Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

oh my Allah give me some strength, ta fa'di gamida sauke numfashi.
"Saif yace Hajiya first aid yana ina, " me zaka yi dashi. "Haidar ne ba lafiya yanada fever. Hajiya tace "kuma" aida asibiti kuka tafi Saifu, Saif yace ya'ki yarda Hajiya.
"Ok ka duba 'dakin Jamila yana ciki idan jikin nasa baiyi sauki ba sai mu tafi asibiti, toh Hajiya Saif ya fadi gamida shigewa, Hajiya ta mike tana fadin barin hada masa ruwan shayi.

"Kwance Saif ya samu Haidar ya du'kun'kune cikin bargo, da 'kyar ya mi'ke yasha maganin nan bacci ya 'daukesa, koda Hajiya ta samu na bacci bata 'daga sa ba. Saif ya isa sashen Hajiya suna tattauna lamarin. Har kusan magrib Haidar be farka ba, Saif ya dawo daga sallah ya le'ka sa, ya samu ya tashi yana sallah, Hajiya da kanta ta shigo tasa Haidar ya saka wani abu a cikinsa,
"Saif ya kallesa bayan Hajiya ta fita yace I'll drive you home, girgiza kai Haidar yayi yace " no am staying here, I can't go there Saif, no one is willing to listen to me. "Saif ya fuzar da iska yace shikenn, idan Allah ya kaimu gobe sai muje mu sami Abba dga nan musake komawa can Lag din. 'Daga kai kawai Haidar yayi ya koma ya kwanta, kana ganinsa kasan 'karfin hali kawai yake amma baya jin da'di.

"Koda Saif ya samu Hajiya da batun taji da'din hakan, tace he needs your company, yanzu ka dauko Shema'u mu kwana da ita, Saif ya mi'ke yana fadin toh Hajiua sai na dawo.

"A parlor ya samu Shema tana kallo, yana shigowa ta 'dale wuyansa tana faman shagwa'ban ya barta ita ka'dai, zama yayi ya daurata bisa cinya gamida dafe kansa. Shema ta kallesa cike da kulawa, " Ya dai Sweet, is all well? Sauke ajiyan zuciya yayi kafin ya gyada mata kai kawai yana shafa gashinta, toh why the long face ta fadi fuskanta dauke da damuwa. Murmushi Saif yayi kafin yaja hancinta yace " tashi ki shirya mu tafi gidan Hajiya. Shema ta kafesa da ido kadin tace " wai meke faruwa ne, pls ka fada mun you making me nervous.
"Rungumeta yayi tsam cikin jikinsa kafin yace " I love you Shema, I love you so much, promise me you won't leave me, we'll always be together for the rest of our life. "Jiki a sanyaye Shema ta matse sa cikin jikinta kafin tace " You know I love you yaSaif bazan ta'ba barinka ba, we'll build our family together. Kiss ya manna mata yace tashi ki shirya. Ta mike ta shirya da kansa ya dauka mata kaya kala biyu. Ita dai sai kallonsa take.
"Zamu kwana gidan Hajiya ne, ta tambaya.
"Hannayenta Saif ya ri'ke ya zaunar da ita bisa gado kadin yace, you need to knw this, ko na 'boye maki zaki sani eventually. Nan Saif ya fada mata Haidar da Hanifa sun samu miss understanding and ya nemi Hanifa ya rasa, she disappeared. Sosai Shema take kuka, tana fadin "where she could have been possibly gone, I don't wanna loose her,.... rungumeta Saif yayi ya shiga bata baki yana fadin za'a sametq ta kwantar da hankalinta. Da kyar ya samu yayi calming Shema snn suka nufi gidan Hajiya. Haka Hajiya tayita rarrashin Shema tana bata baki.
"Saif ya tafi wajen abokinsa.

"Da safe koda Hajiya da Shema suka le'ka Haidar sun tarar na bacci, sosai Shema ta razana da ganin yanda yayan nata ya koma, ta tausaya masa sosai bata ta'ba ganin yayi irin wnn rama ba.

"Misalin karfe 1:15 pm, momma na rungume da Amal dake faman kuka tana daga wa daddynta da Hanifa hannu a babban filin jirgin saman Murtala Muhammed international airport. Saida suka bace masu kafin suka juya suka shige mota, har suka shiga jirgi Hanifa na matsan hawaye, Barrister ya mi'ko mata hanki, ta dagi tana dubansa kafin ta sakar masa murmushi ta kar'ba, daidai lokacin aka soma announcing jirgi zata tashi, cikin mintoci jirginsu ta daga zuwa jhar kano.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
54

"Bayan la'asar Haidar ya 'dan samu strength ya tashi, waya yayi wa Saif yaji ina yake, Saif yace ya fita ba jimawa zaiyi ba amma, Haidar yace ok shiknn ni zan 'karasa gida, Saif yace just wait bit longer ganin nan zuwa Haidar. Fajeren tsaki Haidar yadan yi yace " kana ina ne yanzu, nan Saif ya fada masa street din da yake, Ok zan sameka a wajen, fine sai ka iso.

"Gefen wani shagon aski me kyaun gaske Haidar yayi parking, ya jingina kansa jikin seat yana jiran Saif, kaman ance daga kanka, a daidai traffic ya hango wata bayan taxi kaman Hanifa, zabjra yayi ya kuma goge idonsa dan tabbatrwa, daidadi lokacin Saif ya iso yana fadin mu 'karasa soldier..... Nuna masa motan Haidar ya shiga yi yana fadin " Saif look at that car... Hanifa ce ciki, ka shigo mu bi bayansu za'a basu green light... Saif yace Ok barin shiga motata.... bude mota Haidar yayi ya jawo Saif ya danna sa ciki ya shiga falfala gudu, haka ya rin'ka rough driving dasu kar motar ta 'bace masu, ganin sun 'dau street din unguwarsu yasa Haidar sassauta gudun da yake.
"Taxi din tayi parking daidai gate din gidan Abba, Haidar ma parking yayi a gefe, Sameer ne ya fito daga gaban motan yana murmushi ya zagayo ya bude wa Hanifa, fitowa tayi fuskanta dauke da murmushi, aiko Haidar ya zabura zai nufe su, Saif yayi saurin ri'kosa.
"Taxi driver din ya fito ya bude trunk ya ciro luggage dinsu Sameer ya kar'ba, snn ya wuce, sai snn Hanifa ta lura da motar yaHaidar dake parke a gefe, nan ta kuma jin wani mugun tsanar sa na taso mata, murmushi ta sakar ma Sameer ta soma masa labari suna dariya suka nufi cikin gidan kaman wasu masoya,
"Kan su shige suka ji an finciko Sameer, ya dawo baya, wata naushi Haidar ya sakar masa a hanci saida yayi ha'bo, Ya cukume wuyan Sameer yana fadin munafukin Allah me ya hadaka da matata, " Saif ya shiga jan Haidar yana fa'din pls Haidar behave yor self meye haka kake yi.
"Cikin ki'dima Hanifa take kallon Sameer cike da damuwa, tayi saurin ciro hanki ta mi'ka masa, oh Allah you're bleeding ko asibiti zamu, it hurts ko, kayi ha'kuri mahaukaci ne ba me lafiya bane, mu 'karasa ciki kafin haukan nasa yayi tsamari..... Da mugun mamaki Haidar ke kallon Hanifa, gani yake kaman ba ita ke maganar ba,.... muryan Sameer ya dawo dashi daga duniyan tunanin da ya tafi.... " no no kar ki damu basai munje asibiti ba, amma ko ai bai kamata ake barin iri wadnn mahaukatan ba sai su illata mutane, kamata yayi a killacesa a asibiti cewan Sameer, Hanifa ta ta'be baki tace ai ya jima a asibitin mahaukata inaga ya gudo ne, mu 'karasa ciki pls..... suka nufi cikin gida tana faman masa sannu.

"Kaman gunki haka Haidar ya tsaya yake binsu da kallo har suka 'bace masa, Saif ya dafa sa yace mu 'karasa ciki... Haidar ya juyo da dubansa ga Saif snn yace " didn't you hear what they said, wato mahaukaci ma suka dauke ni, yes am going crazy about you Haneefah, Saif yace duk ba wnn ba yanzu mu 'karasa ciki, Haidar jiki a mace yace "Saif matata nake gani da wani har tana fifitasa akaina, Saif yace pls Haidar let's get going.

