Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai, ta fara ne da koyar dashi yadda ake rike takobi, mashi, adda, da sauransu, sun shafe tsayin wadannan kwanakin tana sakashi yana motsa jiki, gudu sannan ta koyar dashi Azkar and wasu lokuttan tana zaunar dashi tana bashi labarin Hikaya na jarumai da yadda suka yaki zalunci a qarnin da suka rayu, tana nuna mashi darussan dake a ciki, ta zage sosai tana koyar dashi salo da dubarun yaki....
Tace, "Lamido ka sani ba karfi ne kawai yake sakawa aci yaki ba hakanan ba karfin takobi ne yake sakawa ba, suma suna da matuk'ar amfani amma yaki yana da buk'atar nutsuwa, zurfin tunani dahakuri, ka tsaya ka karanci abokin karawarka domin kasan salon da ya dace kaje mashi dashi da kuma takobin da ya kamata kayi amfani dashi...".
A kullum suna wuni ne tana koyar dashi har mamaki take akan kokarinsa da zallar jarumtar da ya samu a cikin k'ank'anin lokaci, suna shafe tsayin lokaci suna karawa ba tareda ya gaji ba, yana da juriya da naci, cikin wannan k'ankanin lokacin ya murde jikinsa ya sauya samfurin jarumai majiya karfi, yayi developing six peck, looking as sadauki as he is, duk nauyin takobi da hannu daya yake rik'eta, ya samu horo matuka gaya a wajen Maryam kuma yana cigaba da amsa domin kuwa abun da zai tunkara ba k'arami bane...
Tunda ya soma amsar horo bai fita ba, a wajen yake kwana, bayan wasu lokuttan yana kira gida su gaisa sannan yayi video call wa little Arfaat....
********
Maryam ce tsaye da wani shu'umin murmurshi akan fuskarta, tace,
"Lamido ka sani cewa dubarun yaki suna da matuk'ar muhimmanci, sai kaga wanda yake da weak sword yayi nasara akan mai strong sword, sai kaga wanda bashi da makami yayi nasara akan wadda yake da makami... Watch and See...".
A take wata sharbebiyar sword ta bayyana a hannunta, ya kalli sword dinta ya kalli sword dinsa wacce ko rabin waccen ba tayi ba, kafin ya ankara ta falfalo da gudu ta afka mashi tana kai mashi attack babu ji babu gani, tun yana defending kanshi har ya kasa, cikin mintunw kadan tayi wurgi dashi a kasa ta aza mashi takobi a wuya saying,
"One-Zero...".
Ta juya ta koma gefe, Lamido ya mike, tace,
"Lamido kadda ka tab'a yarda da kanka... Ka k'ara jajircewa, let reverse the case...".
Tayi nuni da hannunsa a take sharbebiyar sword ta bayyana a hannunsa, ya kalli k'aramar snife dake hannunta, tayi wani shegen murmurshi saying,
"Bar Raina allura itama karfe ce... Attack...".
Lamido ya falfala da gudu yana attacking dinta ta ko'ina, saidai ya kasa cin galaba a kanta duk da yana attacking dinta ne da dukkanin karfinsa, wurgi daya tayi mashi tayi wuf da sword dinsa saying,
"Two-Zero...".
Ta wurga mashi abun kariya kafin ya ankara ta soma mashi ruwan kibau, aikosu take babu ji babu gani, tsalle ya soma yana zille masu yana k'arewa da abun, a wannan bangaren saida ta jinjinawa jarumtarsa, smile ne yayi escaping akan lips dinta tace,
"Two-One... Duk da haka na bigeka da round guda daya...".
Ta wurga mashi k'aramar wuka ya cab'e yayinda ita kuma babu komai a hannunta ta mayar da hannuwanta a baya saying,
"Attack me...".
Lamido yayi shegen murmurshi, Maryam ta girgiza kai tana ganin wautarsa, ya falfalo da gudu yana kai mata attack da wukar tana gocewa ba tareda ya samu damar tab'a jikinta ba, a nan ne ta nuna mashi zallar dubara irin ta mayaka, duk yadda yake attacking dinta amma ya kasa nasara a kanta, saida ya daukesu mintina sha biyar amma babu nasara, ya koma yaja baya yana maida lumfashi, Maryam tace,
"Ko zuwa yanzu ka gane cewa akwai sauran aiki a gabanka... You lose again... Three-One... Koda nace inyi maka nice zanyi nasara torh na barshi... Ka iya ruwa...".
Lamido ya girgiza kai saying,
"No...".
Ta ware idanu saying,
"What munyi tuya mun manta da albasa... Daga yau...".
Kafin ya ankara saidai jin kansa yayi a cikin ruwa, ya soma dauke lumfashi yana sakin bubbles, ta saki kanshi, ya zube a kasa yana tari ruwa suna fitowa daga bakinsa, tace,
"Ka soma koyon ruwa domin kuwa dajin da zakaje yana dauke ne da ruwa masu girman gaske... Ka fadi jarabawarka ta yau... Three-One shima don na tayaka kayi min rinto... Idan ana darasi ka rink'a maida hankali... Be a good student... Uhmm...".
Sai kuma tayi disappearing....
Lamido ya rik'e kugu yana maida lumfashi, tabbas akwai sauran rina a kaba, akwai sauran aiki a gabanshi muddin yana son idan yaje yayi nasarar kwato masoyiyarsa Arfaat, tun daga wannan ranar ya k'ara zage damtse, bayan darussanta ya soma baiwa kanshi horo da kanshi yana mai kirkirar dubarun yaki daban-daban, har mamakinsa takeyi, hangoshi yana tsalle tareda tsallake abubuwa yana kai attack....
Bayan kwanaki talatin da soma amsar horo, Maryam ta gamsu da cewa ya samu horon da ya dace domin a wasu lokuttan dakyar take kwatar kanta a hannunsa, ya kirkiro wani salon yaki mai wuyar ganewa wanda duk yadda kake hasashe sai kaga ya waske yayi wani abun daban....
"A yau ne na kammala baka horo don haka kaje ka huta sannan kayi bankwana da familynka, jibi idan Allah ya kaimu zamu dauki hanya... And you have to prepare for the worst domin duk yadda kake tunanin abun ya wuce nan...".
Tayi mashi waving hand with smile on her face, ta b'ace b'at ya daina ganinta....
Lamido ya tattara abubuwansa ya zuba a bayan mota yayi mata key heading to the main part, duk da a cikin gidan wajen yake amma akwai tazara sosai a tsakani kasancewar mansion ne babba gari guda, har zai wuce sashensa sai kuma ya juya heading to sashen Baraka, ya sameta zaune akan kujera duk ta rame tayi baki, fuskarta babu walwala ko kadan, ya k'arasa inda take saying,
"Baraka meyy ya sameki? Kinyi ciwo ne bayan tafiyata?".
Baraka tayi mashi kallo daya ta watsar saying,
"A'a, dama can haka nike, baka lura ne...".
Lamido yace, "A'a...".
Ji tayi ya k'ara bata haushi ta mike ta wuce upstairs ba tareda ta k'ara mashi magana ba, ya fice heading to his part, saida ya girka abinci yaci sannan yayi wanka ya shirya cikin wani expensive yard ya shiga motarsa ya wuce gidan Ammi....
Baki daya suna zaune a parlor, Little Arfaat ta ruga tayi hugging dinsa saying,
"Abbana...".
Lamido ya dauketa a hannu saying,
"Angel I'm back amma jibi zan koma domin in tafo da Umminki...".
Little Arfaat ta wangale baki saying,
"Yeah... Ummina is coming back...".
Ya zauna akan kujera ya gaida Ammi da Abbi suka amsa da kulawa, Maimoon tace,
"Yaa Lamido Ina kwana?".
"Lafiya lau...".
"Yaa Lamido kaga yadda ka koma kuwa sadauki sak...".
Ammi tace, "Na rigaki a zuciya kin rigani a baki, tabbas horo da ya shafe wata guda daya yana yi ya biya...".
Lamido yace, "Zai biya Insha Allah...".
Abbi yace, "Allah yasa...".
Ammi tace, "Amin...".
Abbi ya lumfasa sannan yace,
"Ya kukayi da ita?".
