Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude daya bangaren Little Arfaat ta shiga sannan ta zagaya bangaren direba ta fita tareda danna motar akan flat kwalta, saida tayi dropping little Arfaat a school sannan ta wuce catering school, tayi parking motarta tareda janyo niqab ta daura sannan ta fito heading to the entry na makarantar koyon girkin....
Bayan sun tashi ta biya ta dauko little Arfaat daga makaranta ta dauki hanyar komawa gida, wayarta ce ta soma ringing ta gangara gefen titi, Little Arfaat tace,
"Ummy mun zo gida ne?".
Arfaat tace, "Zanyi picking call ne...".
Tayi picking call din tareda kanga wayar a kunne saying,
"Salaam alaiki... Maimoon... Twins?... Masha Allah... When?... Kin kyauta da kika kirani Besty ta haihu babu zama...".
Sai kuma tayi hanging call din tareda dialing numbar Lamido, tayi salaam ya amsa....
"Ranka shi dade... Yanzu Maimoon ta kirani Aseeyerh ta haihu twins...".
Daga daya bangaren Lamido dake a cikin asibitin da Aseeyerh ta haihu yace,
"Yeah... Gani a asibitin?".
Arfaat tace, "Besty ta haihu, babu zama...".
Lamido yace, "Kina ina?".
Arfaat tace, "Na dauko little Arfaat ne zamu wuce gida... Please idan muka shirya muzo... Uhmmm... Ranka shi dade...".
Lamido yayi murmurshi saying,
"Alright kuzo, aminiyarki ta haihu babu zama...".
Arfaat tace, "Babu zama sai bayan suna...".
Lamido yace, "Ni kuma sai ayi ya dani, Baby...".
Arfaat tace, "Baby na koma kuma... Ga little Arfaat...".
Sai kuma ta mik'awa Little Arfaat wayar tareda murza key heading to gida, saida suka ci abinci suka huta tayi wanka tayi wa little Arfaat sannan suka wuce asibitin....
Aseeyerh ta haifi twins maza masu KAMANNI da Abeed sak, babu abun da suka baro a kamanninsa, farin Aseeyerh ne kawai suka dauka...
Arfaat ta dauki twins tana kallonsu tana murmurshi, Lamido ya zuba mata idanu yana hasashenta dauke da babynsu....
A ranar aka sallami Aseeyerh suka koma gida, Arfaat da ita aka yi zaman jego har kwana shidda suka cika, ranar suna suka cakare tareda k'awayensu suka sha rawa da kida na kwarya....
Babies sunci suna Mustapha (sunan mahaifin Abeed) da Munner amma ana kiransu Hassan da Hussein....
Lamido yayi hidima sosai a haihuwar nan, duk wata hidima ta sunan shine yayi, hidima aka yi ta girma, anci ansha an taya mai jego farin ciki, ta samu gifts sosai daga en uwa da abokan arziki....

***

Lamido yana zaune a gefen swimming pool yana duba tablet, Arfaat ta fito daga ciki tana sanye da rigar wanka wacce bata ida rufe cinya ba, saman kamar bra yake domin bata da hannu, ta kamata sosai ta manne a jikinta, ta saki gashinta tana tafiya yayinda baki daya jikinta yake girgiza cike da salon daukar hankali, kirjinta ya fito tareda kugunta, dama Arfaat ba dai shape ba, tana tafiya tana girgiza tareda sakin wani shegen murmurshi ta ratsa ta gefenshi yayinda ya zuba mata idanu ba ya koda blinking, a hankali take taka steps zuwa cikin swimming pool din ta soma iyo tana linkaya, ta fito tana karkade gashinta tareda bankaro kirji, tana girgiza jiki tabi ta gefenshi ta wuce, juyowa tayi tareda kashe mashi ido daya tayi mashi waving hand, tayi mashi alamar sumbata sannan ta juya ciki...
Lamido ya mike da sauri yabi bayanta....

