Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinta ya gama macewa, kunna bedside lamp yayi ya 'kuarawa face dinta ido, har lokacin idonta na kulle tana kuka. "Zaki min shiru kose na fasa baki, ya fa'di yana watsa mata mugun kallo, shiru tayi kaman an 'dauke ruwa ta shiga shan zuciya.
"Jawota yayi cikin jikinsa ya rungumeta gamida kwanciya, har lokacin shan zuciya take ta razana sosai da hidiman yaHaidar. A haka barcci mai nayi yayi awon gaba da ita.
"Kurawa fuksanta ido yayi tana barcin, a fili ya furt sleeping Beauty. Kwanciya yayi gamida mannata sosai cikin jikinsa yana sha'kan dadda'dan kamshinta, a haka shima barci barawo ya sace shi, bacci mai da'di wanda ya jima beyi irinsa ba.
"Tana jin fitansa sallan asuba, bayan ya fita ta mi'ke da niyyan fita amma taji 'dakin a kulle alamun kulleta knn yayai. Tsaki taja tace mugu kawai Allah ya isa na wllhi, bathroom dinsa ta wuce tayi alwala tazo ta tada sallah. Bayan ta idar nan kan sallaya bacci ya kuma 'dauketa. "Koda Haidar ya shigo ya ganta be tasheta ba saima daurata bisa gado da yayi. Kwanciya yayi gefenta bacci yayi gaba dashi shima.
" 'karfe 7:12am ta farka ta ganta rungume cikin 'kirjin yaHaidar, ta 'dan juyo tana duban fuskansa, hankali kwance yake barcinsa, kyakyawan fuskansa sai haske yake ta sau'ke idonta kan gashin giransa wanda yake kaman an zana yayi kyau da kyawawan idanunsa dukda a rufe suke. Ta'be baki tayi sanda idonta ya sau'ko kan pink lips 'dinsa a ranta tace "ga mutum har mutum fuska fari tas zuciya ba'kikirin. A hankali ta zare jikinta ta fice daga 'dakin.

_10:00am_
"Tun daga waje kake jiyo hayaniyansu suna murna results din waec dinsu dan masani ke duba masu a computer. Dukansu sun fita da grades masu kyau sai murna suke. "Yana jiyo hayaniyansu yayi tsaki yace a ransa idiots, fasa shiga sashen mamy yayi ya wuce sashen Abba nan ya tarar da mamyn ma, Abba na breakfast mamy na gefe tana hada masa shayi Haidar yayi sallama ya shigo...
"Da murmushi saman fuskokin iyayen nasa ya gaisa dasu. Sai nan nan suke dashi ya jima suna hira nan shima yayi breakfast kafin ya fice yana fa'din bari ya gaisa da Anty Hiba. Mamy tace afff ai bata nan tayi tafiya 'dazun nan.... "Tafiya kuma babu sallama ya fadi yana uban mamy. Mamy tace a a bawai ta tafi ba knn, sun kirata ne daga can kadunan magan NYSC dinsu zasu shiga camp yau dinn so zataje tayi report cewa ita matar aurece. Inaga ma gobe ko jibi ta dawo Ajmal ma na nan. Haidar ya gyada kai yace ok Allah ya kaita lafia.
"Mamy da Abba suka amsa da ameen. Daga nan Haidar ya fice ya nufi sashen Inna...

"Tunda Anty Hiba ta tafi Hanifa ta samu sau'kin zuwa dakin yaHaidar, mamy ko ka'dan bata ta'kurata abinda take so shi akeyi. Lokacin da Anty Hiba ta dawo ma hidiman biki ake ake sosai mutane sun cika gidan da wnn dalili Hanifa ta sami sau'ki amma tasan dabadon haka da Anyy Hiba ta ta'kura ta.
"Me gyaran jiki musamman aka 'dauko daga sudan dan gyaran amarya, dole Anty Hiba tasa akayi wa Hanifa gyaran kwana biyu dukda dogging da tatayi amma saida Anty tasa aka mata, a cewarta gwara ta tashe da gaske kafin 'kadangarun bariki su wafce mata miji, Hanifa kam ta'be baki tayi a ranta tace anyi gyara ma wofi dai...

"Yau ake saka lallen amarya Shema'u su Hanifa ba'a sama ba'a 'kasa biki things kawai💃🏻, rabonta da saka yaHaidar a idonta ta kai kwana biyu. Hakan ba 'karmin da'di ya mata ba, suna zaune a haraban gidan da yamma suna jira isowan 'kawayensu da sukayi sch tare daga KT, Hanifa Sadiya da Sumayya sun sha lalle sun sha kyau musamman Hanifa da aka mata gyaran jiki, saikace tauraruwa haka ta koma asalin kyaunta ya da'da fitowa, wayan Sadiya ne ya hau ruri.... ta dauka da sauri tana fadin kun shigo Kanon ne? Ok drivern ya gane layin toh shiknn, eh gidan ne kuyi horn kawai za'a bude maku gate.... tana gama wayan da mintuna kadan suka ji 'karan bude gate.. ai kuwa wata hamsha'kiyar motace 'kirar BMW ta shigo... driver na gama parking suka karaso da gudu suna rungume juna, irin an jima ba'a ha'dun nan ba," Laila Sirika da Jesmin Masanawa ne kawayensu na sec sch suka halarto bikin.
"Lailo ta kalli Hanifa tace " kambu Hany see how you look fine, as if na you be the bride, gaba daya suka sa dariya, Jesmy tace kunga nifa na gaji mu 'karasa ciki pls, gaba daya suka wuce ciki, saida suka kaisu suka gaidasu mamy kafin suka masu masauki aka cika gabansu da kayan ciye ciye da shayeshaye irir da kala.

"Washe gari akayi kamu da yamma a gidan, amarya da 'kawayenta sunsha kyau, yana zaune a garden yanata raba ido ta ina zaiga Hanifa amma wayam be ganta ba sosai abin ya damesa, musamman tunda aka soma bikin nan be ganta ba duk sai yaji babu da'di wanda shi kansa baisan dalili ba.

"Ranar da aka daura aure akeyin dinner da daddare, yana kwance a 'dakinsa wayan Saif yafi so nawa be 'daga ba yasan zancen bazai wuce ya shirya su tafi event din bane. " can wani tunani ya fa'do masa yasan dole Hanifa zataje kuma yasan dole maza su kalleta tunda event din both maza da mata ne. Kaman wanda aka zabura haka ya mike yana fadin " No, no way it can't be. Shiryawa yayi cikin wata skay blue jampa, ya buga hula zanna bukar, ya daura agogon rollex silver. "Wayyo Allah sosai jampa take fito da Haidar. Turaren Versage ya feshe jikinsa dashi ya saka bakaken covers a kafarsa, woow masha Allah.

"Sanda ya shigo hall din amarya da ango basu jima da shigowa ba, dan haka kowa ya nutsu yanda program din ke ci gaba da tafiya, aiko idon kowa kan Haidar, musamman 'yan matan dake wajen cewa suke Ya Salam ga wani ha'dedden guy wanda ya amsa sunan sa, daga can Saif ya sakar masa murmushi ya tura masa text ya karaso wajen abokansu.. reply ya mayar masa zai zauna a wani wajen dan shi kam bazai shiga cikin 'kannensa ba.
"Lailo ta ta'ba su Jesmy da suke table daya tace guyz see handsome, tayi masu nuni da Haidar wanda ke zama can gefe. Jesmy tace ya salam ke anya mutum ne. Sady da sumy me zasuyi banda dariya. Hanifa kam ta'be baki tayi bata ce komai ba, "Haidar kuwa se raba ido yake ta ina zai hangota... can ya hangota lokacin an kira 'kawaye suyi rawa, tayi masifan kyau wanda har saida yasa fa'duwan gaba, ankon nasu ya kar'beta sosai, dukda bata fito da gashinta waje ba zaka gane turashi akayi na dole cikin head din, babban abinda ya 'daga wa Haidar hankali shine ko mayafin kirki bata rufa ba, take yaji zuciyansa ya shiga bugawa da sauri sauri sanda yaga wani aboki ya li'ke yana mata 'barin ku'di na manni, kai shifa gani yake kaman dukan mazan dake wajen idonsu na kan Hanifa ne. Baisannsanda ya mike ya isa wajen ba, haka ya kuysa ya ri'ko hannunta, su Jesmy se mamaki suke ganin killing guy din nan ya jawo hannun Hany sun fice daga filin rawa.
"Shema ta dan taba Saif tace kaga yaHaidar ko, wllhi na fada maka dama baka kirasa ba ni nasan bazai bar Hanifa a wajen bikin nn ba, Saif yace barin kirasa a waya, Hema tace Allah sa ya saurareka.
"Lailo tace saurayin Hany ne?
"Ke mijimta ne.... cewan Sady.
"A tare lailo da Jesmy suka zaro ido har suna ha'da baki wajen cewa mijinta? Yaushe tayi aure babu ko labari.
"Sumy tace auren ne yazo babu shiri shiasa bakuji ba.
"Nifa gani nayi kaman suna kama, cewan Jesmy.
"Yess brother din mu, ita kuma cousin dinta shiasa kuka ga kamanni, Sady ta fadi.
"Kai amma sun dace wllhi kaman na sure su na gudu, cewan Lailo.... dariya sukayi gaba daya, sumy tace toh lailo sarkin son kyawawa... lailo tace wllhi kedai ki bari kawai, ai da ba don ya samu mata kaman Hany ba da na 'dan kuma dai kun gane.... dukan wasa Sady ta kai mata tace Allah shiryeki Lailo, you wll never change. Haka suka ci gaba da hiransu.

