Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin neck, smile ne yayi escaping akan lips dinta, tace,
"Good morning, heartbeat...".
Lamido ba tareda ya d'ago ba yace,
"Good morning... Kin tashi lafiya...".
Baraka ta zauna gefenshi saying,
"Lafiya lau, d'azu nazo baku tashi ba, Ummy ta aiko Maimoon ta kawo mamu breakfast, tana sauri zata wuce school bata tsaya ba...".
Lamido yace, "Okay, mun gode...".
Baraka tace, "About the breakfast...".
Lamido yace, "Kije zamu zo...".
Baraka tayi jim sai kuma ta mike ta mik'a hannu wa little saying,
"Zo muje...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a tareda turo baki, ji tayi yace,
"Ki barta, zamu zo...".
Baraka ta juya ta fita tareda koma part dinta zaman jiransu....
*********
Little Arfaat tace, "Ab bana... Who's she? Why's she in our house?".
Lamido ya d'ago tareda sakar mata murmurshi yace,
"She's my second wife, matata ce ta biyu, kishiyar Umminki...".
(Ni kuwa nace kishiya kuma babu ko sakayawa, torh nidai babu ruwana, koda yake, torh ya ake cewa in ba kishiya ba, kuzo ku bamu amsa ni da Lamido 😏🤣)....
Arfaat duplicate ta soma kawowa tana daukewa a bayan Lamido, little Arfaat ta zuba mata idanu tareda kallon hoton dake manne akan bango sannan ta juya ta kalli Arfaat duplicate, a hankali tace,
"Ummi... Ummina...".
Ta sauko daga saman kujera ta nufi inda take while saying,
"Ummi... Ummina...".
Da murmurshi akan fuskarta, saidai kafin ta k'arasa har ta b'ace b'at, Lamido ya juyo saying,
"Angel...".
Little Arfaat tace, "Ummi na gani a bayanka kuma ta b'ace na daina ganinta...".
Lamido ya ware idanu yana kallon bayanshi, ji yayi tace,
"Yaushe ummina zata dawo?".
Lamido yayi hugging dinta saying,
"Soon... In shaa Allah... Zata dawo mu rayu a tare a cikin farin ciki...".

WhatsApp 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

[06/03, 10:07] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*


Page 10

*Nace Ba, Hajeer Beauty Ki Fito Mu Gudu Tun Kafin Team Arfaat R Su Kamamu...* 🤣🤣🤣
*Na Tayaku Murna Lamido Yasan Inda Arfaat take... About the other thing sorry fa....* 🤣🤣🤣

Please pray for me, Allah ya biya mana buk'atunmu na alheri


Lamido yace, "Muje muyi breakfast...".
Ya fita heading to sashen Baraka yana dauke da ita, direct dinning room ya wuce yaja table ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita, Baraka ta dauki serving spoon tayi serving mashi sannan ta had'a mashi tea mai kauri....
Lamido yace, "Ita kiyi serving dinta kunun da kosai...".
Little Arfaat ta wangale baki saying,
"Yeah...".
Baraka tayi serving dinta ta ajiye mata plate tareda kofin a gabanta, Lamido yana feeding dinta suna dariya, Baraka tayi serving zata fara ci, Little Arfaat tace,
"Abbana... Wainar kwai...".
Lamido ya d'ago saying,
"Ki soya mata kwai...".
Baraka tayi jim domin yunwa takeji sosai sai kuma ta mike heading to the kitchen, babu abun da babu a ciki, cikin mintina kadan ta soya kwai ta kawo masu ta zauna ta soma breakfast, suna gamawa ya mike yana gogewa little Arfaat baki da tissue paper yace,
"I'm leaving, zan fita da little Arfaat outing... Sai mun dawo...".
Baraka tayi jim sai kuma tace,
"Now?".
Lamido yace, "Zanyi mata wanka ne in shirya...".
Baraka tace, "Ka barta a nan sai inyi mata wankan...".
Lamido yace, "No ba zata yarda ba, k'wuwa ne da ita kamar mi...".
Ya juya ya fice yana jan kumatun little Arfaat tana dariya, Baraka ta bisu da kallo, half hour later taji k'arar fitar motarshi alamar sun fita, ji tayi kuka ya tafo mata ta fashe da kuka, tayi mai isarta ta tattara abubuwan da aka b'ata ta wuce dasu kitchen ta wanke ta dawo parlor, babu jimawa aka kawo mata gara snacks, cincin, dubulan, nakiya, alkaki, man shanu da sauransu, ta kirashi ta sanar dashi ya aiko mata da kudi ta basu, en uwansu sun zo sosai wannan shine ya rage mata damuwar da take a ciki....
Lamido wuni yayi yana tunanin maganar little Arfaat na cewa taga Arfaat, wannan yana nufin taga Maryam kenan....
Bayan sallar Asr gidan ya koma saura Baraka ita kadai tayi wanka a karo na ukku ta cakare cikin riga da skirt na atamfa ta kashe dauri ta zauna a balcony tana zaman jiran dawowarsu saidai har aka yi kiran Magrib har zuwa bayan sallar Isha'i babu su babu alamarsu, lunch da dinner daga gidansu Lamido aka kawo wannan ya saka bata shiga kitchen saidai cousin dinsu da suka zo suka girka suka ci....
Har karfe tara da rabi ta koma parlor tana jiranshi har bacci yaci karfinta ta mike ta wuce sama ta fad'a akan gado, bacci ne yayi awon gaba da ita....
Washegari da sallar subh ya shigo ya tayar da ita kafin ya wuce Masjid, har tsayin kwanaki ukku Lamido bai kulata, harkokin gabansa yake tareda kula da little Arfaat wacce ta kasance wani bangare na rayuwarsa, a cikon kwana na hudu taji ba zata iya jurewa, dure-dure aka rink'a mata tana sha, ta kira wayarshi ta fashe da kuka, yana magana tayi burus dashi tana cigaba da kuka kafin tayi hanging call din....
Babu jimawa ya shigo hankalinsa a tashe ya mik'ar da ita zaune saying,
"Baraka... Mi ya faru dake? Why are you crying?".
Baraka ta tureshi saying,
"Kaine kake damuna and I'm crying because of you...".
Lamido ya ware idanu saying,
"Ni kuma... Mi nayi?".
Baraka tace, "Tunda aka kawoni gidan nan baka kulani ba, and sun dirka min abu cikina sai ciwo yake...".
Lamido ya zauna gefen gado saying,
"Amma Baraka saidai na fad'a maki gaskiya akan Arfaat ita kadai ce wacce take da gurbi a cikin zuciyata kuma koda na aureki ba zan iya maki adalci ba amma kikayi burus dani, kika ce zaki iya, yanzu ba'a kai ko'ina ba kin fara complain, wannan shine abun da nike guje maki...".
Baraka ta fasa k'ara saying,
"Ni dai cikina, wayyo...".
Duk ta rudashi, cikin mintina biyar komai ya faru, yana kwance a kanta yana yi yana ihu saying,
"Arfaat... Arfaat... Arfaat... I love you Arfaat...".
Yayinda Baraka take kukan azaba sannan kuma ga ciwon kiranta da yake yi da sunan wata, ta tureshi ta mike dakyar ta shige bathroom tayi locking dinshi tareda fashewa da kuka...
Daga wannan ranar babu abun da ya k'ara faruwa a tsakaninsu....
*************
Arfaat tana takure a cikin kogon tana binsu da kallo, tunda taga sun taru ta tabbata k'ara tada mata hankali zasuyi bayan abun bakin ciki da suka saka tayi witnessing....
A tare suka fashe da dariya sannan wata murya mai amo tace,
"Arfaat mun sanar dake Lamido ba ya kaunarki, bai tab'a sonki ba amma kikayi burus damu, torh a yau zamu nuna maki karin hujja wacce zata nuna maki cewa Lamido bake yake ba, jikinki yake so, yana tare da wata amma yana kiran sunanki tabbacin abun da yake tunaki saboda dashi kenan, don haka ki manta dashi, mune kadai muke sonki a duniyar nan...".
Arfaat ta fasa k'ara tareda rufe idanunta gam tana tsoron abun da zata ganarwa kanta, she don't want to witness anything like that, ji tayi idanunta sun bude kansu da kansu, sukayi mata nuni da katon dutse inda aka hasko komai b'aro-b'aro, Lamido ne aka nuno kwance a saman Baraka, yana yi yana ihu yana kiranta da Arfaat....
Arfaat ta kawar da kai yayinda sautin muryarsa yake sauka akan kunanta yana kiran sunanta a wannan yanayin saying,
"Arfaat... Arfaat... Arfaat... I Love You Arfaat...".
Ta fasa k'ara ta sulale kasa a sume bata motsi....


Some Days later,
Lamido ne zaune a katon ofishinsa dake a upper floor yana zana potrait din Arfaat yayinda Little Arfaat take zaune akan sofa tana wasa da teddy bear, Arfaat duplicate ce ta bayyana a gareshi saying,
"Lamido...".
Lamido ya d'ago da sauri saying,
"Maryam... Where's my wife? Ina Arfaat take? Ina matata take?".
Arfaat duplicate (that's Maryam) tace,
"A wancen lokacin sun kamani ne suka daure suka jefar dani a wani bangare na duniya amma cikin ikon Allah yanzu na kub'uta, kuma zan taimaka maka domin ka kub'utar da matarka Arfaat amma kafin nan kana buk'atar sanin yadda komai ya samo asali sannan kuma dajin da take a ciki, yana da matuk'ar hatsari, don haka kana buk'atar rike azkar sannan zaka koyi salo tareda dubarun yaki daban-daban domin k'are kanka daga namun daji wadanda zaka tarar akan hanyarka.... Zan koyar da kai Azkar sannan kuma zan koya maka dubarun yaki daban-daban wanda zai iya daukarmu wata guda daya don haka kaje ka shirya ka tanadi waje tareda abubuwan da ake buk'ata ni kuma zan fara baka horo daga gobe in shaa Allah, na barka lafiya...".
Sai kuma ta b'ace b'at, Lamido ya mike tareda sujjada ga Allah madaukakin Sarki, ya mike wanda yayi daidai da shigowar Abeed....
Lamido yace, "You...".
Abeed yace, "Ko baka yi murnar ganina bane ba...".
Lamido yace, "Ina cikin farin ciki ne saboda maryam ta bayyana a gareni...".
Abeed ya zauna akan kujera saying,
"Really?".
Lamido ya kwashe dukkanin abun da ya faru ya sanar dashi....
Abeed yayi murmurshi saying,
"Alhamdullilah... Allah shine abun godiya... Yanzu ya za'ayi?".
Lamido yace, "Zan kai little Arfaat ne wajen Ammi tunda tana yarda da ita, a cikin bangarorin dake a gidana zan ware waje guda daga can baya ta rink'a bani horo a can... About abubuwan da ake buk'ata kayi min order na kayan koyon yaki farare tareda sauran abubuwan da za'a buk'ata... And ka soma bincike akan kayan yaki wadanda zanje dasu zuwa can dajin...".
Abeed yace, "Sure Sir... Congratulations...".
Lamido yace, "You are welcome sir...".
A tare suka tab'a sukayi dariya, little Arfaat ta d'ago tana kallon Abeed da mamaki cox tana busy wasa bata lura da shigowarshi ba, tace,
"Uncle...".
Abeed yayi mata waving hand saying,
"Little... How are you?".
Little Arfaat tace, "I'm fine, ina wasa...".
Abeed yace, "That's good...".
Lamido yace, "Buddy can we...".
Abeed yace, "No I have some business here, zanga Hashim...".
Lamido yace, "Alright...".
Ya dauki little Arfaat suka fita a tare, yabi ta private elevator dinsa yayinda Abeed ya wuce ofishin Hashim, driver ya bude backseat Lamido ya shigar da little Arfaat sannan ya zagaya ta daya bangaren, suka dauki hanya....
Little Arfaat ta dauki littafin zane tareda color tana soma zane tana wangale baki a haka bacci yayi awon gaba da ita....
Lamido ya dauki drawing book din yana dubawa ta zana mace ne da namiji sai kuma karamar yarinya, ta rubuta _Abbana_ a daidai wajen namijin, ta rubuta _Ummi_ a daidai wajen macen sannan ta rubuta _Little Arfaat_ a wajen k'aramar yarinyar, ya bude daya page yaga ta zana mace ta rubuta _kishiyar Ummi_ ya ware idanu bai san lokacin da dariya ta kufce mashi ba....
Direct gidansu ya samu Ammi a parlor, da mamaki take kallonshi tace,
"You looks happy, daga gani kana cikin farin ciki...".
Lamido yayi murmurshi saying,
"Naga Maryam, akwai good news akan Arfaat's whereabout amma bari in kwantar da little Arfaat in dawo...".
Ya wuce sama jim kadan ya sauko, ya zauna akan kujerar da take tareda daura kanshi akan kafafunta, ya kwashe dukkanin abun da ya faru ya sanar da ita....
Ammi tace, "Alhamdullilah... Wannan labari mai dadi ne matuk'a gaya... Bara na kira Hajiya Zainab in sanar dasu...".
Lamido ya bude idanu saying,
"Zanje da kaina in sanar dasu... About little Arfaat zan barta a nan, zan ce mata nayi tafiya ne wajen umminta...".
Maimoon ce ta sauko daga stairs saying,
"Yaa Lamido...".
Lamido yace, "Yeah, what's up?".
Maimoon tace, "You look happy...".
Muryar Abbi sukaji saying,
"Who's look happy?".
Maimoon tace, "Yaa Lamido... Good afternoon Abbi, barka da dawowa...".
Lamido ya mike zaune tareda komawa akan wata kujerar saying,
"Good Afternoon sir...".
Abbi yace, "Kana tafiya...".
Lamido yace, "Lafiya lau...".
Ammi ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanarma Abbi, Abbi yace,
"Alhamdullilah... That's indeed good news...".
Maimoon tace, "Alhamdullilah...".
Ta koma sama domin ta kira Aseeyerh ta sanar da ita....

What'sApp 09169472057


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[08/03, 06:10] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 11

This Page Is Dedicated to you Mamee (Zahra Graphics), Nace Ba, ta iya graphics sosai, kuyi patronising, zaku iya tuntubarta ta what'sApp 08085681798
Team Arfaat R, Ku Lallab'amu Ni Da Hajeer Ku Samu Mu Koma Team Arfaat

Lamido ya kwashe dukkanin abun da ya faru ya sanar da Ummy da Abba, Ummy ta share hawayen da suka zubo mata tace,
"Allah shine abun godiya... Alhamdullilah...".
Abba yace, "Alhamdullilah, that's good...".
Ummy ta lumfasa sannan tace,
"Amma Lamido kana ganin kuwa babu ganganci a wannan abun, kadda kaima ka mak'ale... I'm afraid...".
Lamido yace, "Ummy addu'o'enku kawai nike buk'ata... In sha Allah zanje in kubutar da ita in kawo maki ita har gidan nan...".
Ummy ta share hawayen da suka zubo mata at the same time tana murmurshi....
Abba yace, "Lamido, da fatan kayi magana da matarka...".
Lamido yace, "No...".
Abba yace, "Kaje ka sameta kuyi magana domin tana da hakki a kanka...".
Lamido yace, "Amma Abba tun kafin ta aureni tasan halin da matata take ciki sannan kuma bazan wofantar da matata saboda ita ba...".
Abba yace, "Hakkinta ne don haka ka sameta kuyi magana, kaji...".
Lamido yace, "In sha Allah...".
Murna a wajen Sultan da Nabila ba'a magana, Lamido yayi masu salaam ya wuce gidan Ammi....
A parking lot ya ajiye motarsa heading to the parlor inda ya tarar da Little Arfaat tana cin biscuit, Ammi tana kallo, Maimoon tana karanta handout....
Maimoon tace, "Welcome bro...".
Lamido yace, "Thanks... Ammi na dawo...".
Little Arfaat ta d'ago jin muryarsa, ta wangale baki saying,
"Abbana...".
Lamido ya dauketa tareda zama akan kujera yana mata wasa, Ammi tace,
"Har ka dawo...".
Lamido yace, "Ehhh...".
Ammi tace, "Zaka wuce da ita ne...".
Lamido yace, "No a nan zan barta har zuwa lokacin da komai zai daidaita....".
Ammi tace, "Alright...".
Little Arfaat tace, "Ab bana gida...".
Lamido ya ware idanu saying,
"Gida kuma? Angel, Abba zaiyi tafiya yaje ya dawo sannan ya koma ya tafo da ummi...".
Little Arfaat tace, "Ummina...".
Lamido ya gyad'a kai saying,
"Ehhh inje in tafo da ita... Sai ki zauna a nan gidan tareda Antinki Maimoon da granny...".
Little Arfaat ta gyad'a mashi kai tana murmurshi, ya ajiye mata peck a kumatu sannan ya fice, saida ya shiga yayi bankwana wa Abbi, direct ya wuce gidanshi har ya nufi part dinsa maganar Abba ta dawo mashi a kai, ya juya heading to Baraka's part, tana kwance akan gado ya shiga da salaam akan bakinsa, ya zauna a gefen gado saying,
"Baraka...".
Baraka ta mike zaune tana kallonshi cike da mamaki tace,
"Yaa Lamido...".
Lamido yace, "Ina son zanyi magana dake....".
Tace, "Okay, I'm hearing you...".
Lamido yace, "Maryam ta bayyana a gareni kuma a gobe zata fara bani horo har na tsayin wata guda daya sannan inje in ceto matata Arfaat...".
Baraka tace, "Amma kasan da hakkina a kanka wanda ka gagara saukewa sannan kuma kake maganar tafiya ka barni...".
Lamido ya mike saying,
"Hakanan saboda ke bazan salwantar da rayuwar matata ba, ina son matata Arfaat, Ina matuk'ar sonta, tun kafin in aureki kin san itace rayuwata kuma nayi maki warning amma kika mannewa aurena, bazan saurari wani complain dinki ba domin ke kika ce kinji kin gani...".
Baraka ta mike tareda hugging dinsa ta baya ta fashe da kuka, ya banbare hannunta daga jikinsa ya fice, ta durkushe tareda fashewa da kuka....
**********
Arfaat ce takure a cikin kogon tun bayan mugun ganin da suka tilastata tayi taji komai ya fitar mata a kai, baki daya jikinta is weak, ta rame ta k'ara fari, idanunta sunyi luhu-luhu saboda kuka....
A wannan karon ma tun da taga sun taru ta tabbata wani bala'in zasu k'ara nuna mata, bata ankara ba aka nuno Lamido a cikin the same irin wancen yanayin yana yi yana kiran sunanta Arfaat...
Arfaat ta toshe kunnuwanta tareda fasa k'ara, kamar daukewar ruwan sama tayi tsit bata motsi, unconscious....
***********
Washegari tunda safe ya shirya ya dauki abubuwan da yake da buk'ata ya saka a backseat ya jata motar zuwa wani bangare na gidan, yayi breakfast ya zauna zaman jiran Maryam, yana sanye da fararen kayan yaki har da rawani looking as sadauki, ya zauna zaman jiran Maryam, babu jimawa ta bayyana a gareshi tana sanye da the same fararen kaya na yaki wanda yayi suiting Arfaat looking da ta bayyana dashi...
Tace, "Na barka kana jirana...".
Lamido yace, "No...".
Maryam tace, "Zan fara ne da baka labarin yadda abun yake...".
Lamido ya gyad'a kai, Maryam tayi jim sannan tace,
"Na tabbata har a zuciyarka kana tambayar kanka dalilin da ya saka nike son in taimaka maka wajen kub'utar da Arfaat, zan taimaka maka ne saboda nice sanadin komai ko kuma ince nice mafarin komai amma har sai na baka labarin ne sannan zaka fahimci abun da nike nufi....
Wanda ya haifi kakan kakan mahaifin Arfaat dashi ne labarin ya soma, sunansa Tanko, mahaifinsa ya kasance mutum mai rufin asiri wanda yake da kokarin ganin ya fita hakkin familynsa saidai shi ya kasance mutum mai son jiki ga son abun duniya, ba ya kaunar aikin wahala yafi gane yana zaune kudi suyita sauka, en uwansa sune suke taya mahaifinsu noma wanda idan suka girma yake masu aure sannan ya dauki wani yanki na duniyarsa ya basu tareda gona ta yadda zasu iya rike iyalensu, Tanko shine k'araminsu ba ya son taya mahaifinsu noma koda yaje ba ya tab'uka komai saidai yayi abun da yayi yabi inuwar bishiya yayi kwanciyarsa, mahaifinsu yayi iyakar kokarinsa amma ya fand'are, ba ya son neman kudi sannan ga girman kan tsiya, ba ya jin zai iya tambayar wani taimako, danginsa sunyi aure suna zaune da iyalensu cikin rufin asiri amma ta bangarensa yana sone yayi abun da yafi wanda sukeyi, yana da burin fantamawa a cikin daula mara iyaka... Yayi bikin aure wanda ba'a taba yi ba a kauyensu... Kamar abun arziki ya koma yana taya mahaifinsu aiki, ya fara neman auren wata yarinya a kauyen wacce kowa yasan bakin halin da danginsu suke dashi, sunanta Wasila, danginta ba sha shakkar kowa a kauyen, idanuwansu a bude yake, duk yadda familynsa suke son ganar dashi gaskiya amma ya fand'are, ya nuna ko su aura mashi ita ko kuma ya gudu yawon duniya, karshe ba domin ransu yaso ba suka bari ya aureta, mahaifinsa ya katange mashi sashe guda a cikin gidanshi, babu wanda yake jin dadin zama da wasila saboda babu wanda ta d'agawa kafa, tsula tsiyarta take son ranta idan aka yi magana yace dama tuni suka nuna basu kaunarta... Bayan shekaru biyu suka haifi dansu namiji wanda daga shi basu k'ara haihuwa ba, sunanshi Kamala wanda shine kakan mahaifin Arfaat tun yana yaro halinsa yake baiwa mutane tsoro, dama ance wani d'an gadon sai ya zarce, babu abun da ya baro a bakin halin tanko da wasila, bayan wasu shekaru Allah yayi wa mahaifinsu Tanko rasuwa aka raba gado, sauran en uwansa suka tattara gadonsu suna juyawa, mahaifiyarsu ta koma gidan babban brother dinsu.... A bangaren Tanko shi da wasila suka tusa gadon a gaba suna cin dadi saida sukaga bayanshi har ya siyar da gonarshi ta gado da rabin gidan da suke a ciki, daga nan ne zamansu ya sauya salo domin wasila bad'awa idanunta toka tayi tana wa Tanko rashin mutunci, domin zaune yake kullum a gida, abun da zasuci gagararsu yake, wata ranar saidai suyi kwanan yunwa, gashi ita er aci dadi ce, danginsa suna aiko masu da abinci amma bata godewa.... Wasila da kanta taje ta amsowa Tanko Asiri aka had'ashi dani yana aiki dani yana samun kudi ni kuma yana shayar dani bl**d, a lokacin ban musulunta ba, mugayen ayyukan da aka saka ya kulla basu da adadi domin komai zaiyi indai zaka biya, daga wasu garuruwan ake zuwa wajenshi, ya koma mats***fi, duk yadda en uwansa suke kokarin ganar dashi gaskiya amma yayi burus har da masu barazana akan babu su babu shi idan suka matsa zaiyi mummunan aiki a kansu wanda sai sunji sunfi buk'atar mutuwa da rayuwa... Wasila ta hakince rayuwa sabuwa... Bayan mutuwar Tanko ne d'anshi Kamala ya gaji tsafinsa, matarshi ta farko bokanya ce tana yi yana yi, a daidai wannan b'igiren ne na musulunta na tuba na warware dukkanin wani aiki da nayi amma Kamala ya riga yayi nisa ba ya jin kira yaje aka had'ashi da mugayen aljannu wadanda suka shahara a hatsabibanci, daga nan ne daula ta linka ta da, ya koma auri saki dukkanin wacce ya aura tana samun ciki yake sakinta idan ta haifi yaron ta maido mashi idan kuma bata iyawa ta rike shi babu ruwanshi, shi kanshi bai san adadin yaranshi ba ballantana matan da ya aura ya saki, matarshi ta farko ce kawai take zaune itama yana da dalilinsa na kin sakinta, cikin kankanin lokaci ya shahara, yayi suna saboda yadda aikinsa yake, ya raba uwa da y'ay'anta, ya raba miji da mata, ya raba d'a da ahalinsa, ya tarwatsa family, ya haukatar, ya nakasar, babu abun da ba ya yi, idan nace zan zauna lissafa maka sai mu wuni mu kwana ban gama ba, yayi tsayin shakaru domin saida ya shekara sittin yana ayyukanshi, kakan mahaifinki ya tashi ne a wajen mahaifiyarsa itama kaddara ce ta sakata auren Kamala, ganin yadda gidan yake ya saka ta rike abunta ta nisantashi daga Kamala, kafin rasuwar Kamala dashi da matarshi sukayi wa aljannun alk'awari akan cewa sun mallaka masu daya daga cikin tsatson Kamala, Kamala yasha matuk'ar wahala kafin daga baya yayi mutuwar wulakanci, wanda yazo tareda tarwatsewar y'ay'ansa kowa ya kama gabansa wanda har zuwa wannan lokacin zaiyi wahala a iya had'a kan ahalinsa saidai kuwa ta hanyar bakaken aljannun da yayi amfani dasu, wadanda suka cigaba da bibiyar tsatson Kamala suna neman wanda zaiyi daidai da wanda suke buk'ata a matsayin wanda zaiyi amfani dasu, wanda wannan tasko ya fad'awa Arfaat a yayinda ta kasance wacce take da abubuwan da suke buk'ata daga nan suka cigaba da bibiyar rayuwarta suna mata tayin tayi amfani dasu, taki yarda, duk wanda yayi niyyar cutar da ita zasu shiga jikinta su sauya mata kamanni su k'ara mata karfi na gaske da gaske, suka rink'a kora samarinta har daga karshe ta hadu da kai, suka hana auren kuka matsa daga karshe suka saceta mintina biyar bayan daurin aurenku... Dukkanin wannan abun da ya faru ya kasance ne a sanadin son zuciya da son abun duniya da ababen more rayuwa dake a cikinta... Tanko, Wasila, Kamala da matar Kamala sune sanadin wannan abun da yake bibiyar rayuwar Arfaat duk da tun kafin a haifi kakan kakan mahaifinta aka gudanar dashi, SUNE SUKA JANYO MATA wannan bala'in dake bibiyar rayuwarta wanda ya sakata a matsananciyar damuwa mai tattare da kunci da bakin ciki mai tafiya da dukkanin wani farin ciki da ya tunkaro rayuwarta, aka basu ita har suke ikirarin ita mallakinsu ce... Nice Tanko ya fara amfani da ita a harkar asirinsa shiyasa nace maka nice sanadin komai kuma wannan dalilin ne ya saka nike iyakar kokarina domin gyara abun da aka b'ata a sanadina... Zan baka hutu na tsayin mintina ashirin da biyar daga nan zan soma koya maka salo da siddarabun yaki, yadda zaka rike takubi da yadda zata sarrafata, yadda zaka rike Adda, kibiya, mashi, gatari, abun tare takobi da sauransu... Zan had'a maka tareda darussa domin shi yaki ba karfi kawai yake buk'ata ba, yana buk'atar natsuwa da basira tareda fahimtar situation, tareda lissafi akan motsi na gaba wadanda sannu da hankali zan fahimtar da kai komai har ka zamo sadauki mai watsa taron mayaka komai yawansu....".

WhatsApp 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

[10/03, 10:51] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 12

*Nace Ba, Baraka Ta Bada Sako In Fad'a Wa Team Arfaat R, Masu Cewa Zasu Koreta, Tana Nan Tana Jiransu, Zata Saka Ne A Rink'a Daukarsu Ana Watsawa Waje... Wanda Suka Fi Zakewa Zata Saka A Zaunesu Ne Su Kasa Koda Ihun Neman Taimako...* 😂😂😂

Maryam ce tsaye tana rik'e da katon takobi tana nuna mashi yadda ake rikewa, Lamido ya zuba mata idanu ba ya koda blinking ganin yadda kayan sukayi wa KAMANNIN Arfaat kyau, ya shagala da kallonta, Maryam ta kira sunanshi da karfi saying,
"Lamido...".
Lamido yayi firgigit saying,
"I'm hearing you...".
Maryam tace, "Ba ni zaka kalla ba, hannuwana zaka kalla kaga yadda nike rik'e takobin...".
Lamido ya sosa kai saying,
"KAMANNIN Arfaat da kike zo min dasu ne suke sakawa ina rasa nutsuwa...".
Maryam tayi dariya sannan tace,
"Ni kuma da KAMANNIN Arfaat kawai zan rink'a bayyana a gareka... Wannan ba Arfaat bace, Maryam ce...".
Gani yayi ta saka hannu a kugunta ta janyo wani farin kwalle mai fadi, ta rufe rabin fuskarta dashi saying,
"Are we good now...".
Lamido ya gyad'a

Please Login or Register in order to submit comment