Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gaske ba, Inna dake barci a 'daki a sittin ta fito tana tambayanta lafiya. Ganin leda ajiye gabanta da kanshin kajin da taji yasa Inna gane Haidar ne ya shigo, tambayan Hanifa ta soma, Zaki ne ko nasan shine kadai zai saki kuka cikin daren nan, kwanciya Hanifa tayi cinyar Inna taci gaba da aikin kuka. Haka Hanifa ta kusan kwana tana kukan Haidar yaki sakinta Inna na aikin rarrashi.

"Washe gari tex ya turawa mamy kan cewa ya wuce Lagos, dan Allah su yafe masa yasan beyi daidai ba, su yafe masa dan Allah amma ba zai iya sakin Hanifa ba. Koda mamy ta gama karanta text din sosai 'dan nata yabata tausayi, addu'an kariya ta masa afili da neman samun sau'ki a lamuransa. Abba kuwa sosai yayi fushi da Haidar abun har ba'a cewa komai.

*Lagos*
_Apapa(Maritime)_

"Dashike Friday ne ya iso lagos hakan yasa washi gari bai fita Office ba, koda ya kira Hanifa a waya kin dagawa tayi, daga nan ya kira mamy, mamy ta masa fada sosai ta nuna masa 'bacin ranta. Koda ya tambayeta Hanifa banza tayi dashi karshe ma ta katse kiran, Haidar ya dafe kansa yana addu'an samun mafita.

"Rananar Monday Yayi shirinsa tsaf cikin kakinsa masu gadi sai masa sannu da dawowa yake, wasu daga cikin cliques dinsa suka shiga basa updates abubuwan da suka faru sanda baya nan, duk yanda ya wuce sara masa kawai akeyi. Yana isa Office aka aiko Admiral na son ganim sa....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.....
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
60

"Paul yaci gaba da fadin "Sir idan bakayi gaggawan daukan mataki kan yaron nan ba toh ina me tabbatr maka yana gaf da ganin bayanka, ka duba dai ka gani yanda ya nuna maka yatsa a gaban kowa a gaban Recruits toh ina me tabbatae maka befor you knew it yaron nan ya kawar da kai daga mu'kaminka, ka duba komai yasa a gaba nasara yake gani, kowa yana ganin girmansa yana sonsa, da ace takara ake a samu matsayinka a navy da wann yaro ya fito da kowaye yake takara shi xai lashe. Babban misali kaga yanda kowa yaki sa hannu akan a kori yaron nan.
"Admiral ya fuzar da isaka zuciyansa na da'da tafarfasa da kalaman Paul yace "ai ina mai tabbatar maka I won't allow him to take me down, sai yanda 'karfi na ya 'kare, Paul yayi murmushi snn yace abunda na fada maka hakan kawai za'a yi a kawar dashi.
"Admiral yayi dariyan bosawa yace "da'dina da kai Paul akwai iya mugunta sai da'ki'kanci. Paul yayi dariya daidai nan ya mi'ke yana fa'din barin fita kafin ya iso.

"A floor din Admiral Haidar ya hadu da Paul, nan Paul ya sara masa ya shiga masa zartu da wuce waje. Sars masa kawai Haidar shima yayi snn ya wuce ha'di da ta'kaitaccen murmushi snn ya shige.
"A babban parlorn Admiral na ganawa da baki masinjan Naval Chief of Staff yayi masauki wa Haidar, jim ka'dan Admiral ya fito, Haidar ya mi'ke gamida sara masa, daga kansa kawai yayi snn ya 'karaso, gamida nuna wa Haidar kujera yace have a seat Captain, zama Haidar yayi sanda Admiral ya zauna a daya kujeran,
"Admiral yace " Captain Abubakar ka tafka babban laifi, ka tafi gida without permission, bayan kasan hukuncin hakan a dokar aikinka da kuma 'kasa baki 'daya.
"Haidar yayi gyaran murya snn yace " yeah I admit I did a mistake, I do apologies Sir. "Admiral ya ta'be baki yace, this is not an apology, idan zaka rubuto last ka rubuto later sai a gani ko za'a iya considering dinka.
"Ran Haidar ya 'dan sosu, ya mike yana gyara zanzaronsa kafin yace" I gotta get going sir, I have a lot to do at the office, the apology later will be on process.
"Har ya kai 'kofa Admiral ya tsaida shi, ba tare da ya juyo ba ya tsaya cak. Admiral ya 'karaso gabansa rai 'bace yake kallonsa ji yake kaman ya sha'kesa a nan ya mutu kowama ya huta. "Who do you think you are Captain Abubakar, who give you the right to leave, ban gama magana da kai ba ka mi'ke akaina kana ce mun you got a lot to do, and who cares, ba kai ka tara ma kanka aiki ba, let me warn you for the last time, kar na sake kiranka ina maka magana ka mi'ke kace zaka tafi.
"Murmushin takaici Haidar yayi yace " correction taken sir, now may I leave.
"Tsaki Admiral ya buga snn yace " ka bar latter din, ya miko masa wasu files yace ga wann, Haidar yabi takardun da kallo kafin ya kar'ba yana gani... Transfer aka masa daga Lagos zuwa Nija Delta, ya dago in a shock yana kallon Admiral, " Gyada masa kai Admiral yayi yace "yes zaka koma Nija Delta in the next two months. So za'bi ya rage naka ka za'ba cikin new Recruits wa'enda zaka tafi dasu ka masu training na ya'ki da terrorist din Nija Delta.
"Haidar ya bubbuga files din da hannunsa yana murmushi kafin yace " that will be even much better for me, on the contrary na jima ina son hakan ta kasance kodan hana satan man petur da wasu azzalumai keyi, ya dake sanda yake kallon cikin idon Naval chief of staff yace " Sir, am sorry to say, da ninake matsayinka da na jima da komawa Nija Delta, kodan tsaida doka da oda, amma kai ka tsaya anan iyakacinka Lagos, saboda kana son hole rayuwarka, ka tura wasu can suna maka sata suna fitar maka dasu 'kasashen waje, tun kwanaki da aka turani nayi destroying Ship dinka kayi uwa kayi ma'dauki kan a hana ni tafiya Nija Delta. Fine now the time jas come, yanzu ne zan ruguza duk wani 'kudirinka da shirinka na sata.... har ya juaya zai fice ya dawo yace afff, yana kallon yanda Admiral yayi mutuwan tsaye yana kallonsa yace " na manta ka zauna da zaman shirin binciken mituwan Former Chief of Staff, na samu good evidence kana da hanu dumu dumu a ci...... bai rufe baki ba Admiral ya sha'ko wuyansa yana huci da jin yanda Haidar yasan wnn 'boyeyyen sirrin nasa yace "Captaiiin how dear you. " Haidar ya fincike wuyansa daga ri'kon da Admiral ya masa yace " Let go of me you coward, ganina kawai kake yi, I promise you won't get away with all the crimes you had committed. Ya kada 'dan yatsan sa a fuskan Admiral kafin yace " this is just the beginning mark my words. Snn ya juya ya fice hade da banging 'kofar.
"Admiral kaman ya sha'ke kansa ya mutu haka yaji, he just couldn't believe it, wai Aliyi ke fa'da masa maganganu haka, yaronda yaushe ya gama training dinsa ashe har yayi girman da zaiga bayansa, waima ya akayi yasan wnn 'boyayye da'de'den sirri nasa, take zuciyansa ta shiga raya masa Latifa ce Latifa ce.
"A ranar Admiral baima gane me yake ciki a office ba gaba daya hankalinsa a tashe yake, lallai gwara yayi gaggawan kawar da Haidar kafin komai ya kwa'be masa.

