Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

life babu wata yarinya da zuciyata taji tanaso sai ita pls mom”yakarasa maganar Yana d'ago da kansa daga kwanciyar da yayi Yana ri'ke Mata hannun, fuskarsa hajiya saleemeh ta shafa tana fad'in “yimin bayani meke faruwa wacece ita yimin bayani yadda zan fahimta”

“mommy Sabrine I love her nayi tunanin Inna fad'awa daddy zaiyi farin ciki kasancewar she's one of his students and suna da good relationship between Dad ,he even told me iyayan yarinyar suka bashi amanarta and now Mom nace inason ta but can you imagine abinda dad yace”

Girgida Kai hajiya saleemeh tayi tace“mene shi baban naka yace”dasaurin Adnan ya marairaice Kamar zai kuka yace“mommy yace ban Isa na aureta ba yace karma na fara tunanin aurenta mommy nikuma I love her sosai mom please”

Cike da mamaki sosai tace“shi alhajinne yace bazaka sota ba to akan me ka tabbatar kuma yarinyar mutuniyar kirkice,Taya alhaji zaice haka shida kullum yake fad'a akan ka'ki fito da Mata yanzu kuma yace haka , definitely there's something fishy tabbas akwai wani abu ”tayi maganar had'e da jinjina kai

“mommy wallahi I'm very sure yarinyar kirki ce and inma bahaka ba dad yayi bincike ya tabbatar indai har ansameta da hali Mara kyau to ni nayarda zan hakura dan ita for sure”
Cike da lallashi tace “kaga is okay now I will talk to him kaji inaga kunsami misunderstanding ne Amma yanzu promise me zaka kwanta nikuma zanyi wa alhaji magana and insha Allah nasan zai amince and now sleep kaji”tayi ganar tana tashi tsaye tana masa nuni da ya kwanta ,sai asannan Zuciyarsa tayi sanyi Babu musu ya kwanta ita kuma taja masa blanket ta lullube shi sosai sannan ta kashe masa wutar gaba d'aya ta jawo masa d'akin zuciyar ta fal tunanin wace yarinyace haka har Adnan ya makance a soyayyar ta ,da wannan tunanin har ta Kai section d'in alhaji ta tarar har ya kwanta ,batako saurareshi ba ta kwanta kwai da tunani kala kala aranta ciki harda abunda suka faru wasu shekaru dasuka gabata


Shikuwa Adnan jiyayi bazai iya jiran komi ba yasa hajiya saleemeh nafita kawai ya jawo wayarsa yashiga bangaren Kira yayi dialing number d'in Sabrine aikuwa babu dad'ewa tafara ringing Amma cullertone ne ajiki instead of normal ringing , wata romantic song ne ajiki ta jonnydrill 'kara lumshe ido yayi Yana Kara Danna wayar kunnansa burinsa kwai tai picking call d'in

Sabrine jitai gaba d'aya bacci ya kauracewar idanunta tarasa meyake damunta gashi kusan karfe shabiyu na dare Amma ko alamar bacci babu a idonta , da tayi tunanin ko rashin Granny ne hakan yasa ta kirata tun d'azu sukai waya sosai Amma gashi still kuma Babu abinda ya canja gaba d'aya abinda Latipha ta fad'a Mata bayin dawowar akan Adnan da LEC A. M kemata yawo azuciya duk da tasan cewar LEC A. M ba wani sonta yake ba Amma batasan meyasa abinda Latipha ta fad'a Mata kemata yawo azuciya ba
Da wannan tunanin taji wayarta na rigging , da Bata ko kalli wayar ba Amma saitai tunanin who will call her awannan Daren , sai kawai ta zaro wayar ta ta, ganin ansa Adnan hakan yasa ta d'an bud'e ido alamar mamaki badai wannan likitan bane Yama akai number d'insa tashiga wayarta harda rubuta Adnan,har wayarta tsinke tana kallon sunan ,ahaka wani Kiran yasake shigowa ,kawai saita d'aga ta kara wayar akunne Batare da tayi magana ba kawai tai shiru
Jin ta d'aga wayar batace komai ba har minti d'aya yacika Batare da tayi magana ba sannan kuma Bata yanke wayar ba yasa kawai yayi murmushi sannan ahankali yafurta“sabrine meyasa kike da sonkanki ne dayawa muryar dazaki danyi magana naji dadi shine kikemin bakin cikin hakan ,why Sabrine why please,kinganni fa ko baccin na kasa I'm here only thinking about you ko rufe ido nayi only your face please Sabrine say something to this soul that love you alot pls”yakai karshan maganar dawata shegiyar murya dasaida Sabrine taji wani yarrrrrr ajikinta
Bata ko motsa ba balle tayi tunanin yimasa magana , Dan shiru tayi Bata cemasa komi ba Dan this is the first dawani d'a namiji yayi mata da wannan romantic voice d'in shiyasa kawai taji Tama rasa mezatace masa, ganin Bata da niyar ko yin magana yasa Adnan cikin slow voice irin na Wanda yagama zurmawa a soyayya yace“okay bazaki magana ba kenan ko Sabrine is okay Amma ki shirya ganina gobe Dan dole wallahi saina ganki ni dazaki yadda ma wallahi I will come see right now kinji pls”dasauri Sabine ta kashe wayar tayi wani mugun cusa kanta a pillow Dan wannan mutumin nema yake ya shallakewa tunaninta
Shikam Adnan jin wayar ta yanke yasa kawai yayi murmushi sannan yace “bakyagane wannan yaren Amma kishiryawa yaren dazan fara koyamiki silly girl”yakai karshan maganar had'e da ajiye wayar sannan yayi adduar bacci had'e da lumshe ido , shikanshi besan lokacin da bacci yayi awan gaba dashi ba cike da mafarkin burin rayuwar sa……


*Share and share again habibties😍*

*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


1️⃣7️⃣


Tunda Adnan yafice daga office d'in kansa yake wani bala'in sarawa had'e da juyawa at the same time , driving yake Amma Allah ne kawai yasan halin dayake ciki , gaban wani tamfatsetsen gida ya tsaya a nasarawa G. R. A unguwar tayi shiru kasan cewar unguwar manyan mutane ce , yanayin horn me gadi yazo ya bud'e masa cikin girmamawa dakuma mamakin ganin Adnan Dan sai lokaci zuwa lokaci yakan le'ka wannan gidan , Amma befasa biyan me gadi kud'in sa ba Dan iya shi kawai yake rayuwa cikin gidan, shiyake goge komi nagidan Yakuma gyara komi na gidan babu ko alamar da zai tabbatar ma babu mutane agidan indai akan shara da goge komi ne
Me gadin na gaisheshi Amma be tsaya amsawa ba sa'banin yadda yake zuwa da saiya tsaya ma suyi Hira sosai, ganin yanayin da yake ciki yasa me gadin rufe gate d'in sannan yazo da sauri ya bud'e masa 'kofar motar , cikin juriya da ciwan kan dayake ji yafito ahankali batare dayacewa megadin komi ba illa mi'ka masa key d'in motar da kawai yayi alamar ya rufe motar , kar'ba yayi sannan ya juya da sauri yaje ya bud'e masa 'kofar Kamar yadda yake masa ko yaushe in yazo, d'aga masa hannu Adnan yayi ahankali alamar ya gode , sannan gently yasa kansa cikin 'kayataccen tangamemen parlor d'in , betsaya a Nan ba , kasancewar da 'kofofin d'akuna da ban da ban daya zagaye parlor d'in ciki harda d'akin motsa jiki, direct dakin ya nufa , ga mashinan motsa jiki Nan kala kala

Ahankali ya shiga Yana karewa d'akin kallo thinking of what to do, ahankali ayafara tafiya daidai running machine ya tsaya , kasan cewar kananan Kaya ne ajikinsa and ga weather d'in very Cool , yanayin yafara juyawa na sanyi , unisex trouser ne ajikinsa baki mekyau da tsadar gaske sai sai Small Riga v-neck shirt wadda ta fito masa da faffad'an kirjin sa, dama ayadda Adnan ya shirya direct ganin Sabrine zaije Amma zuciyar kawai ta Umarce shida yaje yabama daddy hakurin akan abinda yafaru yesterday , lokacin dayakai bakin office d'in LEC A. M Kuwa sai aka kirashi shine dalilin dayasa ya tsaya akofar kasancewar yayi picking call yasa ya tsaya Yana waya , tun hankalinsa baya kan abinda dad d'in kecewa har ya zamto yama kashe wayar gaba d'aya Yana sauraron abinda dad d'in kecewa , da farko beson Sabrine yake fad'a wa ba sai a karshan maganarsa ne dayaji ya ambato Sabrine yasashi shiga office d'in da saurin dashi kanshi besan cewa ya shiga ba


Abubuwan da suka farune suka shiga dawo Adnan kansa , gaba d'aya jin abin yake tamkar a mafarki , taya Dad zai masa haka ? Taya zaiso abinda Zuciyar d'ansa keso, Taya zai d'auko abinda zai iya tarwatsa farin cikin family d'insa, meyasa Dad zai haka haka
“why dad , why ,”
Yayi maganar da karfin gaske Yana dukan wani hand machine bakaramin zafi yaji ba Amma zafin dayakeji azuciyar sa ya ninka wannan sau dubu
Haka Adnan ya haukan running machine dinnan yashiga Yi da dukkan karfin , gaba d'aya ya 'kure number d'in tsabar gudun dayake gaba d'aya Yama wani fice a hayyacinsa , kasancewar gudun yayi masa yawa yasa machine d'in yayi wulli da Adnan gefe d'aya


Abangaren LEC A. M kuwa jiyayi kamar ya sauke wani nauyi Wanda yakasa saukewa Abaya, hakannan yaji shi cikin farin ciki, koda Sabrine Bata abince da soyayyarsa ba yariga yafad'i sirrin Zuciyarsa yariga ya sauke wani nauyi daya cika masa zuciya, cikin farin ciki ya nufi gidan sa da fatan Allah yasa Sabrine ta amince da abinda Zuciyarsa ke bukata gunta ,
Yadda hajiya saleemeh taga alhajin yanayin sa yasauya sa'banin 'Yan kwana kinnan da yake kasancewa cikin 'bacin rai dakuma tunani Amma yau ta ganshi cikin walwala har Yana janta da tsokana haka abin yayi bala'in yimata dadi , Dan idan akwai abunda ta tsana aduniya ayanzu shine taga matsala na neman bullowa cikin family d'inta, ranar har samin alhaji tayi ya kawo kansa gurinta ba Kamar yadda ta Saba ita ke zuwa gunsa ba……


Tun jiya Latipha ke tambayar Sabrine abinda ya faru taki fad'a Mata banda kuka Babu abinda take ,abin har ya fara bawa Latipha tsoro Dan zata iya cewa aduk zamanta da Sabrine babu abinda ya taba sata shiga hali irin wannan ,
“dan Allah sabrine kidaure ki breakfast d'innan Kinga jiya baki ci abinci ba kikai bacci Amma yanzu ma kice bakyaci ”

Kallonta kawai Sabrine take , azuciyarta tana fad'in, Ashe dama Latipha duk abinda kike fadamin gaskiya ne meyasa nakasa hango abinda kika hango min , meyasa saboda ni kawai zan tarwatsa farin cikin family guda,
Tana kaiwa karshan tunanin wani hawaye ya gangaro Mata a fuska,cikin fushi Latipha ta Mike zata bar inda take ,dasauri Sabrine ta riko hannun Latipha Dan tasan fushi tai ,dawowa Latipha Tayi ta zauna cikin matukar damuwa ta kalli Sabrine had'e da fad'in “to Sabrine ba gwara na tafi na barki ba tunda bankai matsayin da zaki fad'an damuwar ki ba,Ashe yadda na d'aukeki ba haka kika d'aukeni ba ,nikam nagaji zan Kira Granny right now nafad'a Mata halin dakike ciki kinki sanar dani abinda ke faruwa”takai karshan maganar tana jawo wayar Sabrine,da sauri ta ri'ke hannunta tana hararar Latipha tare da fad'in “kindai San zaki iya ganin Granny ta taso driver yanzu ko”
Buge hannunta Latipha tai “eh ai gwara tazo d'in tafi ganewa kanta”ganin yadda Latipha ta damu da ita sosai yasa ta 'ka'karo murmushi sannan ta kar'bi indomie d'inda ta kawo Mata sannan tace“to gashi dai zanci basai anmin Muna furci ba ”harararta Latipha Tayi had'e da tashi tana fad'in “oho kedai kika sani”
Saida ta faracin indomie d'in sannan ta tabbatar tana jin yunwa Dan Saida taci da yawa sannan tayi wanka ta shirya cikin wani black less dayayi Mata kyau kasancewar ta fara , d'ankwali ta d'auko ta d'aura irin Daurinann ture kaga tsiya, tayi masifar yin kyau Kamar Yar tsana skirt d'in yayiwa hips d'inta kyau kasancewar yadda take da sharp Kamar cok sannan ta d'au mayafi golden color tasa ,
Abinda Sabrine ta barwa zuciyarta shine daga Adnan har LEC A. M bazata Kara barin wata kofa dazata sadasu da ita ba ,duk da azuciyarta bataso rabuwarsu da LEC A. M ta zama haka ba saboda yadda takejin sa azuciyarta tamkar mahaifi Amma kaico da Shima ba Kamar haka ya dauketa ba , datasan cewa abinda zuciyar keraya masa akanta kenan da tuntuni ta yanke alakar ta dashi, badan kasan cewar shi babba ba, hakannan zuciyarta bazata iya kasancewa dashi ba
Kallonta kawai latipha take Dan tana da tabbacin halinda tashiga jiya akan LEC A. M ne dakuma Adnan Amma ta barta ne kawai harsaita fad'a Mata da bakinta dan Sam duk yadda Latipha take da mutum indai be sakota a alamarinsa ba tabbas zata kalli abinne da ido koda tana da shawarar da zata bashi

Ahaka suka fito suka nufi lecture hall gwanin birgewa Dan a school d'in mutane dayawa naso susami kusan ci da Sabrine daga maza har zuwa Mata Amma ita Sam babu wannan a gabanta
Daidai sunzo zasu huce ta wurin wani parking space dake kusa da lecture hall d'insu hakannan taji gabanta yayi mugun fad'uwa Mara misaltuwa da harsai da taja ta tsaya amma kuma Sam ta kasa waigawa. Ganin yadda taja ta tsaya yasa Latipha juyowa tana kallonta ganin yadda tai kamar irin Mara gaskiya d'innan “and what happened again nasamu dakyar kin dawo daidai yanzu meye ya Kara faruwa kuma”tayi maganar tana d'an Waige waige to find wai me Sabrine d'in ta gani, wurin parking space idon Latipha ya sauka , Adnan ne ajingine a jikin wata shegiyar Mota me masifar kyau Fara , yasha shadda fara d'inki daidai da zamani ya murza hula ga watch na iPhone a hannun sa, Yana jingine jikin motar ya hard'e ka fafunsa hannunsa na rugume a kirjinsa tun fitowar su idonsa ya sauka akanta , Zuciyarsa nazafin abinda mahaifinsa yayi Taya zaiso abinda zuciyar d'ansa keso wannan ma ai rashin adalci ne, kwana yayi beyi bacci ba gawata masifaffiyar soyayyar Sabrine dake 'Kara bijiro masa azuciya , shi gaba d'aya ma kansa ya kulle yarasa meyaka Masa dad'i, jiyayi Sam bazai hakura ba Dole saiyazo yaga Sabrine ko Zuciyarsa zatai sanyi


Cike da mamaki Latipha ta Kara kallan inda yake tsaye sannan ta kalli Sabrine da gaba d'aya Bata juyaba Amma tabbas dasuka zo giftawa idonta yayi Mata gizo Kamar shine shiyasa ta tsaya batare da ta juya ba gakuma 'kafarta data ri'ke

Murmushi Latipha Tayi tana leka fuskar Sabrine tare da fad'in “dama shi kika gani kika tsaya kenan”saurin juyawa Sabrine tai beko motsaba Amma idonsa akanta yake Dan ko d'auke ido daka kanta bayaso yayi , yadda Sabrine taji idon Adnan cikin nata Saida kirjinta ya 'Dan buga, da sauri ta juya da nufin barin gurin daidai lokacin daya Mike ya nufo Su, saurin Shan gabanta Adnan yayi ganin hakan yasa Latipha ta kalli Sabrine sannan ta kalli Adnan tace“you guys need to talk” sannan ta kalli Sabrine tace“sabrine please , ”sannan ta juya ta bar gurin tana mamakin halin Sabrine akan me saurayi kamar wannan Yana binta tana guje masa

Kara matsawa Sabrine tai alamar zata bar gurin , shikam Adnan Sam beson irin wannan halin shiyasa kawai yajaa hannun Sabrine har gurin motarsa sannan ya bud'e motar Yana nuna Mata cikin motar alamar tashiga, zatai magana yayi saurin fad'in

“kodai kishiga da kanki ko wallahi zan d'auke ki nashigar dake mark my words”yayi maganar babu ko alamar Wasa a idonsa, ganin haka yasa Sabrine saurin juyawa taga yadda mutane ke zirga zirga gurin , tabbas in akaga ya ta'bata mutuncinta zai zube , yasa kawai Sabrine ta turo baki tare da shiga cikin motar , tana shiga ya rufo kofar sannan ya juya Shima yashiga sit d'in driving sannan ya rufe
Shiru yayi bece komi ba Dan seriously besan ya zai bullowa Al amarin ba, ya bud'e baki zai magana Amma ya kasa , hakan yasa kawai yayiwa motar key , cikin driving me cike da 'bacin rai ya bar cikin school d'in, direct hanyar gidansu yayi Dan yadda yakejin Zuciyarsa beki komi ya faru ba shiyasa kawai ya yanke hukunci ya kaiwa hajiya saleemeh ita ga daddy gashi , kome zai faru ya faru Dan inyacigaba da had'iyar wannan 'bacin Rai to tabbas Zuciyarsa zata iya bugawa,
Kallon sa Sabrine tai cike da tsoro da fargaba tace“ina zaka kaini, meyasa ka d'auko ni, wani abun zakai min ehe ni mene lefi na aciki, pls take me back to school”kamar zatai kuka take maganar, gaba d'aya Adnan bema saurareta ba kawai driving yake,
Suna zuwa kofar gidan yayi Horn cikin sauri megadi yazo ya bud'e kofar cike da girmamawa……

*Share and comments please and please*

*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


1️⃣8️⃣

*BABYLUV✍🏻*
*07038524543*


Hajiya saleemeh da alhaji na babban parlor Azaune, Afiya and deeja sunje gidan kanwar hajiya saleemeh , ita kanta hajiya saleemeh niyar fita take saboda yanzu akai Mata wayar kayan ta sunsu kasancewar yadda take business sosai
Duban LEC A. M tayi kafin tace“nikam alhaji Adnan fa be kwana a gida ba and I called him baayi answering wayar ba and nasan Adnan indai bazai kwana a gida ba saiya Min waya koda patience ne suka masa yawa a hospital Dole saiya kirani but look now nikam tsoro nake ji I hope he's fine”

Tana rufe baki baki Adnan yashigo parlor d'in hannunsa ri'ke Dana Sabrine Wanda ta rufe idonta da gyale da alama kuka take , ganin Adnan da yarinyar ri'ke da hannunta yasa daga hajiya saleemeh har LEC A. M saurin Mi'ke wa , har tsakiyar parlon Adnan yashigo da Sabrine duk da yadda take cijewa Amma hakan besa ya sake fa , tunda yashigo idonsa a mahaifin nasa , yadda idon Adnan yayi jajawur zai tabbatar ma da he's not in good condition
Har gabansa hajiya saleemeh taje tare da karbe hannun Sabrine daka hannun Adnan tana fad'in “adnan from where, who is this girl yimin bayani ”tayi maganar tana zame hannun Sabrine daka fuskarta ta ganin yadda take hawaye yasa hajiya saleemeh cikin fushi take sake fad'an “banason iskanci Adnan kamin bayani wace wannan d'in”
Cikin wata murya wadda ko fita batayi sosai ya furta“she is my world , mommy this girl here itace rayuwata and itace farin cikin yaronki mommy the choice is yours kince nafito da Mata mommy here you go” yakama hannun hajiya saleemeh ya had'a Dana Sabrine, murmushi hajiya saleemeh tayi kafin tace “to meye abin tashin hankali aciki , meye na Bata ran Adnan abinda muke jira kenan dukkanmu daga ni har alhaji abinda muke jira kenan kuma duka zamui farin ciki da hakan sosai right alhaji? ”ta kalli LEC A. M da tun shigowar su idonsa ke kan Sabrine dajin haushin abinda Adnan yayi, kallon hajiya saleemeh LEC A. M sannan ya juya ya kalli Adnan da Shima kallonsa yake sannan cikin bacin rai yafurta“never this will not happen, Don't even think of doing it, I repeat don't even start”yakai karshan maganar Yana nuna Adnan da yatsa”
Cikin wani kallo na abin tausayi Adnan yake duban babansa jikinsa du yayi weak gaba d'aya wani jiri, jiri ya kalli Sabrine da harta durkushe kasa , kukanta har cikin ransa yake ji yarinya karamar wadda Bata San tension ba Amma shida maifinsa sunsata cikin matsala , rintse idonsa yayi sannan ya furta“but daddy why”

Cikin d'aga murya LEC A. M ya furta because I love her, I love her so much”
Da sauri hajiya saleemeh ta dubi LEC A. M dawani shock dayashiga jikinta cikin rashin gamsuwa da abinda ya furta bakinta na rawa tana nuna alhajin ta furta“you…love …her”
Cike da gwarin guiwar yace”yess I love Sabrine and I will not let your son marry her no matter what”

“innalillahi wa innailairrajuun”ta furta tana dafe kirjinta tana kallon Sabrine yadda ko Afiya zata iya girmarta tace“alhaji wai kasan abinda kake fad'a kuwa kasan me kakeyi kuwa wannan ai zubar da mutuncine da kima Taya zakaso sa'ar yaranka alhalin kasan Adnan na sanka ko kasha wani abunne”
Nunata LEC A. M yayi da yatsa kafin yafara fad'in “and Bari kiji akan Sabrine kokece kika bani matsala to tabbas zamu samu matsala dake bama d'anki ba”sannan ya juya ya kalli Adnan had'e da nunashi da yatsaya yace“kai kuma stay away from her I repeat it stay away from her kaji ko”

cikin magana me had'e da kuka hajiya saleemeh tace“if not fa? eye idan ya 'kifa nace?, Alhaji kadawi hankalin ka abinda kake Shirin aikatawa wallahi ba daraja a idon yaranka ba har a idon jamaa sai darajar ka ta zube”juyawa kawai yayi bece komi ba yayi section d'insa
Ita kin Sabrine jin bazata iya jure abin da ke faruwa ba yasa da gudu ta tashi ta fice daga parlon ko takalminta ahannu ta diba tana kuka, Adnan ne yabi bayanta Yana Kiran sunanta amma Ina ko tsayawa batai ba , tana zuwa get man ya bud'e Mata kofa ta fice , fitar ta ke dawiya kuwa tasamu wani me napep ya kawo wasu cikin area din aikam da sauri ta tsada shi tashiga tana masa nuni da yayi sauri yabar gurin, kafin Adnan yazo tuni tayi nisa cikin 'bacin Ran abinda ya faru Adnan ya buga hannunsa ha gate d'in gidan har Saida me gadi ya tsorata Yana gudun yayi masa magana Dan yaga baya cikin tunanin da sosai yasa Dole me gadin yayi shiru Yana jimanta abinda ya faru
Adnan be Kara shiga parlon ba kawai bangaren sa Shima ya huci Zuciyarsa nayi masa

Hajiya saleemeh ma kam kusan mutuwar tsaye tayi da ko zama kasayi tayi gashi tanada problem na ciwan kafa abin du ya hadu yayi Mata yawa ,sai kawai ta sulale a carpet d'in parlon ta zauna bakinta Banda Karan innalillahi babu abinda yake
Tunda LEC A.M yashiga parlon sa Banda Kai kawo babu abinda yake gaba d'aya yarasa nutsuwarsa kasancewar yadda yaga soyayyarsa da Sabrine zata hadda sa masa mummunan tashin hankali a gidan sa ,hakika shikanshi yasan abinda yake shirin aikatawa bame kar'buwa bane a society Amma to ya ya'iya tabbas shijin Sabrine ya a Zuciyarsa sosai meye mafita yanzu…


Tun da ta hau batacewa me napep d'in ga inda zata ba Shima d'in kuma be tambayeta inda zata ba ganin halin da take ciki ,Saida ta fara samin nutsuwa sannan ta fad'a masa ya kaita makaranta ,gudun sa'ido na Yan makaranta yasata goge hawayenta sosai sannan tasa ta kalminta
Har kusan kofar hostel d'in su me napep d'in ya kaita,tunkafin ta karaso ta hango mota Kamar ta Yaya farouk a gaban hostel d'insu,jitayi a Zuciyarta dama ace Yaya farouk da tabbas saita bishi Dan jitai bazata iya Kara ko kwana daya ba batare da taga Granny ba
Sauka tayi sannan ta sallami me napep d'in ya juya ya tafi,tsayawa tayi kafin ahankali ta fara nufar hostel d'insu duk da yadda ta goge hawayen fuskarta Amma hakan bazai sa ka kasa gane kukan da tai ba ,gakuma hawaye daya taru a idon ta Yana Shirin zubowa,

“Sabrine”
Ta tsinkayi muryar farouk a bayanta ,da sauri ta juya,shid'in ne kam Yana sanye da wani yadin kufta a jikin sa mekyau
Jitai wani dad'i ya lullubeta ganin farouk ,. 'karasa takowa yayi har zuwa inda take tsaye ganin yadda idonta yayi kalar na masu kuka had'e da damuwa ,da sauri yace“sabrine meke faruwa ?why are you crying ? Are you sick or what yimin bayani”…

*Aimin share pls free book ne share kawai nake bukata👏🏻*

*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


1️⃣9️⃣


*BABYLUV*
*07038524543*




Please Login or Register in order to submit comment