Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa um bana cewa um um amma kuma ina sane da duk abunda ke faruwa, wnn mutumi ya mayar da 'diyarsa Latifa tamkar matarsa ya lalata mata rayuwarta wnn mutumi shi ya kashe tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa dan ya maye gurbinsa wnn mutumi shi ya kashe mun 'diyata a gabana...... kuka ya kufce mata. " Dan'kari ma'kari, kotu tayi tsit sai sautin kukan mum din Latifa kawai kakeji, da yawan mutane mamakin irin laifukan Admiral da aka zayyano suke, anya wnn mutum ne lallai wnn shime babban shedan.
"Al'kali ya 'dago cike da 'dunbin al'ajabi kafin ya furta " kotu tana bu'katan Naval Chief Of Staff da ya shigo cikin Akulkin tuhuma...." Admiral ya soma 'bari yana fa'din ya me shari'a kar ku yarda da wnn matan ta jima da mutuwa fatalwa ce kawai ta fito... tsawan da aka daka masa yasa yin tsit jiki a mace ya nufi gefen Haidar..." wata mirmushi kawai Haidar ya sakar masa sanda ya tsaya a gefensa.
"Alkali ya soma fa'din" Admiral kaji abubjwan da iyalinka ta zayyano akanka, shin ka yarda ka amsa laifinka kokuwa....
"Admiral kam ganin ta tashi masa yasa duk ya susuce, bai ankaraba ya hango dad din Aisar na 'ko'karin warewa. Da sauri ya nunasa yana fadin ga dayan can zai gudu, Dad din Aisar ya soma fadin" ni kuma me ya hada ni da kai ni babu hannuna cikin mutuwan 'yarka nida ka kamamun mata kasa 'dana bada shaidan 'karya dan kar..... Admiral ya soma fadin karya kake kai ka kawo wnn shawara dan kar asirinka ya tonu abunda kayi shekaru talatin baya kisan Barrister Ridwan Marafa da kayi...... "Ai bai gama rufe baki ba Aisar yayi wata tsalle ya dun'kule hannunsa bai tsaya ko ina ba sai fuskan Dad dinsa ya kai masa wani wawan naushi naushi duk tarin mutanen da suka taru suna ri'ke Aisar ina bai ko sairaresu ba dukan Dad kawai yake da iya 'karfinsa yana fa'din " you blackmail me you monster.... "Dad ya dago kai yana fadin" Aisar kar ka yarda dashi 'karya yake maka... inaaaa Aisar baiji bai gani dukan Dad dinsa kawai yake ya cukume wuyansa yana fa'din am gonna kill you invincible ina ka kai mun mum dina ina mum takeee..." fuskan dad duk jini yake fa'din tana guest house dinshi tana guest house din Admiral..... " A tamanin Aisar ya fice daga kotun..."( jama'a gaba 'daya kotu ta rikice😳) dole Al'kali ya bada hutun rabin lokaci abubuwa su daidaita tare da bada umarnin a tsare Admiral da Dad din Aisar.

"Hanifa tana farkawa sunan yaHaidar kawai take kira, mamy da Inna suka nufota bata tsaya sajrarensu ba dan kuwa komai ya dawo mata, fincike drip din hanunta tayi mamy ta fito a guje ta samu Dr da Abba suna magana.... ai suna ganinta a haka suka nufo ta babu shiri, da kyar mamy ta iya furta ta tashi she's out of control..... a sittin suka koma 'dakin gana 'daya, suka tarar Hanifa sai 'karamin ya'ki take da inna ita fa a barta taje taga mijinta, zasu kashesa, Abba ya ri'keta sosai yana fa'din" calm down Hanifa, ki nutsu nace, baki da 'koshin kafiya..." Abba yaHaidar dan Allah Abba kankaini ni wllhi lafiyata lou, ku kaini kafin nima na mutu dan Allah Abba, Abba wallhi bazan iya tsayuwa a nan ba ba tareds sanin halin da yake ciki ba, Abba ku taimaka mun...."Abba ya dago ya kalli Dr, girgiza kai Dr yayi yace ku kaita ta ganshi ko zata samu sau'kin ra'da'din da takeji.

"Aisar na fita Cheif of defense yasa wasu securities su bi bayansa don taimaka masa suka nufi guests house din Admiral.

"Captain Paul ne ke tsaron mum din Aisar, daya daga cikin yaran Admiral da yaga abunda ya faru a kotu wanda yake tamkar film ai tuni ya shiga neman layin paul, paul na dauka iskil ya labarta masa komai yace gwara yasan nayi ta tashi masu. A a tamin paul ya katse kiran, ya juyo ya kalli mum din Aisar da suka 'daureta matsowa kusa da ita yayi yana raywa a ransa da yayi biyu babu shiba da samun ku'di ba shi da shan wahalan banza ai gwara ya huta da matan nan.
"Matsowa yayi ya shiga shafa fuskanta, "mum ta tsatta masa yawu cike da tsana, kifa maya mari yayi ya shiga cire kayan jikinsa.... da jajayen idanuns Paul ke kallonta kafin yace zaki yabawa aya za'ki zaki san wa kika tsatta ma yawu.
"Mum na kuka take fadin Allah shi zai fitta dani daga sharrinka, shi zai 'kwace ni a hannunka... " Paul ya fizga 'dankwalinta kokawa suka shiga yi d mum yana 'ko'karin jan rigarta kawai sai jin an daki 'kofa sukayi......" Kan uban can..... wani kukan kura Aisar yayi ya haye kan Paul, dukan filin ya'ki kawai yakewa Paul, Mum me zatayi banda murna, ta dauki mayafinta ta rufa, har lokacin Aisar bayaji baya gani dukan paul kawai yake kaman an aikosa, Securities suka 'karaso suna fadin let us handle over captain...." suna jan Aisar Aisar be fasa dukan ba yana fa'din" let me kill this Animal let me finish him, he is not getting away with this......" Haka Paul ya koma tamkar baya numfashi, Aisar ya masa lilis.... " 'Dagowa yayi yana kallon mum dinsa rungume juna sukayi suna kuka me tsuma zuciya, nan securities suka tasa ke'yan paul aka wuce dashi....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
76

"Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci nan Al'kali ya wanke Haidar tsaf daga zargin da ake masa, Sady da Sumy rungume juna sukayi dan murna, Sameer na murmushi yake girgiza masu kai alamun no more kuka, Haidar tsakiyan 'kannensa yaje ya rungume su baki daya.
"Admiral da Dad din Aisar kuwa sai wulli wulli da ido suke, kotu ta yankewa Dad din Aisar life in prison tareda hore me tsanani bisa laifin samun hannumsa dumu dumu cikin kisan Barr Ridawan Marafa, "hannu Dad ya daura aka lokacin da yaji Sentence dinsa, ya juyo yana duban amininsa yana fa'din ka cuce ni Tanimu ka cuce ni...." Al'kali ya buga bnci Silence...." snn yaci gaba da fadin, Admiral. Tanim Razak, an kama da laifuka kaman haka na farko kisan Tsohon hafsun rundunar sojin Ruwa tareda iyalensa, na biyu tauye rayuwar matarka da 'diyarka ta hanyar humiliating dinsu, na uku kisan 'diyarka Latifa tareda 'durawa Captain Aliyu Abubakar sharri...." wadann sune laifukan ka. Kaman yanda take a 'kundin tsarin mulkin 'kasa a matsayinka na soja hukuncinka yasha banban da civilian" kotu ta yanke maka hukuncin daurin rai da rai ta hanyar rataya..... " These are your sentences" daga haka Al'kali ya mi'ke kotu ta amsa da kooooot. Jama'a suka soma turuwan fita, nan da nan aka ka'da 'keyan Admiral da Dad din Aisar.

"Ana 'ko'karin fiffitowa Cheif of defense ya 'karaso gaba Haidar da sauri Haidar ya sara masa, kan kace me shima ya sara wa Hakdar, ya mika masa hannu sukayi musaba snn yace" Captain AA you did a great a job, I salute to you navy, samun irinku a cikin sojoji ALHERI NE, keep on with it, zan bar lagos jibi, so kafin na tafi ina so akwai meeting da zamuyi."Haidar ya kuma sara masa kafin yace" Thank you very much sir, "The pleasure is mine Captain. Daga haka Chief Of Defense ya wuce securities dinsa sukabi bayansa.
"Chief of staff yasa a dauki mum din latifa a kaita asibiti a bata kulawa daga nan sai su nemi relatives dinta.

"Sameer zama yayi dirshan a bakin kotun yana kuka shar shar da hawaye, ha'ki'ka yau mutuwan Dad dinsa ya dawo masa sabo, ashe dad din Aisar da Admiral su suka kashe masa mahaifinsa....." Haidar ne ya 'karaso ya dafa sa, yana 'dago kai suka rungume juna take Haidar ma yaji hawaye na bin 'kuncinsa.
"Haidar ya soma fa'din" Sameer ka kasance 'da na gari, ha'ki'ka yau da mahaifinka na da rai zai yi tin'kaho da kai, Allah ya ji'kansa ya gafarta masa, your Dad is in better place Sameer, yau wa'danda sukayi sanadin mutuwar ga tasu tazo, snn zasu girbe abunda suka shuka.
"Sameer ya share hawayen idonsa kafin yace haka ne Haidar, na gode da kalamanka.
"Haba Barrister ni yafi cancanta na mi'ka godiyata a gareka, dukda kalamai kawai bazasu isa nuna maka irin godiyan da nake maka ba, na hantareka na ci zarafinka na wula'kanta ka, dukda haka baka fasa kyakkyawan 'kudirinka akaina ba, Sameer thank you once again....." pls Haidar ka daina mun irin wnn godiya haka ni da kai 'yan uwa ne....." muryan momma suka ji tana fa'din wnn haka ne 'ya'ya na, a tare Sameer da Haidar suka juyo, Momma na tsakiyan Sady da Sumy ta 'karaso ta ri'ke hannu Sameer da Haidar tace "Alhamdulillah yau Allah ya kawo mana 'karshen wnn shari'a, Allah bazai bar zalunci ta tabbata a doron 'kasa ba, yau azzalumai zasu fara girbe abunda suka shuka tun daga nan duniya har su isa masaukinsu a lahira, Allah ya da'da 'daukaka gaskiua a duk yanda take, snn ya kawar da 'karya a duk yanda take, gaba 'daya suka amsa da ameen.
"Haidar ya dan dube su yace momma Hanee I need go and see her, I can't stay here any long..... gana daya suka sa dariya ganin tsayuwar motar su Hanifah, Haidar ya dan harari Sameer yace " this is not funny Barrister may I've car keys, if you can give me a ride kuma fine, muje ka kaini na gant..... bai gama rufe baki ba ya hangota a guje ta nufo sa.... ai shima a tamanin ya nufeta, a tsakiya suka hade ya kuwa rungumeta tareda 'daga ta sama yana juyi.... Su momma dasu mamy su Inna harma dasu Sumy me zasuyi banda dariya, harta Abba saida ya dara,...
"Sun jima suna rungume da juna kafin ya dago face dinta yana kallo, kallomsa take itama babu ko 'kyafta ido, " yaHajdar what did the judge said, hancinta ya 'danja kafin yace " ba kinji sentences dina ba, yanzu haka an barni na miki sallama ne before a tafi dani....." no no that can't be... ganin ta soma wuri wuri yasa sa saurin rungumeta cikin jikinsa kafin yace" easy Beautiful kar ki mun asara biyu keda unborn dinmu, bakinsa dazu da kika fainting cikin court ba kadan da na zune nima..." yaHaidar ka fada mum pls me ake ciki...." shiru yayi kaman bazaice komai ba sai kuma ya daga ta sama yana fadin " I'm a free maaaaan, wani 'kan'kamesa tayi cikin jikinta hawaye na 'ko'karin fito mata tace" Oh Allah Alhamdulillah, sauran fa ina suke.... sai snn ya juya yamda ake shigedasu Admiral bayan ambulance itama kallonsu tayi. Suna gani aka tasa keyarsu, Har lokacin Haidar na rungume da Hanifah a hankali ya saketa ya nufi gabansu Admiral, kaman bazaice komai ba ya kuwa kai masa wata wawan naushi a fiska saida ya dur'kusa a wajen, "Haidar ya 'dagosa kafin yace " this is for Hanifa, Latifa and Aisar.... " didn't I told you " eventually you'll get what you deserves, now the time has come sir, you'll pay for each and single crime you had committed, ka sani Allah baya mulki da zalunci ya zaka tarar da abunda ka shuka miserable coward, "Admiral be iya cewa komai ba aka tasa 'keyarsa cikin ambulance, Hanifa ta 'karaso ta sakala yatsunta cikin nasa murmushi yayi sanda ya juyo da dubansa gareta...... kaman bazasu bar kallon juna ba haka suka yi " Inna ta ya'be baki tace " oh Mero naga duniya zaku zo mu tafi ne kokuma zaku cinye juna da kallo ne kamar tauraren cikin pilm(film)..... ko kuma kotun ne baku gajimda zamansa bangaba daya aka sa dariya.
"Haidar ya 'dan dubeta ya ta'be baki kafin yace 'karar ki zan shigar dan kina 'ko'karin raba auren soyayya, kuma nasan duk kishi ne ke damunki.
"Ta'be baki inna tayi ta jawo kennensa kafin tace ka gama nacinka sai ka sakar mun jikata..... Haidar ya ri'ke kunnensa yana 'dan 'kara Inna tace ashe sojann'karya ne..... gaba 'daya aka sa dariya Inna harda ranga'da gu'da ta shige tsakiyansu ta rungumesu tana fa'din Alhamdulillah Allah ka cika mun burina ko yau na bar duniya burina ya cika, Aliyu Haidar ya zama *Mijin Haneefah* ba Haidar da Hanifa kawai ba duk sauran mutanen dake wajen saida sukayi dariya.

"Phillips Drivern Haidar ne ya 'karaso da sauri dan murna baisan sanda ya rungume Haidar ba..... Haidar ya dago yana dubansa da mamaki, ai a sittin phillips ya soma shafa kai ya sarawa Haidar yana fa'din " Sorry Sir na kasa 'boye farin cikinane.... Murmushin 'kasaita kawai Haidar yayi ya bubbugi kafa'dan phillips yace is Okay Phillips I understand you, and thank you very much.... haka sojoji 'yan uwansa sukayita congratulating 'dinsa gameda nasaran da ya samu.
"Da kyar Haidar ya samu ya zille bayan yace wa phllips ya matsar da motan daga wajen mutane, Su Abba kam tuni sun wuce, Haidar da Hanifa ne suka rage, yana rungume da ita kaman mai tsoron kar wani abu ya gifta tsakaninsu, gaba daya sai suka koma tamkar celebrities ,haka suka shige bayan mota phillips yajasu, nan Haidar ya cewa phllips gidansu Aisar suka nufa.

"Suna isowa mamaki ne ya cika Haidar ganin motocin su Sameer pake a haraban gidan, Phillips ya fito ya bude masu hade da sara masu, hannun Hanifa Haidar ya sakale cikin nasa suka soma tafiya,
"YaHaidar cikin mutane fah zamu shiga ka sake mun hannuna kaga da alama su Abba na cikin gidan nan, ta fa'di tana kiciniyar kwace hannunta.
"Da'da matse hannun Haidar yayi kafin yace" So, matata ce fa, kikayi wasa 'daukan ki zanyi a hannu kaman baby..... dariya kawai Hanifa tayi ta sunne kanta sanda suke sallama a 'kofan parlorn.


"Gaba daya kallon mutanen dake parlorn ya dawo kansu, idan ka dauke Aisar da gaba daya kunyar Haidar yake ya kasa dago kai ya dubesa, Haidar ya fahimci hakan.
" 'karasowa sukayi suka Haidar ya soma fa'din Abba dama nan kuka nufa, Abba yace ku 'karaso son, Hanifa ta 'karasa ta gaida mum haka Haidar ma, mum ta amsa masu cikin sakin fuska tayiwa Haidar murnan cin nasara shima ya yi mata jajen abunda ya faru gameda dad din Aisar, mum ta 'dan share kwallanta sanda ta juya tana kallon Aisar, shima Haidar kallon Aisar 'din yayi wanda da gani hawayene ke fita daga idonsa koda kan nasa a sunkuye yake.
"Haidar ya mi'ke ya nufi Aisar, kafa'dansa ya soma dafawa yana furta" kayi ha'kuri Aisar komai mu'kaddari ne daga Allah.... Aisar cikinnkuka yana girgiza kai ya soma fa'din" Haidar I don't deserve you, I failed you, bazan iya ha'da ido da kai ba...." Haidar ya soma girgiza kai yana fa'din" haba Aisar ka daina fa'din haka pls, what you did was absolutely right, kar ka mance for the sake of your mum kayi haka, itace wacce tafi kowa muhimmacin a rayuwarka, Aisar I do understand you, idan da bakayi haka bane sai nace you failed, Aisar you really is a great Hero, we are all proud of you, what you did to me was an incredible I can't repay you, kaida Sameer and my entire family Allah ne kawai zai biyaku, I was never be alone, baku bar ni ni kadai by my self ba, " Kaida Sameer banida abunda zan iya biyanku dashi, kunsadaukar da rayuwarku a gareni, kun tsare mun matata snn a sanadiyana aka kidnapping mum dinka, Aisar thank you thank you for all you've done...... " ya riko hannun Aisar ya 'karasa ya ri'ko na Sameer ya hadasu duka baki daya yace" kun tuna lokacin da nake prison haka muka hada hannun mu mukace we're a team..... gaba daya suka murmusa harda sauran jama'an dake cikin parlorn, Haidar yaci gaba da fa'din babu abunda ya rage mun kaman naga 'yan 'kanne na sun samu maza irinku wanda suke fighting wa Family dinsu, ya juyo yana kallon su Abba kafin yace "Abba these my two brothers are madly in love with your daughters I hope zaka basu Abba..... gaba daya aka sa dariya, Sady da Sumy kuwa sunne kai kawai sukayi suna murmushi.
"Abba ya 'karaso ya dafasu dukansu yace "Haidar koda bayan raina ne Aisar da Sameer basu da mata sai Sadiya da Sumayya, burin ko wani uba knn 'ya'yansa su samu mazaje na 'kwarai... Mum na murmushi tace ku dakata wai ina 'yatan take ne nifa ban ganeta ba dan naga duk kamaninsu kusan 'daya, dariya akayi "Aisar ya 'karaso gaban Sady yana 'dan mata hararan wasa da suka saba yace oya jeki gaisa da mum dinki, dan kwanan zaki bar hannun mamy ki dawo hannunta dan nasan mamy ma ta gaji da fitinarki, mum zakiyi handing over, dan wnn new daughter dinki fitinane da ita...... gaba daya aka sa dariya banda Sady da ta gallawa Aisar harara, mum ta karaso ta rungume Sady tana fadin kyalesa daughter zaizo ya sameni ne.
"Abba ne ya masu add'ua kafin a watse saida ya saka ranar bikin Sady da Sumy nan da Wata uku masu zuwa, kowa yaji da'din hakan, koda zasu tafi masauki Mum tace an 'dan bar mata Sady ta 'dan jima mata anjima sai Aisar ya mayar da ita.

"Haka mu, ta wuni rabon fa'dan Sady da Aisar, yamma lis mum tace Aisar ya mayar da Sady bayan ta cikata da kayan arziki, a mota ma haka sukata kasa hali, saida ya biya da ita wani mall ya mata shopping, turo baki gaba tayi tana fa'din nidai wann kaya sunmin yawa bayan wanda mum ta bani, mamy zatayi fa'da, 'keyarta Aisar ya dungure yace" wancan na mum ne wann kuma nawa, cikin ledan recharge card na 'yan 'dari biyu ya fa'do, ta dauko tana bin katin da kallo kafin tace "what's this, murmushi yayi yace kin tuna sanda muka fara ha'duwa akan kina saka katin dari biyu ne kika kasa bani hanya na wuce...... dariya kawai tayi tana binsa da kallo komai nasa na burgeta tana jin sonsa na shiganta." Bu'de mata kofan mota yayi yace" bismillah Queen, murmushi kawai tayi ta shige cikin motan suka soma tafiya.

"A daidai gate din Hotel din sukayi clash da motan Haidar na fitowa shida Hanifa, horn kawai sukayiwa juna sukanshige.

👸🏻Queen Samy😍💄💋.....
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
77

"Haidar ya dubi phillips yace " Phillips just park the car here, anjima ka'dan zan fita, phillips ya amsa da ok Sir snn yayi kaman yanda Haidar yace. Da sauri Phillips ya sau'ko ya bu'de masu 'kofa hade da sarawa, a ladabce ya mikawa Haidar key sukayi sallama, nan fa securities masu tsaron gate suka shiga zuwa 'diban gaisuwa, gaba daya sai murnan dawowansa suke da murnan kawar da azzalumin Admiral.
"Haidar ya juyo ya kalli Hanifa gani yayi ta 'dan langa'be kai a 'kirjinsa dan tsawonta a daidai 'kirjinsa take, murmushi yayi bata ankara ba saiji tayi ya dauketa kaman baby.
"YaHaidar what's this, Haidar baice mata komai ba saida suka iso parlorn su ya ajiyeta, kallonta yake da kyawawan idanunsa kafin yace " I love you Beautiful, murmushi tayi ba tareda tace komai ba, ta 'dan mi'ke zaune tana 'ko'karin gyara mayafinta, hannunsa ya daura kan nata ya zame mayafin kafin yace" see you nan fah gidanki ne ko kin mance ne.
"Murmushi ta kuma yi batace komai ba har yanzu, "
"Beautiful bana son kunya kunyan nan naki, nida ke we are one dan haka ki saki jikinki, ta 'dago dara daran idanunta tana dubansa, giran sama Haidar ya daga mata kafin ya manna mata peck a goshinta, ta 'dan muskuta tace "yaHaidar kaga yanzu za'a kira magrib, tunda na rakoka kaman yanda kace ka tashi ka maidani su mamy kar suji shiru....
"Wani kallo kawai Haidar ya mata ya mi'ke yana fa'din" Beautiful babu wanda zai damu kar ki mance da mijinki kike tare, su mamy ma sun fi son haka. ya soma cire agogon hannunsa yana fadin barin yi wanka, mi'kewa tayi tana murmushi tace toh barin 'dan gyara maka gidan kafin ayi kiran sallah, hannunta Haidar ya riko yace " no way banaso ki wahalar mun da baby, ba Dr ya baki bed rest ba, turo baki ta 'danyi tace " am fine fah yaHaidar wllhi zan iyayi pls.
"Ok fine amma kar kiyi da yawa, kai ta gya'da sanda take rage doguwar rigar jikinta, wani mayen kallo Haidae yabita dashi, ganin yana kallonta yasata 'dan jin kunya zata wuce ya jawota jikinsa ya rungumeta ha'de da lumshe ido yace I love you Haneefah, I love you so much. A hankali ta zame jikinta jin zance na neman canza salo " yaHaidar kayi wankan kafin a kira sallah, murmishi yayi ya sunkuyo da kansa saitin cikinta ya soma magana da cikin" daddy's Champion kar momy ta wahalar mun da kai ko, oya hi five ya wani mi'ka hannu sai ka rantse da wani yake magana.... dariya Hanifa tayi tace" yaHaidar baijinka fah, Haidar ya dago ido yana dubanta yace wayagaya maki yana jina ina jinshi. "Murmushi ta kumayi snn tace" is it daddy's champion or daddy's princess tunda kace yana ji." Haidar yace both duka biyu ne a cikinki daddy's Champ and Princess....." Zaro ido Hanifa tayi tace tab twins fah rainon akwai wuya yaHaidar,
"Aike naki ma 'yan uku ne irin na mamy zakiyi bari ki gani, rufe fuskanta tayi ta wuce kitchen da sauri. Murmushi yayi ya mi'ke ya nufi bedroom 'dinsa.

"Tsaf ta share ko ina ta gyara, wani farin ciki da annashuwa maras misaltuwa take ji, 'dakin Haidar ta nufa ta shiga yare shi tsaf, wardrobe dinsa ta bu'de dan za'bo masa kayan da zai saka, tana bu'dewa tayi tozali da wnn pic din dake saman screen din laptop dinsa, 'daukan hoton tayi tana bi da kallo take taji 'kwalla ya ciko idanunta, murmushi tayi ta shiga shafa hoton da 'yan yatsunta, har Haidar ya fito daga bathroom bata ji fitowarsa ba, a hankali ya 'karaso ta bayanta ya rungumeta sai jin sanyin jikinsa tayi, tayi saurin juyowa ganinsa a haka yasta saurin runtse ido, murmushi yayi ya 'dan yarfa mata sauran ruwan dake hanunsa, zata zille ya ri'keta sosai ya 'dago hannayenta dake da ri'ke da pic din ya ha'da da hannayensa suna fuskanta pic din dukansu biyu kafin yace" kinsan su waye a pic 'din?
"Murmushi ta 'danyi tace" yeah na sani, by the right was my mum, and my Dad by the left andd and you at the middle holding a baby.
"Murmushi Haidar yayi kafin yace" and who was that baby?
"Dariya ta soma yi kafin tace I guess ni ce.... dariya shima yayi yace " yes kece matar Haidar, I was holding my beautiful wife ya manna mata kisss a kumatunta snn ya soma fa'din" Uncle Anty your beautiful baby has grown now, and she became a very beautiful lady with a good soul and lovely heart, and you know the most amazing thing ever, she's my wife and the mother of my future children and also the love of my life, and I promise I'll love her with all of my heart ,give her all the happiness that she deserves in life. Juyo da ita yayi

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

2 years ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment