Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi da za'bi ne illa yayi hakan Dan indai yabari yarinyar Nan ta 'bace wa Ida nunsa besan ya zaiyi ba kuma wata kila yadda yake duba marasa lafiya Shima sai yaje ga anduba shi,Yana niyyar magana wayar Sabrine ta fara ringing ,a kusan tare suka kalli wayar ,ganin me Kiran wayar yasa Sabrine ta 'Dan juyawa Adnan baya Dan yafara takura mata da kallo ,yadda yake kallonta da yadda yake magana saikace irin yansanta dinnan aganinta fa kenan
Yadda ta juyawa Adnan baya yasashi karewa bayanta ido tunda ga kanta ahankali yake saukar da idon sa har zuwa daidai hips d'inta ,wani irin bugawa kirjinsa yayi da karfin gaske Yakuma kasa dauke ido daga hips d'inta,jiyayi kafarsa takasa d'aukansa babu yadda ya iya haka ya zame ya jingina a jikin bango ba tare da ya d'auke ido daka kallonta ba



Cikin karamar murya Sabrine taiwa LEC A.M sallama ,cike da gwarin gwiwa da jin dadi ya amsa had'e da fad'in“ patient Yaya jikin hope an salla meku ”d'an juyawa Sabrine tayi ahankali ta kalli inda Adnan ke jingine a bango Kamar jira yake dama ta juyo suna had'a ido yawani kashe Mata ido d'aya aikam da sauri ta juyar da kanta tana fad'in ‘no sir Amma yanzu am with the doctor Yana niyyar sallamar mu” jin ta ambaci suna tare da likitan Saida kirjin LEC A.M yawani mugu mugun bugawa da karfin da Saida ya Mi'ke daga kujerar office d'in dayake zaune ,Yama rasa mezai ce mata ,cikin murya cike da saita kansa ya furta“you mean Adnan ?”

“nikam ban sanshi ba Amma dai shine zai sallamemu Ina office d'in sama right now ”
Da sauri LEC A.M ya furta “bashi wayar ”
Juyowa Sabrine tai tana furta Allah yasa dai ba kallon nawa yake ba a Zuciyar ta ,aikam kamar ta sani tana Kara juyowa suka Kara had'a Yana jingine abango ya hard'e hannayansa a kirji babu ko kunya ya tsura mata ido ,
Abinne yafara bawa Sabrine haushi ta turo baki had'e da mikawa wayarta inda Adnan ke tsaye tana Kara turo baki tana 'Dan kautar da kanta gefe cikin magana irin ta jin haushi ta furta“ here you go ,zaai magana da Kai a waya ” kallon ta yayi had'e da kallon hannunta kafin ahankali ya tashi daga jinginar dayayi ya iso daidai inda take tsaye ,Yana sani wurin karbar wayar ya had'o harda Yan yatsunta Yana Kara kallon fuskarta Dan so yake kawai yaga ta Kara turo masa wannan mitsitsin Karamin bakinta , da sauri Sabrine ta janye hannunta tana kallon fuskarsa Dan Shima d'in ita yake kallo

“hello” was abinda Adnan ya furta daidai lokacin daya kai wayar kunnansa har lokacin idonsa nakan Sabrine data sunkuyar da kanta hakannan yacigaba da kallon kananun gashin dasukaiwa goshinta ado Kamar anjera

Jin muryar dad d'insa yasashi saurin d'ago da wayar daka kan fuskarsa Yana kallon screen din wayar Dan ya tabbatar , aikam LEC A. M yagani radau akan screen d'in wayar , dasauri ya maida wayar kunnansa Yana fad'in “hi dad is you, dama this girl dakake min magana akanta itace wannan dad wow dad fantastic I'm so glad”


*Please share and share habibties dakuma comments*👏🏻👏🏻🥰

*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_

1️⃣3️⃣



Yess itace and meyasa kuke tare da ita yanzu I mean meyasa baka sallameta ba tace taji sauki ai”kusan a fad'a fad'a yayi maganar Dan gaskiya tsoron Adnan da Sabrine yake kada Yana gefe suzo su fara soyyaya Wanda Sam shi bazai damu da d'an sa bane saiya San duk yadda yayi ya rabasu bama shi kad'ai ba koma waye zai Gina katanga tsakaninsa da Sabrine saiya ruguje

Jin kamar ran dad d'innasa a bace yake yasa shi saurin fad'in “cold down dad babu abinda da zai faru da ita kaji zan 'Kara dubata ne sainai discharge d'inta”yafa da Yana kallon Sabrine aransa Yana fad'in wannan wane irin so dad yakewa yarinyar nan haka
Abangaren LEC A. M kuwa wata irin ajiyar zuciyar yayi kafin ahankali yace“before I leave nayi clearing bills dinsu so babu bukatar subiya komi”
Murmushi Adnan yayi Yana 'Kara takawa har inda Sabrine ke tsaye Kamar Wanda zaiyi hugging d'inta , Yana kallon 'kwayar idonta sosai itama d'in shi take kallo Tama rasa meyasa take kallonsa
Ahankali ya furta“dad Aida bakaje ka biya komi ba , abinda har zaka iya Yi meyasa son 'Dinka bazai ba impact this girl here Is my…”saikuma yayi shiru Yana 'Dan juya kansa ahankali still Yana kallon tsantsar kwayar idon Sabrine sannan yace“dad I will call you later ”kafin LEC A. M yayi yunkurin magana yaji Adnan ya kashe wayar d'uf , kusan kasa motsi yayi sai bin wayar kawai yake da kallo

Adnan na kashe wayar be ce komi ba yashiga Danna wayar , number d'insa yasa sannnan yayi serving da Adnan Yana gama wa ahankali ya kamo hannunta yasa mata wayar sannan yasaki hannun Yana Mata wani mugun kallo da ita kanta ta kasa sanin meyake nufi , tayama zai rike Mata hannu, duk wannan rikicinna Sabrine da masifar, da tsiwar duk kasa Yi tayi ta tsaya Kamar wadda aka bawa umarnin karta motsa Banda kallon Adnan kar tai komi,
Jin karar bud'e kofa yasa Sabrine saurin juyawa zuwa ga 'kofar , shikam Adnan ko gezau beyi ba daka kallon Sabrine
Latipha kuwa kusan mutuwar tsaye tayi ganin yadda tazo ta samesu shi bemasan ta shigo ba , ahankali ta karasa shigowa office d'in tana fad'in “wato kinbarni a mota Ina ta jiranki kinanan kina so…”saikuma tayi shiru ganin Adnan ya kalleta , tayi saurin canja maganar da fad'in “doctor zamu iya tafiya angama? ”tayi tambayar tana so ta danne dariyar ta Dan taga wannan likitan yakamu da yawa
'Daga Mata Kai yayi alamar eh sannan ya juya zuwa table d'insa ya zauna a kujera ya Dora kafa d'aya kan d'aya Yana kallon su Sabrine da Latipha tari'ke hannunta zasu fita ,Saida suka zo dai dai 'kofar a hankali yace

“latipha”

dan yaji sunan da Sabrine takirata dazu , ahankali daga Sabrine har Latipha suka juyo , nuna Sabrine yayi ahankali yace“ please take care of her , duk Wanda yazo gunta kice mijinta zai iya kasheshi akanta”yana fad'ar haka yatashi hade da d'aukan lapcot d'insa ya juya zuwa wannan dakin da ta hango d’azu
Daga Sabrine har Latipha kallon juna sukai kafin Latipha ta kama hannunta suka fice kowa da tunani a ransa

Har acikin mota Sabrine ta kasa magana tayi , to me wannan yake nufi ne , ita gaba d'aya kanta ya kulle Sam, ganin halin da Sabrine tashiga yasa Latipha dake driving fad'in “meye ne kika wani zauna kikai shiru kodai baki warke ba mukoma kokuma dai tunanin likitannan kike kema kin kamu kamar yadda Shima Naga tsantsar sonki a idonsa Sabrine ? Wai Kinga yadda kuka dace kuwa,? kinaji fa wai fad'amin yake duk Wanda yazo gunki zai iya kasheshi ,wai ko dama ya sanki ne taya za'ai awannan 'kan'kanin ganinki da yayi sau biyu zai kamu haka da sonki gasky Sabrine ke yar baiwa ce



Hararar ta Sabrine tai tana Kara kwanciya a motar sannan tace“dan Allah kibar wannan maganar Latipha ni bawani Sona yake bafa kawai yanamin hakanne ganin yadda babansa kekula Dani shine kawai

Cikin rashin fahimta Latipha tace“babansa kuma like how yimin bayani”

“kekam San zance gareki nifa nacemiki ba Sona yake ba yaran LEC A. M ne fa ”ai tun kafin Sabrine ta 'karasa maganar Latipha taja wani mugun birki tana kallon Sabrine Allah yasa Babu kowa a bayansu da zasu iya sawa wani motar ya bugesu
Dafe kirji Sabrine tai tana fad'in “are you out of your since Latipha meye haka sokike mu mutu ne”

Kara juyowa Latipha tayi gun Sabrine da rudani fal fuskarta tace“gaskiya dai kam am out of my since now saboda abinda naji wai you mean Adnan yaran LEC A.M ne for sure ,kin tabbatar da abinda kike fadi“dafe Kai Sabrine tai tana fadin

“ya Salam Latipha meye abin mamaki aciki Dan ya zama yaran sa shine akan hakan zaki ja mu mutu Muna tafiya”

Zaro ido Latipha tai tana fad'in “waikwa kina da hankali Sabrine Kinga abinda na hango kuwa yasalam”kebe baki Sabrine tayi Dan ita Bata gane what Latipha trying to say ba meye ne aciki Dan Adnan yazama yaran LEC A.M harda zaisa tarikice haka “kedai kika sani Kinga nidai kitemakawa Granny kiyi tuki cikin nutsuwa kikaini lafiya”girgida kai kawai Latipha Tayi sannan tayiwa motar key suka fara tafiya

*Dan Allah ku daure kuyi min share habibties*


*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


*Inaso pls nasan wani abu yakamata kowa yayi comments , cikin Adnan da LEC A. M wakukeso ya kasance da Sabrine , Ina jiran raayinku kowa tarubuta cikin comments d'inta kunji bhabibties*🥰😍😍

1️⃣4️⃣


*Rasheedah SULAIMAN* _(babyluv)_


*Forbidden love group*
07038524543

Koda Adnan ya dawo gida jiyayi shi Sam bazai iya jiran komi ba kawai zai fad'a wa daddy cewar yanason yarinyar Nan Dan yasan zaiyi munnna sosai aganin Adnan tunda dad d'in nasonta haka to tabbas zaiyi farin cikin had'a su tare
Dawannan tunanin Adnan yafito daga d'akisa direct part din mahaifinsa ya shiga , part dinnsa nada girma sosai , ahankali yayi nock Yana jiran abashi permit nashiga Dan haka tsarin gidannan yake indai zakaje part d'in dad d'in to Dole saikai nock anbaka izinin shiga haka hajiya saleemeh duka ta daura yarannata a wannan tsarin
LEC A. M na zaune a parlor d'insa Wanda yayi mugun tsaruwa ga kujerun royal masu balain kyau , Yana zaune da jallabiya ajikinsa akan d'aya daga cikin kujerun d'akin da tunani kala kala aransa Dan ayanzu zuciyar sa tagama yanke masa cewa koma mene Dole kawai yafito ya fallasawa Sabrine sirrin dake ransa koma me zai faru kawai ya faru, dawannan tunanin yaji anyi nock d'in kofa ahankali ya d'ago sannan yace come in
Da sallama Adnan ya shiga kansa a kasa kamar Wanda ya dau kayan wani , ganin Adnan ne yashigo yasashi sakin smile Yana fad'in ”adnan come in , zoka zauna Nan ”yayi masa nuni da kusa dashi Fruit da hajiya saleemeh ta yanka masa agabansa, ahankali Adnan ya karasa inda dad d'in nasa yayi masa showing kusa dashi ya zauna had'e da kallon flat d'in dake gaban LEC A. M Yace “dad can I have it”batare da ya kalleshi ba Dan waya yake dannawa yace “yeah sure”sannan ya d'ora da fad'in “adnan pls ga laptop d'ina can pls d'auko zan tura wani mail yanzu”

“okay dad ”ya furta had'e da ajiye apple d'in daya d'auka Yana niyyar Sha ajiyewa yayi sannan ya Mi'ke, yana d'auko masa yami ka masa had'e da fad'in “here you go Dad” thanks ya furta Yana karbar laptop d'in , sannan ya bud'e ahankali , kan screen d'in laptop d'in idon Adnan ya sauka akai , hoton Sabrine ne ya bayyana sosai tana sanye da kayan matriculation rana ta farko a school , gawannan murmushin nata dake killing d'insa , gaba d'aya saboda dariyar datake hakoran kamar an jere dimple dinta sun loba kana ganinta ahoton yanayinta zai tabbatar maka tana cikin farin ciki sosai
Da sauri Adnan yarike hannun Dad ganin zai gotar da hoton daka gun had'e da fad'in “yess Dad please don't Skip this picture I love it”

“you love it” LEC A. M ya furta had'e da wata faduwar gaba data ziyarci kirjinsa , Amma ahaka ya daure ya furta“ wane hoton kake magana ne Adnan”yayi maganar babu ko alamun Wasa ko fara'a atare dashi

Shikam Adnan with one heart yace “wannan yarinyar taka mana dad ”bekawo komi azuciyar sa ba Adnan yayi maganar dan shi yadda yake jin son Sabrine aransa jiyaye gaba d'aya kunyar dad d'inma ta gudu Dan gani yake baban nasa zaiyi matukar murna inyaji cewar Yana son Sabrine

Ajiye laptop d'in LEC A. M yayi sannan ya zare farin glass d'in dake fuskarsa Yana kallon Adnan yace“and what does that mean yimin bayani yadda zan fahimta me kake nufi adnan”

sunkuyar da kansa yayi and said“dad wannan…. yarinyar taka…nidai kawai ka bani ita Dan I love…?”

“dont even start Adnan , karka sake ka fara !! you mean San Sabrine kake for what reason ehe waye yasaka ehe Tell”all this maganan da LEC A. M yake cikin fad'a yake Dan gaba d'aya zuciyar sa bugawa take na 'bacin rai dakuma fargabar abinda zaije yazo
Shikam Adnan kallan Dad d'innansa kawai yake Dan abin ya mugun bashi mamaki meyasa Dad zaiyi fad'a akan yace yana sonta? meyasa ya Bata Rai haka? Ko tana da wani bakin hali ne haka

Cikin sanyin jiki Adnan yamiki Yana fad'in “relax dad please come down this isn't good for your health, kadena fad'a haka pls zauna”yayi maganar ya dafa kafad'ar daddyn da niyyar ya zaunar dashi, Amma LEC A.M ya ture hannun Adnan d'in Yana facing d'insa Yana fad'in “no Adnan bazan kwantar da hankali na ba untill You promise me bazaka 'Karamin zancen kanason Sabrine ba saika min alkawarin you stop loving her sannan hankali na zai kwanta pls promise me kaji”yayi maganar Yana mikawa Adnan hannu alamar yayi masa alkawari

Kallon dad d'in yayi cikin rashin fahimtar abinda dad d'in ke nufi , Taya ma zai masa alkawarin gyale Sabrine ?meye aibu Dan zuciyar sa taji tanasonta , girgida Kai Adnan yayi Yana matsawa baya kad'an had'e da fad'in “no Dad I love her, Ina sonta Taya zan Dena sonta meye aibu dannaso ta ? Shin tana da wata illa ne Dad please tell me so that I will understand your point , kana tacemin karna sota Amma baka fad'a min dalilin ba dad pls fad'a min aibun ta and I. Promise bazan ko kara maganar ta please”
Cikin kama hannun Dad d'in duka yayi maganar Yana rokansa akan yafad'a da masa meye aibun Sabrine har 'kasa ya durkusa Yana rokarsa,
Ahaka hajiya saleemeh ta bud'e kofa tashigo ta samesu Adnan ya durkusa ri'ke da hannanun LEC A. M Yana rokarsa, kusan tun maganar sa ta farko da LEC A. M yayi cikin d'aga murya tazo huce wa hakannan jikinta yabata something is wrong shiyasa kawai direct tayo flat din alhajin to See what's going on, gashi kuma ta tarar da Adnan ya durkusa Yana rokar alhaji akan abinda batasan meye ba
Cikin mamaki hajiya saleemeh ta tako cikin parlour d'in cikin tafiya irin tasu tamanyan Mata wad'anda jin dad'i ya zaunawa ta karaso had'e da dubansu su duka tana fad'in “what is happening here meyake faruwa ne baban yara, Adnan what's going on. Here”babu Wanda yayi magana daka Adnan har LEC A. M , ganin haka ta 'kara furta“can someone pls tell me meke faruwa haka , alhaji najika Kamar cikin bacin Rai , I hope ba Adnan bane ya Bata ma rai…….?

*Adinga share habibties🤗*
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_


*Naji dad'in comments d'inku sosai habibties my group members Ina sonku sosai Dan haka wannan page d'in nakune kuyi yadda kukeso dashi I love you all ,😍🥰💃🏻*


*BABYLUV*✍🏻
*07038524543*


1️⃣5️⃣


LEC A. M bece komi ba cikin Bacin Rai kawai yajuya yashige cikin bedroom d'in sa , Shima cikin sanyin jiki Adnan yamike yabar parlor d'in yazama saura hajiya saleemeh kadai da duka tazubawa sarautar Allah ido ganin yadda kowa beyi magana ba yabarta agun , harta nufi bedroom d'in daddyn Amma saita tuna Yana cikin fushi ita kam a 'ka'idarta Bata yimasa magana cikin wannan yanayin, kawai saita juya ta fita daga section d'in alhajin zuwa nata section damamakin abinda yakawo haka tsakanin alhaji da Adnan what could that be?

Karfe Tara daidai na dare kenan a kaduna , farouk ke gaban mahaifinsa zaune ya sunkui da kansa kasa da alama magana Mai muhimmanci suke Dan Shima alhaji Adamu kana kallonsa zakasan maganar bata Wasa suke ba ,iya yanayin alhajin zai tabbatar ma da hakan , gyara zama yayi sosai Yana kallon farouk sannan yace“banason magana ta Wasa farouk ka tabbatar da abinda kake fad'an I mean ka tabbatar kanason Sabrine banaso nashiga maganar kazo kanamin Wasa ka tabbatar” 'kara sunkuyar da kansa 'kasa yayi sannan cikin ladafi yafara magaba“daddy ba Wasa amaganar Nan abinda yasa nayima magana yanzuma shine duba da tana shekarar karshe a makaranta"

girgid'a Kai alhaji Adamu yayi cike da gamsuwar abinda farouk ke fad'a masa Dan ya gamsu sannan kuma har zuciyar sa yaji dadi saboda Yana d'aya daga cikin abinda da yasa ya takura Sabrine ta dawo gidan sa Dan soyake ya had'a auransu da farouk saboda ya tabbatar da nutsuwar Sabrine da hankalinta ta Amma hajiya tahana shi Amma bega lefinta ba kasancewar yadda ta rasa mahaifiyar Sabrine , ayanzu zata kalli Sabrine ne da gurbin mahaifiyar ta
Komawa yayi ya jingina da kujera dayake zaune sannan ya Dora kafa d'aya kan d'aya had'e da fad'in “tashi kaje sannan katuromin mahaifiyar ka ”cike da ladabi ya Mi'ke Yana fad'in “to daddy thank you”sannan ya fice har lokacin kansa na kasa
Yana niyyar barin parlor saiga hajiya dije wadda ta kasance mahaifiya wurin farouk , tana ganinshi tayi murmushi tare da fad'in “nikam wannan fara'a haka me aka tattauna ne dakai da mahaifinnaka Naga kana ta sakin murmushi ” shafa Kai kawai farouk yayi yace“mama dama alhaji nakiranki dama nizan huce company ne aimana addua”
"To farouk saika dawo Allah ya kiyaye hanya Allah ya tsare”amsawa yayi Yana fita itakuma ta karasa shigowa parlon tana zama kusa da alhaji adamu kasan cewar kujerar 3ster ce ta zauna had'e da fad'in

“alhaji Ashe ka shigo ai ban Shina ba natsaya Kitchen sannu da wowa”amsawa yayi cike da fara'a sosai da harsaida hajiya dije tace“alhaji wannan farin ciki haka wai nikam me kuka tattauna kaida farouk ne Kai farin ciki Shima hakan Haba nima a sanmin mana ”tayi magana cike da zolaya, sosai farin cikin sa ya karu yadubi matarsa sannan yace“aa danki ne yazomin da wata magana data sani farin ciki sosai hajiya”rike ha'ba hajiya dije tayi tace“tooo farouk d'in to sanar Dani nima na tayaka farin cikin ai”gyara zama alhaji yayi had'e da fad'in “yanzu kuwa, farouk ne daga shigowata yasa mene akan maganar yanaso nayiwa , hajiya magana akan yanason Sabrine kuma yanaso as Soon as Sabrine ta gama makaranta ayi auran”

Murmushin hajiya dije tayi ta dubi alhajin sannan tace“lallai abin farin ciki ne kam sosai , Amma alhaji bawai muyi farin ciki ba shi farouk d'in ya tuntubi Sabrine da zancen I mean ita Sabrine d'in ta amince da zancen kasan fa yarannan namu ka haifesune Amma baka haifi halinsu ba ko, ashawarance abinda zaiyiwu alhaji kabari shi farouk d'in yasami Sabrine d'in su daidaita kansu sannan saimu shiga cikin maganar nidai aganina”

Cike da gamsuwa da abinda hajiya dije tace alhaji adamu ya girgid'a Kai sannan yace“maganarki haka take to Amma ke kina ganin Sabrine zata'ki 'Dan uwanta na jini ne kenan"

Girgida danyatsa hajiya dije tayi had'e da fad'in “bance zata 'kishi bane Amma kasan dai halin yaran zamaninnan sai suce basusan auran zumunci shiyasa kawai Naga ya dace shi farouk d'in ya fara tuntu'barta ”

“zancen banza kenan ”alhaji adamu ya katseta sannan yace“zancen banza zancen hofi kamarya basusan auran zumunci to yanzu ko had'a su mukai sai suyi musu , ai wannan maganar banza ce dacewar basusan auran zumunci”

“kaga alhaji shawarar dai Dana fad'a itace mafita nasan halin yaya indai Sabrine tace batason abu to saita goya Mata baya kasan da hakan”

“Shikenam saikiyi wa farouk d'in maganar”yafad'a Yana cire babbar rigar hajiya dije ta kar'ba sannan yace“ Ina yaran suke naji gidan shiru ”
“suna sama suna karatu ,nakawoma furar nasan for now tayi sanyi ”

“eh ”
Mi'ke wa tayi cikin girmama ta tatafi d'auko masa


**** ****


Saida hajiya saleemeh tashirya sosai cikin kayan bacci doguwar riga irin Mara nauyinnan sannan ta fesa turare mekamshi , dakinsu deeja ta fara shiga kasan cewar Afiya tayi candy yanzu tagama boarding school shekaranta Sha takwas yanzu kasancewar tana da 'Dan girman jiki saika zacci tayi shekara ishirin
Deeja ce tayi bacci Afiya ce da system agabanta tana kwance tana kallo
Saida ta tabbatar duka sun kwanta sannan ta rufo musu d'akin tayi section d'in LEC A. M
Baya parlour d'insa Kamar yadda ya Saba zama adaidai wannan lokacin ta danyi mamaki , haka ta nufi bedroom d'insa ta tura 'kofar had'e da sallama , Yana gefen bed d'insa ya sakko da 'kafarsa 'kasa da laptop ahannunsa Amma gaba d'aya hankalinsa baya kan laptop d'in duk yashiga cikin tunani sosai Amma inbaka lura ba zakace hankalinsa nakan laptop d'in
Har kusa dashi taje ta zauna sannan hankalinsa ya dawo jikinsa yabasar Dan beson tasan tunani yake kawai yacigaba da Danna laptop d'in batare da yasanma inda yake dannawa ba
Cikin magana me cike da lallashi hajiya tace“baban Yara Dan Allah nace muyi magana mana”batare da ya bar Danna laptop d'in ba yace “ehen inaji” sotake yabata full attention d'insa Amma taga haka bazai samu ba sai kawai ta fara magana da fad'in “nikam babansu what's happening between you and Adnan Naga Kamar d'azu Yabatama Rai Dan Allah ka fad'a min nasan dai Adnan me ladabi ne ga duk abinda ka fad'a Amma this time around Naga Kamar tasauya zani Amma ka fad'a min”
Dafe kansa yayi da hannu biyu Dan wallahi Sam besan abinda zai fad'a mata ba gaba d'aya yama rasa mezai ce Mata , ahankali yazame hannunsa daka kansa had'e da juyowa ya dubeta sannan ya sauke wata ajiyar zuwa yace“look saleemeh Adnan bemin lefin komi ba Amma I will assure you abinda yake shirin yi ayanzu to tabbas zamu samu matsala me karfi so please go and talk to him yafahimta ya goge abinda yake niyyar aikatawa wannan shine kawai”yana kaiwa Nan kawai yami'ke yad'au wani towel dake rataye Ya nufi toilet, binshi kawai hajiya saleemeh tayi da kallo azuciyarta tana fad'in “nashiga uku meke Shirin faruwa ne ,? What's going on between alhaji and Adnan, jitai kawai bazata iya hakurin jiran gari ya waye ba , kawai ta d'au hijab d'inta dake d'akin alhaji kawai ta bud'e kofa tanufi section d'in Adnan Dan koyayi bacci saita tasheshi yasanar da ita meyayiwa alhaji ,
Tana shiga taga babu haske a parlon Amma , tagano hasken fitilar bacci a bedroom d'insa hakan yasa kawai direct ta nufi d'akin, tana shiga ta kalli bed , amamakinta saitaga taga Adnan azaune yahada Kai da guiwa , abinda bata taba gani yayi ba aduk tsawon rayuwar sa, dasauri ta karasa gefen gadon tana zama kusa dashi had'e da d'ago da kansa tana fad'in“adnan what's happening why are you like this meyasa bakai bacci ba”gaba d'aya rasa me zaice Mata yayi Dan Zuciyarsa zafi take sosai da bazai iya magana ba kawai ya zame ya kwanta acinyar hajiya saleemeh ahankali yafara fad'in “mommy I love her, wallahi inasanta in my holl

Please Login or Register in order to submit comment