"kana ganinsa kasan ransa a 'bace yake, tana masa magana ko kallonta beyi ba balle ya bata amsa, a haka har suka isa wajen da aka tanadar dan parking motoci, motarsa ya bude ya jefata ciki harda 'daura mata seat belt, a ranta tace toh yau kuma se ina oho, gaba daya ta gama razana, zagayowa yayi ya shige mazaunin driver ya shiga falfala gudu kaman zasu tashi sama, magana take masa "yaHaidar fa ba'a gama bikin ba dan Allah ina zamu...... Qiiiiiiiyyyyy 'karan burkin da yaja tsakiyan titi knn dabadon belt din daya daura mata ba da tuni ta buge kanta, Allah yaso babu mota a bayansu a razane ta 'dago ido tana dubansa bata ta'ba ganinsa cikin irin wann 'bacin rai ba. Yana huci kaman zaki ya soma fa'din
" Zakiyim shiru ko saina wurga ki waje, sabida bakida hankali, ke mahaukaciyar inane, wato ha'da kanki kike dasu Sadiya ko, dan rashin hankali ya maki yawa shine zaki fita babu ko myafin kirki, duk tarin mazan nan dake wajen haka suka ganki har kina wani fita kan stage kina rawa saboda gaki shasahsha, ai dole ma bazaki so tafiya ba kinga maza jarabarki ta motsa, wllhi kinji na rantse kika sa tsiya kin gama zuwa biki daga yau. Daga haka bai kuma cewa komai ba ya tada motan yaci gaba da falfala gudu. Jawayene kawai ke zirya a fuskan Hanifa.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/21, 2:01 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
38

" Haka Haidar ya rin'ka kwasan gudu dasu har suka iso gida, yana gama parking ya zagayo ya bude mazaunin Hanifa, fizgota yayi ya shiga janta ga takalmin ta me tudu ne amma ko a jikinsa sai janta yake, daidai hanyan da zai sadaka da sashen mamy suka ha'du da mamy ta fito sashen Abba, da mamaki mamy ke binsu da kallo.
"Hanifa tana ganin haka ta fizge hannunta da 'karfi ta 'buya bayan mamy.
"Meye haka ku kuma me ya dawo daku tun yanzu, ko har an gama event dinne? Mamy ta tambaya.
"Mamy dan Allah kice ya maidani wllhi yanzu aka soma ko rabin event din ma ba'ayi ba fah, yanzu is just 8:30pm, pls mamy.
"Haidar da ya gama 'kulewa ba tareda yace komai ba yasa kai zai wuce.
"Zo nan Haidar, muryan mamy ya dakatar dashi. "Juyowa yayi fuska babu walwala yace gani mamy.
"Wuce ka maida ta wajen bikin, idan kai baza je ba ita ai zata je maza maidata kafin ranka ya 'baci. " shiru yayi kaman bazaice komai ba sai kuma yace
"For goodness sake mamy ki kalli yanda tayi dressing as if ita ba matar aure ba, and harda wani mi'kewa taje tana rawa dan an kira 'kawaye suyi rawa, mamy gaba daya mazan wajen fa ita suke kallo.
"Mamy dai ta 'dago Haidar kishi yake dan haka tace "toh naji maza gyara mayafinki ya sau'ka 'kasa si ku koma.
"Mamy ni dai da kinyi waya wa 'Danmasani ma kawai sai yazo ya maidani.... cewan Hanifa.... wani mugun kallo Haidar ya watsa mata.
"Mamy tace Hidar wuce ka maidata wajen bikin nan kafin ranka ya 'baci.
" 'bata fuska yayi bai kuma cewa komai ba ya isa wajen motarsa.
"Hanifa da cikinta ya gama 'dura ruwa ta dubi mamy tace "mamy nidai kawai ma na ha'kura zan zauna a gida kawai. Hannunta mamy ta ri'ke ta kaita har jikin motan ta bude mata front seat tace maza shiga ku koma. " mamy wllhi na ha'kira zan zauna a gida ta fa'di tana satan kallonsa,
" Haidar kuwa banda hararta babu abinda yakeyi,
"Ki wuce ku tafi banson dogon zance, mamy ta fadi cikin dakewa.
" Kaman wata munafuka haka ta shige cikin motan sai satan kallonsa take, fukan nan nasa tamau babu alaman dariya. Mamy tana barin wajen ya fizgi motan ya fice daga gidan, "suna fita tace " yaHaidar dan Allah ka ajiye ni kaji wllhi na ha'kura zan zauna ma a gida.
"Ko tanka ta beyi ba sai driving yake abinsa. "Ganin ya 'dauki wata hanya aban yasata soma jero addu'o'i cikin zuciyanta, wayyo Allahn ta meyasa ma ta fa'di wa mamy tana son komawa oho, wata zuciya tace tsautsayi.
"Wayo ya rin'kayi da ita cikin garin kano, bai ce mata 'kala ba. Tana ji tana gani ya wuce hotel din da ake gudanar da dinner din, duk a zaton ta zasu koma ne amma taga un wuce. Tun tana tunanin ko ina zai kaita har ta gaji ta daina ta zubawa sarautar Allah ido.
" wayansa ne ta fara ringing, murmushi yayi ganin Latifa ce me kira ko babu komai yanzu zai 'kuntata wa Hanifa, parking yayi gefen titi yayi turning down cool music din daya kunna snn ya 'dauki wayan.
"Hello my Latifa.
"Hello my navy nayi fushi tafiya babu sallama and har kayi almost a week banko sani ba, ta fa'di cikin sigan shagwa'ba. Jin haka yasa Haidar saka wayan a speaker.
"Oh my baby am so sorry I didn't mean to hurt you, kawai tafiyan ne yazo mun in a hurry. Ya kike ya missing din kinayi kuwa.
"Wani murmushi mai sauti tayi wanda hakan yasa wani katutun ba'kin ciki ya tokari ma'koshin Hanifa,
"Kai my navy don't be silly, kaima kasan I must be missing you awfully ma kuwa.
"Oh really baby, same here. Ina missin soft skin dinki da sweet lips dinki.
"Ta sake yin wani murmushi tace " oh honey stop making it difficult, yaushe zaka dawo.
"Karki damu in a couple of days zan dawo,
"Oh honey i can't wait.
" me too dear, ina driving yanzu idan na isa gida i'll phone up you back Okay,
"Okay drive safe honey
" murmushi yayi yace "make sure you take care of your self okay, kisses to you. Kafin yayi hanging up. Da gefen idonsa ya kalli Hanifa data ha'da rai ta turo baki. Murmushi yayi ya kunna motan yaci gaba da driving.

"Daidai wani hotel yayi horn aka bu'de masa, da mamaki take kallonsa shiko ko ajikinsa, ya gama parking ya dubeta yace idan kinga dama kina iya fitowa, daga haka ya soma tafiya. Kallonsa kawai take totally speechless, what does he mean da zi kawota hotel da daren nan, tana cikin tunanin taji yana danna security lock, dole ta dito tabi bayansa, reception ya gama komai ya biya ku'din single room aka basa key tana gani ya wuce lift zai shige ya barta, aiko kafin ya rufe tayi saurin shigewa dan kuwa ya barta a nan bata san yaya zatayi ba, ko kallo bata ishesa ba, banda hararansa babu abunda takeyi, suna isa floor din taga ya nufi wni room, ta'be baki tayi tace " yaHaidar me mukeyi a nan, gani nayi de budurwan taka ba zuwa tayi ba balle kazo kama maku daki.
"Sai snn Haidar ya kalleta full of surprised, kaman ba ita tayi maganar ba, lalle ma yarinyar nan shine ma take gaya masa magana haka kaman sa'anta, bai ce mata 'kala ba ya shige 'dakin, saima da'di da yaji tana kishin Latifa knn, toh ko meyasa yaji da'din hakan oho, shi kansa bai san wnn amsa ba, on the other hand yana jin da'din ya 'kuntata mata.
"Ta gama 'kun'kuninta snn ta shiga, tsayuwa tayi gamida ha'de hannuwanta tana kallonsa, gani tayi ya cire jampan jikinsa yana 'ko'karin cire agogo tace yaHaidar nifa gida nake son tafiya, su mamy will be worried.
"Ya gama cire agogon ya zauna gefen bed, yana kallonta kafin yace, " don't provoke me am warning you, inace saboda kin rainani shine har zakice wa mamy ke wajen biki kike son komawa ko, toh barin fa'da maki tunda abun naki ya zama haka kinngama uwa bikin daga yau, kinga nan a ciki zaki zauna har a gama bikin, snn daga nan ko gidan Abba bazaki je ba Lagos zamu wuce direct. Tunda ke kin zama abimda kika zama, har wani gardin banza ke maki li'ki a wajen biki ke kuma kina jin da'di kina rawa, sa'ansa 'daya banson ruining bikin mutanen da I do care about them ne, but da sai na masa azaba a daren nan..... " Da mamaki take kallonsa kafin ta turo baki tace " toh wai yaHaidar meyasa kake jin haushi idan wani ya gwad damuwarsa a kaina, tunda ba sona kake ba ai sai ka ba..... bata gama rufe baki ba taji ya buge bakin, ta ri'ke bakin tana dubansa.
" ni sa'anki zaki min magana haka, ko don kinga ina 'kyaleki ko, a gabana kike ce mun wasu na sonki , Idan ma kina tunanin na fara sonki ne, you better stop deceiving your self, dan ni Haidar I wll nevr ever love you, kawai dai banson ki kwaso mana zunubi ne that's why.
" tsugunawa tayi a wajen ta shiga rusa masa kuka,.... " kinsan Allah idan baki mun shiru ba zan maidaki mota ki kwana a ciki, idan kuma kin ganin wasa nake ki gwada ki gani... daga haka ya shige bathroom ya barta nan tsugune tana matsan hawaye.

👸🏻Queen Samy😍💄💋.....
[5/21, 2:01 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
39

"Har ya fito daga bathroom din tana nan zaune a wajen tana sa'kesa'ke a zuciyanta, kallo 'daya ya mata ya watsar, kwanciya yayi bisa gado dan is already late.
" ta 'dago ido tana kallonsa taja tsaki a hankali, mi'kewa tayi ta zauna can bisa wata kujera me zaman mutun daya, ga kayan jikinta duk ya dameta tama rasa ta ina zata soma kwanciya da wnn kayan.
"Haidar na kallonta sanda ta cire gwaggwaron kanta tayi jifa dashi, gashin kanta ya bazu zuwa kafa'dunta, ta'be baki yayi yace a ransa "zan koya maki hankali ne 'karamar maras kunya.
"Zama tayi a 'kasa ta kifa kanta jikin kujeran ta shiga rera kuka maras sauti, tafi minti goma tana abu 'daya.... can ya mi'ke yana kallonta yace " kukan uban me kike, bakiji abunda na fa'da miki ba ko, kin samu na taimaka maki na barki ki kwana cikin 'dakin shine kike mun kukan munafunci ko, toh kici gaba idan kinfi son kwanan motan.
"Ni toh fah wnn kayan sun matseni bazan iya barci dasu ba, dan Allah yaHaidar ka maidani gida na yarda bazan sake zuwa ko wani event ba.
"Murmushi yayi yace " yarinya kin makara, a ina kika ta'ba jin soja yayi magana ya sake, straight forward mutane ne, they always stand by their words. Na gama magana a nan zaki kwana yau idan kinga dama kiyi barci idan kinga dama kiyi kwana zaune ya rage naki. Kuma idan kika cika mun kunne da 'kanan kuka kiji a jikinki kinga daga nan kyayi kukan da dalili, useless kawai.
"Share 'kwallan tayi ta narka masa harara sanda ya kwanta ya rufa bargo. Tana nan a dur'kushe a wajen har bacci ya 'dauke ta.... can ya farka ya ganta a haka, gajeren tsaki yayi ya mi'ke ya fice.

"Bayan motansa yaje ya bude ya 'dauko T shirt na kakin soji sabo fil da shi snn ya dawo dakin, 'dagota yayi ya dawo da ita kan gado ya shiga 'ko'karin canza mata kayan, aiko nan ta bu'de ido, da sauri ta mi'ke tana kare 'kirjinta da hannunta.
"Hissing yayi yace " meye kike karewa a nan, me kike da shi, ki bar wahalar da kanki yarinya am not interested. Ya jefa mata rigar yace gashi idan kinga dama kisa ba don halinki ba. Daga haka ya koma yayi kwanciyarsa.
"Mi'kewa tayi tace a ranta " whatever kaikaji wajen, ni nace maka ka saka min wani kaya. 'Daukan rigar tayi ta shiga juyawa ta ta'be baki ta mi'ke ta nufi bathroom ta canza.
"Da san'da ta fito wai kar yaji motsinta ya kalleta, aiko duk bata sani ba idonsa kyam a kanta, rigar yayi mata kyau sosai, ya sau'ko mata har cinyanta snn ya 'dan kamata ta 'kasa kasancewar t shirt din kaman body hook na maza yake. Kalan kakin sosai ya mata kyau, ta ha'de gashinta tsakiyan kanta. Yanda take san'dan yaso basa dariya. Kwanciya tayi bisa rug ta ta'kure saida ya bari tayi nisa da bacci snn ya dauko ta ya azata bisa gadon ya eufa masu bargo. Rungumeta yayi sosai cikin 'kirjinsa, a haka suka samu bacci mai da'din gaske....

" 'karfe 10:13 am su Sady Sumy Lailo da Jesmy ne suka shigo gidan sun fito daga gidan amarya Shema dan a can suka kwana dashike yau ne wunin biki, sashen mamy suka nufa suka gaisheta, nan suka shiga tambayan Hanifa.
"Mamy tace ku dubata can sashen Inna mana, Sady tace bata can fa mamy, kila tana sashen yaHaidar pls ki dan kirasa a waya mamy, zamu koma gidan Shema ne an barta ita ka'dai kuma 11:00am za a fara bu'dan kai 'din.
"Anty Hiba ne ta shigo tana fa'din barin kira Haidar din.... ringing biyu ya 'daga lokacin ya tusa Hanifa a gaba sai taci breakfast.
"my Anty good morning.
"Morning 'dan gida na, ina kuka shiga ne kam su Sadiya nata jiran Hanifa su tafi bu'dan kai, kuma kaima you suppose to show up a bud'an kai 'din.
"Mugun kallo ya watsa wa Hanifa kafin yace "Anty nifa banson event me maza su tafi kawai ita bazata je ba.
"Haba Haidar kan me zaka hanata, pls ka kyaleta ta fito ta shirya.
"Shiru yayi kaman bazaice komai ba sai kuma yace "Ok fine shiknn Anty.
"Yawwa 'dan gidana Anty Hiba tace.

"Yana gama wayan ya watsa ma Hanifa mugun kallo ya mi'ke ya zari carkey yace tashi mu tafi, da sauri ta mi'ke harda 'dan murmushinta suka fice.

"Suna isowa gida ya ska lock ma motan ya kalleta yace, kina jina wllhi kika kuskura na sake ganin ki cikin maza saikinga abimda zan miki, kuma saura kar ki rufe jikinki kiga yanda zanyi dake. Ya bu'de lock din, har tasa kai ta fita yace zo nan, dawowa tayinta tsaya
"Kije ki shirya ki fito, kanta tayi nodding kananta wuce, side dinsa shima ya wuce dan shiryawa.



1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

2 years ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment