Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahaifiyar ki 'Yar shuwa tayiwa sarki sena tona" Da sauri Barira ta zube a k'asa dan wannan sirrin ko Ameena batasan dashi ba

"Ki rufa mata asiri Ranki ya dad'e, wlh duk abinda kikeso zanyi" Murmushi tayi ta kuma gutsirar chocolate d'inta kafin tace

"Karkuyi tsammanin na gaya muku sirrina dan banida wayo, banzo fadaba seda na shirya, neman duniya shine abinda ya fitondani, na gaya muku komai ne daya dace ku sani sabida kusan Ni Hafsatou ban fitoba seda na shirya" Amina manyan munafukai take jiki ya d'auki rawa

"Ranki ya dad'e duk abinda kikeso wlh shi za'ayi, bamu isa muja da maganarki ba, sarauniyar masarautar Dinar inshaa Allahu" Wata dariyar jin dad'i tayi sannan tace

"Ke Barira idan na gama shirya tafiyar ki zaki tafi, ke kuma Amina duk wani aiki da Idan fada suka sakaki ki fara gayamun ni zan gaya miki abinda zaki fad'a musu, sunga alamun inaso na musu zarra shisa suke mun b'oye b'oye, da farko sanda suka turoni aiba haka suke mun ba, nice da masarauta ku bini a hankali ku zauna lafiya" Amina tana fara'a tace

"Ai Ranki ya dad'e mu shaidane akan irin yanda Yarima Hammood yake tattalinki, ko ciwon nan dakikayi waccen uwar mulkin seda suka sab'a da juna, Allah dai yabar k'auna" Tab'e baki tayi

"Ni MOOD bawai ya wani dameni bane, kawai mulkin nake kwad'ayi" Nan suka dinga fadanci itadai ta basu wuri, tana barin wurin ta kira Nigeria, bayan sun gaisa da wacce ta kira tace

"Komai yana tafiya yanda muka tsara, a b'angaren kuyangin khairiyya ma na saye biyu daga ciki, nakuma tsoratar dasu, sedai a tayamu da addu'a Allah ya bamu sa'ar ceto Hammood daga wannan mugwayen mutanen"

"Ameen aka fad'a daga d'ayan b'angaren sannan sukayi sallama.... Hafsat ta wuce zuwa cikin gida tana mamakin sharrin mutane, dukda batada ishashen lafiya sanda suke maganar tona masa asiri amma tanajin su tas, bayan haka wasu abubuwan tana sani take yinsu, ta d'aura niyyan taimakon Hammood dankuwa dabe taimaketa ba da yanzu batasan inda take ba arayuwa. Shikuwa da tun sanda suka fara magana a garden basu san yana nan zaune a cikin manyan itacen banana yana shan islaba, runtse idansa yayi, tabbas shida Hafsat sesunga bayan juna, baze tab'a bari tayi nasara akan saba, su dama wad'an nan yasan da zamansu manya manyan munafukan fada musamman Amina, yajima yana zargin tasan wasu acikin Idan fada, su zuba ita dashi, wato Ita Hafsat aurararsa takeso tayi danta samu dukiya? Shida ita za'aga waye zewa wani kaye, ba boka ba ko shed'an ne akanta seyaga iyakarta.

*Toooh jama'a yanzu littafin tsintar aya ya soma zafi, yanzu ne za'a tsinci iyakar tsakuwar dake cikin ayar, gadai 'yar shara ta d'aura d'amarar taimakawa hammood, amma shi ga abinda yake tunani, shin wazefi shan wahala acikinsu? Shin waye yake baiwa Hafsat information akan su Ameena? Su waye Idan nan na fada? Anya Hammood be d'auka da zafi ba kuwa? Ku biyomu muci gaba da tayasu tsince ayar don ganin inda wannan abun ze kaimu, sonso masoyana kuyi hakuri jiya ban cika alk'awari ba*

*Mom Nu'aiym*

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS*



Mik'ewa yae yana zagayar wurin, kanshi ya d'auki zafi sosai, shin a ina Idan fada suka samo wannan yarinyar? Anya kuwa wannan mutum mace kuwa, gaba d'aya be fahimci zuwanta a rayuwar saba a baibai, ta hanasu fad'n abinda suka gani to kenan shiri take akan ta gaya musu da kanta amma se yaushe? Mesa zata hanasu magana akan hakan? Ba yau aka fara zuwa ace yana magana ba, ba yau aka soma ba'a gansa ba aje ace an gansa sabida kawai anaso a tabbatar da zargi, babban abinda yafi damunsa shine besan su waye idan fada ba, amma gashi Hafsat tace tasan su ita, idan har so take tayi wasa da hankalin sa akan idan fada, idan so take ta kwashe sirrin sa ta gayawa Idan fada to yanada maganin ta, zeyi amfani da ita shima, ze wasa k'walwar ta, dama burinsa yasan su waye idan fada, togashi tace ta sansu bara ya barta sesu buga wasan bari ya gani shida ita waye zeyi kaye.

*************
Shiru d'akin taron ya d'auka ana jiran isowar shugaban k'ungiyar, mutane sunkai su ashirin kowa yayi tsit aciki talatainin dare, se k'arfe biyu daidai sannan shugaban ya shigo ya nemi kukera ya zauna kowa ya mik'e seda ya zauna sannan auka zauna suka gayar dashi tammar yanda suke gayar da sarkin Daulatur Dinar, bayan yayi gyaran murya seya fara magana kamar haka

"Anyi sanya sosai da aikin da aka baiwa yarinyar nan, ance shekarunta 17 anya batayi k'ank'anta ba? Shiru shiru babu wani k'wak'waran bayani daga wurinta yanzu watannin su nawa kenan a k'asar, tahau jirgin banza taje tanashan sanyi a turai ana bata kudad'e amma aikinta sam baya gudu mekenan muke zaune wangale da baki muna jira? Bazata iyaba a datse mata hanyoyin sadarwa inaga yafi" Seda yayi shiru sannan wani daga cikin su yace

"Inaga ba haka zamuyi ba, zaburar da ita zamuyi, a firgitar da tunaninta yanda aka saba, kada muzo ya samu wani ci gaban amma bamu sani ba" Bece komai ba wani daga ciki ya kuma cewa

"Shugaba inaga a matsayin mu da manya masu kaifin tunani sanadi kawai zamuyi masa daze dawo Nigeria, sanda yake kusa damu ai munyi nasarar shiga tsakanin sa da mahaifinsa,kokuma mu kasheshi kamar yanda tun farko mukaso, a wannan karon semu kashe har sarkin sannan mu namu sarkin seya maye gurbin su, danmu har duniya ta nad'e kaine sarkin mu, kuma da izinin Allah kaine zaka zamto jagoran talakawa nanda lokaci k'ank'ani, ko babu komai mahaifinka shine da sarautar nan bashida wani magaji kuwa sekai" Murmushi yayi najin dad'i kafin yace

"Tabbas lokaci yayi dazan nunawa mutumin nan iyakar sa, nayita kallon hankalin sa akan ya bani sarautar nan tunda gadon ubanace amma shi ta kansa kawai yakeyi se d'an cikinsa, nikuma ya mayar dani ko oho, zargina akan tabbas Hammood yana magana yak'i ya tabbata tunda be tab'ayi agaban kowa na, ansha a bisa masallaci ko shago ko dai wani wurin daba gidaba amma sam baya magana, yanzu akwai mutanen mu a U.S takanas nayi sponsoring nasu suke bibiyar sa amma narasa gano kan yaran nan sunce har acen baya magana, sabida haka kasheshi kawai zamuyi, dama naso ace yana magana ne sena tabbatar sena kashe sa, yanzu kuwa kurman gaskene to kuma uban bashida niyyan hanashi sarautar dukda cutar kurumtar daya gada awurin uwarsa, gwanda baya doron k'asar, gwanda ya mutu in huta da zullumi, amma shin anan zamu kashesa kokuwa?" Wani daga cikin su ne yace

"Shi wannan mutumen dasuke kira sarki bashisa adalci kuma be cancanci ayi masa sassauci ba, mahaifinka rik'on k'warya kawai ya bashi se Allah yamai rasuwa shin base ya mayar maka ba?, A'a sabida zalunci seyayi tazarce yace kai yarone a wancen lokacin yanzu ka hayyafa kayi gemu harya fara zama fari amma yana ihun cewar d'ansa ne magajin sa wannan ai mugun xalincine dan haka jininsa dana d'ansa ya halasta, dama duk wanda yakeso ya gifta maka bayan su" Gyaran murya ya kumayi sannan yace

"A shirya masa mugunta, a shirya masa makirci, a lafta masa k'aya ayi duk yanda za'ayi ya dawo Nigeria shida iyalin sa da ajayi masa auren gata yana kurma, ita gaggawa aikine dake b'ata dukkanin shiri sabida haka bazamu aiki da gaggawa ba, amma iyalansa dayake aure zasu shiga cikin sahihin shirin salwantar mana da tunanin sa zuwa tafiya me gangara" Dariya sukayi dan kuwa duk sun gane yaren seda suka tsahirta yaci gaba

"Munada labarin uwarta, muna kuma da labarin ita kanta duk a wurin wani saurayi me suna Bilal,yaran da yakeda video na komai daya shafi lalacin uwarta da ita kanta wanda yayi da ita, ayi amfani da wannan a girgiza duniyar ta, lallai koda k'arfin tuwo ne semun k'wato mulkin dayake mallakin mu munci gaba da wanzar da adalci a wannan masarautar" Nan surutai sukaci gaba na yanda za'ayi tilas Hammood da iyalansa su dawo Nigeria!

**************
*Shin ina labarin Bilal?*

Tun bayan da Bilal ya dawo garin seya samu kansa da bak'in cikin rashin cimma burinsa akan khairiyya, gabaki d'aya hankalin Bilal be kwanta ba musamman saya samu labarin aurenta da d'an sarkin garin dayake zaune, daganan seya k'ulla alak'a da wani yaro me suna Sabir wanda a masarautar yake zaune yana d'aya daga cikin 'yaran kuyangin gidan wanda baya aiki sedai yakanje shago a kasuwa, kuma babu laifi yanada abun hannun sa daidai gwargwado. Bilal ya bashi dukkan dama, hadda kyautar dubu d'ari uku akan ya k'ara jari, Sabir kuwa wannan batu ya masa dad'i yaji a duk fad'in duniyar nan babu wanda yakeso sama da Bilal...... lokacin da tafiya tayi tafiya a tsakanin su wata rana suna zaune agidan Bilal ya gayyato Sabir suna tsakiya dacin abinci se Bilal ya dire cokalin hannun sa ya kallesa yana murmushi yace

"Sabir ina inama nine kai? Ina matuk'ar k'aunar rayuwar sarauta koda kuwa daga sama ne kawai ace gani acikin babban masarauta bad'an kuyanga dake da matsayi ba, kod'an baiwa zanzo danayi farin ciki" Murmushi Sabir yayiwa uban gidan sa yace yana kallon sa

"Ranka ya dad'e rayuwar fada dakake ganinta gaba d'aya ba rayuwa bace me dad'i, banda k'iyayya hasada da kuma bin juna da sharri babu abinda yake cikin sarauta, bamawai awurin wanda sukeda sarautar ba ko magadan sarautar a'a wlh hatta wurin mu 'ya'yan bayi da kuyangi kowa hassada, kowama ji yake tamkar ya kashe d'an uwansa kaga yanxu akan sarautar gidan nan gaba d'aya akwai wata kafaffiyar k'ungiya anrasa waye shugaban ta, sannan koda kai member ne bazaka tab'a sanin wani member ba a k'ungiyar dan kuwa ance se cikin dare suke meeting kuma acikin duhu sukeyinsa sannan kowa da lullub'i a fuskar sa, shugaban k'ungiyar shishi kad'ai yasan kowa, kuma amma zakakeyin waya dasu da sauransu, kamar a film fa, su burinsu kawai su hallakar da sarki da d'an sarki kai ayanda naji ma sune suka kurumtar dashi, kuma baka sani ba ba akan gaskiyarsu suke so suga bayan bayin Allah nan ba wlh, sharri ne kawai irin na d'an adam, anace da k'ungiyar aci duhu amma mu dabamu sansu ba munace dasu idon fada, komai sun sani kuma idan kashiga kace zaka fita bazasu hanaka amma baka isa kayi awa ba'a lahira ba" kallon sa sosai Bilal yayi yace

"To yanxu kai duk ina kasan wannan labarin idan ba cikinsu kake ba" k'urawa juna ido akayi tsakanin Bilal da Sabir na wani lokaci kafin Sabir yace

"Ina d'aya daga cikinsu, sedai kuma aduk duniya kai kad'ai kasan wannan maganar, mahaifiyata ta hanani shiga k'ungiyar amma dolece ta saka na shiga sabida sharrin da akayiwa mahaifiyata, kuma sune suka nemeni akan in k'watar mata hakk'inta" kallon sa Bilal yayi yana wata shak'iyiyar dariya seda ya lafa sannan yace

"Amma kai Sabir wane sharrine zekaika k'ungiyar dasuke iya kashe mutum" Nisawa yayi kafin yace

"Bansan da sharad'in ba seda na shiga kaga ba zancen fita, bayaga haka kuma suna mana albashi duk wata dubu d'ari sabida basu information" kallon tsanaki Bilal ya masa sannan yace.

"Mecece ma'anar k'ungiyar?" Seda Sabir ya d'an waige waige sannan yace "Ture wannan Mulkin sukeso suyi su d'aura nasu sarkin, abinda kenan shine shi sarki meci yanzu yayansane uwa d'aya uba d'aya ya sauka akan mulkin, koda yake ciwo yayi to bayan yayi ciwo seya zamana baya komai kuma babban yaransa be wuce shekaru goma sha biyar na seya d'aura k'aninsa rik'on k'warya seya zamana ya rasu kafin ya warkewa ciwon tofa shine k'anin aka rad'ashi sarki, shikuwa ya kafe sarautar ta ubansa ce abar masa bayan daya girma kenan shiko sarki d'ansa yakeso ya gaji sarautar, to duk wata fitinar data taso a k'ark'ashin wannan mulkin ne" Gyaran zama yayi kafin yace "please tell me more" Murmishi sabir yayi kafin yaci gaba

"A yanzu haka so suke su samu dalilin daze hanawa D'an sarki meci yanzu wato Hammood yin sarauta, kaga sarki idan matar farko daya aura bashi ya fara tarawa da itaba to kuwa baze tab'a mulki ba, an camfa akan idan akayi haka lallai masarauta zat rushe tun kaka da kakakanni, sannan basa son nakasasshe kuma shi kurma ne da farko ammaya samu lafiya yanzu yanaji amma harshensa baya motsi ma'ana baya magana sam" Hannu Billal ya d'aga masa yana murmushi sannan yace

"I've heard enough dakata anan" k'ara nutseshi yayi da ido kafin yace

"Kanaso ka zama gwarzo sosai? Well respected acikin wannan k'ungiyar ka zama kaine kan gaba bayan shugaban k'ungiyar? Murmushi Sabir yayi

"Ranka ya dad'e ai akwai manyana" Shafar gemunsa yayi kafin yace

"Yaro kazo a sa'a ina k'aunarka sosai, ina tsananin sonka Sabir, kasan me? Kallonsa kawai sabir keyi yace

"Inada video na matar Hammood tsirara muna aikata masha'a kafin tayi aure, kuma har wanda nayi sa uwarta inada, kaga idan kashiga k'ungiya bame sanin ka tonima a shigar dani mu kai musu wannan mu tona musu asiri kaga dole a hanashi sarautar, daganan nidakai zamu shana dole a girmama mu a masarautar" Wata mahaukaciyar dariya Sabir yayi kafin yace

"How true? Wayarsa ya janyo ya kunna masa video ya tura agabansa, to waye besan khairiyya ba amaryar Hammood tabbas itace bilal yanata cakalkalarta" Dariya yayi hadda tsalle

"Me gida Allah ya k'ara girma, wlh ka biyani zan b'oye sirrrinka har abada yanzu meye abinyi" ...... Da wannan suka shigar da Bilal acikin k'ungiyar aci duhu wacce akafi sani da Idan fada, sedai kuma gaba d'aya Me neman kujerar sarki be shirya sakin video ba ya shirya amfani da matar Hammood ne ta wannan videos seyaga bayansa cikin ruwan sanyi, acewarsa idan ya sake video za'a zargesa kuma har abada baze bari a gano k'ungiyar saba kodan wasiyyar mahaifin sa........

*Tirk'ashi gadai Bilal, ga kuma khairiyya, ga hammood ga kuma Hafsatuwalle, kowa ya fito tsintar aya, ohh how time flie's, the table shake and turn very first love u bohot bohot readers.....*

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA TARA*

     Zaman fada ake cikin tsananin jin zafin juna, kowanne da abinda yake sak'awa aransa game da d'an uwansa, tsananin takaicin juna akeji a wannan zaman, gyaran murya Me martaba yayi sannan yace

,"Hammood ya bada sak'o a gaya mana ta hanyar kawun sa yana neman alfarmar a k'ara d'aura auren sa da waccen  yarinyar da abu ya had'asu a baud'e" Zabura magatakarda yayi sannan cikin girmamawa yace

"Ranka ya dad'e ayi haka? Kallon sa me martaba yayi sannan ya d'auke dubansa daga gareshi yace yana kallon Jay

"Menene kake tunanin ya dace akan wannan maganar, naso sosai hankalin sa ya soma kwanciya akan matarsa ta farko, banason rigima"  Zubewa yayi yana me bada girmamawa kafin yace

"Idan mukayi duba da yanayinsa na farko akan maganar auren zamu iya yiwa Allah godiya hakan yana nuni ne kai tsaye da cewar hankalin sa ya kwanta da iyalansa har yake sha'awar k'ari, dan haka ina ganin gwanda acika masa burinsa kawai" Magajin garine ya zube kafin yace

"Allah yaja daran sarki, banaji hakan tunani ne me kyau, idan har akayi hakan ita gimbiya khairiyya nasarautarta bazuji dad'iba sam, duba da cewar dududu auren nanfa ko wata shida be rufa ba"  Sarkin baka cikin girmamawa yace

"Mahaifin gimbiya khairiyya yasan da maganar ita wannan yarinyar ai, ai gata ya masa dacen farko kuma yanzu akan gimbiyar ai bazamu fasa cikawa yarima me jiran gado burinsa ba Allah yabaka nasara"  haka kowa da abinda yake fad'a akan maganar daga k'arshe Sarki yace zeyi tunani akai............

******************
Yau Hafsat sun tashi a aschool kai tsaye Bus stop sukaje itada k'awayenta, tunda taketa wannan ciwon tadena yawo ma sam, tana nan zaune suna jiran isowar Bus se ganin Hammood tayi a gabansu, mik'ewa tayi ganin ya jingina da mota ta matsa kusa dashi, seda suka kalli juna na some seconds sannan tace

