Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

suna fuskanta juna kafin yace" Haneefah my love, will you be mine forever. ?..... Rungumesa tayi hawaye na bin 'kuncinta... "Haidar ya shiga shafa bayanta yana fa'din" it's okay Beautiful, I don't wanna see those tears, a hankali ta kwanta luff cikin 'kirjinsa, sun jima a haka kafin zance ya soma canzawa, hannayensa yasa ya soma zame rigar jikinta at the same time yana romancing 'dinta, kuka ta kuma saka masa.... Haidar ya 'dago kai da 'kyar a galabaice yaka fa'din" pls Hanee don't say no, I've the right, remember I missed you Beautiful pls ki bari mu raya wnn daren, I promise you'll be the most happiest woman on the entire universe, I love you Haneefah, my dream is to be with you, pls don't neglect me.
"A hankali ta soma saka rigarta kafin tace "pls yaHaidar this is not the right time, su mamy na jiranmu, they might get worried. Kanta a 'kasa ta fice zuwa parlor. Kallo Haidar yabita dashi har ta fice. Da 'kyar ya mi'ke ya nufi bathroom room ya kintsa jikinsa snn ya dauro alola dan already magrib tayi. Yana fitowa ya shirya tsaf cikin navy blue shirt na Amany da black jeans sai ya fito ras dashi, sallah ya tayar bayan ya gama shkryawa.
"Itama sallan tayi a 'dakinta bayan ta gama dafa masu simple food, sanda Haidar ya fito tana dinning area tana hada su plate, kallonsa tayi ya mata kyau sosai, fuskansa babu yabo babu fallasa ya 'karasa ya 'dauki car keys saman center table, Hanifa na murmushi tace yaHaidar dinner is ready, let's have dinner together before I leave.
"Murmushi ya 'danyi kafin yace" no don't mind am not yet hungry, muje nayi dropping 'dinki first, jikinta ya 'danyi sanyi ta bisa da kallo ganin har ya nufi kofa. A sanyaye ta mi'ke ta dauki mayafin ta ta biyo bayansa.
"Suna 'karasowa jikin mota ya bita da kallo dan gaba daya mood dinta ya canza, hancinta ya 'danja kafin yace" why the long face... turo baki tayi tace ba kaine na maka girki ka'ki ci ba, murmushi Haidar yayi yace" duk akan haka ne aka 'bata wnn beautiful face din, Okay fine, I promise da zaran na dawo zanci. " langa'be kai tayi tana dubansa tace promise? Fuskanta ya shafa da hannunsa yace yeah promise. So shall we.
"Murmushi itama tayi snn ya bude mata motan ta shige, ya zagayo driver seat ya zauna. Suna isowa Hotel din ya bude mata lock bayan ya gama parking, juyowa tayi tana dubansa in a guilty conscious da 'kyar ta iya furta " are you mad at me?
"Kallonta yayi bece komai ba, ta sakala yatsunsu cikin na juna tace" am sorry pls kaji yaHaidar,
"Murmushi yayi snn yace" take care of your self and our unborn for me, okay, ya manna mata peck a goshi yace "I love you Beautiful, kafin ku wuce gobe zan shigo insha Allah, ki gaidasu mamy. Jiki a sanyaye ta amsa da ameen kafin ta bu'de kofan ta fice, har saida yaga shigewarta kafin ya tada motar ya bar wajen.

"Tana shigowa wajen su Sumy ta nufa, aiko suna ganinta suka saka ta gaba da zolaya, Sady tace " Oh ai mun 'dauka kin 'kaura tacan ne, Hanifa ta galla mata harara tace "you started ba, wllhi zan hadaki da yaHaidar ne.
"Sady na dariya tace da'din abun de nima mijina soja ne ya dake ni zai rama mun. Sumy dai banda dariya bata komai, Inna ce ta shigo ta dubi Hanifa tace ke kuma daga rakiya waje saiki bi miji..... "Oh innnnaaa zakisa Sady ta ci gaba da zolayata, Inna ta ya'be baki tace" yo ai gaskiya na fadi, ko dayake ke gwara ki ma'kale wa mijinki kar 'kadangarun bariki su kwace maki shi... Aiko gaba daya suka sa dariya, Inna ta wuce ta barsu sunata faman labarin ana dariya. "Sumy tace wuuuh Shema you missing a lot, Sad tace bari a kirata ayi vid call. Nan suka kira Shema aka hau zuba surutu, Shema kaman tayi tsuntsu haka taji.
"Sumy ta kalli Hanifa tace, baby sis yanzu fa kece big sis, Sady tace "wah she's always be our lil sis kar kisa kanta ya girma, harara Hanifa ta galla mata tace " you're annoying sady ta dau pillow ta jifa mata. Sady dariya kaman cikinta zaiyi yaya tace" aff na mance 'dazu Abba ya aiko kije aka ce kinbi yaHaidar.... "Zaro ido Hanifa tayi tace" Dan Allah, wayyo na shiga uku, dan Allah da gaske kuke..... Sumy na dariya tace don't mind her momyn 'yan hudu 'karya take maki,.... "sauke numfashi tayi tace har kin razana ni wllhi.
"Ta'be baki Sady tayi tace toh wai miye dan kinbi mijinki sekace ba wayis ba nifa bana son irin haka, Hanifa tace tabb wllhi kunyan Abba da mamy nake. "Uhm su in laws ba Sady tace.
"Sai snn magana Sumy ya dawo wa Hanifa tace wai kikace momyn en hudu, ki rufa mun asiri pls ni guda daya ne a cikina, kinaji mamy tpna fa'dan irin wahalan da tayi daku uku ma knn balle har hudu.
"Sady tace ni banson ragwanci miye a ciki, ni biyar ma nake maki fata harara Hanifa ta galla mata tace" thunder go fir your mouth, idan na haifa biyar duk raba maku zanyi ai, gana daya suka sa dariya haka sukci gaba da hiransu gwanin sha'awa,....

๐Ÿ‘ธ๐ŸปQueen Samy๐Ÿ˜๐Ÿ’„๐Ÿ’‹........
[5/21, 10:33 PM] ๐ŸŒน Muhammad๐ŸŒบkabeer๐ŸŒน: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน *Mijin Haneefah*๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
78

"Washe gari Haidar da wuri yazo sukayi sallama dasu Abba sauri sauri ya wuce don yanada appointment da chief of defense, sanda yazo Hanifa na barci dan haka bai samu sukayi sallama ba koda ta tashi sosai taji haushin hakan, Aisar da Sameer kuwa har airport suka rakasu da al'kawarin zasu je masu soon."'karfe 10:00am daidai jirginsu ta 'daga zuwa KN.

"Tun bayan dawowansu Kano kullum sai tayi waya da yaHaidar, babu dare babu rana kullum suna ma'kale da juna a waya, wani sa'in yasata gaba sai ta turo masa pic 'din cikinta waiga girman da ya 'kara lol.
"Babu wanda yasan Haidar na gini a Kano, yana can Lag amma ginin sa yayi nisa sosai a Kano, gida meji da kyau da tsari, yaso zuwa Kano amma aiki ya masa yawa yanzu yau shine Port Harcourt gobe shine 'kasashen 'ketere, wnn aiki da Haidar yayi akan Admiral ba 'karamin girma da marta ba ya samu ba daga wajen 'yan uwansa sojoji kai harma da mai girma shugaban 'kasa.
"Aisar da Sameer sunzo har sau biyu sun zazzaga dangi, Sadaki da lefe duk an kawo rann biki kawai ake jira a ra'kashe ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป, Inna da mamy sosai suke bawa Hanifa kulawa na mussaman, a halin yanzu cikinta ya shiga wata na biyar girmansa kuwa saikace cikin wata bakwai, ta 'dan 'kara 'kiba sai ta 'dan yi duhu kuma.

"Yau ta kama sauran sati uku biki tana zaune tana cin manda'ko da Inna tayi mata a parlorn mamy kaman daga sama tajiyo sallaman sa, daskarewa tayi tana kallonsa cikin kakinsa yayi matukar kyau ,tabbas shine ba gizo yake mata ba, murmushinsa me tsada ya sakar mata sanda yake shigowa, kasa ce masa komai tayi sai kallonsa da take babu ko 'kyafta ido, ya 'kara kyau sosai harda 'dan 'kiba yayi,
"Karasowa yayi ya zauna gefenta ha'de da rungumo kanta cikin 'kirjinsa yace I missed you Beautiful, ya kuke and my baby, ya sunkuyo da kansa saitin cikin yana mamakin yanda cikin ya girma sosai, kiss ya manna wa cikin kafin yace" Oh Champ and Princess daddy is here, you know what guyz I missed you so much.... "Hanifa de kallonsa kawai take, 'dago kansa yayi yana dubanta kafin yace" Beautiful kin 'kara kyau I love you, cikin nan ya maki kyau sosai tashi muga yanda ya maki.
"Bata tashi ba sai ta'be baki datayi, kallonta shima yayi kafin yace" wait aren't you suppose to be happy, ko baki murnan zuwan nawa ne uhum Beautiful. Com on tell me waya ta'ba mun ke ya fa'di yana ri'ko 'yan yatsunta.
"Baki a ture tace " toh ba kaine ba all these while ka'ki zuwa sai yanzu, and daka tashi zuwa koma kace mun kana hanya. "Haidar ya rungumeta cikin 'kirjinsa yana fa'din" Oh am sorry Beautiful I just wanted to surprise you, that's why ban fa'da maki ba, am sorry pls kinji, rashin zuwana kuma aikine ya min yawa Beautiful, nike ri'ke da mtsayin Acting Admiral kafin a saka sabo shiyasa ban samun time yanzu, commitments sunmin yawa Beautiful, yanzu ma zamewa ma ayyuka nayi na taho all the way just to see my Beautiful wife,.... zatayi magana ya zura harshensa cikin bakinta..... sosai yake kissing dinta gaba daya jikinsa 'bari yake lallai yayi missing Beautiful dinsa, gaba daya ya mance a parlorn mamy suke.... " ko kadan basuji 'karan foot step din mamy dake saukowa daga bene ba.... "Hanifa nata kiciniyan 'kwace kanta, "mamy kam sosai taji kunyan ganinsu a haka, da sauri tayi niyyan juyawa karaf sukayi ido hudu da Haidar, matsawa baya yayi yana shafa kai" Mamy sannu da sau'kowa, dole mamy ta amsa masa snn taci gaba da saukowa, Hanifa kuwa kaman 'kasa ya tsage ta shige ciki haka taji. Wani irin kunya ne ya mamayeta.
"Haidar saukan yaushe, mamy ta tambaya.
"Yanzunann shigowata mamy, mun sameku lafiya, nan suka soma gaisawa da mamy. Mamy tace yaya da zuwa kwatsam babu notice. Ko ka sanar wa matanka da zuwan naka ne.
"Haidar ya 'dan kalli Hamifa daketa juya manda'kon dake hanunta ta kasa 'dago ido, yana murmushi yana kallon Hanifa yace a'a mamy kawai ina so na nayi surprising dinku ne. Mamy tace toh ya aiki" Mamy akwai aiki fa sai godiya, Toh Allah ya taimaka, ameen mamy.
"Mamy ta kalli Hanifa ta 'bace shiru kaman bata wajen tace" Daughter ko a 'karo maki mand'konne, Hanifa ta girgiza kai tace a'a mamy na 'koshima ta mi'ke tayi hanyan kitchen...."Haidar ya bita da kallo har ta shige snn ya dawo da dubansa ga mamy yace " Mamy pls wake bata such kind of food,
"Harara mamy ta galla masa kafin tace" abunda take so ai shi za'a bata ban son iyayi. Haidar ya wani marairaice fuska yace but mamy gani nake kaman it will affect the baby, ki gani fah...
"Banson sakarci dankalin hausa nefa ba wani abu ba, murmushi Haidar ya dan yi ya mike yana fadin mamy barin 'karasa nagaida Inna . Mamy tace bazaka ci abinci first ba, no mamy Hanifa ta kawo mun side dina. Daga haka ya fice.
"Hanifa kuwa kasa fitowa tayi daga kitchen gaba daya kunyan mamy take ji sosai, a kitchen mamy ta sameta tsaye, mamy ta kalleta cikeda kulawa tace daughter akwai wani abu ne ko bakijin da'di ne, Hanifa ta 'dan sunne kanta tace a'a mamy lafiyata lou barin duba Sumy...." mamy tace ok ki kirara ku ha'da abincin Haidar sai ki kai masa sasnensa. Hanifa ta amsa da toh mamy snn ta wuce.

"Sanda tayi knocking a 'kofan ya gama shirinsa tsaf knn cikin 'kanan kaya, kallo 'daya ta masa ta sunkuyar da kanta he's always handsome, kallonta yake yanda take tafiya ri'ke da tray din kaman ya mata nauyi, da sauri ya 'karasa ya karbi tray din yana kallonta yace" sannu maman en uku, harara ta galla masa kawai ta 'karasa zata zauna ya wani saurin ri'keta kaman me tsoron kar ta fa'di.... abun saida ya bata dariya. Shima zama yayi gefenta yana binta da mayen kallo, gani yayi duk ranta kaman a 'bace yake.
"Wai ni Beautiful me nayi ne, mutum yazo yau amma ko special tarba bazai samu ba, haba mana, if I'm not welcome ne fine sai nayi tafiyata.
"Hararansa ta kuma kafin tace" oh baka masan abunda kamun 'dazu a parlorn mamy ba koh,..... kan tayi shiru Haidar ya soma dariya yana fa'din" Ai ita kanta mamy tasan nayi 'ko'kari nayi kewan matata, kinga yanzu idan nace zan tafi dake she won't prevent me.... kallonsa Hanifa tayi galala kafin tace" ina zan iya zuwa da wnn cikin kasan ma bazasu bari ba, ni kaina bazan iya zuwa ko ina ba. Haidar ya dan saka fuska kafin yace" ni kuma sai a maidani gauron dole knn, I just couldn't help it anymore, ya rungumota cikin jikinsa sanda yake fa'din Hanee I need you by my side, I want us to be together. A hankali ta zame jikinta tace should I serve you,
"Of course sure, ya fa'di yana gyara zama, ta gama serving dinsa ta mike zata fice, hannunta ya ri'ko yace ban gane miji na cin abinci matansa zata fita ba, na koya maki logic din, the moment mijinki na cin abinci yana kallon beautiful face dinki, soyayanki ne ke 'kara shigansa, so you are not going anywhere until I'm done,
"Yana cin abincin suna hira, saida ya 'koshi sosai, da kyar ya bar Hanifa ta fito daga sashensa. Bacci yayi bashi ya farka ba sai wajejen bayan la'asar, sallah kawai yayi ya fito dan yasan Abba ya dawo.

"Zaune ya samu iyayen nasa a parlorn Abba, gaisawa sukayi Abba ya masa sannu da hanya, nan suka tattauna gameda bikin 'kannensa da ya rage saura sati uku, nan Haidar ma ya shaida wa iyayen nasa ginin da yayi a GRA sosai sukaji da'din haka, Abba yace zasu je su gani insha Allah. Sun jima suna hira kafin Haidar ya fice.

**************************
" Washe gari da yamma yasa Hanifa ta shirya suje wani waje, babu yanda batayi ya fa'da mata yanda zasuje ba ya'ki fir 'karshe cemata yayi gidansu Saif zasu je. Da murnan ta ta shirya Sumy da Inna har na zolayanta, wai tunda Haidar ya dawo an soma ganin fari'anta, bata tanka su ba har ta gama shirinta cikin dohuwar rigar atampa flay ba wani makeup tayi sosai ba amma tayi kyau, ta fito ras da ita.... sashen mamy ta nufa ta fada mata sun tafi gidan Shema da yaHaidar, mamy tace a dawo lafiya snn Hanifa ta fito ta sami Haidar a parking lot.
"Tun daga nesa Haidar ke binta da kallo ta masa kyau sosai cikin nata ya mata kayu a jikinta 'das dashi. Da kansa ya bude mata marfin motan suka soma tafiya.

"Sosai Shema da Saif sukayi murnan ganinsu, Saif sai masa tsiya yake, Shema kuwa jan Hanifa tayu suka shige ciki, sun dan jima suna hira kafin Haidar ya mata waya ta fito su tafi, badan Shema taso ba haka ta rakota har waje.
"Ganin sun 'dau wani hanya daban yasa Hanifa cewa yaHaidar ina muka nufa,
"Saidake zanyi ya bata amsa,
"murmushi kawai tayi bata kuma cewa komai ba, kallonta Haidar ya 'danyi kafin yace "ko zaki driving dinmu ne.
"Girgiza masa kai kawai tayi batare da tace komai ba.
"Haidar yace "Beautiful banson shir shirunkin nan fa, open your mouth and talk, nidake fa we're one. Ko my champion da princess ne ke hanaki magana.
"Dariya kawai tayi sanda yake horn a wani makeken gida wanda basi an fada maka na alfarma ne, me gadi ne ya wangale gate Haidar ya rage glass suka gaisa..
"Hanifa sai bin gidan take da kallo, da gani sabo ne ga flowers ta ko ina, Haidar ya gama parking ya dubeta yace muje ko, ko bazki iya takawa bane na 'dauke ki...
"Kai yaHaidar stop being silly. Ta sa 'ka ta sau'ko tana fa'din ina muka zo yaHaidar, 'karasa yayi jikin 'kofa yasa mabu'di ya bu'de, baice mata komai ba sa suranta da yayi ya nufi cikin gidan da ita.
"Ya salam, ai har interior din yafi wajen, komai 'das 'das gwanin sha'awa dagani furniture din zakasan komai order dinsu akayi.
"Ajiyeta yayi bisa sofa, ya ha'de hannyayensa yana dubanta kafin yace" Mrs Aliyu, take a look of polishing and tell me if there is anything da bai maki ba ko kina so a canza,
"Da mami take kallonsa kafin tace" ban gane ba yaHaidar nan 'din inane.
"Haidar ya mi'ke yana murmushi kafin yace" this is your house, everything here is yours including me my self.
"Murmushi ta soma ta mi'ke ta rungumesa tace" yaHaidar zamu zauna a nan Kano knn, oh am so so glad, this is spectacular, thank you yaHaidar.
"Kiss ya manna mata kafin yace anything for you love, ya rungumeta cikin jikinsa yace kinfi so mu zauna a nan ne? Gyada masa kai tayi tana kwance cikin jikinsa. Shafa gashin kanta yake snn yace" Beautiful yanayin aikina bazai bari mu zauna a nan ba saidai mu riga zuwa hutu.
"Ta 'dan bata fuska tace nidai ka barni a nan.
"Beautiful bazan iya jure rashinki ba, I promise you zamu ringa zuwa hutu akai akai, kinji, ko kinaso nayi retire ne... " A hankali ta girgiza kai alamun a'a, ya wani da'da kwantar da kanta cikin 'kirjinsa yace" idan kinaso sai nayi, your happiness is mine. Oya tashi muje kiga gidanki ko, ri'kota yayi cikin arm dinsa suka soma zagaye ko ina a gidan.

"Three bedrooms ne a asama snn akwai guests room a 'kasa, sai kitchen da mamakeken parlor with dinning area, sosai gidan ya burgeta babu wani shirgi ko ina an sama masa abunda ya dace dashi, daga waje kuwa har jim akwai sai wasu kujeru na sha'atawa, ganin hard playground na yara a gidan yasa Hanifa jin da'di sosai, lallai Haidar zai kasance irin iyaye masu son farin cikin yaransu. Sunzaga ko ina kafin suka dawo cikin gidan.
"Har akayi magrib suna nan, sanda ya dawo daga masallaci zaune ya sameta a 'dakin dake a matsayin nata ta idda sallah, zama yayi hefenta ya shiga ya soma yaye mayafin jikinta.... ta dago kai tana dubansa bata ankara ba saiji tayi ya soma kissing dinta sosai, daga yanda yake sarrafata zaka gane yana tsananin bu'katarta, itako Hanifa ko ka'dan batason shiga irin wnn yanayi, batasan ko cikinne kesata haka ba oho.... turesa ta soma yi tana 'ko'karin 'kwace kanta.... "matseta Haidar yayi cikin jikinsa har saida ya tuna da lular dake jikinta na ciki kafin ya 'dan sassauta ri'kon ya soma fa'din " pls Hanee, don't I beg of you, can't you see am dying to be with you. Kuka ta sake masa jinnyanda yake juyata.
"'Dago idanunsa yayi wanda suka koma jazur kafin yace" ki daina kuka bazan sake ba tunda baki so, but inso ki sani nima mutum ne kaman kowa I also have feelings yeah, ke ka'daice matata kece hakki ya rataya a wuyanki ki sau'ke wnn nauyin, remember I came here for you, na baro tarin ayyuka na ne dan nazo na ganki naji matsalollinki a matsayinki na matata, na sani yau da zan koma bin mata bazaki so ba, kodayake ba sona kike ba shiyasa baki damu da bu'katata ba, you were forced to be with me, ki sani Haneefah I love you with each and every breath, and I will love till my last breath. But I won't force you yo love me back, all I know is that I do love you. Snn idan kince kar na sake kusantar ki zanyi as you wish if that will make you happy, oya tashi mu tafi.... ya mike yana gyara rigarsa.
"A sanyaye ta mi'ke tana share hawayen idonta ta biyosa waje, ko sallama da gate man Haidar beyi ba, yana daga masa hannu ya fice a guje. "Haka suke tafiya cikin motan babu me cewa 'kala.

"Yana gama parking ya bude motan ya fito ko kallo bata ishe sa ba, jiki a sanyaye ta sauko, ba tare da ya juyo ba ya danna security lock daga jikin key.

"Parlorn mamy ta wuce kai tsaye, mamy na ganinta tace kun dawo daughter, kai ta gyda wa mamy tace eh mum dawo mamy suna gaishe ku snn ta karaso ta zauna bisa sofa, zamanta yayi daidai ta shigowan sumy dan dama ta ganta waje tare da telansu, zama Sumy tyi tana mitan wai Sady ta barta da komai ta'ki dawowa. Mamy tace toh zata bar karatunne tozo ta maki me, idan hidiman bikin ne ba gaki a gari ba ke sai ki maku komai ai, tinda tace sai week din bikin ta dawo, Sumy ta dan turo baki tace wllhi mamy da nice Sady fah bazata mun haka ba, Mamy tace ban son shashancin banza idan bakuyi wa 'yan uwanku abu ba ma waye zakuyi. Am sorry mamy Sumy ta fadi a hankali, mamy kam mikewa tayi ta shige t
amsa wayanta dake ringing.
"Hanif dai jinsu kawai take amma hankalinta gaba daya baya tareda ita yana can wajen Haidar...." Sumy ta 'dan ta'ba ta tace maman en 4 na mashi maganan 'dinkin ankonki nace gown za'a maki dan kar ya kasa, inaaa Hanifa kam jin Sumy kawai take amma da alama bata fahimtan me take cewa, 'karshe mi'kewa tayi ta nufi sama,.. "Sumy ta bita da kallo dan tasan definitely wani abun na damunta.

"Basu kuma haduwa da Haidar ba har ta kwanta, ranar gaba daya kasa bacci tayi tana tunanin yaHaidar, ji take bata kyauta masa ba, gaba daya saitaji babu da'di ta k'udiri niyyan bazata sake hanasa kanta ba.
"A 'bangaren Haidar kuwa sosai abun ya damesa, meyasa Hanifa take masa haka, shi a halin yanzu babu macen da yake sin kasancewa da ita sai ita, wata zuciya tace kila bata sonka ne shiyasa taje maka haka tunda bata ta'ba furta maka kalman so ba, take yaji zuciyansa na masa zafi sosai, hukumcin da yanke yafi masa gwara ma kawai ya tafi zaifi samun sau'ki.

"Washe gari wajejen 'karfe 9 saura ya shigo sashen mamy " a 'daki ya smu mamy alamun shigowarta knn itama, mamy ta dubesa da mamaki ganin sa cikin shiri,
"Haidar badai tafiya ba, gaisawa sukayi da mamy kafin yace eh mamy zan wuce dama kwana biyu kawai zanyi, Hanifa da tun shigowarsa ta tashi amma bata bu'de ido ba taji gabanta yayi mugun fa'duwa wanda yasa har abin dake cikinta ya motsa,
"Mamy tace Abbanka ya sani.
"Eh munyi sallama jiya da dare, ya 'karashe maganar yana duban Hanifa dake kwance bisa gado idonta alumshe.
"Mamy ta dune shi ganin yana kallon Hanifa tace" gashi Hanifa na bacci kuma, ko zaka jira ta tashi ne, ko zakaui missing flight ne.
"No mamy karki damu ai mun riga munyi sallama jiya...... "Innalillaji wa inna'ilaihirraji'un haka Hanifa tace a zuciyanta, kardai yaHaidar yayi fushi da ita sosai, wayyo Allahn ta meyasa zai tafi.
"Mamy tace toh bikin fah zaka samu zuwa inji de.
"Ya 'dan dubi agogon hannunsa kafin yace" Mamy gaskiya zuwan nawa is under probability am not quite sure idan zan samu zuwa.
"Haba Haidar ya kamata kayi squeezing kazo ko dan Sameer da Aisar.
"Ok mamy insha Allah zan duba lamarin. Ni na wuce.
"Toh Allah ya tsareko, ka shiga ku sake sallama da Abban naka bai fice ba tukunna. Haidar ya amsa da toh mamy kafin ya fice.

"A hankali Hanifah ta shigar da kanta cikin bargo hawaye na sau'ka bisa 'kuncinta, wani irin son mijinta take ji maras misaltuwa, ji take kaman ta ri'ko shi ta hanasa ta fiya, gashi ko sallama basuyi ba, tana jin fitan mamy ta soma kukan da gaske, 'karshe toilet ta shige tayi me isanta....

๐Ÿ‘ธ๐ŸปQueen Samy๐Ÿ˜๐Ÿ’„๐Ÿ’‹........
[5/21, 10:33
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment