Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiran sallan la'asar, Latifa tace ai nayi duka tun asuba....
"Zaro ido Hanifa tayi da mugun mamaki tace, sallolin ne kika yisu tun asuba, Larifa tace eh haka nake yi kar commitments su mun yawa nazo ban samu nayi ba.
"Hanifa ta girgiza kai tace " babu abunda yake gaba da sallah, duk tarin commitments din da suke gaban mutum dole ne wajibi ne farillah ne na asali ba wanda wani zai iya 'dauke wa wani ba, Sallah itace ginshi'kin aikin mutum, Sallah itace za'a fara tambayan mutum akanta da zaran ya mutu, idan tayi kyau tofah dukkan ayyuka sunyi kyau idan batayi kyau ba tofah sauran ayyuka sun rushe, sallah dolene ko me kike yi da zaran lokacinta yayi ki daina kiyi sallah, babu aikin da ubangijinmu yake so kaman yin sallah akan lokacinta fa'din manzon mu S.A.W.
"Latifa tayi shiru tana kallon Hanifa yanda take kwararo mata bayani, snn tace toh knn sallolin da nayi kafin lokutansu su shiga basuyi ba knn. Hanifa ta gyada mata kai tace 'kwarai kuwa ba'ayin sallah alhalin lokacinta bai shiga ba, 'karamin yaro wanda shari'a bata hau kansa ba, mai bacci mace me jinin bi'ki ko al'ada da mahaukaci sune sallah ta sauka akansu, snn shi me bacci da zaran ya tashi koda lokacin sallahn ta fita to zai rama wnn sallahn kafin yayi wacce lokacinta ya shiga, misali mutum na bacci lokacin azahar ya wucesa bai farka ba sai lokacin da ake sallan la'asar, toh ba la'asar zaiyi ba azahar zai fara yi kafin yayi la'asar din.
"Latifa ta jinjina kai tace na fahimta, yanzu barin tashi na biya sallahn azahar snn nayi la'sar, kuma insha Allah bazan sake yin haka ba. Na gode sisy na Allah ya saka maki da alkhair. Murmushi Hanifa tayi tace ai babu komai Anty Latifa yima wani ai yima kaine. Shgewa latifa tayi tayi sallolinta ta fito ta samu Hanifa tace sisy idan bazaki damu ba muje kasuwa mu sayo littafan addini ki rin'ka koya mun don na gyara ibada na.
"Hanifa ta zaro ido waje tace "kuji Anty latifa dai kin 'dauka ni 'din malama ce, Latifa tace 'kwarai kuwa saidai bazaki koya mun ba, ki taimaka mun pls kinga ni'din marainiya ce babu uwa na tashi snn mahaifina bai bani lilmin addini ba sai na boko, tun a primary da ake mana IRK na tsnci wasu abubuwa snn kinga yanayin environment din dana tashi pls ki taimaka mun kema Allah zai taimake ki.
"Sosai Hanifa taji tausayin Latifa sai yanzu ta gane ashe harda rashin sanin addini ne yasa Latifa shiga wani yanayi na rayuwa, amma ko babu komai tanada good heart snn insha Allah zata taimaka mata da iya 'dan abunda ta sani..... "kinyi shiru sisy "are we good to go, pls don't say no. Murmushi Hanifa tayi tace na yarda zan koya maki dukda nima 'daliba ce, yanzu ki kira yaHaidar kice masa zamu fita.
"Rungumeta Latifa tayi tace na gode sisy barin kirasa, ta kira numbern Haidar yafi abunda yafi amma baya shiga, ta dubi Hanifa tace 'kila suna wajen da babu network. Hanifa tace is possible yanzu dai muje kafin dare yayi idan yaso koda mun dawo sai ki masa waya ki fada masa. Haka suka fice Latifa taja su a motanta kirar 4matic E350, gwanin sha'awa suna tafe suna hira, Hanifa tayita mata hiran su mamy dasu Inna... a haka suka isa kasuwan suka sayo litattafai irinsu Akhadar, tauhidi hadisi da sauransu. Har karatun 'kur'ani Hanifa saida ta koyawa Latifa, kan sati ya zagayo Latifa ta soma picking, kama daga wankan tsarki hada baki alola da sallah duk saida Hanifa ta nuna wa Latifa yanda ake yinsu.
"Sai yanzu ne wani wasan mahaifinta yake da'da tasiri a ranta, hakika ya cuci rayuwarta Allah ne kawai zai mata sakayya. Ya kirata yafi sau nawa bata dagawa wani mugun tsanarsa take ji, batajin zata iya ci gaba da rayuwa dashi
"Yau suna zaune bayan sun gama karatu suka kunna kallo, Latifa tace inga fa cikin satin nan su Aliyu zasu dawo.Saida gaban Hanifa ya fa'di wanda ta rasa dalilin hakan, tayi murmushi on the contrary taji da'din zancen. Tana son ganinsa.... aiko suna cikin zancen wayan Latifa yayi 'kara... ta 'dago da murmushi tana duban Hanifa tace kinga 'dan halak muna zancensa ya kira. Nan Latifa ta 'daga suka gaisa ya shida mata gobe zasu iso lagos insha Allah, Hanifa kam wani 'katutun ba'kin cikine ya tokare mata ma'koshi, ta rasa gane kishi ne ko me.
"Ta mi'ke kawai zata wuce daki, sai jiyo muryan latifa tayi tana fadin gata nan barin bata, alamun YaHaidar ya tambayeta knn, da sauri tace "no pls ki gaishesa I want to use the bathroom, Latifa ta gyada mata kai snn tace da Haidar ta tashi bata kusa saidai ka kira later, jikim Haidar ya basa haushi Hanifa taji dan yasan halinta sosai by now.