"Yana isowa gida ya wuce 'dakin da ya kulleta ita da mahaifiyarta, tana zaune tana bawa mum dinta abinci a baki, Admiral ya banko 'kofan ya shigo, ta razana da ganin yanayinsa, tayi saurin matsawa jikin mum dinta ta rungumeta.
"A fusace ya jawo Latifa ta hanyar jawo gashinta, yana huci yake fadin me kika ce wa Aliyu, na tabbata kin shiga 'daki na kin bu'de safe dina ki saci documents, yaya akayi Aliyi yasan I was behind the death of Former Chief of Staff. ?.... "Zaro ido Latifa tayi ko kadan bata san cikin documents din data bawa Haidar akwai wnn ba, cike da tsoro da firgice take furta " Dad dama kaine ka kashe former chief of staff, hawaye ya shiga zarya a fuskanta tana fadin " kai wani irin maras imani ne dad, wani irin azzalumi ne kai, kaico na inama ni ba 'diyarka bace, ..... marin da ya sauke mata yasta yin shiru tana ci gaba da kuka.... " How dear you ke har kin isa ki tuhume ni ne, akan Ku'di babu abunda bazanyi ba, akan ku'di na mayar da uwarki haka, akan ku'di na mayar dake mistress dita, akan ku'di zanniya halaka koma waye ko yaya maysayinsa yake a wajena, kiyi hankali dani kinga yanda na 'daure ku keda uwarki a nan tsaf zan kashe ku idan asirina yayi gigin tonuwa, dama abunda yasa nake ragar maki dan bokana ya bani la'kani dake ne, dan haka ne careful, yayi jifa da kanta ta gwaru da garu snn ya fice, mum dinta kuwa hawaye ne kawai take iyayi bata um ba um um, Latifa ta tsuguna a wajen tana kuka me ysuma zuciya. Saida tayi mai isarta kafin ta 'karsa ta shiga gogewa mum dupinta hawayenta.
"Dago kan da zatayi ta hangi wayan dad dinta ya fadi, tayi saurin dauka t shiga diling mumbern Aliyu...

"Yana kwance yana duba takardu wayansa tayi 'kara, ganin mumbern Admiral ne yasa sa tashi zaune ya kurawa wayan ido, har ta kusa tsinkewa kaman bazai daga ba sai kuma ya daga.... jin muryan Latifa ce tana kuka yasa sa jan tsaki, har zai ajiye wayan tace " Aliyu ka taimaka mana pls Aliyu...... " dakatar da ita yayi cikin tsan tsan 'bacin rai yake fadin " kin kirane ki sake tricking dina da karyarki like you did before, com on tell me, ok wato kinga wancan did not work out shine bari ki sake shirya wani, you can't fool me again barin fada miki, kar ki damu wancanndinma kinyi succeeding kin raba ni da happiness dina da iyaye na, and you'll pay for It.... cikin ysan tsan kuka take fadin Aliyi dan Allah ka sairareni kajini pls..... ganin mutum akanta yasata yin tsit..... Haidar kuwanajin haka yayi ysaki yayi jifa da wayar yaci gaba da abu da yake yi.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
61

"Jawota dad dinta ya shiga yi a 'kasa yana wani huci yake fadin " do you really want to test my patience, ya mika mata wayan sanda ya kama gashin kanta wanda tsaban ja da yake yi har jijiyoyin kan sun kumbura snn oya go ahead go ahead call him back ki sanar dashi ni Admiral. Tanim Razak your Fucking Father zan kashe ki,
"Kuka kawai Latifa keyi tana fa'din pls let go of my hair, I beg of you pls. Jifa da ita yayi saida ta fasa goshinta. Juyawa yayi da niyan fita ya wani huci.... bai ankaraba yaji sau'kan flower verse a 'keyarsa Latifa ce ta lalla'ba ta 'dauka ta sau'ke masa.
"Abunka da soja wanda yasha training iri da kala, shafe wajen kawai yayi yaga jini..... wata murmushin mugunta yayi ya dawo yanda take..... " Idon Latifa ya 'ke'kashe cikin 'karfin hali take fadin, " Kai ba mahaifina bane, banida mahaifi, wllhi ban ta'ba ganin abun ysana abun 'kyama irinka ba in my whole life time, ka cuce ni ka zalunce ni,
"Latifaaaah ya daka mata tsawa, ko gizau bataji ba taci gaba da fadin " I dont fear you anymore, ka kasheni idan kaso, Alhamdulillah ko a yanzu na mutu na gode wa Allah da ya tsamo ni daga cikin ba'kin duhu zuwa haske, ta juya ta kalli mahaifiyarta dake dashe a wajen snn tace " ka zalunci baiwar Allah nan muma knn wayasan irin zaluncin dakayi wa sauran jama'a, kar ka manta Tanimu duniya ce wllhi ta ishe kowa riga da wondo, kar ka ga Allah ya barka kayita zalunci talala yake maka akwai rananr da zaka biya, ta 'daga hannu sama tace " Allah na ro'keka ka kawo mana nida mahaifiyata 'karshen zama a hanun wann azzalumin bawa naka, Allah na ro'keka kafin wnn bawa naka ya bar duniya Allah ka 'dai'daita shi ka 'kas'kanta shi....... Admiral bai iya jurewa yaci gaba da sauraren wnn addu'o'i na latifa ba ya kifa mata mari.... ya nausheta fa'duwa 'kasa da zatayi ta fa'di akan fashesshen kwalban flowern data jefeshi dashi, aikuwa nan ya huda mata ciki..... " Wani 'kara mai firgitarwa Mum dinta ta sake daga nan ta kwanta luf a wajen kaman bata motsi, 'karan da mum ta sake yasa guguwa ya kaure cikin dakin Lawo ya 'bullo.... " gaba daya Admiral ya rude ya razana da abunda yayi dan Latifa dai kam Allah ya kar'bi abunsa Allahu Akbar.....
"Dad ya shiga jijjiga ta yana fadin Latifa my daughter, meyasa kika mutu meyasa kika za'bi bijirewa umarni na ba da yanzu hakan bata faru ba.... dagosa Lawo yayi snn ya kwashe da wata dariya yace " Admiral. Tanim Razak ka kalli kanka yanda ka wani burkice da wnn 'yar taka mai taurin kan tsiya ta mace, mutuwanta shine rufin asirinka, mutuwanta shine zai maka maganin Aliyu, mutuwanta shine zai binne asirinka da yake gab da fitowa fili na kisan tsohon kwamandan rundunar sojin saman ruwa...... " hawayen taurin raine ke fitowa daga idon Admiral kafin yace Lawo fada mun, fada mun yaya mutuwanta zai zama solution to my problems.
"Lawo yayi wata dariyan basawa snn yace " yanzu kake magana soja, sharri zaka 'kulla wa yaron nan da gawarta shikenan, na baka clue saura ya rage maka ka shirya yanda abun zai kasance. "Kaman wanda ya sami ta'bin kai haka Admiral ya soma fashewa da dariya, har yana juyi a cikin dakin ya shafi kan Latifa yace " am sorry my dear daughter, mutuwanki ya zame mun gobarar titi a jos, ya kalli mum din Latifa yace wnn fah.
"Lawo yayi murmushi yace ka mance ka jima da aura mun ita, ai ranar daka ga wnn ta dawo hayyacinta to ranar asirinka ya tonu ko kuma na mutu.... " Admiral ya kuma fashewa da wata dariya yana jinjinawa Lawo.....

" 'Karfe 11:pm daidai ya gama shirin baccinsa, ya zauna gefen bedside yana kallon hoton Hanifa yana murmushi yana tuna rayuwar da sukayi a gidan tun daga farko har sanda incidence din da ya raba su ya faru, ya share kwallan da suka ciko idonsa, wani hoton ya dauko daga cikin wardrobe dinsa yana shafa mutanen jikin hoton, yake furta... " am sorry uncle am sorry Aunty, I couldn't make it, I have failed, but believe me I love your daughter more than anything in this world, I've a feelings zata haifa mun tagwaye masu kama daku, and I'll name them after you insha Allah.... ya rungume hoton ya furta I love you soo much. Ya jima yana tunanin rayuwa kafin ya dauko wayansa ya shiga neman layin Hanifa, ya kira yafi sau nawa bata daga ba... kasa hakura yayi ya shiga neman layin Anty Hiba dukda dare da ya dan ja....
"Anty Hiba ta razana da ganin wayan Haidar at this hour, ta tashe mijinta ta shiga nuna masa screen din wayan ganin sunan Haidar yasa sa duba agogo, gani yayi karfe 12 saura, shima dai ya dan razana amma kunsan maza ba kaman mata ba, nan yace mata ta daga taji ko lafiya,
"da kyar saida tayi addu'o'i kafin ta daga.... tana dagawa Haidar ya soma mata kuka nan fah hankalinta ya kuma tashi.... salati ta hau yi tana tambayansa meke faruwa.. " da kyar ya samu ya saita kansa kafin ya soma fa'din " Anty why all this, why is this happening, Anty I want her back I want her in my life, I became so miserable without her, why now Anty I couldn't help iy anymore...... " jikin Anty Hiba a sanyaye ta soma fadin " Haidar you need to calm down first idan kana so komai ya dawo maka normal, damuwan da kake yi haka is pointless bazai kara maka komai ba saidai ma ya kara frustrating dinka ya kara maka agony, pls Haidar you need to calm down, before you knw it zaka ji ana maka zance hawan jini sabida depression. Addu'a Haidar addu'a shine maganin komai, nayi niyan maka fada dan ina fushi da kai sabida abunda kayi dan mamy ta kirani and she told me everything, I was mad at you sosai Haidar amma yanda najika yanzu jikina ya mutu kasa bazan iya maka fadan ba, kasan ina sonka Haidar you're my best nephew and best friend, bansan meyasa yanzu kake boye mun abubuwa ba unlike before, idan abu ya shige maka duhu mukanyi magana muyi sorting out, sabida kusan age mates muke, na maka uzuri kai namiji ne ni mace ce na sani as time goes on wataran shakuwan mu zata ragu, but Haidar when it comes to matsala irin haka we need to discuss it before you does something, yeah quite alright nasani Hanifa matarka ce you've every right for her, amma ba ta haka ya kamata kazo mata ba, you'll end up running everything, kaga yanzu duka suna fushi dakai, Abba mamy Inna dakuma Hanifan,
" Murya 'kasa Haidar yace " Anty I admit, I made a mistake but ya kamata su understanding dina I was so desperate, snn su suka da'da sani nayi haka, cewa suke wai sai na saketa, Anty kinsani ever since we were kids, mafarki na shine na zama *Mijin Haneefah* kinsan the last abunda zan iya a rayuwata knn na saki Hanifa. Yanzu dai dan Allah kimin favor daya.
"Anty Hiba ta sauke ajiyan zuciya tace na fahimce ka Haidar, yanzu wani favor kake so na maka.
"Yauwa my best, so nake ki dauko Hanifa ta danyi hutu a wajenki, saboda ta 'dan mance da duk wani hard time that she's going through. Nasan zaiyi wuya ta kuma amincewa dani but with zata gane am the man of her dream, and zatafi zama more company a tareda ke,
"Anty Hiba tace I was thinking of that too, yanzu dai zanje kanon na samu su mamy da Abba insha Allah.
"Yauwa my Anty that's why I always love you, you always understand me. Pls Anty idan kina tare da ita help me persuade her ta yafemun and and.... ta dawo muyi zaman auren mu..
"Taa'kaitacen dariya Anty Hiba tayi tace " Haidar knn *Mijin Haneefah*
"Dariya shima yadan yi yace " wato kin tuno sunan tsokanar da kike kirana dashi then knn,
"Eh mana a lokacin idan na fada sai munyi fada.
"Yanzu kam ki fa'da ki sake fa'da saidai na maiki kyauta ma, ni yanzu zan kara a suna na ma, " Captain AA *Mijin Haneefah*....
"Dariya Anty tayi tace Silly you...
"Toh my Anty na gode sosai, ki gaida Faruq pls na tasar masa mata cikin midnight din nan..... dariya tayi tace zaka sani ai Haidar sai na hadaka da inna kasan itace maganinka.... dariya shima yayi yace ai tana daya daga cikin dalilin da yasa nake so ki dauko Haneefah kar ta koya mata masifa.... dariya Anty Hiba tayi ta tambeyasa aiki daga nan shima ya tambayi Ajmal yace ta shafa masa kansa little soldier kafin sukayi sallama.
"Sosai Haidar yaji dadin a ransa at least yanzu zai dan samu peace of mind, cikin jin dadi yayi kwanciyarsa yana mai tuno kyakkywan fuskar matarsa.