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[15/04, 10:10] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 27



Lamido, Arfaat tareda Little Arfaat ne suka fito daga sashensa, Arfaat tace,
"Sai yaushe zaka dawo kenan?".
Lamido yace, "One week zanyi In sha Allah, daga Moscow zan wuce Paris, Dubai...".
Tace, "Allah ya kiyaye hanya...".
Lamido yace, "Amin... Kinki kiyi min rakiya...".
Saida tayi dariya sannan tace,
"Tuba nike ranka ya dade... Angel kiyi wa Abbanki bankwana...".
Little Arfaat tayi mashi waving hand saying,
"Bye...".
Lamido yayi hugging dinta saying,
"Bye Angel...".
Sai kuma yayi alamar kiss da bakinsa ya kalli Arfaat tareda mata alamar so, Arfaat tayi murmurshi kawai, ta kama hannun Little suka wuce wajen motarta yayinda shi kuma ya wuce domin yayi mata bankwana wa ma'aikatansa....
Saida Arfaat tayi dropping little Arfaat a school sannan ta wuce catering school, saidai har aka tadasu Little Arfaat babu Arfaat babu alamarta, aka kira numbarta bata picking, saidai Maimoon aka kira taje tayi picking dinta tana mamakin abun da ya hana Arfaat dawowa daukar Little Arfaat, ta wuce da ita gidan Lamido saidai a garkame ta tarar da sashen Arfaat, ta tambayi get man...
"Tunda suka fita bata dawo ba...".
Maimoon tace, "Then where is she?".
Da wasa da wasa k'aramar magana ta koma babba, domin kuwa an kira catering school sun tabbatar da Arfaat bata je ba, hankalin kowa ya tashi, Abeed ne yabi diddigin motarta wacce aka samu yashe a saman titi, ga wayarta nan yashe a ciki, da alama ta karfi aka fitar da ita daga motar, tashin hankali wanda ba'a saka mashi rana....
Ummy ta tada hankalinta sosai, sau ukku tana suma, kuka take sosai saying,
"Shin yaushe Arfaat zatayi farin ciki a rayuwa? Daga wannan sai wannan? A ina take? A wanne hali take ciki? Su waye suka saceta? Miye zasu buk'ata? Duk bamu sani ba...".
Saidai daukarta aka yi aka wuce da ita asibiti, Sultan kuka, Nabila kuka, Aseeyerh taje asibitin tareda Ammi, Safnah taje....
Aunty Hajjo, Hajiya k'arama da Hajiya babba duk sunje...
Abeed, Abba da Abbi suna wajen bincike domin gano inda Arfaat take saidai babu wani cigaba....
Kamar daga sama Lamido ya fado ward din, suka juya da mamaki suna kallonshi, Ummy wacce bata dade da farkawa daga allurar bacci da aka yi mata, ta fashe da kuka saying,
"Lamido, Arfaat?... Saidai motarta aka gani yashe a bakin titi, babu ita babu alamarta, an saceta, babu wanda yasan inda take... She's no where to be found... My poor child... She witness alot... Taga taskon rayuwa iri daban-daban, daga wannan sai wancen... My poor child... Shin yaushe ne zatayi farin ciki a rayuwa?".
Lamido ya k'arasa inda take ya kama hannunta saying,
"Ummy ki kwantar da hankalinki, duk inda Arfaat take a cikin garin nan zanje in tafo maki da ita cikin koshin lafiya...".
Ummy tace, "Kasan inda take ne?".


Lamido yace, "Ban san inda take ba, amma akwai abun da zai kaini har inda take, tunda aka shani sau daya na warke, bazan maimaita kuskuren da nayi a shekarun baya ba...".
Ummy tace, "Amma Lamido ta ya zakaje wajen bayan baka san irin makaman da suke dashi ba...".
Lamido yace, "Ummy na ratsa ta dazuka masu hatsari na kub'utar da ita ballantana a nan... Lamido ne... SADAUKI NE...".
Ummy tace, "Alright, Allah ya kiyaye, Allah ya tsare...".
Lamido yace, "Amin...".
Ya juya ya fice, Maryam ce tayi appearing a gabansa saying,
"Lamido ka bari zanje in tafo da ita...".
Lamido yace, "Wannan fad'ana ne kuma bai fi karfina ba... Idan yafi karfina zan nemi taimako daga wajenki...".
Maryam tace, "Okay, amma kafarka kafata...".
Maimoon ta ajiye mashi call, yayi picking, tace,
"Yaa Lamido... Little Arfaat ce sai kuka take tana kiran Umminta...".
Lamido yace, "Maimoon kice mata Abbanta yace zaizo mata da Umminta su wuce gida tare...".
Yayi hanging call din, saida ya tabbata dukkanin abun da yake a jikinsa bullet proof ne sannan ya wuce...
Bayan awa daya Lamido ya shigo asibitin yana rik'e da hannun Arfaat, Arfaat ta ruga da gudu tayi hugging Ummy yayinda suka fashe da kuka...
Dukkanin wanda yake a wajen saida yaji tausayinsu, a take Ummy ta warware aka sallameta suka wuce gida yayinda Lamido ya biya gidansu ya dauki little Arfaat sannan ya koma ya dauki Arfaat daga gidan Ummy suka wuce gida...
Arfaat ta zuba mashi idanu kawai tana tuna yadda yasha artabu kafin ya kub'utar da ita, ya tafo da ita....
Part dinsa ya wuce dasu ya kwantar da Little Arfaat a bedroom dinta dake a sashen sannan ya koma wajen Arfaat wacce take a bedroom dinsa, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa while saying,
"Meyyy yasa? Meyyy yasa kake saka rayuwarka a hatsari a saboda ni? Why? Why? Why are you risking your life because of me? Rayuwarka tana da matuk'ar muhimmanci, akwai mutane masu adadin yawa wadanda suke rayuwa a karkashinka, wadanda komai nasu ya dogara da kai ne... You are precious to them... Why are you risking your life for me? I'm i worth it?".
Lamido yayi hugging dinta yana bubbuga bayanta saying,
"Yeah you are... Arfaat ke rayuwata ce and you are precious to me... You are the love of my life, kaunar da nike maki bata da iyaka, dukkanin ta yadda zakiyi hasashen kaunar da nike maki ta wuce nan... Arfaat ina matuk'ar sonki...".
Arfaat tayi lamo a kirjinsa tana sheshshekar kuka, da kanshi ya rage mata kayan dake a jikinta ya wuce da ita bathroom, a tare sukayi wanka suka fito ya zaro mata riga ya saka mata, boxer ne kawai a jikinsa, ya kwanta tareda hugging dinta tareda tura kanshi a gefen fuskarta....
**************
Shekaru sun wuce amma har zuwa wannan lokacin Arfaat bata tab'a koda b'ari ba....
Tun rashin haihuwar ba ya damun Arfaat har abun ya soma damunta, ta tada hankalinta, Lamido ne yake kwantar mata da hankali, suka shirya sukaje asibiti, aka yi masu gwaje-gwaje inda likita ya tabbatar masu da cewa lafiyarsu lau....
Arfaat da Lamido suna fitowa daga ofishin likita suka ci karo da Maryam, Arfaat tace,
"Maryam...".
Maryam tace, "Kuyi hakuri amma wannan ciwon bana asibiti bane... Wannan yana da nasaba da abun da aljannun nan suka dasa mata a jiki...".
Arfaat da Lamido suka ware idanu suna tuna maganganun Aljanin nan....
"Lamido ka daina ganin ka samu nasarar k'arar damu kuma ka tafi da ita kayi tunanin kayi nasara, tun kafin a fara yak'in mukayi nasara, abun da muka dasa mata a jiki shine zai zame maku bakin ciki a rayuwa, bazai tab'a bari kuyi farin ciki a rayuwa ba, zai hana rayuwarku sukuni...".
Arfaat ta durkushe a kasa tareda fashewa da kuka saying,
"Shikenan sun gama dani, sun mayar dani juya, sun kassara min mahaifa...".
Lamido ya kamata saying,
"Arfaat, ki nutsu...".
Arfaat tace, "Wacce nutsuwa zanyi bayan naji cewa bazan tab'a haihuwa ba, haka zan mutu ban ajiye komai ba... Yaa Lamido kadda ka cutar da kanka kaje ka auri wadanda zasu haifa maka y'ay'a, nikam an kassara ni...".


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

*SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 28
Last Page

Chat me up via WhatsApp 09169472057 domin samun Complete

Maryam tace, "Arfaat... Ni bance ba zaki haihu ba, na sanar daku abun da yake faruwa ne domin kadda kuyi ciwo daban, magani daban... Duk da zaiyi wahala amma idan kuka dage da addu'a, saukar Alk'ur'ani, sadaka, magani da sauransu, In shaa Allah komai zaizo karshe...".
Lamido yaji Arfaat tayi shiru yana dubawa yaga ta suma ne, gado aka bata, ta tada hankalinta sosai, duk tabi ta rame, kullum tana cikin damuwa, ya sanar da mahaifansu halin da ake ciki domin su tayasu da addu'a....
Saida Lamido ya nunawa Arfaat b'acin ransa sosai sannan ta kwantar da hankalinta, saidai sau da yawa tana kulle kanta a bathroom tayi kuka ta wanke fuskarta ta fito....
************
Arfaat ce ta fito daga sashenta tana dauke da warmer heading to sashensa, taci karo dashi, yace,
"Where's Angel?".
Arfaat tace, "Tunda safe ta wuce school, ta makara ne shiyasa bata shiga wajenka ba... Ina son gobe zanje wajen Ammi inyi mata wuni...".
"Alright, babu damuwa, ta wajen Ammi...".
"Alright, na wajen Ummy...".
A tare sukayi dariya....
Washegari bayan tayi dropping Little Arfaat a school ta wuce gidan Ammi, a balcony ta samu Baraka....
"Ammi fa?".
"Tana ciki...".
"Dama wajenki nazo...".
"Allah yasa lafiya...".
"Lafiya lau... Alfarma ce zan nema a wajenki, Baraka rashin haihuwarmu matsalar daga wajena, na gaji da ganin Lamido yana suffering a saboda ni... Please ki taimaka ki aureshi, domin shima ya samu ganin jikokinshi...".
Baraka ta mike da sauri tana kallonta ta kalli gefe da gefe babu kowa, ta maida idanunta akan kofar parlor ta mike taja hannunta zuwa parking space wanda yana da tazara da parlor, ta murtuke fuska saying,
"What? Are you fucking kidding me? Are you messing with me? Kin san wahalar da nasha kafin na kubutar da kaina sannan kizo kije in kai kaina ruwa...".
Arfaat ta hade hannayenta waje guda alamar roko sannan tace,
"Please... Zanyi mashi magana...".
"Arfaat ban tab'a sanin haka kike da san kanki ba, yi mashi magana bazai saka ya soni, beside ni yanzu mijinki ba ya burgeni, na riga na samu the love of my life... Mijinki bana so ki kai kasuwa...".
Arfaat ta fashe da kuka, Baraka tace,
"Dama kinyi tattalin hawayenki, don bazan yarda ki cuceni, ki sakani auren mijinki... Zuwa kice in auri mijinki bayan kin san zaman da nayi dashi is like an insult to me, don haka ki rike girmanki... Kin bani mamaki, really disappointed in you... Gobe za'a kawo kudin aurena, so ki daina wahalar da kanki... Zan cigaba da tayaku da addu'a, Allah ya yaye maku, Allah ya baku zuriyya dayyiba... Kuma zan baki shawara kadda ki sake kiyi wa kanki kishiya da kanki... Kije ki fara koyon yadda ake zama da kishiyar sannan, domin kinga wadanda suka tashi a gidan dake da mata fiye da daya sunfi kowa tsoron kishiya saboda sun gani da idanunsu... Amma fa akwai na kirki wadanda zaku zauna kamar en uwa...".
Ta juya ta koma ciki, Arfaat ta durkushe kasa tareda fashewa da kuka, saida tayi mai isarta sannan ta fiddo bottle daga mota ta wanke fuskarta ta shiga ciki....
Anyi bikin baraka ta tare a Abuja kafin suka lula Spain inda mijin yake aiki...
Little Arfaat ta girma sosai, Nabila tayi aure wani cousin dinsu dake a London, shekara daya da watanni ta santalo diyarta mace mai KAMANNI da ita sak, shiyasa take KAMMANI sak da Arfaat itama, wacce taci sunan mahaifiyar mijin wato Rukayya amma suna kiranta da Meemah, Nabila tana yayeta ta daukota ta kawowa Arfaat, Arfaat ta fashe da kukan farin ciki....
Some years later,
Babu zato babu tsammani ciki ya bayyana a jikin Arfaat, basu lura dashi ba har saida ya girma, farin cikin da wannan family sukayi ba ya misaltuwa, Allah shine abun godiya, bayan watanni tara ta santalo yaranta en ukku maza biyu sai mace daya wacce itace k'aramarsu, kamanni suke da Lamido sak kamar an tsaga k'ara an k'arya, sunyi farin ciki, anyi shagali, yara sunci suna Aryan, Muneer da kuma Zaynerb wacce taci sunan Ummy, suna kiransu Hassan, Hussein and Ummy, shekara daya da watanni shidda ta k'ara haihuwar twins mace da namiji wadanda suka ci suna Abdurrahman da Bilkisu wacce taci sunan Ammi, suna kiranta da Ammi, shima namesake din ranka shi dade suna kiranshi Little Lamido, shekara daya da watanni biyu a tsakani ta k'ara santalo diyarta mace wacce take kama da ita sak ranar suna yarinya taci sunan Arfaat duplicate wato Mariam, sunyi wa Maryam takwara domin nuna godiya akan jajircewa da ta nuna a kansu da damuwar da suka shiga a baya, daga nan bata sake haihuwa ba....
Arzikin Lamido a kullum k'ara k'aruwa yake, gidansa ya cika da yara, Arfaat tana da yara takwas, Little Arfaat, Meemah, Hassan, Hussein, Little Ummi, Little Ammi, Little Lamido, Mariam....
Haihuwa take akai-akai, Lamido a kullum cikin godewa Allah, the live happily ever after, suna rayuwa a cikin farin ciki, baby abun da yaransu suke nema suka rasa, gata na duniya suna samu, amma wannan bai hanashi kula da ilimi da tarbiyyarsu ba...

The end...


Alhamdulillah, a nan na kawo karshen wannan littafi mai suna *SUNE SUKA JANYO MIN...*, kirkirarren labari ne idan yayi daidai da rayuwarku arashi ne, kuyi amfani da darussan dake ciki, ku watsar da kurakuran da suke ciki, wanda wannan littafi ya farantawa rai burina kenan wanda kuma ya b'atawa rai yayi hakuri....


From the writer of
Ban Dace Dashi Ba Complete 600
Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion Complete 600
The Choice I Made Complete 600
Chasing My Heart, A Tsakanin So Complete 600
Yan Mata Return Complete 500
Ba Ni Da Laifi Complete 300
Ni da yaya Hassan Complete 400
Rumana's Diary
And now _Sune suka janyo min book 1 and 2 free book_

Sai mun hadu a sabon novel dina mai suna *YAFI KARFIN KAINA,* _UNCOVERING THE TRUTH BEHIND THE MEMORIES..._ wanda shima paid ne 💃💃 Idan Duk Siya Da Yawa Zanyi Maku Free Book...

For wadanda Zasuyi payment na *YAFI KARFIN KAINA,* _UNCOVERING THE TRUTH BEHIND THE MEMORIES..._ Naira dari ukku ne 300, pay via 9169472057, Aisha, PalmPay, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057, ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057

One love 😍




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment