Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ake Kira da HARAMTACCIYAR SOYAYYA Amma ta wani bangaran wannan babbar nasarace Ashe Sabrine jininkace lallai alamarin Allah me girma ne, Allah yasa mudace”dukkansu suka amsa da Amin

Daidai lokacin alhaji isah ya shigo ganin dukkansu d'auke da murmushi yaji dad'i sosai sannan yacewa Granny tafito su tafi, har gurin motar suka raka ta da alkawarin zasu har gida insha Allah

Granny na tafiya LEC A. M da farin ciki ya cika fuskarsa na jin dadin yasamu jinin Fatima koba komai zainaganin Sabrine yana jin dad'i , yaso ace yaga Sabrine Amma hakan besamu ba Dan sun dad'e da tafiya tare dasu Abban farouk


Tun daga nesa Adnan ya fara hango mahaifinsa awurin masallacin da wasu mutane da besan kosu waye ba suna gaisawa da murmushi fal fuskar LEC A. M sunata musayar hannu da mutane, hakanne ya tabbatar Masa cewa lallai an daura auren daddyn sa da Sabrine cikin Zuciyarsa ya fara karanto“ hasbunallahu waniimal wakil”sannan ya umarci Usman kan yayi parking kafin sukai ga inda su daddyn nasa ke tsaye da jamaa
Dubansa Usman yayi tare da fad'in “buddy what gasu daddy can meyasa zamui parking here? ” Dan dafe kirjinsa Adnan yayi tare da fad'in “i dunno but I'm not okay ussy kirjina namin wani ciwo just now” Yana fad'ar hakan kirjinsa ya sake wani irin mahaukacin ciwo dasaida yad'an saki Kara Yana danne kirjinsa, da sauri Usman yayi saurin bud'e kofar motar batare da ya rufe kofar ba yayi saurin zagayawa inda Adnan ke zaune , sannan ya bud'e kofar gaba d'aya Adnan yayo jikin Usman hannunsa dafe da kirjinsa
Cikin rikicewa Usman ya d'ago ya dubi inda su daddyn sa ke tsaye ya kwalla musu Kira, akusan tare suka kallo inda Usman ke kiransu ganin kaman ya riko Adnan ne yasa gaba d'aya sukayi gurin dasauri kafinma su karaso tuni Adnan ya suma ko motsi ba yayi

“innalillahi wainna ilaihirrajuun”was abinda daddy kawai ke iya furtawa kenan , kafin su mayar da Adnan cikin mota dukkansu suka tafi zuwa asibiti…….

*💫FORBIDDEN LOVE💫*

3️⃣9️⃣ & 4️⃣0️⃣

Granny ce ta fito domin an sheda Mata tayi bako misalin karfe goma na safe ,har mamaki ya kamata kowanene awannan lokacin , umarni ta bayar da Ashigo dashi,
Ganin LEC A. M yasa tayi mamaki tare da fad'in “abdulrashid Kaine da safiya haka bisimillah shigo mana” cikin girmamawa LEC A. M yashigo had'e da gaishe da Granny ta amsa cikin fara'a tare da fad'in “Allah dai yasa lafiya ”jinjina Kai yayi tare da rusunar da kansa kasa gami da furta“to lafiyar kenan Amma abinda ya kawoni gaskiya ba lafiya ba ”shiru Granny tayi tana sauraran abinda yakeson fad'a, ganin hakan ya d'ora da fad'in “hakika bayin tahowarku ne wani firgicin Abu ya faru Wanda shine dalilin zuwana nan”cikin sauri Granny tace“Abdurrashid Dan Allah Yi Maza sanar dani meya faru”gyara zama yayi tare da fad'in

