Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kotu, idan ba kai ka kasheta ba waye ya kasheta, snn kowa ya sani Latifa bata tarayya da kowa sai kai.
"Barr Barnabas ya juyo da dubansa ga Al'kali snn yace" Ya me sha'ria, Captain Aliyu Abubakar ya masa laifinsa a ganan jami'an tsaro a ranar 21 ga watan January bayan an sami gawan late Latifa Tanim a cikin gidansa, da wnn 'kw'k'kwaran hujja nake ro'kon wnn kotu me alfarma data dubi irin rashin adalcin da Captain AA yayi wa shugabansa Naval Chief of Staff Admiral. Tanim Razak ta hanyar kashe masa tilon 'yarsa da ya mallaka a fa'din duniya, ta yanke wa captain AA irin hukuncin da ta dace dashi. Na gode ya me shari'a.... Barr Barnabas ya tafi ya zauna, "Haidar kuwa gaba 'daya ji yake tamkar jijiyoyin jikinsa su daina aiki, yana 'dago ido sukayi ido hudu da Hanifa idonta yayi jajazur, through kawayan idon juna suke aika wa juna sakwanni, take yaji wani strength yazo masa. Zuciyansa tana da'da kara masa 'karfin gwiwa." Admiral kuwa wani da'di ne ya ziyarci zuciyansa, ji yake ya eiga yayi winning case din nan an gama.

"Al'kali ya su kuya yayi wasu rubutu kafin ya dago ya dubi Sameer yace Barr Ridwan ko kanada abunda zaka tambaya daga wanda ake 'kara.
"Eh ya me shari'a Barr Ridwan ya fadi kafin ya fito zuwa gaban kotu.
"Ya dubi Al'kali yace " ya me shari'a ina bu'katan kotu ta bani dama na bu'kci Captain Aliyu ya fa'dawa kotu asalin ala'karsa da marigayiya Latifa.
"Kotu ta baka dama Barr Ridwan go ahead,
"Thank you your honor, Barr Ridwan ya fa'di kafin ya dubi Haidar yace " Captain AA kotu tana son sanin asalin alakarka da latifa... nan Haidar ya fadi komai, cewa shi ba son Latifa yake ba hasalima ita tayi seducing dinsa har suka soma aikata mummunan laifi, snn yayi taking wnn advantage dinne dan ya cimma burinsa na binciken da yake akan mahaifinta.
"Barr Ridwan yayi murmushi kafin yace" Captain ko menene kake zargin Mahaifin nata dashi har ya kasa ha'kura ya la'ka maka sharri...... " Objection my lord, Barr Barnabas yayi interrupting kafin yace" ya mai shari'a ya kamata lawyern wanda ake zargi ya daina shigo da wani shari'a cikin wani shari'a... "Korafi bata kar'bu ba, Barr Ridwan ci gaba da tambayoyinka. "Murmushi Sameer yayi kafin yace na gode ya me shari'a.
"Nan fah idon Admiral ya soma kadawa cikinsa ya shiga kugi, Barr Barnabas ya girgiza masa kai alamun kar ya razana.

"Barr Ridwan yaci gaba da fa'din, ko menene kake zargin shugaban naka dashi Captain AA,
"Haidar yace, ina zarginsa da almundahana da dukiyan 'kasa snn ina zarginsa da hannu a kisa tsohon kwamandan rundunar sojin ruwa.
"Barr Ridwan yayi murmushi kafin yace, knn Latifa tana tayaka binkice akan mahaifinta,
"Kwarai tana tayani, tare da ita muke binkice, hasalima ana gobe za a samu gawarta a gidana munyi waya cikin dare take ce mun na taimaka mata kar ya kasheta, ni kuma ban dauki hakan serious ba dan kwanakin baya tayi mun haka daga baya tace mun wasa take.
"Barr Ridwan ya juyo yana duban Al'kali kafin yace ya me shari'a, Captain AA ya kasance me gaskiya akan aikinsa wanda duk mutanen da suke tare dashi sun san wnn, sann 'ko'kari da yake yi na tono gaskiya shi yasa Admiral yayi 'ko'karin kashe 'diyarsa dan ya daurawa Captain sharri da bazai iya fita daga ciki ba.
"Ya me shari'a ina son gabatar da takardun da Haidar ya samesu ta hanya Latifa daga wajen Admiral.
"Alkali yace kotu ta baka dama Barr Ridwan.
"Na gode ya me shari'a, snn ya miko takardu maga takarda ya kar'ba ya mi'kasu ga me shari'a.
"Al'kali ya kalli takardun sosai kafin ya soma magana" Bisa ga hujjiji da suka gabata a gaban kotu, kotu tana son yin binciken wa'dan nan takardu, dan haka kotu ta 'dage wnn shari'a har zuwa ranar biyu ga watan may. Snn za'a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa ranar da shari'a zai zagayo. Daga haka Al'kali ya mike ya fice, nan mutane suka soma fitowa.
"Aka zo za'a wuce da Haidar kuka sosai su mamy sukeyi, shima kwallan ne yaji ya ciko idonsa ganin mamy ta rungume Hanifa tana kuka......

