Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani tai Kamar canjoshi akai , d'aga Mata gira yayi alamar meya faru, jitai hawaye na neman zubo Mata kwalla du ta cika idonta , hakan yasa kawai ta huce zata tafi ta barshi Dan bataso yaga hawayenta , tazo zata giftashi yayi saurin ri'ke Mata hannu ya dawo da ita baya, tsayawa Sabrine Tai ta kalli fuskarsa , hannu yasa duka biyun a kunnansa ahankali ya furta“i'm Sorry” jitai bazata iya komi ba hakan yasa kawai hawaye suka zubo Mata kawai Tai rungumeshi tasa kuka


Abin kam har mamaki ya bashi yau Sabrine ce ajikinshi , ganin yadda take shasshekar kuka a kirjinsa , hakan yasa hannu yad'an shafa Mata baya yakai fuskarsa daidai kunnenta yace“i'm so sorry sweetheart stop crying okay, Kar mutane suzo huce wa suga nasa matata kuka, ”hannu Sabrine tasa ta d'an Mari fuskarsa irin marinnann na meyasa zakai min haka d'innan,
Bata da niyyar tashi daga jikin Adnan shikuma jiyayi gaba d'aya yanayin sa Yana neman canjawa Dan shi namiji ne ga kuma yadda yajejin soyayyar Sabrine aransa, gashi tazo ta rungumeshi sosai , Yana iyajin breast d'in ta a kirjinta , jiyayi Yana neman shiga wani hali hakan yasa ya d'ago Sabrine daga jikinta Yana goge Mata hawayenta had'e da fad'in “kidena zubarmin da hawayennan me daraja darling”sannan yaja hannunta har gurin daya ajiye motarsa yakaita ya bud'e bayan motar tashiga sannan ya rufe ya zagaya shima ya shiga, yanda yaji kamshin Sabrine ya cika motar hakan yasa yaji yama kasa magana , Amma haka ya daure ya ri'ke hannun Sabrine yana kallonta “baby meya faru why are you crying”cikin rashin wayo Sabrine ta turo baki cikin shagwaba tace“bakai bane ka kashe wayarka Ina ta kiranka a kashe and Latipha says wai kadena Sona ne”murmushi yayi Dan Yama huce murmushi saidai ace dariya, jin Yana dariya Sabrine ta kwace hannunta had'e da fad'in “dariya kakemin so Latipha was right kadena Sona ko”tayi maganar kamar zata Kara saban kuka, cikin dariya Adnan yace“no,no injiwa ye karya take min indai ana so nacireki araina na saidai Inna mutu ne kawai ”
Batasan lokacin data dafa hannun Adnan ma tace“you still love me ? ” kamar Wanda zai Mata kiss a kumatu yace“ forever and ever Mrs Adnan”ahankali tace thanks darling, sannan tace“remain two mouth zanyi graduation”

Ri'ke hannunta Adnan yace “really you mean Nan da four months zamui sure Sabrine and have a kids”tana niyyar magana wayar Adnan tafara ringing ganin ansa sweet mom yasa kafin ya d'aga yacewa Sabrine one minute, d'aga masa Sabrine Tai sannan ya d'aga wayar had'e da fad'in “hello”

Hankalin hajiya saleemeh a tashe tace,“adnan where are you , daddyn ka ba lafiya please kazo gida yanzu”

“what Dad meya sameshi”a rude hajiya saleemeh tace“i don't know Amma kaga kirjinsa yaketa rikewa Adnan pls come home soon kaji”dasauri Adnan yace“okay I'm on my way home”duban Sabrine yayi yace“baby I have to go Dad bashi da lafiya”kirjin Sabrine Saida ya buga tace“meya sameshi ”

“i don't know”yabata amsa Yana bud'e kofar motar sannan ya zagayo ya bud'ewa Sabrine ta fito , gaba d'aya ya rude yace“baby I will come see you tomorrow take care kinji”daga masa Kai Sabrine Tai , tana gurin har Adnan yaja mota yabar gurin sannan tajuya ta tafi

Bazai iya fad'in wane gudu yayi ba , Allah ne kawai ya kawoshi gida Yana zuwa yayi wani mugun horn, get man d'in ya Bud'e get da sauri ko daidaita parking Adnan begama ba ya fito a rud'e yayi cikin gidan bezarce ko Ina ba har section d'in LEC A. M Yana shiga ya tarar da Dad d'innasa hajiya saleemeh na ri'ke da kirjinsa sai jujjuya Kai , kawai yake……


*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_

3️⃣0️⃣

Arikice Adnan yakai kan dad da bama ya cikin hayyacinsa Banda ri'ke kirjinsa babu abinda yake , da temakon hajiya saleemeh suka fito dashi suka sashi a motar Adnan bejira ma hajiya saleemeh ta koma ta d'auko gyalenta ba kawai yaja motar da mugun guda dama tuni megadi ya bud'e get
Hajiya saleemeh na fito ta tarar Adnan ma har yayi nisa hakan yasa ita tashiga motar ta ta bishi
Tana zuwa asibitin har anshiga dashi emergency room babu damar da zaabarta tashiga hakan yasa ta Sami guri ta zauna tana share hawaye
Nurses d'in dakyar suka lallaba hajiya saleemeh suka kaita wani room na guest Dan har meeting sometimes sunayi agun saboda Yana da kyau da tsaruwa sosai

Cikin mintuna da basufi goma ba Adnan ya shawo kan Daddy cikin kwarewa da basirar da Allah ya bashi
Fitowa akai dashi from emergency room aka kaishi wani daki Wanda zai huta anan Amma yasamu bacci sai sauke numfashi yake ahankali irin na me bacci , sannan Adnan ya umarce nurses d'in da su tafi aikinsu yarage dagashi sai Daddy d'in, karewa daddynsa kallon yayi yanda ya rame sosai jiyayi hawaye sun taru a idon Adnan haka ya dora kansa akirjin LEC A. M yasaki wani kasalkan kuka Mara sauti Yana fad'in yana fad'in “hakika daddy bancika d'a na gari ba , tabbas Ina neman sa rayuwarka a hadari dalilin soyayyar Sabrine, Dan Allah ka yafemin, wallahi daddy indai nace Zan rabu da Sabrine tabbas halin da zanshiga saiyafi naka muni”ya Kara sakin kuka sosai me ta'ba zuciyar, hajiya saleemeh da tun shigowar ta tana tsaye tanajin me Adnan yake fad'a jitai itama zuciyarta ta karaya hawaye yashiga zubo Mata , tausayin mijinta yakamata , hakika tanason LEC A. M kuma dukkan wani abu da yafaru harta aikata adalilin soyayyar LEC A. M, ahankali ta furta “astagfirullah Allah ka yafemin”jin Kamar anyi magana yasa Adnan saurin d'agowa Yana kallan bayansa ganin hajiya saleemeh ce yasashi tashi zuwa inda take had'e da fad'in “mommy see daddy's condition , mommy Taya Zan kubutar dashi wallahi nasan dalilin San Sabrine ne yasashi a wannan halin ” dafo shi hajiya saleemeh tayi tare da fad'in “ba laifinka bane Adnan hakika jarrabawa daga Allah , Allah ya bamu ikon cinyewa shikuma Allah ya bashi lafiya” sosai hajiya saleemeh ta lallashi Adnan ita kanta jikinta gaba d'aya yayi sanyi kada dalilin hanashi auran yarinyar Nan yarasa ransa

Har kusan Sha d'aya na dare Adnan yakai a asibitin soyake daddyn ya farka a idonsa Amma saboda allaurar da yayi masa ta bacci yasan sai zuwa safiya Dole zai farka , hakan yasa hajiya saleemeh tilastawa Adnan ya tafi gida ya kwanta saboda kannansa ita zata kwana dashi, badan ransa yaso ba haka yatafi cikin zullumi
Daka deeja har Afiya basui bacci ma suna jiran shigowar su mommy din ganin Adnan shi kad'ai yasa deeja saurin sakin kuka tana rungume Adnan tace“yaya Ina daddyn yake Allah yasa be mutuba zai dawo gida”murmushi sosai Adnan yayi Dan deeja Sam Bata da wayo girman jiki ne kawai Allah ya Basu
Sosai Adnan ya lallaba kannenasa har daki ya raka su Saida suka kwanta sannan ya jawo musu dakin had'e da kashe musu wuta zuwa ta bacci

Yana zuwa dakinsa ya samu yasa ruwa me zafi yayi wanka , yunwa yakeji Amma Sam damuwa bazata barshi yaci abincin ba haka ya gabatar da sallar isha'i sannan yayi lafila ya mikawa Allah kukansa akan ya kawo musu mafita

Yana Nan daddumar wayarsa ta d'au ringing haka ya tashi ya d'auko , ganin Sabrine ce yasa yazame ya zauna a bakin gadon had'e da kishingid'a cikin sanyin murya ya d'aga wayar had'e da fad'in “hello my”
Jin yanayin muryarsa ta tabbatarwa da kansa ha'ki'ka akwai damuwa Dan wallahi ko bacci ta kasa Yi , jin tayi shiru batace komi ba yasa ta sauke numfashi had'e fad'in “meyasa baki bacci ba”kamar zatai kuka tace“baccin yaki zuwa ne Yaya jikin daddyn? Yasamu lafiya ? ” gyara kwanciyar sa yayi sannan yace“daddy Yana can hospital tare da mommy bedai farfado ba sai zuwa da safe inshallah”da sauri Sabrine tace“meya sameshi hakan dama bashi da lafiya”rasama me zecemata yayi jin yadda tayi tambayar, ganin bece komi ta'kara fad'in “meyake damunsa kamin shiru”cikin sanyin jiki yace“sabrine abinda yake damun daddy babba ne just pray for him”jinjina Kai tayi sannan tace“tom Allah yabashi lafiya inshallah zanzo gobe na dubashi kaji , Dan Allah tell me something kaci abinci? ”

Bayaso yamata karya hakan yasa “no banci ba , I don't want to eat Sabrine saidai koda safe”


“dan Allah kasamu kaci wani abu kaji inshallah zai Sami lafiya”jinjina Kai yayi sannan yace“dont worry I will eat my love yanzu dai ki kwanta mayi magana da safe kinji”

“okay”was abinda Sabrine tace sannan ta d'ora da fad'in “gud night”

“okay night baby”yafad'a Yana ajiye wayar, jiyayi yad'an samu kuzari hakan yasa ya Mi'ke ya bud'e fridge ya d'auko hollandia me sanyi sannan ya dawo ya zauna ya Sha sosai kuwa kafin ya kwanta cike da tunani kalala and most of the tunanin akan condition d'in Daddy ne da Sabrine


Washe gari da wurwuri Adnan ya tashi ya shirya cikin shadda black me kyau yayi masifar kyau yasha hula Kamar me Shirin zuwa daurin aure , Saida ya leka su Afiya ya tarar suna breakfast haka suka takura Masa saida yaci Irish poteto da Afiya ta soya musu da black tea sai soyayyan kwai Saida yaci sosai Dan shi kanshi besan Yana jin yunwa ba Saida yafara ci , sukace zasu bishi yace su Bari tukunna badan ransu ba haka yahau mota zuwa asibitin

Yana shiga asibitin direct dakin da Dad d'in yake ya nufa , hajiya saleemeh na zaune gaban daddy a kujera da alama ko cikakken bacci batai sosai ba
Kuma still da alama be farka ba har lokacin , ahaka yashiga ya Sami mommyn tasa , tana ganinsa tayi saurin tashi tana share hawaye had'e da fad'in “Adnan ka gani daddynka har yanzu be farka ba Kar muje ya mutu wayyo Allah na” ta fad'a tana toshe baki jin yadda sabon kuka ya taho Mata, zaunar da ita Adnan yayi sannan yace“mommy he is fine inshallah allurar ce me nauyi Amma inshallah am here zai farka kinji”yana fad'ar haka yad'au wayar sa yakira had'e da bada umarnin akawo Masa wata allura aikam cikin mintuna da baifi miyu ba wata nurse ta kawo masa Yana karba ya had'a yayi daddyn sannan ya umarci nurse d'in data koma bakin aiki shima ya nemi guri ya zauna Yana Kiran farkawar daddyn Dan allurar da yayi masa zata karya wacce allurar da yayi masa ta bacci

Ganin daddyn ya d'an motsa hannunsa yasa daga Adnan har mommy saurin karasawa gun bed d'in nasa , aikam ahankali ya bud'e idonsa tun Yana ganinsu dishi dishi har ya dawo ganinsu radau sannan yad'an lumshe ido had'e da fad'in “lailahaillah Muhammadur rasulillah ”dukkansu suka Amsa da (S. A. W) Kara
Bud'e idonsa yayi ya d'ora akan Adnan , ganin hakan yasa yace“sorry that Yaya kakeji yanzu meke damunka yanzu daddy”wani kasalallan murmushi yayi cikin murya da Bata fita sosai

Yace“kafi kowa sanin abun da ke damuna Adnan ni ba asibtine ya dace Dani ba ”yayi maganar had'e da Kara lumshe idon da , hajiya saleemeh ce tace“baban Yara Dan Allah ka kwantar da hankalinka kome zaiyi daidai inshallah kaji” daidai lokacin Sabrine ta turo kofar had'e da sallama ita da Latipha , LEC A. M najin muryarta yayi saurin bud'e idonsa had'e da fad'in “fatima …Fatima ce” jin abinda daddyn da kefad'a yasa Adnan saurin juyawa , ganin Sabrine ita da Latipha yasashi kara juyawa ya kalli daddyn nasa jin yakira wani suna daban Wanda ba na Sabrine ba hakan yasa shi fad'in “daddy wace kuma Fatima daka Kira yanzu”murmushi LEC A. M yayi yace“itace dalilin son Sabrine azuciyarta hakika inason ganin Fatima bani da wani buri arayuwa illa na ganta , hakika ni bansan komai ga rashin Fatima ba bazance ga abinda ya faruba Adnan yanzu game da Fatima ko Ina zan ganta”yama kasa gane inda maganar baban nasa ya dosa hakan yasa ya juya ya dubi hajiya saleemeh dagaba d'aya ta hade Rai ganin su Sabrine sannan yace“mommy me daddy yake fad'a ne ko kingane maganarsa”da sauri ta furta“ Adnan ka kyale daddyn ka inaga Yana cikin rashin lafiya ne”da mamaki ya dubi hajiya saleemeh yace“taya zakice haka saleemeh Taya zakice Ina cikin rashin lafiya Fatima dince baki sani ba to wai ma tana ina” gaba d'aya tsoro ne ya kamata , shiru tayi masa batace komi ba ta dubi su Sabrine da tun shigowarsu tana tsaye tana jin meke faruwa sannan ta dubi Adnan tace“adnan suwaye wadannan” juyawa yayi gunda Sabrine ke tsaye itama d'in kallansa take Latipha fa samun guri tayi ta zauna dama , karasa inda Sabrine ke tsaye Adnan yayi sannan ya dubi mommyn tasa had'e da fad'in “sabrine ce mommy tazo duba daddy ne ”dasauri Sabrine ta tsuguna tace “mommy Ina kwana ya mejiki” magana ciki ciki hajiya saleemeh ta amsa ganin hakan itakam Latipha taji haushi batare da ta durkusa ba daga inda take ta gaishe da mommyn itama ciki ciki ta amsa Mata, sannan Adnan yacewa Sabrine ta karaso ta gaida daddyn, gabanta sai fad'uwa yake
takarasa gun daddyn sannan ta zauna kan kujerar dake gaban gadon nasa tace“daddy Ina kwana ya jiki kuma ”da murmushi sosai a fuskarsa Dan yaji dadin ganin Sabrine jiyayi kamar an d'auke Masa ciwon dake damunsa yacewa Sabrine “lafiya qalau Sabrine ya karatun”

“alhamdulillah daddy”kara murmushi yayi sannan yace“kada adinga Wasa kinji saura wata biyu azama graduate”kasa da kanta tayi tace“inshaallah daddy Allah ya baka lafiya”latipha ce ta karaso ta gaisheshi tayi masa Yaya jiki ya amsa sannan Sabrine ta Mi'ke tace“mommy muzamu tafi Allah ya Kara sauki”banda idon Sabrine bakan mommyn yake da bazakai tunani ma ta amsa ba Dan maganar Tata iya baki ta tsaya

Itakam Latipha kobi ta kanta Bata karayi ba Dan ta Bata haushi, shikanshi Adnan beji dad'in abin da mommyn tayi ba , suna niyyar fita ne alhaji Hassan da matar sa suka turo kofa da sallama , idon Alhaji Hassan ne ya sauka akan Sabrine dake niyyar fita, ko kiftawa ya kasayi saboda kallan yarinyar harta fita Yana waigenta har haushi matarsa taji Amma Bata nuna ko a fuskaba suka karasa har cikin dakin sukuma suka fita Adnan ya rufa musu baya Dan raka su.


*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


3️⃣1️⃣

_babyluv_✍🏻
_07038524543_

Alhaji Hassan na karasawa dakin kujera yasamu kusa da gadon LEC A. M yazauna ita matar tasa ta zauna hajiya saleemeh mace ta durkusa ta gaida alhaji Hassan ya amsa sannan suka gaisa da matar tasa
Juyawa yayi ya kalli kannin nasa had'e da fad'in “ abdurrashid sannu yajikin meke damunka haka lokaci d'aya kayi wannan ramar”
“dasauki”shine kawai abinda ya fito daga bakin LEC A. M Dan har lokacin kirjinsa na Masa ciwo , hakanne yasa alhaji Hassan duban hajiya saleemeh had'e da fad'in “hajiya meke damun Abdurrashid haka ”tabe baki tayi had'e da fad'in “wallahi maganar Nan ce dai alhaji baban Yara yaki jin magana akan yacire yarinyar Nan aransa Amma yaki har Saida ya kwanta cuta”jinjina Kai alhaji Hassan yayi sannan yace“wai Niko wannan yarinyar data fita wace Kar dai itace wacce Abdurrashid da Adnan keso” Kara ke'be baki hajiya saleemeh tayi tace“wallahi fa itace kaganta Kamar mayya harda biyo shi asibiti”mikewa Alhaji Hassan yayi without saying anything yayi waje daga matarsa har hajiya saleemeh binsa sukai da kallo Dan bece ga inda zashi ba, Yana fita awaje suka had'u da Adnan zai dawo cikin dakin , ganin alhaji Hassan ya fito hakan yasa Adnan fad'in “baba badai ka fito ba”girgids Masa Kai yayi yana Dan duban inda Adnan d'in yataho sannan yace“ Adnan Ina yarinyar Nan danaga kun fita”juyawa Adnan d'in Yana kallan inda Alhaji Hassan ke kallo kafin ya juyo yace“sabrine ai sun tafi ”fuskar sa ce ta nuna alamar beji dad'in hakan ba, ganin hakan Adnan yace“lafiya dai ko baba”girgida Kai yayi yace“lafiya qalau nikam Adnan in tambayeka yarinyar Nan Yar Ina ce”murmushi Adnan yayi yace“ Yar Kaduna ce daddy iyayenta anan suke”

“kaduna” alhaji. Hassan ya maimaita, dasauri Adnan yace“ eh daddy”
Kara girgida Kai yayi sannan yace“okay yanzu yimin bayani meke damun mahaifinka haka”
Yanayin fuskar Adnan ce ta sauya sosai kafin yacewa Alhaji Hassan “baba mu zauna ga guri”wasu kujerune suka zauna sannan cike da damuwa Adnan ya fara magana

“wallahi baba , daddy naneman sa rayuwar sa ahadari duba da yanda yake sa Abu aransa Wanda hakan Sam bedace da lafiyar sa ba ”sannan yayi shiru , kafin ya. D'ora da“ahalin yanzu hawan jini ne Amma duk bawannnan matsalar bace damuwar , yanayin yadda Daddy ke sa kansa adamuwa hakan naneman samasa ciwon zuciya idan har zai Kai kwana ishirin da wannan damuwar aransa ”

“ innalillahi wainna ilaihirrajuun”was abinda alhaji Hassan yace Yana jinjina Kai , kafin ya dubi Adnan cikin magana mecike da lallashi yace“adnan abinda Zan fad'a maka ayanzu kad'auke shi matsayin nasiha , hakika arayuwa 'ya'ya babu abinda bazasu iya sadaukarwa da iyayensu ba domin Basu da Wanda ya fisu , Adnan hakika yanzu rayuwar mahaifinka Zan iya ta'alla'ka a hannunka Kaine me yanke hukunci ayanzu kaida kanka kafad'a idan har mahaifinka yacigaba da sa Abu aransa zai iya kamuwa da ciwon zuciya , yanzu Kaine me yanke hukunci, wannan yarinyar da ake magana akanta bakasan dalilin soyayyar ta agun mahaifinka ba domin kasan Shiba yaro ne ba yakumasan abinda yake inaso kazauna Kai tunani”yana gama fad'ar hakan ya tashi ya koma gurin LEC A . M

Gaba d'aya Adnan rasa me zaiyi yayi, hakan yasa ya tashi ya koma office d'insa Yama kulle kansa, gaba d'aya abinda alhaji Hassan ya fad'a masa ke dawo Masa cikin zuciya , tabbas abinda ya fad'a gaskiya hakika yanzu shiyakamata ya yanke hukunci akan lafiyar daddyn sa , meya kamata yayi shidai yasan Yana son Sabrine haka kazalika yanason daddyn tabbas Yana cikin rudani hakika yanayin dayake ciki me wuyar yanke hukunci ne

Wata zuciyar ce ta fara masa nasiha kan cewa da lafiyar da data Daddy ba d'aya bace saboda da shekarunsa Dana daddy akwai banbanci abinda zai iya d'auka tabbas shi daddy bazai iya d'auka ba

Har kusan karfe biyu na Rana Yana cikin office Dan sallah ma a office yayita
Yana zaune ne wayarsa ta d'au ringing ganin mahaifiyarsa yasa ya d'aga wayar
“Adnan kaga mahaifinka nasake ri'ke kirjinsa pls come”da sauri ya Mi'ke had'e da d'aukan wayarsa Yana zuwa ya tarar da daddynsa na juye juye holding his chest ,beko saurari kowa ba ya bud'e wata drawer ya zaro wata allura yayi masa sannan ya fara Dan dannan Masa kirjinsa ,cikin hali na ciwo daddyn ya fara magana kamar haka“adnan yanzu haka zaka bar mahaifinka baka tausayin halin danake ciki ,kadenamin allura kadena bani magani Adnan kawai ka kyaleni”hawaye ne ya fara zubowa Adnan yanajin maganar mahaifinsa har cikin Zuciyarsa ,
“daddy I'm sorry inshallah komi yazo karshe kaji ”ahaka bacci yad'au keshi holding adnan's hand ,
Juyowa Adnan yayi ya dubi hajiya saleemeh tare da fad'in “mommy inshallah komi yazo karshe”sannan ya juya ya fita had'e da fad'in “Ina zuwa ”


Motar sa ya d'auka ya nufi school d'in su Sabrine Dan koshi dayake likita condition d'in daddy yafara bashi tsoro sosai
Kusan karfe hudu ya isa school d'in lokacin fitowar su Sabrine kenan daga meeting holl Dan sun fara shirye shiryen graduation

Ganin motar Adnan a kofar hostel d'insu tayi mamaki sosai Kamar yasan tunaninsa take,Yana cikin mota be fito ba ,jin an kwankwasa Masa glass d'in mota yasashi kallon Sabrine Dan niyar kiranta yake awaya dama
Da hannu yayi Mata nuni kan tashigo motar ,yanayinsa ta gani Sam ba daidai ba hakan yasa ba musu ta zagaya tashiga motar ta zauna had'e da kallon tace

“what happened ? Lafiya dai ko Yaya jikin daddy”duka kallonsa take Tai Masa tambayar, numfashi Adnan ya sauke kafin ya dubi Sabrine yace“jikin daddy da sauki and abinda Yama kawoni kenan Sabrine”

“okay inaji fadamin”gyara zama Adnan yayi yace“abinda nakeso na fad'a Miki Sabrine banaso kiji aranki cewar banasonki wallahi bahaka bane I love you so much Amma condition d'in dad ayanzu yasa gaba d'aya zuciyata ta kamu da tsoro da kuma fargaba”ganin Kamar idon Adnan naneman zubar da kwalla yasa Sabrine cikin 'kaguwa taji mezai fad'a Mata hakan yasa tace“dan Allah kamin bayani yadda Zan fahimta meke faruwa don't tell me Dad yarasune”
Girgida Kai yayi had'e fad'in “ ko d'aya daddy is still alive Amma condition d'insa is very critical Sabrine” cikin razana Sabrine ta dafe kirji tace“ innalillahi wainna ilaihirrajuun wai meke damun daddy haka why not a fitar dashi waje adubashi”
Murmushi Adnan yayi irin me ciwo d'innan yace“sabrine kenan fitar da daddy waje bashine solution ba domin a 'kasar wajan ba zata yiwu nida nakenan akirani na dubashi Dan yanzune na bijire nakeson 'kasata ta amfana Dani Amma ada kafin kafinna dawo Nigeria acan nake aiki, Amma ayanzu medicine ko wani abun asibiti bazaisa daddy samun lafiya”cikin rashin fahimta tace“to mene zaisa daddy samun lafiya kenan”

Cikin rawar baki da murya Adnan “sabrine is you, kece kad'ai zakisa daddy samun lafiya ayanzu all what Daddy needs now is you if not wallahi munaji Muna gani daddy zai bar duniya Sabrine because of your love”

Dafe kirji Sabrine Tai had'e da zaro ido tare da fad'in “ni kuma Adnan…I mean Taya haka zai faru you know how much I love you Taya zakace haka”hawayen da Adnan ke boyewa Dan Sam bayason zubar hawaye gun namiji gani yake tamkar ragontaka ne Amma sai ayanzu ya fuskanci cewa wani zubar da hawayen shine samun sassauci a zuciya
Riko hannunta Adnan yayi tare da fad'in “meze hanashi yiwuwa Sabrine she is my…”kuka ne yaci karfinsa Yama kasa magana, gaba d'aya jikin Sabrine rawa yake tagaza gane abinda Adnan d'in keson Fad'i
Daurewa yayi ya d'ora da fad'in “ Sabrine daddy means a lot to me , idan har banbawa daddy abinda yakeso ba hakika bancika d'a nagari ba hakika ni mezuwa ko Ina ne na nemo Masa farin ciki Taya kuma farin cikinsa na hannuna naki bashi”hawaye ne sosai ke zubowa Sabrine ta kar'bi hannunta cikin na Adnan tace“no Adnan Dan Allah kada kasa zuciyata bugawa , kada kasa nayi abunda kaima kasan bazan iya ba ”kara ri'ko hannunta Adnan yayi “sabrine bantaba rokarki wani abuba Amma ayau gani nida mahaifina Ina neman temakonki kiceci rayuwarsa inaso ki amince ki auri daddy na not me Dan Allah sabrine kada kice a'a Dan Allah”

Kallonsa kawai take Dan wallahi Allah ma yasani bazata iya son wani inba Adnan ba hakan yasa tace“ Adnan I love you akanme zaka bani abinda bazan iya ba”
Dasauri yace“becouse of my love nakeson kiyi wannan sacrifice d'in Dan Allah sabrine kada akanki narasa mahaifina” toshe kunnanta Sabrine tayi tana rintse idonta jitai ma bazata iya tsayawa taji ba kawai ta bud'e kofar motar ta fice da gudu

Dafe kansa yayi hawayen dayake dannewa suka zubo Masa haka yaja motar sa yabar school d'in da rokon Allah yasa Sabrine ta abince da bukatar sa

Ahaka ya koma asibtin ya tarar lokacin dad d'in na zaune mommy na fama kan yaci abincin Amma ya kasa ,
Da hannu Adnan yayi Mata nuni kanta bashi abinci , tashi tayi ta bashi sannan ta fita daka dakin gaba d'aya

Zama Adnan yayi sannan ya ajiye fatan doyar a gaban daddy sannan yad'an 'ka'kalo murmushi sannan yace“dad promise me zakaci abincinnan saboda Zan baka wani latest story akan Sabrine”da sauri LEC A. M ya d'ago ya kalli Adnan yanaso ya tabbatar da abinda yake fad'a

Please Login or Register in order to submit comment