Lamido yace, "Tace jibi in shaa Allah zamu wuce... Ina so idan na huta zanje inyi bakwana wa Ummy da Abba...".
Abbi yace, "Hakan yayi, Allah ya bada sa'a...".
Lamido yace, "Amin...".
Ammi tace, "About your second wife, Baraka...".
Lamido yace, "Idan na koma zanyi magana da ita idan bata iya zama ita daya sai ta dawo nan ko kuma ta koma gidansu har zuwa lokacin da zan dawo...".
Ammi tace, "That's good idea...".
Lamido yace, "Bara inje in kwanta I'm tired...".
Mikewa yayi yana dauke da Arfaat, wayarsa ce ta sub'uce daga hannunsa cikin zafin nama yayi wani juyi ya tareta ta fad'a akan palm dinsa, baki daya da mamaki suke kallonshi, smile ne yayi escaping akan lips dinsa ya juya heading to hanyar da zata sadashi da sashensa, dakyar ya samu little Arfaat tayi bacci yayinda shima bacci yayi awon gaba dashi....
Karfe hudu saura ya farka ya duro daga saman gado heading to the bathroom ya watsa ruwa tareda dauro alwalla, ya zura jallabiya ya wuce Masjid akan hanya yayi dialing numbar Maimoon tana picking yace,
"Ki dauko Angel daga sashena kiyi mata wanka ki shiryata zata rakani gidansu Arfaat...".
Daga daya bangaren Maimoon tace,
"Sure amma zanyi sallah tukunna...".
Lamido yace, "Okay...".
Hanging call din yayi ya k'arasa Masjid, ya jima zaune yana azkar sannan ya fito ya koma gida ya shirya cikin expensive shadda brown dinkin zamani, kayan sunyi suiting sadauki look dinsa, ya feshe jikinsa da perfumes masu matuk'ar kamshi, ya fito ya wuce sashen Ammi yayi mata salaam sannan ya amshi little Arfaat a wajen Maimoon ya fito ya shiga motarsa yayi mata key, direct ya wuce gidansu Arfaat...
A parlor ya samu Ummy da Abba, Sultan yana London a can yake karatunsa, Nabila ta zama en mata tana SS3 ne, little Arfaat ta manne mashi tana kallonsu...
Ummy tace, "Uwar k'wuwa, nidai kishiya ce, kina haka sai in amshe mijin ni daya...".
Lamido yayi murmurshi tareda gaidasu sannan ya sanar dasu lokacin tafiyarsa, Ummy ta share hawayen da suka zubo mata saying,
"Allah ya kiyaye, Allah ya tsare, Allah ya bada sa'a...".
Lamido yace, "Amin... Ummy ki daina kuka Insha Allah zan kawo maki Arfaat har cikin gidan nan...".
Ummy ta share hawayen saying,
"Kukan farin ciki ne...".
Abba yace, "Lamido ka kula ban da sakaci da addu'a, ka kula da azkar na safiya da marece...".

(Ku shirya wacce bata tab'a karanta littafin YAKI ba ta shirya farawa domin nima zan kwada kwanyata inga idan zan iya...)...


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[12/03, 22:25] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 13

*This Page Goes To Mub'Ash and Sofiyya, Really Appreciate your dogon sharhi...*

Lamido yace, "Sure... Insha Allah...".
Nabila ce ta sauko daga stairs, da murmurshi akan fuskarta tace,
"Yaa Lamido...".
"Yeah sis... How's your study...".
Nabila tace, "Alhamdullilah... Angel zo muje...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a tareda turo baki, Nabila tace,
"Indai nice zaki ganni ne wajen Maimoon inyi kamar ban sanki ba...".
Little Arfaat tace, "Aunty Na bi...".
Duk saida sukayi dariya, Nabila ta amsheta daga hannunsa suka wuce balcony bayan da ta zuba mata snack a plate...
A unguwar yayi sallar Magrib saida sukayi dinner a can sannan yayi masu salaam ya amshi little Arfaat da tayi bacci ya wuce, saida ya sauketa gidan Ammi sannan ya dauki hanyar gidanshi....