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
62

" 'Karfe 8:01am daidai ya fito cikin shirin fita office, as usual yana sanye cikin farar kakinsa yayi kyau sosai, da mamaki yake kallon motan Latifa dake pake can gefe, ta'be baki yayi a ransa yace kome ya kawota nan this early morning kuma oho, cikin ko in kula yaci gaba da tadiyarsa sanda yake danna security lock daga jikin key dinsa ya bude motar, a haka ya karasa parking lot ya shige yayi tafiyarsa, masu gadi na faman gaishesa.

"Asubanci Anty Hiba tayi ta dira a garin KN, bata wani sha wahala ba wajen amimcewan su Abba, hasalima sunji dadin hakan, Hanifah ma hakan yafi mata sauki, tunda kullum ita kadai ke wuni Sumy na zuwa sch sai ko Inna, mamy kam tun bayan abunda ya shiga tsakaninta da yaHaidar wani irin kunyan mamy takeji, duk wani shwagwa'ba da take mata a da yanzu ta rage, sosai take jin nauyinta, ita kanta mamy ta gane hakan, kasancewar Kaduna da Kano ba wani tafiya me nisa bane yasa suka juya Kaduna a ranan, Hanifa sai dauki take Sumy ma ta waya sukayi bankwana.

" 'Karfe 4:00pm ya gama duk wani abumda zaiyi a Office ya tarkasa ya nufo downstairs, Captain Paul da Admiral ya hanga daga can suna tattaunawa, daga nesa Paul ya dago masa hannu yana sara masa, murmushi Haidar yayi ya jefa masa yarensu na sojoji, ko kallo Admiral bai ishe Haidar ba ya shige motarsa ya bar wajen, Paul ya sheke da wata dariya yace I pity your life navy.... Admiral yayi wata mirmushi kafin yace yanzu zai gane ba'a ja da babba a waje, Paul are you sure kunyi aikin nan da kyau, paul yace haba sir ko ka mance ni na halaka chief of staff balle wani Haidar karamin kwaro, ai kawai yana isa soldiers zasu bi bayansa a bincike sa,.
"Admiral yayi dariya yace" Captain AA this is your end. Paul ya sheke da dariya ya sara ma Admiral, daga na suka wuce paul na binsa a baya kafin cheif security dinsa ya karaso yana sara masa.

"Saida ya biya wani store ya danyi minor shopping dangin su coffee da sauransu kafinnya nufo gida.... " Tun daga Main gate yaga navys kota ina an kewaye, fannin en securities, sosai abun ya basa mamaki kafin kaga haka sai wani gagarumin abu ya faru, bai gama shan mamaki ba saida ya iso cikin building dinsu dan ko ina securities ne ana bincike, yana gama parking ya fito.... " Daga nesa Admiral ya fara nunasa cikin zafin rai ga hawaye na bin kuncinsa yake fadin, there he is, arrest him, arrest him he's a murder, he killed her he killed my only daughter..... gaba daya Haidar be fahimci abunda Admiral ke fada ba, ganin Admiral gadan gadan ya nufosa yasa akayi arresting Haidar " you're under arrest sir..... " da mamaki Haidar ke binsu da kallo kafin yace, what do you mean I'm under arrest, this is ridiculous, out of my way. 'Kin matsawa sukayi saima dada arresting dinsa da sukayi daya daga ciki yace " muna zarginka da kisan 'yar Admiral ta baro hida jiya da daddare ta taho gidanka kwana, " tsaki Haidar ya buga snn yace thus is nonsense, will stop this stupid acquisition, "bindiga ya daura a 'keyar Haidar yace "am sorry Sir, but we need to check in your house..... " securitin ya shiga dagawa sauran hannu yana fadin " let's ho in... Haidar baice komai ba ya hangi Admiral yana tsaye can gefe an daddafesa, girgiza kai yayi yasaka key ya bude gidansa, nan aka shiga bincike ta ko ina, har sun fito suna girgiza kai ba komai, dayan yace " are you sure you search everywhere, no Sir except the bathroom,

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

2 years ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment