Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Taya zakai haka Adnan fisabillahi na amince da duk abinda kace meyasa zaka tafi kuma eh meyasa zaka tafi ragone Kai Ashe shiyasa zaka gudu”sosai take kuka, cikin murya da Bata fita sosai Adnan yace“tabbas Sabrine hakika ni ragone akan soyayyarki bani da abinda zanyi sai hakan I can't stay Naga ana daura muku aure da mahaifina I can't Sabrine that's why I'm here to say bye I'm so sorry Sabrine” yafad'a Yana kasa da kansa Dan beso ma yaga kukanta“dan Allah Adnan karka tafi ka barni stay here with idan Ina ganinka saina fijin confidence na auran daddy Amma karkai min nisa hakan Dan Allah”tayi maganar tana had'a hannunta guri guda tana rokar Adnan , girgiza Kai Adnan yayi alamar bazai iya ba hakan yasa Sabrine fad'in “tonaji kaje ko Ina ne but promise me you will attend my graduation and weeding fatiha promise me zakazo aurena Dan Allah Adnan”kallanta yayi yama rasa ya amsa Mata ko karyayi hakan , d'aga Mata Kai yayi da murmushin da gwara mutum yayi kuka kozai Sami sauki acikin ransa sannan yace“dont worry Sabrine indai akan wannan ne I promise zanzo kinji goodbye Allah ya sada mu da alkahairinsa”yana fad'ar hakan ya bud'e motarsa had'e da Yi Mata key sannan ya ja yabar gurin ” kallon motar Sabrine kawai take hawaye gaba daya kamar kunnashi akai Yama ki tsayawa gaba d'aya har ta Dena ganin motar Adnan , jirijri taji tanayi hakan yasa ta ja kafafunta dasukai Mata nauyi, ahankali take tafiya tanaganin dishi dishi ta tekamakon Allah takai kofar dakinsu jikinta du ba kwari ta bud'e kofar tashiga, ganin yadda take da sauri Latipha ta taso da sauri ta kamo Sabrine tana fad'in “lafiya meke faruwa Sabrine”kallanta kawai Sabrine take tama kasa magana sai kallon Latipha kawai take hakan yasa tace“kiyi magana mana baki da lafiya ne” kawai Sabrine ta kwanta ajikin Latipha kamar wata karamar yarinya ta rushe dawani kuka me tsuma zuciya had'e da fad'in “latipha ya tafi he is gone wai sallama yazomin dagaske ya tafi”tagane me takeson ta fad'a hakan yasa Latipha Bata Hana Sabrine kuka ba gwara tayi Kota Sami sauki azuciyarta ita kanta Latipha Saida taji hawaye ya zubo Mata ganin yadda Sabrine ta riketa sosai tana kuka Kamar wata itace mahaifiyarta

(Kai ya Salam ni babyluv am crying too!!)

Tunda Adnan yabar gun Sabrine sai asannan yaji wasu hawaye masu zafi sun zufo Masa Yana iya jin yadda hawayen ke da dumi a fuskarsa, direct MALAM AMINU KANO AIRPORT yahuce yasan Usman ya jiransa acan Dan sunyi waya shi zai dawo da motar Adnan Yakuma tabbatar Masa saura minti talatin jirgin zai tashi, yana zuwa kuwa yango Usman na jiransa , yana yin picking ya fito gaba d'aya fuskarsa babu annuri Usman dinne ya temaka Masa ya d'auko akwantinsa Dan yawancin abinda yadauka takardunsa ne sai wasu file masu amfani sai kayansa set biyu Suma d'in Dan yasan bayaso Yana zuwa ya fita

Saida suka daidai inda zasu rabu kawai Adnan yaji he need someone to hug, kawai ya rungume Usman, yafahimci situation d'in da Adnan ke cike kuma yasan komai ayanzu Dan Saida ya takurawa Adnan sannan ya fad'a masa abinda ke faruwa Dan ko baban sa Alhaji Hassan be fad'awa Usman abinda ke faruwa da abokin nasa ba

Bubbuga Masa baya Usman yayi yace“take heart buddy be men pls be strong inshallah komai zaiyi daidai buddy sorry”ahaka Adnan yayi sallama da Usman ya tafi , befi mintuna goma ba Usman yananan tsaye yaji an sanar ta tashin jirginsu Adnan , sannan ya shiga mota ya nufo gida……


_comments and share habibties_

*💫FORBIDDEN LOVE💫*


3️⃣4️⃣

_babyluv_
_07038524543_

*Dedicated to dear NIMCYLUV (sarauta) and my group members I love you all*


Tunda Sabrine ta tabbatar cewa Adnan Yama bar kasar gaba d'aya hankalinta yayi bala'in tashi Dan wallahi jitake ko joke Adnan kemata Amma babu yadda ta iya Dan takira wayarsa sau ba adadi Amma Ina bayama tafiya haka ta gaji ta hakura, batin kuka kuwa harsaida ya zamto tanemi hawayen da zaizubo Mata ta ji dad'i ta rasa, Latipha face kullum ke tausarta akan tayi hakuri abinda Adnan yayi shine daidai koba komai zata samu sauki daga rad'ad'in datake ciki muddin ta tabbatar yayi nesa da ita, hakan kuwa akai Dole Sabrine haka ta tursa sawa kanta Dena tunanin Adnan duk da tasan hakan bamai yiwuwa bane , Amma ta kudire aranta cewa inshallah bazata bawa Adnan kunya ba akan auran LEC A. M zata tabbatar Masa da sanda takeyi Masa dakuma tabbatar Masa tana girmama rayuwar mahaifinsa data iyalansa baki daya
Ayanzu babu abinda Sabrine ke tunani sama da Granny d'inta ta yadda zata kar'bi abun tasan yadda Granny ta kar'bi Adnan zataso ace ta aure shi Amma idan taji sa'banin Adnan ya zamto ma mahaifinsa zata aura abin kam is hardly Granny ta yarda ta aure shi.

Ranar da LEC A.M ya tabbatar wa da hajiya saleemeh Adnan yabar kasar ne gaba d'aya fad'in tashin hankalin data shiga ba Mai misaltuwa bane ,kuka kam babu kalar Wanda batai ba har Allah ya Isa taiwa LEC A.M ganin ta shine sanadin faruwar komi kuma tace taga ta yadda zai auri Sabrine d'in da har akanta d'anta Wanda tafiso fiye da komi yayi Mata nisa har ya iya barin kasa batare da izininta ba akan yanaso mahaifinsa yasamu farin ciki,hakannan taci alwashin farin cikin da Adnan ke fatan mahaifinsa ya samu har yabar kasar inshallah Allah bazai sameshi ba saidai sa'banin hakan
LEC A.M yashiga matukar tashin hankali Dan abin matar tasa harya fara huce gona da iri,abin har mamaki yake bashi zai iya cewa aduk iya kacin zaman sa da hajiya saleemeh Bata ta'ba kwatanta Masa hali irin wannan ba hassalima zai iya cewa baisanta da wannan dabiar ba ,Amma gaisawa sunce baka sanin wani abu akan mutum har sai wani abun ya zamto sila


Misalin karfe hudu na yamma Sabrine na zaune Latipha na tayi Mata hira as usual wayanta yad'au Kara ganin LEC A.M ke Kira yasa gaban ta yayi mummunar fad'uwa Dan rabonta dashi tunda sukaje duba shi asibiti ganin haka yasa Latipha fad'in “ya dai meye ya faru Naga mood d'inki ya canja” nuna Mata wayar Sabrine ntai tare da fad'in “kinga LEC A.M ke Kira na”

Da sauri Latipha tace“tosai me ki picking call d'in mana dama Ina da niyyar nace Miki ki kirashi Amma tunda ya Kira aisai ki d'aga ko”kamar zatai kuka Sabrine tace ke'be fuska tare da mikawa Latipha wayar tace“ni wallahi naji bazan iya d'agawa ba Latipha bansan meyasa ba nauyinsa nake ji”ture hannunta Latipha Tayi tare da fad'in “kinga Dan Allah ki d'au wayar nan”zata d'auka kenan Kiran ya katse ,ganin hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tana ajjiye wayar,kafin ta d'auke hannunta wani Kiran yasa ke shigowa babu yadda ta iya ganin yadda Latipha ta zuba Mata ido yasa ta d'au wayar had'e da Kara ta akunne batare da tace komi ba tana kallan idon Latipha alamar nifa bazan iya d'innan ba

Shikanshi rasa mezai cemata yayi Dan harga Allah yanason Sabrine Amma sai yaji acikin Zuciyarsa Kamar abin da yake bekamata ba be kuma dace ba Amma wata zuciyar saita ce Masa hakan dayake daidai take
Yarda da abinda Zuciyarsa tace yayi sannan ya Mi'ke daga kujerar office d'insa dayake Kai sannan yaje zuwa ga window d'insa yace“babu gaisuwa yau Sabrine”yake tayi Wanda yafi kuka ciwo tace“ina wuni”be amsa illa cewa yayi “come to my office right now inyaso saina amsa ko”yana fad'ar hakan ya yanke wayar sannan ya nemi guri ya zauna yana tunanin abinda yakamata yacewa Sabrine

Itakam tanajin ya yanke wayar ta kalli Latipha tare da fad'in “i can't Latipha ni bazan iya zuwa gurinsa ba ”

“to ai shikenam Ashe alkawarin da kikaiwa Adnan karya ne”babu yadda Sabrine ta iya haka ta Mi'ke tasa hijab d'inta har kasa ta nufi office d'in LEC A. M, koda taje kofar office d'in kasa shiga tayi Dan jitai jikinta yad'au rawa Amma daurewa tayi ta Murda kofar tashiga with sallama, ganin ta da yayi ba Karamin farin ciki yayi ba hakan yasa yace Mata ta Sami guri ta zauna, babu musu kam ta zauna kan kujerar kanta akasa tana Wasa da zoben hannunta
Gyaran murya yayi kafin ya kalli Sabrine yace“kiyi hakuri Sabrine nasan Ina matsanta Maki Amma ni kaina bansan dalilin yin hakan ba inaji araina Kamar duk abinda nake Yi tilasta min akeyi Amma wallahi acan cikin zuciyata nikaina inaji abinda nake ba daidai bane ” d'agowa Sabrine Tai ta kalleshi wallahi duk abinda yake fad'a ta yarda dashi kuma ta tabbatar da abinda yake fad'a , cikin sanyin jiki Sabrine tace“sir kadena fad'ar hakan nida kaina na yarda Zan zauna dakai ba Dole akaimin ba fatana Allah yabamu fahimta juna”jin abinda Sabrine tace yaji Zuciyarsa tamasa sanyi Amma ya dubeta Dan yanason karantar wani abun sannan yace“amma Sabrine inaji araina ba kyauta nashiga tsakaninki da Adnan Wanda hakan Sam be daceba”daga Masa hannu Sabrine Tai ta dakatar dashi idonta ya taru da hawaye jin ya ambaci Adnan hakan yasa tace“banaso kanamin zancen Adnan saboda bekamata ba kawai kabar zancen sa xaifi”ta fad'a tana goge kwalla a idonta, jinjina Kai yayi Dan yagane bataso aimata zancen Adnan Kamar yadda shima Adnan d'in yasa kafa yabar kasar, dubanta yayi sannan yace“yanzu Sabrine inaso naje gurin maga batanki domin neman izinin su Amma yakike gani”saida gabanta ya Fad'i jin ya ambaci sanarwa dasu Granny tasan halinta tsaf zatace Bata amince ba gwara ita Sabrine d'in ta fad'a Mata da bakinta zata fi amincewa hakan yasa Sabrine fad'in “na fahimta Amma zaifi ace ta fara ji daga bakina kuma ninasan Kai mutumin kirkine bawani zance bincike dazan Bari ayi akanka and pls Sir pls Sir idan ba damuwa inason weeding fatiha d'ina ranar graduation d'ina pls”kallanta yayi da mamaki jin abinda tace hakan yasa yace“sabrine how can that be possible niyakamata naje har gida na nemo aurenki Taya kuma zaa daura Miki aure a kano Taya haka zai yiwu”goge hawayenta tayi da bayan hannunta tace“yeah nasani but nafison in family na sukazo graduation d'ina inyaso ahuce mosque nanan school sai a daura anan I will make my Granny understand”jinjina Kai kawai LEC A. M yayi Dan all abinda Sabrine keyi yasan dalilinta be huce avoiding d'in San Adnan ba hakan yasa yace“idan har sun amince babu matsala your wish is my command”daga Masa Kai kawai tayi , sannan yace is okay Zaki iya tafiya , taji dad'in fad'in hakan Dan sotake tayi kuka sosai ko zataji dad'i aranta hakan yasa ta Mi'ke da sauri had'e da fad'in “thank you”har takai bakin kofa cikin sanyin jiki LEC A. M yakira sunan ta hakan yasa ta juyo ta kalleshi sannan yace mata“im sorry kinji”da sauri tafice daga office d'in tana fita Saida tasami gurin da babu mutane kasancewa yamma ce aikam kawai tasa kuka, Saida tayi me isarta sannan ta goge fuskarta ta nufi hostel

Kasancewar sun gama test gaba d'aya final exam suke jira kawai gashi kuma ya kasance Friday hakann taji tanason zuwa gun Granny kodan ta kwanta a cinyarta kotaji dad'i, hakan yasa adaren ranar ta Kira Granny tace ta turo driver gobe da wuri ba Karamin dad'i Granny taji ba Dan taji Yan kwanakinnan tana jin Sabrine cikin damuwa so gwara kawai tazo taji halin da take ciki sannan Tai Mata zancen Adnan Dan sotake tanayin graduation Tai Mata aure danshi ne kwanciyar hankali kowane iyaye

Aikuwa karfe Sha d'aya na safe driver yazo Dan dama tagama shiryawa jiransa take , Yana zuwa kam suka d'au hanyar kaduna ita kanta Latipha tana ganin Sabrine ta tafi ta shirya ta gudu gida Dan dama ita saboda shakuwar da sukai da Sabrine kawai Tai deciding ta koma hostel da zama

Yadda Granny taga Sabrine ta rame Saida taji tsoro Amma batace Mata komi ba Saida ta Bari washe gari ta gama hutawa tazo ta lafe kan cinyar Granny tanai Mata susar Kai sannan Granny tace
“nikam Sabrine har kiyi cuta ki warke ban sani ba wakika samu Yana kula dake har haka keda ko ciwan Kai kikai saikin fad'a min” Kara gyara kwanciya tayi kan cinyar Granny tare da fad'in “granny nifa lafiya ta lau ni banyi cuta bafa I'm absolutely fine”murmushi kawai Granny Tai tace “maji zuwan da dawowar kam” sannan tace“kishirya to da yamma kije gidan su yusrah Kinga tana ta zuwa weekend ko kinzo Amma Bata saminki”dan turo baki Sabrine Tai tace“ni I will call her nacemata tazo kawai”sarai tasan me take gudu shiyasa bazata ba hakan yasa Granny fad'in “gaskiya kam kinki yayanta ba Dole ki 'ki zuwa ba saboda kinajin kunya ko”batace Mata komi ba ta juya Dan wallahi abinda take jin nauyi kenan karsu had'u da daddyn farouk dashi kanshi farouk d'in

Granny ce tace wa Sabrine “kinga Mi'ke muyi magana”saida gabanta ya Fad'i Amma Mi'kewa tayi zaune tana kallan Granny taji mezatace“nikam Sabrine ya maganar da mukai dake akan farouk da Adnan kinmin shiru har yanzu kosokike na yanke hukunci ne? ”ta Yi maganar babu ko alamar Wasa a tattare da ita hakan yasa Sabrine taji gwara ta sanarwa da Granny abinda ke faruwa hakan yasa ta riko hannun Granny tace“granny I want to tell you something Dan Allah ki fahimci abinda Zan fad'a kinji Granny ta”kallanta Granny kawai keyi sannan tace “ehen inaji Fad'i naji” Kara ruko hannun Granny Tai sannan ta fara fad'in “granny ni duk cikinsu biyun babu Wanda Zan aura daga Adnan har farouk”cike da mamaki Granny tace“to saiwa kenan”cikin sanyin murya tace“granny ni LEC A. M Zan aura”

“what!!!! LEC A. M kuma baki da hankaline Sabrine banason shiriri ta” jitai ta Sami kwarin guiwa hakan yasa tace“Allah ba shiriri ta nake ba Granny I want to marry LEC A. M not Adnan”bata Rai sosai Granny tayi tace“leave my hand Sabrine” ganin yadda Granny ta Bata Rai sosai yasa kwalla taruwa idon Sabrine tace“granny Dan Allah kiyi hakuri ki fahimci abinda Zan fad'a miki kada kiyi saurin yanke hukunci”gamsuwa da abinda Sabrine tace tayi hakan yasa tace“wane Abu Zaki fad'an na yarda kenan wai tukunna ma jinake wannan LEC A. M shine baban Adnan wai Taya Zaki fara hakan wannan ai cin fuska ne ” hawaye ne yazubo Sabrine jin Granny ta ambato Adnan hakan yasa Sabrine kwashe duk abinda ya faru har izuwa condition d'in daddy dayake ciki har izuwa hukunci da Adnan ya yanke dakuma barinsa kasa dakuma alkawarin da taiwa Adnan na cetar rayuwar mahaifinsa Datai alkawarin Yi sannan ta kalli Granny with full tears on her eyes ta Kara holding hannun Granny sosai tace“granny nasan Zaki fahimceni shiyasa na yanke hukuncinnan sannan Granny wallahi daddyn Adnan zai iya rasa Rai akaina Granny, narasa wane irin so yakemin haka Wanda na Gaza gane wanne yafi tsakaninsa da Adnan ” shiru Granny Tai tana duban Sabrine sosai sai take gani kamar mahaifiyar Sabrine ce agabanta kamar yarinyarta ce alokacin da itama take Mata magana makamanciyar wannan hakannan taji tsoro ya kamata na loosing d'in Sabrine tace“kinga Sabrine na fahimceki da duk abinda kika fad'a Amma I will think about it, zamui magana da alhaji karami bawai ban amince ba Amma Sabrine Dole zan bincike akan shi LEC A. M idan har babu wani bad habit dayake dashi fine saina aura Miki shi kinji”dasauri Sabrine tace“granny idan na rantse Miki da Allah wallahi bazan kaffara ba LEC A. M mutumin kirki ne banaso kiyi wani bincike Granny wallahi LEC A. M mutumin arziki ne bashida wani bad habit” shiru Granny Tai sannan ta girgiza Kai had'e da fad'in “bazan ja dake ba Sabrine Allah yasa hakanne mafi alkhari arayuwarki fatana duk inda Zaki kisamu farin ciki fiye da Wanda kike samu anan gurina kin”

Amin Sabrine tace sannan ta kalli Granny tace“sannan Abu na biyu Granny inason cire Adnan daga cikin rayuwata ne Wanda nasan hakan bazai samu ba har sainayi aure shiyasa nake aranar graduation d'ina nakeso adauramin aure a masallacin. School d'inmu Granny ni banason wani taro Dan Allah everything ahakura dashi idan yaso bayan graduation d'in nawa koda sati biyu ne saina tare”

Harararta Granny tayi tace“abin naki kuma yayi yawa Sabrine bikin jikartawa wadda nake ji da ita ace bazan taro ba haba”kamar zatai kuka tace“dan Allah Granny ni kibar komi karkiyi banaso , ”. Babu yadda Granny ta iya haka ta gasgata abinda Sabrine tace Mata Dan harga Allah tanason ta bataso tayi wani abu Wanda bataso shiyasa kawai Granny ta hakura ta amsawa Sabrine sannan tace sa fara Shirin biki tunda dai graduation d'in kam ya taho
Awashe garin ranar kam Granny ta tara dukkan Wanda tasan yakamata agidanta ciki harda mahaifan farouk ta sanar musu cewa Nan da wata d'aya da Yan kwanaki zata daurawa Sabrine aure domin ta bada ita, dukkansu mamaki ya kamasu taya Granny zatai haka sai kace wata tufafi zatace wai ta bada ita , Amma kasancewar yadda kowa ke shakar Granny sai ya zamto babu Wanda ya iya cewa uffan sai Allah Sanya alkhari ya kaimu lokacin hajiya Granny kam ta amsa da Amin,abinda yasa Granny tace ta bada Sabrine kam bataso ya kasance sunce ta goyi bayan yarinya karama alhalin basusan abinda ita Granny ta sani ba gwara ta Dora lefin a kanta

Maman farouk ce na tayi karfin halin fad'in “to yanzu Yaya babba Aina sirikin namu yake ko zaizo ya gaishemu mu shirya, kicin kicin granny tace sa had'u ran daurin aure kowa yasan shi tunda shima zai zamto member na family , babu Wanda ya Kara cewa uffan har taro ya tashi
Ranar kam Sabrine ita kad'ai tayi kukan da ya isheta domin alokacin ta tabbatar ta rasa Adnan tarasa mafarkin rayuwarta abinda yafi d'aga Mata hankali shine kowane hali Adnan ke ciki oho……

Washe gari ranar lahadi da safe Saida Sabrine ta had'a Granny da daddy awaya suka gaisa sannan yaji da kunnansa cewa Granny ta amince, samun kansa yayi shiba farin ciki ba shikuma ba bakin ciki ba yarasa wanne zaiyi
Da yammacin ranar lahadi driver ya dawo da Sabrine makaranta sakamakon exam dazasu fara Monday, Latipha ta Riga Sabrine dawowa Dan ita da safe ta dawo

Kwanci tashi babu wuya ya rage saura sati d'aya graduation sannan kuma da daurawa Sabrine aure, inkaga Sabrine zaka zacci kamar ba bikinta zaai ba saidai ta Kara Rama sosai takuma Yi duhu domin yadda suke exam babu ji babu gani babu kuma interval , ayanzu kam Sabrine tacire komi aranta sai jarabawar da suke domin ita tafi damunta arai , Granny kam shirye shirye sosai takeyiwa Sabrine Dan tayi alkawarin ko an daurawa Sabrine sai tayi wata d'aya sannan zata kaita dakin miji domin saita had'a ta sosai , itakam hajiya saleemeh tanaji tana gani haka ta hakura tazubawa sarautar Allah ido domin tagama give off sannan dama malam ya tabbatar Mata cewa tsakanin Adnan da mijinta to gashinan kuma ya tabbata ayanzu tasan asirinta zai tonu aikam du ta rame
Aranar da take sanarwa yaranta Mata cewa babansu zaiyi aure Afiya ba Karamin tashin hankali tashiga ba Dan cewa tayi har school d'insu Sabrine saitaje taci Mata mutunci Amma hajiya saleemeh ta dakatar da ita ta tabbatar Mata indai har ta sake taje saita Bata Mata Rai aikuwa wuni tayi tana kuka Tama kiyiwa banbanta magana, ita deeja kam ko ajikinta Munna ma tayi zata Sami step mom……


*Congrats Dad hhh lol😍😆🥲*


*💫FORBIDDEN LOVE💫*

3️⃣5️⃣

_Rasheedah sulaiman shuaibu(BABYLUV)_
*07038524543*

Ahankali motoci kala daban daban ke shigowa cikin makarantar BUK dake garin kano, yanayin yadda school d'in ke acike misalin karfe Sha d'aya na safe zai tabbatar ma tabbas akwai special. Occasion dake Shirin faruwa acikin school d'in duba da yadda family kala daban daban ke a cikin school d'in, wasu rukunin motoci Wanda zasu Kai akalla guda goma suka shiga yin parking ajere, ahankali mutanen dake cikin motocin suka fara sakkowa Wanda most of them Maza ne suna sanye da saffin haddaun shaddodi Banda walwali babu abinda suke, fuskokinsu d'auke da fara'a , wasu big cars ne guda hud'u Wanda cikinsu duka Mata ne suna cikin kwalliya ta cikkakun masu kud'i suke sakkowa , hajiya dije wato mahaifiya ga farouk itace ta bud'e wa Granny mota ta sauko tare d'auko Mata jaka sannan ta rufe kofar tare da fad'in “hajiya alhaji ne ke tambayar number d'in LEC A. M wato angon Sabrine tunda Kinga karfe Sha biyu zaa daura auren ko” jinjina Kai Granny Tai , hakannan Granny kejin gabanta nawani irin fad'uwa Wanda Sam ta kasa sanin meyasa , zuciyarta ce ke Mata aiyane aiyane atun Daren jiya Wanda take alakanta hakan da daurin auren Sabrine, hakannan tsoro da fargaba ke ziyartar zuciyarta akan biyewa Sabrine datai akan binkicen LEC A. M hakannan taji wani irin faduwar gaba yasake ziyartar ta jitsi zuciyarta nasan ganin this LEC A. M suyi magana ta ganshi ta tabbatar da hankalin shi da nutsuwarshi ko hankalin nata zai kwanta,
Gaba dayansu cikin wani babban hall dake cikin buk suka nufa Wanda da alama anan zasu yada zango before sukoma kaduna, farouk na hango kusa da mahaifinsa fuskarsa kam babu yabo babu kuma fallasa Amma da alama tilasta masa akai zuwansa

Yusrah dake cikin kwalliya me kyau ta zauna kusa da Granny had'e da fad'in “granny can't wait to see angon Sabrine nasan he's damn handsome nasan yadda take had'addiya haka yake I'm so happy Sabrine is getting married”hajiya dije ce ta dubi Sabrine tare da fad'in “yusrah banason shirme bakya ganin cikowar mutane ”

Da hannu Granny taiwa alhaji isah alamar yazo dukda Yana cikin taron mutane ya gano hakan yasa yazo yad'an risina gaban Granny tare da fad'in “hajiya gani kinyi kira”wayarta ta Mi'ka masa tare da fad'in“kafita inda babu hayaniya ga lambar angon Sabrine d'in call him for me kace lallai yanzu yazo ya sameni kaji nasan yananan kusa”karbar wayar alhai isah d'in yayi kafin ya kalli Granny da fad'in “hajiya ai yanzu muke Shirin tafiya masallacin dazaa daura auran and nasan shima Yana cikin mutane ai da kin Bari an daura auran saimu taho tare zaifi ai ko”girgiza Kai Granny tayi narashin gamsuwa da abinda yace tare da fad'in “no issa important call him I need to see him ”be tambayeta dalili ba ya juya Dan aiwatar da abinda ta sashi ya fice daga hall d'in gaba d'aya saboda hayaniyar family dan duk yawanci family ne agun da important mutane dasuka zo ba Kamar normal daurin aure ba

Cikin babban masallacin dake cikin buk Wanda yake sanne duk da yadda yanayin daurin auren yazo bakowa ya sani ba Amma hakan be Hana masallacin cika ba yawancin familyn daddy ne dakuma Yan uwa da abokan arziki wa inda bazaa rasa ba,
LEC A. M na zaune acikin masallacin yaci manyan Kaya shadda mekyan gaske Banda walwali babu abinda take Yi yaci babbar Rika Wanda tasha aiki tun daga sama har kasa, Yana zaune kusa da alhaji Hassan yaji wayarsa ta d'au ringing duk da bajin ringing d'in yake ba Amma kasancewar da akwai vibration awayar yasan cewa kiransa ake , hakan yasa yamike tare da yiwa Alhaji Hassan nuni da hannu cewar Yana zuwa

Fitowa Wajan masallacin yayi inda Babu hayaniya sosai

Please Login or Register in order to submit comment