Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye akan table saying,
"Thanks...".
Ta koma ta zauna akan kujerar da ta tashi, dukkanin abun da yake faruwa Ammi tana lura dasu, Abeed yayi spoon daya na couscous, yace,
"This is not delicious... Not yummy fa... Baraka ashe baki iya girki ba...".
Lamido ya kanne mashi ido saying,
"Hala gishiri yayi yawa...".
Ammi tace, "Kai ban san shakiyanci don kunga ita kadai ce, bata da mai tare mata shine zaku tarar mata ita daya...".
Abeed yayi dariya saying,
"Laifinta ne tasan zata zo wajen abokan wasa (y'ay'an maza da y'ay'an mata) kuma bata da baki sai tazo da mai tare mata...".
Ammi tace, "Zan shigarwa diyata ne, daga mai jinyar har wanda yake jinyarsa in had'asu duka, babu ruwana...".
Lamido yana gamawa yace,
"Kinyi breakfast?".
Baraka ta girgiza kai ba tareda tayi magana ba ballantana kuma ta d'ago ta kalleshi, ji tayi yace,
"Kiyi serving sauran kici...".
Saida tayi jim sannan tayi serving ragowar ta saka spoon, abincin yayi mata dadi har ga Allah, ta cigaba da ci a nutse....
Aseeyerh ta shigo tana tafiya sannu a hankali irin tafiyar masu tsohon ciki, tace,
"Sis Baraka...".
Baraka ta d'ago saying,
"Aseeyyy... Maman baby...".
Aseeyerh tace, "Sis Baraka enjoy your food... Ammi, bara naga big bro...".
Lamido ya kama hannunta yana murzawa a hankali, yace,
"Our little didi...".
Aseeyerh ta turo baki saying,
"Yaa Lamido you looks sad...".
Lamido ya ware idanu saying,
"But I'm smiling...".
Aseeyerh ta girgiza kai saying,
"Pretending kawai kakeyi... Yaa Lamido ka kwantar da hankalinka In shaa Allah Arfaat zata dawo garemu a cikin koshin lafiya, ka cire damuwa daga ranka... Mun yanke shawara dani da Yaa Abeed wannan cikin dake gareni, idan har na haifi mace zamu saka mata sunan Arfaat ne za'a rink'a kiranta little Arfaat, zamu bar maka ita, a wajenka zata zauna har zuwa karshen rayuwarta...".
Lamido ya juyo inda Abeed yake, murmurshi yayi mashi tareda gyad'a kai, Lamido ya lumshe idanu ya bude yayinda murmurshi ya bayyana akan fuskarsa, yana murza hannunta a hankali yace,
"Thanks so much...".
Aseeyerh yace, "Ban san thank you, damuwa ce bana son gani a tattare da kai wannan shine godiyar da zakayi min... Ammi na soma jin yunwa...".
Lamido yace, "Kin koma acici dai...".
Aseeyerh tace, "Da lafiyata gwara inci...".
Ammi tayi serving mata breakfast da suka kawo, Aseeyerh ta zauna tana ci hankalinta kwance, wannan cikin yana sakata cin abinci ne sosai....
Doctor ne ya shigo yayi discharging tareda bashi shawara akan yadda zai kula da lafiyarshi....
Aseeyerh tace, "Kaji dai Yaa Lamido don haka ka cigaba da kula da lafiyarka saboda masu kaunarka...".
Doctor ya dubi Baraka yace,
"Itace Madam din...".
Lamido zaiyi magana, Abeed yayi karaf yace,
"Wannan amaryar ce... Amaryar uwar gida...".
Doctor yace, "Allah ya kaimu lokacin...".
Abeed yace, "Amin...".
Doctor ya fice bayan da ya basu discharge letter, Lamido yayi wa Abeed wani mugun kallo, Abeed yayi kamar bai lura ba, Ammi murmurshi kawai tayi....


Lamido da Abeed ne suka fara shiga parlor, Ammi tana biye dasu followed by Aseeyerh da Baraka, Maid suka biyosu suna dauke da kaya niki-niki....
Baraka tace, "Ammi bara inje in gyara mashi bedroom dinsa...".
Lamido zaiyi magana, Ammi ta rigashi saying,
"Okay kije ki gyara mashi... Allah yayi albarka...".
Baraka tace, "Amin...".
Heading to the staircase....
Ammi ta bita da kallo tana murmurshi, a hankali tace,
"Lamido ya kamata ace kayi aure?".
Lamido yace, "Amma Ammi shekarar da ta wuce da kuka matsa min na yarda amma Mom tace bata san zancen ba, ni kuma yanzu bani da ra'ayin auren...".
Ammi ta girgiza kai kawai ba tareda tace komai ba...
Baraka tana shiga bedroom din ta rike kugu tana bin ko'ina da kallo, ko'ina clean and neat yake, babu dirt, Frames ne a kowacce kusurwa kowanne an rubuta Arfaat da style mai kyau, tareda zanen potrait dinta, ta rumtse idanu ta bude ta cire veil dake akan shoulder dinta ta zage ta gyara ko'ina na part din tun daga kan parlor, bedroom har zuwa bathroom, ta saka turaren wuta, part din ya dauki kamshi mai sanyi, ta fito zuwa parlor saying,
"Ammi na wuce gida...".
Ammi tace, "Tun yanzu, kije bedroom dina akwai leather din perfumes akan bedside table ki dauka...".
Baraka tace, "Na gode...".
Jim kadan ta dawo tana dauko da leather tace,
"Ammi na gode...".
Ammi tace, "Ki gaida Hajiya Murjanatu...".
Baraka tace, "In shaa Allah... Yaa Lamido, Allah ya k'ara sauki...".
Lamido yace, "Amin...".
Ammi tace, "Aseeyerh ki tashi kibi mijinki ku wuce gida...".
Aseeyerh ta b'ata fuska saying,
"Ammi korata kike, torh kafin in tafi a bani dambun nama inci inyi guzuri...".
**********
Hajiya k'arama tace, "Hajjo sai ku tashi muje mu dubasu...".
Ummy tace, "D'azu naji ana cewa za'a sallameshi amma bari in kira Hajiya Bilkisu inji idan suna can kadda kuje ku samu basa nan...".
Aunty Hajjo tace, "Ki kirata sai muji...".
Ummy ta jima akan waya tareda Ammi sannan tayi hanging call din, saying,
"Anyi discharging dinsu, suna gida...".
Aunty Hajjo ta mike saying,
"Sultan... Nabila... Ku tashi... Hajiya Zainab ki rage sakawa kanki damuwa ko domin wadannan yaran, suma kina sakasu cikin damuwa ne, kadda hakan ya tab'a rayuwarsu...".
Hajiya k'arama tace, "Ga issue din lafiyarki...".
Ummy tace, "In sha Allah zan kiyaye...".
Hajiya k'arama, Aunty Hajjo, Nabila da Sultan suka fita, direct suka wuce gidansu Lamido, maid suka tarar a parlor ta k'arasa dasu har falon Ammi, Ammi ta tarbesu da fara'a saying,
"Sannunku da zuwa... You are welcome... Safiya ki kawo masu drinks da snacks...".
Suka mata ya mai jiki, ta amsa da fara'arta, Ammi tace,
"Bara in kira maku shi...".
Aunty Hajjo tace, "A'a, kadda ki tasoshi, shi da baya da lafiya, zamuje da kanmu mu dubashi...".
Maid ta rakasu har bedroom dinshi, yana kwance akan sofa ya k'urawa ceiling idanu, jallabiya ce a jikinsa, ya mik'a zaune saying,
"Aunty Hajjo... Aunty Maijidda...".
Ya bude hannuwa, Nabila da Sultan suka ruga, yayi hugging dinsu, Aunty Hajjo da Hajiya k'arama suka zauna....
"Ya jiki?".
"Da sauki...".
"Allah ya k'ara sauki...".
"Amin...".
"Ka rage damuwa, ka daina sakawa zuciyarka abubuwa...".
"In shaa Allah...".
"Muna ta ganin abubuwan alkhairi... Allah ya k'ara budi...".
"Amin..".
Sun dan tab'a hira kafin suka mike, Aunty Hajjo tace,
"Kuma ina nan ina jiran ka kawo min surukata ko kuma inyi maka auren dole, nidai babu ruwana...".
Lamido yace, "Na tuba Aunty Hajjo...".
Aunty Hajjo tace, "Babu wani dadin baki da zakayi min...".
Lamido yace, "Da girman kujerarki...".
Aunty Hajjo tace, "Oho... Nabila, Sultan, ku tashi muje...".
Lamido yace, "Zasu zauna a nan, da marece sai in saka a mayar dasu gida...".
Aunty Hajjo da Hajiya k'arama suna komawa parlor suka tarar da Mom zaune ta daura kafa daya akan daya tana yatsine fuska...
"Hajiya Murja... Barka...".
Babu yabo babu fallasa Mom tace,
"Barkanmu...".
Ammi tace, "Bara a kira maki shi...".
Mom tace, "Kadda ki damu tunda ni ba bakuwa bace ba, er gida ce, dake dashi ku sameni a sashen yaya...".
Sai kuma ta mike ta wuce tana tako daya bayan daya, Aunty Hajjo da Hajiya k'arama saying,
"Mu mun wuce, Lamido yace saida marece zai saka a mayar dasu...".
Saida Mom ta rakasu har mota sannan ta juya ta wuce sashen Lamido, tare dashi suka wuce sashen Abbi....
Mom tace, "Yaya dama nazo ne in baku shawara akan rayuwar da kuka saka yaron nan duk da dai dama ba jin maganata kukeyi ba, ni koda kun watsa kasa a idanu bazan damu ba tunda dai na fad'a maku gaskiya...".

WhatsApp 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰


💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 6


*This Page Is Dedicated to Shinkafi (admin sune suka janyo min 2), and of course team Arfaat R...*


Abbi yace, "Mi kike so kice? Ina jinki?".
Mom tace, "A halin da yaron nan yake a ciki ya kamata ku nemo mashi mata yayi aure sannan he have to be in therapy, therapy session...".
Lamido yace, "Ban shirya k'ara aure ba saboda matata zata dawo gareni same with the other thing, and gobe first thing in the morning zan wuce Italy akwai business seminar da zanyi attending...".
Ammi tace, "What? Baka da lafiyar zaka tsallake ka bar kasar...".
Mom tace, "Aww ashe kin damu da lafiyarsa dama amma kika bari aka had'ashi da dangin mats*fa...".
Lamido ya rumtse idanu saying,
"Mom ki daina aib*ta matata, ban san kice nayi maki rashin kunya...".
Mom ta dafe kirji idanu a waje saying,
"Kace... Koda yake ba laifinka bane tunda baka tab'a min ba, wa ya sani ko har Alj*nnunta sun fara shafarka... Yaya sai ku had'a mashi har da maganin alj*nnu...".
Lamido ya d'aga murya saying,
"Mom please... Damn it...".
Sai a lokacin Ammi ta saka baki saying,
"Lamido kadda in k'ara jin kayi magana a wajen nan...".
Lamido yace, "I'm sorry but domin inyi wa maganarki biyayya I have to walk out of this place, I can't stay inda ake zagin matata Arfaat...".
Ya mike heading to the door...
Da kakkausar murya Abbi yace,
"Lamido dawo ka zauna... Murja kadda in k'ara jin bakinki a nan tunda kun gama maganganunku sai ku bari ni kuma in yanke hukunci a kai...".
Saida ya lumfasa sannan yace,
"Lamido a gabana kake rashin kunya wa Auntynka... Ke kuma murja da kike kiranta dangin mats*fa, na tabbata idan aka makaki k'ara a kotu baki da hujja... Ka bata hakuri ke kuma ki iya harshenki...".
Lamido ya rumtse idanu saying,
"Mom kiyi hakuri...".
Mom tace, "It's okay...".
Abbi yace, "Back to shawarar da kika kawo, Murja ya kike son muyi.. Shekara guda da ta wuce muka tursasashi har ya yarda zai auri Baraka amma kika hana... Saboda a wancen lokacin da kika samemu maganar had'asu aure bamu amince ba, ki tuna a wancen lokacin kin zo min da maganar ne bayan da na gama magana da mahaifin Arfaat... Shin so kike in koma ince mashi na fasa zan aura mashi diyar k'anwata ne?".
Mom tace, "Yaya Muneer ba haka bane, na hana auren ne saboda ina gudun kadda alj*nnun dake akan Arfaat su cutar da ita...".
Abbi yace, "Here you are again kina maganar Alj*nnu...".
Mom tace, "Dole inyi maganarsu saboda abun tsoro ne musamman na saman kan wannan yarinyar... Zan wuce...".
Abbi yace, "Koma ki zauna...".
Mom ta koma ta zauna ba don ranta yaso ba, Abbi ya lumfasa sannan yace,
"Murja... Shin har yanzu Baraka tana son Lamido?".
Mom tace, "Har gobe tana sonshi saidai...".
Abbi ya katseta saying,
"Wannan kawai nike son inji... Tun da har yanzu tana sonshi, ki turo min ita, na gama yanke shawara akan maganar auren nan...".
Lamido yace, "Abbi bana son in k'ara aure sannan mi kake tunanin iyayen Arfaat zasu ce akanmu... Beside I don't want to tie the knot with any girl again, matata Arfaat zata dawo gareni...".
Abbi yace, "Na riga na yanke shawara, baka isa ka mayar dani tsohon banza ba, ka saka a rink'a maganganu a kaina a gari ba...".
Lamido ya mike saying,
"I'm leaving now, business seminar da na fad'a maku, zai daukeni watanni biyu sannan in dawo...".
Abbi yace, "Ina nan ina jiranka hakanan itama maganar auren... Allah ya kiyaye hanya...".
Lamido yace, "Amin...".
Direct ya wuce bedroom dinsa, yayi dialing wata number saying,
"I'm leaving now...".
Cikin kankanin lokaci ya shirya cikin wata expensive suit, fara da brown, yayi wanka da designer perfumes, saida ya saukesu Sultan gida ya shiga gaida Ummy....
Ummy tace, "Daga discharging dinka daga asibiti sai ka dasa aiki kamar agogo...".
Lamido yace, "Dama shock ne kawai kuma na samu sauki... And tareda likita zamuje...".
Ummy tace, "Alright, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bada sa'a, Allah yasa albarka...".
Lamido yace, "Amin...".
Thirty minutes later private jet dinsa ya lula a sararin samaniya, ya zurawa window idanu yana tunanin matarshi Arfaat, fuskarsa tana dauke da damuwa, Shin mi ya saka suke mashi haka? Shin mi ya saka ba zasu fahimceshi ba? Shin mi ya saka ba zasu mashi uzuri ba? Shin mi yasa suke son sakawa yayi mata kishi bayan ya samu tabbacin har yanzu tana raye? Yana kaunar matarshi... Shin mi yasa ba zasu gane cewa matarshi tana a raye ba? Shin mi yasa ba zasu fahimci matuk'ar son da yake mata ba? Arfaat ce kawai wacce yake so a cikin zuciyarsa, ita kadai dinta....
Ya tsiyaya drinks ya kafa lips yana sirfing a hankali....
Business trip yayi daga wannan kasa zuwa wancen saida ya shafe watanni biyu bai waiwayo Nigeria ba, dama ya saba dadewa fiye da haka, a ranar da ya cika watanni biyu, a ranar ne nakud'a ta kama Aseeyerh, ta sha wahala sosai kafin ta santalo diyarta mace mai KAMANNI da ita sak wannan ya saka take KAMANNI da Lamido, cute baby, Masha Allah, babu zato babu tsammani suka ganshi kamar wanda aka jefo...
Lamido ya amshi baby yana kallonta yana murmurshi yayinda yake jin kaunarta har a cikin zuciyarsa, baby ta wangale baki tana mashi murmurshi...
Abeed yace, "Kayi mata huduba da sunan Arfaat...".


Lamido ya kalli inda Aseeyerh take, ta gyad'a mashi kai da murmurshi akan fuskarta, hawayen farin ciki ne suka soma zubowa daga idanunsa, ya goge yayi mata huduba da sunan Arfaat wato Lailaturrahman amma zasu rink'a kiranta da little Arfaat...
Abeed yace, "Daga yau har zuwa karshen lumfashinta zata rayu a matsayin diyarka, wacce kake da cikakken iko a kanta... Mu Aunty da Uncle dinta ne kawai, da zarar ta yayeta zamu damkata a hannunka...".
Lamido yayi murmurshi yana mai kallonsu cike da kauna, the more ya kalli little Arfaat the more yake jin farin ciki a cikin ransa...
Da marece aka sallamesu, tun daga ranar da aka haifi little Arfaat, har zuwa ranar suna dukkanin kudaden da aka kashe Lamido ne ya bada, kashe kudi yake kamar bai san zafinsu ba, yayi kyauta marar adadi, shi kanshi bai san adadin kudaden da ya kashe ba, kaya niki-niki ya aikowa baby da maman baby na siyayyar da yayi masu...
Tuni ya warewa little Arfaat bedroom a katon mansion da ya gina, wanda yake da girman gaske kamar wani estate, ya zuba kayan wasan yara masu tsadar gaske, bedroom ne mai girman gaske wanda yake dauke da abubuwan more rayuwa....
Ummy taje barka, ta koma suna tareda Hajiya k'arama da Aunty Hajjo, har hawaye tayi a ranar da ta soma tozali da takwarar gudan jininta...
Ranar suna daga restaurants dinsa aka girka abinci ana shigowa dashi, cikin takeaway, rubber tareda manya-manyan warmers, dukkanin wanda yazo sunan sai yaji babu waje, kaji ne ga su nan birjik, raguna aka yanka da shanu....
Come and see TEAM ARFAAT Rescue suna ta kaiwa da komowa domin tabbatar da dukkanin members na group da sukaje sun samu abinci, sau ukku ina amsa ina cin fuska akan ba'a bani ba 😂😂😂, ZAHRA GRAPHICS ita ce incharge of raba Kaji (idan kin san baki samu ba, ki nemeta ta baki 😂), HAJEER BEAUTY itace take raba abinci shinkafa da miya, fried rice, tuwo, sai abun da kake so, ku matsa mata ta baku har kuyi guzuri, maganar naman rago da sa wannan bangaren SOFIYYA ne, OUM MINAT drinks suna a wajenta, maganar kullinku snacks da sauransu wannan ku samu DOCTOR TEEMERH, ita kuma RAMSY RAHMAT itace zata maku sannu da zuwa ta baku kujerar zama, idan kinje baki samu kujerar zama ba, laifinta ne, ahtou 😂😂😂....
Two days after the naming ceremony, Aseeyerh ta koma gida wanka tareda baby, a kullum Arfaat tana a hannun Lamido har tafi sabawa dashi fiye da kowa, tana tozali dashi zata soma wangale baki tana murmurshi, tana hangoshi zata soma mik'a mashi hannu ya amsheta yana mata wasa, jinta yake har cikin ranshi, the more ya ganta the more yake jin damuwar dake a ranshi ta gushe....
Hoton little Arfaat ne sosai a social media dinsa da wayarsa, zai goyata with abun goyo ta gaba, yana yawo abunsa, taking pictures, ta zame masa wani bangare na rayuwarsa....
************
Arfaat ce takure a cikin kogon tana binsu da kallo cike da tsana, saida suka fashe da dariya sannan daya daga cikinsu yace,
"Yake shugabarmu, ki farka daga son wanda ba ya sonki... Lamido wanda kika kwallafa rai a kanshi yana can yayi wa wata mata ciki har ta haifa mashi diya mai KAMANNI dashi, idan kina ganin baki yarda ba zamu nuna maki zahiri...".
Yayi nuni zuwa wani kutse a take hoton Lamido ya bayyana yana dauke da little Arfaat yana mata wasa yana dariya, Arfaat ta kalleshi ta kalli babyn yayinda taga matuk'ar KAMMANI da suke kamar kobo da kobo...
Da sauri ta kawar da kanta, ji tayi yace,
"Don haka ki manta dashi, ki daina wahalar da kanki a kanshi, ki soma amfani damu kina shayar damu bl**d mu kuma zamu baki taskar arziki...".
Arfaat ta toshe kunnuwanta tareda fasa k'ara saying,
"No... No... K'arya ne... No... K'arya ne...".
The more ta rufe idanunta the more take hangoshi rike da babyn wadda suke matuk'ar KAMMANI, yayinda maganganunsu yake dawo mata a kwakwalwa, mikewa tayi yayinda jire yake debarta saidai gani sukayi ta zube a sume...
**************
Little Arfaat ta taso cike da wayo, tana da shekara daya amma idan ka ganta sai kayi tunanin ta shekara biyu ne, tana da shekara daya da wata daya ta yaye kanta da kanta, Aseeyerh ta kawowa Lamido, daga nan ne zamanta ya koma a wajenshi, rayuwa take cike da gata da kulawa babu abun da ta nema ta rasa, bedroom guda daya aka ware mata ya saka mata kayan more rayuwa amma koda yaushe tana tare dashi har office take binsa a wasu lokuttan, shi yake mata komai, ko maid bai yarda suyi mata ba, idan yana gida torh kuwa tana manne dashi tana kiranshi da Abbana.....
Zaune yake a parlor yana dauke da Arfaat yayinda yake aiki akan system yana duba wani project da zasuyi....
Baraka ta shigo da salaam akan bakinta ya dago tareda amsa mata sai kuma ya cigaba da abun da yake, ta zauna kusa dashi tana yi wa little Arfaat wasa, tace,
"Ina wuni... Yaa Lamido...".
Ba tareda ya d'ago ba yace,
"Lafiya lau...".
"Little k'wuwa takeyi min...".
"Da ni kawai take yarda sai tayi selection koda tana ganin mutum kullum...".
"Indai nice ina zaune zaki zo ne... Abbi yana nan kuwa?".
Lamido ya d'ago da sauri saying,
"Abbi kuma?".
Baraka ta gyad'a kai saying,
"Ehhh ya kirani ne...".
Lamido ya ware idanu yayinda gabanshi ya yanke ya fad'i, ashe har yanzu maganar auren nan tana nan, ya maida hankalinsa a kanta saying,
"Baraka ke er uwata ce bana son kiga kamar na cutar dake shiyasa nike kaucewa auren nan... Arfaat ce kawai wacce nike so a zuciyata, koda na aureki ba zan iya maki adalci ba... Ki rabu da aurena kije ki auri wanda yake kaunarki a inda zaki samu nutsuwa, hankalinki ya kwanta...".
Baraka tayi murmurshi saying,
"Kadda ka damu zan iya zama da kai a kowanne yanayi saboda ina matuk'ar sonka...".
Lamido ya dafe kai saying,
"Baraka ina son fahimtar dake gaskiya amma kina burus dani...".
Baraka ta mike saying,
"Zan je in gaida Ammi... Na barka da lafiya...".
Ta wuce sama ta barshi zaune kamar wanda aka dasa yana binta da kallo idanu a waje, he's totally speechless....

Wata tace tambayata a cikin books dina wanne yafi dadi ta siya
I was like 🫡🫡🫡
Saidai in fad'a maki wanda aka fi siya
Which is
Ban Dace Dashi Ba
Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion
The Choice I Made

Yeah
Ban Dace Dashi Ba, shine book dina da aka fi siya
Followed By
Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion
Then
The Choice I Made
Chasing My Heart, A Tsakanin So

Zaku samu complete na kowanne da zarar kun biya

This Three Books

Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion
The Choice I Made
Ban Dace Dashi Ba

Duk wacce bata karanta ba, an barta a baya

Guda daya 600
Guda biyu 1000
Guda ukku 1200

9169472057
Aisha
Opay Digital Service

WhatsApp 09169472057

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰

💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 7

*This Page Goes To Mub'Ash, Sarauniyerh, and Jidderh...*
*Nace Ba, Team Arfaat R, In Fada Maku Gaskiya, Ko In Barku Sai Kunje Kun Kwatota Tace Bata Gode Ba, Tunda Bakuyi Yaki Kun Hana Ayi Mata Kishiya Ba... Ku Fara Mata Yakin Gidan Tukunna... Kishiya Ba Dadi...* 🤣🤣🤣
*Hirar Arfaat Da Sharhi Da Kuke Yana Matuk'ar Sakani Nishadi, Ina Son Shiga Ina Gudun Mu Koma Gidan Jiya...* 🤣🤣🤣


Lamido ya d'age shoulder saying,
"Whatever tunda ba'a kaina za'a daura min ke ba, na fad'a maki gaskiya, komi ya biyo baya kece kika janyo wa kanki, na fita hakkinki...".
Little Arfaat tace, "Ab bana pupu...".
Ya wuce da ita toilet ya daurata akan fo ta gama ya wanke mata, ya cigaba da aikin da yake yayinda take wasa a kasan carpet....
Five Munutes Later, Abbi ya aiko kiran Lamido saida ya kai little Arfaat wajen Ammi sannan ya wuce sashen Abbi yayinda gabansa yake faduwa domin ya tabbata maganar Baraka ce...
Baraka tana zaune a kasan carpet, ya zauna ta daya bangaren saying,
"Barka da warhaka... Abbi...".
Abbi ya ajiye newspaper dake a hannunsa saying,
"Barkanmu... Baraka ke nasan bani da damuwa da ke... Lamido ka sani na kiraka ne domin in sanar da kai hukuncin da na yanke, wanda shine hukunci na karshe, wannan kuma umarni ne ba shawara ba don haka bana buk'atar jin ra'ayinka... Kayi tafiyar da kace zakayi kuma ka dawo, na zuba maka idanu ne saboda ban san in raba maka hankali akan Little Arfaat yanzu kuma tana hannunka ne don haka nan da wata guda za'a daura aurenka da Baraka... A wancen lokacin nayi maka komai yanzu kuma tunda kana da kudadenka, kaine zakayi wa kanka komai na hidimar bikin, nawa shine sanya albarka... Za'a daura auren nan da wata mai zuwa...".
***********
A daya bangaren, Ummy ta fito daga bathroom taci karo da Arfaat duplicate tsaye a gabanta tana motsi da lips amma bata jin abun da take cewa....
Ummy tayi pointing dinta muryarta na rawa saying,
"Arfaat dama duk tsayin wadannan shekarun kina tare damu...".
Arfaat duplicate ta soma girgiza mata kai saidai Ummy bata jin abun da take cewa, Ummy ta nufeta da sauri da nufin rungumeta saidai gani tayi tai going through her ba tareda tayi mata katanga ba, Ummy ta fashe da kuka ganin tana daukewa tana dawowa tace,
"Arfaat kaddai fatalwa suka mayar min dake...".
Arfaat duplicate ta cigaba da girgiza mata kai tana magana wacce bata fitowa ballantana wanda yake saurarenta yaji abun da take son sanar dashi, kuma Ummy batayi dubarar karanta motsin lips dinta ba saboda rikicewa da tayi, kamar kyaftawar idanu ta b'ace b'at....
Ummy ta fasa k'ara tareda zubewa a sume, Abba, Sultan da Nabila suka rufa a kanta, aka ciccibeta aka wuce da ita asibiti inda aka soma bata taimakon gaggawa, babu abun da take ambata sai....
"Arfaat... Arfaat... Na ganta tana tare damu, sun b'atar da ita ne bamu iya ganinta... Ni Zainab na boni, sun maida min y'a tamkar fatalwa...".
Saida sukayi mata allura suka samu tayi bacci...
************
Lamido ya ware idanu saying,
"Abbi... In one month kuma?".
Kafin wani ya k'ara samun zarafin magana, wayar Lamido ta soma ringing, yana dubawa yace,
"Sultan ne... K'anin Arfaat...".
Abbi yayi mashi alama da yayi picking, ya ware idanu saying,
"What... Which hospital?... Gani nan zuwa...".
Abbi yace, "Mi ya faru?".
Lamido ya mike tsaye hankalinsa a tashe saying,
"Ummy ce ta suma, yanzu haka tana a asibiti...".
Da sauri ya fita ya koma bangaren Ammi ya dauki Little Arfaat bayan da sanar da ita abun da ya faru da Ummy, ya bude bangaren mai zaman hakanan ya saka Little Arfaat sannan ya zagaya bangaren direba, direct ya wuce asibitin yayinda Ammi da Abbi suka mara mashi baya, zuwa ward da aka kwantar da ita....
Abba, Sultan, Nabila da Safnah ne tsaye a kanta tana bacci...
Lamido hankalinsa a tashe ya shiga saying,
"What happened to Ummy? Mi aka yi mata?".
Safnah ta amshi little Arfaat daga hannunsa saying,
"Babu wanda yasan takamaimai abun da ya faru, muna zaune parlor ne mukaji k'ararta muna zuwa muka sameta kwance a kasa, she keep saying something like taga Arfaat, fatalwa...".
Lamido yace, "What?".
Abba ya kamashi tareda zaunar dashi saying,
"Calm down Lamido... Insha Allah babu abun da zai sameta...".
Lamido ya zuba mata idanu da tunani barkatai a cikin zuciyarsa....
Babu jimawa Abbi da Ammi suka iso aka soma jajantawa juna wannan al'amari da ya faru....
Two Hours Later,
A hankali Ummy ta soma bude idanunta, ta bude baki dakyar saying,
"Arfaat... Arfaat...".
Nabila tace, "Ummy nice.... Ummy ta farka...".
Da sauri suka rufa a kanta, Ummy tace,
"Lamido... Ku kira min shi in sanar dashi yadda aka yi da matarshi...".
Lamido ya rike hannunta saying,
"Ummy gani a kusa dake... Ki kwantar da hankalinki Arfaat zata dawo garemu, zan kub'utar da ita daga garesu...".
Ummy ta girgiza kai saying,
"Lamido b'atar da ita sukayi ba'a ganinta amma tana tare damu...".
Dukkanin wanda yake a wajen saida ya girgiza da jin wannan al'amari duk da kuwa ya tab'a kasance a shekarun baya da suka shude, kimanin shekaru hudu kenan...
Ummy tace, "Yau na fito daga bathroom naga Arfaat da idanuna, tana motsi da baki amma ban jin abun da take cewa...".
Ta kwashe dukkanin abun da ya faru tun daga fitowarta bathroom har zuwa sumanta ta sanar

Please Login or Register in order to submit comment