Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da mamaki, baki daya ya sauya mata, wannan ba shine Lamido da ta sani ba, ya sauya baki daya....
Koda suka dira a Shanghai a hotel suka sauka, tunda suka ci abinci suka rama sallolin dake a saman kansu, ya shirya ya fita bata k'ara ganinsa har tayi bacci, both dinner da lunch, room service suke kawo mata ta bude kofa ta amsa ta koma ciki, har gida ta kira sannan kuma Sultan ya kira sun jima akan waya baki dayansu saida suka zubar da hawaye....
Washegari, Helcofter ya daukesu zuwa airport daga nan suka bi private jet dinsa zuwa Italy, Lamido's busy yana duba system yana amsa waya, Arfaat ta zuba mashi idanu idan ya d'ago saidai yayi mata murmurshi kawai....
A hotel suka sauka dogon gini iya ganinka, awanni biyu yayi ya shirya ya fita bata k'ara ganinsa ba har tayi bacci kamar ba'a nan ya kwana ba, da safe dai ta farka ta ganshi, bai jima ba ya k'ara fita, ta mike tayi walking tareda yaye curtain tana kallon kasan ginin tareda gine-gine da suke a birnin, a kwana na ukku ya fita tareda ita suka shiga gari ya nuna mata wajaje saida dare sannan suka koma hotel da suka sauka...
Washegari tun kafin ta tashi ya fita saidai farkawa tayi bata ganshi, tarar da breakfast dinta akan table, tayi wanka tareda sauya kaya sannan taci, ta tsaya a gaban window tana kallon gine-gine dake a birnin, wayarta ce ta soma ringing ta janyo video call ne ta zauna akan cushion, Safnah ce, a tare suka fashe da kuka, Safnah tace,
"Alhamdullilah... Arfaat you are safe... Allah ya kub'utar dake...".
Arfaat tace, "Safnah kece kika koma haka kinga yadda kika k'ara kyau...".
Safnah tace, "Ai ban kaiki ba... Wannan shine yarona yaqub, meet my husband Salim...".
"Hi Salim...".
"Hi Arfaat...".
Ta haskashi bayan sun gaisa ta wuce bedroom, sun jima suna hira tareda jajantawa juna abun da ya faru sannan tayi hanging call din....
Bayan sallar Isha'i ya shigo yayi hugging dinta saying,
"Sorry sweetie na barki ke daya...".
Arfaat tace, "D'azu Safnah ta kira har na gaisa da mijinta har d'a gareta...".
Lamido yayi murmurshi saying,
"Safnah... Your other half... Har kin tuna min Aseeyerh ta kira tana son magana dake...".
Sai kuma ya had'asu video call ya shige bathroom, ya barta akan video call da Aseeyerh, har ya fito suna akai ayi dariya ayi kuka a tuna baya, ciki ne da ita, saida ya gama shiryawa sannan yayi hanging call din saying,
"Hirar ta isa haka tunda kuka kike saka matata...".
Arfaat ta mike ta wuce bathroom tayi wanka tareda saka doguwar riga ta bacci, tana fitowa ta tarar an kawo masu dinner, suka ci, ta koma bathroom tayi brush tareda alwalla sannan ta fito ta haye saman gado taja blanket tareda lumshe idanu....
Lamido ya kwanta akan sofa....
Washegari sukabi private jet dinsa to india, suna sauka ya shirya ya fita bata k'ara ganinsa ba saida dare, the following day ya fita da ita ya zaga da ita taga wajaje saida dare sannan suka koma hotel da suka sauka....
The following day ya shirya ya fita saida rana sannan ya dawo, tana cikin bathroom ta fito ta ganshi, murmurshi yayi mata tareda nuna mata gado saying,
"Guess what? Bude ki gani...".
Arfaat tayi taking steps ta bude sari ne expensive kalar brown mai kyau, ta bude daya jewelry ne, ta bude daya takalma ne, ta kirkiro murmurshi saying,
"Wow... Thank you...".
