Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ZAI SAMU NASARAR KUBUTAR DA ARFAAT?
SHIN MI ZAI FARU?
SHIN TA YA ARFAAT ZATA AMSHESHI BAYAN ABUN DA ALJANNUN SUKA SAKA TAYI WITNESSING?
SHIN KODA YAYI NASARA KUB'UTAR DA ITA TA YA ZAI RATSA DA ITA A CIKIN WADANNAN DAZUKA GUDA HUDU WADANDA SUKE DAUKE DA NAMUN DAJI MASU HATSARIN GASKE?

MU HADU A NEXT... PAGE... DOMIN JIN YADDA ZATA KASANCE...
SADAUKI NE....


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

[18/03, 20:42] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 16

Lamido yayi tafiya kadan sannan ya shiga dajin, a hankali yake tafiya yana mai kasa kunnuwansa at the same time yana mai karanta addu'o'en tsari saida yayi tafiya ta kusan awa daya da rabi sannan ya soma jiyo wani motsi wanda bai yarda dashi ba, ya tsaya waje tareda janyo takobinsa ya gyara mata zama a hannunsa, kafin ya ankara wasu gungun birirrika marar adadi suka zagayeshi, jikinsu sai salki yake suna kallonshi suna dariya, suka murtuke fuska, a hankali ya mayar takobin da ya zaro, ya zaro k'aramar wuka ya gyara mata zama a hannunsa tareda gyara tsayuwarsa....
A tare suka yo kanshi saida ya karanta addu'o'en tsari sannan shima ya afka masu suka soma artabu, yana caka masu wuka a wuya, ya rink'a tsalle a tsakaninsu yana caccakar masu wuya suna sakin ihu tareda zubewa a kasa suna komawa tiny dust, saida ya daukeshi awanni biyu suna artabu amma baiga alamar suna raguwa ba, kamar k'ara k'aruwa sukeyi, duk yadda yake kashesu amma yawansu ba ya ragewa....
Kamar hadin baki suka soma ja da baya suna tunanin salon da zasuyi amfani dashi suci galaba a kanshi, yana tsaye yana haki, gani yayi sun juya sun haye cikin itacen sun buya, babu zato babu tsammani guda ukku suka kawo mashi hari suka yankeshi a mabanbantan wajaje, zafi yaji har cikin kansa, da sauri yaja baya tareda maida wukar dake hannunsa ya zaro kibiya ya soma masu ruwanta, guda ukku yake had'ewa dukkanin wadanda suka kawo mashi farmaki tun suna a sama yake sakar masu kibiya su tarwatse a sama matattu, salo suka sauya suna fitowa a guda biyar, ya rink'a daka tsalle yana gocewa tareda harba masu kibiya babu ji babu gani, kamar string ya rink'a tsalle yana masu ruwan kibiya suna fadowa kasa matattu, amma sunki k'arewa kuma saura iccen kibiya kadan ya rage mashi, salo ya sauya ya rink'a rolling a kasa yana tsintar iccen kibiyar yana harbinsu, yana mai karanta addu'o'en tsari, saida suka wuni duhu ya kawo kai sannan ya k'arar dasu yayinda dajin yayi shiru, ya zube a kasa yana maida lumfashi, shi kanshi har mamakin kanshi yake ganin yadda ya wuni cur yana artabu ba tareda ya sare ba, tabbas tasirin addu'o'en da yayi ne, ya mike zaune ya janyo guzurinsa yaci ya kora da ruwa ya gyara raunikan da sukayi mashi ya wanke inda jini ya b'ata mashi sannan yayi alwalla ya rama sallolin da suka riskeshi a lokacin da yake artabu dasu, a nan ya yada zango ya karanta addu'o'e ya tofe wajen sannan ya kafa tanti ya shiga ciki, bayan ya gama sallar Isha'i ya jima a zaune yana azkar sannan ya shafa addu'a ya kwanta babu b'ata lokaci bacci yayi awon gaba dashi, sai gefen sallar subh sannan ya farka yayi alwalla ya soma jera sallah, yayi sallar subh ya koma bacci saida gari yayi haske sosai sannan ya farka yayi kalaci ya tattara abubuwansa and the journey continue....