Baraka tana zaune akan gado tayi tagumi, ya shiga, tayi saurin janye hannunta daga tagumi da tayi, tayi mashi kallo daya ta dauke kai, ya zauna a kusa da ita saying,
"Jibi In shaa Allah zan wuce, idan kina ganin ba zaki iya zama ke daya ba, kije gidan Ammi ko kuma kije wajen Mom...".
Baraka tace, "Is that it... Well Naga ay koda kana gidan ba ganinka nike ba, don haka babu inda zanje, ina nan a gidan mijina, ok... Good Night... Idan ka fita kaja min kofa...".
Ta kwanta tareda jan bargo, Lamido ya bita da kallo cike da mamaki sai kuma ya mike ya fice....
Washegari tunda safe ya shirya yabi companies dinsa daya bayan daya yana bankwana wa employee dinsa, a can ya wuni sai bayan sallar Magrib sannan Abeed yayi dropping dinsa a gida, inda ya samu Aseeyerh sukayi bakwana ya k'ara bankwana wa Ammi da Abbi, yayi hugging Little Arfaat, sai around goma da rabi sannan ya wuce gida, ya samu sashen Baraka a kulle yayi knocking bata bude ba, ya juya ya wuce sashensa...
Washegari tunda safe ya dauki trolley wacce take dauke da abubuwan da yake da buk'ata ya janyota parlor sannan ya wuce sashen Baraka, tana kwance a bedroom tana bacci ya shiga har ya nufi inda take sai kuma ya juya ya dauki paper and pen yayi dogon rubutu yayi mata dropping akan bedside drawer....
Fitowarsa tayi daidai da shigowar Abeed, ya koma ciki ya dauko trolley da ya ajiye a parlor, Abeed ne yayi driving dinsa har zuwa wani katon fili wanda yake a cikin gidan, suka fito daga cikin mota suna jiran Maryam....
Lamido ya fito ya shiga wani k'aramin room na wood dake daga gefe ya shirya cikin kayan yaki na sulke, ya b'oye adduna da takubba a mazauninsu, kananan wukake suma yayi hiding dinsu, ya zuba guzurinsa wanda zai iya daukarsa kwanaki ukku, ya fito, Abeed ya ware idanu saying,
"Sadauki...".
Ya soma daukarshi caption yana kashe mashi pictures....
Maryam ce ta bayyana a garesu kamar koda yaushe da KAMANNIN Arfaat ta bayyana, Abeed ya ware idanu saying,
"Arfaat...".
Maryam ta girgiza kai saying,
"Maryam dai... Arfaat's duplicate...".
Abeed yace, "Mun gode da taimakon da kikeyi akan ganin an kub'utar da Arfaat...".
Maryam tace, "Kadda ka damu dolena ne in taimaka saboda nice sanadin komai, komai ya fara ne daga ni... Ka juya baya kadda in baka tsoro...".
Abeed ya girgiza kai saying,
"No...".
Maryam tace, "As you wish...".
Maryam ta girgiza ta rikid'a ta koma katuwar tsuntsuwa wacce basu tab'a ganin tsuntsuwa wacce ta kaita girma ba, Abeed yayi baya da sauri yana mai zaro idanu, Lamido ya zuba mata idanu yana nazari bai tab'a ganin irinta ba sannan bai san daga wanne specie take ba, amma watakila ta tab'a wanzuwa a wasu shekaru masu yawa da suka wuce...
Ji sukayi tace,
"Lamido muje...".