Lamido ya ware hannuwa saying,
"Zo kiji...".
Arfaat tayi jim sai tayi tako tareda shigewa jikinsa yayi hugging dinta....

Lamido yace, "Gobe zamu wuce Nigeria, surprise zamuyi masu, babu wanda ya sani saidai su gammu...".
Arfaat ta gyad'a kai kawai...
Washegari Helcofter ya daukesu zuwa airport daga nan suka bi private jet dinsa to Nigeria, suna sauka Lamido ya janyo wayarsa yayi dialing number saying,
"Abeed... Muna a airport... Ka taho tareda little Arfaat... Surprise mana...".
Mintina goma a tsakani, Lamido ya janyo wayarsa ya duba sai kuma ya mike saying,
"Muje...".
Arfaat tabi bayanshi suka sauka daga saman jirgin, security ne ta ko'ina, Abeed yana jingine da mota yana dauke da little Arfaat, Lamido yayi murmurshi tareda amsarta, Little Arfaat ta wangale baki saying,
"Ab bana...".
Lamido ya lakuci hancinta saying,
"I miss you Angel...".
Little Arfaat ta zubawa Arfaat idanu sai kuma tace,
"Ummina... Laa Ummina... Ka kawo min ita...".
Lamido yace, "Ehhh na kawo maki ita...".
Arfaat ta dubeta kawai, ji yarinya a ina ta santa da har take kiranta ummi, kuji yarinya da kwanare da iyayi....
Lamido ya mik'a mata ita, ta amsheta tana murmurshin dole, suka shiga wata doguwar mota suka hau hanya, Lamido yace,
"Zamu wuce can gida wajen su Ammi daga nan sai in kaiki gidan Ummy...".
Arfaat ta gyad'a kai, yace,
"Koda yake bari mu wuce gidana...".
Arfaat ta dubeshi da sauri tareda ware idanu, yayi dariya sannan yace,
"I'm joking...".
Little Arfaat ta tusa Arfaat a gaba tana mata surutu tana yi tana kiranta Ummi, ita dai Arfaat ta zubawa sarautar Allah idanu, ita ba da shiga labour room din an kakab'a mata diya, diyar ma wacce aka haifa out of wed lock (that's base on karyar da aljannun sukayi mata)....
Direct gidan Ammi suka wuce, aka bude mashi kofa ya fito sannan ya zagaya daya bangaren ya bude ta fito, ya zura hannu ya fiddo little Arfaat ya dauketa a hannu suka jera suka shiga, looking, perfect family....
Lamido yace, "Ammi... Surprise...".
Ammi tace, "Tun da mutum yace surprise zaiyi sai yaci sauran abincin gida domin kuwa ni ta d'iyata nike...".
Lamido ya b'ata fuska saying,
"No... Aahhh...".
Ammi ta girgiza kai saying,
"Like father like daughter...".
Ammi tayi hugging Arfaat saying,
"Daughter... Welcome back home... Sannu kinji... Allah ya k'ara tsarewa... Allah ya kiyaye gaba...".
Arfaat tace, "Amin... Ammi Ina wuni?".
Ammi tace, "Lafiya lau... Kina tafiya?".
Arfaat tace, "Lafiya lau...".
Maimoon dake saukowa daga stairs ta rugo da gudu tayi hugging dinta saying,
"Welcome... Sis Arfaat...".
Arfaat tace, "Maimuna...".
Maimoon tace, "Maimoon dai...".
Lamido ya ware idanu saying,
"Laa na manta ashe daa Maimuna kike...".
Maimoon ta b'ata fuska, a tare sukayi dariya, Ammi tace,
"Dama yanzu zamuyi lunch... Muje...".
A tare suka wuce dinning room, Lamido yaja mata kujera ta zauna, ya zaunar da Little Arfaat a tsakiyarsu, Maimoon tayi serving kowa, Little Arfaat tace,
"Ummi... Feed me...".
Ammi tace, "Eyerh wato kinga Umminki kin manta dani... Zamu gauraya ne...".
Maimoon tace, "Tace ta daina yayina ta koma maki, taga Umminta ta kyale Ammi, yau ranar cin dariya...".
Arfaat cike da mamaki take kallonsu, Lamido yace,
"Little Arfaat kinga Ummi ta gaji ki bari ni sai inyi feeding dinki... Uhmm Angel...".
Little Arfaat tayi rau-rau da idanu saying,
"Ohhh... Ohhh... Ummi nike so...".
Arfaat tayi jim sannan tace,
"Alright...".
Ta dauki spoon ta ciko ta kai mata baki, ta amsa, ta k'ara wani spoon ta k'ara kai mata baki, Little Arfaat ta gumtse baki, Arfaat ta dubeta da mamaki...
Lamido yace, "Kina bata kina ci otherwise ba zata ci ba...".
Arfaat ta dubeta ta kalli spoon din, no way zatayi wannan kazantar, tana dagowa zuka had'a idanu and she have no choice, tana bata tana ci har suka koshi, Lamido ya dauketa suka wuce parlor, Maimoon tace,
"Bara in kira in fesawa Nabila...".
Ta wuce upstairs da gudu ta dauko waya....
Ammi tace, "Lamido kaje da ita sashen Alhaji ta gaidashi sai ka wuce da ita...".
Lamido ya gyad'a kai saying,
"Arfaat... Muje...".
Ammi tace, "Allah ya kiyaye kinji... Allah ya k'ara tsarewa... Zan shigo har gidan, ki gaida Hajiya Zainab...".
Arfaat tace, "Zataji... Na gode...".
Lamido dake dauke da little Arfaat yana gaba, Arfaat tana biye dashi har sashen Abbi, yana zaune a parlor yana kallon News, yayi masu nuni akan kujera suka zauna, Arfaat tayi kasa da kanta saying,
"Ina kwana Abbi... Barka da warhaka...".
"Lafiya lau... Kun zo lafiya...".
"Lafiya lau...".
"Sannu kinji... Allah ya kiyaye gaba... Allah ya k'ara tsarewa...".
Arfaat tace, "Amin... Na gode...".
Abbi yace, "Little zo...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a saying,
"Ohhh... Ohhh... Ummi zan bi...".
Abbi yayi dariya saying,
"Zaki dawo ma... Lamido kuje ka sauketa gida, daga nan ka wuce gidanka...".
Lamido yace, "In shaa Allah... Arfaat muje...".
Arfaat tace, "Abbi... Na gode...".


Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰
[29/03, 22:26] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 23

Lamido yana gaba tana biye dashi suka fita suka shiga mota, direba ya jasu, da mamaki take kallon yadda garin ya koma har ta kasa hakuri ta juya saying,
"Yaa Lamido... Ina ne nan?".
"Sabuwar unguwa...".
Ta dubeshi da mamaki saying,
"Sabuwar unguwa kuma... Ina roundabout mai kworya da lidde da kuma kofar kaura...".
Lamido yace, "Flyover...".
Little Arfaat tace, "Flyover...".
Lamido yace, "Yeah... Flyover... Angel zaki bini gida ne ko kuma in barki wajen Ummi...".
Little Arfaat ta wangale baki saying,
"Ummi...".
Lamido tace, "Okay then sai in barki wajen Ummi...".
Da sauri Arfaat ta dubeshi jin abun da yace saidai bata ce komai ba, har compound motar ta shiga dasu...
Lamido yace, "Akwai kayanta a nan, ki gaida min da Ummy, zan shigo zuwa gobe, ban san ganin hawayenta ne kuma na tabbata idan ta ganki sai tayi... Za'a shigo maki da kayanki...".
Arfaat ta gyad'a kai ta fito Little Arfaat ta rik'e mata hannu gam, Lamido yayi masu waving hand da murmurshi akan fuskarsa, ta juya suka shige ciki, da mamaki take kallon gidan ganin ya sauya baki daya kamar bashi ba, an k'ara mashi girma, an sauya ginin, da salaam akan bakinta suka shiga parlor....
Arfaat da mamaki take kallon manya-manyan akwatuna da ake shigowa dasu parlour, kamar wacce zata bude boutique....
Nabila dake zaune a parlor tana kallo, ta fasa ihu tareda rugowa da gudu tayi hugging dinta, a tare suka fashe da kuka...
Ummy ce ta fito daga kitchen, ta juya tareda goge hawayen da suka zubo mata tace,
"Ina Lamido?".
Arfaat tace, "Yace sai zuwa gobe zai shigo ba ya san ganin hawayenki...".
Da gudu tayi hugging dinta tana kuka, Ummy itama kukan take, abun gwanin ban tausayi....
Little Arfaat ta fashe da kuka, suka juya da mamaki suna kallonta, Nabila tace,
"Angel mi kikeyi wa kuka? Mi aka yi maki?".
Little Arfaat tace, "Aunty Nabi... Granny ce take saka Ummina kuka...".
Nabila da Ummy suka saka dariya yayinda Arfaat take jinjina sunan granny, abun babba ne, yarinyar da ya haifa out of wedlock (according to her base on karyar da Aljannun sukayi mata), yace mata akwai kayanta a gidan nan kuma gashi tana kiran Ummy da granny and she's calling Nabila with Aunty Nabi, da alama ta sansu sosai....
Ummy tace, "Torh shikenan ki daina kukan na daina sakata kuka...".
Arfaat ta zauna akan kujera, little Arfaat ta bita kamar bindi ta zauna kusa da ita ta manne mata tana wasa, Arfaat tace,
"Nabila... Ina Sultan?".
Nabila tace, "Yana London karatu, bai san da zuwanki ba, da ya tafo...".
Ummy tace, "Arfaat kuzo kuci abinci...".
Little Arfaat tace, "Mun koshi mun ci abinci gidan Ammi... Ko Ummina?".
Arfaat ta kawar da kai sai kuma ta kirkiro murmurshi saying,
"Mun ci abinci gidan Ammi...".
Ummy tace, "Kuje sama ku huta... Nabila ki rakata bedroom dinta...".
Arfaat tace, "Bara na zauna a nan, nayi kewar gidan, rayuwa kenan...".
Little Arfaat tace, "Ammi... Pupu...".
Arfaat tace, "What?".
Nabila tace, "Angel muje in rakaki kiyi...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a tareda turo baki saying,
"Ohh... Ohh... Ummina nike so...".
Ummy tace, "Nabila kuje ki nuna mata bedroom dinta, tunda yanzu ba zata gane kan gidan ba... Arfaat kuje tunda tace ke take so...".
Arfaat tayi jim sai kuma ta mike suka wuce upstairs, Little Arfaat ta saki hannunta ta ruga da gudu ta bude wani kofa, Nabila tace,
"Bedroom dinta ne...".
Arfaat tace, "Har daki gareta a gidan nan...".
Nabila tace, "Ehhh...".
Suka shiga, already tana cikin toilet, Nabila ta zauna a gefen gado, Arfaat tace,
"Tun da ta shiga bara in koma parlor wajen Ummy...".
Nabila tace, "Okay...".
Arfaat ta juya ta fita ta koma parlor, bata dade da zama ba, Nabila ta sauko saying,
"Taqi yarda tace ke take son ki wanke mata...".
Arfaat ta ware idanu saying,
"What? Not again, na gudu still ban tsira ba...".
Ummy tace, "Ki tashi kije ki wanke mata...".
Saida tayi jim sannan ta mike ta wuce sama, tana gama wanke mata ta juya zata fita, Little Arfaat ta janyo hannunta ta kunna fanfo ta tara ruwa tana watsa mata saying,
"Kiyi min wanka... Wanka...".
Arfaat ta daka mata tsawa saying,
"Ke... Dubi yadda kika jik'a min kaya... Ina wasa dake ne, sai kwada maki mari...".
Little Arfaat ta tale baki tareda fashewa da kuka saying,
"Abbana... Abbana...".
Arfaat tayi banza da ita, kukan little Arfaat ya janyo hankalin Ummy, ta shigo saying,
"Mi ya faru?".
Arfaat tace, "Na wanke mata shine take watsa min ruwa wai inyi mata wanka, duk ta jike min kaya da ruwa...".
Ummy tace, "Daga tace kiyi mata wanka shine zaki sakata kuka, diyarki ce, idan bata ce kiyi mata ba, wa zata ce yayi mata, ban san sakarci... Kadda in k'ara jin kukanta...".
Ta juya ta fita...
Arfaat kamar zatayi kuka tace,
"Ke kiyi min shiru zanyi maki wankan...".
Little Arfaat tayi shiru, Arfaat tana mata wanka tana watsa mata kumfa duk ta b'ata mata jiki, ta kule, ba abun tayi mata ihu ba ta saka kuka ta tara mata jama'a, ta gama tana mata shafa mata cream tana wasa har ta gama ta taje mata kai, Little Arfaat ta bude closet tana mata pointing wasu kaya saying,
"Wadannan...".
Da mamaki take bin closet din da kallo ganin tulun kayan dake a ciki, gaskiya abun ya wuce tunaninta, ta dauko kayan data nuna mata ta saka mata...
Little Arfaat tace, "Perfume...".
Arfaat ta dauko daya daga cikin turaren har ta bude, Little Arfaat ta koma baya saying,
"Ba shi ba, wancen...".
Arfaat ji tayi kamar ta daka mata tsawa sai kuma ta fasa, ta rufeshi ta ajiye ta dauko wancen ta fesa mata, ta nufo waje, Little Arfaat ta kama mata hannu suka sauko kasa....
Arfaat kamar zatayi kuka tana kallon kanta daga sama har kasa tace,
"Ummy ki duba yadda tayi min...".
Ummy tace, "Diyarki ce dole zaki hakura da ita a haka... Kece dolenta... Nabila ki rakata bedroom dinta...".
Nabila ta mike tayi gaba suka bi bayanta, Nabila tace,
"Haka takeyi wa kowa, idan tace kiyi mata wanka kema ki shirya yi domin sai ta watseki da kumfa...".
Arfaat dai bata ce komai, Nabila ta bude wata kofa suka shiga, Arfaat tayi still tana bin bedroom din da kallo, duk da an sauya mashi fasali amma kamar wancen yake, har furnitures irin wadancen ne saidai wadannan zasu fi wadancen tsada...
Ta shiga bathroom, Little Arfaat tana manne da ita, ta bude kofa ta juyo har zata mata tsawa ta tuna Nabila tana nan, tace,
"Ki jirani wanka zanyi...".
Little Arfaat ta juya ta haye saman gado tana wasa da teddy bear dake a hannunta, Arfaat ta shiga bathroom ta jima sannan ta fito tana daure da towel yayinda jikinta yake dropping ruwa, ta zauna akan mirror tana shafa cream, Little Arfaat tana mata surutu saidai mata uhm ko kuma tayi mata banza, ta bude daya daga cikin akwatunan da aka shigo mata dasu, wasu daga cikin kayan da ya siya mata ne a kasar da suka baro, ta zaro gown ta saka, bacci ta soma ji, Little Arfaat tace,
"Cartoon...".
Arfaat ta sauke ajiyar zuciya saying,
"Kije parlor kice Nabila ta kunna maki...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a tareda nuna mata television dake a bedroom din, Arfaat ta kunna mata sannan ta haye gado, bacci ne yayi awon gaba da ita...
Cikin bacci taji ana tashinta, Little Arfaat ce take tsalle akan gadon saying,
"Ummina... Indomie...".
Arfaat ta bude idanunta saying,
"Kije kice Nabila ta dafa maki...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a tareda tale baki zatayi kuka, Arfaat tace,
"Kinga kadda ki ja min, Ummy tace dukanki nayi, muje in girka maki...".
Arfaat tana gaba, Little Arfaat tana biye da ita suka sauko kasa, Arfaat kamar zatayi kuka tace,
"Har na fara bacci ta tadani in dafa mata Indomie...".
Ummy tace, "Kuje ki dafa mata...".
Arfaat kamar zatayi kuka tace,
"Ummy bacci nike ji kuma ni ba komai zan iya tunawa ba...".
Ummy ta ware idanu saying,
"Miye haka ke shagwab'a diyarki shagwab'a... Nabila kuje ki nuna mata sai ta girka mata...".
Nabila ta mike suka wuce kitchen, Ummy ta cigaba da amsa wayoyin en uwa da abokan arziki dake kiranta suna tayata murnar kub'utar Arfaat tareda dawowarta gida...
Arfaat ta dauki Indomie guda daya ta saka zata rufe tukunya...
Nabila tace, "Hold on... What? Ki saka biyu don cewa zatayi saidai kina bata kina ci idan kuma ya k'are bata koshi ba, kuka zata saka maki sai kin k'ara dafa mata...".
Arfaat tace, "What? But...".
Nabila tace, "Haka zaki hakura...".
Arfaat ta saka har guda ukku, Nabila tace,
"Kamar yayi yawa...".
Arfaat tace, "Sai in saka maki sauran...".
Cikin k'ank'anin lokaci ta gama suka fito ta wuce da ita dinning tana feeding dinta tana ci har ta ture fork din, ta mik'a mata ruwa, Little Arfaat ta nuna mata gefen bakinta, Arfaat ta yago tissue ta goge mata, ta bata ruwan tana gama sha ta wuce parlor ta zauna tana wasa da teddy bear...
Arfaat ta soma tattara kayan da suka b'ata, Nabila tace,
"Ki barshi kije ki kwanta zan wanke...".
Arfaat tace, "Okay, thank you...".
Ta wuce upstairs to her bedroom ta kwanta bacci ne yayi awon gaba da ita....
*************
Lamido ya b'alle murfin motar ya fito har ya nufi sashensa sai kuma ya juya ya wuce sashen Baraka, ya saka code bai bude ba, da mamaki akan fuskarsa ya danna bell, wata yarinya ce sanye da kayan maid ta bude mashi kofar, ta matsa tana gaidashi, ya d'aga mata hannu kawai yana kallonta cike da mamaki, ya shiga ciki ko'ina tsaf-tsaf yake, kamshin turaren wuta yana tashi, ya haye upstairs to the parlour, tana zaune akan sofa tana waya tana kyalkyala dariya, tana ganinsa ta ajiye wayar da sauri, yayinda lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya, ya zauna saying,
"Wacece na gani a parlor?".
Baraka tace, "Itace er aikin da na dauko...".
Lamido yace, "Da kikayi shawara da wa?".
Baraka tace, "Da nayi shawara da kaina tunda ni daya ce a gidan tsayin shekara guda daya...".
Lamido kamar zaiyi magana sai kuma ya d'aga shoulder ya mik'e zai fita, tace,
"Ji mana ay tafiya bata ganka... Ina da magana da kai...".
Ya dawo ya zauna akan kujera saying,
"Ina jinki...".
Baraka tace, "Kadda ka damu, zan dawo kanka ne, bara na fara mai wuyar...".
Ta kware murya saying,
"Jumala...".
Maid ta iso da sauri saying,
"Gani ranki ya dade...".
Baraka tace, "Kayana da na had'a a boxes ki dauko ki kai min mota, kema ki dauko kayanki ki kai...".
Da mamaki yake kallon maid dake fita da boxes niki-niki, yace,
"Miye haka Baraka?".
Baraka tace, "Abun da ya dace, ka aureni ne against your will, sai yanzu na gane abun da kake son ganar dani a wancen lokacin shine na dauki hanyar gyarawa... Lamido, zuciyarka ba zata tab'a sona ba don haka na hakura, ka sakeni...".
Lamido ya ware idanu saying,
"In sakeki, kina hauka ne, kina so ne ki b'ata mamu zumunci...".
Baraka tace, "Dole ne zaka sakeni ko ta tsiya ko ta arziki... Idan ka sakeni ta arziki babu abun da zai tab'a mana zumunci domin zan koma gidanku a can zan zauna which means na toshe bakin en gulma... Idan kuma kace ba zaka sakeni ba, zan makaka kotu ne, which means saidai inje gidanmu, dole kuwa zumunci ya b'aci... Nayi kuskure a rayuwata yanzu na dauki hanyar gyarawa don haka zanyi yaki da dukkanin wanda yace zai hanani... The ball is on your ball, a cigaba da zumunci ko kuma a tarwatse, zumuncin shekara da shekaru ya lalace...".
Ganin ba ya da niyyar magana, ta nufi kofa saying,
"Be my guest, mu hadu a kotu, tunda baka ji kunyar kin sakeni ba duk da baka sona, nima kuwa ba zanji kunyar makaka a kotu ba, in nemi saki...".
Kamar zaiyi kuka yace,
"Baraka na sakeki saki daya...".
Ta fiddo paper ta ajiye mashi saying,
"Rubuta a rubuce...".
Duk da har yanzu ba ya jin sonta a zuciyarshi amma ba ya son rabuwa da ita, ya rubuta ta dauka saying,
"Ina mai baka shawara duk juyin da zasuyi kadda ka sake ka mayar dani, domin wallahi bazan k'ara zama da kai ba, na rantse koda ka mayar dani sai na kashe auren ko ta tsiya ko ta arziki... Dani da kai munsan cewa baka sona don haka ka barni in gyara rayuwata inyi farin ciki, ina mai baka hakuri akan b'ata maka dani a tsayin wadannan shekarun, ka yafe min, nima na yafe, Allah ya had'a kowa da rabonsa...".
Ta juya ta fice, ta shige motarta ta jata heading to gidansu Lamido inda a nan ne ta shirya cigaba da rayuwa....

Hafsat Hisham (Aysher Angel) 🥰😘🥰


[01/04, 21:26] Angel: 💨 *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* 💨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 24

A fusace Mom tayi parking motarta ta shiga ciki, tun daga compound take masifa har ta shiga parlor....
Ammi, Abbi, Baraka da Lamido ne kawai a parlor....
"Aikin banza, aikin wofi, har ni za'a wulakanta a idon duniya, saboda matarshi ta dawo shine zai sakar min da diyar, ya mayar min da ita k'aramar zawara...".
Lamido yace, "Mom, kiyi hakuri kiji abun da ya faru... Baraka ki fad'a mata...".
Mom ta ware idanu saying,
"Wacece da zaka kirani da Mom? Kirani da Murjanatu, that's my name, ay dama zumunci ne ya saka kake kirana mom, tun daga lokacin da ka saki Baraka ya tarwatse... Baraka tashi muje, ina a raye ba zaki zauna a gidan da basu san girman zumunci ba... Babu ni babu ku...".
Baraka ta ware idanu saying,
"Mom, muje ina kuma? A gida nike, gidan kawu ne fa...".
Mom tayi dakuwa tareda sakin ashariya sannan tace,
"Ay tun kafin in haifeki nasan gidanshi ne, dallahi tashi muje mara zuciya, duk gidan uwana dake a garin nan ki rasa inda zaki zauna sai a nan gidan...".
Baraka tace, "Amma Mom gidan Dan uwanki ne, uwa daya, uba daya...".
"Na raba zumuncin, babu ni babu ahalinsa...".
"Mom, kin raba zumuci dai, Alright amma Mom gaskiya idan zaki raba zumunci da dan uwanki uwa daya uba daya, ni bazan iya raba zumunci da Uncle dina ba...".
"Eyerh shine ina magana kina maidawa, tashi mu wuce, zumunci ne ni na had'a kuma na raba, ay ta dalilina kika had'a jini dashi, torh na raba...".
"Mom wannan zumunci bai rabu ba, a nan zan zauna, zan rink'a kawo maki ziyara...".
Ta tashi ta wuce sama, Mom ta rike hab'a saying,
"Ikon Allah, what have you done to her...".
Abbi yace, "Nothing, kin gama ne yayi maki bayanin abun da ya faru...".
Mom ta mike tana tab'e baki saying,
"Da shi wannan munafukin da ya had'a da kai daka goya mashi baya ay babu wanda bai san hanyar gidana ba...".
Ta fice fuu, Abbi yace,
"Sai mun zo...".
Tace, "Whatever, kuma ku tabbata kun tafo min da d'iyata...".
"Baraka kam tana gidan kawunta zama daram....".
******
Lamido yayi parking a compound, ya aika maid ta sanar da zuwanshi, suna zaune a parlor take sanar da zuwanshi, Umma ta tab'e baki ta mike ta wuce ciki....
Arfaat tace, "Kije ki manta dashi...".
Jin shiru ya d'aga kafa heading inside, kamshinsa tareda takonsa ne ya sanar da ita shigowarshi....
Ya zauna a kusa da ita saying,
"Ranka ya dade, miye na fushi kuma? Ay kin bari inyi maki bayani abun da ya faru, beside kefa kamata yayi kiyi murna yanzu baki da kishiya...".
Arfaat tace, "Yeah... It deserve happy, happy after happy... Ka wanko min iv in rabawa en uwa da abokan arziki mijina ya saki kishiyata saboda dawowata...".
Lamido ya rumtse idanu saying,
"We are not doing this... Ummy fushi take dani... Ina little Arfaat?".
Arfaat ta mike a fusace saying,
"Na siyar an bani, idan baka yarda dani ba miye na barinta a wajena, sai ka dauki abunka ka wuce...".
Lamido yace, "Calm down, Baraka da kanta ta nemi in saketa ko kuma ta makani kotu wanda zai iya raba zumuncin dake a tsakanin iyayenmu, shiyasa na saketa...".
Arfaat ta ware idanu saying,
"It's that easy amma na zauna ina wahalar da kaina da igiyar aurenka... Abdurrahman kodai ka sakeni ko kuma inje har gidanku inyi wulakanci da kansu zasu saka ka kasheni kuma su raba zumunci dake tsakani...".
Lamido ya mike da sauri saying,
"What are saying? Are you out of your mind?".
"Hell yes, I'm fucking out of my mind, try me and see, za kaga zahiri ne a tsakar gidanku...".
Ta wuce fuu, saidai k'arar fitar motarta yaji, da gudu ya fita yaja motarsa yana mai kiran numbarta, tayi picking saying,
"Miye?".
"Please ki tsaya da motarnan muyi magana...".
"Ay idan kaga na tsayar motar nan ka sakeni ne, yean, sakeni sai in juya da motata in koma gidan ubana...".
"Please don't do this to me...".
"You force me to...".
Duk yadda yaso ya shiga gabanta ya kasa, saida gabansa ya yanke ya fad'i a lokacin da motarta ta shiga gidansu...
"Ki tsaya muyi magana...".
"Try me, kazo ka tari gabana ka gani, zan fara ne da

Please Login or Register in order to submit comment