Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma before ya d'au Kiran wayarta yanke , ko second biyu baai ba wani Kiran ya sake shigowa hakan yasa ya d'aga had'e da sallama, dagacan alhaji isah ya amsa tare da gaisawa cikin aminci sannan ya gabatar Masa da kansa tare da sheda Masa Kiran da Granny ke Masa na gaggawa, Saida gabansa ya Fad'i domin tun da safe dama yake jinsa wani iri fatansa Allah yasa badai hanashi auran Sabrine zaai ba dan dama Yana ta tunani akai, amsawa Alhaji isah yayi sannan ya tabbatar Masa cewa Yana zuwa yanzu

Komawa yayi inda alhaji Hassan yake yad'an Rad'a Masa akunne , sannan gaba d'ayansu suka Mi'ke sukayo waje , LEC A. M ya dubi alhaji Hassan had'e da fad'in“wallahi tsoro nakeji kada naje ko hanani Sabrine zaai”murmushi alhaji Hassan yayi yace “banda abinka ai Dole sai dangin yarinyar Nan su ganka Taya dama zaai aure basusanka ba ni dama Naga wautarsu saboda aure ba abin Wasa bane , Amma abinda zai faru ga mota tacan sai muje mutafi ko kaga saimu dawo tare da su masallacin muyi abin da yakawomu ko” yarda da abinda yayan nasa ya fad'a yayi sannan ya juya suka nufi parking space dake massalacin domin amsa Kiran Granny……




Babban filin tashi jiragai wato malam aminu kano international airport dake 50 danjuma way cikin garin kano
Yadda mutane ke saukowa daga jirgin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali gwanin birgewa , ahankali shima ke sakkowa daga cikin jirgin, cikin shigarsa ta ba haushe yaci shadda gezner Banda walwali babu abinda take wadda taci aiki irin na kasar waje , idon sa manne da farin medical glass Wanda kake iya hango fararan idanunsa , sai akwatin dake hannunsa, yayi haske yayi kyau tubarkalla Masha Allah duk da yadda ya rame hakan behana kyawunsa bayyana ba yayi masifar kyau gaskiya ADNAN wutar kyaune( kowa yace Masa ya dawo oho mtwee)

Ahaka ya fito Yana Jan wata karamar akwati mekyau , bayin fitowar sane zuwa gurin da Yan uwa ke mararin d'aukan Yan uwansune yasa yad'an fara hange hange, Usman ya hango Yana Dan d'ago Masa hannu shima yaci farar shadda mekyau, Saida gaban Adnan ya Fad'i azuciyarsa kawai yake fad'in “innalillahi wainna ilaihirrajuun”ahaka ya karaso inda Usman yake sukai hugging juna sannan suka rankaya inda yayi parking motarsa kafin su shiga motar ne Adnan ya dubi Usman tare da fad'in “please tell me anyi daurin auren ko dad ya auri Sabrine ko” shiru Usman yayi masa sannan ya kar'bi jakar hannunsa ya bud'e bayan motar yasa sannan ya rufe, had'e da dawowa ya Bud'ewa Adnan car d'in tare da fad'in “shall we”shiga yayi ba tare da yayi magana ba sannan shima Usman d'in ya shiga had'e dayiwa motar key cikin kwarewa da driving ya fara tuki batare daya bawa Adnan amsa d'in saba

*More comments more typing😂 please share habibties*


*💫FORBIDDEN LOVE💫*


3️⃣6️⃣


Sunayin parking gaban hall d'in gaban LEC A. M yayi wani mugun bugawa da har saida alhaji ya kalle shi had'e da fad'in “lafiya dai”dan kirjinsa ya dafe tare da fad'in “bansan meyasa Amma jinake kamar akwai abinda ke Shirin faruwa Dani wallahi gaba daya na rasa nutsuwata” d'an dafashi yayi sannan yace “kaga kayi addua kawai inshallah babu abinda zai faru sai ikon Allah”yarda da abinda yayan nasa yace yayi , hakannan yaji bayasan shiga taron mutanen shiyasa ya yanke shawarar Kara Kiran lambar daaka kirashi d'azu, ringing biyu Granny ta d'aga wayar ganin sunan LEC A. M akai , sotake suyi magana ta nutsuwa hakan yasa Granny tabawa LEC A. M umarnin ya jirata awani Karamin hall dake kusa da Wanda suke ciki domin safiyin magana ta fahimta, amsawa yayi sannan dashi da alhaji Alhaji Hassan suka fito suka nufi inda Granny ta ambata, Yana zuwa me gadin gurin cikin girmamawa dasauri ya bud'e musu kofa suka shiga sannan LEC A. M yabashi umarnin idan Granny tazo yabarta tashigo Dan gurinsa tazo me gadi ya amsa cikin girmamawa
Kiran alhaji isah da alhaji Musa wato mahaifin farouk sannan da hajiya dije Granny tayi dukkan su sannan ta basu umarnin su biyota zuwa gurin LEC A. M domin su ganshi idan sun yaba da hankalinshi shikenam sai su huce daurin auren kawai, babu musu dukkan su suka bi bayan Granny d'in Dan suna matukar girmamata

Tun kan su karaso me gadin ya taso da sauri had'e da rusunawa ya gaishe da Granny had'e da shauran gaba d'aya sannan ya tabbatar musu cewa LEC A. M naciki Yana jira dukkan suka nufi cikin gurin

Yana zaune kirjinsa kawai bugawa yake hankalinsa yakasa kwanciya alhaji Hassan ne ke karfafa Masa guiwa akan inshallah babu abinda zai faru sai alkhari Amma hakan San besa hankalinsa ya kwanta ba burinsa yaji Kiran me Granny ke Masa , Yana cikin wannan tunanin ne Granny ta Shigo da sallama fuskarta a sake Dan magana suke da alhaji isah Yana sanar Mata an tabbatar Masa LEC A. M mutumin kirkine bashida wata matsala shiyasa abun yayi Mata dad'i
Fuskar Wanda ta ganine yasa taji kafarta ya wani mugun rikewa dawata faduwar gaba at the same time har Saida jakar hannunta ya Fad'i saboda yadda hannunta ya d'au rawa tashiga d'aga hannu tana nuna LEC A. M da hannu bakinta ma yakasa magana gaba d'aya jikinta ya d'au rawa dakyar ta iya furta “ *Abdurrashid*” shima d'in wata irar zabura yayi ya Mi'ke ganin fuskar Granny , hakannan yaji kansa na wani irin juyawa , abubuwa da yawa suka shiga dawo Masa kansa,fuskar Fatima ce lokaci d'aya ta bayyana cikin kwakwalwarsa har zuwa idanunsa , Kamar me neman wani abu ya taho da sauri Yana dube dube , har kusan gurin kofa ya fita Yana dubawa ganin bega abunda yake nema ba hakan yasa ya dawo Yana nuna kofar waje Yana fad'in “fatima! Fatima fa tana ina” wani irin gigitaccen Mari Granny tayi masa afuska hawaye na zubo Mata afuska, daga alhaji Hassan har alhaji Musa da hajiya dije mutuwar tsaye sukai ganin LEC A. M kowa abubuwa daban daban na Masa yawo cikin zuciya shikuwa Alhaji Hassan Banda salati cikin Zuciyarsa babu abinda yake Dan Yama kasa yunkurin komi, ko ajikinsa marinda tayi masa Dan ko jinsa beyi ba Dan Kara cigaba yayi da waige waige Yana fad'in “fatima fa Dan Allah Ina Fatima innalillahi wainna ilaihirrajuun”kawai ya zube agurin ya fashe da kuka , awata kujera Granny ta zame ta zauna tare da fashewa da kuka abin tausayi hajiya dije ce ta d'an riko Granny gudun karta zame ta Fad'i, cikin kunar Rai da tsantsar bacin Rai alhaji isah ya nuna LEC A. M tare da fad'in “meye ya kawo ka Nan akan me zakazo Nan , saboda rashin tsoron Allah , akan me zaka nuna kanka ayanzu ? Akan me yanzu zaka bayyana alhalin kace babu mu babu Kai !! Wato saboda kasan babu ranta yanzu ko ” yadaga hannu zai Mari LEC A. M Granny Tai saurin dakatar dashi cikin muryar kuka , Mi'kewa tayi ta tako har inda yake tare da fad'in “meye ya kawoka Nan gurin akan me zakazo Nan gun tukunna ma Ina LEC A. M d'in kenan abokansa ne ku ko? Shine dalilin kasancewar ku anan tabbas idan har ka kasance abokinsa bazan ta'ba bashi auran Sabrine ba domin shima zai kasance me irin halinka ne ” tayi maganar cikin bacin Rai, alhaji Hassan ne yayi kokarin furta “hajiya duk wannan abin bashine mafita ba kamata yayi mu zauna muyi magana domin daga mu harku muna cikin rudani, sannan LEC A. M d'in dakike magana bawanine ba face Abdurrashid”da wani irin sauri Granny tayi baya tana riko hannun alhaji Isa hawaye na zubo Mata jikinta na rawa ta rufe bakinta tana fad'in “innalillahi me muke Shirin aikata wa”...

*💫FORBIDDEN LOVE💫*

3️⃣7️⃣

Alhaji Hassan ne ya dubi su alhaji isah Wanda fuskokinsu babu walwala ko kad'an, abin yayi mugun bashi mamaki shi atunaninsa zasui murnar ganin kaninnasa ne Amma kuma saiyaga sa'banin hakan, toko dai akwai wani abu dabai sani ba ne? Kodai akwai lauje cikin Nadi ne?

Alhaji Hassan ne cikin magana me cike da sanyin jiki yace“ Dan Allah kuyi hakuri yakamata muzauna muyi magana akan abinda ya faru shekarun baya domin ninaga sa'banin abinda nake tunani tabbas akwai abunda mu duka bamusan dashi ba , sannan batun Hana auran Sabrine ni aganina bekamata ku Hana abdurrashid auranta ”katseshi Granny Tai da fad'in “auran Sabrine kake magana Hassan, kasan kuwa wace Sabrine har da kake fad'in haka,? ”ta fad'a tana dubansa , zaiyi magana takatse shi da fad'in “idan har soyayyar da LEC A. M keyiwa Sabrine ta aure yake Mata to tabbas wannan soyayyar sunanta HARAMTACCIYAR SOYAYYA Dan kuwa Sabrine dayake gani jininsa ce ! Sabrine 'yarsa ce ta jini hakika yayi HARAMTACCIYAR SOYAYYA”shiru tayi kafin ta nuna LEC A. M Wanda kansa ke kasa Banda hawaye babu abinda yake tare da fad'in “Allah ne ya nuna Masa ishara akan wofantar da yarsa ta jini dayayi , sannan hakika jini baya buya wannan dalilin yasa yaji yanason Sabrine har yayi tunanin auranta to ita d'in jinin wadda ka wulakantace ita din jinin wadda ka rabu da ita rabuwa ta rashin mutunci ita d'in jinin Fatima ce” wani irin zabura daga alhaji Hassan har LEC A. M sukai jin abinda Granny ta fad'a, durkushewa LEC A. M yayi agaban Granny cikin kuka yake fad'in “ innalillahi wainna ilaihirrajuun dama Fatima tana da ciki Ashe dama zan Kara ganin Fatima wallahi wallahi ba abinda kike tunani bane ni ban saki Fatima ba na rantse da Allah ni ban saketa ba wallahi ki kirata naganta ki tambayeta agabana ni bansaketa ba wallahi”kawai ya fashe da kuka, wani irin kallo Granny keyiwa LEC A. M Dan Sam ta Gaza gane abinda yake fad'a , cikin bacin Rai tace“wato akirata ka tambayeta kake cewa? Daka tabbatar Bata raye kake fad'ar hakan ko dakasan cewa Fatima ta rasu Dole kace haka ”

“Ta rasu ”alhaji Hassan ya fad'a cikin kidima, shikuwa LEC A. M wani irin zabura yayi kamar Wanda baya tare da hankalinsa yace“dan Allah hajiya ki hukun tani Kota wace hanyace akan abinda kike tunanin na muku Amma kada ki hukuntani tanhanyar sanar min cewa Fatima ta mutu, wallahi kullum inaji arayuwata kamar akwai abinda baya kusa Dani Wanda ya kasance rayuwa agareni sai ayanzu nasan cewa Fatima ce nifa bansan meya faru ba muna zamanmu lafiya kamar yadda kika tafi kika barmu wallahi bayannan bansan komi ba”ya fad'a Yana Kara fashewa da kuka , tabbas ayanzu Granny ta yarda da duk abinda yake fad'a dama tayi tunanin hakan Dan abin har kullum Yana Bata mamaki burinta ta had'u dashi taji yadda abubuwa suka faru hakan yasa Granny duban LEC A. M tare da fad'in “abdurrashid tashi ka zauna inaso muyi magana wadda tun shekarun baya nake bukatar amsar su”tashi yayi ya zauna Yana Yana goge hawayen daya kasa tsayawa a fuskarsa , sannan Granny duk tabawa kowa damar ya zauna ciki harda alhaji Hassan

Gyaran murya Granny tayi sannan ta dubi LEC A. M dayama kasa had'a ido da ita tace“abdurrashid hakika ban ta'ba kokwanto akan halinka na kirki ba sannan ban ta'ba tunanin abinda ya faru zai faru ba , ayau inaso ka bayyana min abun da yawakana tsakanin ka da Fatima” kukansa ne ya karu kamar wani yaro ya fara magana cikin muryar kuka“wallahi Granny inason matata kullum burina naganni tare da ita , Fatima Bata ta'ba batamin Rai ba har kawo yanzu danake Miki maganar Nan wallahi idan Zaki yanka no bazan fad'a Miki komai akai ba
Saboda bansan komi ba”yakai karshan maganar dawani kuka me cike da tausayi, alhaji Hassan ne ya dubi Granny tare da fad'in “hajiya wallahi ni kaina har yanzu Ina cike dason sanin abinda ya wakana tsakanin Fatima da abdurrashid , gashi iya lalubena narasa inda Zan sameku domin naji komi daga bakinta ”

Sautin kuka sukaji daga bakin kofa hakan yasa dukkan su saurin juyawa domin suganewa kansu Wanda ke kukan,

Hajiya saleemeh ce Wanda duk taji abinda ke mafaruwa , taso ace ta juyawa ta koma batare da sanin kowa ba , Amma Sam ta kasa juyawa domin wannan ranar take gudu Dan tasan koba yauba Dole sai asirinta ya tonu hakika tana matukar tsoron abinda LEC A. M zai yanke akanta idan har yaji sillar afkuwar komi cewa itace , Amma akullum idan ta tuna abubuwan datayi tanaji zuciyarta babu dad'i koda bacci take Bata samin nutsuwa hakika gwara yau ayi komi ya Kare domin tunda ga Granny koba komi mahaifiyar Fatima ce tanemi yafiyarta

Tana kuka haka take takowa cikin hall d'in sautin kukanta Yana karade hall d'in, ganin matarsa ce hakan yasa yayi saurin tasowa Yana duban hajiya saleemeh tare da fad'in “saleemah meye ya kawoki nan? Meye yasaki kuka? Duk akan auran nawa ne” gaba d'aya ya Watso Mata tambayar lokaci d'aya” dur kushewa tayi gaban LEC A. M tana wani kuka me cike da ladama tafara fad'in “baban Yara ka yafemin Dan Allah ka yafemin”ta fad'a tana Kara fashewa da kuka , juyowa LEC A M yayi suka had'a ido da alhaji Hassan sannan ya juya ya dubi saleemeh had'e da fad'in “wane lefi kike magana ne saleemeh nibaki min komi ba , yarinyar Nan da ake magana wadda kike kishi akai babu aure tsakaninmu itadin yarinyata tace saleemeh ita d'in jinace” yafad'a yanajin ciwon abinda yafaru yadda ya dinga cewa zai auri Sabrine Ashe yarsa ta cikinsa ce, shiyasa yakejin soyayyarta daban acikin Zuciyarsa, hakika be ta'ba tunanin auran Sabrine ba , tunani yayi akan zatai aure ta rabu dashi tayi masa nisa hakan yasa ya yanke hukuncin aurenta koba komai zai dinga jinsa kusa da ita batare da tayi masa nisa ba

Tashi hajiya saleemeh tayi ta taka har gaban Granny ta dur kushe agabanta tare da goge hawayen fuskarta ta fara magana Kamar haka“hakika babu abinda zai iya sanar Miki akan abinda ya faru Yakuma Yi sanadiyar rabuwarsa da yarki wato Fatima”cikin rashin fahimta Granny ta dubeta Dan Sam Bata santa ba, alhaji isah ne ya kalleta tare da fad'in “kedin wacece ”

“matar abdurrashid ce”alhaji Hassan ya bashi amsa, sai asannan Granny ta Kara maida hankalinta kan hajiya saleemeh tare da fad'in “idan ban tambayi abdurrashid ba akan rabuwarsa da yarinyata wakikeso na tambaya? Kodai kina da masaniya akan abinda ya faru ne”ta fad'a cikin nutsuwa domin taga Kamar akwai abinda hajiya saleemeh keson fad'a da sauri ta d'aga Kai hawaye na sake zubo Mata ta fara fad'in “hakika dama nasan wannan ranar tananan zatazomin , domin sihiri baya tabbata hakika komi ya faru tsakanin Fatima da mijina nice sanadi , nice sanadin komin” wata irin zabura LEC A. M yayi zuwa inda hajiya saleemeh take yawani irin finci Kota tare da jijjigata Yana fad'in “mekike nufi saleemeh kece sanadin rabuwata da Fatima ? ”ya fad'a Yana Mata wani irin kallon , tsanarta lokaci d'aya ya dirar Masa zuciya , Alhaji Hassan ne ya taso tare da janye LEC A.M yace“yimin bayani saleemeh ma , hakika dama ban yarda da auran ki da abdurrashid ba na lokaci d'aya, Amma kasancewar yadda kike girmama ni da dukkan shauran family hakan yasa ban zurfafa bincike akanki ba domin matata Tasha sanar min cewa Bata yarda dake ba Amma Sam na Gaza gasgatata , Amma yanzu inaso ki dubi Allah kifada Mana abinda kika aikatawa Fatima” due kushewa tayi sosai a kasa ta saki kuka , Granny ce tayiwa

Alhaji isah magana cewa yaje dashi da alhaji Musa my tabbatar sun sallami kowa sannan subawa mutane hakuri

Cikin biyayya suka Mi'ke Dan aiwatat da abin da tasasu sannan ta juyo zuga saleemeh tare da fad'in “ina so ki bayyanamin abinda ya faru Wanda kike neman gafara akansa”cikin sauri hajiya saleemeh ta fara Basu labarin abin da ya faru dakuma yadda akai ta auri LEC A. M…

*💫 HARAMTACCIYAR 💫*
*💫SOYAYYA💫*

3️⃣8️⃣

Hakika tunda Allah yasa na Dora idona akan abdurrashid duk duniyarnan naji babu wani Rai Dana ta'ba so kamar sa, ni nayi karatu a saudia ne Kamar yadda alokacin shi Yana daf da kammala karatunsa acan , cikin ikon Allah lokacin daya gama karatu saboda hazakar sa suka nemi daya zauna a can yayi musu aiki Wanda aikinnan ba Karamin aiki bane domin bazaka samu albashi me tsoka ba idan a Nigeria zakayi, kamar yadda kowa yasani cewa irin wannan aikin a saudia indai har mutum bashi da aure to tabbas bazasu Bari yayi musu aiki ba domin wannan itace dokar saudia, alokacin abdurrashid hankalinsa ya tashi domin babu wata yarinya dayake soyayya da ita alokacin, duk da shekarun mu d'aya dashi Amma hakan besa na fasa Sansa ba, Danaga alamar kamar be gane Sansa nake ba hakan yasa na damu sosai Amma hajiya zainab wadda ta kasance aminiya agareni tace kada na damu takuma bani shawarar kan nashiga jikinsa muzama abokai kasancewar garinmu daya a Nigeria wato kano
Haka kuwa akai munzama abokai sosai nida abdurrashid soyayyarsa na Kara shiga zuciyata Amma kuma shi agurinsa abin yasha banban domin na fahimci babu soyayyata a tare dashi kwata kwata alokacinne Wani ai aki ya kawo mahaifin Fatima Nan saudia idan Zan tuna alokacin aikin wata uku ne kawai zai d'auke shi lokacin yazo daidai da ummara hakan yasa yataho tare da mahaifiyar Fatima da ita kanta Fatima suka tare awani gidan maaikata Wanda ya zamto kusa da gidan Abdurrashid, tunda Abdurrashid ya kyalla ido yaga Fatima shikenam ya rikice Yana sonta Dan kullum sai yaga lokacin da suke fitowa daga gida , aduk lokacin Fatima tana lura dashi saidai tana da karancin shekaru, adaidai lokacinne saudia suka Kara matsantawa Abdurrashid akan maganar aure shiyasa yaga bashi da za'bi illa wannan yarinyar domin yaji kullum sonta karuwa yake a Zuciyar sa hakan yasa ya tinkari mahaifinta da maganar Amma Sam yaki amincewa yace yarinyarsa karatu take alokacinne ya sameni da maganar, jinai kamar nai hauka jin cewa Yana son wata bani ba Amma haka na daure na bashi shawarar yaje gurin mahaifiyarta domin zatafi fahimtarsa, cikin ikon Allah ta Fahimce shi takuma San muhimmancin aikin dayake kokarin rasawa, tasami mahaifin Fatima dakyar ya amince Amma da sharadin bayan an daura aure Dole zai dawo Nigeria ya Had'a shi da iyayensa dakuma Yan uwansa , sannan kafin auran yace Dole saiyaga wani nasa sannan Dole yayi masa alkawari Fatima zatai karatu anan haka kuwa akai domin dama yayan abdurrashid wato alhaji Hassan yazo umara saudia hakan yasa ya kaishi gidan su Fatima akai magana tsayayyiya sannan mahaifin Fatima ya fahimci su abdurrashid masu mutuncine cikin abinda befi wata d'aya da rabi ba aka daurawa abdurrashid aure da Fatima anan saudia

Soyayya da shakuwa me karfi ta kullu tsakaninsu Dan Fatima nasansa sosai ganin yadda yake kula da yarsu hakan yasa sukaji hankalinsu ya kwanta daga mahaifiyar Fatima har mahafinta , haka suka tafi suka barta a saudia gurin abdurrashid
Alokacin Kamar Zan mutu domin hankalina ya balain tashi gaba d'aya abdurrashid ya juya mini baya d'an lokacin danake samu muyi magana naji dad'i gaba daya na rasashi, cikin kuka na fad'awa hajiya zainab tacemin karna damu, lokacin iyayen Fatima sunyi sati biyu da komawa Nigeria hajiya zainab ta daukeni mukaje gurin wasu Mata da ni bansan suwaye ba Amma dai zuwa sukai Dan ba larabawa bane, haka na zaiyyana musu bukatata akan nidai sonake abdurrashid nima ya aureni kamar yadda ya auri Fatima , Amma suka tabbatar min indai har Yana tare da Fatima to tabbas auranmu bazai taba yiwuwa dashi ba, tun kafin nai magana hajiya zainab tace a kashe auran abdurrashid da Fatima arabasu sannan asa soyayyata a Zuciyarsa, nidai banji dad'i ba Dan naso ace kawai ya aurenine munzauna mu biyu Amma banaso a raba auransu

Sati daya atsakani kuwa yafara juyawa Fatima baya had'e da rashin mutunci kala kala sakamakon lemon danaje har office d'insa gaisheshi na bashi matsayin kyauta kuma ya kar'ba yasha
Babu dad'ewa yaje ya biyawa Fatima kudin jirgi domin dawowa zuwa Nigeria sannan ya had'a Mata da saki guda uku , lokacin befi wata shida da auransu ba Dan alokacin saura wata biyu sukoma gida shi da ita kamar yadda yayi alkawarin cewa zai dawo ya had'a su da iyalansa

Lokacin da yasaki Fatima lokacin ya dawo gurina da soyayya Kamar hauka Dan mutuminnan baya barina kullum Yana makaranta Muna hira har cewa yake nazo gidansa mu kwana Amma Sam naki amincewa
Naji tsoron Kar mahaifan Fatima suzo saudia gurin abdurrashid hakan yasa muka koma gurin matannan domin inaso Kota halin Yaya ne inaso abdurrashid ya koma Nigeria da zama inaso ya Dena aiki anan saudia, haka kuwa akai nanda Nan yacemin shi bayason aiki anan zai koma gida da zama
Dama ninasawa zuciyata barin school Dan bazan iya kyale soyayarsa acikin zuciyata ba haka nabiyoshi muka dawo gida
Babu yadda iyayena basui ba akan nakoma saudia Amma fafur naki nakuma shedamusu aure zanyi babu yadda suka iya haka suka dauramin aure da abdurrashid shine muke har kawo yanzu.……”

Kawai ta fashe dawani irin kuka na tashin hankali, tunda LEC A. M yaji abinda yake fitowa daga bakin matarsa Banda salati babu abinda yake, jiyake Kamar dukkan zaman su da hajiya saleemeh kamar a mafarki suka yisu ba agaske ba domin gaba d'aya ayanzu bayajin wata soyayarta kokadan saina wani irin tsanarta dake taso Masa cikin Zuciyarsa

Jinjina Kai kawai Granny Tai tana Tino abubuwan dasuka faru bayin dawowar Fatima , hakika dama kafin mahaifin Fatima ya rasu ta shaida Masa cewar hakika akwai wani dalili babba tsakanin rabuwar su Fatima Dan ita kanta Fatima batasan tana da juna biyu ba Saida tayi rashin lafiya sosai kamar zata mutu aka kaita asibiti likita ya tabbatar musu tana da ciki har wata uku

duban hajiya saleemeh Granny tayi tace“hakika kin aikata babban zunubi , abinda Zan fad'a Miki anan shine cewa kikoma ga Allah kiyi istigfar domin Allah gafururrahimu ne sannan maji rokon bawansa ne, sannan kiroki mijinki ya yafe Miki abinda kikai kokyasamu rabauta Rana gobe kiyama”
Cikin fuskar ladama hajiya saleemeh ta juyo zuga LEC A. M da Yama rasa abinda zaice tunda Granny ta shaida Masa mutuwar Fatima gaba d'aya ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali hakan yasa ya d'agawa saleemeh hannu alamar baya bukatar neman yafiyarta sannan yayi Mata umarnin kanta tashi ta fita baya bukatar ganin ta , cikin kuka ta d'au Jakarta ta fita cike da danasanin abinda Tai dakuma kunyar yadda ta tozarta a idon mijinta kuma uban yaranta


Har kasa LEC A. M ya durkusa gaban Granny tare da fad'in “hajiya hakika bani da bakin yimiki magana Amma inada bakin dazan nemi gafararki , tabbas banyi adalci ba namuku alkawarin kulawa da Fatima Amma na gagara yin hakan Ina neman yafiyarki Dan Allah ki yafemin”murmushi Granny tayi sannan tace“dan Allah Mi'ke abdurrashid hakika abinda ya faru babu sa hannunka aciki domin baka da lefi, saidai inaso na tunasar dakai akan yawan azkar hakika Sakaki da mutane keyi akan azkar Yana kawo saurin kamun sihiri ajikin mutum kaji ni nayafe maka Allah ya yafemu baki d'aya”wani hawayen farinciki ne ya zubo Masa ya Mi'ke tare da fad'in “Allah ya Kara girma Allah kuma ya Kara lafiya”alhaji Hassan ne ya taso ya karaso inda suke da murmushi fal a fuskarsa yace“hakika rashin sani yafi dare duhu lallai wannan

Please Login or Register in order to submit comment