi, ya mike zumbur yana neman inda zai hango jirginsa, can gefe ya ganshi a cikin yashi, yana tafiya yana layi ya nausa a cikin tsibirin ya tsinki fruit yasha, ya dawo yayi picking small dabbobin ruwa dake a gabar ruwan ya dafa yaci, yayi linkaya a cikin ruwan, ya fito ya sauya kaya yayi alwalla sannan ya rama sallolin da suka riskeshi yana a sume, kwanaki biyu yayi a wannan tsibirin yana shiga ciki yana tsinko fruit tareda farauto kananun dabbobi ya gasa ya ajiye, saida ya tabbatar ya had'a enough guzuri sannan ya shiga kwale-kwale and the journey continue, ji yayi ya soma kewar gida tareda daukin haduwa da matarshi Arfaat, a kwana biyu yana tafiya a ruwan ya soma jiyo motsi kafin ya ankara wani katon kifi ya wintsilar da kwale-kwalen upside down yayinda dukkanin guzurinsa tareda abubuwan da ya tafo dasu suka tsine a ruwan except some da ya saka igiya ya dauresu da jirgin and his makamai dake a kugunsa....
Katon kifin ya kawo mashi cafka yayi nutso dashi a cikin ruwan saida yaji ya kasa lumfashi, dakyar ya sulale yayi sama tareda sakin lumfashi yana tarin ruwan da ya sha, ya hanga iya hangowarsa amma baiga alamar kwale-kwalensa ba, kafin ya ankara kifin ya k'ara kawo mashi hari har saida yaji mashi ciwo a gefen hannunsa na haggu, ji yayi ya fusata ya zaro mashi dake a jikinsa suka soma artabu yayinda yake cakarshi, amma sosai ya galabaita saboda fad'an a cikin ruwa yake....
Sunyi artabu sosai kafin ya samu nasarar cakar makasarsa ta hanyar shammatarsa ya zaro katuwar wukar ya caka mashi, yayo saman ruwan yana maida lumfashi tareda tari mai tafowa da ruwa yayinda kifin yayi kasan ruwan a matacce....
Lamido ya hanga iya hangensa ya juya kudu ya juya arewa, ya juya gabbas ya juya yamma amma babu kwale-kwalen babu alamarsa, yaja lumfashi tareda nutsewa a cikin ruwan amma still babu kwale-kwalen babu alamarsa, yayo sama yana maida lumfashi, da alama sunyi tafiya sosai a artabu da sukayi har yayi nisa wa kwale-kwalen sannan kuma bai san ta inda zaiyi domin nemansa ba saboda zasu iya shan banban....

Lamido's have no choice than yabi direction daya ya soma iyo yana nutsewa yana neman kwale-kwalen amma har dare yayi bai ganshi ba, abu ya janyo daga kugunsa ya saka a wuyansa yayinda wave yake janyi yana tafiya dashi a ruwan, saida ya daukeshi sati ukku yana tafiya a cikin ruwa, yana wondering, tun yana da kuzari har karfinsa ya k'are, ruwa kawai yake sha for the past three weeks babu abinci, suma yayi wanda daga nan bai kuma sanin inda kansa yake ba saidai farkawa yayi ya ganshi a wani tsibirin daban, ya d'aga kai dakyar ya rarrafa ya dauki fruit wanda ya fado a kasa ya soma ci babu ji babu gani, sai kuma ya dakata tareda dafe cikinsa ya soma kwarara amai, saida ya amaye baki daya abun da yaci sannan yayi lamo a kasa yana maida lumfashi, few minutes later ya dauki sauran yaci ya mike ya k'arasa a wajen ruwan ya saka hannuwansa ya tari ruwa yasha sannan yayi alwalla yayi sallah tareda fara rama sallolin dake a kanshi, ya jima zaune yana azkar sannan ya shafa addu'a ya mike, yana juyawa ya hango kwale-kwalensa can nesa dashi, yashe a cikin yashi, yayi hamdala tareda godewa Allah madaukakin Sarki sannan ya falfala da gudu yana duba jirgin duk da ya samu damage amma kadan ne, a kullum zai shiga cikin tsibirin ya tsinko fruit tareda farauto dabba, yayi itace ya dawo ya soma gyara kwale-kwalen, saida ya daukeshi sati guda yana had'a guzuri tareda rama sallolin dake a saman kanshi, tuni ya gama gyara kwale-kwalensa, ya had'a enough guzuri sosai ya had'asu ya saka a jirgin ya saka igiya ya daure komai tareda daurawa kugunsa igiya sannan ya daure da kwale-kwalen, ya turashi a cikin ruwan, ya haye and the journey continue saida ya daukeshi kwanaki biyar yana tafiya ba tareda ya samu damuwa ba domin yana da enough guzuri sannan yana samun nasarar kama kifaye ya gasa a kwano da kwano, ya k'ara sauka a wani tsibiri ya k'ara had'a guzuri sannan ya dasa, washegari ya tsinci kanshi a siririyar hanya wacce ruwan ya ratsa ta tsakanin kasa da duwatsu, motsi ya soma jiyowa daga cikin ruwan ya mike tsaye tareda rike takobi yana jiran ko ta kwana, wata katuwar kada ce tayi tsalle tareda kawo mashi farmaki ya daka tsalle ya fad'a a cikin ruwan yayinda kadar ta wawuri kwale-kwalen ta tarwatsashi into piece, Lamido ya zaro idanu yana ganin muguwar b'arnar da aka yi mashi, baki daya guzurinsa da komai dake a kwale-kwalen ya nutse a kasa, ya tsira ne kawai da makamai dake a jikinsa, kafin ya gama jimami kadar ta kawo mashi farmaki har taji mashi ciwo a hannun haggu, ya cigaba da artabu da ita da mashin dake a hannunsa, suna nutso a cikin ruwa suna dawowa sama, cike da zafin nama ya gama da kadar a cikin k'ank'anin lokaci, ya sauka a doron kasa, ya yada zango ya had'a itace ya had'a tanti ya nausa a cikin dajin yayi farauta ya dawo ya gasa yaci ya kora da ruwa...
Washegari, ya cigaba da tafiya, yayi tafiya sosai, yana haduwa da dabbobi wadanda basu farmakar mutane wadanda suka had'a da giwaye, zebra da sauransu, yana tafiya ne gefe-gefen ruwan yayinda ya dauko taswirar dake hannunsa yana mai tabbatar da bai b'acewa hanya ba, da safiyar wata rana yaci karo da kura, ta kawo mashi farmaki yayi tsalle tareda durewa a bayanta ya saka kafa yayi ball da ita saida tayi rolling a iska sannan ta fad'o a kasa, ta mike tareda girgiza jikinta ta k'ara kawo mashi hari, suka cakame da artabu, cikin k'ank'anin lokaci ya had'a mata jini da majina itama taji mashi ciwo amma kadan, ya k'ara ball da ita, ta juyo ta k'ura mashi idanu shima ya k'ura mata idanu yana mai zarosu, gani yayi ta juya ta wuce, ya zauna tareda jingina da wata bishiya ya gyara raunikan da yaji sannan ya mike ya cigaba da tafiya, saida ya dauki kwanaki shidda yana tafiya sannan ya kawo karshen kasar ya tarar da ruwa wadanda sune na karshe da zai tsallake ya shiga daji na biyar wato daji na karshe...
Ya yada zango, a kullum yana shiga dajin ya hado itace, ya tsinko fruit tareda farauto dabba, yaci ya ajiye na guzuri at the same time yana had'a kwale-kwale, saida ya daukeshi kwanaki ukku sannan ya kammala komai, ya had'a guzuri sosai, ya tura kwale-kwalen a cikin ya shiga ciki and the journey continue, kwanaki biyu yayi yana tafiya a cikin ruwan, a ranar kwana na ukku yana tsaka da cin abinci, wasu manyan kifaye guda biyu sukayo sama suna yin tsalle sama suna dawowa kasa duk yadda yaso kauce masu amma saida sukayi rugu-rugu da kwale-kwalen shima dakyar ya dure cikin ruwan, ya saka abu a wuyansa ya cigaba da iyo, ruwa kawai yake sha babu abinci, tun yana da karfi har karfinsa ya soma k'arewa, saida ya daukeshi sati biyu sannan ya soma hango kasa, dakyar ya k'arasa gaba, ya mike yana layi ya dauki wani fruit da ya sinkuyo kasa yaci kadan ya kwanta yana maida lumfashi, saida ya dauki mintina sannan ya k'arasa cinye sauran ya kora da ruwa, yayi alwalla ya tada sallah tareda fara rama sallolin dake a saman kanshi....
Saida ya shafe sati biyu yana shirya kanshi domin shiga wannan dajin, guzuri kadan ya had'a, ya yanko itace ya had'a iccen kibiya masu tsini da yawa, ya k'ara wasa wukakensa, ya k'ara wasa mashinsa and the rest, a lokaci guda yana k'ara baiwa kanshi horo saboda tashin hankali dake jiransa a dajin dake tako kadan daga inda yake wanda yake dauke da hatsabiban aljannu nau'ika daban-daban....
Washegari bayan yayi sallar subh ya jima a zaune yana azkar sannan ya shafa addu'a, ya nausa a cikin dajin ya farauto dabba ya dawo ya gasa yaci ya kora da ruwa sannan ya kimtsa takubansa, ya rataya jikarsa a bayansa, ya nausa a cikin dajin yana tunkarar daji na biyar wanda yafi dukkanin dazukan da ya baro a baya tashin hankali, ba ya da girma domin a cikin wuni guda daya zaka iya kaiwa karshensa amma tashin hankalin dake a cikinsa ya wuce tunani saidai abun da idanu suka gani....

SHIN MIYE ZAI TARAR A WANNAN DAJI MAI TATTARE DA HAD'ARURRUKA MASU YAWAN GASKE?
SHIN ZAI SAMU NASARAR ZUWA HAR KASHENSA?
SHIN

Please Login or Register in order to submit comment