Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daidai ba haba alhaji come back to your senses mana this is too much”daga Mata hannu sama yayi kafin yace“bafa abinda na tambayeki kenan ba saleemeh, this is between me and you”sannan yayi shiru Yana dubanta kafin ya dora da fad'in “you are asking mena gani akan Sabrine har nakesonta right? ”karayin shiru yayi na wasu minutes kafin ya Kara da fad'in “baki lura da Sabrine sosai ba saleemeh ki kalleta wallahi exactly like Fatima”da sauri hajiya saleemeh ta Mi'ke tana Dan dafe kirji tare da furta “fatima!! Kuma alhaji ”d'aga Mata Kai yayi alamar eh, wasu sabbin hawayenne suka zubo Mata ta dubeshi tare da fad'in “yanzu fisabilillahi alhaji akan tana kama da wannan me idon mayun shine zaka tada rigimar auren ta alhaji”wani irin bacin Raine ya ziyarci LEC A. M tare da nuna hajiya saleemeh danyatsa Yana fad'in “aduk abinda zaki furta kada ki kuskura ki aibata Fatima kinji na fad'a Miki , now get out of my side” yafada da wani irin fad'a har Saida hajiya saleemeh taji tsoro tana kallonsa,

“out!!! ” ya Kara fad'a cikin d'aga murya, cikin sanyin jiki hajiya saleemeh ta janye jiki tana mamakin yadda akai alhaji ya juye ya zama haka, cikin kuka ta juya tabar dakin, Afiya na ganin fitowar ta da kuka taji zuciyarta tayi zafi kawai ta juya tashige d'aki

Hajiya saleemeh nashiga d'aki tai ta sunturi ta kasa zaune ta kasa tsaye, samu tayi ta zauna gefen gado had'e da lalubo wayarta , contact d'inta tashiga tai typing hajiya zainab Amma Sam lambar Bata fito ba , tagama duba dubenta har Gmail Bata ganta ba , dafe Kai tayi had'e da furta innalillahi , shiru tayi nawasu Dan lokuta saikuma tayi dialing wata number ansa hajiya murja , ringing biyu tayi aka d'aga had'e da fad'in “hajiya Saleemeh manyan gari”cikin daure wa na Hana kanta kuka ta furta“murja Dan Allah temako zakimi ”
Dagacan wadda aka Kira da murja tace“dama tunda Naga kiranki nasan in kaji gudu da labari to inajinki wane temako”dasauri tace“dan Allah kituromin number d'in zainab”

“too ikon Allah zainab fa kikace , ”cikin 'kaguwa hajiya saleemeh tace“kinga Dan Allah nidai ki temakamin ki turomin” dagacan akai dariya had'e da fad'in “to zan duba Miki Allah yasa tana gari Dan zainab kafar yawo ce”da sauri hajiya saleemeh tace“nidai ki turo min ”

“zan turo Miki yanzu”tanajin hakan ta yanke wayar ta Matsu a turo Mata , kusan mintuna goma Sha biyar sannan wayar hajiya saleemeh ta fara ringing, da sauri ta d'aga had'e da fad'in “baki turomin bafa ”dagacan hajiya murjar ta furta“aikuwa nikam du na duba banganta ba wallahi bansan ya akai ba ”
“ innalillahi wainna ilaihirrajuun yanzu Dan Allah murja Ina zan Sami zainab koma number d'inta wallahi Ina cikin matsala” ta fad'a tana Mi'kewa daga kan bed d'in datake, hajiya murjarce dagacan tace“kinga kibani Nanda gobe inshallah zan Samo miki number d'inta amam gaskiya ayanzu bansan Ina take ba”da sauri hajiya saleemeh ta furta“yauwa hajiya murja nagode Allah yabar zumunci saina jiki”daga haka suka yanke wayar da fatan Allah yasa dai Sami hajiya zainab d'innan


Alhaji Hassan ne ya dubi matarsa wadda itama ta bashi hankalinta Dan abinda yake Shirin Gaya Mata tabbas me muhimmanci be
“Abinda na Tara gidan ABDURRASHID ya girmi tunanina can you imagine wai yarinya d'aya suke so shida Adnan gaba d'aya abin ya girmi tunanina”
“ikon Allah ”matar tasa ta furta cike da mamaki sannanta Dora da fad'in “yanzu shi tayaya zai so abinda dansa yake so fisabilillahi kayi hakuri Amma kaninnan naka baya kyautawa wallahi sam”tayi maganar cikin fushi da bacin Rai, murmushi alhaji hassana yayi kafin yace“nima hakan naji abinda kika hi yanzu bayin hajiya saleemeh ta shaida min abinda ya faru a waya, Amma kinsan me”girgida Kai tayi had'e da fad'in “saika fad'a”cikin murmushi yace“natambayeshi dalilin dayasa yakeson yarinyar Amma abinda yafadan sainaji Ina goyan bayansa”damamaki matar tasa tace“kaikuwa mezai fad'a maka da har zaka goyi bayansa fisabilliahi alhaji”wani Saban murmushi yayi tare da fad'in “kema kanki zaki ji dad'in abinda zan fad'a domin abdurrashid da kansa yake shaida min cewa yarinyar kama take mai da fatima ”cikin dafe kirji matar tasa tace“fatima kuma alhaji yanzu shi yafadi sunan Fatima da bakinsa ” cikin tsantsar farin ciki Alhaji Hassan yake maganar Dan iya fuskarsa zata tabbatar maka da hakan“wallahi abinda mukai dashi kenan shiyasa nafi goyan bayansa fiye da Adnan domin wata kila hakan da Allah yayi wata gaskiya ce take so ta bayyana”cikin d'aga hannu matar tasa tace“Allah na gode maka inshallah Allah zai fito da gaskiyar damuke jira shekara da shekaru hakika na goyi bayan abdurrashid sosai akan wannan Al amarin tabba alhaji kaiyafi dacewa kasami Adnan kabashi hakurin ya hakura da yarinyar ya barwa mahaifinsa”shiru yayi kafin yace “um um bahaka ne zai faru ba mudai zuba ido mucigaba da addua Allah zai kawo mafita”

“Amin ”matar tasa ta furta had'e da Mi'kewa tana Kara jinjina abin da alhaji Hassan ya sanar Mata


Kamar Wasa haka soyayya me karfi ta kullu tsakanin Sabrine da Adnan Amma ba tare da ita Sabrine ta sanda son Adnan take aganinta kawai Yana burgeta ta ne , and he's so nice, shine dalilin dayasa ma taji tana son dawowa school Dan harga Allah Tama manta relationship d'in dake tsakanin Adnan da LEC A. M gaba daya , Adnan ya mantar da ita komi , abin har mamaki yake bawa Granny especially taji ma Sabrine tace zata koma makaranta , abin yayiwa Granny dad'i sosai tayi adduar Allah yasa haka ne mafi alkhari tsakanin ta da Adnan Dan harga Allah Adnan yashiga zuciyar Granny sosai
Adaren ranar da Sabrine ta dawo school Bata sanarwa Adnan da wowarta ba dan tabbas da saiya zo, washegari da safe wurin karfe Tara na safe wayar Sabrine ta d'au ringing daidai lokacin tana wanka hakan yasa har Kiran ya katse , jin Kira ya sake shigowa yasa Latipha kallan wayar ganin an rubuta Adnan yasa Tai murmushi had'e d'aukan wayar Tai picking call d'in, cikin shagwaba Adnan yace“ Sabrine konayi Miki lefi ne pls am sorry amma karki hukunta ni ta hanyar 'kin d'aukan waya ta inba haka ba yanzu ki ganni a kaduna”ya Kare maganar da wata sexy voice , dariya Latipha Tayi tare da fad'in“ai bama saikasha wahalar zuwa kaduna ba kawai ka taho school”jin muryar Latipha Adnan yad'an zaro ido had'e da fad'in “latipha you mean sabriny ta dawo school”

“eh mana”latipha ta katse shi, sannan ta Dora da fad'in “ don't tell me Bata fad'a maka ta dawo ba”

“yeah is okay thanks for this wonderful news, idan ta fito kice Mata I will come anjima”

“yeah sure”ta fad'a tana kashe wayar daidai lokacin Sabrine ta fito daure da towel tana goge jikinta tace “who call? Granny d'itace ko”harararta Latipha tayi tare da fad'in “a'a wannan kam darling d'inki ne”

“darling ”Sabrine ta furta tana kallon Latipha

“idan baki yarda ba saiki duba ai”aikam da sauri Sabrine tazo ta kar'bi wayar hannun Latipha tana dubawa , “and yace he is coming anjima” Latipha Tayi maganar tana shigewa bandakin Dan itama wanka zatai suna da lecture


“what you mean kin fad'a masa na dawo”daga bandakin Latipha tace“an fad'a d'in anaso ana kaiwa kasuwa , idan LEC A. M d'in kikeso ai saiki bayani”
Dafe Kai Sabrine tayi had'e da fad'in nikam shurutunki Latipha wani sa'in beyi ba wallahi yanzu kinsa ni amatsala
Ta fad'a tana ajiye wayar tana d'auko Mai ta shafa,
Har suka gama shiryawa ita da Latipha Sabrine na mita akan Bata kyauta Mata ba itakuwa Latipha ko ajikinta dariya ma takeyi,ahanya ne Sabrine take tambayar Latipha meyasa ita Bata kula kowa Amma ita ta dage Dole saita saurari Adnan
Dariya Latipha Tayi kafin tacewa Sabrine

“sabrine kenan ,saboda banaso kishiga halin danashiga ss
Sabrine wallahi rayuwar nan kullum Kara tsada take samun miji nagari kullum wahala yake Sabrine wallahi ayanzu duk wacce tasamu miji indai me nagarta ne gwara tayi auren ,shine dalilin dayasa kikaga na takura Miki akan Adnan”dakatawa Sabrine Tai da tafiya tare da fad'in “latipha tell me what's too special da Adnan ke dashi”dafa kafad'ar Sabrine Tai tare da fad'in “wallahi Tako Ina Adnan mutumin kirji ne kodan yadda yake binki Sabrine zakisan hakan ki duba yadda yawan Yan Mata suke wadanda ko kansu zasu iya bashi Amma Dole ke yakeso, kuma Nina fad'a Miki zakizo ki bani labari for sure”tana fad'ar hakan ta kama hannun Sabrine suka karasa lecture hall d'insu,tun kafin su karasa shiga Sabrine ta hango LEC A.M takan iya ganin yadda du ya rame,jitai tausayinsa ya kamata , sa'banin yadda Sabrine Bata iya zama Abaya sai agaba ,Amma wannan Karan can baya ta nema ta zauna Dan sotake ta bawa kanta distance da LEC A.M ko hakan zai zama mafita gareshi ya Dena santa,
Yadda LEC A.M yaga Sabrine tayi hakan ya tabbatar masa cewa Sabrine gudunsa take ,gaba d'aya jiyayi ya kasa lecture d'in Amma haka ya tilastawa kansa yadinga Yi cikin salo yadda dalibai zasu game
Karfe biyu suka fito daga lecture d'in tacan kofar baya Sabrine ta fita tana jiran Latipha da fito,Amma tananan tsaye taga LEC A.M ya tun karo inda take tsaye zuciyarta ce ta fara dukan uku uku, kirjinta ya dinga bugawa da sauri ta juya ta fara tafiya ahankali kamar wadda kwai ya fashewa Amma ta tsinci muryar LEC A.M ya furta
“Sabrine ”tsayawa da tafiyar Sabrine Tai Amma ta kasa juyowa ,ahaka yazo ya sameta har gabanta yaja ya tsaya ,kanta a'kasa gaba daya takasa d'agowa hannunta har rawa take ta kasa holding littafan sosai……





*Marasa comments dakaina zanyi remove inshallah*


*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_

2️⃣6️⃣


“Sabrine” yasake Kiranta, dubantasa tayi cike da sanyin muryar, cikin rawar baki Sabrine tace“sir…Ina wuni”wani kasalallan murmushi LEC A. M yayi had'e da fad'in “ Sabrine guduna kike ”girgid'a masa Kai tayi still kanta a kasa, “guduna kike mana , just because I Sayed I love you Sabrine shine zaki bani distance haka? Akan me bazaki Soni ba ? Saboda shekaruna? Ko saboda Adnan? Ko saboda iyalai na ? Pls tell me ? ”
Jin yadda yake maganganu cikin pain kana ganinsa kasan basai anfada ba akwai abinda yake damunsa ba, kwalla suka taru idonta tasa bayan hannunta ta share batare data Yi magana ba

“say something Sabrine Dan Allah ki fad'an meye matsalar, you see my age thinking of you alot isn't good for my health, ”muryarsa har rawa take ”

Ahankali Sabrine tafara fad'in “i'm sorry to say this Amma bana tunanin abinda kake tunani , I love you sir Amma ba irin love d'in dakake tonani ba , inasanka amatsayin malami na sannan inasanka amtsayin Wanda yake kula Dani , believe me sir you are like father to me, Amma bazan iya…….”daga Mata hannu yayi ganin hakan yasa Sabrine tayi shiru tana kallansa ya dafe kirji , sannan slowly yajuya ya barta agurin Yana jin jiri jiri Kamar zai Fad'i ahaka yakai gurin motarsa duka Sabrine na kallansa , gaba d'aya taji tausayin sa ya kamata , ahankali hawaye suka zubo Mata ta goge sannan Afili ta furta“i'm sorry but I really love your son sir, wallahi inason Adnan, jitai
An dafa Mata kafad'a tanaa juyowa taga Latipha aikam ta fad'a jikin ta , Tai hugging d'inta with so much tears tafara fad'in “latipha Kinga ko, kekikace min naso Adnan fa and ayanzu inajin Sansa azuciyata, nakasa nunawa Adnan irin sanda nake masa ne saboda LEC A. M, yanzu ma nasan LEC A. M haushina yakeji Latipha”ta sake fashe da kuka tana d'ago wa daka jikin Latipha tana girgiza kai tare da fad'in“anya kuwa Latipha nakyau? Anya nakyautawa zuciyar Wanda tunda nazo school d'innan burinsa ya kyautata min burinsa ya ganni cikin farin, Anya na kyauta”tasake sa kuka sosai, Latipha d'an bubbuga bayanta take sannan ta fara fad'in“ cool down Sabrine take heart , inshallah zamu Samo solution kuma Allah zai shiga lamarin, Amma doesn't mean zaki hakura da son Adnan , kin fad'a soyayyar Adnan wadda kekanki baki saniba but keep praying Sabrine nima zan tayaki kinji,”sannan taja hannunta ganin yawan mutanan dasuke hucewa sun karu tace“zo mutafi Dan Allah stop crying”taja hannunta suka tafi

Tunda LEC A. M yashiga mota kirjinsa ke masa wani zafi , ahankali ya d'auko wayar dake kusa dashi , bansan dai waya Kira ba ana d'aga wa yace“no lecture today we will meet next week”yana fad'ar haka ya kashe wayar sannan yayi wa motar key yafara driving da tunanin abinda Sabrine ta fad'a masa , Zuciyarsa na Kara masa Amma shi yasan Sabrine zata dawo gareshi domin aduk adduar dayake betaba jin bazai samu Sabrine ba

Ahaka ya Kai gida yayi horn driver ya bud'e masa get yashiga , yayi parking ya fito ko jakarsa be d'auko ba yayi cikin gida
Hajiya saleemeh na zaune a babban parlo tayi tagumi haka yashigo ya sameta hakannan yaji haushinta yakeji shikanshi beson dalili ba kawai yahuce yayi section d'insa, hajiya saleemeh jitai wayarta ya fara ringing ganin ansa Murja, dasauri tami'ke zuwa dakinta da sauri sannan ta d'aga wayar had'e da fad'in “murja harnayi jira na gaji Allah yasa andace”dariya murjartai tace lallai na yarda kina cikin matsala hajiya
Saleemeh”

Cikin 'kaguwa hajiya saleemeh tace“kinga murja Dan Allah kibar zancennan kifad'amin kinsamu”

“ai kafin na kiraki namiki sending ki duba naturo miki”wata sassanyar ajiyar zuciya saleemeh ta sauke had'e dayiwa murja godiya sannan ta kashe wayar tashiga Kiran number d'in da ta turo Mata, kusan Kira goma Tai Amma ana cemata not reachable babu yadda ta iya haka ta hakura da Kira ta zauna zuciyarta fal zulumi



Dakyar Latipha ta rarrashi Sabrine har ta daure tayi wanka , lokaci zuwa lokaci Latipha ke Jan Sabrine da Shira saboda bataso ta Kara tunanin LEC A. M da halin da yashiga
Karfe biyar Sabrine na kwance tana sanye da wasu Italian Pakistan black sunyi Mata masifar kyau rigar ta kawo Mata har guiwa Sai wandon Shima be kamata ba sai gelan kayan tayi kyau sosai , tana wance a gadonta Dan Latipha bacci ya dauketa itakuma taji Sam bazata iyayin baccin ba ahaka taji wayarta ta fara ringing , tana dubawa taga lambar Adnan ceke Kira aikam Taki dagawa, harya katse wani yasake shigowa duk a idonta Saida yayi wurin five missed call batai picking ba , wayarta ce yayi Kara alamar shigowar message dasauri ta d'auko ta duba shidinne yayi Mata message dasauri tashiga ta duba

_dram queen yanzu kuma meya faru , pls pick the call_

Tana karantawa kawai ta cinki kanta da murmushi batare da Tai masa reply ba , kafin ta d'auke hannunta wani message d'in ya sake shigowa

_i'm out side nabaki five minutes wallahi inbaki fito saina shigowa har ciki_

Dasauri Sabrine ta Mi'ke tana kallon kofar dakin dake rufe , tasan Hali wallahi inbata fita ba tabbas saiya shigo , gyra mayafinta tayi sannan ta d'au wayarta ta fita

Yana tsaye jikin mota yasa wata shegiyar shadda Banda kyalli babu abinda take sai waya a hannunsa yana latsawa

Tunda ta fito idonta ke kansa Dan yayi Mata wani masifar kyau ga sumar kansa tayi wani baki sosai , d'ago wa yayi Dan jikinsa yabashi kallonsa ake aikam karaf ya kama Sabrine ta kura masa ido babu ko kiftawa , ganin ya kamata da kallon sa yasa ta Dan kautar da fuska batare da ta 'karaso inda yake tsaye ba, ganin Bata da niyyar karasowa yasa shi ya tako zuwa inda take ahankali ya Mata kallo Kamar ya hadiye ta yace“kinga Dena kallon haka no one will take away your boyfriend ki Adana kallonki sai mun aure”ya 'karasa maganar yana lakuce Mata hancinta, samun kanta tayi da murmushi dimples d'inta harsai da suka loba, Dan zaro ido Adnan yayi had'e da dafe kirjinsa yace“ this smile of yours will make me crazy sweetheart, Dan Allah karkinawa kowa murmushi sai no d'aya kinji”ita dai batai masa magana ba sai murmushin ta dake karuwa Dan kallamansa dad'i suke Mata kodan Bata Saba ji bane oho
Nuni yayi Mata da motarsa had'e da fad'in “lets go” Dan dubansa tayi alamar Bata gane ba , d'aga Mata gira yayi tare da Dan Dan langwabar da wuyansa ya furta “please” jitai ta kasa yimasa musu Dan wallahi yanzu Sansa take over
Ahankali ta furta “where”
Murmushi yayi tare da fad'in “bazan fa saidaki ba and I promise bazan komi ba saimun aure”batai masa magana ba kawai ta huce Dan seriously tayi trusting d'insa Bata kokwanto akansa , hakan yasa kawai ta nufi motar da sauri Adnan ya biya , tasa hannu zata bud'e motar yayi saurin ri'ke Mata hannu kallonsa tayi batasan meyasa Adnan bayajin shakkar ta'ba ta ba , kashe Mata ido d'aya yayi ahankali yace“my job not yours ”sannan ya sakar Mata hannu ya bud'e Mata murfin motar, shiga tayi sannan ya rufe Mata kofar Shima ya zagaya zuwa nashi ma zaunin ya zauna, dubanta yayi sannan ya saki cute smile yad'an lankwaso da kansa daidai kunnan ta yace “i love this dress thank you”sannan ya juya yayiwa motar key , d'agowa Sabrine Tai ta kalleshi Kamar ma bashine yayi wannan shegiyar maganar yanzu ba , Amma ko ajikinsa shi baruwan sa
Juyowa yayi ganin tana kallonsa , hure Mata ido yayi tare da fad'in “stop staring drama queen” da sauri t sunkuyar da kanta shikuma ya fara driving ahaka suka bar school d'in

Suna hanya ne , Latipha ta Kira Sabrine Dan ta tashi Bata ganta ba, tana d'aga wayar Latipha tace“sabrine where are you natashi banganki ba”shiru Sabrine Tai saikuma tace “ina dawo anjima kad'an ”tunawa da cewar da safe Adnan yace zaizo yasa Latipha nta harbo jirgin yasa tace“uhm masoya meye na karyar to kice Ina gaidashi ya kula dake ”tana fad'ar hakan ta kashe wayar , murmushi Sabrine Tai , kakar shigowar message ne ya shigowa wayar Sabrine , akusan tare ita da Adnan suka Kai idonsu kan wayar ta , suna LEC A. M ne yafito rad'au kan screen d'in wayar , tana ganin hakan tadauke kanta daga kallan wayar ta juyar da kanta titi
Hakannan yanaso ya San what his dad says shiyasa Zuciyarsa kawai ta yanke ya d'auko wayar yaduba
Hannu yasa ya kar'bi wayar daga hannun Sabrine sannan yarage tukin dayake , da sauri Sabrine ta juyo ta kalleshi jin ya d'au wayarta
Danna wayar yayi message d'in yafito rad'au yashiga karanta sa'kon Kamar haka

_sabrine wallahi duk duniya jinake nafi kowa sonki , jinake rayuwa ta Kamar tazo karshe inbake Dan Allah kiban dama koda kad'an ce_

Yanayin fuskarsa ce ta sauya sa'banin yadda suka taho fuskarsa a sake hakannan ya tsinci kansa da tsayar da tukin ya Danna reply sannan ya mikawa Sabrine wayar yace“tell him I love you the most and I will be there at any cost, Sabrine Dan Allah kifadawa daddy ni kikeso not him ko zai barmin ke wallahi bakisan yadda zuciyata keyi kamar zata buga ba Inna tuna daddy na sonki, but I know indai kin fad'a masa ni kike so zai kyaleki please Sabrine kinji”

Kallonsa take Amma takasa rubuta abinda Adnan keson ta rubuta , tayarda zuciyarta Adnan takeso Amma bazata iya fad'awa LEC A. M haka ba
Hakan ne yasa ta sunkuyar da kanta daka barin kallon Adnan tare da fad'in “i'm sorry”

“sorry”ya maimaita sannan yace“you mean you love Dad not me, daddy na kikeso? ”girgiza masa Kai Sabrine Tai alamar bahaka take nufi ba, jiyayi tana Bata masa lokaci hakan yasa ya dau wayar tata ya fara typing message kamar haka

_no I love Adnan not you pls get me marriage to your son_

Yana gama typing ya tura sannan ya ajiye mata wayar akan cinyarta
Yacigaba da driving , wani babban super market yayi. Parking sannan ya fito ya bud'ewa Sabrine.

*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


2️⃣7️⃣


Siyayya sosai ya jubgowa Sabrine Dan ita Sam Tama kasa magana , yanayin dataganshi Kamar ransa abace saboda abinda ya faru yasa batayi masa magana akan ya rage siyyarba kawai tana binshi da yadda yakeso,
Saida suka gama siyyar kaf sannan ya juyo ya dubeta had'e da fad'in “say something please sweetheart why silent pls”dan turo baki Sabrine Tai tana Dan kallansa tace“i wanna go home”sai alokacin yayi murmushi sannayayi magana kamar me Rad'a “golden voice”yana fad'ar hakan ya ja 'katon basket d'in dasuka ciko da siyayya yayi guriin biyan kud'i yace Sabrine tajirashi he's coming, Amma daka inda yake yana iya hangota ,
Wani alhajine har zai huce ya hango fuskar Sabrine tayi masa wani kyau , har zai huce yaji ya kasa kawai yayo gurin Sabrine da take tsaye tana Danna waya tana ganin lokaci karfe bakwai gari har ya fara duhu tana waje
Jitai anmata sallama yasa ta d'ago Kai , tama Yi zaton shine ya dawo Amma taga wani daban yasa ta dubeshi ba tare datayi magana ba ,mutumin yayi murmushi had'e da fad'in “you are so beautiful ki'kara godewa Allah kinji”d'an juyawa tayi taga ko Adnan na kallonsu ganin baya kallanta yasa tace“thanks”

Mutumin yasake fad'in “sansamu ki bani wata Yar dama , irinku baku da yawa”

Karaf idon Adnan yakai gun Sabrine ganin wani agunta yanai Mata magana yaji zuciyar ta d'au zafi ransa ya baci sosai , amma yad'an daure ya kar'bi ATM d'insa sannan yace maaikatansu sukaimai cikin mota sannan ya nufi inda su Sabrine d'in ke tsaye , jiyayi shi Sam bashida lokacin sauraran Wanda suke

Sabrine ta bud'e baki da nufin cewa mutumin da mijinta ta ke tare kawai daji Adnan yayi Mata kiss a kumatu had'e da kashe Mata ido d'aya sannan yace“wifey let go home kinji kar baby na ya wahala kinsa munzo siyawa baby chocolate ne fa”gaba d'aya Sabrine jitai kalamanta sun tsaya yawun bakinta ya kafe , especially mutuminan dayake jira Sabrine ta bashidama Kota kansa Adnan bebi ba kawai yaja hannun Sabrine suka tafi , kafin yazo duk sun ajiye masa kayan a ledoji Yana zuwa ya bud'e musu bayan motan suka shiga zuba masa aciki
Sannan yasake Jan hannun Sabrine yaje ya bud'e Mata motar gaba d'aya kallan sa take da mamaki


Amma shi ko ajikina tana shiga ya rufe ya sallami masu kawo masa kayan sannan yashiga motar, Yana shigowa tasake kura masa ido yasan dalilin dayasa take kallonsa haka yasa ya juya ya kalleta had'e da sakin wani cute smile sannan yace “why are starting, abinda na fad'a ba gaskiya bane? You are my wife, and my future children nake nufi fa”yafad'a Yana dariya Dan harsaida hakoransa suka fito , dariyar tasa ta mugun Mata kyau hakan yasa itama ta tsinci kanta dayin dariya tanayin kasa da kanta, sunkuyowa yayi kunnenta yace“kinsan Allah idan kika Kara sauraran wani while Ina gun Allah I will hug you and kiss you kinsan Allah har d'aukanki zan I swaer” juyowa Sabrine tai yawani kashe Mata ido d'aya , turo baki tayi tace“ don't even think of doing that”shima turo baki yayi had'e da kwaikwayon maganar ta yace“and don't even start ”dukkansu sukai dariya atare sannan ya d'an tsagaita da dariyarsa , had'e dayin kasa da muryarsa yace“ I love you Sabrine so Dan Allah karki kula kowa saini kinji” murmushi kawai Tai , ganin hakan ya'kara fad'in “pls Sabrine promise me kinji” murmushin tane ya karu

Please Login or Register in order to submit comment