Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuyanta seta dena numfashi, kamar ance ta waigo segata tana kallon sa, da fara'arta ta mik'e tazo daf dashi tace

"So nake inje inyi wanka aruwan sama, amma ba'a ruwan sama ya zanyi?" Wani irin kallon tsana ya wurga mata sannan ya janye jikinsa daga nata ya nufi sama, bin bayanshi tayi ta rik'e masa riga ta baya

"Dan Allah yaushe za'ayi ruwa, nace dakai so nake inyi shillalo na aciki" Hannunsa yakai ya bige mata hannu cikin fusata ya d'are matattakalar da gudu yanzu kam, shagwab'e fuska tayi wane zatayi kuka, shikuwa seda ya d'are sannan ya tsaya ya waigo yana kallon ta cikin wani yanayi mara misaltuwa tana abin yara tace

"Niko Niko banama sonka, idan kaga ina wasana karkazo kace ka sanni ma,nama gaya maka" Ta koma kan kujera ta zauna ta sadda kanta acikin cinyoyinta tanata k'unak'uni!!!

Ameena ce ta kalli barira suka shek'e da dariya k'asa k'asa, Barira tace "Sabon salo gemu a kafad'a yarinyar nan fa da sabon samfuri ta dawo daga asibitin nan, batasan d'an kurma bane ba, zataci ubanta" Amina na dariya tace

"Bakisan iskancin datamunba d'azu ai, kawai basega yarinyar nan ta zauna duk ta b'ata wuri da soyayyen k'wai ba, kamar 'yar shekaru biyu fa, aikuwa na fakaicin ido na mammari shegiya, abinda yaban haushi ma shine yanda ta koma tana kuka tamkar wata k'aramar yarinya" Tsaki Barira taja

"Tsiya d'inkin ludayi, ni kuwa d'azu rok'ana tayi in kunna mata TV cikeda ladabi, nace a ina suka samo wannan wawiyar, wai a haka prince mood zata aura, Allah da farko naso sosai tabar gidan nan, naso idan Fada abinda suka soma yad'awa ya yad'u" Tab'e baki Amina tayi

"Dama ta koma gidan princess Barra niba k'aramin dad'i najiba, ko uban me tazoyi mana yau oho" Dariya Barira tayi me sauti

"Ameena sekinyi kyau da zama princess, kafatanin hadimai da bayin gidan nanke babbar suce a iya iya hege,idan yau ace ki zama sarauniya niko zanta miki bauta kodan indinga kallon yanda zakike yarfa mutane" Kan Amina ne ya kumbura tana wata tafiya tace

"Da kuwa tafiyana ma canjashi zanyi zuwa irin na Prince D'an galadima" suka kuma kwashewa da dariya har suna tafawa...

Wayarsa ya zaro a aljihunsa yana mamakin zuwanta gidan, wane irin behaviour ne haka yarinyar nan kanta d'aya kuwa, da sauri ya rubuta wa anty Barra message

"What is she doing here?" Anty Barra tana zaune kusa da Mami suna magana da yaren kurame wayarta tayi k'ara alamar shigowar sak'o, a hankali ta d'aga wayar ta duba, murmushi tayi, gaba d'aya mur'add'en hali irin na kurma yana bata mamaki, tana tunanin amsar dazata bashi kawai wani text ya kuma shigowa

"She's acting wired! please take her away" Kallon Mami tayi damuwa bayyane a fuskarta, cikin tsananin damuwa ta soma mata magana

"Mamina wannan itace alfarmar dazakimun, ku baiwa yaran nan time, a k'alla 6 month or a year Mami, abin ze masa yawa wlh" Mami cikin fad'a ta soma magana da yarensu tana demonstration da hannu

"Da yasan ba auren yakeso ba meya kaishi lalata yarinyar mutane, Barra kinsan masarautar nan da idanduna dubu kunnaye dubu ko ina kabi kunne ne da ido caa a kanka, harse yaushe Hammood ze dena janyomun magana ina zaman zamana, tun yana k'aramin sa komai aka bud'i baki Mood baya koyi da galadima sam, shi haka yaga anayi, shine d'an cikin gidan shine d'an gidan amma d'an rik'o yafika iya sarrafa masarautar ka, ni mulkin be damen ba, amma k'imana ya dameni, babu wani me martaba dazanje incewa wai a janye maganar auren nan amma ke zaki iya zuwa da kanki" Dafe kai Barra tayi

"Amma Mami kun tabbatar haka d'inne shine ya aikata, saraki fa Mami baya auren macen da k'afar wani ya riga tasa shura"

"Koda shine ya shureta a sahun farko idan ba daga ciki bane babushi babu sarauta har abada" Da sauri ta d'ago ta kalleta cikin tsananin takaici muryanta har yana rawa tace

"Mami haddake a tsanar Kurma wlh, ku zurfafa bincike ku sauraresa, niya gaya mana komai kuma mun yarda dashi, idan akawa yaran nan haka sam ba'a masa adalci ba" Mik'ewa Mami tayi

"Barratu ki tashi ki tafi" Tana kuka ta mik'e tsaye itama

"Mami please listen to me" Hararar ta Mami tayi tana me k'ara jaddada mata barin wurin da hannunta, badan tasoba ta fita, yayinda mami bak'in ciki ya tarnak'e ta shige cikin d'akinta ta rufo k'ofa, zama tayi a bakin gado tana mayarda numfarfashi, tasani sharri akebin kurma dashi, tasan mak'iyane barkatai akan kurma, tasan duk wannan abubuwan sharrin sarautar nan, akan mulkin masarautar Daulatul Dinar aketa so a kashesa, tanatayi masa nasiha, tanata nunar masa yayi taka tsantsan amma sam kurma baya fahimtar komai, yanzu ya basu dama zasu dama shikuwa ko oho, ta godewa Allah da kurma be dogara ga sarautar ba, sam shi busineses d'insa yake kuma masu kawo ci gaba da samu me tsananin yawa, dabadan hakaba daya kad'e bashida madafa sam!

Barra replying message nasa tayi da "On My way to ur part" sannan da sauri ta kama hanyar dukda tafiyar akwai nisa sosai bako kad'an ba.

A bed room nasa ta taddashi ya had'a kai da gwiwa abin tausayi, zama kusa dashi tayi ta dafa kafad'arsa, a hankali ya d'ago jajayen idansa ya sauke su a kanta, yau bayajin yin bayanin da hannayensa ko kai dan haka jotter ya janyo da biro ya rubuta

"Ant please help me out, Am not ready to marry 2 girls, bama d'ayaba mena musu, kowama ya zama munafiki so suke su kasheni, yes zan auresu but ayishi d'aya bayan d'aya shi d'inma banan da sati biyu masu zuwaba, su barni in huta for a year or 2,please aunt help a soul" Kallon sa tayi yanzu kam kanta a matuk'ar d'aure, cikin mamaki tace

"Two girls @ a time how? Jotter ya karba ya zayyane mata komai da yanda sukayi da Sarki ya kara da cewar

"K'imana ya zube Aunt, Me martaba kawai ya gayawa Sarkin Baiha komai batare da shaida ko hak'ik'ani ba, kawai ni an wulak'an tani" Nisawa Tayi sannan tace tana mik'ewa

"Ya isa haka Mood, yanzu kam gwanda masarautar nan ta girgiza kowama ya huta, i will have to act fast" Rik'o hannun ta yayi ta waigo suka kalli juna, saketa yayi ya had'e hannayensa biyu idanshi ya saukar da ruwa har saman wuyansa, alamun ta taimakesa he's deeply in pain, share k'wallan idanta tayi sannan tace

"Prince calm down kaji, komai ze wuce soon inshaa Allah" Mik'ewa yayi ya sake d'akko jotter d'insa ya rubuta

"That piece of trash! tabar nan b'angaren please" Dariya tayi dukda k'walla ne a idanta sannan ta gyad'a masa kai alamar ok.

******************
Kai tsaye wurin mahaifiyar ta taje a fadar SARAUNI, Sarauni bahar tana ganin Barra ta washe baki tare da gyaran zama a saman kilisarta, tsohuwa shekaru sunja amma se dad'a jin izzar mulki take da cikar kamala, zubewa Barra tayi ta gaisheta sannan tana fara ta amsa tace

"Barratu, Bahar tana fushi dake! gabaki d'aya bakya ziyartar Fadar Sarauni sekinada matsala ko" Murmushi tayi har duka hak'waranta suka bayyana, sannan tace

"Bahar afuwan, kinsan ina zuwa aiki, kuma wannan yasa koda wane lokci ina makale dake awaya" Tab'e baki Bahar tayi

"Tambad'a banza, yooni wannan wayar dakike damuna dashi ciwon kunne yake sakani, tuni na la'anci me k'erin waya" Dariya tayi dama tasan dirama se anshata anan yanzu zata fara la'ance la'ance

"Hakuri zakihi Bahar, waya zamanine yazo dashi domin sauk'ak'a mana al'amura" Tab'e bakin ta k'ara yi

"Na la'anceta dai niba ruwana, zamanin ma na la'ancesa, yazo ya sauya mana komai, banda lalacewar zamani da la'ancewa ace sarauniya guda tana yawo da yagaggen zani irin na jikinki Barratu, ina kayan jida mulkin naki duk kin watsar, da anyi magana kice zamani la'antacce" Wannan dalilinne ya sanya Barra sam bata zuwa wurin Bahar, masifaffiyar tsohuwa ce tamkar ba itace ta haufe taba,ga bakinta ya saba da kalmomin da irin na rashin dad'i da dinga la'ance la'ance kenan indai abu be mata

"Bahar nifa wata magana ce ta koroni wurinki" Kallonta tayi

"Dama ince nikam ai banza bata tab'a kai zomo kasuwa har abada Barratu bazakizo gaisheni ba se inkinada matsala, kamar bani na haifeki ba, nidai ban tab'a la'antar kiba, banda albarka ba abinda na tab'a saka miki amma sekace na tsinance miki bakya zuwa neman tarin albarka" Nisawa tayi, satin daya gabata ma iwar haka a wurin Bahar ta wuni me takeso ta mata ne wai?

"Bahar sharri akawa kurma akace yayiwa wata fyad'e, yaran nan yace bashi bane amma sun kafe akan lallai sesun aura masa ita, bayan haka suka dad'a cewa zasu aura masa 'yar sarkin masarautar Baihatul mulk Khairiyya, dududu shakarun kurma nawa dazasu aura masa mata biyu, kuma ba wacce yakeso, nayi nayi Mami ta taimaka ta dakatar da abun itama ta goyi bayan su, narasa yanda zanyi shine nazo wurinki kawai" Mik'ewa tayi jikinta har yana rawa

"Wasu la'anan nunne suke tattalin yiwa Hammude sharri? aiko wlh sesun san shayi ma ruwa ne, sena tsine musu yau, shikuwa Tahir harya isa? a harya isa ya yankewa Hammude hukunci inada rai ban saniba, idan na mutu yaya kenan? la'ana suke nema zanko la'ancesu ayau, fyad'e a zuri'ata, aimu ba la'anannu bane ba bare wani acikinmu yayi fyad'e, tashi muje fada" Barra ba haka take soba, a nutse takeso ayi komai, amma taga Bahar ta d'auka da zafi

"Bahar ba haka ya dace kiyi ba, a nutse ya dace muyi komai" Harara ta wurgawa Barra

"Kina haukane? La'anace akaina dazan bi wannan maganar a hankali? ai wannan tambad'addiyar maganar ba abin bi a hankali bace, niba tambad'add'iya bace ba bare nabi komai a sannu" Mik'ewa itama tayi

"Bahar kinsan halin me martaba, Allah yaa Tahir seya b'allani, sedai kije ke kad'ai" Hannunta ta kamo

"La'anace zata hau kan duk wanda ya nemi miki koda kallon banza ne, kurma meya musu, bawan Allah, ga yanda Allah ya haliccesa kuma bazasu barshi ya hutaba, tunda yaran nan ya taso yake ganin tasku, dududu shekarun sa nawa, Tahir yana sani yamun wannan sharrin, danyasan k'a'ida sarki baya magana biyu shine ze zalincin yarn nan, wannan karon wlh sedai nabar masa gidan amma seyayi magana biyu" Nan danan tasa kuka abinda ya rud'a Barra, shisa taso b'oye maganar bataso Bahar taji dantasan tsohuwar yanzu zata tarwatsa masarautar!!

**************
Bilal yayi iyakacin kok'arin sa wurin samun lambar Princess Riyya amma sam bata tafiya, kwata kwata ma ba'ace masa komai kiran yake katsewa, yashiga damuwa me yawa, gashi acikin kwana biyun nan ya fahimci cewar ba sa'ar sa bane ba,dankuwa ko a school d'in ganinta ya masa wuya, yama rasa tsakanin soyayyar ta da kuma son zaluntarta wanne ne yafi dakumsa, yaudai yaci alwashin ganinta kota halin yaya, bazeyiyu kawai tazo tayi tafiyarta a banza ba, alhali yanaso ya jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya koba komai the way her taste is super amazing, yakosan tsohuwa da wannan dad'in yakenan awurin yarinya...... Luckly for him yana zuwa school se gashi sun had'u a mini mart, tana zaune a cafteria tanacin chips with salad, da fara'arsa ya zauna a kujerar dake fuskantar nata

"Good morning your highness" Ya fad'a yana me washe bakin sa" Batako kallesaba tace

"Morning, can u excuse me please?

"Your highness baki gane niba? Kallon wulak'anci ta dire masa sama da k'asa sannan ta wurga idanta kan agogon hannunsa ta k'are masa kallo na wuccin gadi, she hate cheap people though dai yana girmamata but he's too cheap for her as friend,cikin k'yama tace

"Aughhhh disgusting" A sarari, d'an karkace kansa yayi tamkar bejiba

"Pardon? ya furta yana me k'ura mata ido, gajeran tsaki taja

"Waye kai? wani k'ululun bak'in cikine ya tokare k'irjin Bilal, shi yarinyar nan zata rainawa hankali? cikin tsananin b'acin rai ya kalleta amma ina, baze iya fad'a ba, baze yadda tayi nasarar wargaza masa shirinsa cikin sauri haka ba, dannewa yayi ya k'ak'alo murmushi

"Bilal ne your highness, wawan gayen daya b'ata miki rai kwana biyu a cafteria nan, damuka zama friend's harna karb'i number wayarki? D'an shiru tayi tana yamutsa fuska kafin tace

"What is the code then?" Ta k'arashe maganar tana wara yatsunta k'waya biyu dasuke d'auke da manya manyan Nails farare tas se shek'i sukeyi.... Wasu yawu ya had'iya kafin yace yana nazari

"3753" A tak'aice, murmushi tayi sannan tace

"Good, zan yadda cewan kai friend d'inane sabida ka fad'a wannan code, badan hakaba ni bazan iya tuna inda naga face d'in kaba" Shiru yayi yaba zuba yak'e ita kuwa ta zauna tas ta cinye abinta sannan ta mik'e da zummar barin wurin yace da sauri yana kallonta

"Your highness ke nake jira fa" Sauke wata nannuyar ajiyan zuciya tayi sannan cikin kosawa tace

"Immaka me? Dukda yaji zafin kalamanta amma seyace

"Dama so nake ince dake wayanki koyaya nayi trying bayya tafiya" Yamutsa fuska ta kumayi kafin tace

"Did u try sending the code" shi ta soma k'ular dashi komai turanci ubanwaye be iya turancin ba, shegiya da iya kirsa kamar uwarta ya fad'a a zuci, a sarari kuma seyace

"Pardon i dont grab" "Idan harni na baka number na then try sending the code via sms to me, i will save ur number then zaka iya samuna,if not har abada bazaka sameni ba" Mik'ewa shima yayi

"But ur highness kene da kanki kika bani number ai" Ya k'arashe maganar abun tausayi, tab'e baki tayi

"Thats the main reason why i need to confirm, see i dont normally give my number to stranger's, and when ever i do i need to confirm first, so if kanaso ka kirani ka samu send the code for confirmation" Tana kaiwa nan ta soma tafiya bin bayanta yayi

"Your Highness the code is 3753"

"Via sms" Ta furta dad'an k'arfi sannan ta k'arawa tafiyarta sauri zuwa barin inda yake........Tsayawa yayi yana kallonta harta b'acewa ganinsa, gaba d'aya ta rikirkitasa @ first ya zata ya gama kamata a hannu, se yanzu ya gano cewar da sauran rina akaba, seyabi da lallab'awa kenan, amma ba komai kowane irin wulak'anci ze jure harseya cimma burinsa akanta kamar yanda uwarta tayi masa,tun yana d'an shekaru 17 yanzu gashi yana 25 amma bata bar tsuliyar sa ta hutaba kullum yana kanta yana sukuwa!

******************

Lokacin da Bahar ta fito daga fadar Sarauni kai tsaye fada ta wuce jikinta har rawa yake, hannunta rik'e da hannu Barra, se zare ido barra keyi alamun rashin gaskiya ita sam ba haka tasoba, so kawai tayi Bahar Sarauni ta nemi Me martaba daban bawai fad'a a fada ba! Seda suka shiga har cikin fada sannan ta saki hannun Barra ta daidaita nutsuwarta, gabaki d'aya mutanen fadar dake zazzaune sunyi zaman tamutela suna fuskantar juna ana tattauna maganganu masu muhimmanci ganin Bahar Sarauni mik'ewa sukayi suka sunkiya suka gayar da ita ta kwashesu kawai ta zubar bata amsaba, Barra kuwa jikinta se rawa yake dan kuwa ganin yanayi irinna sarki ya tabbatar mata ya gane me tayi, bayan sarki ya mim'e ya gayarda mahaifiyar sa dama tsarin fadar akwai wurin zaman manyan iyaye irinsu wanda yake agefen sarki idan maganar dole ta kama sesunzo to anan suke zama, Bahar sarauni bata zauna ba dukda tayin zaman da akayi mata ta kalli d'aukacin 'yan fadar tace

"Waye yazo da maganar yarinyar da ake cewa Hammude kurma yayiwa fyad'e?" Tsit fada ta d'auki shiru tamkar ba kowa agun" Gyaran tsayuwarta tayi

"Bazan k'ara maimaita tambaya naba, amsa nake jira" Me martaba ne yace

"Ammu Bahar, D'annGaladima ne da idan fada suka ganshi suka tabbatar da hakan" cikin takaici tace

"Suka ganshi k'irik'iri akan 'yar mutane yana mata fyad'e? Da sauri kowa ya kalleta

"Ba haka bane Ran Bahar ya dad'e" Sarki ya fad'a yana k'ara k'ask'antar da kansa cikeda ladabi

"Inajinka gayamun da bakinka yanda komai ya faru" Seda sarki ya kalli mutanen wurin sannan yace yana gyaran zaman rawanin sa

"Ku bamu wuri" D'aga murya tayi

"Zan La'anci duk la'anannen daya fita daga fadar nan, tare daku aka k'ulla agabanku za'a warware komai, Kai Tahir maza ka aika kiran Hammude da gaggawa" Cikin girmamawa ta bada umarnin kiram kurma, sannan ya fuskance ta sosai ya kwashe komai ya sanar da ita, seda yakai aya sannan tace

"Su waye shaidun kace"

"D'an galadima ne da kuma idan fada"

"Su waye idan fada, munafukan fada zakace, kai Tahir ashe bakada hankali? me irin tunaninka samshi ba sarki bane, ban tab'a ganin sarki mara adalci irinkaba, katab'a gani ko a hikayar marasa hankali mutum yayiwa yarinya fyad'e daga waje ya kawota gidansu to tamasa me? tukunna ma ka saurari nashi b'angarin dalilin kawota gidan? Cikin sanyin Jiki yace

"A'a Ammu, naga zahiri shisa ban nemi jin mezaice" Dage gira d'aya tayi ta k'ank'ance ido

"Zahiri kake k'ara gayamun ka gani, Tahir anya sanda malamin islamiyyar ku ke zuwa kana saurarar sa kuwa? bakasan musulunci baya karb'ar shaidun zinaba harse mutane hud'u sun shaida sunga mazinatan turmi da tab'arya, kai jini kawai shine shaidarka, tukunna ma wai ka shirya gayawa Allah ka sauya nashi shaidun zuwa naka dankai sarkine? cikin rawar murya yace

"Subhanallahi, Ammu ba haka nake nufi ha wlh" Suna haka segashinan ya shigo yauma kamar kullum da gudun sa, a gabanta ya tsaya ko haki gudun be cika sakashiba sabida ya zame masa d'abi'a, dafa kafad'arsa Bahar tayi tace

"Harse yaushe zaka dena wannan guje gujen Hammude? Murmushi ya sakar mata abinda yake fin wata beyiba sannan ya mata alama da hannu akan ze dena" Tana murmishi tace

"Nasanka da saurin rubutu, maza mazq rubutamun duk abinda ka sani akan yarinyar da ake zargin ka mata fyad'e" Jinjina kansa yayi lokaci d'aya annurin fuskarsa ya kau, ya zaro jotter da pen a aljihunsa, cikin lokacin dabe gaza 10mns ba ya fayyace labarin iyakar abinda ya sani!!!!!

Barra ce ta karance tsaf a tsanake kowa yayi tsit yana sauraren ta harseda ta kammala.Nisawa Bahar Sarauni tayi yanxu kam ta fahimci duk abinda ya faru, tana jinjina kanta tace

"A matsayinmu na masu hankali be dace sabida munga jini acikin yarinya muce fyad'e aka mata ba, musamman shi jinin kawar da budurci baya zuba bare harya d'iga, kai Galadima baka tab'a kawar da budurci bane, kainkuma D'an galadima kaima matanka biyu ko dukkansu ba sabon takinka bane ba, Sarkin yak'i kana me akayi wannan shirmen ina matanka hud'u harda k'wark'wara? so kake kacemun bakasan jinin kawar da budurci ba, kaikuma sarkin baka, inace matanka uku, dukkanin ku anan kunada mace sama da d'aya cikin hadda sarkin ku? idan har kun d'auka yawan jikin daya zuba haryana d'iga ajikin yarinyar jinin kawar da budurci ne to kuwa dukkanin ku anan an rigaku takin takalminku, in hakane har sarki sena saukeshi a kujerar mulkin sa? kokunsan a k'a'idar mulkin k'asarnan idan ka taki takalmin sauri a matsayin auren fari baka mulki? Kame kame kowa ya hauyi, atake ta tsawatar akayi tsit ta waigo ta kalli D'an galadima ido cikin ido tace

"La'anannen nan dukshi ya shirya komai, soyakeyi tarihi ya maimaita kansa, ba'a rufin asiri nina rufa maka, idan tunanin ka zanje kabari da sirrin ka tokama janye, d'anka yana naj ajiye, kuma kafin aurenka kayiwa baiwar ciki niwa na gayawa? na tilastaka aurenka ne ? abinda kake gudu nan gaba kad'an asirinka ya tonu mulki ya tashi a hannunka, hak'uri zakayi rashin kamun kanka ya b'ata komai, magaji kuma kurma ne, koda kuke cewa kurma ne kunyi kuskure, kurma shine wanda bayaji, Amma Hammude yanajin magana tsaf, lalurarsa a harshensa take bawai a kunnen saba, kuma inshaa Allahu ze mulkeku koda bakwa so, ina abun yin Allah ne bana la'anannun Allah bane irin ku" Kowa yayi tsit taci gaba

"Da D'an galadima da idan fada, suje su yad'a cewar Bahar tayi bincike ta gano cewar yarinya jinin hailarta ne ya zuba a k'asa bana kawar da budurciba, Kurma taimakonta yayi kamar yanda kukaji bayani yanzu a kuma tabbatar cewar lallai munafukai sunyi nasarar da kowa ze wanke kurma daga zargi" Amsa mata akayi cikeda ladabi ta waiga suka fuskanci juna da kurma tace cikin nutsuwa

"Acikin yaran guda biyu da akeso a aura maka waccece kake so,waye kuma bakaso, idan duka kana sonsu zansa a aura maka dukkansu, idan kuma duka baka sonsu zan tsinewa wanda yayi gigin koda tashin maganar ne in la'ancesa har k'arshen rayuwarsa" A hankali Kurma yake kallon ta ya gama karantar iyakar gaskiyarta kenan, sauke idansa yayi zuwaga mahaifin sa cikeda kulawa danyasan akan sa aka tozartar da mahaifin nasa agaban bayinsa da mukaraban sa, bashida zab'in daya wuce zube idanshi a wurin da ake kallon sa, gaba d'aya jikinsa yana bashi Uncle Jay yana kallonsa, jira yake yaji mexaice, kallon juna suka tsayayi na wuccin gadi, ga Uncle Jay acikin manyan fada a jere dan kuwa shine wakili a wannan masarautar amma ba bakin magana, seda ya gama karantar zuciyar uncle Jay sannan ya mayarda dubanshi zuwaga Bahar Sarauni......

******************

*To nima dai gani na kasa kunnen sauraren wacce kurma xe zab'a, shin anya ze zab'a kuwa, befasan koda fuskar khairiyta ba, gashi ya tsani Yar shara.....*


*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*JOIN OUR TELEGRAM PAGE THROU THE LINK BELOW*
https://t.me/joinchat/FgfKMiS_mYc-DIjC.

*Assalamu Alaikum, Readers hak'uri zamuyi da juna, kui hak'uri zakuyi inkeyin post yau gobe bazan yiba, kunga ina sab'a alk'awari gwanda na daina, dan Allah kumun wannan alfarmar, Nagode.*

   *SHAFI NA BAKWAI*

Jotter sa ya mik'a hannu ya karb'a a hannun Barra sannan ya rubuta

"Bahar i will marry them both, but please not now, se bayan shekara d'aya, and lastly i want to leave the country kafin lokacin auren, i really need some fresh air, this place is like a hell, bazasu tab'a bari in samu nutsuwaba" Barra ya mik'awa seda ta karance sannan seta sauya maganganun daga yanda yayisu, tace tana kallon Bahar

"Ammu Bahar, yace ze auri yaran duka amma yana neman alfarmar abari senan da shekara d'aya, kuma dan Allah a rok'a masa izinin sarki yanaso yabar k'asar kafin zuwan lokacin sabida akwai wasu ayyuka dazeyi k'asar dazeje" Nisawa Bahar tayi dajin hukuncin daya yanke tace a nuste tana kallon sa

"Kada tsoron wasu la'anannu ya sanya ka amsa abinda bashine bane aranka, ka tabbatar haka kakeso? A hankali ya gyad'a mata kai, yayinda me martaba ya sauke wata nannauyan ajiyan zuciya, ta waiga ta kalli Me martaba tace

"Hammude ya zab'i barin k'asar, yakuma ce aure zeyi dasu duka amma se bayan shekara d'aya sabida haka yanda yakeso haka za'a masa, a k'ara masa da miliyan goma sabida yanayin tafiya, a bashi bayi maza da mata ko wanne b'arin k'waya goma sannan kuma kamar ko yaushe a karrama tafiyarsa" Badan sarki yaso hukun cinba ya amsa komai da "to"

"Yarinyar  da ake magana akanta a mayarmun ita b'angarena kafin musamu iyayenta,kuma kafin ta samu lafiya" Nanma To aka amsa mata dashi ba musu ta kuma cewa

"Tafiyar sa Nanda sati biyu nakeso a shirya komai" Cikin girmamawa Sarki yace

"Amma ya dace yaje yaga ita Khairiyya d'in, tunda yake ba sanin juna sukayi ba Ammu, kinga daganan ma sesu fahimci juna kafin yabar k'asar kuma" Jinjina kanta tayi alamun gamsuwa sannan tace

"Zeje ya ganta" Iyakar abinda tace kenan ta juya, Barra da sauri tabi bayan ta cikin sassarfa, gogan ko motsawa beyi ba daga inda yake har ammu dabar fadar, Me martaba yayi fushi sosai da faruwar wannan tozarcin, Takowa yayi har zuwa gaban hammood ya tsoma idansa ana sa, shikuwa yana nan tsaye tamkar wani statue, ganin idan Me martaba ya masa k'warjini ya sanyashi sauke nasa idan a k'asa acikin zuciyar yace "Abi am so sorry" A sarari kuwa idan nan yayi jajir, cikin murya kamar meyin rad'a Me martaba yace

"You broke ur promise Hammood, haka mukayi dakai? da dare ka sameni a taska" Lumshe idansa yayi yana tunano alk'warin dayayiwa mahaifin nasa amma ya zeyi, Abi d'insa ya sauya masa, Abi ya soma bin maganar mazuga, Abi yabi layin masu yi masa caaa a kullum, Abi yana d'aukan komai dayaji da zafi akan sa koda bekai abun zafi ba ya zeyi? D'aga masa kansa kawai yayi alamar to ya kauce daga wurinsa ya juya, yau beyi guduba a hankali ya taka har gaban D'an galadima daketa muzurai cikin tashin hankali, kallon juna sukayi na seconds haka, sannan se Mood ya soma wani shu'umin murmushi a hankali har Murmushin sa ya koma dariya

Please Login or Register in order to submit comment