Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dariya yake yajima agidan kafin yatafi da niyyar zuwa kasuwa wurin baba domin bai iskeshi agida ba yasamu yafita kasuwa acan ya shantake wurinsu baba wanda gaba daya shagunan dake layin duk na dattijai ne kamar baba shiyasa suke zamansu zama na mutunci ga yar majalissarsu nan gaban shagunansu karkashin wata bishiyar darbejiya, gefe fahad yakoma yayi zamansa yana sauraren hirar su baba irin tasu ta manya, rabonshi da yazo shagon baba yayi zama irin wannan har yamanta amma yau acan yayi sallar azahar ma nan aka kawowa su baba damammiyar fura cikin katuwar kwarya tasha sugar da gasasshen nama, cups aka fito dasu daga wani shago kowa yana diba sosai abin ya kayatar da fahad wato zama irin na iyayenmu da kakanni abin burgewa ne domin kowa yasan yanda zai zauna da kowa.

Abangaren bilkisu kuwa neman duniya tayiwa wayarta amma tarasa sai babbar amma sama ko kasa tarasa karamar, babu inda batayi checking ba agidan amma bata ganiba daga karshe dai tagane cewa fahad ne yadauka nan ta sake hawa ta cika tayi famm tana jiran dawowarsa amma shiru har hamood yakirata a daya layin nata dake kan babbar wayar yana fada mata irin zagin da fahad yayi masa hakan yasake tunzurata,shi kuwa fahad sai yamma yabar wurinsu baba yanufi shagonsu bayan magriba yakoma gida taso masa bilkisu tayi tamkar zata dokeshi,

"Bani wayata fahad, waye yace ka daukar min waya? Wai menene amfanin zama da mutumin da shi baya son zama dakai? Wacce riba zaka samu?"

Zama yayi saman kujera yana kallonta duk tabi ta hargitse,

"Bilkisu yakamata ki nutsu ki gane mai sonki da gaskiya, wallahi mutumin can yaudararki yakeyi, kiyi hakuri ki karbeni a matsayin miji nikuma nayi miki alkawari bazan baki kunya ba amma wallahi shi ba sonki yakeba dagaske nine nan masoyinki na gaskiya..."

"Ni ba dogon jawabi na tambayeka ba cewa nayi kawai ka sakeni babu ruwanka da rayuwar da zan shiga, babu ruwanka da yana sona ko sabanin haka sannan kabani wayata...."

"Anhanaki wayar kizo ki kwata ai kinada karfi......"

Yafada yana mikewa tsaye babu shiri taja da baya tana kallonsa, nunata yayi da dan yatsa,

"Bari infada miki fa kibar ganin ina kyaleki bafa tsoronki nakeyi ba kawai ina rabuwa dake ne saboda ina respecting dinki ko kina tunanin idan karamar yarinya nake aure age mate dina ko wadda na girma the same way zanyi treating dinta kamar yadda zanyi treating naki? amma wallahi idan kika kaini bango zaki fahimci bakida wayo zaki gane shayi ruwane, tunda kika zo gidan nan abinda kika gadama shi kikeyi ban taba takura miki ba to nima baki isa kin takura min ba, saki ne kuma baza ayiba idan kina iyawa ki saki kanki mana, haba kin takura min dayawa alhalin nikuma bahaka nake yimiki ba daidai da hakkina wannan ba taba bani akayi ba saboda Kin rainani amma ban taba takura miki akan hakanba bayan kuma inada karfin da zan kwata da karfin tsiya..."

Zaro idanuwa tayi tana hawaye cikeda masifa da jin haushinsa tace,

"Dama abinda ke ranka kenan so kake kayi min fyade to kazo kayi idan baka da imani..."

"Zaki gane banida imani sai ranar da na daureki nayi kaca kaca dake nayi round biyar akanki ranar ne zaki san banida imanin...."

Daga haka yawuce cikin bedroom yabarta anan tana sharbar kuka amma hankalinta yayi mugun tashi da jin kalamansa na karshe gaskiya idan fahad yayi mata haka ya cuceta idan ya rabata da martabarta bazata taba yafe masa ba kai wallahi muddin yanemi aikata mata abinda yafada saita raunata shi, zama tayi awurin taci gaba da risgar kuka har tsawon wani lokaci. Shikuwa fahad lokacin da yashiga daki dariya ma dramar su tabashi wato bilkisun nan shegen tsorone da ita sai son girman tsiya domin ya hango tsoronshi karara acikin idanuwanta da dukkan fuskarta gaba daya. Wanka yashiga yayi yafito yunwa na ciciyarshi domin bai wani ci isasshen abinci ba, daga shi sai gajeren wando da farar vest yafita yana janye singiletin zuwa saman kirjinsa sai shasshafa cikinsa yake yi,tana zaune inda yabarta bai ko kalleta ba yawuce dining kamar yadda ya tsammata batayi girki ba sai dafaffen shayin na'a na'a cikin tea flask wanda yanzu shi tamayar abincinta, babu yadda ya iya shi dinma tea din yasha ya dauki slice bread yashafa butter ajiki yaci yana tasowa ta mike tsaye duk da atsorace take dashi amma haka tayi karfin halin yimasa magana,

"Kabani wayata tun muna shaida juna...."

Banza yayi da ita yanufi bedroom,

"Wallahi ko kanaso ko baka so sai ka...."

Juyowa yayi yadawo da baya tana ganin haka ta dora hannu akai tafasa ihu saboda duk atunaninta abinda yafada dazu zai aikata, tsayawa yayi gabanta ya zuba mata ido,nan taja baya cikin sauri,

"Daina gudu karki damu yanzu babu abinda zanyi miki amma duk ranar da nahau kanki wallahi sai kin gane bakida wayo ai nafada miki sai nayi round 5, idan banda rashin tunani irin naki ya za ayi kinada aure ki zauna kina sauraron tatsoniyar wani jahili awaje? Me hakan yake nufi? To wallahi this is the last warning babu ke babu shi, ban son dakikanci da shashanci..."

Idonta fall hawaye muryarta adashe ta kalleshi,

"Fahad ni kake fadawa haka? Ni kake addressing da dakikiya jahila shashasha?"

Sauke idanuwansa kasa yayi sannan cikin sanyin murya yafurta,

"Am very sorry...."

Daga haka yajuya yashiga daki ya kwanta amma baya jin zai iya bacci adaren yau kamar yadda itama bilkisu baccin ya gagareta, inbanda sakawa da kwancewa babu abinda yakeyi har dare ya tsala. Kwana biyu haka nafaruwa har lokacin bai bata wayarta ba kuma bai sanarwa da kowa ba wani lokacin sai yaji kamar yafadawa koda wani daga cikin yayunshi ne amma sai wata zuciyar ta haneshi, gaba daya bilkisu ta hana kanta sukuni danma tana dan shakkarsa yanzu bata son yayi abinda yayita ikirarin zaiyi akanta, yau da safe yana daki kwance yamike yafito falo kwance ya sameta wayarta ya mika mata,

"Bilkisu ga wayarki.... Shi masoyi akoda yaushe yana kokarin ganin yayi abinda masoyinsa zai kasance cikin farin ciki koda kuwa shi din zai dawwama acikin bakin ciki, kamar yadda kika nema kije na sakeki saki daya...."

Cikeda farin ciki ta mike,batace komaiba tawuce bedroom taje tafara hada kayanta, duk abinda zata nema tazuba cikin babban akwati nan ta janyoshi tafito tana rikeda handbag dinta da akwatin,

"Ga akwatinan lefenka can harda sadakinka duk yana ciki..."

"Nabar miki saboda banyi miki dan nakwace ba..."

Bata sake cewa komai ba tasaka kai tafice daga cikin falon, wasu hawaye ne masu dumi suka zubo daga idanuwansa......


*Yar uwa littafinnan na siyarwa ne idan kina so ki biya saiki karanta*


*_Ummi Shatu_*

© *HASKE WRITERS ASSO.*


*KAMAR DA WASA....!*


_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*28*


***Runtse idanuwansa yayi yana jin wani irin kunci acikin zuciyarsa, hawaye yayita yi awurin har saida yaji kansa yasoma sara masa sannan yasamu yatashi yana share fuskarsa da handkerchief din dake cikin aljihunsa, wayarsa kawai ya dauka sai keys dinshi yafita daga gidan dan baya jin zai iya sake awa daya acikin gidan tunda wacce yake zaune saboda ita bata nan, Babur dinshi yabuga yabar gidan bayan ya rufe ko ina, kai tsaye gidansu salim ya wuce yabude dakin salim din yashiga ya kwanta yana jin kansa na cigaba da sassara masa saboda kukan da yayi domin rabon da yayi kuka irin wannan har ya manta. Yana kwance yarasa meke yimasa dadi har salim yashigo ganin idanuwansa arufe yasashi zaton fahad din kila bacci yakeyi wannan dalilinne yasashi ficewa batare da yayi masa magana ba.

Har wurin 12 na rana fahad na kwance dakin salim saida yaji dan dama dama sannan yatashi yatafi gidansu, bai shiga cikin gidanba yabude dakinsu nada shida Abba yashiga yasake kwanciya babu wanda yasan yashigo gidan domin ko babur dinshi bai ajiye wurinda za aganiba, sai lokacin yasamu damar yin kukan bakin ciki nan yarinka yi kamar karamin yaro babu jimawa yafara jin zazzabi zazzabi ajikinsa amma dai yadaure bai tashiba har azahar tayi, anan daki yayi sallah dama wayarshi akashe take saboda bama yason wani ya kirashi, salim ne yabiyoshi gidan bayan yakoma dakinsa yaga baya nan sannan har gidansa yaje amma gidan akulle ga kuma wayarshi akashe. Yana kwance duk jikinsa nayi masa ciwo salim yashigo ganinsa kwance alamun ba kalauba yasa salim fara tambayarsa amma fur fahad yaki magana sai ko ido da yake bin salim dashi,ganin yaki magana yasa salim shiga cikin gida wurinsu ayiyah domin karbo musu abinci, ayiyah na tsame alalan da ta dafa cikin cooler ita kuma mamuh na dama kunun gyada suna aikinsu suna hirarsu, koda salim yafada musu abinci yazo karbar musu shida fahad wanda ke dakin abba basu kawo komai ba suka zuba musu yakoma wurin fahad, dakyar da fada da komai fahad yatashi suka ci alalan domin kwaya daya ma yaci sai dan kunun da ya kurba yakoma ya kwanta,juyin duniya salim yayi akan fahad yasanar dashi abinda ke damunsa amma yaki daga karshe salim yatashi yafita. Tunda salim yatafi fahad ke kwance ya rufe kofar dakin shiyasa babu wanda zai tsammaci cewar da akwai mutum aciki,ahaka yakwana yawuni har dare yayi sai dai idan lokacin sallah yayi yatashi yayi yakoma ya kwanta,har dare atakaice dai acikin wannan halin fahad ya kwana agidan babu Wanda yasani har saida safiya tayi lokacin da baba zai fita yazo saitin kofar dakin yajiyo fahad yana yin tari cikin mawuyacin hali, buga kofar baba yashiga yi wanda har karar bugun ta janyo hankalinsu ayiyah suka fito domin ganin meke faruwa, cikin mawuyacin hali yataso yazo ya bude kofar yana jin kamar zai fadi saboda rashin karfin da jikinsa ke fama dashi,wuri yasamu yazauna ya jingina da bango yana kallon su baba dake kokarin shigowa cikin dakin,

"Muhammadu... Ya akayi? Tun yaushe ka shigo cikin dakin nan?" Baba yafara tambayarsa cikin mamaki,

"Tun jiya ne baba..."

"Ikon Allah, to ya zakazo kashiga daki karufe kanka kai daya, ina matar taka?" Mamuh tafada cikeda mamaki,

"Na saketa...."

Ai gaba dayansu jin maganar tasa sukayi tamkar saukar aradu acikin kunnuwansu.

"Saki.....?"

Su ayiyah suka fada cikin razani har bakinsu na haduwa wurin tambayarsa,

"Muhammadu meyasa kayi haka? Meyasa ka yanke hukunci da kanka batare da ka tuntubemu ba?" Baba yafada cikin kwantar da murya,

"Baba kuyi hakuri dan Allah....."

Dukansu samun wuri sukayi suka zauna cikeda jimami, sunfi mintuna goma ahaka babu wanda ya iya yin magana zuwa can baba yaja gwauron numfashi cikeda damuwa yace,

"Fahad meyasa ka saki yarinyar nan yar mutunci yar gidan mutunci? Laifin me tayi maka haka...?"

Kasancewar dan jiri na daukarshi yasashi zamewa ya kwanta idanuwanshi taf da hawaye,

"Baba ni bata yimin laifin komai ba..... Kawai..... Kawai dai.... Kawai bazan cigaba da zama da ita bane...."

"Me? Fahad acikin hankalinka kake kuwa? Wannan wanne irin shashanci ne? Ina kataba ganin anyi haka? Kowa da yake zaune da abokin zamansa ba hakuri yakeyi ba?" Mamuh tafada cikin fada,

"A'ah yimasa ahankali.... Ai ba tatashi zamu biyaba, ni yanzu haka ta gidansu yarinyar zanbi inbaiwa mahaifinta hakuri sannan innemi bikonta adawo da ita dakinta tun abu baiyi nisa ba.... Saki nawa kayi mata?" Baba yakarashe maganar yana kallon fahad wanda idanuwanshi ke rufe,

"Baba babu aure atsakaninmu fa yanzu saboda saki.... Saki ukun...."

Ai tun kafin yarufe bakinsa su ayiyah suka rufeshi da fada ta inda suke shiga ba tanan suke fitaba shi baba sai shiru ma yayi yana saurarensu daga karshe ayiyah tatashi tafita cikin fushi, saida itama mamuh tafita sannan baba yadora da nasa fadan amma shi nasa cike yakeda nasiha, sun jima baba yana yimasa fada sannan yatashi yafita bayan yasanar dashi cewa gobe zaije gidansu bilkisu su gana da mahaifinta, agaba baba yasashi suka shiga cikin gida har dakin ayiyah yakaishi sannan yafita shikuma fahad ya kwanta nan saman daddumar dake shimfide a falon, sam ayiyah bata saurareshi ba bare ta kulashi sai can wurin azahar sannan tashigo wurinsa dauke da kwanon kunu wanda ta dama masa domin ta fahimci baici komai ba kuma yana tare da yunwa domin gashi nan duk yafige ya fita kamanninsa, yako ji dadin kunun nan domin da zafinsa haka ya zauna yasha da yawa sannan yakoma ya kwanta yana jin irin sarawar da kansa keyi masa.

A bangaren bilkisu kuwa tana fita daga gidan fahad sai kuma hawaye suka fara gudana daga idanuwanta, dama mata haka suke wani lokacin sune zasu nemi sakin da Kansu amma ana sakinsu kuma sai sufara kuka karasa dalilinsu, napep ta tare tahau tana kuka har sukaje kofar gidansu, da yake safiya ce Abba yana gida ko fita baiyi ba, ammah tana kitchen itada Rabi mai aikinta suna hadawa Abba abincin karyawa.

Fuskarta sharkaf hawaye tashiga cikin gidan shiyasa kallo daya ammah tayi mata tagane cewa ba kalau ba musamman ma da taganta da sanyin safiya irin wannan, barin abinda takeyi tayi suka shiga cikin falonta har lokacin bilkisu kuka take wanda ita kanta bata san dalili ba,

"Mai gado duk yanda akayi ba lafiya ba saboda idan lafiyace takawo ki bazaki taba zuwa da safiya irin hakana sannan bazaki shigo kina kuka ba...."

Hawayen fuskarta ta goge yayinda wasu ke kara zubowa,

"Ammah ya sakeni......"

Salati ammah tashiga yi tana karawa cikeda tashin hankali,

"Saki mai gado? Saki fa kikace? Meya hadaku? Wani abun kikayi masa?"

Girgiza kanta tayi tana hawaye,

"Babu abinda nayi masa..."

"To Allah yarufa asiri... Zauna nan zan kawo miki abin karyawa"

Tashi ammah tayi takoma kitchen suka karasa hada kayan karin kumallo ta dauki na bilkisu takai mata sannan ta dauki na abba tanufi wurinsa cikeda karfin hali take gudanar da komai, cikin farin ciki da annashuwa suka karya tareda Abba saida suka kammala sannan tayi kokarin sanar masa,

"Ga mai gado can fa tazo dazun nan babu jimawa...."

Shiru abba yayi yana kallonta,

"Lafiya kuwa?"

"Ba najin lafiya ce takawo ta gaskiya"

"Kira min ita naji"

Tashi ammah tayi takwashe kayan da suka gama amfani dasu tafita, yanda tabar bilkisu haka takoma ta sameta tana zaune sai faman goge hawaye take,

"Zo abbanku yana kiranki...."

Wata mummunar faduwar gabace ta ziyarceta, tunda aka fara rigimar sakin nan bataji ko darr ba sai yanzu saboda bata tanadi amsar da zata baiwa abba ba, gabanta na faduwa har suka shiga falon Abba,

"Uwata lafiya? Meke faruwa?"

Zama tayi gaban Abba,

"Abba sakina yayi..."

"Saki.... To laifin me kikayi masa?"

"Babu abinda nayi masa"

"Babu abinda kikayi masa?" Inji ammah, daga kai bilkisu tayi alamun ehh,


"To shikenan zan kira mahaifinsa dashi kansa yaron suzo aji mai yafaru saboda shi aure gyarashi akeyi akoda yaushe saboda yafi rabuwar tunda ba asan abinda Allah ya boyeba..."

"Abba saki ukune fa...."

"What...? Yana shaye shaye ne?"

"A'a baya shan komai"

"Amma har saki uku? Yanzu abinda yaron nan zaiyi mana kenan ina yimasa kallon mai hankali? Shikenan tashi kije, Allah yazaba miki abinda yafi zama alkhairi arayuwarki.... Kiyi hakuri kinji uwatah, wannan jarrabawa ce babu komai insha Allah zaki samu wanda yafishi"

Tashi tayi tafita har lokacin bata daina kukaba yayinda shikuma Abba da ammah ke can sunata jajanta abin gaba dayansu zukatansu babu dadi.Tana nan zaune falon ammah ta kifa kanta jikin kujera ammah tashigo cikeda damuwa ta zauna sannan daga bisani ta daga kai ta kalleta,

"Mai gado wannan kukan da damuwar babu abinda zai tsinana miki sai ko ma yakara miki damuwa dan haka ki tattara komai ki mikawa Allah lamarinsa sannan kibaiwa zuciyarki hakuri amma wannan kukan ba mafita bace.... Ga abinci nan dauki kici..."

Batayi musuba ta share hawayenta taja abincin da Ammah takawo mata soyayyiyar agada da kwai sai farfesun hanta da ruwan zafi, kadan ta dan tsakura tahada tea tasha ta mayar ta rufe kwanukan, kafin wani lokaci har ammah tasa angyara mata tsohon dakinta nada wanda yanzu yake arufe babu kowa aciki domin mai aikinta ba kwana takeba da safe take zuwa tatafi da daddare, komai da take bukata akwaishi acikin dakin gashi Rabi ta shirya mata kayanta cikin drewar, bata yarda sunyi waya da hamood ba domin suna tare da ammah duk tsawon yinin ranar sai dai wani lokacin idan tayi shiru sai tarinka tambayar kanta anya kuwa tayiwa fahad adalci? Anya kuwa tayi abinda yadace? Haka take ta yawaita yiwa kanta wadannan tambayoyin amma daga karshe tayi fatali dasu tana ji aranta abinda ta aikata daidai ne domin ita hamood takeso ba fahad ba. Tun aranar dukkan yan uwanta suka samu labarin abinda yafaru marar dadi wai auren bilkisu da fahad ya mutu, duk waya suka bugo mata suna tayata jaje da jimami kafin suzo gidan gobe, duk da yinin ranar tayishi sukuku ne amma da daddare tasamu kuzari domin sunyi waya da hamood ta zayyane masa dukkan abinda yafaru yayinda shikuma yace da zarar ta kammala iddah zai fito sai maganar aure.

Fahad haka yawuni kwance yana ciwon kai sai daf da magrib yasamu yayi wanka bayan ayiyah ta dafa masa ruwan zafi gashi throughout baici komai ba sai ruwan kunu da yaketa sha sama sama, gaba daya yayunshi fada suka rinka yayyafawa lokacin da labarin abinda yafaru yaje musu shi dai yaki magana domin shi kadai yasan abinda yake ji. Yana fitowa daga wanka yadauki t shirt acikin kayan abba yasaka da wando yayi salla ya kwanta har saida baba yashigo sannan yaga ayiyah tashigo rikeda maganin ciwon kai da balangu wanda baba yakawo, agaba tasaka shi har saida yaci naman yasha magani sannan tafita tabarshi babu jimawa bacci ya daukeshi ko sallar ishah bai samu damar yi ba. Washe gari ma da ciwon kan yawayi gari ga rashin iya cin abinci dake damunsa aranar da salim yazo yasan komai na daga abinda yafaru amma fahad bai sanar dashi gaskiyar abinda yafaru ba kawai dai yafada masa cewa sun rabu da bilkisu rabuwa ta har abada. Atakaice dai saida fahad yayi kwana uku akwance ganin haka yasa su ayiyah matsanta masa akan yaje koda chemist ne idan bazaije asibiti ba, wanka yayi ya shirya cikin kayanshi wanda salim yaje ya debo masa jiya, riga kalar ruwan toka mai botira sai wando rouser baki, ahaka ya daure yafita zuwa chemist din daga can kuma yawuce shago iya tj da customers dinsa guda biyu wadanda ke jiran yagama yimusu dinkinsu yabasu kadai yasamu acikin shagon, zama yayi kan keken hamza bayan sunyi musabaha da tj, yana nan zaune yana hango mutane daketa kaiwa da kawowa awaje ya hango husnah wacce tafito yin cefane direct shagon tashigo ko cefanen bata kai ga yiba, fuskarta da alamun damuwa ta karaso gabansa ta zauna,

"Haba ya fahad.... Ina kashiga kwana biyu dan Allah? Gaskiya ka sani acikin damuwa wallahi...."

Tagumi ya rafka yana kallonta,

"Husna banida lafiya ne...."

"Ayyah my prince sorry.... Tun yaushe? Meke damunka? Kaje asibiti?" Tajero masa wadannan tambayoyin cikin damuwa,

"Yanzu ma haka daga chemist nake nabiyo ta nan...kinga magungunan da nakarbo nan....."

"Ayya sannu... Muji... Da zazzabi?"

Tafada cikin sanyin murya tana kai hannu goshinsa zuwa wuyansa, baiyi yunkurin hanata ba har tagama tattabashi domin jikinsa akwai alamun fever kawai dai bai gama sauka ajikinsa bane,

"Sorry bari naje kasa nasamo allura nayi maka saboda bana so zazzabin yarufeka...."

Baiyi magana ba sai kai da yadaga mata kawai nan tayi maza ta sauka kasan plaza din tashiga wani pharmacy tayi amfani da kudin hannunta tasiyo alluran da take bukata guda uku takoma wurin fahad lokacin tj yafita masallaci sallar azahar customers dinsa kuma sun tafi, zama tayi gabansa tana hada allurar sai faman girgiza kai takeyi alamun tausayawa,

"Ya fahad kayita zama da ciwo ajikinka tun tuni baka nemi magani ba...."

Hannunshi daya ta kama ta yimasa allurar a damtsensa sannan takara yimasa wata daga bisani takoma daya hannun tayi masa guda daya.Jiri yaji yafara daukarsa nan yayi gaggawar riketa gudun kada ya fadi ai kuwa ta riku a hannun maza domin ji tayi kamar zai ballata, saida tajira allurar ta dan fara sakinsa sannan ta fita takira mai napep yazo har gaban plaza din ya tsaya, cikin shagon takoma ta kamo fahad suka fito dai dai lokacin da tj yadawo daga masallaci shine ya rike fahad din yataimaka masa yakaishi cikin napep, tare da husnah suka tafi gidansu yayinda shikuma tj yakoma shago, har gida husnah ta rakashi amma bata shiga cikiba daga waje ta tsaya bayan taga shigarshi gida itama tajuya tatafi.

Sosai bilkisu ta ware ta sake bata saka damuwar komai aranta ba dan kamarma harsu maama sun fita damuwa amma ita ko ajikinta saboda sunata shirya yanda al'amuransu zasu kasance itada hamood sannan kullum sai yabita office sunsha hirarsu ta soyayya shiyasa basuda matsalar komai, bayan sati biyu da faruwar lamarin suka shirya zuwa kwaso kayanta agidan fahad itada su maama dama shi fahad rabonsa da gidan tun ranar da bilkisu tasa kafa tabar gidan dan hatta kayan sawarshi ma da sauran kayan bukatunsa na yau da kullum sai salim ne yaje ya debo masa shiyasa ranar da zasu kwashe kayanma sai salim dinne yaje yabude musu gidan tunda gidansu fahad din suna da masaniyar za azo adebi kayan saboda baba har gidansu bilkisu yaje suka tattauna da Abba akan maganar tareda baiwa juna hakuri akan abinda yafaru, wuni su bilkisu sukayi suna aikin tattare kayan zuwa karfe uku na yamma sun kwashe komai babu abinda suka bari sai akwatunan lefen fahad kamar yadda ta sanar dashi tun farko, salim bai bar kayanba ya kwashesu zuwa gidan anty fauziyya can yabarsu sannan yakoma wurin fahad wanda ke kwance ciwon kirji da ciwon kai na addabarshi,

"Salim ta kwashe komai nata ko? Dama nasani..."

Kallonsa salim yayi cikin tausayawa,

"Wai abokina ya akayi hakan tafaru? Meyasa ka saketa? Yanzu baku saniba ko kilama tanada juna biyu kuma katashi ka saketa...."

Girgiza kai fahad yayi,

"Bata da wani ciki saboda babu...."

Sai kuma yayi shiru bai karasa ba,

"To ai laifinka ne, danme zaka zuba mata ido kazauna kana kallonta? Da ace kayi abinda yadace da tuni yanzu wallahi kuna tare tunda ko bata zauna dan kaiba dole ta zauna dan cikin jikinta...."

"Salim mubar wannan maganar kar zuciyata tafashe..."

"Allah ya sawwake yabaka lafiya, amma yakamata kayi gaggawar cireta aranka kamar yadda itama tayi..."

Shiru fahad yayi masa domin shi kadai yasan abinda yakeji, haka yayita murkususu har zuwa dare danma tare da salim din yanzu suke kwana, karfe 9 nadare a asibiti tayi musu saboda tsananin da jikin fahad yayi wani zazzafan zazzabine ya mamayeshi inbanda karkarwa babu abinda jikinsa keyi ga ciwon kirji dake barazanar tarwatsa mata hakarkari wannan dalilinne yasa su baba kaishi asibiti shida salim, babu bata lokaci aka bashi gado nan aka shiga kara masa ruwa babu ji bare gani saboda jikinsa yagama galabaita sosai.......


*Idan har kin san baki biya ba kiyiwa kanki adalci nima kiyi min karki karanta.*



*_Ummi Shatu_*

© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*KAMAR DA WASA...!*



_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*29*



***Tunda aka kai fahad asibiti yake cikin mawuyacin hali gaba daya bai san a inda yakeba bare yasan wanda ke kansa, babban likitan da yake dubashi sai faman fada yake tayiwa su baba yana cewa ya za ayi abar karamin yaro kamar fahad yakamu da ciwon hawan jini wanda ke barazanar taba kwakwalwarsa da lafiyar jikinsa? Domin acewar likitan Allah ne kadai ya takaita abun aka kawoshi asibiti dawuri amma da ace ba akawoshi tun wuriba to irin wannan ne kesawa mutum yana tsaka da tafiya ya yanke jiki yafadi shikenan yahadu da babbar lalura dan haka yazama dole asan yanda za ayi yanisanta kansa da damuwa da yawan tunani domin jininsa yayi masifar hawa hawan da ba aso dan haka yanzu dole akan magani zasu dorashi domin lalurar ta rigada ta kamashi. Daga ayiyah har mamuh kuka suke yi jin wai dan karamin dansu yahadu da cutar zamani ta hawan jini tunda ko su da suke tsoffi basu gamu da irin wannan ciwonba lallai wannan jarraba ce daga Allah, kullum a asibitin suke wuni suna kula da fahad, salim da ya Abba wanda yazo gida saboda dan break din da suka samu na good friday Easter monday, suke kwana awurin fahad sannan suna kula dashi, husnah ma kusan kullum sai tazo asibitin ta dubashi wani lokacin ma har girki take iyo masa, shi dai fahad tunda yafara bude ido dishi dishi yake kallon kowa baya ganin mutane clearly sai ahankali sannan ganinsa yasoma washewa har yadawo daidai acewar Dr Allah ne yarufa asiri abun bai shafi ganinsa ba, tunda yafara gane mutane bai furta koda kalma daya ba har yaji dan sauki, karin ruwannan da aketa yimasa har yagaji dashi gashi duk jikinsa ciwo yake yimasa saboda alluran da aka huhhuda jikinsa dasu, satinsa

Please Login or Register in order to submit comment