Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa kofa yana bacci sai ya lakada mata duka. Dakinsa yawace ya rage kayan jikinsa sannan ya kwanta yana nazarin rayuwa, ganin tunanin nasa yana neman yin zurfi yasashi katseshi ta hanyar daukar wayarsa ya fada yanar gizo yana duba labaran abubuwan dake faruwa aduniya.

Har karfe goma saura yana haka zuwa can yatuna da bai turawa rabin ransa good night massage ba dan haka yayi hanzarin tura mata yana lumshe idanu kamar tana kallonshi.


***

Abangaren bilkisu ganin takasa gano wanda yake turo mata da massages dinnan sai tunaninta yabata cewar ya mudan ne cousin dinta wanda sam jininta bai hadu da nasa ba, wani tsaki taja bayan tagama karanta massage din da yashigo yanzu wanda take sa ran nashine, duk ji tayi kunci ya rufeta har saida takira hamood sukayi hira sannan taji damuwa da bacin ran dake tattare da ita sun kau.

Washe gari bayan tataso daga aiki kamar ta biya ta shagon su fahad sai dai tafasa saboda tasan su ammah na can gida suna jiranta saboda gobe za akawo lefen Hindu shiyasa suketa shirye shirye domin bata son lokaci yakure ba ashirya komai ba kuma tasan baza ayi komaiba agidan har sai anjira zuwanta.

***

Shi kuwa fahad yau tunda yafito shago suke tare da husna duk da ba wai yana son zaman nata bane domin kallo daya zaka yimasa ka fahimci haka sakamakon fuskarsa dake hade babu alamun fara'a ita kuwa husna duk inda yayi sai binsa take da kallon so cikeda burgewa domin sosai yau yayi mata kyau,

Yana dinka kayansu Hindu sai labari take bashi na garinsu shi dai kawai jinta yake amma bawai yana son labarin bane.

Yan shagon nasu kuwa kowa sai kallonsu yake yana yiwa fahad dariya kasa kasa,ganin bata da niyyar tafiya shi kuma ta takura masa yasashi fitowa fili yace taje ta tafi da yamma saita dawo, ai tana tafiya babu jimawa yagama abinda zaiyi yabar shagon, shagon su saleem yaje acan suka sha hirarsu wadda kusan rabi ta Bilkisu ce da take can bata san yana yiba. Saida sukayi sallar la'asar sannan suka nufi gida, koda yaje gida abinci kadai yaci daga nan ya kwanta baccin nasa na sabo nan yayishi har na tsawon rabin awa, karfe biyar da wani abu yafarka yayi wanka yafita filin ball duk da yau baya sha'awar buga kwallon amma yana son ya zauna ya kalli masu bugawar, ear piece yasaka acikin kunnenshi yafita yana sauraron wakar fall in love, kamshin oad kawai yake zubawa da haka ya isa filin kwallon yakama katanga yahau ya zauna yabi sahun wadanda ke zaune suna kallo, wayarshi ya ciro yayi dialing number din Bilkisu domin amatse yake da jin muryarta lokacin da ya kirata tana tsakiyar hayaniyar jama'a domin yan kawo lefen basu tafiba suna dai niyyar tafiya matsawa gefe tayi tai sallama cikin muryarta mai mutukar zaki wadda ta saukar masa da kasala mai nauyi cikin sanyin murya ya amsa bayan ya lumshe matsakaitan idanuwanshi sannan yabude su akan masu buga kwallo,

"Mai gado i really loves u...."

Jin abinda yace yabata mamaki duk da bata fahimci wayeba amma tagane itace number din da aketa damunta da turo mata massages dinnan, yanzu kam tagama yarda cewar ba yaya mudan bane wani ne daban wanda bata saniba.

"Uhmmm.kefa? Kina sona?"

Jin abinda yace ta dan nisa kadan sannan tace,

"Yanzu ina cikin wani uzurine amma idan anjima zan kiraka"

Kitt ta katse wayar takoma taci gaba da abubuwan dake gabanta yayinda shikuma tabarshi da faduwar gaba domin bugawa kirjinsa yashiga yi da sauri da sauri......




*_Ummi Shatu_*


© _*HASKE WRITERS ASSO*_


*KAMAR DA WASA.....!*



_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*6*



***Bilkisu bata samu kanta ba sai dare bayan sallar isha domin har karfe 9 saura na dare mutane basu bar shigowa kallon kayan ba, sai tara da wani abu ta samu tayi wanka tayi shirin bacci domin a mutukar gajiye take jinta yau tsabar busy din da ta shiga sau daya kawai sukayi waya da hamood, yanzunma bata jin zata iya kiranshi shiyasa kawai ta kwanta taja bargo. Tafara bacci sama sama taji karar wayarta,idonta cikeda bacci ta kara wayar a kunnenta,

"Love..... Bacci kikeyi?"

Jin muryar da bata saniba yasata katse wayar tareda kasheta gaba daya domin bacci take so tayi. Wurin sau biyar fahad yana gwada kiranta sai yaji akashe daga karshe dole sai hakura yayi shima ya kwanta din yana tunata acikin ransa.

Washe gari misalin karfe 10 nasafe ta sauka agaban shagonsu ita kadai domin ta baro khulsum a office tana fassara labaran turanci zuwa hausa itama kawai bikin nan da ya karato ne m d yake daga mata kafa, anutse take takawa babu hayaniya ta nufi shagon su fahad, yana daga waje kofar shagon gaban wani tebur yana yanka uniform din husna da ta kawo masa wuyansa rataye da tape na aunawa, sallamarta ce tafara shiga cikin kunnuwansa yayi saurin waiwayawa ganinta yasashi fadada murmushinsa yana sake bude kofofin hancinsa domin shakar kamshinta dakyau,

"Shiga ciki mana hajiya"

Murmushi tayi tanufi cikin shagon tana cewa,

"To nagode, Allah dai yasa ka cika alkawari"

P cap dinshi ya maida baya yabi bayanta yana murmushi,

"Ah haba hajiya ai ni bana magana biyu"

Kanta tabawa mazauni agaban kekenshi tana kallon cikin shagon wanda babu kowa aciki yau da alama sauran yan shagon sunyi nisan zango.

"Am nace nawane ma ragowar cikon kudin dinkin gaba daya?"

"Dubu biyar banda naki"

Tana kokarin bude jakarta batare da ta kalleshi ba tace,

"Ban gane banda nawa ba, ni baka dinka nawa kayan bane ko yaya?"

Zama yayi a mazauninsa yana wani murmushi mai kayatarwa,

"Na dinka miki, kawai dai ni ka'idata ce haka"

Dan dakatawa tayi daga binciken cikin jakarta da takeyi ta dago ta kalleshi cikin rashin sa,a idanuwanshi suka sarke cikin nata domin shima lokacin tsaka yake da kallonta, ahankali ta janye nata idanuwan ta maida kan jakarta tana cewa,

"Haka ka'idarka take kamar yaya?"

Tallafe kumatunshi yayi da hannunshi guda daya,

"Akaron farko nakan yiwa customer dina ragi ko indinka masa kyauta saboda ina son yakara dawowa so idan yadawo sai infara yimasa na kudi..."

Murmushi tayi tana jijjiga kai alamar gamsuwa murmushin da yakusa sumar da fahad azaune, kasa koda motsi yayi sai uba uban kallon da yake faman binta dashi har ta ciro kudin ta mika masa, karba yayi yana lumshe idanuwana sakamakon kamshinta da ya kusantoshi mutuka.

Sam ita bilkisu bata san abinda yakeyi ba dayake ma lokacin wayarta tana karar neman agaji alamar ana kiranta, ciro wayar tayi ta daga domin amma ce, tana dauka taji muryar meenah na cewa,

"Adda labour ba amma bace nice, dan Allah ko zaki taho mana da kayan kamshi?"

Agogon hannunta ta kalla na silver wanda yayi mata das,

"Meenah kufa matsala gareku,sakonku baya karewa, bari zan dubo"

Bata jira abinda meenan zata ceba takatse wayar ta cilla cikin jaka sai lokacin fahad ya dauke idonshi daga kanta,

"Am muga dinkunan...."

Fito dasu yashiga yi daya bayan daya, nan bilkisu tasoma santinsu tana yabawa dasu domin ba karamin tsaruwa sukayi ba koda tazo kan nata ai sai ta raina nasu mamaa domin har na amaren bafin nata kyau yayiba gashi dinkin yafitar da shape mai kyau,

"Kai amma fa dinkin sunyi kyau gaskiya nasamu tailor insha Allah daga yanzu kai zan rinka baiwa dinkuna na"

"To hajiya Allah yakawoki"

Daga haka yadauko babbar leda yafara ninke kayan yana zubawa aciki tana tayishi sai yabon dinkin take, daf da zasu gama zuba dinkin cikin leda ya dubeta ta kasan ido,

"Hajiya ba zaki gayyaceni bikin ba kuma?"

Murmushi bilkisu tayi,

"To ai sai dai ingayyaceka daurin aure"

"Ai ban san angwayenba"

"To zan gayyaceka dinner"

Sai da ya dan bude idanuwanshi sosai sannan ya marairaice murya,

"To ai idan nazo baza abarni inshiga ba tunda babu wanda yasanni"

Murmushi ta kumayi ta mika hannu zata dauki ledar kayan amma sai ya hanata yaci gaba da rikewa,

"Karka damu kowa zai shiga tunda bamu raba gate pass ba"

"To shikenan zanzo insha Allah hajiya.... Kodan inga yanda kayan nan zasuyi miki domin zanso ingansu ajikinki"

Ya karashe maganar ciki ciki ta yadda bazata jiba, ai kuwa bata ji dinba tadai ji abinda yafada dafarko amma daga karshe bata jiba, tana kokarin daukar kayan ya hanata ya daukar mata yana fadin,

"A'a hajiya bari na rakaki dashi"

"Ok nagode amma ina son shiga kasuwa ne akwai abinda zan siya"

"Karki damu babu komai muje"

"To nagode"

Handbag dinta ta dauka suka fito yana biye da ita, suna fitowa hamza na zuwa dan haka fahad bai rufe shagonba yawuce yabi bayanta, har cikin kasuwar ya rakata ta kammala siyan kayan kamshin sannan suka fito bakin titi inda zata hau napep, shine yatsaya domin tare mata amma duk wanda yatare sai yaga da namiji aciki sai yace suje da haka har yatare kusan guda uku ana hudunne yaga namiji daya mace daya, cemata yayi ta zagaya ta saitin macen saita zauna, hakan kuwa tayi ya kinkimi kayanta ya mika mata tana yimasa godiya, baice mata komaiba sai murmushin da yake aika mata dashi can akasan ranshi kuma yana cewa,

"Zanyi missing dinki"

Yana tsaye har saida yaga sun kule sannan yakoma shago, yana shiga da kamshinta yasoma yin arangama nan ya lumshe idanuwanshi aranshi yafurta,

"Kamshinki yafi na kowacce mace"

Zama kawai yayi saman benci yakasa cigaba da aikin da yafara, sai hamza yake tayawa hira wanda ke kan kekenshi yana dinka wani leshi, ahaka yar nacin nasa husna tazo ta sameshi, shifa yarinyar nan har mamaki take bashi kamar ba daliba ba yawonta yayi yawa yakan kasa gane lokacin da take shiga class, yana mata dinkin yana daddaure fuska ita kuwa ko ajikinta dan sai zuba take kamar kanyar da bata da zaki.

***

Haka al'amura suka cigaba da tafiya, abangaren su bilkisu dai kowa kagani acikin hidima yake domin biki yazo gaba daya gidansu angyarashi ansake masa sabon fenti sannan kayan falon amma suma ansakesu tun daga kan kujeru har tv da labulaye da sauransu, ada carpert ne malale afalon amma yanzu tiles akasa mai tsada sai katuwar plasma tv da aka manna abango ga kujeru kirar royal chairs nan falon ammi ya dawo tamkar na yarinya duk da tanata rokon Abba akan yabar gyaran haka yaji da kayan dakin yara domin aurar da yanmata biyu lokaci daya ba wasa ba amma yace itama so yake yadawo da ita amarya ai kuwa hakance tafaru domin gidan ba karamin kyau yayiba dan hatta dakin bilkisu Abba yagyare mata shi ansake mata labulaye sabbi sannan ansaka mata tv yar madaidaiciya abangon dake kallon gadonta sannan gefe ga dan fridge dinta ga uban fenti da dakin yasha nan daki yafito yayi fes dashi. Ana saura kwana biyu biki dakyar bilkisu tasamu ta tafi saloon da kunshi itada kawarta khulsum ba ita tadawo gidaba sai karfe biyar saura tana shiga dakinta tajiyo sallamar mutanen garko wato su iyallo, kasancewar daga ita sai daurin kirji yasa bata fitoba domin tana jiyo maganar ya mudan da alama shine yakawo su. Kai tsaye iyallo dakin bilkisu tashiga lokacin ita kuma tana toilet, ganin irin gyaran da dakin yasha yasata rike haba tana tafa hannaye tana zuba salati,

"Ah lallai wannan shine zama daram wato babu ma ranar tashi, irin wannan daki haka kamar agidan miji? Tab... To Allah yasawwaka, iye... Lallai.... Duniya sabuwa"

Juyawa tayi tabar dakin tafita ta nufi cikin gidan wato falon amma wadda ke can tana gaggaisawa da baki domin iyallo ba ita kadai tazo ba su wurin takwas sukazo ciki harda yayarta inna maigado takwarar bilkisu da kuma yayanta guda biyu wato kannen Abba gwaggo uwa da yafendo sai "yayansu,nan tazauna tana tabe taben baki da harare harare, sama sama ta amsa gaisuwar amma nan da nan aka cikasu da ruwa, lemo da abinci tunda dama ansan da zuwansu, shi dai ya mudan bai wani jimaba yakoma yabarsu anan. Bilkisu sarai taji abinda iyallo take fada lokacin da tashigo dakinta, tana wanka tana zancen zuci,

"Su iyallo trouble maker ansauka, haka kuma za ayita fama har sai ranar da kika bar gidan nan, Allah yarabamu lafiya"

Da zancen zuci tagama wankan tafito, ta shirya agaggauce tana saka kaya su Hindu na shigowa shiyasa koda tafito tare suka rankaya falon amma........



*_Ummi Shatu_*

© _*HASKE WRITERS ASSO.*_


*KAMAR DA WASA....!*




_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*7*



***Su maama sai yaba kunshin nata sukeyi yayinda ita kuma take yaba kwarewar mai gyaran jikinsu domin kwana uku kacal da fara yimusu har ta sauya musu kamanni, Hindu da maama sarakan rashin kunya ganin takalmansu iyallo tuni suka tura dan kwali gaban goshi duk da hararar da bilkisu keyi musu haka suka dauke kai, itace tafara shiga cikin falon uwar harara iyallo ta tarbeta da ita tana tabe baki sabanin inna mai gado da ta washe hakora tana yimata lale tamkar zata goya bilkisu dan murna da tsantsar kaunar da take yimata, suna tsaka da gaisawa su maama suka shigo, maganar iyallo ita ta katse kowa daga gaishe gaishen da akeyi,

"Ke samodara daga ina kika tafi kika bar yar labibiyar yarinya dan tsabar rashin hankali?"

Dauke kai maama tayi saboda tasan da ita take bata amsa mata ba ta nufi inna maigado domin duk sunfi sakewa da ita,

"Yanzu ke kuma dan Allah bakiji kunyaba? Kiduba ki gani duk kannenki sunyi aure sun barki, gaku nan ku hudun duk kanku daya" Iyallo tafada tana hararar bilkisu, ai rufe bakin iyallo keda wuya Hindu ta dora,

"Kuji iyallon nan da takura, to dan munyi aure mun barta sai me? Kuma ma naga ba wuce shekarun auren tayiba..."

"Ke kika kulata ma, wai wani nan munyi kai daya da ita to ai halittar tatace mai kyau shiyasa har ba a iya banbance itace babba cikinmu....kum...."

Tsawar da ammah ta daka musune yasa maama yin shiru bata karasa fadar abinda tayi niyya ba nan amma tashiga yimusu fada ta inda take shiga bata nan take fitaba, ita kuwa iyallo cewa take,

"Rabu dasu kibarsu su zageni kamar yadda suka saba, fitsararru dama me suka iya inbanda rashin kunya da rashin arziki? To wallahi bari uban naku yazo..."

Inna maigado ce tasoma tausarta tana bata hakuri ita dasu yafendo, su Hindu kuwa ko ajikinsu asalima tashi sukayi suka bar wurin suka wuce dakinsu.

***
Tunda su iyallo suka zo kowa yashiga takura acikin gidannan gata da fadan tsiya ga sa ido gashi bata iya gani tayi shiru komai tagani sai tayi magna,abinda inna maigado bata iyaba kenan shiyasa kullum cikin yimata fada take wannan dalilinne yasa su bilkisu basa son zuwa garko wurin iyallo saboda fadanta da masifa su maama ne kadai daidai da ita domin basa bar mata.

Haka dai aka cigaba da lallabawa, gida ya cika dam da yan uwan Abba da amma domin itama ana igobe sa lalle yan uwanta suka zo daga dawakin tofa, mota uku suka ciko da yayyenta da kannenta da sauran 'yayan yan uwa, bilkisu kam yanzu tazama ba zama domin har tafi amaren zama busy, ko hamood dinta sai yar hi hi sukeyi, haka shima fahad yanzu bai fiya samunta ba duk da hakan yana sakashi cikin damuwa amma yazaiyi dolensa ya hakura.

Ranar alhamis aka fara gudanar da biki domin ranar ne sakun lalle anan unguwarsu gidan aminin babansu mai sabulu anan akayi kamun kamar yadda al'ada ta tanadar,amare sunsha kyau mutuka cikin shigar da sukayi ta ruwan bula, itama bilkisu itada mama wani leshi suka saka dan ubansu sai walwali suke, an cashe mutuka sannan anwarwasa haka aka tashi kowa cike da farin ciki, agajiye likis bilkisu takoma gida bayan sallar magriba ga dakinta ma cike yake da baki dole sai dakin Abba taje tayi shirin bacci dayake har lokacin shi bai shigoba, ko takan wayoyinta bata biba taje ta kwanta adakinsu meenah domin ta huta.

Washe gari aka daura aure kuma ranar ne zasu gabatar da dinner party dinsu a al-mukarram event center,tun safe amare basu samu zama ba hakama bilkisu bayan an idar da sallar juma'a a babban masallacin dake cikin unguwar tasu ta hotoro aka daura auren, auren Hindu da angonta Mus'ab aka fara daurawa kasancewar itace babba akan sadaki naira dubu talatin sannan aka daura na meenah da angonta Isma'il itama akan naira dubu talatin,gidansu kancame yake da hada hadar jama'a koda akazo yin albishir din daura auren iyallo yada magana tai tayi da habaice habaice duk inda bilkisu tawuce kuwa ko amma ko su Hindu sai ta rakasu da harara su kam basu san tanayiba domin sabgar gabansu sukeyi, maama cema da hudah tayi kashi taje tana cire mata pampers iyallo tazo zata isheta da fadan akan me zatazo gaban rijiya tana yiwa mutane kazanta, ita kuwa maama ta gurmuda mata baki tana farfara ido rankwashi iyallo takai mata tana fadin,

"Fitsararriya yau dinma fitsarar zakiyi min abainan nasi?"

Maama bata kulataba ta sabi yarta tayi falon amma wadda ke can itada danginta da abokan arziki sukuwa su iyallo tasu tawagar ta yan garko suna sitting room.

K'arfe takwas da rabi aka fara tafiya wurin dinner,amare da angwaye ba karamin kyau suka sha ba haka itama bilkisu ta hade cikin material din da fahad ya dinka mata tayi masifar kyau tasha head golden dama yau babu maganar mayafi daga ita har kawarta khulsum basu samu zama ba domin sune masu tsara komai.

Cikeda doki fahad yasha wankansa cikin blue din tissue sabo fil da hularsa samfurin minister wacce ta saku da asalin dinkin hannu yayi kyau har yagaji, turaren Amirul oad yayi amfani dashi ya gauraya da turaren black xxs nan fa yafito tsaf dashi saurayi kalar birni, bakin takalmi sau ciki yasaka yadauki agogo yafita lokacin karfe takwas daidai na dare, sai da yashiga cikin gida yayiwa su ayiyah sallama mamuh sai tsokanarsa take tana cewa yagaida budurwar tasa, su Mariya kam saida ya cafki Maryam ya zuba mata rankwashi sannan yafita domin sashi sukayi agaba da dariya da kus kus, yayansa Abba yana zaune akofar gida yafito, shi dinma kallonsa yayi cikeda tsokana yace,

"K'anina yau hira aka nufa ne?"

Dariya yayi yawuce yana fadin,

"Wallahi wani biki zanje"

"To adawo lafiya"

Saida ya amsa sannan yawuce, koda ya isa almukarram event center tuni har wurin ya dinke da jama'a sai kawo mutane akeyi a motoci yayinda wasu sukazo a keke napep wasu kuma da kafarsu ma suka shigo cikin wurin, abangaren fahad shima yabi sahun wadanda suka shigo da kafarsu domin tafe yake hannunshi daya cikin aljihun wandonshi dayan kuma yana latsa wayarshi ta hannu, duk wanda ya kalleshi kallo daya baya iya gamsar dashi har sai yakara na biyu.

Yana isa gaban hall din yayi tozali da yanmatan amare sunsha anko kowacce naji da kanta, ido yashiga ciccilawa yana son yaga ta ina zai hango tauraruwar tasa amma bai samu damar ganinta ba har aka gama shigewa cikin hall din nan shima yamaida wayarshi aljihu ya shiga, kusa da wasu samari su uku yaje ya zauna dama mazaunin mutum hudune domin kujerun guda hudune, gefensu kuma wasu matane suma zaune su hudu, bai kai minti biyu da zamaba ya hango bilkisu tana rikeda hannun khulsum da wasu abubuwa a hannunsu wanda bazai iya gane ko menene ba, ji yayi yana dana sanin yimata wannan dinkin domin jikinta babu ko mayafi amma fa tasha kyau har tagaji kayan sunyi mata dadas ajikinta dukkan shape dinta yafito masha Allah, goshinsa yadafe ya sunkuyar da kai sakamakon sara masan da yaji kan nasa yayi, hankalinsa bai kara tashi ba sai da ya hangota kan step taje wurin amaren suna yin kus wadda babu wanda zai fahimci me suke cewa domin wurin sautin kidane yake tashi ahankali cikin wakar Umar m Sharif ta ranar kuke jira....!, yayi nadamar yimata dinkin nan domin gani yake kamar kowa na wurin ita yake kallo, sai da kowa ya nutsu sannan aka fara gudanar da shirye shiryen da aka tsara, taro da addu'a aka fara budewa sannan aka gayyaci babbar yaya wato bilkisu domin tabada tarihin amarya amma guda daya daga ciki, abunku da yar jarida wacce tasaba nan tazo ta zayyano tarihin Hindu daga karshe tajuya tana kallon isma'il angonta,

"Ango amaryarka tana da kiriniya sosai ada musamman wurin zane domin gaba daya bangon dakinsu da jikin wardrobe dinsu zanen tsintsaye ne da ciyayi, muna addu'ar Allah yasa bazata Zane muku bangon dakunanku da zanen tattabaru ba...."

Kowa na wurin saida ya dara nan ta sauka tabada abin maganar aka kira maama itama tabada tarihin auta minah. Duk inda tayi idanun fahad na kanta ji yake kamar yatashi yaje ya kareta mutane su daina kallonta amma babu damar hakan, lokacin da aka fara raba abinci da abin sha hirar matan dake zaune kusa dasu taja hankalinsa,

"Yanzu dai Yahanazu tagama auren yaranta saura maigado kuma babbar banza ko kunya bataji duk takai kannenta daki ita tana zaune agida..."

"Bakiga harda sake gyaran dakiba domin a tabbatar mana da ba ranar aure"

"Ai uwar tata ke daure mata kugu, idan taki fito da miji basai su hadata da duk wanda suka so ba..." Daya matar tafadi cikin takaici, idonshi ne yakai kan bilkisu wacce ke tsaka da hidimarta khulsum ta miko mata wayarta nan ta Karba ta nufi kofar baya, zip din rigarta ta baya ya dan sauka har hannun farar bra din jikinta ta dan leko amma saika lura dakyau zaka gani, cikin azama, kirjinsa yana fat fat yabi bayanta tana tsaye tana waya gadon bayanta duk awaje, cikeda kishi karara yatsaya abayanta ya kareta, jin tsayuwarshi yasata juyowa ta kelleshi bayan ta maida wayar kunnenta......



*_Ummi Shatu_*

© _HASKE WRITERS ASSO._


*KAMAR DA WASA....!*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



*8*


*Mai fitarmin da book kiji tsoron Allah haka kuma wadanda ake turowa kuji tsoron Allah kudaina karanta min mutukar ba siya kikayi ba saboda kamar da wasa wannan karon na kudine,idan kina so ki biya ki karanta.*


***Sai da idanuwansu suka sarke da juna sannan tajanye nata ahankali bayan ta juya masa baya, bayan nata yake bi da kallo kasa kasa, jin takun tafiya abayansu alamun wani na zuwa yasashi saurin kai hannu kan zip din yayi sama dashi hakan yayi daidai da karasowar khulsum wurin, saurin matsawa baya yayi yayinda ita kuma Bilkisu tajuyo atsorace amma ganin khulsum tsaye bayanta tana waya yasata sauke ajiyar zuciya domin tagane itace taja zip dinta ko kadan bata kawo cewar fahad ne ba, ita kuwa khulsum bata ma san abinda ke faruwa ba kawai dai ta iskesu tsaye ne, yayinda gogan ke tsaye yayi mata kurr da ido hannayensa sanye duka cikin aljihun wandonsa.

Kusan tsawon mintuna biyar ta dauka tana wayar daga bisani sukayi sallama da hamood dinta takatse wayar tajuyo tana kallon fahad dan tuni khulsum tabar wurin,

Langabe kai yayi yana kallonta tamkar wani yaro,

"Kazo ashe?..."

"Uhm hajjaju nazo tun dazu"

Murmushi tayi tana duba wayar dake hannunta,

"Zaka jira atashi ai ko?"

Girgiza kai yayi har lokacin kansa langabe yake,

Please Login or Register in order to submit comment