👸🏻Queen Samy😍💋💄.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
71

"Banda safa da marwa babu abunda yake cikin tapkeken parlornsa wanda yasha furniture na alfarma, dun'kule hanunsa yayi ya daki garu yana furta" Damnn it Damnn everything.... that little Brad really wants to die just like the way his invincible father does, you really don't know who you messing with 'karamanin 'dan iska. Tsaki Admiral ya buga jin waya landline dake ma'kale a parlorn na ringing..... " A hasale ya 'daga yana fa'din" what's this again, didn't I tell you, I don't wanna seee anybody..... "Am sorry sir " NNPC chairman really wants see you, he said you have an appointment.
"A sittin Admiral yace " let him in...

"Dad din Aisar na shigowa Admiral ya mike yana fa'din" Alhj Hashim everything is just trying to turn to a disaster. "Dad din Aisar ya mika masa hannu yana fadin" calm down pls Admiral,
"No I can't possibly calm down, your son ruined everything, kar ka mance Alhj Hashim if I go down you'll go down too, I can't loose my carrier and my wealth, wllhi akan matsayina da dukiyata zan iya kashe komawa waye kai kasan da haka. You perfectly know sabida kai muka kawar da Barr Ridwan, toh yau dai Barr Ridwan is back again, dan gaba 'daya 'dansa be rage masa komai ba harta taurin kansa irin na ubansa ne, maganan da nake maka a yanzu *Chief of defense staff*( commander in heads na rundunar sojojin Kasa, Sama da kuma Ruwa) also knows about the case, snn idan na bari aka tabbatar ni na kashe former cheif of naval staff ta 'karemun,. Yaran nan sun dage sai sunga bayana and this is all your fault..... " Enough Admiral, Dad din Aisar ya dakatar dashi kafin yaci gaba da fa'din" ya kamata ka daina daura duka blames din akaina navy, what could I possibly do, sanin kanka ne saboda kai nayi abandoning Aisar na lokaci me tsawo despite the fact tun tasowansa bai samu wani soyayyata da kulawata ba, kai kasa nayi forcing dinsa ya zama soja duk a tunaninka zaka samu goyon bayansa, toh dan an samu akasi sai ka ringa ganin laifina, I've nothing to do with what's going on between you, and let me remind you this, Aisar is my own son, and I still love him no matter what he does, So am advising you not mess with him.
"Da mugun mamaki Admiral ke bin Dad din Aisar da kallo, kutt he couldn't just believe it, wai Alhj Hashim ke ya'ba masa maganganu haka akan 'dansa, " murmushi Admiral yayi kafin ya 'karaso gaban Dad din Aisar cikin takun isa da gadara ya shiga buga kafa'dunsa kafin yace" NPPC National Chairman, yayi wata mirmishi mai sauti ya shiga tafe hannayensa yana fadin " bravo gaskiya ka birgeni, ashe dama kana son 'danka lallai kuwa bakayi shirin neman duniya ba, toh abokina naji I won't mess with your precious boy, but don't forget that sirrinka yana tafin hanuna, and if I exposed you will loose everything, everything mr chairman, and when I say everything kar ka mance harda dear son dinka, your wife carrier and all. Dan haka ina shawartakan abokin ta'ddanci na, yanda muka soma mu 'karasa if not zan fasa da'd'den sirrinka. Kasan kuwa yaron nan yasan cewa you were the one who took his Dad, he will never let you get away with it, so advisibly ka bini a sannu and don't do anything stupid.
"Dad din Aisar ya share gumin da ya karyo masa dukda sanyin ac din dake blowing a cikin parlorn, yayi gyaran murya yace "so now meye abunyi, Admiral ya mi'ke yana murmishi ya nufi bear bar dake cikin parlorn ya zuba masu a cup snn ya mi'kawa amininsa yace" now you are talking my friend.
"Barr Barnabas ne ya fito daga wata 'kofa, ya mi'kawa Dad din Aisar hannu suka gaisa kafin yace" I'm Barr Badamasi Barnabas, nine lawyern abokin ka, and I'm the key to your solution, without going through all details ina son ka bani hadin kai Mr Chairman, inaso ka fahimci abunda zan fa'da for your own good.
"Dad din Aisar gaba daya he's lost dan shi baya nan akayi shari'a yau ya dawo daga Abuja.
"Barr Barnabas yayi murmushi kafin yace" kasan yanda zakayi a matsayinka na mahaifin Aisar ka shawo mana kansa yaje yabada testimony na karya on our up coming trial..... " What! Dad din Aisar ya fadi gamida dago kai, no this is impossible Aisar will never do that kai ka sani Admiral, kasan shi kasan shine ke tsaye kan shari'an Haidar, snn idan nace masa haka zamu iya samun matsala koma yayi making complaints against me.
"Barr Barnabas yayi murmushi kafin yace " zamuyi kidnapping mum dinsa sai muce idan har baiba da shaidan 'karya akan Haidar ba zamu kasheta, he can't file a complaint against you dan yana son mum dinsa I suppose. "Kaga idan anyi haka shiknn bamuda sauran damuwa, tunda kowa ya sani Haidae bashi da aboki kaman Aisar, snn duk shaidan da ya bayar kotu zata amince, kaima kaga asirinka zai rufu babu me kuma binnewa.
"Zufa ta ci gaba da karyowa dad, Admiral na zaune saman kujera yana girgiza 'kafa yana kora bear yace " toh abokina yaya ka gani.
"Barr Barnabas yayi dariya yace a bashi nan da two days yayi tunani akai tunda we still have time before the trial, munada almost two weeks agaban mu.
"Admiral yayi murmushi yace wnn haka ne, ya mike ya nufi dad din Aisar wanda shima mikewa yayi da niyan tafiya, gaisawa sukayi kafin yace sai najika abokina...

"Zaune suke gaba daya a parlorn momma, da gani kasan har yanzu hankalinsu a tashe yake, sallahn la'asar da aka kira yasu mi'kewa dan gabatar da nasu ibadan, kowa ya kalli Hanifa sai ya tausay mata dan ta rame sosai ga laulayin ciki da take fama dashi,.
"Abba ne ya kira mamy a waya ya shaida mata lallai idan zasu taho masau'ki su taho da Hanifa yana son ganinta, hakan kuwa akayi bayan la'asar sukayi sallama da momma da Inna dan Inna kam tana gidan momma bata bisu ba.
"Suna tafe a mota Sady ta rike hanun Hanifa dake gefenta, a zuciyanta take tuno rayuwarsu a da, Allah sarki Hanifa 'kawar fa'dan ta gashi yanzu gaba 'daya tayi sanyi magana ba bata faye ba saidai um ko umum, wani sabon tausayinta ya kuma shiganta, a haka har suka isa masauki. "Mamy ta ri'ko Hanifa suka wuce ciki, yayinda Sumy da Sady suka tsaya da Sameer a haraban wajen, Sady tace uhm barin shige ciki nasan na ta'kura maku, daddyn Amal daga gani bakin ka akwai magana, dariya kawai Sameer yayi daidai nan Aisar yayi parking a gefensu,.
'Gajeren tsaki Sady tayi tace ni na wuce kafin Abba yace ina muka tsaya. Daga Sameer har Sumy sun gane take taken Aisar da Sady," Aisar ya karaso ya mika wa Sameer hanu suka gaisa Sumy ma ta gaishe shi, Sady kam tsaki ta 'danyi tace na shige nikam..... Hanunta Sumy ta ri'ko tace I guess you don't have to leave sis, why not mu zauna gaba daya a kujerun can mu 'dan ta'ba hira, let's have some fun,
"Aisar ya 'dan ta'be baki yace " no no let her go, no one needs her here, besides she's only disturb you with her noisy character.... " Sady ta galla masa harara kafin tace " in the first place wama ya gayyace ka nan hum, tunda ba akanka zan zauna barima ka gani, karasawa tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun, Sameer da Sumy me zasuyi banda dariya, haka suka zauna gaba daya a kujerun rabin hiran fa'dan Aisar da Sady ne, "Sumy tace waini haka za'a yi auren naku kullum kuna cikin fa'da.... " waye zan auran wnn tab niko Allah kiyaye ni, ai wnn duk mijin da zai kwasheta yanada aiki sosai.
"Dogon ysaki Sady taja kafin tace" you know what it's not funny.... ta mi'ke zata tafi Sameer ya bata ha'kuri kafin ta dawo ta zauna,
"Aisar yace ai dama baka bata ha'kuri ba nasan bazata iya tafiya ta barni a nan ba, right sweet, ya fa'di yana wani kashe ido daya.... gaba daya saida sukayi dariya harta Sady dake faman bonewa.
"Sun 'dan jima suna hira kafin Aisar ya mike yana fa'din " toh sweet am leaving now, anything for me, " tsaki Sady tayi kafin tace" and who cares ka tafi mana dama wa ya ri'keka on the contrary munfi son haka ma.
"Sameer na dariya yace so soon navy.
"Eh wllhi Dad ya dawo daga Abuja dazun ni kuma in court so bamu ha'du ba,
"Ok nima inaga I'll take my leave akwai abunda zanyi, gameda maganar documents dinn, Aisar yace no kar ka damu will talk later ai yanzu tunda *Chief of defense Staff* yasan da shari'an komai zai zo mana da sau'ki, will keep on touch kaikam. Suka yi musabaha, Aisar yayi sallama da Sumy, kafinnya juyo wajen 'yar rigimarsa.
"Nan Sumy ta dan takawa Sameer har wajen motarsa kafin sukayi sallama.

"A parlor ya samu Mum tana kallon tv, zama yayi a gefenta fuskansa dauke da murmushi ya gaisheta, mum na mirmushi tace yaya dai son, " bisa ga dukkan alamu akwai hope,
"Yeah mum akwai hope insha Allah, mum guess what. " kallon shi ta danyi kafin taja hancinsa tace "just tell me.
"Ok kinsan meye mum, "I finally met her again, mum kin tuna yarinyar da nace maki na ganta a ABU, mum tace na tuna So?
"Mum ashe 'kanwar Haidar ce, su three plets ne mum, dayar tayi aure, dayan kuma ita Sameer ke son aura, and itace dayan your in law..... murmushi mum tayi ta rungumesa tace" am so happy for you son, har naji ina sonta tun kafin na ganta..... " Muryan Dad ne ya katse su, " A a Son what are you celebrating, da mamki Aisar ya dago yana duban dad dinsa dan kuwa bai ta'ba ganin haka daga garesa ba, duk da sun shirya amma dai baya treating dins haka, dan kuwa kodawasa bai ta'ba jin Dad dinsa yace masa Son ba, ita kanta mum tun shigowarsa gidan yake bata wani kyakkyawan kulawa.
"Dan murmushi Aisar yayi yace" Sannu da dawowa Dad, dad ya matso ya rungume Aisar yana fadin "I miss you Son, hope na sameku lafia,
"Sosai abun yayi wa Aisar banbarakwai, ya danyi murmushin ya'ke yace lafia dad.
"Mum kuwa wani farin ciki ne ya ziyarce ta irin rayuwan da ta jima tana masu fatan samu knn, mikewa mum tayi tana fadin "I'll cook dinner for us, Dad yace sounds good, karfa ki mance favorite din Son zaki girka. "Aisar de gaba daya he's lost, what's going on, why all this..... muryan Dad ne ya katsesa
"Dad ya dubi Aisar yace "Aisar I want us to talk......

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
72

*This chapter naku ne masoya littafin mijin haneefah, ina matukar jin da'din yanda kuke biye dani a wann littafi nawa ILYSM❤*

" Aisar ya tattaro nutsuwarsa ya fuskanci mahaifinsa yana sauraren me yake cewa.
"Son, tun tasowarka we never spend much time together, I haven't been a good father to you and I treated you badly, muryan dad ya soma rawa, until now I still can't forgive my sef..... "da sauri Aisar ya matso kusa dashi jiki a sanyaye ya rungume mahaifinsa yana fa'din" please dad stoo saying all this, besides yanzu muna tare gana daya ni kai and mum, and we're living a happy family, this is our dream, gashi Allah ya cika mana burinmu, mum is happy now, you are still my only Dad no matter what, and I love you dad, I'll do everything to pleased you.
"Dad ya dago kai yana kallon Aisar kafin yace" shiyasa nake ga ya kamata mu tafi hutu koda na sati biyu ne, mu mance da wani stress na aiki da saurnsu, let's spend time together and know each other well. Ko yaya ka gani Son, please don't reject my offer, kar ka mance ban ta'ba tambayan ka mun wani abu kaman haka ba, please son.....
"Girgiza kai Aisar ya soma kafin yace" Dad ba wai ban son tafiyan bane this is not the right time, am busy now, besides kasan yanayin aikina it will affect my job idan nayi tafiyan...
"Ka bar zancen aiki Son, idan kaso ko yanzu zaka iyayin ritaya ni na tara maka abunda zaka bu'kata na cash har 'karshen rayuwanka dama zuriyan da zaka haifa, please son let's leave this place for a while..
"Dad try to understand me, bazan iya tafiya na bar Haidar ba a wann situation din, snn maganar aiki kuma sai yanzu nake da'da jin son aiki na, am proud to be Navy Dad, am sorry but I can't leave right now, why not ka bari some other time sai muje, zan dauki hutu sai muje where ever you want us to go...
"Haba nan fah hankalin Dad ya soma tashi, dan gaba daya ya kasa samun goyon bayan Aisar..... " A fusace ya mi'ke yana nunasa da yatsa" kai bakayi girman da zan saka abu ka 'kiyi ba, dan haka dole ka bini mu tafi ko kana so ko baka so, ni bazan tsaya a 'kasan nan ba, abubuwa suna neman kwa'bewa, Aisar saboda kai nake son mu tafi muyi nisa daga nan, na hanaka sa kanka cikin shari'an yaron nan ka 'kiji ka 'ki gani, toh wllhi dole ka bini mu tafi, I don't care about your so called job, na riga na tara maka ma'kudan ku'di you are my only son bazan iya zama inaji ina gani na rasa ka ba...... " Haba Dad meyasa kake fadan irin wadan nan kalaman, kai da bakinka kace mun ka canza, gashi yanu ina ganin akasin haka....." Ran Aisar yayi matu'kar 'baci, jijiyoyin jikinsa suka yi ra'da ra'da idanunsa sukayi jazur, ya matso kusa d Dad yana girgiza kai yake fad'in" no no I can't do that, bazan iya tafiya na bar Haidar ba, mutumin da ya zamar dani mutum, mutumin da yayi sanadiyan rabuwata da shan giya, mutumin da yayi sanadiyan rabuwana da bin mata, mutumin da ya rescuing live dina lokacin da kayi abandoning dina, and last kar ka mance he's the reason why am here with you today, yanzu yana gidan yari akan laiffin da be aikata ba and you're asking me to leave him all alone, no Dad think of..... " Enough Aisaaar, Dad ya daka masa tsawan da yasa mum ta fito babu shiri, " Barin fa'da maka like it or not dole mu bar kasan nan har sai al'amura sun daidaita, dan haka tun kan ranka ya 'baci ka kawo mun passport dinka...... " Cikin tsan tsan 'bacin rai Aisar ya soma fa'din" don't tell me you have something to do gameda abunda ya samu Haidar Dad, ka fada mun dad are you behind this..... wani wawan marin da dad ya kifa masa ne yasa yin shiru hade da dafe kuncinsa..... mum ta karaso tana fa'din haba haba Alhaji wai yaushene kai da Aisar zaku zauna 'karkashin inuwa guda, haba haba.... " Ranar da 'danki ya gane cewa I'm his father and I've every right for him, na baku kwana biyu rak keda 'danki ku shirya mu bar 'kasan nan daga haka ya wuce ya barsu tsaye a wajen.
"Mum ta rungume Aisar tana lallashinsa, zama sukayi bisa sofa mum na duba fuskan 'danta yanda aka sharara masa mari, saida yatsun dad suka fito. Da sauri ta dauko iceblog tazo tana danna mas wajen, "Son kayi hakiri pls kasan halin dad dinka ka ringa binsa a sannu.... " Haba mum yaushene dad zai gyara halinsa, tunda naga yana acting strangely nasan wani abun yake shiryawa, kuma wllhi babu yanda zanje bincike yanzu na soma, idan da hanunsa akan abunda ya samu Haidar he must pay for it...." Enough ya isheka haka, mahaifin naka kake fadan abubuwa akansa, ni na gaji da wnn hali naku Aisar, dole mu tattara mu tafi idan hakan zai zame mana sau'ki daga haka itama ta mi'ke ta bar parlorn, kallo kawai Aisar ya bita dashi har ta haye sama....

"Ana gobe su mamy zasu tafi Hanifa tayi bleeding sosai sida ak kaita asibiti, Dr yace dole ya riketa a asibiti na ysawon sati guda dan tana bu'katan hutu damuwa ya mata yawa, snn tana risk na rasa babyn dake cikinta, wai karkaso kaga tashin hanakli wajen su mamy, gaba daya hankalinsu y tashi dukda Abba yaso su tafi tare amma wann matsala da ya auku yasa dole su barta da Inna anan, sosai Abba ya lallasheta yace ta daina sa damuwa a ranta, hakan kuwa akayi da kyar mamy dasu Sumy suka rabu da Hanifa, Sameer ne ya kaisu airport suka daga zuwa jihar kano.

"Sosai ake bata kulawa a asibiti, haka Inna da momma suna bata kulawa sosai, satin ta guda aka sallameta ta dawo gida, ko ka'dan basu barinta ita kadai bale ta shiga wani tunani, mamy kuwa kullum sai sunyi waya.

"A 'bangaren su Aisar kuwa abu ya 'kara damewa, baga mum ba ga dad dinsa ba, shide Aisar ya kafe yace babu yanda zaije, ga Admiral yasa Dad din Aisar a gaba idan beyi wani kata'bus ba tofa asirinsa shima na iya tonuwa.
"Karshe dad dai lalla'ba Aisar yayi ya nuna masa komai ya wuce, he's willing to give him his unconditional support akan shari'n da suke, abun har ya bawa mum mamaki, shi dai Aisar yaji mahaifin nasa ne kawai amma yana taka tsan tsan dashi dan kuwa haka kawai yake jin be yarda dashi ba.

"Ana sauran kwana uku a koma kotu, yau Aisar ya dawo gida ya samu Dad dinsa zaune a parlor ga securities dinsa sai kai komo suke a gidan, Dad na ganin Aisar ya mike da sauri ya 'karasa ya rungumesa yana kuka shar shar da hawaye, abune me kaman wuya kai shi tun tasowansa bai ta'ba ganin hakan daga mahaifinsa ba, dan haka jikim sa yayi sanyi sosai, ya kira chief security din Dad dinsa yana tambayansa lafiya me ya faru, shima kasa basa amsa yayi ya sulale ya gudu, mikewa yayi ya nufi sama yana kiran mum....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
73

"A staircase Aisar ya hadu da jumy me masu aiki, kallonta yayi yanda yaga itama jikinta a sanyaye tana gaishesa ko amsawa beyi ba ya shiga bu'de 'kofoffin yana fa'din mum! Mum! Mum, fitowa yayi a guje ya dur'ko daga stirs ya nufi kitchen yana tambayan maikatan ina mum, babu wanda ya iya basu amsa cikinsu, a tamanin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment