Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk ya rasa wanne zeyi gashi shine me jahorantar tafiyan. Idan kaga Haidar dole ka lira da raman da yayi. Ana gobe zaiyi tafiyan ya kirs wayan Hanifa. Tana ganin my handsome ne ta dauka cike da murna.

"Hello, Beautiful.
"Hello Handsome.
"Beautiful how you and our unborn doing .
"Am doing great, ya aiki.
"Alhamdulillah, but am damn missing you, I just couldn't help it.
"Murmushi tayi tace" same here yaHaidar, ina missing sweet luv dinka.
"Kar ki damu Beautiful we will soon be together, zan tafi Turkey gobe but ba jimawa zanyi ba just a couple of days kawai zanyi na dawo, bazanfi 5 days ba at most. Kin yarda naje Beautiful.
"Dariys me sauti tayi kafin tace" don't be ridiculous Handsome,Allah ya kaiku lafiya ya dawo mun da kai lafiya. promise me da zaran ka dawo zaka zo mun.
"Murmushi shima yayi kafin yace "you have my word ina dawowa ke zan fars zuwa na gani insha Allah. Kisses to you..... ya fadi kafin sukayi sallama.....

_Manage this ba yawa_

*Sorry for the late post, you guys should bear with me pls, am quite busy ne this dayz insha Allah book yazo 'karshe, Taku har kullum Queen Samy🌹💋.*

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
81


"Tunda Haidar ya tafi sau biyu sukayi waya, kasancewar island 'din dasuke gudanar da Exercise 'din a 'kasar Turkey birnin Izmir babu enough service a wajen an ke'be wajen ne kawai mussaman dan horar da 'kwararrun sojoji musamman sojin ruwa.
"Hankalin Haidar duk baya jikinsa ya 'kagu su gama gudanar da wnn Exercise din su koma gida, Aisar ne ya hangosa zaune saman wani reshen wata bishiya data sau'ko 'kasa, 'karasowa Aisar yayi gamida sara masa kafin yace" Sir may I seat.... "Kallonsa kawai Haidar yayi dan gaba 'daya baya fahimtarsa, gajeren tsaki Haidar yayi yace" Whatever kana iya zama, wai wnn girman da kake wani bani fah, nifa banson haka...."Dariya Aisar yayi kafin yace" you deserved it Our Admiral the youngest Naval Chief Of Staff ever, mutumina zakayi breaking record ba'a ta'ba samun wanda ya 'kure Rank na Navy a shekarunka ba early 30's fa kake.... "Kanna wutanka Admiral ka duba fah duk tawagan nan are under your command..... "Stop talking ridiculous Aisar, ni Acting Naval chief of staff ne, snn bana fata na samu wnn mu'kami da wanne zanji da family koda aiki, I valued my Family more than anything else, Kasancewa da Beautiful yafi mun komai..... Dariya Aisar yasa yana fa'din kaji Romieo ba *Mijin Haneefah*.
"Tsaki Haidar ya kuma yi yace " You know what am damin tired of this place, kai nifa Nija nake son komawa, I need to see my Beautiful.
"Uhum , muma de naga munda matan nan haka muka tafi muka barsu.... "Hararan da Haidar ya narka masa ya hanasa 'karasa maganar wani navy ne ya 'karasi wajen ya sara masu kafin yace da Haidar" Sir we're done with exercise *Crocodile Smile* Haidar ya gya'da kansa yace good, ya juyo ya dubi Aisar yace Captain takeover, ka nuna masu exercise *Harbin kunama* A kifa jirgin kowa ya zube cikin tekun let them rescued their selves....Sara masa Aisar yayi ya dubi daya Captain din dake gefensa yace let's get going...... da poppoti suka karasa wajen sojojin.... nan suka ci gaba da horass dasu.

"Washe gari suka tafi Capital dinsu wato Istanbul dan ganawa da me girma shugaban 'kasan Turkey, sosai yaji da'din yanda Haidar ya jagoranci tawagar ake basu horaswa na 'kwararrun soji, take ya mi'ka 'ko'kon baransa dan a horas da Navys dinsu nacan, babu hali Haidar yayi rejecting dinsa kodan tarban da suka masu a 'kasarsu, dole suka 'kara kwana biyu suna horas da sojin ruwa na kasar Turkey.....
"Zaune suke a Maharas Hotel bayan sun gama ganawa na mussaman shida Kwamanda Hafsin rundunar sojin ruwa na 'kasar Turkey, ganawa ce sukayi 'yar sirri na dabarun ya'ki da abunda ya shafi Naval. Sosai Admiral. Saral Karem yaji da'din zuwan su Haidar 'kasarsu dan haka ne ya ha'da masu gagarumin dinner da daddare a farfajiyan Maharas Hotel. Duk yanda ka wuce sojin ruwa kawai kake gani kowa cikin Uniform 'dinsa gwanin ban sha'awa,....." Haidar ya 'dan matsa gefe nata faman neman layin Beautiful amma baya shiga, ya kira na mamy yafi sau nawa ba'a 'daga ba, ya kira na Inna ma same abu ba'a 'daga ba, sosai hankalinsa ya tashi, kana ganimsa kasan akwai abunda ke damunsa. "Aisar nata lura dashi ya bisa da kallo yaga ya mi'ke ya nufi restroom, shima mi'kewa yayi yabi bayan Haidar yana jiransa a 'kofar restroom, wayan aisar ne ya soma ringing ganin My Queen yasa saurin dauka yana fadin "Queen darling...... muryansa ne ya sar'ke jin muryan Sady na rawa... King I just couldn't help it, am so terrified.... "Aisar hankali a tashe yake fa'din" Queen put your self together and spell it out, meke faruwa...
"Ta 'dan share hawayen idonta tace "King tun jiya muka zo Kano nida mum, and mun tarar Hany na labour, toh tun jiyan bata haihu ba gashi har yanzu... likitocin sunata kai komo wai baby 'daya ya fita daga mahaifa kuma akwai risk na rasa maman babys din idan akayi Cs,..... kuka ya kuma kufce mata tana fadin Aisar bada son raina na kiraka ba dan basu so yaHaidar ya sani dan Allah kar ka fa'da masa nima na kasa samun nutsuwa ne shiyasa na kiraka to calm me down.....
"Innalillahi kawai Aisar ke nanatawa a zuciyansa kafin yace" Ki kwantar da hankalinki komai zai zama normal insha Allah, Hanifa zata haihu lafiya da izinin Allah, Allah zai sau'keta lafiya...... muryansa ne ya sar'ke sanda ya 'dago ido sukayi ido hu'du da Haidar... take Aisar ya juya zancen yana fa'din" Ok ok eh ai mun kusa dawowa yawwa queen will call you later.... ai beko jira cewa Sadiya ba ya katse kiran,
"Kallonsa kawai Haidar keyi yana son gano wani abu, Murmushin ya'ke Aisar keyi ya soma fa'din " I was waiting for you, I I also want to use the restroom..... "Kallon mamaki Haidar ke masa kafin yace" what do you mean Aisar, nanne kawai restroom gaba daya Hotel din nan, wait a second, are you hiding something from me...." Da sauri Aisar ya soma girguza kai kaman wanda yayi wa sarki 'karya yace" no no am not hiding anything, besides why would I do that.
"Haidar ya kafesa da ido kafin yace" who just called you on the phone? Girgiza kai Aisar ya kuma ya dagi yana kallon Haidar snn yace" stop being ridiculous Haidar,.... "karasowa Haidar yayi ya fizge wayan yana duba last call, Wueen ya gani wato Sadiya knn ta kirasa, harara kawai ya narkawa Aisar kafin yayi dialing....
"Sadiya kuwa tana gani ta daga da sauri a zatonta Aisar ne, nan ta soma fa'din" King 'dazu yaHaidar ne ya zo yanda kake ko, nasan shiyasa ka canza subject, pls king yaHaidar must not know about that....." Cikin hasala Haidar ya soma fa'din Sadiya fa'da mun meke faruwa, what happened to Beautiful?..... Innalillahi wa inna ilaihirraji'un haka Sadiya tace a zuciyanta shiknn yaji komai.... "Tasawan da ya kuma daka mata ne ya razana ta.... ta daburce tana 'kokarin kashe wayan Haidar yace" Are you deaf or what, don't you dear hang the phone, ki fa'da mun what's goin on there.
"Aisar ya 'karaso rai 'bace yana fadin " haba Haidar you need to calm down, why must you yelled at her, Ok fine bani wayata ni zan fa'da maka.... Sady kam kuka kawau tasa ta daura hannu aka.

"Haidar ya fizgo hannun Aisar suka bar wajen kafin yace oya inajinka meke faruwa,.. da kalamai masu 'karfafa gwiwa da tawakkali Aisar ya soma magana wa Haidar....."Look Aisar just get straight to the point, me Sadiya take cewa kar a fa'da mun..... "tunkan Aisar ya soma magana yaji zuciyansa ta karaya, fuskan nasa tayi jazur, a guje ya fice yana fa'din " now I get itm it's Haneefah, Aisar ma a guje yabi bayansa yana fa'din Haidar Haidar pls ka tsaya is not what you think.... Inaa bai samu Haidar ba sai cikin room dinsa, fizgo kaya kawai yake daga sip yana fa'din, I need to go and see her, Aisar ya soma fadin Haidar calm down first, pls don't panic, Ba abunda kake tunani bane.
"A hasale Haidar ya dago gamida jifa da rigar hannunsa yace " then what, mutuwa tayi, yes ta mutu ko Aisar.... take yaji kuka na shirin kufce masa. Girgiza kai ya soma yana fa'din I can't loose her, she's all I have, she's my happiness she's my inspiration..... "Rungumesa Aisar yayi gaba daya shima jikinsa yayu sanyi, I need to go there, am leaving this place first thing tomorrow morning...
"Aisar yayita bawa Haidar baki, gaba daya Haidar gani yake daren ya masa tsawo. Wnn dare ma iya cewa babu baccin da Haidae yayi, gari na wayewa yayu handling komai wa Aisar ya nufo Nigeria.....

"Flight dinsa a Lagos ta sauka, yana sauka ya shige na Kano ko gida beje ba ya nufi asibitin dayasan nan take awu. Su Abba duk suna reception sukaga Haidar kaman diran yeso, Haidar na ganinsu jigum jigum yaji kwalla yaciko idanunsa ko 'kafarsa ya gagara dagawa kafin ya 'kara step 'daya, cikinsu babu wanda ya iya masa magana, sai Abba da ya mi'ke ya ri'kosa. Mamy kam a hankali ta kauda kanta gefe hawaye na kokarin ambaliya a fuskanta.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋....
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
82

"A hankali Abba yaja Haidar suka fice haraban asibitin, kaman ra'kumi da akala haka Haidar ke bin Abba, kafa'dun Haidar Abba ya dafa yace" Son don't panic, Dr suna iya bakin 'ko'karinsu, snn kai musulmi ne nasan kayi imani da 'kaddar me kyau da maras kyau, da sannu Allah zai raba matarka da abunda ke cikinta lafiya, so I want to you to be very strong, save your strength remain a soldier, Allah na jin ro'kon bayinsa koda yaushe dan baya gyanga'di balle barci.
"Kalaman Abba sun 'karfafa wa Haidar gwiwa, gya'da kansa yayi kafin yace" haka ne Abba, insha Allah zanyi yanda kace, but Abba idan da hali inaso a fita da ita waje koda States ne ko wata 'kasa masu 'kwararrun likitoci sai a kaita... " girgiza kai Abba ya soma kafin yace " Haidar wnn duk me yuwuwa bane, ta riga ta fara labour snn suma likitocin nan sunada nasu 'kwarewan duk yanda mutum yaje idan Allah ya 'kaddara faruwan abu tofah sai ya faru dan haka fawalla wa Allah komai shine mafi alkhairi.
"Haidar ya gya'da kansa yace hakane Abba..... daidai nan Dr Kasim ya fito ya nufosu.... A tar suka nufesa suma.
"Haidar baki na rawa yace" How is she, how is my wife Dr, tell me pls how is she doing...... "Dr Kasim ya dafa kafa'dun Haidar yace" Navy you need to calm down everything is gonna be alright.
"Can I see her pls, I really want to see her, Haidar ya fa'di kaman me shirin sa kuka. Gaba 'daya yabawa Dr Kasim tausayi, ko jira sauraren amsan da Dr Kasim zai bashi beyi ba ya nufi cikin asibitin.
"Dr da Abba suka bisa da kallo cike da tausaywa, Dr ya maida dubansa ga Abba yace" Alhaji we need to talk mu 'karasa office dina, ba musu Abba yabi bayan Dr suka wuce.

"Abba ya jigum yana sauraren Dr sanda yake fa'din" Alhaji the truth is that, her condition is getting critical, we have no other option dole mu mata aiki dan ta riga ta galabaita, though aikin akwai ha'dari babba a ciki kashi 'daya ne cikin 'dari akasari suke tashi idan masu, she doesn't have any strength, she can't even breath yanzu haka oxygen ne a bakinta. So we need her husband to sign here tunda ya riga yazo.
"Inna lillahi wa inna'ilahiraji'un kawai Abba keta nanatawa a zuciyansa, duk sanyin dake Office din saida yaji zufa na karyo masa, tunowa yayi da 'kaninsa da kuma 'kanwar matarsa wato iyayen Hanifa, ya kuma tuna sanda suka kawota gidansa yaye wanda zuwan nata knn har ranar da ya aurar da ita ma Haidar, ya kasance yafi sonta fiye da 'ya'yansa na cikinsa, wasu hawayene suka zubo daga idon Abba, girgiza kai ya soma yana fa'din" Haidar bazai iya signing takardan nan ba na sani, jikin Dr yayi sanyi sosai ganin babban mutum kaman Abba na hawaye.... basu ankara ba sa ganin Hannun Haidar sukayi yana 'ko'karin kar'ban takardan daga hannun Abba, Abba ya 'dago kai yana kallonsa shima hawayene kwance a fuskansa, da kyar ya iya furta" I can do this Abba, if that's the only way... rungumesa Abba yayi suna matsan hawaye. Haidar da kansa yayi signing... Dr Kasim ya wuce aka soma preparation.
"Ana shirin shiga da ita Haidar ya ri'ko hannun Dr Kasim yace "let me see her pls even for a while, I won't take long..... "Dr ya gya'da masa kai ya uamarci sauran likitocin da nurses din su fito.

"Tun daga nesa ya hangota cikin ya girma sosai oxygen na manne a face 'dinta, idonta a lumshe tamkar me bacci, ji yayi 'kafarsa sun kasa 'daukansa, rayuwansu da ita kawai yake tunowa tun tashinta da kuma aurenta da yayi, da irin azaba da wahalan da ya bata a baya, har I zuwa lokcin da suka zama cikakkun ma'aurata masoya junansu..yana tafe yana tunanin har ya 'karaso jikin gadon da take, hawaye kuwa nata faman ambaliya a fuskan sa, shafa fuskanta ya shigayi yana hawaye yake fa'din" hey I know you can go through this, you're a fighter..... kwantar da kansa yayi gefen gadon yana ri'ke da hannunta maras cannula yake fa'din" don't leave me Hanee, you're the luv of my life, I luv you with all of my heart, I can't loose you..... kuka me sauti yake sosai kansa na bisa gadon a gefenta, saida nurses suka shigo tura gadon Haidar ya mi'ke har lokacin na ri'ke da hannunta, Dr Kasim yana 'ko'karin jansa inaa yana rike gam da hannunta har suka fito zasu wuce theater room, su Abba mamy Inna duk suka nufosu, da kyar Abba ya zare hannun Haidar daga na Hanifa, gana daya kuka suke idan ka 'dauke Abba dake rarrashinsu, Haidar ya kamo hannun mamy suka zauna waje daya mamy ta kwantar da kansa bisa cinyarta tana share masa nawayensa tana fa'din" kuka ba namu ba Haidar let's pray for her okay.
"I luv her mamy, ya fa'di yana me dago kai yana duban mamy, gyada kanta mamy tayi tace" I knw Son, na sani she'll be fine kaji insha Allah. Juyawa yayi ya kalli Inna duk ta ji'ka bakin zaninta tana share hawaye ya mi'ke ya 'karasa wajenta ya zauna a gefenta" hannun Inna ya ri'ko cikin nasa yace " addu'a zamu mata kinji Inna Allah yasa ayi a sa'a, Inna ta amsa da ameen Zaki, ta rungumosa cikin jikinta tana goge ragowar hawayen.

"Su Hajiyan Saif, Mum 'din Aisar, Shema da kuma Sady harma da Saif ne suka shigo, Haidar na hango Saif ya mi'ke ya nufesa suka rungume juna.
"Asibiti ta cika dam kowa da kalan addu'an da yake yi, lallai Hanifa 'yar dangi ce inji Queen Samy.

"Mintoci suka shu'de haka awanni ma, Dr ne ya fito yana since abin rufe hanci, gaba daya suka mi'ke suka nufesa.... A tare suka hau tambayansa meke faruwa. "Kallonsu yake cike da tausayawa kafin yace" Alhamdulillah the operation was quite good, take kaga annuri ya bayyana a fuskokinsu banda hamdala ga rabbil izza basa komai....."muryan Dr ne ya katse su sanda yake fa'din" but unfortunately we couldn't save...... Ai Haidar be gama ji ba ya soma fa'din" no no that's not true..... "Dr yace calm down Soldier, let me finish my statement first, babyn da ya fice daga placenta ya riga ya mutu, and Furtunately the remaining two babies and their mother are still alive.... "Haidar kam besan sanda ya zube yayi sujidi shukri ba, ya dago ya rungume Abba yana fadin" Abba Hanee is alive, my wife is alive..... "murmushi kawai Abba keyi ganin duk yanda Haidar ya daburce sabida murna, yace" Son mun gode Allah, Allah ya 'kara mata lafiya, gaba 'daya jama'an wajen bazan iya kwatanta maku irin farin cikin da suka shiga ba tareda mi'ka godiyansu ga ubangijin talikai.

"Su Sady suka soma fa'din Dr can we see the babies, Dr yace sure yanzu za'a fito dasu bayan an gama shiryasu..... aiko bai gama rufe baki ba nurses biyu suka fito dasu ri'ke a hannunsu, gaba daya mutanen wajen hankalinsu ya koma kan babies idan ka 'dauke Haidar da ko kulawa beyi ba, shi haushima suka basa, ya galla ma Sady harara a zuciyans yayi tsaki yace sarkin 'yan rawan kai.
"Bayan Dr Kasim yabi yana tambayansa, " Dr zan iya ganin matata, murmushi Dr Kasim ya danyi kafin yace" Soldier naga alama sunanka zai koma romieo fah irin wnn soyayya haka, Haidar yace pls Dr may I,
"Dr ya dan dara kafin yace" muna son ta 'dan sami hutu, snn ba yanzu zata farka ba ko ka shigama bacci take.... " yeah koma me take yi nide kawai son ganinta nake, Haidar ya katsesa.
"Ok fine zaka iya shiga but pls navy don't take long,.... gyada kansa yayi yace " yeah sure, Dr yayi directing Haidar room din da aka kwantar da Hanee, ji yake kaman ya maidata cikinsa dan so da 'kauna haka yayita kallonta yana shafa mata addu'o'i 'karshe ya manna mata peck a kumatunta kafin ya fice.

"Inna na ri'ke da macen ta mi'kawa Haidar tana fa'din" ungo kar'beta ka ganta mana, a yatsine ya kalli Inna kafin yace" wato duk baku damu da halin da Beautiful ke ciki ba duk kun maida hankalinku kan babies. ?..... "Baki sake Inna ke kallonsa kafin tace "toh sannu tsuntsun soyayya, kai zaki ban son iyayi baka fimu sonta ba ehe, idan baka son 'ya'yan kuma toh,... "Haidar ko saurarenta beyiba ya soma kallon yarinyar yana murmushi ya kai hannu ya kar'beta yana fa'din" welcome princess ya manna maya kiss a goshi, mamy ce ta 'karaso da namijin Haidar ya ha'desu duka biyu ya kar'besu tareda yi masu kiran sallah a kunnuwansu na dama.
"Sai lokacin Haidar ya samu zarafin zuwa gida yayi wanka ya wuce gidan mamy ya 'dan sami wani abun yaci.

"Sanda ya dawo asibiti mamy ya samu a tareda Inna ta wuce gida dan kintsawa.
"Beautiful ya fa'di yana riko hannunta, mamy ta mi'ke tana duba yaran dake kwance bisa gadonsu....
"A hankali ta bu'de idonta fuskan Haidar ta gani yana mata murmushi. Murmushin itama ta 'danyi, Haidar ya sunkuyo ya manna mata kiss goshi yace sannu Beautiful 'dina, how you feeling. "A hanakali tace" da sau'ki Handsome, jawo kujera yayi ya zauna gefenta hannunsu cikin na juna.
"Handsome yaushe kazo.
"Kissing hannunta yayi kafin yace" ai na fa'da maki zanzo,
"Toh aikin...... "shiii ya daura hannu bisa lips dinta kafin" yace Dr yace babu yawan surutu, keep calm ok, I luv you...."Murmushi ta 'danyi tare da gya'da kanta a hankali.
"Sosai Haidar da Haneefah suka burge mamy tana jin sonsu har cikin ranta fatanta Allah ya barsu tare. Sun jima a haka yana ri'ke da hannunta har bacci ya kuma yin gaba da ita.
"Namijin ne ya soma kuka yana wutsil wustil, mamy ta mi'ke da sauri ta 'dagosa.... "A hanakli Haidar ya ajiye hannun Hanifa ya nufo mamy. "Mamy me yake so ko yunwa yake ji, yayi magana cike da kulawa.
"Yunwa yakeji daga gani zaiyi tsotso, gashi bata fara basu nono ba. "Mamy ko madara za'a basu,. "Eh toh amma gwara idan ta dawo hayyacinta ta fara basu nono kafin a basu wani madara.... "Haidar ya mi'ka hannu ya kar'besa yana jijjiga sa yana fa'din" it's Okay Champ daddy is here, zaka tashi momy da princess, sai sunbatu yake da jariri, mamy kam har dariya abun ya bata.... "'Karshe Haidar ya'dan saka masa le'ben bakinsa na 'kasa nan da nan kuwa ya kama yana ja.... da haka har yayi shiru ya koma bacci.
"Mamy tayi murmushi tace" Son ka iya raino fah, lallai daughter ta huta, murmushi Haidar yayi cike da kunya....


"Gaba 'daya Haidar ya tare a asibiti idan kaga ya tafi toh darene, a haka har tayu kwana biyar a asibiti kafin aka sallame ta, sosai Inna da mamy ke bata kulawa, Haidar yaso a wuce da ita gidanta amma fir Inna ta'ki tace gwara su tafi can gida, mamy ma ta goyi bayan haka, babu yanda Haidar ya iya dole ya ha'kura. Amma kullum na gidan mamy yana tareda Beautiful dinsa da Champion da kuma princess dinsa.
Su Sumy harma da momma sun samu isowa, kowa sai sha'awan yaran yake, Shema ma kusan kullum sai tazo duba Hany, Su Sady da Mum kuma sun wuce Zariya duba dangin mum kafin zuwa ran suna su zagayo.
"Hanifa ta sami 'karfi sosai, kamarba cs aka mata ba, ta warware sosai tana samun kulawa na mussaman daga masoyanta, bama kaman Haidar baijin kunya agaban kowa yake nuna mata tsantsan soyayyansa.

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
83


"Gidan cike yake da mutane kai kace biki ake, yara sunci sunan Umar (Farouq) da kuma Khadeejah( Deena). Gata da soyayya kam wa'en nan yara sun ganshi tareda mamansu, tun safe Haidar be sakata a idanunsa ba dan kuwa ta ko ina mutane ne ma'kil a gidan, da yamma misalin 'karfe 5:00pm ya shirya tsaf cikin sky blue jampa da hula dark blue zanna bukar yayi kyau sosai kaman ka sace ka gudu, gidan ya nufa a tunaninsa tunda yamma tayi 'kila an 'dan ragu 'yan suna tinda waliman da rana akayi.

"Kai tsaye cikin gidan ya nufa sashen mamy, su Inna da wasu gwaggwanayen su zaune a parlorn ana ciye ciye an ta'ba hira anga dangi. Aiko yana kutso kai suka soma ga angon 'karni, Haidar gaba daya kunya ya kullu'besa, ya'dan tsuguna yana gaishesu, duk suka amsa masa da sakin fuska tare da masa barka, ya mi'ka yana 'ko'karin juyawa" goggo Rabi tace" tashi abinka ka shiga kaga yaranka. Inna ta ya'be baki tace" wa yace maki yaran yazo kallo, shi yasan wacce yazo gani uwar yaran yazo gani, ni mero ban ta'ba ganin soyyaya irin na Zaki da Hanifa ba, wai kunsan basa kiran juna da sunansu sede kiji yace mata bintiful(Beautiful) itakuma kiji tace Haso( Handsome)..... "Gaba daya suka sa dariya, Inna larai tace yo ai gaskiyansu haka muke so gwara suso junansu, kode kishi kike ne yaya mero. Dariya Inna tayi tace wa ni ai na sallama wa Hanifa suje can suci soyayyansu ita da taga zata iya rayuwan saman ruwa, ni mero ina zan iya salon kifi ta cinyeni... aka kuma saka dariya gaba 'daya..." Haidar ya mi'ke yana sunne kai..." caraf Inna tace" meye kake 'ko'karin juyawa mun san wajenta kazo, maza 'karasa nasan itama yau seta kusa zazza'bi tinda ta yini bata ganka ba.." kallon zamu

1 Comments On MIJIN HANEEFA
avatar
aisha-musa

2 years ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment