Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fyad'e ne" Cikin tashin hankali ya kalleta

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, khairiyya yaushe haka ta faru ban saniba? share hawayen ta tayi

"Babu wanda yasan ammun fyad'en dagani se wanda yamun fyad'en se momy se kuma mijina" Mamakin sane ya k'aru
"Momy kuma da mijinki? why ? nisawa tayi sannan a hankali ta soma labarta masa komai har kawo aurenta da Hammood ta k'ara da cewar

"Ni abinda yake damuna shine gaba d'aya na rasa meya hau kaina na gayawa Hammod sirrin mahaifiyar mu tabbas bana cikin hayyacin kaina, gaya masa sirrin momy yafi damuna akan maganar abinda Bilal yamun, ze iya tausayamun akan ba laifina bane amma mutuncin mahaifiya fa, anya Yaa Bilal inada kai kuwa? meya kaini gaya masa? mema yasa na masa bayanin wani abu? gabaki d'aya narasa yanda akayi nayi wannan katob'arar, narasa meke kaina, narasa inda hankalina ya tafi, mutuncin mahaifiya na sayar na tona mata asiri duk sanda na tuna wannan abin it keeps hunting me" Nisawa yayi yana d'auke hawayen idansa kafin yace

"Am so sorry khairiyya, duk wannan abun ya faru dakene sabida am not a good brother, da ina kusa dake bazaki bi shawaran wani banza ba, nice na wofintar dake nabarki bana tuntub'ar inji me kike ciki,ki gafarceni k'anwata kinji, wannan abun da Bilal ya miki na godewa Allah dabe samu sa'a duka a kanki ba, dana shiga uku, momy kuwa banaji abinda take ya shafeni ko wanda tayi itada Allah abu d'aya na sani dolene mu mata biyayya, dolene mu saurareta mu mata wa'azi, dolene mu kwantar mata da hankalin ta, dolene ayau musan me take ciki, bata kyautaba data lalata yaran mutane amma shima k'wad'ayayye ne and for abinda ya miki wlh senaga bayansa acikin ruwan sanyi, seyasan cewa ni Bilal sunan mu kawai iri d'aya amma hali yasha banban, abinda kika gayawa mijinki ki manta dashi kawai haka Allah ya tsara ba tsarinki bane ba, amma dolene kiso Hammood idan de ke 'yar halas ce, dolene ki masa biyayya ki kuma so duk abinda yakeso He sure is a good husband"Nisawa tayi cikin jimami

"Now i am relieved, now i can rest, now i can sleep in peace, at last na gaya maka abinda yake cina, maganar momy dakake cewa yaya zan b'ullowa labarin toh? nifa ta gagara ma ko kirana a waya" Murmushi yayi yace

"Allah sarki Momy, bazata ita kiraba ai, Allah ya k'yaleta tanata aikata masha'a tazata taci bulus ashe akanmu abin ze k'are kada ki damu kinji, zan kirata a waya anjima zan bata numberki na nan ita da kanta zata kiraki, ki dena damuwa kinji" Jinjina masa kanta tayi alamun to sannan sukaci gaba da tattaunawa.

***************
Mood bebi takan Hafsat yayi tafiyarshi yabar gidan, sanda ya dawo ma beko tunata ba danshi bata gaban sa, yau dai ya kula Khairin sa tana cikin damuwa wannan ya sanya ya zaunar da ita a k'asa yashiga yamutsa matsa sumar kanta yana sosawa a hankali, murmushi take zuba masa tana so suyi hira amma rashin sa'arta d'aya mijin nata baya magana, nisawa tayi data tuna yanda yanzu take tausayin rashin maganar sa, inama ace wannan kyakyawar fuskar tabud'i baki tayi magana, ta tabbatar da babu abinda ze hanawa muryar sa dad'i, kwantar da kanta tayi asaman k'afafuwansa fuskar ta tazo sama, suka sakarwa juna murmushi, tace dashi

"D'azu Bahar Sarauni tazo neman ka Hammood, wai wannan yarinyar bayada lafiya ta suma kuma bata farfad'o ba dan haka sunje asibiti da ita, tace baka d'auki wayaba idan kazo in gaya maka, mantawa nayi se yanzu gashi kuma har k'arfe shabiyu ya gota" Shiru bece mata komai ba amma aranshi yanajin wani iri me kuma ya sameta? ya tambayi kanshi ganin babu amsa ya sanya bata kuma magana ba.

Tunda ta tashi takejin ta tamkar babu abinda ya sameta jiya, kallon Bahar tayi data tare k'ofar wai bazata fita zuwa school tana dariya siririya ta fad'a jikinta

"Ammu na, nafa warware, kuma yau zamuyi test ne so kike karnaci komai, nanfa ba kamar Nigeria bane Ammu, idan na fad'i da gaske bazan kara ajin gaba ba" Nisawa Ammu tayi cikin tausayi

"Kiyi ki gama wannan test d'in, gwanda kawai amiki aikin nan ki huta, nayi nayi ki gayamun meke damunki kink'i, waye yake takuraki agidan nan? Murmushi ta k'ara k'ak'alowa

"Ammuu!! kina kusa dani fa, waye ze takurani, ni bansan tunanin meye akai naba" Murmushi Bahar tayi

"Waye ya isa ya tab'aki yau la'ana ta tabbata akansa shalelen Bahar" Rungumeta tayi tana dariya, bahar tace tana janyeta ajikinta

"Zata b'alla tsohuwa, yanda kiketa murjewa hakan nan nikam nace anya Hansatu bazakike sanya k'aton skirt zuwa makarantar nan ba, koma ki dinga sanya hijabi kawai" Kallon kanta tayi tana murmushin takaici

"Allah kuwan Ammu nikaina nasan banyiwa addinina adalciba, ba yanda zanyine amma wannan bujen shisa na matsu in kammala karatun nan, kalleni fa" Dariya Ammu tayi

"To kike sanya wani abu akai kafin kine school d'in" jinjina kai tayi tayi tana dariya

"To Ammu inna dawo yau zansan abunyi kinga yanzu Bus ze iya tafiya yabarni" Janye mata tayi tana mata addu'a ita kuwan ta wuce tana tunanin yanda xata kaya ance yau zasuje da Hammood bud'e acc d'inta a bank..... Tundaga nesa ya kafeta da ido, tana sanye da skirt wanda kad'anne ya wuce cinya, doguwar safa ce a k'afarta har zuwan gwiwar ta sannan kuma da rufaffen takalmi a k'afarta fari kamar yanda safarta take fara, kalan skirt d'in nata light brown ne kaman amma shirt d'inta me d'auke da tie fara k'al se tie dayake brown kalan skirt d'inta ta d'aura sweater brown bud'add'iya agaba asaman kanta d'an kwaline datayi ado dashi wurin d'aure gashin kanta, tana rataye da jaka brown wacce ta bala'in karb'e ta, daga nesa zaka iya jiyo k'amshin turarukan data haddabi jikinta dasu masu sanyin k'amshi, amaimaikon tafiya d'an tsalle take tana wak'a tanabin layin interlock tamkar wata k'aramar yarinya, tanada tulin tarin damuwa sedai harko yaushe bakinta ne take taimakar ta, dan kuwa dashine take mayarwa setaji wasai, abinda tayiwa Mood jiya ya dameta bata kyautaba amma bazata iya bashi hak'uri ba sam, Allah ya rabata da wannan me fad'in ran, harta matso daidai gate inda yake ta tsallen wasa da interlock take tana rera wak'ar ta, k'ara gyaran tsayuwa yayi ya hard'e k'irjinsa da hannayensa yana sauraren gaisuwar ta amma ga mamakin sa wucesa kawai tayi tana wak'e wak'en ta, Murmushin dabesan dalilin saba ya sub'uce masa aransa yace

"Sakarya me halin yara, inbanda shiririta ina ita girman ta 17yrs ina rawa banda hauka? Juyawa yayi kawai se karo yayi da Khairii datake shirin d'aukan shawarwarin yayanta akan girmama mijinta ta koyi san sa, murmushin sa ya fad'ad'a dankuwa dama murmushin ne a fuskar sa ya k'arawa tafiyar sa sauri ya zuwa gabanta, rik'o kafad'unta yayi ta sakar masa murmushi sannan tace

"Dama zuwa zanyi inje in duba jikin waccen data fita, amma naga se tsallen rawa take ga alama she's a good actor naga ko gayar dakai ma batayi ba" Murmushin sane ya k'aru da hannu ya nuna mata alamar dama yasan k'aryane ba abinda ke damunta. Murmushi tayi kafin tace

"Breakfast ya kammala, kazo muje muci abinci" Jan hannunta yayi suka shiga ciki sannan ya wuce da ita kai tsaye a d'akin sa, k'ananun kayane dama ajikin ta hannunsa ya d'aura akan waist d'inta sannan a kankali ya rik'o hab'arta ya manna bakinsu awuri d'aya, passionately yake kissing nata wanda atake itama abin ya soma fizgarta dama khairii tanada yawan sha'awa kawai d'auke idanta take idan yana yagalgalarta, hannu takai a bayansa batare datasan abinda take ba tasoma shafa bayansa a hankali, shi kanshi Hammood besan abinda yakeyi ba, kawai abinda ya sani yanayin daya gani a tattare hafsat na tsantsar k'uruciya ya tattare nutsuwar sa sunyi garin gumel, bashida zab'in daya wuce rage zafi awurin Khairin sa, koba komai itace zab'in sa, tun suna tsaye har tsayuwar ta gagari dukkan su suka saukewa gado nauyin dasuka ebo suna sauke numfarfashi atare, yanaso ya kankare abinda yakeji amma sam ya ratsa nutsuwar sa gaba d'aya, biye masan da khairiyya tayi shine abinda ya k'ara ruruta wutar sha'awar sa yasoma azalzalarsa zuwaga tilastawa kansa shiga hurumin rigar mamanta, lokacin dayakai hannunssa akan dukiyar mamanta atare suka nemi suma, dan kuwa dukkansu se shan barkono sukeyi, Hammood yacika namiji dankuwa be sassautawa khairii ba harseda ya cimma burinsa sosai akanta, dukda beyi tsammanin matsewarta ba amma haka yasha mamakin yanda take gagam, sedai kam yasha raki dan har yakushinsa seda akayiyi, lokacin daya dawo hayyacin sa kunyar khairii ce ta kamasa, aibedace ya mata hakan ba da sanyin safiyar nan amma shin ya zeyi, seda ya taimaketa wurin yin wanka da gyara jikinta sannan ya sanya sukayi salla sukayiwa Allah godiya kafin yabar d'akin, message ya tura mata bayan daya bar gidan

"Its a blessing to have you as a wife, Allah ya miki albarka, yakuma albarkaceki da dukkan ni'imomin sa" She boost in to tears sanda ta karanta sak'on sa, Hammood wane irin mutum ne me karamci? wane irin mutum neshi me sowa kowa abinda yake sowa kanshi, Allah ya saka masa da alkhairi ta furta a sarari.

************

Be dawo gidan ba seda yaje ya saya mata wasu dogayen riguna masu kyau, da rigunan sanyi da kuma zoben gwal harma da sabuwar waya k'irar iphone, zumudi yake akan khairii ba abinda ya hanashi kusantarta illah tunanin bata warke raunin taba, Hammood irin mazan nan ne masu son kulawa, yana tsananin son soyayya ya tab'a dating wata yarinya a Nigeria yana son yarinyar amma sabida baya magana ta nuna sam koshine sarki bama d'an sarki ba bazata auresa ba, haka ya hak'ura dukda yarinyar tanada kulawa sosai, ya sani zigata akayi akan sa, tunba yauba yakeso yayi aure amma ya sani tabbas duk macen datasan baya magana bazata aure saba, wannan ya tilasta masa shafawa kansa lafiya. Sanda taga kayan banda washe baki babu abinda take, duk da khairii yarinya ce me tsananin kud'i hakan be hanata godiya wa mijintaba musamman wani had'add'en turare daya d'auki hankalin ta k'amshin sa me sanyi, kallon sa tayi tana dariya

"Thank you so very much husband, i love you" rungumeta yayi yana dariya har tana jiyo sautin fitowar dariyar daga k'irjin sa, kallon sa tad'anyi bayan ta janye jikin ta

"Idanda Allah yayika me magana na tabbatar da sautin muryarka seyafi kyakyawar fuskarka kyau, inama ace Allah ya baka ikon bud'e kace khairii kawai dana zama mace mafi sa'a a duniya" K'ureta yayi da kallo abubuwa da dama suna masa yawo, batare dayace komai ba ya janyota ya rungume yashiga shafan sumar kanta.
Hafsat dama ta shirya tsaf domin rama cin fuskar da ake mata koda kuwa zata wahala, dan haka ta kimtsa ta sanya doguwar riga bak'a wacce take a d'ame daga saman ta, amma daga kunkuru zuwa k'asa tanada fad'i sosai, tufke gashin kanta tayi a tsakiya ta yane kanta da mayafin abayar, turare kuwa seda Bahar tayi masifa akan haramcin sakashi sannan ta sarara masa, ta sanya maroon lipstick a fuskarta, sannan kuma ta shafa poundation da powder kalar fatarta tayi kyau sosai dukda iya abinda ta saka kenan, takalmin k'afarta jane me tsini cylia ne ta batashi sabo dal, tayi kyau fiye da tunanin me tunani, kallon Bahar tayi tana takun gayu

"Ammu na yakika ganni? ta k'arashe maganar tana juyi, dariya Ammu tayi kafin tace "Hoo yar sababi, kinyi kyau wlh tamkar jinin larabawa, to se ina kuma? tana murmushi tace

"Yaa Mood ne yace na shirya zancen bud'a acc d'ina, k'arfe biyu yace ban iya fitinar saba shisa nayi salla na shirya abuna" Rik'e hab'a tayi

"Ohh na tuna kuwa, to kinga yi maza ki samesa a b'angarensa kuje ku dawo da wuri ba nason shiririta" Gaba tayi tana mata sallama, kai tsaye part d'in ta nufa aranta tana rok'on Allah yasa karta karaya akan shirinta na wargaza farin cikin khairiyya tunda take shirin takurawa rayuwar ta. Da sallama ta shiga parlor d'in tana mamakin babu wanda ya tab'a cewa ze saya mata waya, ita bazata iya cewa a saya mata ba amma cylia ta fara tambayar ta akan rashin wayarta, har kunya taji, bayi kawai ta tarar a wurin kitchen kallo d'aya tamusu ta d'auke kanta, gayar da ita sukayi cikin ladabi sannan ta zauna a kujera ta d'aura k'afarta d'aya akan d'aya tana k'arewa parlon kallo, khairiyya ce ta fito ganin Hafsat a zaune ba k'aramin kayar mata da gaba yayi ba, da k'yar ra saisaita kanta ta soma yamutsa fuska, Murmushi Hafsat tayi tace

"Khairiyya sannu da gida" Bata amsa mata ba taci gaba da tafiya zuwa kawai tayi ta nemi wuri ta zauna, ta d'aura k'afarta d'aya akan d'aya tana yauk'i tace da kuyangar dake binta

"Ku dafamun Noodles da lemo me sanyi" Hafsat dai ko motsawa itama batayi ba taci gaba da k'urawa TV ido wanda zahiri bashi take kallo ba, k'amshin turaren daya daki hancin tane ya sanya ta waiga tana kallon k'ofar, ganin Hammood ita kanta seda k'irjinta ya doka, daure wa tayi tace tana kallon sa

"Sannu da gida Yaa Hammood" Kallonta kawai yayi ya d'auke kanshi, k'irjinsa yanaci gaba da lugude, ya rasa dalilin dayasa zuciyar sa take masa lugude a duk sanda yaga yarinyar nan, zama yayi a kusada khairi ya d'auki remote ya sauya channel, itako seta lank'washe k'anta ta d'aura akan kafad'ar sa tana murmushi

"Dear harka fito" Sumbatar kanta yayi yana murmushi ya zagayeta da hannayensa zuwa k'irjin sa

"Wayarsa ya zaro ya rubuta tana kallon sa

"Zanje bud'awa waccen acc ne, ni take jira, mezan zo miki dashi? kallon sa tayi ta shagwab'e fuska

"Honey zan bika dan Allah" Murmushi yayi ya mata alamar ta tashi su tafi" Haka suka fita itama seda ta cab'a uwar kwalliya, tare da driver suke dan haka duk a baya suke zaune, Khairiyya ce a tsakiyar su ta wane nannad'e ajikin mood, har suka isa bank d'in basu koda kalletaba, ita ba waya bare tayi aikin gabanta, duk setaji ta tsargu.... Seda suka kammala komai a banka sannan suka wuce shopping acen suketa jibgar kaya itadai tana biye dasu ba abinda ta d'auka, seda ya gaji dan kansa a waya rubuta mata

"Me kikeso ne banga kin d'auki komai ba" Haska masa wayar yayi ta kalli screen d'in, seda ta gama kalla sannan ta kallesa tana wani lumshe idanta kamar yanda cylia ta kouar da ita tace

"Ni waya kawai nakeso, k'awayena kowa yanada waya ni banida shi, ko abun school me muhimmanci ne akwai group amma ni banida waya" Tsatsareta yayi da ido yanda take magana tamkar daga tsayen bacci ze kwasheta, kawar da kansa yayi daga dubanta sannan ya rubuta mata

"Ok" Juyowan da Khairiyya tayi anan ta gansu a tsaye tanacen tana kwasar kayan kwalliya, gaba d'aya ranta seda ya jagule amma batayi magana haka ta tako tazo taja hannun mijinta tana masa lank'wasa, Hafsat murmushi kawai tayi dan ita harga bazatace ga wani namiji a duniya dazata so har take gwada kishi sosai akansa haka ba...... Khairiii tsabar bak'in ciki bata shiga shagon sayar da wayoyin ba, iya Hafsat da Hammood ne suka shiga, lokacin datake zaban wayar acikin wayoyin da aka jere mata k'irar iphone wata fara ta d'auka tana kallon wayar, murnushi tayiwa me shagon sannan tace

"I like this, but pink color" Daga gefen ta taji wata murya dabata tab'a jiba tace

"Your too childish me zakiyi da waya pink kuma?" waigowa tayi suka kalli juna ita da wanda ke maganar a tare suka zare ido, shiya rufe bakinsa ita kuma ra nunashi da yatsa tana k'ok'arin yin magana amma gaba d'aya ta kasa furta komai tsabar mamaki..

*Mu had'u gobe inshaa Allah danjin shin waye wannan kuma maganar sa ta rikitar da hafsat..*

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

*NA:BILLY GALADANCHI*

-Babu wata k'awa datake tona miki asiri face kin tonawa kanki asiri, ku dena ganin laifin k'awaye dan abu ya had'aku dasu kuma sun muku tonon silili, kece kika gaya musu kikace kuje ku fad'a.Ba zancen dena yin k'awa kuyi k'awayen ku na alkhairi amma ku adanawa cikinku abinda be shafeku dasuba, koyin tsegumin wani, idan kika sirrinta sirrinki babu wata wacce ta isa ta yayata sirrinki.-

*SHAFI NA GOMA SHA BIYAR*

     Cikin wazgewa ya sauke hannun sa, jotter sa ya zaro a hanzarce ya rubuta

"Your wasting my time" Haska mata jotter yayi amma be kalleta ba, waige ta shiga amma tana mamakin mesashi gwale ido hadda rufe baki, babu kowa awurin se ita dashi kawai se kuwa mutumin dake gaban table nashi yana displying mata phones dasuke dasu, kallon rubutun tayi sannan setayi wata siririyar dariya tace a sarari

"Zargina ya tabbata kenan" Amma bashi take kallo ba koda tayi maganar, d'auke kai tayi ta ksrb'i farin wayar kawai suka bar shop d'in bayan ya biya kud'in, seda ya saya mata sim cards har biyu da layinsa akayi gwaji sannan suka d'auki hanyar gida, lokaci zuwa lokaci a mota suna satar kallon juna wanda khairiyya ma ta kula dukkansu basa cikin nutsuwar zuciya kaman yanda suka fito agida, amon sautin muryar Mood yana ratsa dodon kunnen Hafsat, tabbas magana yayi wannan shine karo na biyu dataji maganar sa sedai kuma wancen karon waya kawai ta hango yanayi amma ta tabbatar magana yake, yanzu kuma murya rad'am lafiya lau mezaisa yayi hakan to? akan wane dalili ze takure rayuwar sa alhali yana magana? to kuma ance mahaifiyar sama kurma ce kodai ita d'inma tana magana akwai abinda yasa sukewa mutane kwantan b'auna? zuciyarta tana azalzalarta akan sanin waye Hammood menene ainahin gaskiyar labarin sa shida mahaifiyar sa, daga wacce masarautar suka fito ance kakansa ma na wurin uwa sarkin wata masarautar ne shin menene dalilin dayasa Uncle Jay yana k'anin Ummin hammood amma yake zama a masarautar da yayarsa ke aure a maimakon tasa masarautar, batada wata alak'a da kowacce masarauta seta k'auye, a k'auyensu mahaifinta mahaifinsa shine me garin k'auyen nasu amma banda hakan batasan komai akan sarauta ba, abu d'aya ta sani akwai mak'iyan Hammood a masarautar daga lokacin da akace ze aureta mutane sama da goma sunce ta kashe sa zasu bata dukiya, kodai itama kurmar zata zama ne sabida ta samu amsar tambayoyinta? Har suka isa gidan batasan sun k'arasa ba, seda Driver ya mata magana so kusan uku sannan tafita tabi bayansu tana godiya wa Hammood.

     Kai tsaye Toilet ya fad'a ya sakarwa kansa shaya, ya akayi yayi sub'utar baki haka? ze iya cewa a shekaru biyun dayayi a Nigeria koda kuskure be tab'a yiwa wani magana ba seso d'aya shi d'inma a wayane, wayar kuma ta zama dole ne sabida daga U.S d'in aka kirasa, lumshe idansa yayi ruwan me zafi yana sauka ajikinsa, dukda dad'in ruwan dayakeji hakan be hanawa xuciyar sa cunkushewa ba, idan har zargin sa akan Hafsat hakane na turota akayi ta dagula lissafin sa tabbas yau ta samu makamin dashi kad'ai ya ishi mak'iyansa kawar dashi dan kuwa sun saki jikine akan bazasu tab'a bari kurma ya mulke suba, daga lokacin dako yau akace sunsan yanxu ya samu lafiya yana ji yana kuma magana tokuwa sesun yi duk yanda zansuyi sun kashe ruwan daya cika masa baki ya furzar sannan ya fito yabzura bathrobe d'insa ya zauna a bakin gado, wayarsa ya janyo ya k'urawa number ta daya gwada kira d'azu, shin magana ze mata ko me, kokuma ya bata kwana biyu ya gani koda zatayi wata alamar dake nuni da cewar taji kai tamaji, reaction d'inta kawai ya isa ya nunar masa cewar tabbas taji yayi magana, ajiye wayar yayi agefe ya shafi sunar kansa datasha gyara tamkar ta larabawa anyi style da sumar ata gaban kansa, Khairii ce ta shigo ta zauna a kusa dashi

"Menene yake damunka you look really tensed, tunda kuka fito shagon wayar nan naga mood naka ya sauya, kaddai wani izgilin waccen wawiyar tayi maka" Murmushi yayi ya janyita gaba d'aya ya ringum'e a k'irjin sa, sumba ya manna mata a goshi yanajin sonta yana ratsa shi, be tab'a zata qrayuwa zeso wata mace kamar yanda yakeson khairiyya ba amma me wannan yarinyar ta gama da ilahirin gabb'an jikin sa da zuciyar sa, bece komai ba a haka suka fad'a sabuwar duniya, ga alama khairiyya tanada yawan sha'awa sedai kuma tabbas raguwa ce, batason sakin jikinta ayi sha'ani daga zaran tabiya buk'atarta a wurin wasanni seta soma yangace masa ala dole ita ta gaji.

Kai kawo hafsat keyi da wayar dake hannun ta ta rasa tunanin da take, bazata iya ci gaba da rik'e wannan abun a ranta ba, dole acikin biyi setayi d'aya, kodai ya sanar mata gaskiyar maganar sa kokuma ta nema da kanta amma bara ta jarraba magana da Bahar. A zaune ta taddata tanacin Apple zama tayi ta d'auki d'aya itama ta gutsura tana murmushi tace

"Ammu hutawa ake tayi" Murmushi Bahar tayi

"Yo wane hutu da jiki irinna na tsufa kuma? aiba zancen hutu kedai se abinda Allah yayi, likita yace inta faman shan 'ya'yan itatuwa yana k'ara lafiya shisa kikaga gaba d'aya na duk'ufa da shansu" Kwantar da kanta tayi a saman cinyar Bahar kafin tace

"Ammu nikuwa wani abu yana damuna?" Kallon ta Bahar tayi

"Kaddai yawan ciwon kanne ko? Yamutsa fuska tayi tace

"Bashi bane Ammu, kawai akan rashin lafiyar Hammood ne, wainikam anya ba iska bane dashi, amma ayi mutum yana ji amma baya magana? Nisawa Bahar tayi kafin tace

"Hammude haryakai shekaru tara a duniya bayaji bakuma ya magana, makaranta ma seda yakai aka sakashi ta kurame, yanada shekaru goma a duniya akayi masa aikin k'walwa anan garin aka samu nasarar jin sa ya dawo sedai maganar ce tak'i yiyuwa, ita kanta maganar likitoci cewa sukayi damu daga lokacin da akayi aikin zuwa kowane lolaci ze iya dawowa yana magana kamar kowa tunda yake lalurar tasa bada ita aka haife saba, dankuwa harya soma yin magana yanada shekara da wata uku, Abbi Ummi duk fad'a yake, ni kaina yakan fad'e sunana Bare uncle Jay, tuni ake cewa UJay , yaro wasa wasa ya dena magana mun zata shiru shiru ne bayason surutu sekuma abu ya dawo kiyita masa magana baze waigoba sekin tab'asa, koda akaje asibiti sukace cutar kurumta ce akayita magani abun beyiba, jida farko ina kallon komai a matsayin wasa har ina ce masa kurma amma daga bisani sema abun ya shallake tunanin mu, akace a k'walwarsa ne jini ya shiga wani wurin akayi aiki so 2 amma ba nasara, seda yakai 9 aka sake aiki anan akayi nasarar ji ya dawo amma babu magana, Kurma ya wahala arayuwa Hafsat ina masa fatan macen dazata yi tattalin sa, dukda na kula jininku be had'u ba amma inaso kiyita hak'uri da kurma, yakai matsayin da be yadda da kowa ba a duniya sabida wahalar daya sha abaya, idanda yanada bakin magana daya gaya miki irin wahalar dayasha a hannun mak'iyan sa, har gobe sharri ake k'ulla masa agun mahaifin sa, sannan sun kasa aiwatar da komai akansa, kurma yayi kud'in da ko mahaifin sa banaji yanada rabin su, ya samu sa'ar k'warewa a harkar zane da taimakon Shammaz (Likitan yaso a littafin Sa'a tafi manyan kaya), yanzu haka yana kulanda babban kamfanin sa dake UK, ya k'ware a zanen motoci da jirage ke harma da kekuna, ya kware sosai a zanen komai ma daidai da kamfanin k'era tile Hammood ne yake zana desighn duk sanda zasu fito da new, ya shahara a harkar dukda haka nake tilastawa mahaifinsa bashi kud'i sabida kawai yaji kwanciyar hankali akan cewa yanada mahaifa, a Nigeria seda masu tsaro yake yawo, sannan bazaki gansu tare dashi suna yawo ba amma duk inda ya saka k'afarsa suna cen a b'oye. Mangalo dan Allah karki guji Hammude akan halinsa, karkice zaki gujesa sabisa lalurar sa ni nayaba da hankalin ki, wannan ya sanya nake masa sha'awarki dukda dai dayake ina duniya babu wanda ya isa ya miki dole" Nisawa Hafsat tayi kafin tace

"Amma kun k'ara bincikawa koda maganar tasa ta dawo? Dariya Bahar tayi"Ai sunce indai ta dawo muna zaman mu zamuji yana magana, so munata dai addu'a amma har yau shiru" Nisawa tayi

"Allah ya bashi lafiya me dorewa Ammu, inshaa Allah wata rana se labari" Shafa sumar kanta Bahar tayi "Hafsatu, Allah kuma ya bani ikon aske kan nan

Please Login or Register in order to submit comment