"Tarba me kyau Abba da Mamy suka ma Sameer, sai haba haba suke dashi harma da Inna wacce take ji kaman ta dau zani ta goya Sameer, Hanifa na ma'kale jikin mamy sai zuba mata shagwa'ba take, Mamy inasu Sumy ne ban gansu ba, mamy tace Sumy tana faman registration a nan BUK, Sady kuma jiya muka kaita ABU, amma anjima kadan Sumayya zata dawo.... daidai nan Saif da Haidar suka yi Sallama.
"Gaisuwan Saif kawai Abba da mamy suka amsa inna ma harda basar da Haidar kaman bata san ya shigo ba. Sameer ya mike yana fadin toh Abba ni zan wuce masauki, Abba yace aff ko abinci baka ci ba a'a haba dai, ka saki jikinka Barrister nan gidanku ne, a ina ne masau'kin naka.
"A'a dama hotel zan wuce Abba, Sameer ya fadi,
"Haba Barrister dan Allah ka dauke mu tamkar iyaye, a nan zaka sauka babu batun zuwa Hotel, cewan Abba. "Haidar sai satan kallon Hanifa yake, itama ta saci kallom nasa yanda taga yayi rama kaman me cuta.
"Abba ya dubi Saif yace "Saifullah ga key din guest room a can maza 'dauka ka raka sa, Saif ya mi'ke yana fadin toh Abba ya karasa ya dau key din Sameer ya mike yana godiya, su Abba suka ce " haba ai mune da godiya ka isa ka huta yanzu za'a kawo maka abinci.

"Mamy ta mi'ke tana fa'din barin ha'da masa abincin, Hanifa ta mike tana fadin I'll ho with you mamy. Abba yace zauna daughter zamuyi magana. Zama tayi tana fadin toh Abba, Abba ya dubi mamy yace jeki dawo Mariya magana zamuyi. Mamy tace toh I won't take long kafin ta wuce cikin sauri.
"Haidar da har lokacin yake durkushe yana satan kallon Haneefah, ya hango dan sauran bandage a goshinta take yaji gabansa ya fadi "Oh Allah me ya sameta. Inna ce tace meye kake wani satan kallonta hankalinka yanzu sai ya kwanta tunda ta dawo, shafa kansa yayi ya mi'ke yana shirin fita muryan Abba ya dakatar dasi, "ina zaka je, dawo ka zauna. Ba musu ya dawo ya zauna.

"Mamy ce ta shigo tana fadin daughter ko zakici abinci yanzu ne, no mamy sai nayi wanka. Mamy ta karaso gamida jawo Hanifa jikinta.

"Abba ne yayi gyaran murya ya soma fadin " Alhamdullah, dukkam godiya ya tabbata ga Allah wanda bayyanar mana da 'diyar mu cikin 'koshin lafia. Ya dago yana duban Haidar kafin yace " Aliyu ina so ka sanar damu me ya ha'daka da matarka har kayi sakaci da rayuwarta ka barta ta 'bace maka a garin da babu wani nata.
"Haidar ya hadiyi miyau, ya dago yana duban Hanifa, wani uwar harara ta sakar masa gamida kau da kanta gefe. Kirjinsa yaci gaba da lugude, yanzu me zai ce wasu Abba idan suka san asalin dalilin 'bacewar Hanifa yasan abun bazai kyau ba...... "Kai muke saurare Haidar, muryan Abba ya katse sa.... " Na'am na'am Abba, cewan Haidar a ki'dime... "I suppose kaji abunda nace Abba ya fadi fuska babu alamun wasa,
"Abba ga Hanifar nan ita ta fa'da da bakinta..... Abba ya juyo yana duban Hanifa kafin yace " daughter me ya hadaki da mijinki har kika yi sakaci da rayuwarki kika fice ba tare da saninsa ba, wanda ba don Allah yasa kin fada hannun na gari ba da bamu san yanda abun zainkasance ba.... "Hanifa baki a ture tace " Abba ai shi yasan me ya mun, shi ya fada..... " Abba ya kuma tambayan Haidar, gaba daya Haidar ya rasa me zaice... bama son sakarcin banza kar ku maida mutane kanan yara, Mamy ta fadi a hasale. Inna ta kalli wnn ta kalli wann, ikon Allah ni Mero naga duniya wajen yaran nan kowa ya'ki fa'di saidai yace wann ya fada, toh Habubakar kar ka kuma saurarensu, sha'kiyanci ke damunsu, ai sai ku tattars ku koma gidanku an gama sulhu..... wani ihu Hanifa ta sake ta rungume Mamy tana fadin mamy wllhi ni bana sonsa wllhi bazan koma ba, cikin kuka ta soma fadin wllhi zan fa'da abumda yayi mun.
"Banda innalillahi babu abunda Haidar ke nanatawa cikin zuciyansa shikenan ta faru ta 'kare zata fa'da.... muryan Hanifa ya katse masa tunaninsa sanda ya runtse ido yana saurarenta...
"Abba wllhi kullum giya yake sha ya kuma kawo 'yan matansa gidan, kullum yasha giyansa sai yayi mun dukan tsiya ga bauta da nake wa 'yan matansa... shine da azaba ya ishe ni na gudu..... kuka ya kuma kufce mata. Haidar kam hamdala yayi cikin ransa yafi masa sau'ki da baya fa'da asalin laifin ba.
"Abba ya dubi Haidar yace hakane Aliyu, abunda Hanifa ta fa'di gaskiya ne. Haidar cikin rawan murya yace "hakane Abba, gaskiya ta fadi amma wllhi nayi nadama bazan sake kwatan ta makamancin haka ba.... Mamy kam bata san sanda hawaye ke bin 'kuncinta ba, Mata Haidar mata da giya.... Inna banda rafka salati tana tafe hannu bata komai, " haba ai biri yayi kama da mutum, shiyasa idannka tafi kudun har baka son waiwayo mu ashe hole raywarka kake, toh bari kaji in gaya maka jikata ba jaka bace, dakasan baka sonta ai sai ka fadi kafin a aura maka ita, mugu kawai ka tafida 'yar marainiyar Allah tana maka bauta kana azabtar da ita, ta mi'ke tana gyara daurin zani ta isa gaban Haidar ta mika masa hannu tace bani takardan sakinta tunda ni na ha'da auren naku sai kaje ka auri karuwan naka.... Galala Haidar ke kallonta kafin yace " wallhi wallhi ina son matata bazan iya sakinta ba, aiko baka isa ba sai ka saketa dan bazata iya zama da kai ba, Allah sa ma bata 'kunso cikinka ba,..... Abba da mamy kam kasa cewa komai suka yi, Mamy banda hawaye babu abunda take... da kyar ta iya fadin " Haidar sakayyan da zaka mana kenn, irin tarbiyan da muka maka knn, dole ka saki Hanifa dan bazata ci gaba da zama da kai ba... Mamy pls kumun rai wllhi ina sonta bazan iya rauyuwa babu ita ba... Har lokacin kuka Hanifa take tana da'da jin tsanar Haidar a cikin ranta. Abba kam jiki a sanyaye ya mi'ke ya nufi saman sa. Inna ta mike tan fa'din inazakje Habubakar gwarama ka dawo kasaka 'danka ya sakar mun jikata, dan bazata kuma kwana da urensa a kanta ba. Abba kam baima san inna na magana ba har ya haye sama yana ganin bibbiyu. Ta 'karasa ta jawo hanun Hanifa tace wuce muje zai biyo ki da rasit dinki fuuu suka wuce.
"Sosai mamy ke kuka, Haidar ya 'karasa zai ri'ke 'kafarta mamy ta mike da sauri ta fice daga parlorn. Zama yayi dirshan a wajen yana sheshekan kuka.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
55

"Mi'kewa Haidar yayi yana fitowa sashen sa ya wuce ya dauko ba'kin glass ya saka a idonsa, daidai nan suka hadu da Saif ya fito sashen baki, wanu mugun kallo Haidar ya watsa wa Saif kafin yace kaikuma shine har zaka tare ka zauna wajen wanacn 'dan iskan mutumin me bin matan mutane ko, dariya Saif ya 'kunshe kafin yace you suppose to thank him, he saves your wife, anyway wllhi he's a nyc guy very dude, har ya fada mun jira yake ka saketa ya aur.... bai gama rufe baki ba Haidar yace "watch your mouth kar kasa na zubar maka da ha'kwara.
"Saif ya kama cikinsa yana dariya yace goga na Hanifa bada kanka a sare, har fever fah saida kayi tsaban soyayya
"Haidar yayi wata murmushi yace , yanzu zanje na sameta ta sallamesa daga gidan nan kafin ranta ya 'baci ko kuma ya kwana yana frog jump. Saif yayi wata dariya yace har ka gama kukan akanta zaka koma mata hali ko, kasan yanzu mun samo weak point dinka soldier, ai bansan kana kuka ba saida Hanifa ta 'bace, Haidar yayi murmushi yace shiasa ma na saka shades din nan kartaga kaman nayi kuka ta raina ni kaga ai GIRMA YA FADI. Saif yace there you go again, wllhi ka kuma tunzurata ta gudu zaka nemi me nemo maka ita. Haidar yace ai ta dawo knn nida ita mutunka raba. Saif na dariya yace " ni zan wuce na sanar da su Hajiya so that they shouldn't worry.
"Haidar ya gyada kai yace sai munyi waya kafin yasa kai ya nufi sashen Inna, ya wani daure fuska kaman bashine yake magiya dazun gabansu Abba ba, Inna na zaune a parlor tana cin gya'da Haidar ya shigo. Kallonsa tayi galala tace meye haka kaikuma zaka wani shigo wa mutane babu sallama, bai ko kalleta ba ya sa kai zai shige 'kuryan 'dakin, mikewa Inna tayi tasha gabansa ta ha'de giran sama da 'kasa tace malam nace lafia, cire shades din idonsa kawai yana mata mugun kallo bata san yana ji da haushinta ba dama, dariya tayi tace toh ka ciro idon naka mana kawai ka huta, ni dai bazaka shige mun daki ba. Gajeren tsaki yayi snn ya juya kaman zai fice, ta koma ta zauna tana sababi, aiko tana zama Haidar yayi wuf ya shige dakin ya maida kofa ya rufe. Nan fa Inna ta soma fadin wllhi bakamisa ka biyota har nan ka daketa ba, zaka fito ne ka sameni waye me tsoronka toh bindiga ma yaci uwashi, kurin 'karya Allah yasa anan muka ga hawayenka, ashe ma 'karyan jarumtaka kake
"Hanifa da bata san da mutum a 'dakin ba ta sa kai ta fito daga bathroom daure da towel a kirjinta da alama wanka ta fito, tana ganinsa ta razana ta juya da sauri zata shiga bathroom, fincikota yayi ta fa'do jikinsa, suna iya juyo 'dumin numfashin juna, ya kuwa 'kura mata ido baisan sanda ya cire shades din idonsa ba ya shiga kallonta kaman ya ha'diyeta. Ganin ya kurawa 'kirjinta ido yasata saurin kiciniyar 'kwace kantq tana fadin "dalla malam ni ka sake ni.... matseta yayi cikin jikinsa yace " ma waye kike wa mahaukaci.... ture sa ta shiga yi da iya 'karfinta tana fadin " toh nida kai nake, waima iana ruwanka dani ne, bata ankara ba taji ya saka bakinsa cikin nata ya shiga kissing dinta, sosai take turesa aikuwa ta hade hkwaranta ta gantsara masa cizo, da sauri ya cire bakinsa saida fatan bakin ta 'kara ja dama yaya, kallonta yake da mugun mamaki kafin yace "kije ki sallami wnn 'dan iskan mutumin tunkan ranki ya 'baci.... "Galala take kallonsa kafin tace " ba 'dan iska bane tunda da aure yake sona snn bazai ta'ba mi'kani wa 'yan iska ba zaintsare ni ya kare mutunci na..... bata gama rufe baki ba Haidar ya buge bakin yana huci yake fa'din " a gaba na kikce da aure yake sonki da urenki a kaina. Kika sake gigin fa'da mun makamanciyan wnn maganar sai kin raina kanki... dogon tsaki taja tace toh ai gani nayi takardan saki na zaka bani koh.
"Take jijiyonyin jikinsa suka tashi ya koma Aliyu Haidar dinsa, yana mata mugun kallo yace ki cire maganar saki tsakanin mu NI DA KE babu saki a tsakaninmu har abada.
"Mtsew nide bana sonka bana sonka ka sake ni mana ka huta,
"buge bakin yankuma yi yace toh waye me sonnaki, danma za'a taimaka maki.
"Oho dai bana son taimakon nace ka sakeni ai ba dole.
"Idan kika sake furta kalman sakin nan wllhi zaki raina kanki, ya fadi yana mayseta cikim jikinsa. Na fada miki ki sallame mutmin nan kafin ranku ya 'baci. Daga haka ya fice ya samu Inna zaune ta hada tagumi, kallonsa tayi kafin tace jarabebbe duk jarabarka haka zaka barta dole ka saketa. Ficewa yayi bai ce komai ba.

"Hanifa yana fita ta shiga goge bakinta tana jan Allah ya isa, mugun banza ai me hali baya canzawa, dama nufinsa knn akanta yasa ya sauya mata kwanaki, Inna ce ta shigontana fadin me ya maki kuma, tsaki ta danyi tace Inna dan Allah kisa Abba yasa yaHaidar ya sakeni wllhi ko ganinsa bana sonyi. Inna tace sha kuruminki saki dole a rubuce take ni dai Allah sa baki da juna biyu kinga daga kin gama idda sai mu sha bikin ki da wnn loyan, Hanifa ta yatsina fuska tankalli Inna galala tace "ni bani da wani juna biyu innma juna biyar ne duk bani dashi ni babu abunda ya ta'ba shiga tsaknina da shi, aure kuma ba yanzu zan 'kara ba makaranta zan koma....
"Baki sake Inna ke kallonta, wai babu abunda ya ta'ba shiga tsakanin su... murmushi tayi tace ai kinga yazo gidan sau'ki babu iddansa akanki ma, yana sakeki nidai ki auri loyan nan yanada hankali gashi fuskansa a sake kullum farai farai. " bata kuma cewa komai ba har ta gama saka kayan jikinta.

"Koda Sumy ta dawo daga sch kaman zata cinye Hanifa dan murna, Hanifa tace ke wani course aka baki, Sumy tace Maths education, Shema kuma information technology, Hanifa tace kai na maku murna wllhi, Sady fa 'yan ABU
"Sady microbiology take yi.
"Nima dai jamb kawai zan sake na koma sch, Hanifanta fadi tana duba handouts din Sumy.
"Sumymta riko hannayen Hanifa tace " baby sis ha'kika you went through a lots of difficulties, nasan tun da jurewa kawai kike da halin yaHaidar saboda biyayya wasu Abba, Allah ya saka maki da alkhairi ya baki ikon cin jarabawarki. We'll aways be there for you kar ki mance, we all lve you much. Rungumeta Hanifa tayi tace haka ne Sumy nasan kuna sona nima ina sonku, Mamy da Abba bani da iyayen da suka fisu, iyayena haifata kawai sukayi amma Mamy da Abba sune komai na sai kuma ku 'yan uwana masu 'kaunata,
"Sumy tace haka ne Allah ya shige mana gaba, ameen Hany ta amsa. Kafin tace ya labarin abokin... Sumy tayi dariya tace 'Danmasani ana can yakusa gamawa gana daya ai, gidan duk babu dadi, babu Shema babu Sady babu 'Danmasani, at least yanzu na sameki. Hanifa tana dariya tace indeed. Mamy ce ta shigo tana fadin ku tashi ku hada abincin Barrister, gaba daya suka mike suna fadin toh mamy.
"Tare tare sukayi komai, sai murna da ganin junansu suke... Hanifa na ri'ke da jug Sumy na ri'ke da tray suka nufi sashen baki. Saida sukayi nkckn ya basu izinin shiga snn suka shiga, da murmushin sa suka gaisa, Hanifa tayi introducing Sumy, nan suka 'buge da hira da Sumy dukda ba wani surutu ne da ita ba, Hanifa tace bari akawo maka flask din, yayi nodding kansa yana ajiye remote. Sumy ta mi'ke da niyyan binta sai juyo muryansa tayi yana fadin a'a yaya za'a bar guest shi kadai gashi ba'ayi serving dinsa ba, murmushi Sumy tayi ta dawo ta zauna tana fadin ai bansan cikin naka bane, murmushi shima yayi yace aiko yakamata ki sani tunda lissafi kike karantawa, da mamkimta dago tana dubansa tace "how do you know,
"Murmushi Sameer yayi yana daga gira sama yace " I just guess, kinsan na iya guessing,
"Hum gaskiya you guess right, nan ta shiga zuba masa abinci a plate saida ta kusan cikawa, ya kwalalo ido yana kallonta yace ina zan kai wnn saidai idan tare kika zuba mana ne toh,
"Dariya tayi tace haba ai nasan lawyers da cin tsiya saboda su samu strength na depending clients dinsu.
"Dariya Sameer yayi yace Ok fine, but gaskiya ki rage yayai min yawa, kadan ta rage, ya langabe kai yace ki dai kara ragewa, saida ta rage sau uku kafin tace final, bazan sake ragewa ba idan ba so kake

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

2 years ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment