Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu a asibiti aka sallameshi bayan andorashi akan magani sannan duk karshen wata zai rinka zuwa yana ganin likita, da yamma aka sallamesu suka tattara suka koma gida. Wanka yashiga yasamu yayi yafito Abba da salim na zaune saman katifa salim na karanta labaran da BBC suka saki akan Facebook,yarfe hannu fahad yayi domin har lokacin hannunsa na dama akwai cannular ajiki wadda har hannun ya dan kumbura kadan musamman ma wurin da aka saka cannular din, zama yayi gefen katifar yana duba kayan da zai saka yana ji aransa dole yabar garin kano domin yayi masa zafi bazai taba iya cigaba da zama agarinba,

"Yazama dole ma inbar garin nan wallahi....."


Dagowa Abba yayi ya kalleshi sannan yagyara kishingidar da yayi agefen katifar,

"Kamar ya?"

"Ya Abba wallahi bazan iya cigaba da zaman garin nan ba.... Gaba daya garin yafita akaina"

"To ina zaka tafi?" Salim ya bukara yana kokarin tashi zaune,

"Salim karatu zan koma...., kuma ba arewa ba, kudu zan tafi idanma son samune inbar kasar gaba daya ko Niger ne intafi"

"Fahad kenan sai hakuri fa rayuwar nan, kayi hakuri kadauki abinda yafaru dakai a matsayin jarrabawa...."

Jin abinda yaya Abba yafada yasashi yin murmushin dole shi kansa ajikinsa yana jin irin ramar da yayi duk yadawo wani shafal shafal dan har yakasa da akiba, bai sake magana ba yadauki bakar round neck t shirt mai gajeren hannu yasaka sannan yasa blue din wando yamike yana laluben turarensa yana jin zuciyarsa na suya,

"Bilkisu wallahi kin yiwa zuciyata tabon da bazai taba gogewa ba har abada......" Yafada acikin zuciyarsa yana kokarin feshe jikinsa da turare, yana gamawa yanufi kofa zai fita domin so yake ya dan fita ya zagaya ko zai ji karfin jikinsa saboda yanzu kam baida wani karfi na azo agani,maganar salim ta dakatar dashi daga yunkurin fitar da yayi niyya,

"Lover boy ga husnah fa na magana a whatsapp....."

Komawa yayi da baya yakarbi wayar yana duba sakon nata kamar haka,

_My prince ya jikin? Kasamu kayi wankan kaci abinci....? Dan Allah karka zauna da yunwa_

Murmushin karfin hali yayi yana kallon salim da ido salim yayi masa alamar tambaya, daga girarsa guda daya yayi ya tsuke baki har lokacin fuskarsa dauke da murmushi, dariya salim yayi,

"Abokina kenan.....,husnah fa kullum idan taje dubaka sai tayi kuka"

Kafin fahad yayi magana Abba yatashi yafita yabar musu dakin gaba daya dan suji dadin tattaunawa dakyau, su dinma basu wani jima acikin dakinba suka fita, da kafa suka dan bi lungunsu fahad har zuwa bakin titi domin fahad ya ware kafarsa sai magrib sannan suka koma gida. Cikin kwana biyu jikinsa ya dan warware yaji dama dama amma kuma har lokacin raunin dake cikin zuciyarsa bai warkeba kawai yana daurewa ne sannan yaji dadin cewa baba saki uku yayiwa bilkisu domin da yace saki dayane yasan dole atursasasu sake zama da juna koda kuwa bata so shikuma bazai so hakanba.

***

A bangaren bilkisu kuwa tana kammala idda abba yace hamood dinta yafito saboda kowa agidan yasan hamood hatta iyallo mutanen garko tasan da zaman hamood domin har gida yaje ya gaisheta yakai mata sha tara ta arziki, khulsum itama ba abarta abayaba wurin yiwa hamood campaign saboda tasan asalin soyayyarsu tun farko duk da bataso rabuwar bilkisu da fahad ba kuma hakan bawai yayi mata dadi bane to amma babu yadda za ayi tunda bilkisu tace saki ukune shima kuma fahad din kamar hadin baki saki uku yace yayi mata. Cikin kankanin lokaci hamood yatura uncle dinsa yaje wurin Abba nan zancen aure ya kullu domin shi Abba baya son zaman zawarcin nan shiyasa yakeso shima ayi bikin da gaggawa, shima senator barewa baija lokacin da tsawo ba yace nanda wata daya sai asha biki sannan kar akai bilkisu da ko cokali yadauki nauyin komai saboda gaba daya 'yayansa ne, aifa nan bilkisu aka shiga shirye shirye da gyare gyaren jiki kowa na gidan cikin farin ciki yake saboda bilkisu baza tayi dogon zawarci ba su elmustapha ne kadai da suka zo hutu basu ji dadin aurannan da zatayi ba domin haka kawai sukaji jininsu bai hadu da na hamood dinnan ba, biki saura sati biyu aka kawo lefe akwatuna goma masu tsada da kyau komai naciki na dunbin kudine nan shirye shirye suka sake zafi babu kama hannun yaro domin hamood yace har dinner zasuyi domin wajibine suyi kara'i. Cikin kankanin lokaci aka kammala komai bilkisu ansha gyara iya gyara duk wani gyara na amare tasha shi sannan tasha tukudi kamar babu gobe domin iyallo ce tazo dashi galan galan tun ana saura sati daya biki dama burinta taga bilkisu tayi sure bawai tasake zama agida ba shiyasa farkon mutuwar auren tazo tayita zuba masifar da kowa na gidan saida yayi la'asar kuma tace lallai lallai bilkisu tafitar da miji tana gama idda aure zatayi wannan dalilinne yasa lokacin da aka gabatar mata da hamood tarinka taka rawar murna. Ranar juma'a aka daura aure ranar asabar akayi yinin biki kuma aranar za akai amarya dakinta sannan za aje dinner, daga amarya har ango farin cikinsu bazai misaltu ba da misalin karfe 8 aka tafi wurin dinner sannan daga can za awuce akai amarya, amarya da ango sunsha dark purple din kaya sunyi kyau mutuka kuma sun burge, har karfe 10 ana wurin dinner din daga can aka raka amarya sannan kowa yasan inda dare yayi masa, gidan amarya yasha kyau a unguwar sabuwar G R A, babban gidane mai dauke da upstairs kasa falo da kitchen da dining area da bedroom guda daya sai sama mai dauke da corridor da kuma bedrooms guda biyu, gaba daya yanda aka tsara gidan yaburge bilkisu, bata wani jima ita dayaba hamood yashigo dauke da kaji da kayan motsa baki, zama yayi kusa da ita yana murmushi,

"Sweetheart yau dai burinmu ya cika, muna yiwa Allah godiya..."

Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, kamar yadda addini ya tanadar saida sukayi salla raka,a biyu sannan suka zauna zaman ciyar da juna abinda yashigo musu dashi sunayi suna yan wasanni irin na masoyan da zuka jima acikin tafkin kauna suna linkaya, dakinsa yakoma domin yin shirin bacci kafin yadawo tuni itama tashirya cikin nata kayan baccin masu daukar hankali, tana kwance lamo yashigo sanye da riga da wando dark blue yazo ya kwanta abayanta tareda dora kansa bisa nata, ahankali yake yimata tafiyar tsutsa agashin kanta wanda yasha gyara dan gaske, sun dan fara nisa kadan cikin kogin so suka fara jiyo bugun kofa mai sa firgici wanda ke nuni da ba lafiyaba domin Wanda ke yin bugun tamkar zai balle kofar haka yake yi, cikin bacin rai tare da jan tsaki hamood yatashi yamaida rigarsa yafita dan ganin ko waye itama batayi kasa agwiwa ba tabi bayanshi bayan ta mayar da kayanta, tana zuwa falon kasa yana bude kofa, wata farar matashiyace tashigo taci daurin dankwali irin na yan duniya gaba daya zubinta ma irin na yan bariki ne, wani kallon baki isaba tasoma watsawa bilkisu daga sama zuwa kasa sannan tamaida dubanta ga hamood,

"Meye haka? Me zan gani ni wasila? Dama munyi haka dakaine?..."

"Yi hakuri wise bakya ganin yanzu dare ne?"

"Ina ruwana da wani dare? Malam bafa haka mukayi dakai ba.... Wato kai ga ango ko jikinka sai rawa yake zakasha angonci, to ayi angoncin nagani..... Wuce mutafi...."

Matsawa sosai bilkisu tayi tana karewa matar da hamood yakira da wasila kallo wacce ahaife bazata girmeta ba,juyawa yayi ga bilkisu cikin sanyin murya yace,

"Bilkisu yi hakuri bari naje nadawo, karki damu zuwa safe zan dawo...."

Wani kallo bilkisu tayi masa sannan tamaida kallonta ga wise wacce ke tsaye tana karkada kafa ta taro dan kwalinta gaban goshi alamun no respect,

"Haba hamood ina zakaje awannan daren? Ita wannan din wacece? Menene matsayinta agareka? Meye hadinka da ita da har zatazo ta fitar dakai daga cikin gidanka a wannan daren....?"

Bai samu damar amsa mata tarin tambayoyin da ta jero masa ba sai kwaya daya inda yafurta,

"Matata ce....."

Kafin bilkisu tayi magana wise ta rigata,

"Kana bata min lokaci fa..."

Bai sake bi takan bilkisu ba yawuce gaba wise na biye dashi kamar wani danta, akan idon bilkisu suka shiga motar wise suka bar gidan, kallonta ta maida kan agogo karfe 1 saura nadare......


*Dan Allah idan har kin san baki siyaba karki karanta min littafi domin na siyarwa ne.*


*_Ummi Shatu_*


© *HASKE WRITERS ASSO.*


*KAMAR DA WASA....!.*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



*30*



****Zama bilkisu tazame tayi awurin tana dafe kanta da hannunta guda daya wanda yasha kunshi radau,

"Wannan wacce irin masiface? Adaren amarcina za azo atafi min da miji abarni ni kadai....."

Agogo tasake kalla nan ta kura masa ido kamar tana son gano amsar tambayarta awurinne domin ko kiftawa batayi, tsabar bakin cikima ko tsoro nemarsa tayi ta rasa dadinta daya dai gidan akwai mai gadi, ganin zaman da take babu abinda zai amfana mata yasata tashi dakyar kanta yayi mata masifar nauyi taja kafarta wadda ta tari jini saboda tsabar zama atakure tawuce cikin bedroom, tana kwanciya idanuwanta suka kai kan wayoyin hamood guda biyu dake kashe ajiye kan bedside drewar sai agogonshi na azurfa wani abu taji yataho ya soke mata zuciyarta sai kuka kamar anbude bakin fanfo, har asubah takai tana hawaye domin tarasa gane da wacce kalma zata kira wannan abinda yafaru shin da wulakanci zata kirashi ko kuma da tozarci?.

Har asuba bata samu ta runtsa ba saida tayi salla ne bacci ya kwasheta nan kan rug din da tayi sallar, bacci tayi mai cikeda mafarkai daban daban wanda takasa tunawa bayan ta tashi, wanka tayi ta shirya duk zuciyarta akuntace domin tana cikin matsananciyar damuwa, sake kwanciya tayi domin bata san me zatayi ba kwata kwata ahaka har rana tafara yi nan yunwa tasoma damunta, fita tayi zuwa falon dake kasa,abubuwan da hamood yashigo dasu adaren jiya su ta dan kakkarima taci tsabar bakin ciki ko wayarta bata kunna ba domin bata bukatar kowa ya kirata. Karfe sha biyu da wani abu su iyallo sukazo itada dasu Hindu sun rakota zatayi ma bilkisu sallama saboda ayau zata koma garko, su elmustapha ne suka kawosu shiyasa bilkisu ta dan samu ta warware daga kuncin da take ciki domin ko ba komai ganin yan gidansu yasata farin ciki,

"To shikuma mamuda yake ko hamidan yana ina?"

Iyallo tajefeta da tambaya tana tsaka da kwankwadar lemon kankana mai sanyi, saida kowa yayi dariya jin sunan da iyallo ta kakabawa hamood,

"Yanzun nan yafita iyallo dan bamu san zakuzo bane ma da babu inda zaije sai ya jiraku...."

"Allah sarki ai babu komai, nidai abinda zan fada miki shine kinga dai ke yanzu ba yarinya bace, dan haka ke zaki yiwa kanki fada basai kin jira wani yayi miki ba, kiyi hakuri ki zamanki adakinki kamar sauran yan uwanki..... Allah yakawo kazantar daki, mai gado kema Allah yabaki magaji, Allah yabaki yara masu albarka kisamu na aike....." Ajiye lemon hannunta tayi tahau matsar ido nan maama ta dunguri meenah suka hada kai suna kuskus,

"Hajiya iyallo to kuma menene abin kuka?... Kufa matsalata daku bakwa rabo da koke koke...." Inji emustapha,

"Ai sabgar mata akwai ban haushi malam.... Komai abin kukane... Suyita yiwa mutane kuka akan abinda bai kai yakawo ba" El'ameen yakarbe zancen,

"Kai naci gidanku.....kai mai sunan malam jakar ubaka..."

Dariya el'ameen yayi yamike yana gyara earpiece din dake kunnensa,

"Oho dai idanma kin zagi ubana ai danki kika zaga...."

Salati iyallo tafara yi tana fadan wai ita ba danta ta zaga ba domin danta dan albarkane yakaita hajji yakaita umarah sannan yagina mata gida mai kyau dan haka babu abinda zatace dashi sai Allah yayi albarka, duk da bilkisu natare da damuwa amma caftar su iyallo da jikokinta tasata nishadi ba kadan ba, kayan zakin da suka kawo mata cikin bokitai suka shigar mata kitchen sannan suka tafi ai kuwa ji tayi kamar ta dora hannu aka tafasa ihu. Har kofar gida ta rakasu saida taga tafiyarsu sannan takoma ciki, kwanciya ta sake yi saida aka kira sallar azahar sannan tatashi, tana cikin yin sallar taji zuwan wasu bakin shiyasa ta hanzarta ta idar tafito, yan gidansu hamood ne da matar uncle dinsa da yaran gidan guda biyar sudinma sallama suka zo yimata saboda zasu koma birnin tarayya ayau, basu wani jima ba shiyasa ko snacks din da takawo musu basu ciba sai packaging dinshi tayi musu suka tafi dashi. Ahaka takarasa wuninta cikin rashin walwala da bacin rai har dare babu hamood babu labarinsa gashi yabar wayoyinsa duk agida bare ta tuntubeshi taji a ina yake. Daren yauma sai bacci barawo amma tajima batayi bacciba tanata sakawa da kuncewa, washe gari ma hakance ta kasance hamood shiru har kirjin azahar dai dai lokacin khulsum tazo tanata tsokanar bilkisu ita dai bata da tacewa saboda damuwar dake cikin ranta tafi gaban kwatantawa,

"Wai ina angonne inyi masa tsiya, shikenan sai ya boye min kawata ko awaya inkasa samunta?"

Murmushin yake na dole bilkisu tayi tace,

"Ai kuwa yafice tun sassafe saboda yanada uzuri kin san kamfanin saida motocin uncle dinsa shike kula dashi to shine aka kirashi...."

"Ahhh cewa zakiyi yatafi yasamo muku kudi dai labour..."

Dariyar da ta tsaya a iya fatar baki kadai tayi,da taimakon khulsum suka dan girka abinci bayan tabawa mai gadi yaje ya iyo mata cefane, har yamma khulsum na gidan tana bata labarin saurayinta wanda take son aure, ita dai bilkisu kawai tana zaune ne amma gaba daya tunaninta na ga hamood kacokan tana ta son sanin inda yatafi, daf da magriba khulsum tatafi nan kuma taci gaba da zaman kadaici da damuwa.

Wasa wasa saida hamood yayi kwanaki hudu sannan sai gashi da ranar Allah yashigo yasha farar shadda kal sabuwa fil da hula harda dan farin glashinsa na ido dayake shima kyakkyawane babu laifi domin black beauty ne ga hanci, mikewa bilkisu tayi cikeda fushi ta juya masa baya alamun tana cikin bacin rai, kamota yayi yadora akan cinyarsa,

"Hamood ashe haka amana da soyayya suka ce?"


"Sweetheart.... Kiyi hakuri.... Tun farko ban sanar dake cewa inada mata ba wallahi babu yanda zanyi ne.... Hadin iyaye ne shiyasa kawai ban fito na fada miki ba...."

"Ni hamood ba wannan ne damuwata ba, damuwata shine yaza ayi adaren amarcinmu wata mata tazo ta tisaka agaba tatafi dakai kuma wai kabita baka dawoba saida ka shafe kwanaki hudu..... Saboda Allah kun yimin adalci?"

"Kiyi hakuri sweetheart...ai ban sanar da ita bane shiyasa amma nayiwa tufkar hanci hakan bazata kara faruwa ba...."

Duk da haka nunawa tayi bata hakura ba nan yasoma lallashinta wanda daga karshe lallashin yasoma canja salo domin gaba daya ya canja akalarsa izuwa wani fannin daban, bedroom din dake cikin falon suka yiwa shigar bazata domin farantawa junansu, al'amari yafara nisa amma kuma sai me kwata kwata hamood ji yayi baida kuzarin da zai iya aiwatar da wani abu awannan lokaci domin gaba daya halittarsa bata koda motsi tamkar lagwanin da yayi shekara acikin kalanzir yayi laushi haka yazama nanfa wani tashin hankali da damuwa da bacin rai suka dirar musu daga bilkisu harshi domin kowa anasa hasashen laifin dan uwansa yake gani kokuma matsalar kowa gani yake daga daya bangaren ne banasa ba.......



*Kamar da wasa na siyarwa ne, me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*


*_Ummi Shatu_*

© *HASKE WRITERS ASSO.*



*KAMAR DA WASA....!*



_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*31*



****Cikin fushi da bacin rai hamood yafice daga cikin dakin yakoma falo daga shi sai gajeren wando, sam batayi yunkurin binsa ba saboda ita dinma cike take da bacin rai, kusan mintuna ishirin ta debe ahaka kafin tatashi saboda jin anata kiraye kirayen sallar la'asar, lokacin da tafito falon abinda idanuwanta suka gane mata yayi masifar razanata, hamood zaune yadora daya akan daya idanuwansa jajur hannunsa rikeda tabar sigari yana busawa shiyasa gaba daya falon ya turnuke da warin sigarin,

Gabansa taje gabanta sai faduwa yake zuciyarta na bugawa,

"Hamood.... Meye haka kakeyi? Subhanallahi dama kana shan sigari.....?"

"Idan raina yabaci ba.... Ai dole nasha sigari mai gado... Irin wannan zafi da kika hada min ai yazama confirm in dan wartsake...."

Gaba daya ita rasa ma abinda zatace tayi saboda mamaki da takaici shiyasa kawai tawuce sama tashiga dakinta tayi wanka tazo tayi salla tana idarwa ta sauko amma wayam babu hamood wato har yasake komawa inda yafito batare da yayi mata sallama ba ko? Ta ayyana hakan acikin ranta, sosai taji hakan yayi mata ciwo, kitchen tawuce ta debo snacks tazo ta zauna taci. Zaman kadaici tayi har dare yayi tanata zuba idon hamood shiru gashi bai dauki wayoyinshi ba kai asalima tunda yashigo gidan bai leka ko cikin bedroom ba iyakscinsa bedroom din da ke kasa, har lokacin bacci yayi taje ta kwanta hamood bai shigo cikin gidanba ita kanta gaba daya takasa bacci daren wannan rana sai misalin karfe 12 nadare hamood yashigo cikin gidan cikin yanayin da yakara tsorata bilkisu game dashi domin acikin maye yashigo har dakinta yafado yana hada hanya yana layi,

Cikin zazzare ido tamike zaune tana kallonsa bakinta yana rawa,

"Hamood.... Innalillahi.... Wai dama kana shaye shaye ne? Haba hamood meyasa zakayi min haka? Wannan wacce irin rayuwace?...."

Cikin maye ya nunata da dan yatsa,

"Babu ruwanki da rayuwata..... Ko kabarinmu daya? Bana son takurawa...."

Mikewa tsaye tayi cikeda damuwa da bacin rai,

"Ai ko ba kabarinmu daya ba yazama dole infada maka gaskiya amatsayina na abokiyar zamanka, yau kwata kwata kwananmu hudu zuwa biyar da aure amma gashi nan munanan dabi'unka sun fara bayyana... Seriously am highly disappointed....."

Ai kafin tarufe bakinta ya dauketa da wani gigitaccen mari, dafe kuncinta tayi cikeda mamaki baki abude tana kallonsa,nan ya nunata da dan yatsa,


"Idan kika kara zagina sai na ballaki....."

Bai kara magana ba yafada saman gadonta yakwanta rub da ciki, ko takalmin kafarsa bai cireba, gaba daya tayi mutuwar tsaye ita kam ganin irin marin da hamood ya zabga mata she can't believe wai yau itace acikin wannan rayuwar itada hamood, tajima tsaye kamar wadda aka kafa kafin tanemi wuri ta zauna tana kallonsa yanata sharar baccinsa cikin maye,

"Ohhh Allah.... Ya Allah kayi min maganin wannan masifa...."

Dakyar da sudin goshi tasamu bacci ya dauketa saboda tajima bata samu bacci ba kai rabonta da bacci isasshe kuma mai dadi tun kafin bikinta. Asubar fari ta tashi tayi salla tsakanin mata da miji sai Allah hakan yasa tasoma tashin hamood akan yatashi yayi salla amma fafur yaki tashi daga karshe ma da ta matsa masa afusace yabude ido yadago ya daka mata tsawa,

"Malama wai sallar nan ubanki zan yiwa? Karki sake ki kara tashina..."

Jin abinda yace yayi mutukar razanata, wai ita hamood ke fadawa haka? Rabuwa dashi tayi saboda taga kamar har lokacin mayen bai gama sakinsa ba, anan ita kam taci gaba da zama har gari yagama wayewa, wanka tayi tashirya ta sauka kasa ta shiga kitchen duk ranta adagule zuciyarta a cunkushe wato dama ance zauna da mutum kaga halinsa wato shi hamood wadannan ne nasa halayen kenan? Ahaka ta kammala hada breakfast dinta tanata zancen zuci bayan ta kammala takai kan dining takoma sama lokacin karfe goma tawuce, sai lokacin hamood yatashi bai ko kalleta ba yashiga bathroom babu jimawa yafito yawuce dakinsa domin shiryawa bin bayansa tayi agabanta yashirya yasake fitowa tana ganinsa baiyi salla ba nan abun yasake daure mata kai, kai tsaye dining yaje tana biye dashi yaja kujera ya zauna itama haka,

Chips yasoma ci da spoon yana kunna wayarsa wadda bilkisu bata san da itaba sai yau,

"Hamood ina kwana....?" Takatse shirun nasu,

"Lafiya lau sweetheart...."

Shiru dukkaninsu sukayi sai zuwa can ta saki ajiyar zuciya dama ita ba abincin take ciba kawai tana jujjuyashi ne,

"Hamood meyasa dan girman Allah ka dauki dabi'ar da ban sanka da itaba ka yabawa kanka....? Hamood dama kana shaye shaye ne? Jiyafa da daddare har marina kayi sannan da asuba ka zagi ubana, gashi yau ko sallar asubah banga kayi ba...."

Saida ya ja wasu seconds sannan yadago ya kalleta,

"Kiyi hakuri sweetheart wallahi duk wadannan abubuwan ban san lokacin da nayisu ba, amma hakan bazai sake faruwa ba, jiyane kin bata min rai dayawa wallahi, duk yanda akayi tsohon mijinki dinnan banzan yaron nan baiso aurenmu dakeba shiyasa yayi min asirin da zan kasa kusantarki..."

Ajiyar zuciya taja ta sauke tana kallonsa,

"Bana tunanin fahad zai aikata abinda kake fada nidai ashawarata kaje asibiti sannan ka binciki wannan matar taka...."

"Matata bata aikata komai ba bilkisu ni nafi danganta matsalar dake tunda ita ko yaushe naje gareta lafiya lau nake gabatar da al'amurana kinga kuwa idan hakane matsalar daga gareki ce..."

Shiru tayi saboda ta fuskanci hamood bazai taba ganewa ba tunda bai san kaidin mataba, har ya kammala babu wanda yasake cewa komai mikewa tsaye yayi,

"Ni nafita.... Zanje office"

Bai jira cewarta ba yafice, tagumi ta rafka bayan tasauke ajiyar zuciya, ranar ma bai dawo gidanba sai 12 amma ba acikin mayeba.


Haka dai aka cigaba da zaman doya da manja domin ta fuskanci salla kwata kwata bata dameshi ba gashi da saurin fushi abu kadan zai hau yafara zagin mutun ko zagin iyayenshi, satinta biyu agidan ranar da yamma daf da magriba sai gashi rikeda babbar trolley wasila na biye dashi tasha attach da wani siririn mayafi, tana zaune afalo suka shigo dama gama girkinta kenan tayi tuwon semo miyar agushi wacce taji busasshen kifi, ganinshi tareda wasila abin yayi mutukar Sosa ranta shiyasa ta dauke kanta. Cikeda rashin damuwa suka karaso ciki hannunsu sarke cikin na juna, wani kallon banza wise kebinta dashi amma ita bata saniba saboda bata ko kalleta ba, gabanta hamood yakarasa yana kallonta,

"Sweetheart dan Allah wasila zata dan zauna damu na tsawon wani lokaci....."

Dagawo tayi ta kalleshi kallo mai kunshe da ma'anoni daban daban batare da ta tanka masa ba tawuce tanufi sama, ajiye trolley din yayi yabi bayanta,

Tana zaune kan stool din dake gaban dressing mirror tayi tagumi tacika tayi famm, tsugunnawa yayi agabanta,

"Haba sweetheart bai kamata fa kiyi hakaba, menene abin damuwa anan? Wasila fa bazata wuce 2 weeks ba zata tafi...."

Harararsa tayi sannan ta kawar da kai gefe,

"To meya hana tazauna anata gidan da zata biyoka nan?"

"Dan Allah kiyi hakuri gidan nata ake dan gyara mata kin san kuma mata da neman fitina musamman wadanda aka yiwa kishiya kiris suke jira suce kayi musu laifi...."

Dakyar dai yasamu ya lallasheta ta sauko,

"To tashi muje kasa..."

"Kaje ina zuwa, sallah zanyi"

Tashi yayi yafita ita kuma tashiga toilet tayi alwala tazo tayi salla tasake gyara fuskarta sannan tasauka kasa, wani karin bakin cikin ta tarar domin hamood ne da wasila kan dining sun gama cin abincin da tasha wahala ta girka kuma ita girkinta batayi da wise ba iya daidai cikinta da na hamood tayi tunda bata san da zuwan wise dinba, fuskarta adaure ta bubbude flasks din nan taga wayam sai ko gutsattsari nanfa tasake hasala ta kalli hamood yayinda ita kuma wise ke kallonta up and down,

"Hamood meye haka dan Allah? Waye yasa ku cinye min abinci?"

"Ayya sweetheart ai nazaci kinci naki wannan nawane shiyasa muka ci...."

"Koda nakane ai kamata yayi kujirani nasauko bawai kawai ku saka agaba ku cinye ba"

"To dai aikin gama yagama just kawai kisake shiga kitchen and find something sharp sharp sai kici ko indomie ne...,bari ni naje nayi salla"

Daga haka yamike yafita ita kuma wise tatashi tawuce bedroom din kasa, kallon wurin da suka ci abincin tayi duk sunyi kaca kaca dashi da miya kamar kajine suka ci kokuma masu bulallen baki, cikeda bacin rai tagyara wurin taje kitchen ta dafa tea taci da snacks takoma daki. Tunda wise tadawo gidan sai abubuwa suka sake kazanta domin ko abinci taci anan zata bar flate din bazata daukeba sai dai bilkisu ta dauke sannan baza tayi girki ba sai wanda bilkisu tadafa zata ci da bilkisu tasamu hamood tayi masa complain sai cewa yayi ita wise bata iya girkiba dan ko shiga kitchen wahala yake mata tayi hakuri har sai ranar da wise din takoya, maganar matsalarsu kuma da ta tuntubeshi akan suje asibiti sai cewa yayi shifa lafiyarsa kalau dan haka babu asibitin da zaije saboda awurinta ne kadai yake fuskantar wannan matsalar amma awurin wise rass yake, ita dai adaddafe tazauna da wise har na tsawon sati biyu kowa harkarsa yakeyi ba ruwan kowa da kowa aikin gidanta kuwa ita keyin kayanta amma wise ko cokali bata dauke mata wani lokacin ma idan tagama cin abinci haka zata yi ball da kwanon komai tsadarsa shiyasa daga ranar da tazo gidan

Please Login or Register in order to submit comment