Lamido ya juya yayi hugging Abeed, ta ajiye fiffikenta a kasa, Lamido ya taka ya haye sama, ta ajiyeshi a saman bayan sannan ta tashi ta lula a sasarin samaniya wanda ya tayar da iska saida Abeed ya rik'e wani abu, ya d'aga kai yana hango yadda suka lula a sararin samaniya tun yana hangoshi har suka b'acewa ganinsa, suka lula a gajimare, gudu take sosai sallah da cin abinci ne kawai yake tsayar dasu sannan su k'ara tadanar wani guzurin saida ya daukesu kwanaki biyar sannan suka isa, ta dure a kasa tareda ajiyeshi a doron kasa sannan ta rikid'a ta koma KAMMANIN Arfaat, tace,
"Lamido zuwa nan ne daidai inda zan iya kawoka, sauran aikin naka ne, amma wannan dajin da kake gani yana hatsari sosai akwai namun daji masu hatsari a ciki wadanda baka tab'a ganin irinsu ba... Wannan daji yana dauke ne da bangarori guda biyar masu mabanbantan yanayi... Bangare na farko yana dauke ne da damshi tareda bishiyoyi masu tsayi wanda ya saka mashi duhuwa... Bangare na biyu yana dauke ne da k'ankara ne wanda ita kanta zata iya daskarar da mutum... Bangare na ukku yana dauke ne sahara wacce take dauke da yashi da rana babu ruwa babu abinci babu shuka saidai zeroplyt... Bangare na hudu shine yake ruwa wanda dole sai ka hau kwale-kwale sannan zaka haurashi, yana da matuk'ar yawa domin zai daukeka kwanaki kana bi ta cikinsa kana sauka a tsibiri daban-daban kafin ka wuceshi... Daga nan ainihin tashin hankalin zai soma wato bangare na biyar sannan kuma na karshe, a nan ne Arfaat take... Bangare na karshe shine inda Aljannun suke, yana dauke da nau'ikan dodone da halittu masu ban tsoro, dukkanin abun da zaka wuce a sauran bangarorin bai kai kaso biyu cikin dari na tashin hankali dake a cikinsa, duk da ba ya da tsayi... Dukkanin sauran bangarorin kowanne yana dauke da nau'ikan dabbobi daban-daban masu hatsari... Na barka lafiya... Allah ya bada sa'a... Ka rik'e addu'a kadda kayi wasa da ita..".
Sai kuma tayi girgiza ta b'ace b'at....

Da sanyin safiya ne a lokacin Lamido ya yada zango, ya zaro jikar guzurinsa yaci abinci ya kora da ruwan dake a cikin sulkarsa, ya tsinko fruit ya saka a jikkar guzurinsa, ya soma tafiya, yana cikin tafiya ya samu korawa ya cika sulkar ruwansa yayi alwalla ya kama hanya ya shiga cikin dajin wanda yake dauke da damshin ruwa tareda dogayen itace with small grasses a sanadin damshi dake akwai, yayi tafiya sosai ba tareda ya hadu da wani abun tsoro ba saidai gani yake kamar yana kewaye dajin ne yana komawa inda ya baro but he don't have to choice than to continue with the journey, lokacin sallar zuhr ya yada zango yayi alwalla yayi sallah yaci abinci ya huta sannan ya dasa, abun da bai sani ba shine yana zagaya waje guda ne a dajin wannan shine ya saka yake ganin ba ya gaba ba ya baya, sallah ce kawai take tsayar dashi idan yaci kishirwa ya d'aga sulkar ruwansa ya kwankwada sannan ya mayar da ita inda take, gefin Magrib ya tsaya da tafiyarsa ya yada zango, ya buga tantari, ya shiga cikin dajin ya hado itace ya kunna wuta, yaci fruit da ya tsinka, bayan sallar Isha'i ya jima yana jera salloli sannan ya karanta addu'ar kwanciya bacci ya shiga tantinsa ya kwanta with his sword around his right hand gudun ko ta kwana, Alhamdullilah har lokacin sallar subh babu wani abun da ya farmakeshi, ya tashi yayi sallah yayi kalaci ya tattara kayansa ya cigaba da tafiya saidai ya shafe rabin wuni yana tafiya amma daga karshe ya tsinci kansa a daidai inda ya kwana wanda ya tabbatar mashi yana wondering a waje guda ne shiyasa tafiyar tasa taki gaba taki baya, ya rik'e kugu yana neman mafita, ya zaro wuka daga kugunsa yana tafiya yana alama akan dukkanin iccen da ya tarar ta hakan ne ya rink'a gane hanyar da ya wuce and the his journey continue, gab da sallar Magrib ya k'arasa wani bangare wanda yafi dukkanin dajin duhuwa, tsit wajen yake babu motsin halitta koda guda daya wanda hakan ya matuk'ar bashi mamaki, ya janyo takobinsa ya soma tafiya cikin sand'a yana mai kasa kunnansa waiting for abun da zai bujiro, amma to his biggest surprise har yayi tafiya mai nisa babu abun da yayi attacking dinsa, smile ne yayi escaping akan lips dinsa, ya maida takobinsa a kubenta, ya cigaba da tafiya hankalinsa kwance, babu zato babu tsammani, wasu manya-manyan tsuntsaye sukayo kansa suka yanyameshi suna farmaka dakyar ya zaro takobinsa yana k'are attack da suke kawo mashi amma sarkin yawa yafi sarkin karfi, sun yanyameshi ne tamkar wadanda suka wuni babu abinci sannan suka ci karo dashi, fad'a suke yasu-yasu kowanne yana son yayi sama dashi, da baki daya karfinsa yake tare farmakinsa amma yawansu ya wuce tunaninsa, saida ya yanke tsammani akan rayuwarsa, duk yadda yake k'are kansa yana kai masu sara yana ji masu ciwo amma babu daina attacking dinsa ba, tamkar basu jin zafi a jikinsu, daya daga cikin tsuntsaye tayi sama dashi, sauran tsuntsayen suka mara mata baya suna fad'an kwatarsa, ana kwatarsa daga waccen zuwa waccen duk a saman iska....
Arfaat ce ta fad'o mashi a rai tareda maganganun Maryam, ji yayi ya samu karfin gwuwa ya zaro takobi tareda fille kafar wacce take rike dashi, yayi rolling tareda dura a saman daya daga cikinsu ya zaro kibiyarsa ya cigaba attacking dinsu da kibiya babu ji babu gani, ya cigaba da masu ruwan kibiya, wadda yake a samanta ce tayi zillo tareda watsar dashi a iska, yayi rolling tareda dura a saman wata, tunda ya gano makasarsu ya addabawa rayuwarsu ya cigaba da zaftaresu a kasa, amma saboda naci basu barshi ba haka yake tsalle daga saman waccen tsuntsuwa zuwa saman wata, saida sukaga yayi masu barna sosai sannan suka juya suna gudun ceton rai, ya maida kibiyarsa a inda take, tsuntsuwar da yake a samanta ce tayi watsi dashi a iska ta gudu, daga nan bai kuma sanin inda kansa yake ba....
Da sanyin safiya ya bude idanunsa ya tsintar kansa yayi yashe a saman wata bishiya, a galabaice yake, ya duro dakyar ya kwankwadi ruwa sai kuma ya soma tari ya zube a kwance yana maida lumfashi, ya jima sannan ya mike zaune yaci abinci tareda gyara raunikan da ya samu, ya wanke inda jini ya b'ata mashi sannan yayi alwalla, ya rama sallolin dake a kansa sannan ya mike yana nazartar dajin wannan dajin yayi daban da wanda ya baro hakan ne ya tabbatar mashi da cewa tsuntsuyen nan sunyi tafiya dashi sosai, and thanks to that sunyi mashi tafiyar da zai shafe kwanaki biyu baiyi ba, cike da taka tsantsan ya nausa a cikin dajin yana mai nazartar abubuwan da yake dauke dasu, ya farauci dabba ya gasa yaci har ya adana wani ya kora da ruwa sannan ya cigaba da tafiya....
Lokacin sallar zuhr ya yada zango yayi alwalla ya tada sallah, cike da nutsuwa, motsi ya soma jiyowa ta kusa dashi kafin ya ankara wasu dabbobi wadanda bai tab'a ganin irinsu ba suka mamaye inda yake suna masu tsayawa kamar suna nazarin wani abu, bai razana ba ya cigaba da sallarsa saboda yasan Allah shine mai tsarewa, yana sallah yana mai karanta addu'o'en tsari, suka rink'a zagaye inda yake har wasu suna sinsinar inda yake, can suka juya suka arta da gudu wani bangare na dajin a sanadin motsi da suka jiyo, a cike da nutsuwa ya gama sallah ya jima zaune yana azkar sannan ya mike, abun da ya fahimta da dabbobin kamar basu gani sosai sannan suna detection abun farautarsu ne ta hanyar sauti....
Lamido ya goya jikkarsa tareda rataya takobinsa ya cigaba da tafiya....
Daga nan bai k'ara haduwa da wani abu ba har ya yada zango da daddare, ya kwana, bayan yayi sallar subh yayi wanka a wasu ruwa da ya gani ya kimtsa ya dauki hanya, amma lokaci zuwa lokaci yana cin karo da kartar icce ko kuma rami da wajen hutawa na wasu dabbobin amma bai ci karo da daya ba, babu zato babu tsammani yana tsaka da tafiya ya soma jiyo wani sautin tako yana tunkaroshi kafin ya ankara yaci karo da Zaki a gabansa, Zaki ne kato gawurtacce wanda yake ji da karfi....

KU BIYONI GOBE IN SHA ALLAH DOMIN JIN YADDA ZATA KASANCE...
SADAUKI NE....
You can chat me up via WhatsApp domin mallakar paid books dina 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[14/03, 21:36] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 14

*Nace Ba Team Arfaat Kun Ce Zaku Raka Lamido Kwato Arfaat Amma Har Yanzu Bamu Jiku Ba, Kodai Kun Tsorata Ne Kun Gudu, Mu Team Baraka Muzo Mu Tayashi....*


Lamido ya nutsu tareda tattara hankalinsa waje guda yana karantar Zakin dake a gabansa yana tunano salon da zakuna suke amfani dashi wajen farmakar abun farmakinsu, strategy, zakuna suna farmakar the weak one ne ko kuma wanda ya ware kansa gefe ko kuma wanda ya gudu that's idan abun farmaka suna a group ne, sannan yana farmakar makasar abun harinsa ne ta yadda zai kashesa ba tareda ya samu damar kubuta ba, and yana mugun kamu ne da hokoransa masu kaifi....
Lamido ya k'ara nutsuwa yana karantar Zakin, yayinda Zakin yayi mashi zuru yana jiran lokacin da zai kai mashi farmaki, Lamido ya janyo hular karfe ya saka a kanshi tareda gyara tsayuwarsa, babu zato babu tsammani Zakin yayi tsalle tareda kawo mashi cafka, Lamido yayi tsalle yayinda Zakin ya cafki isa suka dure a kasa tareda juyowa a cikin zafin nama....
Zakin yayi gurnani tareda daka tsalle ya k'ara kawo mashi wata cafkar, Lamido ya sunkuya tareda zillewa ta kasa, a nan zakin ya fusata ya kawo mashi wata mahaukaciyar cafka suka kacame da artabu, k'ura ta tashi ta yanyane wajen, ya kama kafafun zakin da yake so yayi amfani dasu wajen tumurmusashi, Lamido ya tattara karfinsa tareda wurgar dashi gefe, kafin ya mike Zakin ya k'ara kawo mashi farmaki ya kaiwa hular karfen cafka wanda ya haddasa sauti saidai babu abun da ya samu hular kasancewata tana da quality sosai, Lamido ya kwaci kansa tareda damkar wuyan Zakin yayi wurgi dashi, wannan shine ya k'ara bata ran Zakin yayi tsaye kamar mai tunani sai kuma ya kawo mashi cafka suka kacame da fad'a wanda ya daukesu mintina talatin sannan Zakin ya rabu dashi ya juya heading to cikin dajin....
Lamido ya zube a kasa yana maida lumfashi saida ya kwankwadi ruwa sannan ya mike ya rataya jikarsa ya cigaba da tafiya, kayan yaki da yake sanye dasu sune suka saka Zakin bai ji mashi ciwo sosai ba saidai abun da ba'a rasa ba shima kuma yayi treating dinsa, gab da sallar zuhr ya shiga wani bangare wanda yake da saukin duhu saidai lokaci zuwa lokaci yana jin motsi, cak ya tsaya tareda kasa kunne domin jiyo ta inda sautin yake fitowa, a hankali ya zaro takobi daga kugunsa, kafin ya ankara wasu irin halittu masu kafafu guda hudu, suna tsalle tareda hawa bishiya suka mamayeshi, a nutse yake juyawa yana kallonsu yana nazartar wani abu sai kuma ya maida takobinsa ya zaro k'aramar wuka dake a

Please Login or Register in order to submit comment