“wallahi hajiya munyi kwanan tashin hankali domin Adnan ne babu lafiya maganar danake Miki Yana asibiti Dan harda Aman jini yayi jiya sannan likitoci sun tabbatar Mana cewa damuwa ce tasashi cikin halin dayake ciki sannan idan baayi gaggawar yimai abinda yakeso ba to tabbas zai iya rasa rayuwarsa wannan dalilin ne yasa kika ganni da wannan safiyar haka”sosai Granny tayi salati tare da fad'in “taya akai sakaki haka I mean mene yasashi wannan damuwar haka”cikin sauri yace“sabrine hajiya domin Adnan na mugun son Sabrine Amma dalilin soyayayar dayakemin hakan yasa ya hakura ya sallamamin ita tare da barin kasar gaba d'aya , ita Sabrine d'in ce ta nemi dayazo daurin aurenta tare da graduation d'inta , dawowar sa ke dawuya abin ya faru aduk zaton aure ya wakana tsakanina da diyata Sabrine besan cewa gaskiya ta bayyana ba besan cewa itadin jininace ba”shiru Granny tayi tare da duban abdurrashid kafin ta sauke wani nannauyan numfashi tare da fad'in “ikon Allah Amma ai abinda bazai yiwu bane daka sanar Masa cewa Sabrine kanwarsa ce Aure ya HARAMTA garesu koh ai babu hali”

Murmushi LEC A. M yayi Dan ya gane me Granny ke nufi hakan yasashi fad'in “ai ba Kamar yadda kika fahimta bane hajiya shi Adnan yaron saleemeh ne na farko Wanda tayi auran zumunci kafin muyi aure , Allah ne yayiwa mijinta na farko rasuwa ,nikaina bansan cewa saleemeh nada yaro ba domin Bata ta'ba sanarmun ta ta'ba aure ba , Dan bayan da mijinta ya mutu ne iyayenta suka yanke hukuncin ta koma karatu shine taje saudia karatu Hakika Ina da tabbaci akan tarbiyar Adnan domin kusan nine na Raine harna fitar dashi waje karatu, ayanzu Adnan na neman temako na domin nine sanadin shigarsa wannan halin”bakaramin jin dad'in cewa Adnan ba Dan LEC A. M bane domin harga Allah Adnan ya kwanta Mata arai tanajin cewa shine mijin daya dace da Sabrine , hakan yasan cikin farin ciki tace“to ai Dani dakai du d'aya ne domin mahaifin Sabrine ne Kai, kana da damar Bata duk Wanda kaso abdurrashid ”

Yaji dad'i sosai hakan yasa yad'an sunkuyar dakai da fad'in “dama nazo ne kan kibani Sabrine tayi ko kwana biyu ne aguna tasaba dasu Afiya domin da Afiya da Sabrine kusan shekarunsu d'aya domin duk ayear d'aya aka samesu sannan shikanshi Adnan d'in ganin Sabrine zai sami lafiya hajiya” ta fahimceshi hakan yasa Granny fad'in “babu lefi hakan ai Bari na kirawo ta ai saita shirya ko”jawo wayarta Granny Tai tare da dialing number d'in Sabrine hade da Bata umarnin ta sauko kasa, cikin abinda befi minti biyar ba Sabrine ta fito sanye da wata doguwar Riga tayi kyau sosai , ganin mahaifinta hakan yasa taji wani mugun dad'i ya kamata , domin tunda aka sanar Mata cewa LEC A. M shine mahaifinta ne takejin soyayyar sa ta Kara nunkuwa cikin ranta , hakan yasa ta saki dariya had'e da tafiya da sauri ta fad'a jikin LEC A. M had'e da fad'in “daddy is you ” yadda takirashi da mahaifi har kwallar farin ciki Saida LEC A. M yayi domin tunowa da mahaifiyar Sabrine wato Fatima, kallonsu kawai Granny take cikin jin dad'i sannan tace“kinga indai har mahaifinki ne saikin gaji da ganinshi domin yazo tafiya ma dake ne”dadi yayi mugun kama Sabrine da Saida tayi tsalle tare da fad'in “granny hadda ke zamu tafi ko”harararta tayi tace“ah lallai hankali be isheki ba nikuma Ina zani” nandanan fuskar Sabrine ta canja ta turo baki tace“granny ni bazani gurin matar Daddy ba kartaje taimin wani abun Kamar yadda taiwa mamana” jawota Granny Tai tare da sanar Mata yadda saleemeh tayi nadama sannan tacemata sati daya zatai saita dawo, aikam haka Sabrine ta had'o kayanta cikin wata karamar akwata sukaiwa Granny sallama suka nufi kano


Ansamu Adnan ya farfado kasancewar da doctor hakan yasa Usman ya nemi a dawo dashi gida zaina zuwa dubashi agida haka kuwa akai kafin LEC A. M ya dawo daga kaduna Dan babu Wanda yasan inda ya tafi aka dawo da Adnan daki Dan har sannan be farfado ba Amma dai bacci yakeyi , iya fuskarsa ka kalla zaka tabbatar ya rame yafad'a sosai abin tausayi,

Gaba d'aya hajiya saleemeh Bata cikin hayyacinta Dan LEC A. M besanar da ita rashin lafiyar Adnan ba impact batasan ma ya dawo kasar ba , ko lokacin da LEC A. M ya dawo gida ya shirya zuwa kaduna ko kallon inda take beyiba ba Dan har ga Allah darajar Yara kawai zai zauna da ita Amma Banda haka da tuni ya rabu da ita Amma tabbas Dole yayi Mata hukunci daidai da abin da ta aikata, tsoron hajiya saleemeh kada yaranta su ji abinda tayi fatanta Allah yasa kada yasanar dasu Adnan lefin da tayiwa Sabrine


Lokacin dasuka zo shiga cikin gidan LEC A. M Saida gaban Sabrine ya Fad'i zuciyarta ta fara aiyana Mata Adnan koyana Ina oho? Dama ace tana shiga taganshi da taji dad'i arayuwarta , ganin halin data shiga LEC A. M ya dafata tare da fad'in “welcome to your sweet home daughter”murmushi ta saki ganin yadda yayi maganar saita Dan ji dad'i sosai tare da fad'in thanks Daddy

Dukkan su fitowa sukai sai alokacin Sabrine ta Samu karewa gidan mahaifinta kallo lallai gidan hadaddene ya mugun burgeta, get man d'in gidanne ya karaso da sauri Dan yasami labarin Sabrine diyar alhaji ce hakan yasa yace“barka da zuwa hajiya karama”dadi taji sosai hakan dayayi saitaji uwa baba me gadi na gidan Granny , gaisheshi tayi kasancewar ba yaro bane , umarni LEC A. M yayi kan ya d'au kayanta ya shigar Mata da shi ciki , aikuwa da sauri ya aikata abinda aka umarce shi, shikuma daddy ya kama hannun Sabrine zuwa cikin gidan

Dukkan su LEC A M ya hadasu a palour Banda hajiya saleemeh da batama ji shigowar sa ba,
Cikin fara'a deeja tace“daddy itace Sabrine d'in ”daga Mata Kai yayi tare da fad'in “mamana itace anty Sabrine Kinga ga anty Afiya ga anty Sabrine ko” tashi tayi ta koma kusa da Sabrine tana fad'in “anty Sabrine a bed d'ina Zaki kwana Dan Allah kafin agama gyra Miki room d'inki kinji pls”tayi maganar tana ri'ke hannun Sabrine , Banda murmushi babu abinda Sabrine keyi, harararta Afiya tayi tace“lallai ma yarinya sa'aninki ne mu , aikuwa bed d'ina Zaki kwana ”itama tayi maganar da murmushi a fuskarta , Dan tun jiya hajiya saleemeh ta sanar musu cewa Sabrine Yar uwarsu ce ta jini takuma fad'a musu cewa mahaifiyar Sabrine rasuwa tayi , Amma Sam Bata sanar musu cewa itace sanadin komai ba , shiyasa Afiya tayi ladamar yadda ta tsani Sabrine Ashe Yar uwarta ce tajini

Jin kaunar yaransa yake sosai ganin yadda dukkansu suka Aminta da juna hakan yasa ya dubesu dukkansu yace“abinda zai faru dukkanku saiku kwana a bed d'aya ai shikenam ko”dukkansu suka sa dariya ,Dan tunda aka fara maganar Sabrine batace komi ba illa dariya kawai take ,hakan yasa deeja turo baki ta dubi LEC A M tace“daddy kagani har yanzu anty Sabrine d'in batai magana bafa ” dariya Sabrine tayi ta riko hannun deeja tace“ai harma Abu na taho Miki dashi keda sister Afiya fa”aikam suka karasa dariya cikin kaunar juna ,Afiya ce ta Mi'ke tare da zuwa inda Sabrine take ta riko hannunta tace“kinga deeja bazata barki ki huta ba ,taso muje daki inkin huta sai muje gun mommy tana ciki inaga bacci take”sannan tacema da deeja ta d'auko akwatinta, dukkansu suka tafi shikam LEC A.m binsu kawai yayi da kallo Yana jin wani dad'i aransa Afili ya furta“ ALHAMDULLAHI BINI'IMATIHI TATIMMUSSALIHA”
*💫FORBIDDEN LOVE💫*

4️⃣1️⃣

_babyluv_
_07038524543_

Bayan sallar isha'i tana kwance kusa da deeja datai bacci hakanan taji son Adnan na mugun taso Mata , all she need shine ganin Adnan Tama rasa yadda zatai , maybe ma yanacan kasar wajen yamanta da ita yasami wasu matan, hakannan taji ranta ya fara baci ko kishine oho,
Afiya na gefenta tana Danna waya , cikin son ta Sami information gun Afiya Sabrine ta kalli Afiya Dan pictures take gani awayarta , ganin Adnan kan wallpaper d'inta yasa tad'an gyara kwanciyar tare da matsawa kusa da Afiya had'e da fad'in “kamar Adnan ba”dan duk tunanin Sabrine afiya batasan da soyayyar su da Adnan ba, murmushi Afiya tayi tace“eh Yaya Adnan ne yayi kyau ko” Bata amsa Mata ba illa Kara tambayarta datai “tunda ya tafi kasar wajen kunyi waya kuwa”ganin da gaske information take nema hakan yasa Afiya gyara zama tare da sanar da ita halin da Adnan ke ciki, sannan ta Dora da fad'in “nayi tunanin duban brother kikazo mafa”
Zunbur Sabrine ta Mi'ke tana dafe kirji jin yadda yake bugawa tare da fad'in “innalillahi wainna ilaihirrajuun you mean Adnan na cikin gidannan? ” d'aga mata Kai Afiya tayi had'e da furta “eh yaya ussy ke kula dashi”mikewa Sabrine Tai hawaye suka fara zubo Mata tacewa Afiya “inane room d'insa please Afiya help me I need to see Adnan right now”ganin yadda ta furgice yasa Afiya fad'in “cool down Sabrine kibari da safe kya ganshi Mana please”girgida Mata Kai tayi tana riko hannun Afiya tana d'an ja alamar ta Mi'ke tare da fad'in “no please show me his room kinji”

“okay okay cool down karki karyamin hannu I will tell you his room , Yana upstairs left hand d'inki”
Aiko karasa Bata Bari tayi ba ta saki hannun Afiya tayi waje ganin yadda ta fita babu ko hijabi and gashi kayan bacci ne. Ajikinta yayi bala'in showing jikinta impact ko bra Babu yasa Afiya fad'in “sabrine nashiga uku please Kizo kisa hijab ”ai ko jinta Sabrine batai ba tayi sa'a babu kowa a palour d'in hakan yasa direct ta nufi upstairs kamar yadda Afiya ta sanar Mata haka tabi location d'in

Allah ya temaketa Dan fitar Daddy kenan daga dakin yazo dubawa yaga koya farka but still bacci yake hakan yasa ya Kara d'an lullubeshi Dan yanayin weather d'in is so cold , Sabrine Saida ta tabbatar daddyn yashiga room d'insa sannan ta fito daga inda ta buya , gently ta bud'e kofar without making any sound

Yana kwance Yana bacci cikin kwanciyar hankali da alama daddy drip ya cire Masa, ajikin kofar ta tsaya tana Dan kallo face d'insa duk da kasancewar duhu ne but bedside lap ya d'an haska Masa fuska, ahankali take takawa har zuwa bed d'in , tausayin Adnan ne yayi mugun kamata , fuskansa ya fad'a sosai sai haske da yakara Yi sosai hakannan taji yamata kyau afuska , batasan lokacin da ta fara hawaye ba bakinta ya fara furta“ni inacan Ina jin haushinka kan kamanta Dani, inacan Ina tunanin kana kula wasu matan not me , without knowing you are here dying for my love sweet Adnan”kawai tasa kuka tawani irin kwanciya jikin Adnan tana ri'keshi tana kuka with so much tears, hawayenta ne suka sauka fuskar Adnan, aikam kamar cikin bacci yakejin wani irin sanyi da iska me dad'i had'e da wani dumi bamai cutarwa ba, ahankali ya fara motsa hannunsa Yana Dan motsa jikinsa, ganin Kamar motsi yake yasa Sabrine Dan dakatawa da kukan datake hade da Mi'kewa kad'an tana kallon fuskar Adnan, ahankali yafara motsa idonsa Yana kokarin bud'e idonsa, da sauri Sabrine ta sa hannunta ta kunna fitilar dakin bame haske sosai ba, ahankali ya fara bud'e idonsa tun Yana ganin Sabrine dishi dishi har ya ganta sosai, hannunsa ya d'an d'ago Yana kallon Sabrine Dan he wanna confirm ko itace kokuma mafarkin daya Saba ne, Amma ga mamakinsa yaji ya ta'ba soft skin d'in Sabrine, da sauri ya janye hannunsa tunowa da yadda yaga daddy na fara'a Yana gaisawa da mutane alamar finally an daura auransa da Sabrine, ahankali yaji wani hawaye ya zubo Masa me zafi Yana kallon face d'in Sabrine ahankali har zuwa kirjinta , saurin d'auke idonsa yayi saboda abinda ya gani , cikin muryar da Bata fita Adnan ya fara fad'in “sabrine shikenam na rasaki, shikenam mafarkina bazai cika ba? Shikenam you are not my, gwarama na mutu akan…”saurin Dora hannunta tayi saman bakinsa batare da ta daukewa ba ta sakar Masa wani murmushi tana kallon tsantsar idonsa ta fara fad'in “yaya Adnan I'm yours for ever ever, this lady here will soon become your wife , you are mine Yaya Adnan isn't what you are thinking”kallonta kawai yake, yanajin kamshin turaren hannunta na dukan Masa hanci Yama gaza gane metake Shirin fad'a, ganin be gane ba yasa ta Kara sakar Masa murmushi ta riko hannun sa tare da fad'a masa abinda yafaru in brief Dan labarin nada yawa , tun kafin ta karasa Adnan yawani irin jawota jikinsa ta fad'a ahankali ya fara lalubar kunnenta had'e da fad'in “please sweetheart what you are saying da gaske ne pls stop kidding me”samun kanta tayi da sa bakinta kunnansa cikin slow voice “i'm not kidding darling Sabrine is yours for ever Dan Allah kaji sauki kaji”wani irin matseta Adnan yayi jin yadda voice d'inta ke karade ko Ina a jikinsa, wani Dan Kara Sabrine Tai tare da fad'in “yaya Adnan zaka karyane”shikanshi besan lokacin dayawani had'e bakinsa Dana Sabrine ba out of control yafara wani irin eheeee kugane mana(😂🤭)

*duk wacce taji dad'in this page expecially masoya Adnan let me see your comments hhh lol Adnan you are too bad bakada kunya sam🤦🏻‍♀️*

*💫FORBIDDEN LOVE💫*

4️⃣2️⃣

Yanayin yadda Adnan ya tashi washe gari abin har mamaki ya bawa LEC A. M Dan Sam be tunanin zai samu sauki recently haka ba , Banda yanda yad'an rame zakace bemayi wata cuta ba,

Da safe kafin su fita breakfast bayin deeja ta bar dakin Afiya cikin tsokana take ta kallon Sabrine, tsarguwa Sabrine tayi da kallon bayin fitowarta daga wanka hakan yasa tana goge ruwan jikinta da towel tacewa Afiya “why staring at me haka Afiya”murmushi Afiya tayi taje har inda Sabrine ke zaune gaban mirror tace“just want to find out Ina sister na ta kwana jiya Dan harnai bacci banganta ba” wani irin lumshe ido Sabrine Tai tuno yadda Adnan ya haukatar da ita da kiss ita kanta batasan lokacin da murmushi ya kubuce Mata ba , hakan yasa Afiya yin dariya tana tafa hannu tare da fad'in “i get it yarinya adaiyi ahankali” tana fad'a tafita tana dariya, kayan baccin da Sabrine ta cire da sauri ta d'auko su had'e da manna hancinta jikin kayan jin yadda kanshin turaren Adnan ke tashi daga kayan, dakyar ta iya ajiye kayan dan gaba d'aya tarasa meke faruwa da ita har tsigar jikin tashi take

Lokacin data gama shiryawa tasa wani Riga da skirt da atamfa daya fito Mata da sharp yamata kyau , tunda tafara nufo dinning table d'in Adnan ya kafa Mata ido gaba d'aya Yama manta akwai daddy zaune agurin har ta iso ta zauna kujerar dake facing tasa

Sosai wata irar kunya taji ta kama hajiya saleemeh Dan tunda Sabrine tazo wasan buya suke da ita , takasa manta abinda taiwa mahaifiyarta, fatanta Allah yasa Sabrine Bata kallonta da abin
Yadda Adnan ya zuba Mata ido taji gaba d'aya Sam ta kasa sakewa ahankali ta d'ago kanta tare da gaishe da LEC A. M dake kusa da ita, cikin jin dad'i ya amsa sannan ta gaishe da hajiya saleemeh , dasauri ta amsa Dan batai tunanin Sabrine zata gaidata ba

Dakanta hajiya saleemeh Tai serving Sabrine , godiya Sabrine Tai Mata sannan taja pancake d'in data saka Mata , ta d'auka zata fara ci Adnan ya kwace na hannunta , da sauri Sabrine ta d'ago ido ta kalleshi, yawani mugun kashe Mata ido d'aya Wanda yasa Tai saurin sunkui da kanta kasa ta d'au wani, daddy na kallonsu Amma yayi Kamar bema gani ba , hajiya saleemeh ce ta Dan doki kafadar Adnan had'e da harararsa batare da tace komi ba

Haka Adnan yashigo da wata sabuwar tsurfa saiyayi karyar bashida lafiya abawa Sabrine food d'insa ta kaima sama kawai Dan yayi hugging d'inta, gaba d'aya Adnan ya fara kwancewa Sabrine notin kanta , kullum cikin tunaninsa take har wani imagine take ita dashi in one bed omo ranar za'a kashe arna for sure yadda ya kamata

All abubuwan dake faruwa daddy yayi noticing hakan, shiyasa yayi deciding mayar da Sabrine gaban Granny Dan ya fuskanci Sam Adnan bashi da kunya kada ya jawo musu abin fad'a

Ranar kam tana kwana biyar daddyn yace inta cika week zata koma gida aikam tad'an ji daddy koba komi tabar Adnan karya zautar da ita

Ana washe garin zata tafi taci kwalliya misalin Sha d'aya tayi kyau over sun fito harabar gidan ita da deeja Dan garden d'in gidan zasuje, daidai lokacin Adnan ya fito cikin haddaiyar shadda Banda d'aukan ido babu abinda take , yayi kiba lafiya ta samu sosai
Gano su Sabrine yasa yayi gurin su , tunda ta ganshi murmushi kawai ta ke nenuna komi agaban deeja ba yace“auta kamar naji mama nakira fa”aikam cikin rashin wayo deeja ta nufi gida da Dan sauri
Ganin ta tafi yasa Adnan duban Sabrine tare da fad'in “madam zomuje Adan rakani hospital mana”zatai magana yace pls
Babu yadda ta iya haka ta bishi suka tafi


Har cikin office d'insa sukaje , Yana ta tsokanarta Time dinda Atipha ta kawo ta hospital d'insa, sai turo baki Sabrine take Yana ta Mata dariya

“yaya Adnan pls ka kaini gidansu Atipha kaji ”bemata musu ba yace ta zauna ta jirashi zaije duba patient, bedawo ba sai wurin Sha biyu sannan ya dauketa suka nufi gidan su Atipha da zumud'in San ganinta bayin sunyi parking atafkeken gidansu Atipha a Dan ladi na sidi wato gidan Yan majalissu kasancewar mahaifinta house rep ne a majalissa

Zata bud'e kofa ta fita Adnan na sani ya kulle kofar motar, Dan juyowa Taita kalleshi kamar zatai kuka tace“yaya Adnan what now please open the car I can't wait to see Atipha batasan zanzo ba fa impact batasan Ina kano ba”

Dan turo baki Adnan yayi alamar Sabrine taimai kiss, no'ke kafad'a Tai alamar bazatai ba Dan taga abin na Adnan Kara yawa yake,

Ganin ta Bata Rai yasa bece Mata komi ba ya bud'e Mata kofar da sauri ta fita da d'an gudu gudu

Wani mugun murna Atipha tayi ganin Sabrine Dan kwata kwata batai expecting ganin Sabrine ba, kusan awan Sabrine d'aya Dan Saida Tai sallah , shima Adnan d'in. Cikin masallacin gidan yabi jam'i

Da Sabrine zata tafi maman Atipha gift kala kala tabata Tai Mata godiya sosai, har gurin motar Adnan ta rakota be fito daga motar ba illa bud'e motar da yayi alamar Sabrine ta shigo

Tasan fushi yake hakan yasa ta bud'e bayan motar ta zuba abin da aka Bata sannan ta bud'e tashiga, Dan sunkuyowa Latipha Tayi tare da fad'in “ranka ya dad'e ango”shikanshi besan ya saki murmushi ba jin ta kirashi ango , angonma na Sabrine,

“ayi hakuri mun barka kuma Bata fadamin tare kuke ba daka shigo ai kun gaisa da mom”
Murmushi yayi tare da fad'in“no Nina ce mata Zan jira ana ya kowa da kowa”

Kowa lafiya , sannan ta Dora da fad'in “sabrine shikenam goben Zaki tafi gida”daga Mata Kai Sabrine Tai alamar eh , sannan Tai Mata adduar sauka lafiya , har suka bar gidan tana tsaye sannan ta juya ta koma gida


Ganin yadda shi a Dole bacin Rai yake abinma saiya Bata dariya, hakan yasa cikin Rad'a tace“sweetheart”kara had'a fuska yayi shi adole bacin Rai, yasata Kara fad'in “darling me” shima ya Kara had'e rai , saikawai ta rintse ido tace “0kay I agreed let see where I will give you the kiss”aikam yasaki murmushi tare da juyowa ya kalleta , tsabar rashin kunya harda turo baki alamar ana zatai Masa kiss , babu yadda taiya Amma takiyi Masa a baki kawai ta juyar da fuskarsa Tai Masa a kumatu, aikam ya langwabar da fuska yace“ina Zaki gobenne wai”

Babu ko shakka tace“gida”

“amma nizan kaiki ba”

“a'a” tabashi amsa

Jiyayi gaba d'aya mood d'insa ya d'auke besan meyasa yakeson Sabrine har haka ba , wallahi yarinyarnan kullum cikin Zuciyarsa take kawai gwarama ai aure ahuta Kar ya ja magana


Yayanayin parking yad'an juyoya kalleta ,
“sabrine will you come please”kamar zaikuka yayi maganar Dan he really want to hug Sabrine before she leave, Bata gane meyake nufi ba hakan yasa yace

“come where Yaya Adnan”babu ko. Shakka yace “my room tonight please Kinga tafiya Zaki baki tausayina”dan zaro ido tayi tana tuna abinda ya faru ranar yadda kiss kawai Saida taji jiki aikam ta. Girgiza Kai tace“aika banni zuwa Yaya Adnan”tana fad'a ta bud'e motar ta fita had'e da bud'e bayan motar ta kwashi kayanta ta barshi zaune acikin motar..


*💫 HARAMTACCIYAR*💫

Please Login or Register in order to submit comment