"Washe gari tun safe Latifa ta tashi ta shiga gyaran gidan, koda Hanifa tace zata tayata 'kin yarda tayi, wai bazata saka malamanta aiki ba lol, Hanifa ma kin ha'kura tayi sai tayi, haka dai suka raba aikin, gwanin sha'awa suke gudanar da ayyukansu.
"Dakin Haidar Latifa ta shiga dan gyarawa, ta share ko ina ta gyara, har zata fita taga wani dan box a gefen bedside, ya mata kyau sosai jikin box din yasha zanen hearts da flower, a ranta tace 'kila Aliyu zai proposing mata ne at last, 'kilama ring ne a ciki, haka kawai taji zuciyanta na son ganin meke ciki, ta shiga budewa kuwa, gabanta ne yayi mugun fa'duwa ganin hoton Hanifa a ciki, ga red flower an daure shi da wata zoben diamond, tana gama gani jiki a sanyaye tana mamakin wani irin so Aliyu keyi ma 'kanwarsa haka, soyayyan yafi kama dana ma'aurata. Tana cikin tunanin wata 'yar takarda ta fado, a jiki an rubuta.
_to my dearest wife Haneefah, I love you with all my heart and soul, bansan ina sonki ba saida na soma zaman tsakani da Allah da ke na cire son zuciya, I hope zaki kar'be ni muyi zaman mata da miji mu cika wa iyayen mu burinsu, ni Aliyu Haidar na amince ni *Mijin Haneefah* ne...... this is from the burden of my heart. Captain Aliyu Abubakar........._ jiriri ne ya soma diban Latifa tana shin abunda take gani gaskiya ne. Shin dam Aliyu *Mijin Haneefah* ne ba wanta ba......

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
46

"Mutuwan tsaye Latifa tayi tana bin takardan da kallo, she couldn't believe what she's seeing. Ta jima tana juya takardan tana kuma karantawa... muryan Hanifa da ta jiyo tana ranga'da mata kira yasata saurin saita kanta, ta mayar da takardan cikin box din ta maidashi yanda ta gani snn ta fito daga 'daki.
"Kallo Hanifa ta bita dashi ganin yanayinta ya sauya tayi wata sukuku da ita. Da sauri Hanifa ta matso ta ri'ke hanunta tace" what's wrong Anty Latifa, wani abune ya faru. Kallon Hanifa kawai take wani mugun tausayinta ya dira mata. Murmushi tayi tace" ba komai sisy, kinsan me nake so dake, Hanifa ta girgiza kai alaman a'a. Latifa tace fine, dauko mayafi mu fita. Galala Hanifa take kallonta kafin tace" where to, Latifa tace kedai dauko muje pls it's urgent.
"Kallonta Hanifa tayi fukanta dauke da damuwa tace, kinyi waya da yaHaidar ne? Wani abu ya samesa ne? Pls ki fada mun meke faruwa.
"Hannunta Latifa ta ri'ko ta saka mata mayafi tajata suka fice, Hanifa dai kallonta kawai take amma ko ka'dan hankalinta baya jikinta gani take kaman wani abin ne ya sami yaHaidar.
"Basu zarce ko ina ba sai saloon, Latifa tasa aka gyarawa Hanifa gashinta, akayi coiling dinsa nan da nan tayi kyau, makeup artist dake shagon ta mata makeup dukda dan light ne amma ba 'karamin kyau tayi ba kai kace gasan sarauniyan kyau zatayi. Kallo kawai Latifa tabita dashi a fili ta furta " tsarki ya 'kara tabbata ga mahallicin wnn kyakykyawan hallita.
"Kallonta Hanifa take galala kafin tace" what's all this for? Murmushi kawai Latifa tayi bayan an gama mata kwalliyan ta biya charges din suka fito, kai tsaye wani boutique suka wuce, kaya masu kyau da tsada ta za'ba mata ta manna shi jikin Hanifa tunkan tasa taga yayi fitting dinta. Babban yatsanta ta 'daga mata alaman jinjina tace " Superb 👍🏼. Hanifa dai gaba daya she's lost ta rasa gane dalilin Latifa nayin wnn hidima.
"Basu suka dawo gida ba sai wajajen 2:15pm, Latifa tayi girki meji da da'di ta jere komai kan dinning, babu yanda Hanifa batayi ba ta tayata aikin se mata tayi ta barshi ita zata yi kar ta 'bata kwalliyanta. Dole tasta ta saka rigan da suka sayo, wata gown ne red me ba'ka'ken duwatsu snn ya kamata sosai, daga 'kasa kuma yasha tsagu har zuwa cinya, ta zubo mata da gashinta dayasha gyara, "Ya Salam" abinda Latifa ta iya fa'di knn, tace sisy " you look gorgeous, masha Allah.
"Wai ni dan Allah wnn kwalliyan duk meyene, nifa ban gane ba I need an explanation, Hanifa ta fa'di baki a ture.
"Zama Latifa tayi bisa stool kafin tace "wnn kwalliya is for husband.
"A zabure Hanifa ta 'dago ido tana dubanta snn tace" sorry I don't get you, me kike nufi.
"Yes abinda nake nufi na tarban mijinki ne Aliyu, karki da mamu sisy na riga nasan cewa Aliyu mijinki ne, you don't have deny it anymore.
"Girgiza kai Hanifa ta shiga yi tana fa'din " no no Anty Latifa, you've got this wrong, yaHaidar yaya nane ba mijina ba, beside ke sahida ce ai kina gani..... dariya sosai Latifa ta shiga yi ganin yanda Hanifa duk ta daburce tana musa Haidar ba mijinta bane,.... Hanifa ta 'dan 'bata fuska tace "this is not funny, it's not a joke,... da kyar Latifa ta saita kanta kafin tace " you guys are funny wllhi, ban ta'ba jin irin soyayyanku ba not even in a film, but anyway kunzo da sabon salo kuma kun burge ni, dukanku kuna sonjunan ku but you don't even realize, koda yake Haidar ya gane yana sonki, and believe me he's ever ready to show his love for you, ta taso ta ri'ke hannun Hanifa tace " Hanifa, Haidar loves you with all of his heart, I was stupid back then da na yarda karatu kika zo yi nan a matsayin 'kanwarsa, inspired of abunuwan da sukata faruwa a tsakaninku, ke kina kishinsa snn shima yana kishinki, now is the sisy, lokaci yayi da zaki ri'ke mijinki hannu bibbiyu.
"Wafce hannunta Hanifa tayi daga ri'kon da Latifa ta mata tana girgiza kai take fa'din" no no that can't be, you miss understood that, ni da yaHaidar bama son juna, hasalima mun wasa juna,on the contrary he tried to treat me nicely all of a sudden, but nasan hakan ba wai yana nufin sona ya fara ba, he'll never love me yasha fa'da mun haka, ke shaida ce ke yake so kece budurwansa....... "da sauri Latifa ta toshe bakin Hanifa da hanunta ta soma fa'din " pls don't say that, wllhi Haidar baya sona in fact bai ta'ba sona ba, ni ce dai me sonsa, bazai ta'ba sona ba, and ina 'kara ro'konki ki yafe mun akan abubuwannda suka faru tsakani na da Haidar a baya.
you are the love of his life Hanifa, you are his destiny his soul mate, you guyz do love each other, pls stop suffering, and accept the fact that you love each other.
"'Kwalla ne ya ciko ido Hanifa, Latifa ta ri'ko hannayenta tace " oh no pls, don't let those tears spoil the makeup, promise me zaki kula da Haidar yau, pls pls I beg of you say yes kinji sisy.
Hanifa ta 'dago tana duban Latifa wani tausayinta ya kamata ta sani tana tsananin son Haidar, murmushi tayi tace "just because you insist, rungumeta Latifa tayi tana 'ko'karin maida 'kwallanta tace " thank you sisy, zan tafi gida yanzu idan Aliyu ya iso ki gaidasa pls and maybe na shigo gobe.
"Marairaicewa Hanifa tayi tace " no pls don't leave Anty Latifa, I beg of you pls.
"Murmushi Latifa tayi tace " kinga tunda nazo ban dubo Dad dina ba, so I've to go and check on him. I promise you zanzo gobe.. ta juya ta fice gamida jawo luggage dinta,.... kallonta Hanifa take yi har ta isa kofan parlorn, ta juyo tace mata "na gode Hanifa, na gode da ceton rayuwata da kikayi daga duhu zuwa haske, Allah saka maki da mafificin alkhair. Hawaye ya zubo ma Hanifa, ta 'karsso da gudu ta rungumeta.... da kyar suka rabu da juna tana mata waving har ta shige motan ta fice daga gate din.

"Sosai Hanifa tayi kewan Latifa, tana sonta for the sake of Allah. Ta zauna nan tana tunanin rayuwa, kwata kwata bati 'karan bell da ake dannawa ba, can taji anata faman knocking, ta taso gamida saita kanta ta nifi 'kofa.......
"Yana sanue cikin kakinsa hannunsa daya na cikin aljihu daya kuma na rike da luggage dinsa..... bata san sanda murmushi ya subce mata ba.... kallonta yake babu ko 'kyafta ido bai ta'ba zaton kyaunta ya kai har haka ba snn har wani girma ta 'kara masa,..... bai iya yace mata komai ba sai jifa da yayi da luggage dinsa ya rungumota ya shiga kissing dinta.... yana sunbatu yana fadin I miss you, I missd you so very much Angel. Ya jima yana kissin dinta kadin ya saketa, Hanifa kam gaba daya sanyi jikinta yayi, ta rasa gane meke faruwa da ita, batasan me take ji gameda yaHaidar ba.
"Kallonta yake babu ko kyafta ido, tayi kyua sosai yana ji a ransa bazai iya rayuwa babu iya ba. Hannayenta ya ri'ke suka zauna bisa kujera yace " you looks gorgeous spectacular, tell me meye Latifa take baki kikayi wnn kyau haka. Sai snn Hanifa tayi 'dan dariya tace " you see she's very kind and adorable person, she treats me like her own sister. Naji da'dinnzama da ita sosai.
"Murmushi yayi yana 'daga gira sama kana yace "I see, so tell me did you missd me? Ya 'karashe magann yana wani kashe murya
"No not all, ni banso ka dawo yanzu ba ma coz banso Anty latifa ta tafi ba.
"'Bata fuska yayi yace " fine idan ke bakiyi missing din ba ni nayi missing dinki so awfully. Dariya tayi tace just kidding, nayi missing dinka yaHaidar yanzu muje kaci abinci.
"Murmushi yayi ya manna mata peck a kumatu yace " let me take a shower first. Kallonsa tayi har ya shige 'daki snn ta suke ajiyan zuciya tace "I don't but imada bad feelings gameda canzawanka yaHaidar. Amma dai muje zuwa..... mi'kewa tayi ta shiga hada abinci a dinning.

"Mintuna ka'dan ya diba ya gama shiryawa duk ya 'kagu yaga beautiful face dinta, ya fito cikin 'kann kaya sun kar'besa sosai, kallo ta bisa dashi a ranta tace "he's always handsome.
"Zama yayi tayi serving dinsa koda tazo tashi hanata yayi wai saidai ta zauna ya ringa kallonta, haka Haidar ya ringa janta da hira yana son su saba sosai.
"Bayan ya gama cinnabinci ne tace ya kira Latifa ya fa'da mata ya iso, hakan kuwa akayi yayita kiran Latifa bata 'daga ba, Hanifa tace kila bata kusa but nasan idan taga missed calls dinka zata kira.
"YaHaidar, Hanifa ta kira sunansa, dagowa yayi yana kallonta kafin tace, there's something I want to ask you. Ajiye remote din hanunsa yayi yace "ehen go ahead, go ahead and ask.
"Dama so nake ka kaini gidansu Anty Latifa, their's something I need to discuss with her. Shiru yayi kafin yace,
"Kin gane sun tashi daga gidansu dana sani sun koma sabon gida dab da zamuyi tafiyan nan, but kar ki damu da zaran munyi waya da ita zan tambayeta sai na kaiki.
"Gyada kant tayi tace na gode, murmushi yayi ya rungumota gamida lumshe ido, abubuwa da yawa yake ji, ya dau alwashin yau da daddare zai fayyace mata zuciyansa.

"Daidai goshin magrib, Dad din Latifa da baisan da dawowan latifa ba, yayi shirin shiga 'dakinsa na tsafi, ya saka faran zanin sa ya doshi dakin, Latifa dake tsaye jikin staircase ta razana da abunda ta gani daga mahaifinta, snn ta 'kara samun wasu takardu da take kokarin damka su wa Haidar,
"A hankali tabi bayan dad dinta........

👸🏻Queen Samy😍💄💋.........
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
47

"A hankali take binsa sanin babu kowa a gidan yasa be damu ya rufe 'kofa ba, yana shiga yayi yanda ya saba, hango mutum kamar mahaifiyarta yasa jikinta ya soma kyarma, bakinta ya kasa furta komai sai 'bari take..... "A hankali ta ciro wayanta ta shiga dialing lamban Haidar...... Daidai nan ta ture flower vase ai kuwa nan yayi interrupting *Admiral. Tanim Razak*, a zabure ya juyo yana dubanta, gudu ta soma zata sauka kasa daidai nan Haidar ya 'dau wayan... cikin tsananin tashin Hankali take fadin " Alliyu pls I need your help, pls kazo gidanmu kafin ya kashen...... Lawo ne ya 'bullo a gabanta nan Latifa ta sake wata 'kara gamida jifa da wayan... "Haidar ya cigaba da fa'din hello, hello Latifa can you hear me.... ina daga nan bai kuma jin komai ba... Sosai hankalin Haidar ya tashi kardai ya jefa rayuwan Latifa a halaka, dan yasan muddun Admiral. Tanim yasan Latifa is spying on him bazai kyaleta ba, " dafe kansa yayi yace "oh no ya Salam. Idan wani abu ya sameta nine naja mata, I need to do something..... balcony ya tafi ya shiga neman layin Aisar, bugu biyu Aisar ya 'daga.... "Hello man what's up... Aisar ya fa'di... cikin tashin hankali "Haidar yake fadin "Aisar kasan sabon gidan da Admiral ya koma pls idan ka sani just texts me the adress. Aisar yayi murmushi yace don't tell me baka daina binciken wahalan da kake akansa bane. Ciki kosawa Haidar yace pls ka fada mun before it's late.
"nima ban sani dan ka san ba kowa ya sani ba, tunda all of recent ya koma, amma nasan suna exchanging map din gidajensu with my dad.
"Oh pls Aisar do something I beg you pls.
"Murmushi Aisar yayi yace zan kawo maka map din but only in one condition.
"Pls tell me what was that.
"Zaka bani chance just for once na fita date da 'kanwarka...bai gama rufe baki ba Haidar yace " what, are you stupid, do you really knw ehat you're saying.
"Ok fine ka ri'ke 'kanwarka na ri'ke map dina, and don't forget your life is in danger soldier coz you are messing with the Admiral your boss...... "shutt up Aisaaaar. Ya daka masa tsawa gamida kashe wayan... ya zauna dirshan a wajen ya dafe kansa. "Tunani ya shiga yi, yanzu idan ya bar Latifa haka ya mata adalci knn, idan ya barta bai ta'buka komai ba ya mata adalci knn, Latifa batayi deserving ya kyaleta haka kawai ba, she's doing all this for him, ta amince a tona asirin mahaifinta despite the fact he's her father.....
"Wani murmushi Aisar yayi yace this is the time Aisar, now or never. Yayi wata murmushi gamida mike kafafu...... yana a haka wayan Haidar ya sake shigowa, murmushi Aisar yayi yace "nasan zaka kuma kira snn ya 'dauka....

"So kana son map din knn.
"Promise me you won't do anything bad, promise me fita kawai zakuyi bazaka mata komai ba.
"Murmushin cin nasara Aisar yayi yace " you have my word navy, I promise I won't do anything stupid. Na maka al'kawari fita kawai zamuyi bazan cutar da ita ba Haidar.... " ya isa am waiting for the map, Haidar ya fadi cikin rawan murya.
"Ok am coming right the way....

"Yafi minti biyar a wajen ba tare da ya moysa koda yatsansa ba..... "Hanifa dataji shiru yayi yawa ta shiga dubasa a gidan, a balcony ta gansa yana zaune a 'kasa yayi tagumi.... 'karasawa tayi ta dafa sa "yaHaidar meke faruwa.... dago kai yayi yana kallonta ya rungumeta... a hankali yace " hug me tied Hanifa, pls don't let me go.... da mamaki take fadin lafia yaHaidar. 'Dago kansa yayi hadi da 'ka'karo murmushin karfin hali ya riko hannunta suka shigo parlor, kai tsaye dakinta suka wuce, ita dai kallonsa take jiki a sanyaye. Wardrobe dinta ya bude ya ciro mata wata ash din doguwar riga yace ta saka, babu musu ta karba ta saka.
"Are we going out, ta tambaya tana dubansa, murmushi ya mata ya gyada kansa kawai. Da murnan ta ta saka harda dan dad gyara duskanta.

"Yana zaune yana jiranta a parlor, yaji karan bell alamun Aisar ya iso, mikewa yayi daidai lokacin da Hanifa ta fito, ya bita da kallo, ya karasa ya rungumeta ya shiga kissing dinta.... a hankali ya soma fadin "I love you, I love you Hanifa don't forget that. Saida ya shanye jan bakinta gaba 'daya kafin ya daina kissin dinta. Duk jikinta ya mace, bata ta'ba jin yaHaidar ya furta mata kalman so ba sai yau. Hannunta yaja har zuwa waje yanda Aisar yayi parking motar sa.... Aisar na ganinsu ya fito yana murmushi yayi kyau cikin yanayin shigarsa. Haidar ya hadiye wani katututun bakin ciki .
"Kallonsa Hanifa tayi kafin tace, yaHaidar wai meke faruwa ne ina zamuje. Mota ya bude ya sakata ciki, Aisar ya mika masa map din..... kallon su take da mugun mamaki jiki a mace me suke nufi, sayarda ita zai yi kome, Aisar ne ya zauna a mazaunin driver du a tuaninta Haidsr zai shiga ne amma sai gani tayi Aisar ya fizhe mota sun bar haraban waje.
"Da mugun mamaki ta juyo tana kallon aisar kafin tace "malam ina zaka kaini, ka tsaya na fita, nace ka tsaya na fita.... ta shiga kokarin bude motan amma saiji tayi ya saka central lock, ..... tana kiciniyan bude motan da iya 'karfinta, ta tsinkayi muryan Aisar yana fa'din " relax baby, we are just going out to have some fun, don't you like it. Bansan saboda me yayanki yake ta'kuraki a gida ba, yanda kike gorgeous din nan kamata yayi kiyi living life dinki yanda kike......... abubuwan da ta iya ji knn daga bakin Aisar, tun daga nan 'kwa'kwalwarta ta shiga juye, innalillahi wa inna lilaihirra'aji'un abunda bakinta ya iya furtawa knn, zuciyanta da 'kwa'kwalwarta suka shiga wasu tunani...... "shin dama nufin yaHaidae knn akanta, shin dama abunda yake shirya mata knn, shin dama tsanar da ya mata har ya kai haka, da aurensa akanta ya mi'kata ga wani na miji, wnn wani irin tijara ne da jahilci, wata zuciya tace ba jahilci bane tsaban ya tsaneki ne ya miki haka....... har suka isa guest house din dad

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

2 years ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment