Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan kaji sunyi wata magana dake nuni da cewar basusan komai akanta ba, ka dubafa ka gani muhseen awurin dana sameta ita kad'ai ba kowa, jinin dake fita ajikinta is not real, they planned everything they set me up" Ya k'arashe alamar maganar da hawaye a idanshi" Jinjina kai Muhseen yayi

"Yanzu na hango abinda kake hangowa tun d'azu mood, yanzu na harbo jirgin tabbas shirine, amma ya zamu b'ullowa lamarin? Da hannayensa yaci gaba da amfani da sign language wurin yi masa magana

"Sun rigada sunje sun gayawa Mami nssani, bansan mezance mata ba yanzu, she will not listen to me, please muhseen help me out" Rungumesa D'an uwan nasa yayi yana patting bayansa a hankali

"Calm down mana Mood, komai zezo ya wuce ne kamar yanda na baya suka wuce kaji" Shiru dukkabsu sukayi se sauke ajiyar zuciya da Mood keyi cikin jin zafin zuciyar sa.

**********

Gabaki d'aya kan Hafsat ya d'aure, bazata manta meya faruba itada wad'an nan gayun, lokacin da take k'ok'arin tserewa se k'afafunta suka gaza, k'unar dake k'afarta ya tsananta azaba, hakan ne ya tilasta mata tsayawa tana mayarda numfarfashi har suka cimmata, a lokacin ne ogansu ya musu umarni akan su b'are masa ita haka suka dinga jan kayan jikinta har sukayi nasarar rabata da zaninta da hijabinta suka kuma yaga mata rigarta, tayi iya k'ok'arinta taga cewar ta k'waci kanta amma haka suka daddage seda suka rabata da har pant d'inta, sesukayi rashin sa'a tana period, bayaga haka kuma ya b'alle mata tamkar ruwa sabida tsananin firgicin datake ciki, ogansu dayaji haushin haka seyace shiba k'azami bane bazeyi ba amma gudun data sakashi su lakad'a mata shegen duka, wannan ne abinda ya k'ara haukatar da ita dan kuwa tasha duka sanda sukaga bata iya koda iya d'aga k'afarta sannan suka tsere suka barta agun tsirara! To meyasa wad'an nan mutane masu magana daban suke cewa wani ya mata fyad'e ita babu wanda ya mata fyad'e, hasalima a fuskar wanda suke alak'antawa da fyad'en bata tab'a ganin saba, dan harga Allah sanda yaje gunta bataga fuskar saba batamasan me take ba, shin meke faruwa da itane a rayuwa? su waye anan kuma waya kawota nan d'in?.......

***************

Lokacin da Hammod da Muhseen sukazo wurin Mami sun jima a zaune kafin ta fito, bayan sun gayar da ita ta amsa sekuma sukayi shiru, sedaga bisani Muhseen ya gyara zamansa ya kwashe komai ya gaya mata yanda ya faru da yanda abubuwa suka juye, kallon nutsuwa tayi masa sannan dayake matsalar ta iri d'ayace da Hammood sunaji amma basa magana seta shiga mayar masa da sighn language cikin fad'a

"Shishi kad'ai yafi kowa yawan mak'iya a masarautar nan, idan bashi bane yayi meye nakaita d'akinsa, idan taimako yakeso ya kawota guna mana, koya kaita wurin daya dace, yakaita a sibiti mana ko ya kira en sanda, yanada iko isa da matsayin daba wanda ze tunkareshi akan yayi karya idan ya aikata d'aya daga cikin wad'an nan, ina goyon bayan me martaba, hukuncin sa daidaine tabbas seya aureta" Tana k'arashe maganar ta mik'e zuwa ciki ranta a b'ace. Mik'ewa Mood yayi ya lumshe idansa, banda mahaifiyar sa, baze tab'a jurar fushinta akan saba har abada, Muhseen da azama ya mik'e ya rik'eshi amma seya zame hannun sa ya soma aikin daya saba wato gudu yana zuwa b'angarensa gaba d'aya yayi umarni akan a sallami hadiman sa baya buk'atar aikin aransa yana nazarin yanda zeyi sa wannan wawiyar yarinyar seta yabawa aya zak'inta seya wulak'anta asalinta indai sunan sa Hammood!!

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK


*BILLY GALADANCHI*


*SHAFI NA HUD'U*


kai tsaye d'akin da aka tanada dominta ya shiga yana me banke k'ofar da iyakacin k'arfin sa, idanuwansu suka tsark'e dana juna atake jikinta ya soma b'ari tana zaune asaman gado ta takure wuri d'aya se rarraba ido takeyi! Yafi mintuna goma a tsaye yana kallonta bece komai ba, seda dan kanshi ya gama tunanin dayake sannan ya juya da zummar barin d'akin abinda yajiyo je daga waje ya dakatar dashi ad'an lobin dake tsakanin waje dacikin d'akin

"Bari bari bari prince mood anji haushi, ai yanzu ance ko sarki yaji komai, jakadiya ta tabbatar wa sarki wannan yarinyar 'yar hannu ce cikine sukaje su zubar yazo da gaddama, ance tutsiye yarinyar akayi ta fad'i gaskia akan dama saurayintane dasukaje azubar da cikin daya mata shine fa aka samu matsala seya d'akkota ya kawo ta nan besan asirinsa ze tonu ba" Dariya d'ayar tayi

"Daba sunce aure zasu masa da itaba? to yanzu naji ance sarki yace a koreta tunda abun hakane, yazata hakk'inta yaci daze d'aura aurensu yanzu kuwa korace" Tafawa sukayi

"Bakiji yanda na tsani yarinyar ba wlh, da akace ze aureta nace su kurma an iya zab'e wannan yarinyar kyau kamar aljana shegiya se gashi,yanzu danaji labarin za'a koreta se wani sanyi ya mamayeni, dankuwa ni wlh inasan sa haka" Duka d'ayar ta d'aka mata a cinya

"Banza yafi k'arfin ma'aikata da bayi ki kama kanki" Be jira sun k'ara wata maganar ba ya fito daga d'akin,yauma kamar kullum beko kallesu ba ya shiga d'akinsa jikinsa a matuk'ar mace wai meke faruwa ne? menene gaskiyar maganar mutanen nan su kuma manyan munafukai ba? yaya yakejin maganar tana juyawa up side down?..... Mik'ewa yayi yanzun ma da sassarfa ya sakko k'asa ya nufi motar sa, beko nemi Muhseen ba dankuwa yaga motarsa a sukwane ya nufi gidan *UNCLE JAY*.......

Tunda Anty Barra taji tsayuwar motar da gudun tasan D'an kurma ne agidan yau kamar yanda take kiranshi, dan hakanda azama ta juya daga parlor zuwa ciki

"Uncle Jay bazan iya da rigimar Kurma ba, naji tsayuwar motarsa nakumaji gudunsa dan Allah ka tashi kaje" D'ago kai yayi ya kalleta yana murmushi

"Dama nasan zezo ban tsammanin zezo yanzu bane ba" Murmushin ta mayar masa "amma lafiya dai?"

"Ba lau ba dai, Mood ne bashida wayau ko kad'an, duk abinda zeyi seya saka rashin wayau se uban zurfin ciki da miskilancin tsiya" Tana kallon sa harya kai aya, nisawa tayi tace

"Ka saurareshi yanzu, tunda yazo mayi maganar daga baya" Mik'ewa yayi

"Noo wife agabanki zamuyi maganar muje kawai, its good kina wurin with those ur boosting idea's i belive abubuwan zasuje mana da sauk'i" Ba musu suka fita atare hannayensu sak'ale ana juna, a parlor suka sameshi harya shigo yana zaune akan sopa ya sunkuyar da kanshi hannayensa duka cure acikin sumar kansa. Gaisawa sukayi dashi da yarensa sannan ya mik'awa Uncle Jay duk abubuwan da suka faru a rubuce a takarda har gulman dayaji ma'aikatan dayace a kora sunayi, ga alama be isa yace ayi ba ayi a yanzu! Tare da Barra Jay ya zauna suka karance takardar tatas kallon sa yayi sannan yace

"Naje gidan da safe gun Maminka tamun bayanin farko akan yanda ka shigo da ita, dakuma ya da maganar ta k'ara juyewa akan na ciki, sedai sarki be yarda da maganar jakadiya ba akamar yanda kaji ana tsegumi, hasalima ya kashe wannan maganar, abu d'ayane ya dai ya kafe akan seka auri yarinyar ranar juma'a" Da sauri ya d'ago ya kallesa,cikin yare irin nasu kurame da tsananin b'acin rai ya soma magana da hannayensa wannan karon har kansa da wuya mosti yake yana yi tamkar ze tashi sama. Seda ya lafa sannan Uncle Jay ya kalli Barra

"Barra me kike hasashe, da gaske kema abinda muke zargi akan had'in bakine da yarinyar haka kema kike zargi" D'an shiru tayi na wani lokaci kafin ta nisa tace

"kaso saba'in harda biyar acikin d'ari yana nuni kai tsaye da cewar had'in bakine musamman idan akayi duba da yanayin yanda al'amura suke tafiya acikin fada tsakanin Mood da sauran 'yan uwansa kai harma da mahaifin sa daya haifeshi da cikinsa,na biyu kuma ita yarinyar bata musa akan dikkanin abubuwan da ake cewa ba alhali ya tabbatar mana cewar ta ganshi sanda yaje d'aukan ta har tashi tayi se kuma ta kasa, kaga anan ya dace ta kareshi idan har taimakon daya mata yakai mata matsayin taimako bawai sharri ake k'ulla masa da ita ba. Abu na biyu kuma shine kaso 25 acikin d'ari suna nuni da cewar faruwar komai co-incidence ne kawai aka samu, duba da irin wowtar dashi yayi, mesa sanda ya d'aukota bezo nan gidan ba, besa beje wurin Muhseen ba, shin mema ya hanashi zuwa gun Mami koya sanar da ita a waya, wannan zargine dabaze goguba musamman da idon Fada suka tabbatar k'arfe biyu ta wuce sanda ya shigo da ita, CCTV ma ya shaida hakan, bayaga haka ga jini kuma, bansan yaya ze faruba su k'ulla sharri irin wannan hadd fake jini, kaina yana k'ullewa sosai" Ta k'arashe maganar taname jingina bayanta da bayan kujerar. Gyaran zama Jay yayi

"Melon think mana, say something please" Nisawa tayi

"I need an audience with the f**king bitch, kafin ince komai Swt" Ta k'arashe maganar tana me zube lumsassun idanta akan mijin nata" Mik'ewa yayi

"Get ready now, kema kinsan halin kurma baze barni in hutaba harse ance an fasa aura masa Munafuka kamar yanda yake kiranta" Dariya sukayi sannan suka wuce d'aki a tare, shikuwa yana nan zaune dafe da kansa yana lissafa maganganun Anty Barra.

Tunda suka doshi b'angarensa aketa kallon su, shi yasan duk munafukai ne suke kallon sa, 'yan sa ido masu jira suji me zasuyi anan, sanda yakai k'ofar hawa a saman sa sannan ya tsaya ya kalli wani daga cikin securities d'insa dasuka shigo tare dashi ya mik'a masa hannu alamun ya bashi paper da pen, da sauri ya d'akko ya mik'a masa shikuwa ya rubuta

"Dismiss everyone from here" Da sauri ya juya ya soma aikin tattara mutanen har zuwa sama.

*****Da sallama suka shiga d'akin sedai yauma kamar kullum atakure suka tadda 'Yar shara rakub'e ta k'ule a k'arshen gado k'afarta d'aure da bandage duka biyu alamun an mata dressing na wutar har an rufe ta. Jay da Mood akan kujerar dake d'akin suka zauna yayinda Barra ta zauna asaman gado ta tattare hankalinta duka zuwa kan 'Yar shara tana sakar mata lallausan murmushi a fuskarta, tsorone bayyane akan fuskar 'yar shara wanda yasan abinda ake cewa tashin hankali yana kallonta ze tabbatar cewar hankalinta a tashe yake

"Sannu yarinya ya jikin naki kuma" Tsatsareta tayi da ido tana rarrabasu akan ta amma batace da ita ci kanki ba, anty Barra ce ta kuma cewa

"Wannan Uncle d'in Hammood d'in sunansa Jamil ni kuma matarsa ce sunana Anty Barratu amma yara kamarki suna kirana da Anty Barra, yayinda shi kuma kawun naku ake kiransa da suna Uncle Jay, dafatar zamu zama Ant da Uncle naki kema" Nanma batayi magana se k'ara matsawa take akuryar gadon sekace wacce za'a yanka.Shiru Barra tayi na adadin wasu seconds sannan ta kuma cewa da ita

"Banaso kiji kunyar idon mu ki gagara gaya mana gaskia, so bake ki gayamun tiryan tiryan meya faru, da gaske Mood shine ya miki fyad'e? Ta k'arashe maganar da alamar tambaya tana me nuna Hammod dake zaune yana fuskantar su" Jikin 'Yar shara ne ya shiga shivering lokaci d'aya duk sanyin ACn seya haifar mata da saukar wata iriyar zufa me wahalar controlling, idan ta ya kawo ruwa sosai har lokacin Barra take kallo amma batayi magana ba, banda ma rawa da jikinta ke k'arayi sekace wacce ta d'aura aure da zazzafan zazzab'i. Mik'ewa Barra tayi ta zagaya ta rik'o hannayenta duka biyu se a lokacin ta kula da cewar jikinta ciccira yake ma bako karkarwa ba, tsatsareta itama da ido tayi sannan tace

"Yarinya ya sunanki? kuka wiwi tasomayi sedai batayi magana ba sam,kan anty Barra sosai ya d'aure ta waigo tana kallon su Jay wanda suma mamakin sukeyi, amma kafin wani acikin su yayi magana se ji sukayi an bud'e k'ofar d'akin an shigo, atare suka kalli k'ofar Me martaba ne dasu D'an Galadima da sauran manyan fada, bayansu kuwa likita ne wanda sananne ne agidan, MOOD ne kawai baya dubawa shi likitansa daban. Mik'ewa sukayi Me martaba ya zauna sannan suka zube suka gayar dashi,Mood ya had'e rai tamkar an aiko masa da manzan mutuwa, ita kuwa Yar shara ganin Me martaba da wannan tawagar ba k'aramin tsoratata yayi ba atake tashiga zare ido fiye da da, wanda Barra tana lura da yanayin sabon firgicin data shiga ganinsu, d'akin ya d'auki shiru bakajin komai se saukar numfashin mutanen dake d'akin dakuma k'arar AC da Fan dake yawo a d'akin, seda aka shafe sama da mintuna bakwai sannan Me martaba yayi gyaran murya yace

"Abinda ka aikata Hammood ka cutar da yarinyar mutane, gashinan yanzu likita ya tabbatar mana tayi loosing memory d'inta, abun ma tamkar ace ya shafi kanta ne, ko sunanta bata sani ba, gabaki d'aya ma ga alama kanta ba saiti, sabida hakankamar yanda na fad'a kaine zaka aureta, tunda mu munyi k'ok'arin sanin ina iyayenta suke amma batada bakin magana dan batasan komai nata ba, sakamakon fyaden daka mata yasa k'walwarta ta shafe komai ba abinda take iya tunawa dan gane da abinda ya shafi rayuwar ta ta baya, wani lokaci cen idan Allah yaso zata warke seta mana bayanin dangin ta, dan haka na yanke hukuncin d'aura maka aure da ita a babban masallacin juma'a ranar juma'ar bayan an idar da sallah" Har me martaba ya gama maganar dayake kan Mood a k'asa yake be d'ago ba, babu me halin yiwa Me martaba musu seda Jay ya tattaro courage d'insa sannan yace

"Amma ranka ya dad'e tunda har an tabbatar ta manta ita wacece aibe dace a d'aura mata aure dashi ba, idan kuma memory d'inta ya dawo aka kuma yi rashin sa'a da aure akanta fa? bayan haka ni Hammood ya tabbatar mun bashi yayi mata fyad'e ba" Mik'ewa me martaba yayi

"Yarinya dai batada aure dan kuwa k'aramar yarinyace likita ya duba raunin ta ya tabbatar mana sabon shiga ce, se abu na gaba maganar bashi yayi ba idan bashi bane kaine? Da sauri Jay ya d'ago ya kalli Marik'insa tun yana yaro se kuma ya sunkuyar da kansa Tuba nake ranka ya dad'e ka gafarceni" Yana wani k'arewa d'akin kallo yace

"Hammood shine ya mata fyad'e Jay, banza girman mahaukaci akace k'aramin me wayau ya fishi" Shiru d'akin ya d'auka, me Martaba ya kalli Barra datake k'anwa awurinsa uwa d'aya uba d'aya yace

"Barratu dama inaso nayi kiranki, ki d'auki yarinyar kije da ita wurinki, bamusam menene a k'afarta ba amma dai nasan k'unace kamar an manna mata wani k'arfe me wuta dan akwai zane da tambari ajikin wutar se ayita kulawa, kullum akaita dressing asibitin Dr mark'az" Cikin ladabi tace

"Inshaa Allah Me martaba" Daga haka ya juya muk'arrabansa suka rufa masa baya se likita ne ya tsaya yana yiwa Barra bayanin yanayin wutar da abubuwan daya dace amata.
Mood idanshi yayi ja sosai, jijiyoyin wuyansa sunyi rud'u rud'u, ilahirin muscles nashi sun mik'e sun fita sunyi rad'am se k'yalli suke alamar ya fusata, yanayin yanda sautin numfashi da bugun zuciyar sa ke fita kanaji kasan a tsananin fusace yake, watsa idanshi yayi akan Hafsat datayi saurin janye nata har lokacin cikin tsananin rawar jiki take,tas ya k'arewa yarinyar kallo be yadda da ita ba, da ita aka shirya komai itama munafuka ce, koda yazo da ita bayan ta farka aida magana abakin ta, yanzu za'a gayan masa maganar kawai akan me!!!! Wani duka ya kaiwa Table dake gefensa gashi glass ne take ya tarwatse be damuba ya bige side lamp d'in dake kan bedside duka ya tarwatse komai duk iya k'ok'arin likitan da Jay akan su hanashi amma be hanu ba seda yajiwa kanshi ciwo, duka hannayensa glass ne, karo na farko dayayi hargowa irin na bebaye sannan ya buga kansa da gina, be saurara ba seda ya dena motsi dama abinda Jay yakewa gudu kenan, ya tabbatar idan me martaba ya matsa se ankaiga fin haka ma, ya tabbatar idan aka aurawa Mood yarinyar nan wannan ciwon nashi ya taso komai ma ze iya faruwa, besan mesa me martaba baya duba condition na Mood ba, besan menene tsakanin uban da d'ansa ba, Mood yarone me tsananin nutsuwa da kawar dakai, besan yanda akayi mahaifin sa baya gani ba, damuwa tayiwa yaran nan yawa har yana ganin tamkar kowama ya tsane sa, duk k'arfin hali irin na Jay seda yayiwa Hammood kuka, yasan yaron is innocent akan abinda yake zargin sa, sedai fuskar yarinyar ma looks so innocent bayaji wani conspiracy aka shirya harda ita, amma bari Barra ta nutsu zeji meta karanto akan yarinyar..... Likitan ne yayi k'ok'arin taimakawa Mood amma ya kasa dole aka wuce dashi asibitin sa dannkuwa likitansa baya gari, sedai asibitin likitan nasa suda suke da record na komai daya shafi rayuwar sa.

*****************
Lokacin da suka barta ita kad'ai acikin d'akin lokacin ne ta firgita sosai da ganin haukan da wannan yakeyi, mutumin data gane shine wanda aketa ik'irarin ya mata fyad'e kuma za'a aura masa ita, me yasa abubuwa suke faruwa da rayuwarta cikin sauri tamkar a mafarki,yaya wannan mutumin ze kashe kansa akanta, akan me zasu masa haka, bari taje ta gayawa wannan matar gaskiya, kome zasuyi sesuyi Allah baze kama taba danta fad'a gaskia, a hanzarce ta sakko daga kan gadon bata damu da irin azabar ciwon da k'afarta ke mata ba, so take taje kawai ta samu wannan matar datace sunanta anty Barra ta gaya mata gaskiya, so take taje ta samu wannan balaraben ta sanar masa gaskiya karya kashe kansa, ina zatakai hakk'i idan ya mutu?..... Da gudu ta fito a d'akin tana k'ok'arin sakkowa k'asa domin ta taradda Anty Barra setayi rashin sa'a Ameena ce a saman tana mopping, da gayya ta sanya mop stick a k'afarta abinda yajanyo ta fad'i harta soma gangarowa daga matattakalar benen babu inda kanta be daka ba kafin ta gama gaggarewan banda ihu babu abinda takeyi tun tana ihun zuwa lokacin data gama gangarewa ko motsi batayi, harga Allah Ameenan bawai da miyya tayi ba, tsammani take zata d'an zamene sesuyi dariya kamar yanda suka tab'a yiwa abokim Mood, segashi yarinya ta gangare harma ga alama ta suma.

***************
Jay kanshi yana kallon sama sanda Barra ta shigo d'akin lokacin tafito daga wanka d'aure da k'aramun towel a k'irjinta, saman kanta kuwa sanye da hulan wanka take, zama tayi a kusa dashi tana goge fuskarta da gefen towel d'in jikinta, hankalin ta kacokam ta mayar a kanshi sannan a hankali tace

"Jay" Be kalletaba yace

"Water melon" Murmushi tayi jin sunan daya kirata dashi sannan tace "Swt kasaka damuwa sosai aranka akan issue d'in nan, dan Allah ka ragewa zuciyar ka nauyin daka d'aura mata, kasani Mood baya buk'atar komai sama da addu'a a yanzu, bamuda wata hanyar dazamu karkare ko goge masa wannan mugun tabon, ubangijin daya k'addaro faruwar hakan shishi kad'ai ya isa ya warware matsalar nan" Nisawa yayi yana matuk'ar k'aunar barra, batada had'i agunsa shikam komai bata da dogon nazari take aikatashi, cikin tsananin damuwa yace

"Melon baki gayan komai dangane da abinda kika fahimta akan yarinyar nan ba d'azu" Lumshe idanta tayi sannan ta bud'esu a hankali ta zube su a kansa

"Jay yarinyar tasan wani abu, and ba wani memory datayi loosing,after that kuma duk abinda aka shirya da ita bawai bisa son ranta bane tsorata ta akayi da wabi abu gaskiya, na hango tsananin tsoro a idanta nakuma hango gaskiya shinfid'e a fuskarta" Zaune ya tashi ya karb'i man shafawar datake k'ok'arin bud'ewa ya b'alle murfin seda ya tsiyaya a hannun sa sannan ya sako k'afafuwanshi agefen bazaunanta ya sanya ta a tsakiya a hankali ya zame towel d'in jikinta ya soma shafa man a gadon bayanta a hankali

"Me kenan ya dace muyi yanzu barratu na" Ya k'arashe maganar habarsa tana kan gefen wuyanta yana goga masa gashin gemunsa a hankali, tare suka lumshe ido sannan cikin wani yanayi tace

"A haka kakeso muyi magana me muhimmanci Jay" Murmushi yayi

"Wannan irin zaman da akazo akamun, da wannan k'amshin dake tashi ajikinki kin fito daga wanka yaya kikeso nayi dan Allah Melon? Hmm ina magana" Shiru batace komai ba sabida harga Allah yanayin sak'on dayake aika mata tako ina ya soma karb'ar jikinta, tanaso ta gaya masa labari akan yarinyar data fad'o daga kan stair case d'azu amma batason d'aga masa hankali, bataji ya zata abun yayi tsanani har yanda aka sanar mata, yana cikin damuwa sosai ta ina zata fara? hannunta takai ta shafi gemun sa sannan tace tana me manna gadon bayanta asaman k'irjin sa

"Jay nice ma nake k'amshi, so kake ka kasheni da wannan salon, a duk lokacin daka mannamum wannan had'ad'en gemun naka ajiki, wani irin electric shock ne yake d'ibana wani zubin harsenaje America da k'afa ban sani ba" Siririyar dariya yayi ya d'aura hannunsa asaman dukiyar fulaninta yana shafawa a hankali, shiru wurin ya d'auka na wani lokaci banda saukar numfashin su babu abinda kakeji da ganta ta juya ta lalubi bakinsa ta saka a nata, passionately take kissing nasa tana murza wuyansa zuwa bayan kunnensa da d'ayan hannunta d'ayan kuma yana safa da marwa a bayansa cikin salon tafiyar tsutsa irin na k'warewa, bashida zab'in daya wuce sakar mata akalar rayuwar sa tayi yanda takeso dashi, seda ta gama kashe masa jikinsa sannan tabi lafiyar faffad'an k'irjinsa ta shige tare da d'aura kanta asaman k'irjin nasa, gsrgasan dake kwance luf akan k'irjin ta soma wasa dashi sannan a hankali tace

"Jay yarinyar nan tamkar anyi magana da bakin mala'iku, likita ya gayamun da yamma danaje asibiti cewa zamuyi CT scan, so munje munyi but before the result comes out nabar asibitin se yanzu Mami tamun waya" Hannunshi akanta yana shafa sumar kanta daya zare hular wankan dake kanta yace

"Emhm metace"

"Akwai matsala akan buguwar da kan nata yayi suna tsammanin cewar zata dawo tana wani behaviour kamar na yara haka, ban gama fahimtar bayanin Mami ba dai, amma akwai 'yar matsala" Wata iska me zafi ya furzar har lokacin idansa a lumshe sannan yace

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, abubuwan nan suna yawa fa Barra, na rasa ta ina zan b'ullowa al'amarin nan, Allah kayi mana maganin musiba"

"Ameen" ta furta a hankali sannan tace

"Jay Zulaiha tana jiranka fa, ko wanka bakayi ba, ga 8 ya gota tuni please ka tashi" Shagwab'e fuska yayi

"kema kinsan banason fita idan ina tare dake, ni tausayin kaina ma nake duk ranar dazan kwana ba tare dake ba" Zame jikinta tayi a nasa

"Jay ya zakayi? Ehm dole dai kayi adalci ka sani, ni bazan iya kallo kake wuce ka'idar tafiya ba" Mik'ewa shima yayi bece komai ba ya fad'a wanka ita kuwa anan tayi wata irin rikitacciyar kwalliya ta d'auka hankali acikin atamfa kalar ka me ratsin fari da kuma bak'i tayi kyau ainun, kallon farko zaka d'auka cewan wurin wani taron biki zataje amma zahiri mijinta daze koma b'angaren abokiyar zaman ta shitayiwa kwalliyar ban kwana.... A parlor ya sameta ta gama turara gidan da turaruka masu k'amshin gaske, tana k'ok'arin goge takalmin da ze saka, murmushi tayi sanda ta hangoshi sannan da hanzari ta ruga ta rungumeshi tana dariya

"My jay kayi kyau kamar ango, irin wannan karkace hula harkasa naji kamar ka zauna inta kallon ka" Murmushi yayi ya zagaye kunkurunta da hannayensa

"Melon da safe zanzo muje wurin Mood, hankalina sam baya jikina, gabaki d'aya tunanina yana wurin yarancen idan ya farfad'o lafiya k'asar zansaka ya bari, hanlalina yafi kwanciya ace Mood baya k'asar akan wannan wahalan dayske sha sekace mara gata" Gemunsa ta shafa

"Please karka fita anan da damuwa Jay, banaso katafi ka barni da tunanin damuwar da kake ciki sam bazan iya bacci ba" Sumba ya sauke mata a wuya

"Bazan shiga wata damuwa ba Melon, wannan kalan wankan dakika mun sallama dashi kad'ai ya isheni guzurin dare, Allah ya miki albarka" Ringumeta yayi sannan sukayi sallama cikeda shauk'in juna, ko wannensu yanaji yana tsananin kewar d'an uwansa....

Tun daga k'ofar parlor part d'in zulaiha wani wari mara dad'i ze fara taryarka, bayaga haka kuma kana shiga acikin part d'in zaka soma cin karo da abubuwa kamar su kopi plate da sauransu, kawar da kanshi yayi ya zaga ya shige bedroom nashi, yafi awa biyu a gidan amma zulaiha bata nemeshiba, daga baya ma dayaje neman ta seya tarar tana kwance tana sharar bacci abinta.

Please Login or Register in order to submit comment