Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, d'aga masa Kai Adnan yayi alamar da gaske take, ahankali LEC A. M yace“are you sure” da sauri Adnan yace
“very sure Dad just eat the food”badan ransa yaso ba haka Adnan yafara bashi doyar Yana karba yanaci Saida adnan ya tabbatar yaci sosai yasha ruwa sannan ya ri'ko hannun daddy yace“daddy inshallah zaka fita daga condition dinnan because I talk to Sabrine about you”sai yayi shiru idonsa duk ya taru da kwalla muyarsa tashiga sarkewa yace“dad inshallah you will marry Sabrine”kawai yasaka kuka Yana kwanciya kan LEC A. M………

*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_

3️⃣2️⃣

_babyluv_
_07038524543_


Ganin yadda Adnan ke zubar da hawaye jikin LEC A. M yaji gaba d'aya jikinsa yayi sanyi tausayin Adnan ya kamashi , tabbas yauya Kara gasgata zuciya Bata da Kashi , hakika babu abinda bazai iya mallakawa Adnan ba babu kuma abinda bazai iya nemo Masa ba afadin duniyar Nan , Amma gashi ya gagara bar Masa Sabrine gaskiya Zuciyarsa batai Masa adalci ba
Hawayen dasuka taru a idon LEC A. M yasa hannu ya goge sannan ya d'ago Adnan yafara goge Masa hawaye had'e da fad'in “stop crying my son hakika mahaifinka becika uba ba ayau, hakika mahaifi ya man sadaukar da abinda yake mallakinsa Dan farin cikin yaransa Amma ayau na gagari haka am so sorry Adnan ka yafewa mahaifinka”hawaye yashiga zubowa Masa Yana Kama hannun Adnan Yana rokarsa kan ya yafe Masa , riko hannunsa Adnan yayi tare da fad'in,“dan Allah daddy kadena roko na daddy lafiyan ka yafiyemin komi a rayuwar Nan idan har banceci lafiyar mahaifina ba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba sannan idan wani abu ya sameka bazan ta'ba yafewa kaina ba , inshallah daddy Zan shawo hankalin Sabrine kuma she will marry you….not…m…” kasa karasa maganar yayi saboda yadda Zuciyarsa ke Masa zafi , rungumeshi daddy yayi Dan hakika Adnan ya haifu hakan yasa LEC A. M fad'in “i love you son”

Yana Kara kwanciya jikin daddyn nasa Adnan yace“love you too Dad I really don't want to loose you”



Tunda Sabrine ta koma daki take tunanin maganganun Adnan Taya zata so Daddy, kenan duk son da Adnan keyi mata dama karyane? Ashe zai iya sadaukar da soyayyarta? Shin Yana tunanin zata iya rayuwa da LEC A. M ne, mutumin da har kullum kallan mahaifi take masa Taya zai juye ya zama mijinta

“this is in possible”sabrine ta fad'a a fili tana tare kukan dake Shirin zo Mata, Latipha data shigo sannan yasa ta juyo inda Sabrine ke zaune tace“meye ne impossible d'in? Kefa na fahimci matsalar ki Bata karewa Sabrine karki samin ciwan Kai please” ta fad'a tana zama kusa da Sabrine d'in, hawaye suka zubowa Sabrine ta dubi Latipha tace“latipha bani nake kirkiro matsala ba matsalar ce da kanta take damuna”kawai tasa kuka had'e da kwashe dukkan yanda sukai da Adnan ta fad'a wa Latipha sannan ta d'ora da fad'in “taya hankalina zai kwanta ? Tunda nake a rayuwata bantaba shiga hali maka mancin wannan ba Latipha please help me out , meyakamata nayi wallahi kaina ya kulle Kona Kira Granny? Kona amince na auri farouk ne? Granny tace Dole na fidda miji before graduation d'inmu if not ta tabbatarmin saina auri farouk” kawai tasa kuka tana kwanciya kafadar Latipha, jinjina kai Latipha Tayi tabbas Sabrine nacikin tsaka Mai wuya hakan yasa cikin muryar lallashi Latipha ta fara fad'in “sabrine komai kikaga yasami bawa mu'kaddarine daga Allah, hakika Allah yanaso ya gwada imaninki ne shiyasa ya jarrabeki ta hanyar soyayya domin itama babbar jarrabawa ce, wasu suna ganin soyayyya kamar bawata aba bace Mai muhimmanci Amma tabbas sunyi kuskure , domin da soyayya ma Allah zai iya jarra baka ga kuma misali Nan kin gani akanki”sannan tayi shiru jin yadda Sabrine ke sauke ajiyar zuciya hakan yasa ta Kara da fad'in “sabrine ada bana goyon bayan LEC A. M akan son da yake Miki Amma idan Zan fad'a Miki gaskiya ayanzu bazan goyi bayan ki auri Adnan ba”dasauri Sabrine ta d'ago fuskarta me cike da hawaye tace“meyasa zakice haka Latipha kece fa kika bani kwarin guiwar naso Adnan meyasa yanzu Zaki janye maganar ki haka”murmushi Latipha Tayi sannan tace“ada anyi tunanin LEC A. M yayi Dan zuciya dazai so yarinya kamarki wadda Bata fi Saar yarinyar sa ba, Amma ayanzu nafahimci wani abu guda d'aya, soyayya kala kala ce akwai wadda Zaki ga mutumne ya d'orawa kansa kuma zai iya cirewa kansa ita idan yaso, sannan akwai SOYAYYA ta gaskiya wadda Allah ne ke d'ora bawansa saboda wani dalili mekyau , wadda Ina da tabbacin itace irin wadda LEC A. M kemiki Sabrine , Bari kiji idan har kika Bari LEC A. M yarasa ransa ta dalilinki hakika hakkinsa bazai barki ba sannan Adnan zai tsaneki komai San dakike ganin yake Miki , zai dinga ganinki sanadin mutuwar mahaifinsa kuma Ina da tabbacin bazai aureki ba, sannan mahaifiyar Adnan da shauran kannansa duka zasu tsaneki Ina da tabbacin wannan tunanin Adnan yayi yasa yace ki auri mahaifinsa instead of him saboda guje wannan abubuwan Dana lissafo miki”

Sannan Latipha Tayi shiru kafin ta dafo kafad'ar Sabrine hade da fad'in “sabrine you are wise enough and you are educated both Islamic and social one inaso kiyi tunani akan abubuwan Dana fad'a Miki kafin ki yanke hukunci kinji”tana fad'ar haka ta Mike tabar Mata gurin
Bin Latipha kawai da kallo SABRINE tayi wani hawaye ya gangaro Mata kafinta rungumo pillow ta kwantar da kanta akansa , maganganun Latipha suka shiga yimata yawo acikin kwakwal warta tabbas abinda ta fad'a gaskiya hakika Sabrine bataso tayi sanadin Rai guda ata dalilinta sannan hakika idan Adnan ya tsaneta bazata yafewa kanta ba sannan koba komai yadda takeson Adnan zata iya Masa komi arayuwa domin family d'insa tabbas nata ne itama

Har kusan karfe shabiyun dare idon Sabrine abude yake babu ko alamar bacci Banda tunanin maganar Latipha data Adnan babu abinda take hakan yasa ta yanke hukuncin tashi ta dauro alwala ta fara gabatar da nafila domin neman zabin Allah, hakika ayanzu ta gama amincewa da auran LEC A. M koba komai tanason Adnan sannan tasan bazata ta'ba auran farouk ba dawannan tunanin bacci ya d'auketa akan daddumar bacci mecike da tunani kala kala , Taya zata auri LEC A. M ta dinga ganin Adnan akusa da ita shine abinda yafi tsayawa a Zuciyar Sabrine

Ata bangaren Adnan kam abin haryafi na Sabrine bayin sun dawo gida tare da daddy Dan har yafara jin kwarin jikinsa hakan za'a iya allakanta shi da sacrifice d'in da Adnan yayiwa Daddy na bar masa Sabrine

Bayin Adnan yakai daddy har dakinsa Saida ya tabbatar ya kwanta sannan ya fito zuwa sashensa , Dan har jiri yake Kamar zai Fad'i kansa Banda sarawa na ciwo babu abinda yake , shima din daurewa yayi ya gabatar da sallar nafika sannan ya roki Allah da yabashi dangana da hakurin rashin Sabrine sannan yayi addua sosai , wayarsa ya d'auko yashiga number d'in Sabrine ya tura mata message kamar haka

_sabrine Dan Allah kiyi tunani mekyau kafin zartar da hukunci domin ayanzu rayuwar daddy na na hannunki kada kidubi soyayyata da halin dakike tunanin Zan shiga kidubi rayuwar mahaifina_

Yana gamawa ya Mi'ke zuwa bed d'insa sannan ya kashe wutar dakin , ya dad'e bacci baizo masa ba kafin daga bisani wani bacci yayi awan gaba dashi me cike da fargabar rashin Sabrine atare dashi, sa'banin daddy Wanda rabon dayayi bacci me dad'in Wanda yayi yama manta Zuciyarsa fal farin ciki dakuma rokar Allah yasa Sabrine ta amince , itakam hajiya saleemeh fargaba da abinda ke Shirin faruwa ne suka cika Mata zuciya Tama rasa abinda zatai tazubawa sarautar Allah ido ne taga abinda zai faru Dan bataso ta koma gurin wani malami ta Kara aikata wani zunubi, Wanda tayi ma tana rokar Allah ya yafe Mata aduk sallar dazata gabatar domin sharrin shedan dakuma San LEC A. M sune suka tunzurata ta biyewa San zuciyarta Wanda ayanzu take ladamar abin datai , ta tabbatar akwai wani abu dake Shirin faruwa Nan kusa Wanda shine dalilin tonuwar asirinta kamar yadda malam boka ya fad'a fatanta koma mene kada ya bullo ta hanyar Sabrine amin

Da asuba Latipha ce ta fara farkawa ganin Sabrine ke kwance akan dadduma yasa taji tausayin Sabrine ya Kara kamata kana ganin fuskarta yadda take baccin kasan ba Mai dad'i bane , babu yadda ta iya haka ta tashi Sabrine Tai sallah
Bayin idar da sallar ne ta fara azkar da adduo'i sosai Dan neman zabin Allah akan abubuwan da suka shige mata duhu , bayin ta kammala me ta d'au wayar ta, sa'kon Adnan ne ya bayyana afuskar wayar jin yadda yake rokar ta akan mahaifinsa yasa tashiga yimasa tamin akan yazo da safe ya sameta , tana gama turawa ta Mi'ke ta koma bed d'in ta , tana zama ta budo alqur'ani me girma a wayarta cikin burya Mara sauti dakuma dadin sauraro ta fara rerawa


Misalin karfe Sha d'aya na safe bayin ta gama breakfast tana zaune , Kiran Adnan yashigo wayarta , ganin Adnan ne yasa batare da tayi picking call d'in ba kawai ta Mi'ke ta ja wani hijabi daya sakko Mata harkasa bazakai zaton kayan bacci jikinta ba duba da yadda ya rufe Mata ko Ina sannan yayi Mata kyau sosai, ahaka ta fito ta dubi Adnan dake tsaye jikin motarsa ya Kara haske Amma ya rame Amma ramar sai tai masa , ahaka ta iso inda yake , gaba d'aya Masa d'auke idon sa yayi daga kan Sabrine saboda zai iya cewa wannan shine first time dayaga hijabi jikin Sabrine ganin tayayi tamkar Yar tsana saboda yadda tayi kyau , kasa da kanta Sabrine tayi tare da fad'in “ina kwana ” be amsa ba Dan kallonta yakeyi sosai Zuciyarsa namasa aiyane akan abinda yake Shirin Yi na sacrifice Yana Shirin ai kata kuskure ne Amma atake wata zuciyar ta karyata shi
D'ago was Sabrine Tai had'e da Kara fad'in “ina kwana ”ajiyar zuciya Adnan ya sauke kafin yace“lafiya qalau”bata Kara cewa komi ba takumayi kasa da kanta hakan yasa Adnan fad'in “sabrine ke nake jira naji decision d'inki akan condition d'in mahaifina kuma kinyi shiru”yana fad'ar hakan idon Sabrine ya kawo kwalla kafin ta d'ago ta dubi Adnan cikin murya Mai kuka tace“Adnan bani da wani za'bi akan abinda ka yanke , tunda kana ganin mafitar mu shine na auri mahaifinka na bark…”tayi shiru tana goge hawayenta da bayan hannunta kafinta Dora da fad'in “na amince Zan auri daddy Adnan not you idan har hakan zaisaka farin ciki idan kuma har hakan zaisa daddy yaji sauki ”tana gama fad'ar hakan tasa duka hannuwanta biyu a fuska ta fara rera kuka me cike da tausayi , jin abinda Sabrine tace Adnan rasa me zaiyi yayi shin farin ciki zaiyi akan amincewa da soyayyar daddy da tayi ko kuwa bakin ciki zai akan bazai auri farin cikin rayuwar Saba? Ganin yadda Sabrine ke rera kuka hakan yasa ya fara takowa zuwa gun Sabrine had'e da Mi'ka hannu zai rarrasheta Dan jin kukan yake har cikin Zuciyarsa , Zuciyarsa ce ta dakatar dashi daka ri'ke Sabrine tare da tuna Masa yanzu takusa zama mallakin Daddy hakika yanzu ta HARAMTA gareshi “innalillahi wainna ilaihirrajuun”Adnan yafad'a Yana ja baya Yana jin wani jiri naneman d'ibansa ya dafa motarsa , d'agowa Sabrine Tai ta kalli Adnan ta bala'in tsorata ganin yadda idon Adnan yayi wani mugunja jijiyar kansa tayi bala'in tashi , tsagai tawa da kukan tayi ganin Yana neman fad'uwa Amma ya ri'ke mota , Mi'ka hannu zata dafashi tayi kafin ta tabashi ya d'aga Mata hannu alamar ta Bari sannan ya furta“sabrine thanks for saving Daddy's life thanks so much Sabrine ” Yana fad'ar hakan ya bud'e motarsa ya shiga sannan ya ja motar ahankali , tun sabrine tana gano shi har ya bace Mata da gani , gaba d'aya rasa me zatai tayi kawai ta tsugu agun ta fara kuka , Allah yasa Latipha ta fito ganin Sabrine atsugune yasa ta karasa da sauri tana d'ago ta had'e da Sabrine “mene kike haka Sabrine kamar 'karamar yarinya taso , taso muje ciki”haka ta lallabata suka koma daki



Tunda Adnan yabar school d'insu Sabrine kasa Kai kansa gida yayi hakan yasa yayi parking yad'au wayar sa had'e da dialing d'in wata number ringing biyu yayi akai picking had'e da fad'in “buddy ya what's up”

Ahankali Adnan yace“where are you”jin muryar Adnan ba daidai ba yasa yace“am at home ”

“come to A.A foundation middle of the line and pick me up”bece komi ba dayake babu nisa tsakaninsa da inda sukai waya yasa a kasa yafito be d'auko mota ba cikin three minutes ya karaso ya hango motar Adnan a gefen hanya , Adnan na ganinshi ya fito ya koma d'aya mazaunin shima Yana zuwa batare da yayi masa tambayar komi ba yashiga mazaunin driver yaja motar zuwa gidansu

Babban gida ne duk da bekai nasu Adnan ba Amma shima da girmansa dakuma kyau, Yana yin parking a compound d'in gidan ya fito ya zagayo ya bud'ewa Adnan kofar yafito Yana dafe kansa , ganin Kamar bayama cikin hayyacinsa Yana neman fad'uwa yasa Usman saurin riko shi suka nufi wani part a gidan da alama nashine

Suna zuwa ya zaunar dashi kan doguwar kujera had'e da jinginar dashi ajikin kujerar, wuyansa ya ta'ba yaji zafi sosai da mamaki ya Kara duban Adnan dama bashi da lafiya ne, ganin yadda ya dafe kansa alamar ciwo yake Masa gakuma yadda yadan fad'a yasa Usman ta'ba head d'in Adnan tare da fad'in “buddy kana da headache ne?” batare da Adnan yayi masa magana ba kawai ya


D'aga masa Kai alamar eh , kyaleshi agun ya tashi yashiga bed room d'insa befi minti uku ba ya dawo d'auke da drip ahannunsa anan parlon Usman ya daurawa Adnan drip sannan ya sa masa injection na fever and headache a ciki , ko cikakken minti biyar Adnan beyi ba bacci yayi awan gaba dashi...
*💫FORBIDDEN LOVE💫*

3️⃣3️⃣

_babyluv_
_07038524543_

_inshallah zanyi kokari cikin week d'innan Zan sauke forbidden love👏🏻👏🏻masu jin haushin haushina akan Adnan kawai kufito mu danbatu🤥☺️😚🙃sapnah, maman hanif, maman yaseer, maman nabeela, maman abul , maman Muslim, Salma gaya, sbr, ubaida , da shauran duka kutaho_


Hakika halin da Adnan yashiga akan Sabrine bazai kwatantuba domin gani yake tamkar rayuwarsa ce tazo karshe , rashin Sabrine tamkar rasa rayuwarsa be
Abangaren LEC A. M kuwa yaji sauki sosai zamu iya alakanta hakan akan albishir din da Adnan yayi masa akan Sabrine harya fara tunanin komawa school Dan sun bashi Hutu akan rashin lafiyar dayayi, Sabrine kam akullum Latipha ke tausasarta akan son Adnan tana nusantar da ita cewa hakan da Adnan yayi shine daidai koma shine kasan cewar yaro nagari, sau kusan uku Sabrine nakiran wayar Adnan Amma Sam baya d'auka haka ta hakura da kiransa badan ranta yaso ba saidai babu yadda zata iya , Amma akullum tunaninsa na manne cikin zuciyarta

Misalin Sha biyu na Rana ne Adnan na zaune gaban LEC A. M da alama Adnan ya gama fad'a masa wata magana data d'aga masa hankali ne duba da yadda yanayin fuskar LEC A. M d'in take

“Adnan hakika wannan hukuncin daka yanke beyi daidai ba Taya zakace zaka komar da aikinka turai alhalin kamin alkawari kasarka zakai was aiki , Taya yanzu zakazo min da wannan maganar, Dan Allah Adnan Ina rokonka kada lefina yashafi mahaifiyarka hakika ” yadda Adnan yadago kansa ya dubi babansa abin har tsoro yaban duba da yadda ya rame ga duhu dayayi abin tausayi idonsa yayi jajawur ya d'ago kansa tare da fad'in “abbba nikaina fa basan komawa nake ba babu yadda na iya ne Dole hakan yakamata nayi Abba Dan Allah kada ka hanani nemarwa kaina mafita kada ka hanani komawa kasar waje daddy wallahi bazanyi irin wannan zaman danai Abaya ba zanna zuwa daddy saboda contract d'in da nasa hannu da Nigeria ne da can England kaga ai zanna zuwa gunku ko”girgida Kai LEC A. M yayi na gamsuwa da abinda Adnan ya fad'a sannan yace“adnan ayanzu banine abin ji mahaifiyarka kasan dai tashin hankalin data shiga akan waccan zuwan naka ayanzu kam indai taji nasan bazata Bari na”

“nasani Daddy”ya fad'a Yana yin kasa da kansa Dan jiyayi kamar zai hawaye sannan yace“daddy sonake sai bayan natafi zaka fad'awa mommy sannan ka Bata hakuri Daddy”kara jinjina Kai LEC A. M yayi sannan yace “shikenan Adnan Dan Allah banaso ka kalleni Amara adalci arayuwarka akan shiga tsakaninka da…”daga masa hannu Adnan yayi alamar yayi shiru kafin yace“daddy ayanzu bani da hadi da Sabrine yanzu takusa zama taka kaga step mom d'itace”jin Adnan yace haka jiyayi gaba d'aya kunya ta kamashi harya kasa kallon Adnan, sosai Adnan yafahimci hakan Mi'kewa yayi tare da fad'in “daddy let me go”shima d'in Mi'kewa yayi tare da fad'in “yaushene zaka tafi”murmushi Adnan yayi tare da fad'in “daddy ni fa fad'a ma ne banyi ba nagama komi jirgina ma yau misalin karfe takwas na dare zai tashi ”rugumshi daddy yayi , ganin hakan Adnan shima yayi hugging d'insa tare da fad'in “i will missed you dad, pls make mom understand kada Tai fishi dani”girgida Kai LEC A. M yayi tare da fad'in “pls forgive me Adnan kaji I'm so sorry”sosai Adnan yakara hugging daddyn nasa tare da fad'in “stop saying so daddy ”
Ahaka Adnan yayiwa mahaifinsa sallama yabar section dinnasa , har zai huce yaji bazai iya tafiya baiga mahaifiyarsa ba hakan yasa kawai yayi part d'inta, Yana shiga hajiya saleemeh tayi saurin ajiye wayar ganin Adnan , yafahimce Kamar mahaifiyarsa bataso ganinsa awannan lokacin ba yasa yad'an juya zai koma had'e da fad'in “im sorry Naga like you are busy”da sauri hajiya saleemeh ta tsayar dashi hade da fad'in “no Adnan please come in”dawo yayi had'e da neman guri kan wata kujera dake dakin tare da fad'in “mommy Ina wuni”amsawa Tai cike da sakin fuska gudun Kar Adnan yayi zargin komi , sannan Adnan ya dora da fad'in “mommy dama ankirani Abuja zanje duba marasa lafiya Wanda akaiwa operation beyi kyauba akace nazo na duba inshallah karfe takwas na Daren yau jirgina zai tashi ”hakannan hajiya saleemeh taji hankalinta be kwanta da tafiyar ba Amma babu yadda ta iya hakan yasa ta dubi Adnan tare da fad'in“Adnan waikuwa kana ganin kanka amadubi yadda duk haskenka kayi duhu ka rame meke faruwa Anya kana ma cin abinci kuwa”murmushi yayi tare da fad'in “kinsan fever d'in Dana danyi ne amma soon Zan dawo daidai mommy ”
Cikin rashin yadda tace“nidai ka kula da kanka kuma Allah ya kiyaye hanya Allah nya Kare kaji inshallah zaka samu farin ciki arayuwarka Adnan”jin adduo'in da mahaifiyar tasa keyi masa hakan yasa yad'an ji sanyi a tafiyar tasa , yayi Mata sallama ya tafi


Section d'insa ya nufa yayi wanka ya shirya cikin wasu bakakken Kaya wando da Riga masu balain kyau sai wata back p-carp dayasa dama tun daren jiya ya had'a duk wani abu me amfani dazai tafi dashi yasa driver yasa Masa shi a mota, Yana cikin daura wani takalmi red a kafarsa wayarsa ta kawo haske sakamakon data d'insa da ya Bari a bud'e da alama message d'in Whatsapp ne , hoton Sabrine ne ya bayyana akan wayarsa tun wani hoto daya tura a laptop d'in daddy ranar tana cikin kayan matriculation Time d'insu na farko a school kana ganinta kasan tana cikin farin ciki duba da yadda take murmushi mekama da dariya , gaba daya hakoranta sun bayyana reras ta cikin idonta kana iya karantar farin cikin datake ciki, tun ranar daya tura hoton ya d'ora shi a wallpaper d'in wayarsa , babu wani lokacin da Adnan baya karewa hoton kallo Dan Yana sashi nishadi hakannan indai ya kalla koda baya cikin mood mekyau sai yayi murmushi, yanzun ma hakan ne ya faru ganin hoton Sabrine Saida yayi murmushi har cikin Zuciyarsa yaji San ganin Sabrine yake, hakannan yakeso ya Kara ganin Sabrine gani na karshe amatsayin masoyiyar sa kafin ta kasance mallakin daddyn sa, hakannan yabi raayin Zuciyarsa Yana gama shiryawa ya d'au key din motarsa misalin karfe biyar na yamma yanufi makarantar su Sabrine

Sabrine na kwance ta lafe a kan gado hannunta ri'ke dawani littafi na azkar tana karantawa Amma can cikin zuciyarta tunanin Adnan ne fal aranta dalilin hakanne ma ta fara karanta azkar d'in Dan so take ta kawar da tunanin Adnan a ranta
Kamar a mafarki wayarta tad'au ringing cike da mamaki taga sunan Adnan kan screen d'in wayar, idan Sabrine tace bataji dad'in kiranta da Adnan yayi to tabbas tayi karya , fatan ta ace tana d'aga wayarnan Allah yasa Adnan yace Yana waje Yana jiranta Yakuma sheda Mata cewa daddy yajanye maganar aurenta, dawannan tunanin Sabrine Tai picking call d'in, abinda kunnenta yaji jitai tarasa inda zata tsoma kanta Dan dad'i burinta na farko ya cika saura nabiyu Allah yasa yace daddy ya janye auranta
Hakannan Sabrine ta tsinci kanta da d'aukan mirror tana kallan fuskar ta Dan tama manta rabonta da kallan fuskar ta, samun kanta tayi da d'auko lipstick ta shafa Dan kasancewar yadda take da haske Bata shafa powder Dan ita ko cikakken make up bayi take ba Amma yadda take kyau ko wata wadda ta kashe kud'i Tai make up Sabrine ta fita kyau
Gyalenta ta d'auko Wanda be cika girma sosai ba tasa kasancewar doguwar rigace ta atamfa me golden ajikinta sai flat din takalmi datasa sannan ta nufi kofa Dan ganin Rabin ranta
Yana tsaya jikin motarsa sai tashin kanshi yake yayi kyau sosai cikin kayan dayasa kamar wani Wanda ba d'an 'kasarnan ba , tun fitowar Sabrine idonsa ke kanta Yama kasa d'auke ido daga kanta sakamakon kyan dayaga ta karayi Masa yau, itama din Sabrine kallonsa take kamar Wanda Bata sanshi ba yau tafara ganin sa p-carp d'in taima fuskarsa kyau

Tana zuwa ta tsaya murmushin ta yakasa boyuwa a fuskarta Dan Allah yagani jira kawai take taji me zaice Mata hakan yasa tace“manya dama ana ganinku kinyi wuyar gani”
Smile back yayi batare dayace komi ba hakan yasa Sabrine Kara yimasa magana“ wannan murmushi haka saikace Wanda aka daurawa aure” ayanzu kam murmushinsa ne ya d'auke tare da Dan had'e fuskarsa guri guda yace“wato kin cire ni daga rayuwarki Sabrine har kikemin tunanin auren wata ba ke ba koh” Nan take mood d'insa ya canja gaba daya kafin Sabrine ta bud'e baki Tai magana yace“is fine Sabrine dama haka raguwata but inason kisan wani abu yadda Allah ya dasamin sonki anan ”yayi maganar had'e da nuna kirjinsa sannan ya d'ora da fad'in “babu ta yadda Zan na cire shi saidai idan har rayuwatace tazo karshe ”
Ta Kara bud'e baki zatai magana Adnan yace“i came to say goodbye” cikin rashin gane abinda Adnan keson cewa ta Kara maimaita abinda yace“goodbye”daga Mata Kai yayi alamar yess idonsa yayi ja sosai kirjinsa har harbawa yake yace“yess Sabrine I will go far away from you Sabrine zanyi nisa nisan da wata kila acan Zan mutu wannan dalilin yasa nazo nai miki sallama I'm going…back…to…England” yayi maganar muryarsa na rawa sosai kamar me Shirin kuka
Gaba d'aya Sabrine jitai tanajin maganganun Adnan asama tama kasa jin abinda yakeson cewa hakan yasa ta d'aga masa hannu gaba d'aya idonta ya kawo ruwa hawaye wani na korar wani tace“

Please Login or Register in order to submit comment