Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wankeka da mari kafin in k'arasa ciki...".
"Please...".
"Then ka sakeni...".
"No, I can't...".
"Then, you left me with no choice than inyi rashin mutunci...".
A guje ya nufi inda motar bazai tab'a bari ta shiga gidan nan ba, yana bude motar ya ci karo da direbanta a ciki, yace,
"What?".
Direba yace, "Hajiya ce ta aikoni in kawowa Ammi...".
Ya nuna mashi foodflask dake a backseat....
Lamido ya maida wayar a kunnansa saying,
"Arfaat...".
Arfaat tace, "Tayi maka barazana ka saketa tun a gida, amma ni har anzo gidanku amma kaki sakina, kadda ka rainawa kanka hankali, dama can kana son sakinta ne, aikin banza aikin wofi, ko kaine autan maza ne kai na hakura da zama da kai...".
Tayi hanging kiran....
Lamido ya rasa yadda zaiyi da kansa....
*****
Arfaat tayi wurgi da wayar tareda fasa ihu, the more ta kalleshi the more take hangoshi kwance akan wata yana making love yana kiran sunanta, komai fitar mata a kai yake, kishi ya tafo mata, ji take kamar tayi hauka, duk sakin baraka da yayi ba ya gabanta, tana son tayi amfani dashi ne ta rabu da wannan damuwar....
Little Arfaat ta shigo tana turo baki saying,
"Ummi... Kunu?".
Arfaat ta zare mata idanu saying,
"Dan ubanki, uban waye zai dama maki kunu, nace na maki nayi kama da er gidan kunu ne, ko ki fice daga bedroom ko kuma inyi maki dukan tsiya a gidan nan, shashasha, kuma ki bari Ummy ta shigo tayi min fad'a, dare yayi in rufe daki inyi maki dukan tsiya sannan in koraki inda kika fito...".
Little Arfaat ta fita da gudu tana kuka, akan hanya Nabila ta ganta tana kuka, tana mata magana bata tsaya ba, ta wuce dakin Arfaat inda taga ta fito...
"Angel, mi kikayi wa little ta fita tana kuka?".
A fusace Arfaat tace,
"Miye kuke son inyi daku, ban shiga Labour room ba amma kun kakaba min diya, wacece waccen yarinyar? Who the hell is she?".
Nabila tace, "What are saying? Little Arfaat, diyar Aseeyerh ce, bayan b'acewarki Lamido yana cikin damuwa shiyasa suka bashi ita tun da aka yayeta take a hannunshi...".
"Amma mi yasa suke kamanni?".
"Are you kidding me, Aseeyerh da Lamido suna kamanni, shiyasa little take kamanni dashi... Mi kikayi mata?".
Arfaat tace, "Ta shigo tana min rigima ne, daga na mata ihu shine ta fita tana kuka...".
Nabila tace, "Da kin bita a hankali, bara inje in dubata...".
Maryam ce ta bayyana a gareta...
"Maryam...".
Maryam tace, "Arfaat kinyi babban kuskure da har kika yarda da maganar wadannan azzaluman wadanda a wannan lokacin suna neman hanya ne ta yadda zaki manta da komai, kiyi abun da suke so... For now an cire maki tantama akan maganar Arfaat, saura abun da suka saka kika gani... Arfaat ina so ki saka kanki a matsayin Baraka ace kece yake tare dake yana kiranta, meyy zakiji...".
Arfaat tayi jim tana tunani sai kuma ta janyo wayarta da sauri tayi dialing numbar Safnah, ringing daya, biyu, ukku, tayi picking, bayan ta amsa salaam da tayi mata...
Arfaat tace, "Safnah ina sone in tambayeki wani abu... Mutum yana da mata guda biyu amma a duk lokacin da yake tarayya da dayar sai ya rink'a ambaton sunan gudar, what does that means...".
Safnah tace, "Wannan yana nufin yafi son wacce yake ambaton sunanta, idan nice dayar bazan lamunta ba...".
Arfaat tace, "Okay... And Safnah ranar da kika zo tareda k'awayenmu naga suna tayi min godiya, and I don't know why...".
Safnah tace, "Wannan aikin Yaa Lamido ne, tun bayan b'acewarki yake k'ok'arin taimakawa duk wanda yake da muhimmanci a gareki, dukkaninsu babu wacce bata ci arzikin saninki da tayi ba, Itama Mardiyya kamfanin babanta ne yake neman durkushewa har ya sakashi kasuwa amma Yaa Lamido ya taimaka mashi da kudi wadanda yayi amfani dasu ya cigaba da gudanar dashi... Ita kuma deejerh karayar arziki ta samu mahaifinta Yaa Lamido ya taimaka shi da kudade... All of them except few, there's story behind godiyar da sukayi maki... Arfaat kin more miji... Yaa Lamido mijine na gari, abokin rayuwa na gari sannan kuma masoyi na gaske...".
Arfaat tayi jim sannan tace,
"Okay, zamuyi magana... Na gode, sai munyi waya, ki gaida min Yaqub...".
Maryam tace, "Yanzu ta share maki tantama akan wancen har da wani bangare na abun da nike son sanar dake a yanzu... Yanzu zan baki labari akan yadda rayuwar Lamido ta kasance da abubuwan da suka faru bayan b'atarki...".
Maryam ta kwashe labarin komai ta sanar da ita, babu abun da Arfaat take sai kuka tana nadamar daukar maganganun Aljannun nan....
Maryam tace, "Arfaat kinyi babban kuskure, ki gyarashi tun yanzu da kike da damar gyarawa amma sai kinyi amfani da basirarki kin kasance mai zurfin tunani domin kadda ki b'allo wata maganar a yayin gyara wata.... Think and act wisely...".
Sai kuma tayi disappearing, Arfaat ta fashe da kuka saying,
"What have I done...".
Kafin ta sake magana, Nabila ta shigo a rude saying,
"Mun boni, Little bata gidan nan kuma mai guard ya tabbatar min da cewa yaji k'arar bude kofa a lokacin yana toilet...".
Arfaat ta daura hannu a kai saying,
"Na boni, kadda diyar mutane ta b'ace, muje mu dubata, amma muje mu biyu kadda Ummy ta sani...".
Ta daura veil akan gown dake a jikinta suka fita, sun nemeta a layin amma babu ita babu alamarta, babu wanda yaga mai KAMANNI da ita, ta fashe da kuka, ta rasa inda zata saka kanta, tana son ta kira Lamido ta sanar dashi halin da ake ciki amma ta rasa yadda zata ce dashi, can ta cewa,
"Tabarmar kunya da hauka ake kwasheta...".
Ta danna mashi call, hankalinsa ya tashi sosai jin tana kuka, yace,
"Angel... Mi ya faru?".
Cikin kuka tace,
"Lamido ka cuceni, dama tarbiyyar da kayi wa diyata kenan, yarinya daga nayi mata fad'a tabar gida basu san inda take ba...".
Bai san lokacin da ya mike tsaye ba saying,
"What?".
"Ay kaji da kyau, kuma tun wuri kazo mu nemeta tare don idan wani abun ya sameta bazan yafe maka ba...".
Hankali a tashe ya shiga motarsa yayi mata key zuwa inda suke, Nabila ce take mashi bayanin abun da ya faru....
Tare dashi suka dasa nemanta, Arfaat babu abun da take sai kuka, da yayi magana ta hau fad'a saying,
"Duk laifinka ne ba kayi wa yarinya tarbiyya ba, daga fad'a, mudai ganta tukunna zataga abun da yafi fad'a Dan ubanta...".
Dakyar suka sameta, a wani shago wasu mata suna tambayarta gidansu tana kuka....
Lamido yayi hugging dinta yana masu godiya, yana rarrashinta saying,
"Sorry little, miye?".
Ta nuna Angel tana kuka saying,
"Tayi min ihu...".
Yace, "Sorry ba zata k'ara ba...".
Little tace, "Kuma na b'ata da ita...".
Arfaat tana jinsu tayi banza, da sauki tun da an sameta...
Direct gidansu Arfaat ya wuce yana driving saying,
"Zan wuce da ita gidana...".
Yayi kallo tayi mashi, babu shiri yayi shiru, yana parking ta janyo little ta cigaba da tsula mata bulala saying,
"Dan ubanki, ke diyar uban waye da baza ayi maki fad'a ba, daga nayi maki fad'a shine zaki fita...".
Little tana kuka calling him, Arfaat tace,
"Idan ka matso zamu samu damuwa ne, ni zanyi mata tarbiyyar daka kasa mata...".
Tana tsula mata bulala tana fad'a, Little Arfaat taji zafi ta soma bada hakuri....
Ummy dake tsaye a balcony ta soma tab'a hannuwa saying,
"Good... Kin kyauta, tarbiyya kike badawa a haka, kina zagi a gabanta... Kai kuma ban san lokacin da ka koma mijin tace ba, da alama itace mijin yanzu... Ki sameni a parlor...".
Lamido bai yarda suka had'a idanu har ya zauna, Ummy tace,
"Dagowa zakayi ka kalleni, ashe bayan auri saki, har da tsoronta ka koma...".
Lamido ya sosa kai saying,
"Ba haka bane, Baraka da kanta ta nemi in saketa...".
"Shine sai ka saketa saboda tace ka saketa... Ke kinji sai ki iya bakinki cox idan kika ce ya sakeki sakinki zaiyi...".
Referring to Arfaat...
Lamido yace, "Ummy...".
Ummy tace, "Don't ummy me... Yau zan kawo karshen komai... Ina maka kallon mai hankali ashe baka dashi... Daga tace ka saketa sai ka saketa... Kirata, I mean Baraka, ka kirata tazo...".
Lamido yace, "Ummy...".
Ta daka mashi tsawa saying,
"Call her...".
Babu shiri ya danna mata call, babu jimawa tazo, ta gaida Ummy kafin ta zauna a oneseater, Ummy tace,
"Lamido, mayar da ita...".
Baraka ta ware idanu saying,
"What! Ummy don't do this to me... Na saka ya sakeni ne saboda shine mafitata, na aureshi against his will, wanda sai bayan auren na fahimci abubuwan da yake k'ok'arin fahimtar dani... Bayan tafiyarsa saura kadan in fad'a halaka Allah ya cetoni shiyasa na zab'i ya sakeni cox wannan ne mafita a gareni... Arfaat ce kawai a zuciyar Lamido, babu wata mace da zata samu gurbi bayan ita, shiyasa na rabu dashi domin in samu wanda yake sona in rayu a farin ciki, Lamido mijin Arfaat, kiyi min addu'a Allah ya kawo min na gari... Tun tuni ina son zuwa gaidaki saidai ina kunyar abubuwan da suka faru a wadancen shekarun...".
Ummy tace, "Don't be, ki rink'a zuwa kina zumunci, duk lokacin da kikaji kina son komawa gidan Lamido kiyi min magana, zan saka ya mayar dake dole, kuma duk wanda ya b'ata maki rai a cikinsu ki sanar dani, in b'ata mashi daga shi har ita...".
Baraka tace, "Kun dai ji, Ummy bata hadani da kowa ba, don haka ku bini a hankali... Ummy na gode sosai Allah ya k'ara girma...".
Ummy tace, "Amin...".
Tayi masu nasiha sosai musamman Lamido....
"Arfaat ki bishi ku tafi, Hajjo zasu biyoki da kayanki...".
Arfaat ta zaro idanu saying,
"Tarewa kuma?".
Ummy tace, "Zaki tashi ki bishi ko kuma sai nayi maki irin hukuncin da kika gama yi...".
Babu musu ta mike tabi bayanshi, ta bude backseat ta shiga, little tana a frontseat tareda Baraka, yayi wa motar key....
Baraka tace, "Sai fa nike ji kamar in saka a mayar da auren nan, zan tsula tsiyata ne, da kunyi min abun da baiyi min in kira Ummy tayi min maganunku...".
Lamido yayi dariya saying,
"Idan kin shirya a shirye...".
Baraka tace, "Wake up, koda kudinka babu rabonka, dama can kyanka ne yake rud'ata, sai yanzu na lura da katon kai ne da kai, farin ne kawai ya ceceka...".
Lamido yace, "Dama abun da ba zaka samu ba, hadashi kake da baka so...".
"Gaskiya dai, ka saukeni a bakin get ku wuce... Aunty Arfaat, Allah ya bada zama lafiya... Don't mind us, abokan wasa muke... As far as akan zuciyar yaya Lamido ne, ke kadai ce a ciki...".

Hafsat Hisham (Aysher Angel) πŸ₯°πŸ˜˜πŸ₯°
[07/04, 20:27] Angel: πŸ’¨ *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* πŸ’¨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)
*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*

Page 25


Bayan da sukayi dropping Baraka da Little Arfaat a gidansu Lamido, karfe goma daidai private jet dinsa ya lula dasu a sararin samaniya, Arfaat ta kasa had'a idanu dashi, kamar zatayi kuka tace,
"Yaa Lamido kayi hakuri akan abun da nayi maka, Aljannun nan ne suka fad'a min k'arya tareda had'a tuggu wanda na kasa ganewa... Please kayi hakuri... Duk da bazan iya fad'a maka aihinin abun da ya faru ba...".
Lamido ba tareda ya d'ago yace,
"Ashe haka masifa take maki kyau... Dole in rink'a tokaloki domin kiyi min in gani, ai koda kudina sai in siya...".
Arfaat tace, "Why are you avoiding me?".
Lamido yayi wani shegen murmurshi ta gefen baki sannan yace,
"I'm not avoiding you... Ina busy ne, there is alot for me to take care of... Kadda ki damu zan kulaki ne idan muka sauka...".
Bayan sunyi landing a London, convoy na motocinsa suka wuce dasu villa dinsa dake a can, sukayi sallah sukayi wanka, suka sauko parlor....
Lamido ya wuce kitchen, zata bi bayanshi, yace,
"No... Ki jirani a parlor...".
Ta juya parlor ta zauna, ya jima a kitchen, fitowa da warmers yana ajiyewa akan table, Arfaat ta mike heading there, yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna opposite da ita, yayi serving plate ya tura a gabanta, ya saka kaza guda daya wacce ya soya mata sai kamshi takeyi, ya tura mata saying,
"Eat... Kici...".
Kadan ta deba ta kai bakinta ta lumshe idanu saboda yadda yayi dadi, ta yagi kazar tana ci ta kora da milk...
Ya mike saying,
"Muje...".
Suka wuce upstairs, ya bude wani kofa ya shiga tabi bayanshi, gado ne kawai a ciki sai television da fridge tareda closet, ta zauna a gefen gado yayinda shi kuma ya shiga closet jim kadan ya fito ya ajiye mata half night gown tareda perfumes, yace,
"Ki shirya... Kiyi alwalla...".
Ya juya ya fice, Arfaat ta d'aga rigar tana kallo, ba zata wuce daidai gwuwa ba sannan shara-shara take kamar matacin koko wadda da ita da babu duk daya ne, she have no choice than ta mike ta wuce bathroom ta watsa ruwa sannan ta wanke bakinta tayi alwalla, ta fito tayi applying cream sannan ta shirya a cikin rigar, ta dauki hijab dake a gefe ta zura bayan da ta feshe jikinta da perfume da ya ajiye mata wanda kamshinsa yayi mata dadi sosai....
Lamido ne ya shigo yana sanye da jallabiya, ya jasu sallah raka'a biyu, ya dafa kanta tareda karanta addu'a, saidai ji tayi yayi sama da ita ya dure a saman gado tareda zare hijab dake a jikinta ya soma yamutsata yana gurganani tareda maida lumfashi, tun tana daukar abun a wasa har taga da gaske yake, ta soma sheshshekar kuka, ganin kamar ban san tana yi ba, ta kware baki ta fashe da kuka, ya hade bakunansu yablna mai cigaba da yamutsata, taci wuya, tayi kuka har ta gaji, duk jini ya b'ata bedsheet....
Lamido murmurshi ya kasa gushewa daga saman fuskarsa, yana saka mata albarka tareda furta mata kalamai na soyayya, da kanshi ya dauketa ya wuce da ita bathroom ya had'a mata ruwan zafi, ya gasata sosai sannan ya fito ya barta tayi wankan tsarki, ya cire bedsheet ya sauya da wani, jim kadan ta fito tana dangashi, ta kasa had'a idanu dashi, ta tsaya cak tareda ware idanu ganin ya nufo inda take walking like a model, yana sakar mata murmushi, kafin ta ankara saidai gani tayi ya sunkuya tareda sama da ita, ta fashe da kuka marar sauti ganin ya nufo gadon da ita, ya ajiyeta tareda pecking goshinta saying,
"Love you...".
Saida tayi bacci sanann ya mike ya wuce bathroom yayi wanka, ya fito ya kwanta tareda hugging dinta yana jin sonta yana k'ara shiga ranshi....


Washegari koda ya tadata sallar subh kasa had'a idanu tayi dashi, ya jasu sallah, ta koma akan gado bacci ne yayi awon gaba da ita, saida ya had'a mata breakfast ya kai mata har bedroom sannan ya fita, throughout the day ba ya gida saidai love message da yake tura mata from time to time, order din lunch yayi mata aka kawo mata har gida, same with dinner....
Bayan sallar Isha'i tana zaune akan sofa, ya shigo da murmurshi akan fuskarsa saying,
"Angel...".
Arfaat ta kalleshi sai kuma tayi kasa da kanta, ya k'arasa inda take ya durkusa tareda daura mata wani k'aramin kit a hannunta, yace,
"Ki bude... Ki gani...".
Arfaat ta dubeshi ya gyad'a mata kai yana murmurshi, ta bude yayinda wata expensive sarkar diamond ta bayyana, ya amsa tareda sunkuyawa ya dauketa ya ajiye a gaban mirror ya saka mata sarkar tareda hugging dinta, ya ajiye mata peck a gefen fuska saying,
"I love you Arfaat... You are the love of my life...".
Da kanshi yayi mata wanka ya saka mata kaya ya kwantar da ita akan gado tareda hugging dinta, ta soma mutsu-mutsu, a hankali yace,
"Ki nutsu, babu abun da zanyi maki...".
Tayi lamo, bacci ne yayi awon gaba da ita saida baccinta yayi nisa sannan ya saketa ya duro daga saman gadon ya dauki system yana aiki....
Bayan sun gama sallar subh ta koma bacci, saidai farkawa tayi taga inda ya kwanta wayam, da mamaki take kallon bedroom din wanda aka sauyawa kamanni da decorations masu dauke da kalmomin soyayya, ta taka har inda ya jera mata lafiyayyen breakfast, flowers ne a gefe tareda card mai dauke da zallar kalaman soyayya, saida tayi wanka tareda saka rigar da ya ajiye mata wacce sabuwa ce ya siyo, ta saka sarkar tareda gyara dogon gashinta tayi parking dinsa, the breakfast's delicious and yummy, tana ci tana lumshe idanu, ta dauki wayarta ta saita camera tana bin wakar soyayya tana far idanu tareda turo baki looking breathtaking and gorgeous, ta dauki video ta tura mashi...
Both lunch da dinner order yayi mata, har tayi bacci bai dawo ba, cikin bacci taji yayi hugging dinta, ta gyara kwanciya a jikinsa tareda sakin murmurshi, yace,
"Sleeping cute...".
Tace, "Uhmm...".
Lamido ya gumtse dariya dake son kufe mashi yace,
"Angel... Meyy za'a bani ne?".
Ba shiri ta soma mutsu-mutsu saying,
"Na boni...".
Yayi dariya saying,
"Wasa nike maki...".
Ya ajiye mata kiss a kumatu tareda k'ara kankameta a kirjinsa....
The following day bayan sun gama breakfast suka shirya suka fita zaga gari har ya kaita makarantarsu Sultan, saida daddare sannan suka koma gida sukayi dinner tareda wanka suka kwanta....
Arfaat ce tsaye a gaban window tana kallon waje, Lamido yayi hugging dinta ta baya tareda tura kanshi gefen wuyanta, ta soma zillewa tana dariya, ya sunkuya tareda daukarta ya wuce bedroom tareda rufa a kanta yana b'alle bottom din rigarsa, da gudu na fice kadda yayi light na buge goshi😏.....
Washegari Helcofter ya daukesu zuwa airport inda suka bi private jet dinsa to Egypt, saida sukayi kwanaki ukku sannan suka wuce dubai, sunyi yawo sosai wanda zan iya kiranshi da honeymoon, despite that ba ya dadewa a tare da ita amma yana nuna mata kulawa sosai in his own way, been busy bai hanashi nuna mata kulawa ba....
Daga Dubai suka juyo back to Nigeria, saida suka fara zuwa gidan Ammi suka dauki Little Arfaat sannan ya wuce dasu suka gaida Ummy tareda basu tsaraba da sukayi masu, Ummy tayi masu nasiha sosai kafin suka wuce gidanshi.....
Lamido ya fito yana dauke da Little Arfaat wacce take bacci, Arfaat ta mara mashi baya, sashensa ya wuce ya kwantar da little Arfaat a bedroom dinta dake a can sannan ya wuce bedroom dinsa, Arfaat tace,
"Ina ne sashena?".
Lamido ya kashe mata ido daya saying,
"Gobe zan kaiki... Yau a nan zaki kwana, love of my life...".
Arfaat tace, "Love of my life..".
Lamido yayi hugging dinta saying,
"Of course Angel...".
Washegari suna gama sallar subh ta sauko kasa tareda shiga kitchen dake a sashen, ta zage ta had'a masu delicious breakfast, tayi kosai da koko saboda little Arfaat....
Ta koma sama ta tsala wanka tareda shiryawa cikin wasu riga da wando ta saki gashin kanta....
Little Arfaat ce ta shigo ta haye saman gadon tana tsalle a kai saying,
"Abbana... Wake up...".
Arfaat tace, "Kadda ki tayar dashi...".
Lamido ya bude idanunsa tareda hugging little Arfaat yana manna mata kiss a kumatu, yace,
"Na riga na tashi... Morning, Angel...".
Little Arfaat tace, "Morning Abbana...".
Lamido yace, "Morning, Angel...".
Arfaat tayi far da idanu sannan tace,
"Ina kwana ranka ya dade...".
Lamido ya kwaikwayeta saying,
"Lafiya lau ranki ya dade...".
Arfaat ta soma dariya har tana dukewa, the more take dariya the more take k'ara mashi kyau, ya saita mata camera yana mata video....


Hafsat Hisham (Aysher Angel) πŸ₯°πŸ˜˜πŸ₯°
[12/04, 11:22] Angel: πŸ’¨ *SUNE SUKA JANYO MIN*
*BOOK 2...* πŸ’¨
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

*The writer of Ban Dace Dashi Ba... The Choice I Made... Chasing My Heart, a tsakanin so... Ban Aikata Ba, Confusion Upon Confusion... Zan Bi Zab'in Ummana, Koda Zuciyata Bata So... Kamanni... Y'an Mata Return...*


Page 26

For wadanda suke son paid books dina
9169472057
Aisha
Opay Digital Service
Sai tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057
Shima Barka Da Sallah nah ta can zaku tura 😎😎😎


"Angel the more kike dariya the more kike k'ara kyau, komai kyau yake maki...".
Little Arfaat tace, "Abbana... Wanka...".
Arfaat tace, "Tafo muje inyi maki...".
Little Arfaat ta mak'e kafad'a tareda turo baki saying,
"Ni Abbana nike so...".
Lamido ya sauketa daga saman gadon saying,
"Kije bathroom gani nan zuwa...".
Little Arfaat ta wuce da gudu tana tsalle, ya duro daga saman gadon yana walking toward Arfaat, ta kalleshi ta kalli kofar bathroom da Little Arfaat ta shiga, yayi hugging dinta yana shakar kamshinta tareda tura kanshi a gefen wuyanta saying,
"Kinyi min wannan wankan bazan bari Little Arfaat ta b'ata shi ba, ban gama kallo ba...".
Tana kallon kofar kadda Little ta fito ta gansu, tace,
"Okay, kuyi sauri, breakfast is ready...".
"Yaushe kika tuna kadda muci muji gishiri yayi yawa...".
Arfaat ta turo baki tareda b'ata fuska, Lamido ya lakuci hancinta saying,
"Like mother like daughter... A bani breakfast...".
Saida Arfaat ta rufe idanu sannan ta ajiye mashi light kiss, ta kwace ta gudu waje, ya bita da kallo yana dariya....
Tana zaune a parlor ya sauko yana dauke da Little Arfaat, ta gyara ko'ina tsaf-tsaf sai tashin kamshi yake, Lamido yace,
"Angel... Yaushe kikayi duk wannan aikin?".
Ta d'age brow saying,
"Today...".
"Allah yayi maki albarka...".
"Amin... Ranka ya dade...".
Tayi serving kowa, Lamido yayi spoon daya ya b'ata fuska, Arfaat ta ware idanu, ta tsure, ya kalleta ya kalli abincin, ya fashe da dariya ganin reaction na fuskarta, yace,
"It's delicious...".
Ta sauke ajiyar zuciya, bayan sun gama, ta tattara abubuwan da suka b'ata ta wuce dasu kitchen ta wanke, ta fito tarar da Little Arfaat tana kallo a parlor....
Lamido yace, "Muje in rakaki sashenki...".
Arfaat tace, "About the catering school?".
Lamido yace, "Mu gama more amarcinmu tukunna... Daga nan sai ki rink'a dropping Arfaat a school...".
Arfaat ta kawar da fuska, yace,
"Uhmm...".
Yana mai leken fuskarta, tace,
"Na gode ranka ya dade...".
"You are welcome...".
Yana gaba tana biye dashi har suka shiga sashenta wanda yake babba sosai har yafi wanda Baraka ta zauna, an zuba mata expensive furnitures tareda electronics, ya zaga da ita ya nuna mata kitchen, parlors, bedrooms, balcony, wajen swimming pool, garden, parking lot da sauransu, ta rakashi wajen mota tana mashi waving hand har ya danna motar ya fice daga wannan get din, yayinda ita kuma ta juya ta koma ciki ta kunnawa Little Arfaat kallo sannan ta soma gyara sashen duk da baiyi datti ba....
Lamido wuni yayi a office, da rana ta dafa masu fried rice, da marece taje sashensa ta gyara tareda kunna turaren wuta, ta koma part dinta ta soma girkin dare, tuwon shinkafa tayi da miyar taushe, ta gama ta zuba a warmer ta daukesu ta wuce dasu sashensa, bayan ta gama sallar Isha'i ta tsala wanka tareda shiryawa cikin half night gown, ta daura doguwar gown a samanta tareda daura madaurin sannan ta wuce sashensa, ta kwantar da Little Arfaat a bedroom dinta dake a sashen sannan ta zauna a balcony ta daura kafa daya akan daya tana jiranshi....
Motarshi ta danno kai, yayi parking, ta nufeshi tana tafiya a nutse yayinda baki daya jikinta yake girgiza, tayi hugging dinsa tareda ajiye mashi peck a kumatu tace,
"Sannu da dawowa ranka ya dade...".
Ta amshi briefcase dinsa ta juya tana taking steps baki daya jikinta yana girgiza, tana wani irin tafiya mai tafe da salo na daukar hankali, yabi bayanta heading to his part, ta taimaka mashi ya rage kayan dake jikinsa ya rage daga shi sai guntun boxer, yayi tsaye yana turo baji tareda mata alamar shima ta cire, tayi rolling idanu tana wani shegen murmurshi, ta kama kamar zata cire ta tsammaceshi ta juya ta fice da gudu tana mashi gwalo, ya rike beard yana dariya saying,
"Yarinya, lada ta wuce ki...".
Da kanta tayi serving mashi abincin yana ci yana lumshe idanu tareda saka mata albarka, ya wuce parlour yayinda ita kuma ta tattara kayan da suka b'ata ta wuce dasu kitchen ta wanke...
Bayan ta gama ta samu yana kallon News a parlor tayi joining dinsa, ya sauya channel zuwa na movie na soma hamma, mikewa tayi ta saki wata mik'a mai tattare da daukar hankaki kafin ta cire dogon gown dake jikinta, ya rage daga ita sai guntun night gown mai shara-shara kamar matacin koko, ya ware idanu yana kallonta ta juya ta k'ara juyawa cike da salo na daukar hankali...
Babu shiri Lamido ya kashe kallon yayi sama da ita to the master room, nima na tattara na koma inda na fito, saida safenkuπŸ˜πŸ˜‰....
Washegari bayan ta had'a masu breakfast tayi wanka, tayi wa Little Arfaat ta shiryata cikin kayan makaranta sannan itama ta shirya cikin doguwar rigar shadda wadda tasha stone work, Lamido ya sauko kasa cikin shiri yace,
"Angel en makaranta...".
Little Arfaat ta ruga da gudu tayi hugging dinsa, yayi wa Arfaat alama, ta mak'e kafad'a, ya nuna mata kirjinsa ta kawar da kai, suka zauna a dinning table tayi serving kowa sannan ta zauna, Lamido yana feeding Little Arfaat yana ci har ya koshi, suka mike, Arfaat ta janyo long hijab dinta da ta ajiye akan kujera ta zura suka fita, yace,
"Muje inyi dropping dinku...".
Arfaat tace, "Idan aka yi haka ranka shi dade, waye zai dauko little da ni kuma...".
Lamido yace, "Alright then... Bye...".
Little Arfaat tayi mashi waving hand saying,
"Bye...".
Arfaat tayi mashi waving hand saying,
"Bye...".
Saida ya wuce sannan taja hannunta suka wuce inda motocinta suke, ta

Please Login or Register in order to submit comment