Tafiya kadan yayi ya soma jiyo wani gurnani mai tsoratarwa saida ya toshe kunnuwansa, kafin ya ankara wasu halittu masu kafafu guda shidda tareda kawuna guda biyu suka tare mashi hanya, saida ya firgita da ganinsu, suna da girma sosai, guda goma ne cur, a lokaci guda sukayi kanshi suna kai mashi attack da dukkanin kawunansu and kafafu, ya rink'a tsalle yana k'arewa tareda sararsu saidai takobin ta bada sound amma bata huda jikinsu, takobin ba ya tasiri a kansu tamkar yana dukan dutse haka yake ji, tun yana gocewa sararsu basu samunshi har suka fara samun nasara a kanshi, cikin k'ank'anin lokaci suka mashi jina-jina, ya gama gabaita, daya daga cikinsu ta saka jela ta wurgar dashi ya bugi icce ya fado kasa tareda sakin k'ara...
Sukayi kanshi zasu gama dashi, fuskar Arfaat ce ta fad'o mashi a brain yayinda maganar Maryam ta dawo mashi a kunne inda take cewa...
"Kadda kayi sakaci da addu'a...".
Lamido ya bude idanunsa yana mai karanta addu'o'en tsari, kamar iccen kibiya haka yayi tsalle ya rink'a falfala gudu a kansu yana mai karanta addu'o'e yana sararsu yayinda suke ihu sassan jikinsu suna fadowa kasa, ya addabesu, ganin haka suka ja da baya tareda wangame baki suna harbo mashi wani dogon abu mai tsini, cikin zafin nama ya rink'a rolling a sama yana kaucewa tareda wawuro garkuwa yana tsalle yana rolling tareda k'are abun da suke watso mashi, a nan ne yakin ya sauya salo, ba ya attacking dinsu yana defending kanshi ne kawai, ganin zasu samu lagonshi, ya rink'a shammatarsu yana harba masu mashi yana farmakar tsakiyar kansu yayinda suke faduwa a kasa matattu, ya rink'a tsalle yana rolling yana k'are farmakinsu tareda farmakarsu da mashi, cikin mintina biyar ya gama dasu ya zube a kasa yana maida lumfashi, ya jima a haka sannan ya mike zaune ya gyara raunikan da suka ji mashi, ya wanke jini da ya b'ata mashi kaya, yayi alwalla ya rama sallolin da suka riskeshi yana artabu dasu saida ya gama sannan yaci abinci ya kora da ruwa, a lokacin bayan sallar Asr ne idan yace zai cigaba da tafiyar bai san abun da zai tarar ba don haka ya tofe wajen da addu'o'e ya kafa tanti....
Washegari ya tattara kayansa ya cigaba da tafiya, tako kadan yayi yaga yanayin dajin ya sauya mashi dukkanin inda ya saka kafarshi yana takawa ne a cikin tabo ne, kafin ya ankara yaji an riko kafarshi tareda janshi a ciki, cike da zafin nama ya fizge kafarsa yayi tsalle ya duro a gefe saidai a inda ya duro shima kafar aka rik'e mashi, ya fizge yayi tsalle tareda k'ara sauka a wani wajen still bata sauya zani ba, wannan karon hannuwa biyu ne suka kama mashi both kafafu suka soma janyoshi a ciki....
Cike da zafin nama ya fizge kafarsa yayi tsalle tareda rolling a sama ya sauka a saman bishiya, yana nazarin wajen, ya zaro reshe ya wulla a kasa saidai babu abun da ya bayyana....
Durowa yayi daga saman bishiyar wanda kamar jira ake hannuwa guda hudu suka kama kafafunsa suna janyeshi da nufin nutsar dashi a cikin tabon....


Lamido ya zaro Adda daga kugunsa ya karanta addu'a tareda farmakarsu a take ya sare both hannuwan suka zube a cikin tabon, yayinda wajen yayi wata girgiza ya tarwatse, ya k'ara tako guda biyu yayinda wasu hannuwan suka k'ara rik'e kafafunsa tareda fizgarshi a ciki, ya saka addarsa ya fillesu wanda ya faru tareda tarwatsewar wajen, daga nan ne suka sauya salo suna janshi ba tareda sun bayyana hannuwan ba, da karfi ya fizge kafarsa yayi tsalle tareda rolling a sama ya sauka akan bishiya ya dana kibiya tareda harbata a daidai inda aka rikeshi karshe, wata k'ara aka saki, wajen ya tarwatse, ya k'ara sauka hannuwa suka rikeshi ya fizge tareda sauka akan bishiya ya sakarwa wajen kibiya, a take wajen yayi bindiga, a haka ya rink'a masu dauki daya-daya, daga baya suka sauya salo suna sauya waje da zarar yayi tsalle before yayi attacking dinsu, ganin haka hankalinsa ya tashi ya rasa ta inda zai bullo masu, wata dubara ce ta fad'o mashi, ya rink'a observation wasu abubuwa tareda d'ana kibiya guda ukku a tare sannan ya saki, a take wajajen suke tarwatsewa, a take dajin ya soma girgiza yayinda wasu munanan halittu suka bayyana, cike da zafin nama Lamido ya maida kibiyarsa a inda take ya zaro gatari guda biyu yayi rolling tareda sauka kasa yana attacking dinsu yana mai karanta addu'o'en tsari, ya rink'a sare masu hannuwa da kafafu da kawuna saidai su fadi a kasa matattu, yana kashe wasu ne yayinda wasu suke fitowa daga kasa, saida suka kai har bayan Isha'i suna wannan artabu sannan ya samu nasarar kashesu baki daya, yayinda yanayin dajin ya koma daidai ya zube a kasa, yana maida lumfashi...
Saida ya huta sannan ya mike yayi alwalla yayi sallolin da suka rikeshi yana yakin sannan yaci abinci ya d'aga sulkarsa ya kwankwadi ruwa, ya kwanta bacci ne yayi awon gaba dashi....
Washegari bayan ya kimtsa ya dasa tafiya, saida awa biyu yana tafiya, a wannan bigire ne yaga dajin ya soma sauyawa yayinda wasu kananun halittu suka tare mashi hanya suna rik'e da makamai masu hatsari, katuwar takobinsa dake rataye a bayansa ya zaro ya rik'eta da hannu biyu yana kallonsu, a tare suka kawo mashi hari suka yanyameshi suna farmakarsa ta kowanne bangare, ya rink'a tsalle a tsakaninsu yana wulle kanuwansu yayinda suke kamawa da wuta suna b'acewa, ya rink'a kutsawa a cikinsu yana masu b'arna, yana tare attack da suke mashi yana attacking dinsu, cikin kankanin lokaci ya gama dasu duk da yawa da suke dashi, ya zube a kasa yana maida lumfashi yayinda dajin ya koma yanayinsa na ainihi, yayi alwalla yayi sallar zuhr yaci abinci ya kora da ruwa sannan ya mike ya cigaba da tafiya gab da sallar Asr ya isa wani waje mai dauke da wasu kananan ramuka ya rink'a bi ta gefensu, yana tako a hankali yana mai rik'e da takobinsa...
Saida ya kai tsakiya wasu dodanni suka soma fitowa daga ramukan suka zagayeshi kafin ya ankara saidai ji yayi an buga mashi guduma a saman kai saidai yayi sama-sama sannan ya fado kasa a sume....
Saidai farkawa yayi ya ganshi underground, an daureshi a sama upside down, sun kunna wuta sun daura wani katon tukunya suna dariya, yayi lamo kamar bai farkaba yayinda a lokaci guda yake karanto addu'o'en tsari, ya zaro wuka cikin dubara ya rink'a yanka igiya dake a hannunsa har ya yanketa yayi wuf ya datse ta kafarsa yayi rolling tareda durowa a kasa, ya zaro takobinsa yana mai kabbara, a tare sukayo kanshi ya rink'a tsalle yana taka kanuwansu yana fille masu kai, tareda had'a masu da naushi a kai yana ball dasu, saidai ya kasa kashe koda daya daga cikinsu domin yana fille kansu yake komawa yana manne kansa da kansa, hankalinsa ne ya tashi ya soma tunanin yadda zai bullo masu, wani abu ya gani a gefen kugunsu wanda yake hallawa lokaci zuwa lokaci, yayi tsalle tareda rolling a sama, yana a saman iska ya zaro kibiya ya saita wajen ya harba kibiyar ta shige yayinda halittar ta fasa ihu ta tarwatse, a nan ne ya soma samun nasara a kansu ya zaro wata zabgegiyar bulala mai hade da tsini ya rink'a tsalle yana tsune wajen suna tarwatsewa, duk wanda yayi attacking saidai ya tarwatse, ganin haka suka k'are wajen, ya maida bulalar tareda zaro takobi ya rink'a farmakarsu babu ji babu gani, duk wanda ya shagala ya fille wajen yayinda zai tarwatse a haka ya k'arar dasu yayinda wajen ya soma girgiza ya koma aihinin dajin sab'anin before da yake a underground....
Lamido yayi alwalla tareda yin sallah yaci abinci ya kora da ruwa, yayi addu'a tareda kafa tanti, a nan ya kwana....
Washegari gari ya dasa tafiyar, tako kadan yayi ya soma jin girgiza yayinda wata katuwar halitta ta bayyana a gareshi, saboda girmanta bai wuce finger dinta guda daya ba, ya soma falfala gudu yayinda take saka kafafu zata takeshi, ya rink'a guje-guje yana goce mata, cikin kankanin lokaci ya galabaita, kabbara yayi yana mai karanto addu'o'en tsari yayi tsalle ya haye saman kafarta ya rink'a falfala gudu a samanta duk yadda take saka hannuwa tana bugeshi amma ta kasa, saida ya dangana da kanta sannan yayi wuf ya shige cikin kunnanta ya dangata da can ciki ya fille makasarta yayinda yayi fitar bullet daga ciki ya soma saukowa a sama yayinda ta fasa k'ara tareda tarwatsewa a iska, yayi rolling tareda sauka a kasa saida kafafunsa suka amsa saboda nisan tazarar dake tsakaninsa da kasa amma abun mamaki babu abun da ya sameshi....
A wannan dajin ya yada zango ya kwana sannan washegari ya dasa with the journey, saida yayi tafiyar awanni hudu sannan ya soma hango wani katon dutse, ya zaro taswirar dake hannunsa ya duba, wadda ta nuna a daidai cikin dutsen ne Arfaat take, hamdala yayi tareda godewa Allah, ya k'ara sauri, yana k'ara matsawa ya hango wasu gungun aljannu masu siffar mutane wadanda suke dauke manyan makamai suna zagaye da wajen, yawansu ya kai dubu dari da doriya....

SHIN YA ZATA KAYA A TSAKANIN LAMIDO DA WADANNAN GUNGUN ALJANNU DA SUKE TSARON DUTSEN DA TAKE A CIKI?
WANI IRIN ARTABU ZASUYI?
SHIN ZAI SAMU NASARAR K'ARAR DASU HAR YAJE ZUWA GARETA?
SHIN TA INA ZAI IYA SHIGA WAJEN YA KUB'UTAR DA ITA TUNDA DAI BABU KOFA A CIKINSHI SANNAN KOFA DAYA CE TA SAMA KUMA BABU HALITTA DA ZATA IYA TSALLAKAWA HAR SAMA SABODA MATUK'AR TSAYONSA?
SHIN IDAN YA SAMU NASARAR FITA DA ITA DAGA WANNAN DUTSEN ZAI IYA SAMUN NASARAR FITA DA ITA DAGA DAJIN BAKI DAYA?

KU BIYONI A NEXT PAGE DOMIN JIN YADDA ZATA KASANCE...
SADAUKI NE....


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[20/03, 22:01] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 17

*Ban Dace Dashi Ba Complete 600, Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion complete 400, chat me up via WhatsApp 09169472057... Pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai ku tura recept via WhatsApp 09169472057....*

Lamido ya zaro takobinsa ya durfafi dutsen, suna hangoshi suka soma mashi ruwan kibiya yayinda ya saka garkuwa yana tarewa tare tsalle yana rolling a sama shima yana aika masu da kibiya yayinda wuta take kamasu suna konewa, yana mai karanta addu'o'en tsari yana rolling tareda tsalle yana k'are farmakinsu, kamar daukewar ruwa suka daina harbo mashi kibiya yayinda wasu gungun katti daga cikinsu wadanda akalla zasu kai dari daya suka nufo inda yake, suka kacame da yaki yayinda yake kabbara yana farmakarsu tareda tare farmakin da suke kawo mashi, saida suka wuni suna fafatawa sannan ya kashesu baki daya, ya d'aga sulkar ruwansa ya kwankwada sannan ya falfala da gudu ya kutsa ta cikinsu suka cigaba da artabu, yawansu ya zarce tunaninsa domin gani yake kamar k'ara yawa suke, yadda suka farmakarshi naci da karfin addu'a ne kawai ya saka suka kasa galaba a kanshi, ya rink'a tsalle a tsakaninsu yana farmakarsu tareda kare farmakinsu, saida suka kwana suka wuni suna fafatawa, duk yadda yake tare attack dinsu amma saida suka ji mashi raunika masu yawa, ya zube a kasa yayinda suka zagayeshi suka fashe da dariya ya rumtse idanu yana mai karanto addu'o'en tsari, a take suka rink'a ihu suna kamawa da wuta suna tarwatsewa har suka k'are baki daya, yaja jiki ya jingina da bangon ya gyara raunikan da sukaji mashi yaci abinci ya kora da ruwa sannan ya rama sallolin da suka sameshi yana artabu dasu, bacci ne yayi awon gaba dashi saidai farkawa yayi yaga haske yayi, ya mike tsaye yana kallon dutsen amma babu ta inda zai shiga ciki, kabbara yayi tareda saka hannu ya tura dutsen a take wata katuwar kofa ta bayyana, ya tura kai ya shiga da addu'a akan bakinsa....
Wasu gungun aljannu ya tarar rike da manya-manyan takubba suna fuskantarshi yayinda Arfaat take rakube daga gefe, ta ware idanu tana kallonshi saying,
"Yaa Lamido...".
Lamido yace, "Arfaat...".
Daga daya cikin aljannun ya daka mashi tsawa sannan yace,
"Ka juya ka koma inda ka fito domin kuwa baka isa ka fitar da ita daga wajen nan ba...".
Lamido yace, "K'arya kake, kamar yadda da taimakon Allah madaukakin Sarki na samu galaba akan sauran hakanan kuma zan gama daku sannan in kub'utar da matata Arfaat...".
A tare suka fashe da wata mahaukaciyar dariya sai kuma suka murtuke fuska tareda afka mashi suna kai mashi farmaki ta kowanne bangare....
Arfaat ta ware idanu tana ganin yadda Lamido yake daka tsalle yana rolling a saman iska tareda kai masu hari da takobinsa yana fille masu kai, yana yawo a cikinsu yana tare attack da suke kawo mashi tareda attacking dinsu, gani tayi ya k'ara zaro wata takobin yayinda Aljannun suka zagayeshi, ya rink'a tsalle a tsakaninsu yana farmakarsu yana sauke masu kawuna, cikin kankanin lokaci ya gama dasu....
Daga daya cikinsu wanda yake kakarin mutuwa ya kalli Lamido cike da tsana sannan yace,
"Duk da ka gama damu amma akwai sauran rina a kaba domin kuwa akwai tawaga guda wadda zata iya k'araso nan a kowanne lokaci, sune manyanmu...".
Sai kuma ya fasa k'ara yayinda jikinsa ya kama da wuta ya kone kurmus...
Lamido ya k'arasa inda take tareda duk'awa ya kama hannunta saying,
"Arfaat... I'm here... Your husband is here for you... Tashi muje tun kafin wadanda yace suzo...".
Arfaat ta mike tsaye ya kama hannunta tana yunkurawa long gown dake jikinta ta harde mata kafafu, tayi taga-taga ya tarota, ya kalleta ta nuna mashi gown dake jikinta wadda har tana sharar kasa ne, ya saki hannunta ya zaro wuka tareda sunkuyawa ya tattara kasan rigar ya yankeshi, ya yanke hannuwan wadanda suke dogaye sannan ya kama hannunta suka bar dutsen yana rik'e da hannunta suna gudu, tsayawa yayi cak ya dubeta yace,
"Arfaat zaki iya cigaba da gudun ko kuma in goyaki...".
Arfaat ta girgiza kai saying,
"A'a...".
Suka cigaba da gudu, wata iska kasa mai tattare da yashi-yashi ce ta taresu saida suka duka saboda karfinta, rundunar mayakan aljannu suka bayyana...
Lamido ya kalli girma da yawan rundunar sannan ya juya ya kalli Arfaat, ya sauya direction yana falfala gudu yana jaye da ita yayinda rundunar aljannun ta mara masu baya, ba suyi nisa ba suka cimmasu suka zagayesu ta kowanne bangare....
Wani katon aljanni marar kyan gani dake a sahun gaba ya dakawa Lamido tsawa sannan yace,
"Kayi kadan kazo har fadarmu kayi mamu b'arna ka kashe mamu mutane sannan kuma ka koma inda ka fito lafiya, dole ne sai munyi maka kisan wulakanci... Sannan kuma kayi kadan kazo har fadarmu sannan ka gudu da Lailah domin kuwa ita mallakinmu ce...".
Lamido ya daka mashi tsawa saying,
"K'arya kake... Arfaat ba mallakinku bace ba... Ku matsa ku bani waje in wuce da matata ko kuma in fille kawunanku sannan in taka ta samansu in wuce...".
Aljannin ya fusata saying,
"Ku afka mashi ku gama dashi, ku fille mashi kai ku miko min nan... Ita kam kadda wanda ya tab'a koda silin gashinta... Shugabarmu ce...".
A tare suka afkawa Lamido yayinda ya zaro takobinsa, ya juya ya dubi Arfaat saying,
"Ki matsa kiyi zamanki a can kafin in share maki hanya...".
Sai kuma ya daka tsalle tareda rolling a saman iska ya afka a cikinsu, suka kacame da artabu, Arfaat ta ware idanu tana kallonshi cike da mamaki....

Lamido da dukkanin karfinsa yake yak'arsu yana tarwatsasu suna faduwa kasa a sandare, yana fille masu kai da kafafu suna faduwa kasa yayinda wuta take kamasu suna tarwatsewa, saida ya daukeshi awanni ukku yana artabu dasu sannan ya k'arar dasu baki daya, yayi tsaye yana maida lumfashi tareda kallon dayan aljannin wanda yake kallonshi a matuk'ar fusace, ya fasa ihu saidai dajin ya amsa sannan ya rikid'a ya koma wata mummunar halitta yayo kanshi, suka kacame da yaki, duk yadda Lamido yake k'ok'arin tarewa amma ya kasa saboda karfin ba daya ba, karfin addu'a ne ya ceceshi da tuni ya gama dashi ta sanadin b'acewa da yakeyi yana bayyana ta wani wajen yana kawo mashi attack, ya saka kafafu yayi ball dashi saidai Lamido yayi sama-sama sannan ya fad'o a galabaice, ya k'arasa ya daukeshi tareda damkar wuyansa ya mik'ar dashi tareda rabashi da kasa, Lamido ya soma kakarin mutuwa...
Arfaat ta fasa ihu saying,
"Yaa Lamido...".
Lamido ya bude idanunsa yana mai karanto addu'o'en tsari sannan ya shammaceshi ya zaro k'aramar wuka saidai yayi kabbara sannan ya caki saitin zuciyarsa, babu shiri ya sakeshi yayi taga-taga ya fad'i kasa yayinda jikinsa ya soma kamawa da wuta, yayi murmurshin mugunta sannan yace,
"Lamido ka daina ganin ka samu nasarar k'arar damu kuma ka tafi da ita kayi tunanin kayi nasara, tun kafin a fara yak'in mukayi nasara, abun da muka dasa mata a jiki shine zai zame maku bakin ciki a rayuwa, bazai tab'a bari kuyi farin ciki a rayuwa ba, zai hana rayuwarku sukuni... Tun ran gini tun ran zane, ba zaka tab'a samun zuciyarta ba, ke kuma kiyi sani cewa namiji zai iya komai domin samun abun da yake kwadayin samu... Yanzu wasan zai soma...".
Lamido ya zaro mashi ya wurga mashi yayinda yayi ihu tareda tarwatsewa into piece, lokaci guda dajin ya soma girgiza, Lamido ya falfala da gudu tareda hugging Arfaat wacce ta gama rudewa, kamar daukewar ruwa komai ya tsaya yayinda dajin ya sauya zuwa ainihin yadda yake....
Lamido ya zube a kasa yana maida lumfashi, ya zaro sulkarsa ya mik'a mata tasha sannan shima ya kwankwada, suka huta, ya mike saying,
"Muyi sallah...".
Ya mik'a mata abun ruwa dake wajensa yace,
"Kiyi alwalla...".
Saida ta zagaya sannan ta kama ruwa ta dawo ta soma alwalla tana yi tana kallonshi kamar wacce taga sabuwar halitta, idan suka had'a idanu yayi mata murmurshi, tana gamawa ta mik'a mashi ya amsa yayi, ya mik'a mata wani katon bargo ta yane kanta dashi sannan ya jasu sallah, bayan sun gama ya dauko fruit daga cikin guzurinsa yace,
"Kici wanda kike so, idan kuma baki son wannan sai in shiga cikin dajin in farauto maki dukkanin abun da kike so...".
Arfaat ta girgiza kai ba tareda tace komai ba ta dauki one of the fruits ta soma ci, shima ya dauka yana ci yana mata murmurshi, bayan sun gama ya hado itace ya had'a mata tanti, yace,
"Ki shiga ki kwanta zanyi gadinki, kadda ki damu ki kwantar hankalinki kina tare dani, nayi wa Ummy alk'awarin zan kai mata ke a cikin koshin lafiya kuma in shaa Allah zan cika alk'awarin da na dauka mata...".
Arfaat ta mike ta shiga cikin tantin yayinda ya had'a wuta a waje, ya lullub'e da bargo yana maganin sanyin dake shigarsa, Arfaat ta leko tana kallonshi ta jima a haka saida taga zai juyo sannan ta juya ciki ta kwanta, bacci ne yayi awon gaba da ita yayinda maganganun aljannin nan suke dawo mata a kwanya inda yake cewa....
"Abun da muka dasa mata a jiki shine zai zame maku bakin ciki a rayuwa, bazai tab'a bari kuyi farin ciki a rayuwa ba, zai hana rayuwarku sukuni...".
Bacci ne yayi awon gaba da ita....
Throughout the night Lamido bai rumtsa ba yana guard dinta, lokacin sallar subh ya tayar da ita ya jasu sallah, suna gamawa ya soma gangandi, bacci ne yayi awon gaba dashi, ta zuba mashi idanu kamar wacce taga sabuwar halitta, saida gari yayi haske sannan ya farka, ya dubeta saying,
"Sorry ina ta bacci... Muje ki rakani inyi mamu farautar abun da zamuci...".
Mikewa yayi yana gaba tana biye dashi, ya farauto masu dabba suka dawo ya gasa suka ci suka kora da ruwa sannan ya mike ya tattara abubuwansa suka nausa a cikin dajin, sallah ce kawai take tsayar dasu sai kuma abinci sai kuma idan ta gaji su tsaya ta huta yace,
"Arfaat, ki bari in goyaki...".
Arfaat ta girgiza kai saying,
"Zan iya...".
Gab da sallar Magrib suka isa gab'ar ruwan, suka yada zango ya kafa tanti, ya ratsa ta cikin ruwan yayi collection small dabbobin ruwa dake a gabar ruwan, ya dawo bayan sunyi sallar Magrib da Isha'i ya kunna wuta ya gasa masu suka ci, ta shiga cikin tantin ta kwanta yayinda yake zaune a wajen wutar, bacci ne yayi awon gaba dashi sai gab da sallar subh sannan ya farka ya mike da saurinsa ya leka tantin hangota yayi kwance ya dawo ya zauna yana mai sauke ajiyar zuciya....
Da safe bayan sunyi kalaci da kifin da ya kamo masu, ya dubeta saying,
"Kiyi wanka...".
Arfaat ta dubeshi ta dubi wajen da mamaki akan fuskarta, Lamido yace,
"Kadda ki damu....".
Sai kuma ya mike ya nausa cikin dajin ya dawo da itace ya kewaye cikin ruwan yabar waje ta inda ruwan zasu rink'a shiga, ji yayi ta fasa k'ara ya

Please Login or Register in order to submit comment