"Yaa Mood Barka da rana" kallon sa take yanda yake wani yamutsa fuska kuma ga mamakin ta seya motsa bakinsa amma ba magana yayi ba, hannu ya nuna mata ta shiga mota seda ta gama karantar yanayin sa sannan ta juya dayiwa cylia da chidi sallama ta bud'e gidan baya ta shiga, shi d'inma baya ya zauna ya janyo New's paper ya soma dubawa abinda yake shirinyi rayuwarsa banda harbawa babu abinda take amma duk yanda yaso yaji maganar Uncle Jay yau ji yake baze iya ba, shi d'inma namiji ne, ya mallaki hankalin kansa, yanada matuk'ar muhimmanci ya yak'i mak'iyansa, yanzune lokacin daya dace ya zauna acikin mak'iyansa ya dena tsoron su ya nuna musu iyakar su....A b'angaren Hafsat kuwa Allah ya halicceta da saurin karantar halayen mutane, indai har ta nutsu mutum ya nutsu tokuwa sedai idan bashi take kallo ba, amma muddin idanta yana kan mutum to kai tsaye zata iya karantar zuciyar sa akowane yanayi suke atare musamman idan akace idansu yana sark'e dana juna, a irin hakan ta karance Bilal tunkafin ya bayyana manufar sa akanta, a irin haka ta karance halin da Bilal da momy suke ciki tun kafin ta fara jiyo sautuka muryoyin su suna shek'e ayarsu, a irin haka take janye jikinta daga duk wani me sak'a gadar zare iri biyu a rayuwar ta, Hafsa yarinyace da magana be wani dameta ba, amma tanada wayau fiye da tunanin duk wani me tunani, wayonta yakaita gacin nasara ta k'waci kanta a hannun Bilal! Wani mayaudarin murmushi ta sakarwa kanta tunawa da yanayin idan, labarin da zuciyar sa ke bata daban akanta amma idansa yana yawan k'aryata nazarin sa, zuciyar sa tak'i tsayawa akan cutar dashi zatayi idan nashi ma basu gama yadda da hakan ba, abinda ta lura dashi a yanayin sa na yanzu akwai abinda yake shirin aikatawa sedai ya gagara nutsuwa ya aikata koma menene, kawar da kanta tayi daga dubansa zuwa ga hanya taga gaba d'aya ba hanyar gida suka d'auka ba, wani siririyar dariya tayi me had'e da Hmm tana son wannan baiwar da Allah yayi mata, tana tsananin jin dad'i idan tayi karatun faifan fuska da zaren zuci ta canka daidai kanta har wani fad'i yake, d'agowa yayi ya kalleta idansu ya sark'e dana juna ko wannensu ya gagara d'auke idansa ana d'an uwansa har lokacin murmushi ne k'unshe a fuskar ta yayinda yake k'ara had'e tasa fuskar sa a zuciyar sa yanaji tamkar yarinyar nan ta gama raina masa wayau dariyar me take, k'ara fahimtar abinda yake tunani aransa ya tilasta mata k'arayin wata dariyar babu shiri wacce a wannan lokacin kasa hak'ura yayi ya damk'o k'aramun d'an k'walin data rufe kanta dashi me zubin hankici ya had'o tare da sumar kanta, idansa anata amma ga mamakin sa go gezau batayi ba, bata motsa ba, bata kuma nuna alamar taji zafin rik'on ba, d'auke nashi idan yayi anata sannan ya cillar da ita gefe yana jan gajeran tsakin daya fallasa tabbas harshensa yana motsawa ya kwantar da kansa akan jikin sit motar yarasa mesa hankalin sa yake yawan d'aukewa zuciyar sa bata masa sassauci akan kai hannun sa jikin Hafsa, besan wane irin k'i yake mata ba haka, koda yake shi halittarsa ce k'in duk wani mak'iyin sa indai har ya fahimci kai mak'iyin sane tokuwa tabbas shima daga ranar ya dena sonka har abada, driver daya gaji da shawagi dasu seyace

"Yallab'ai ina zamuje? Beyi magana ba bashida niyyan yi, har yanzu yana b'oye ainahin gaskiyar magana hafsat ce ta kallesa ya lumshe ido amma bashida niyyan magana tace

"Take us home" Bud'e idanshi yayi ya zube su tas akanta tace tana gyaran sumar kanta

"Take me home i mean, bansan inda yakeso yaje ba shi, amma ni gida zanje" Parking driver yayi ya waigo yace "yallab'ai muje gida ne?" A hankali ya gyad'a masa kai ita kuwa ta d'auke kanta ganin driver ya d'auki hanyar gida tace a sarari

"Ko'a tarihin hikayoyin da suka gabaci zamanin mu ban tab'ajin labarin ko wanda ya tab'a ganin kurma wanda takejin komai amma baya magana ba, se kai yaa Hammood kai d'an baiwa ne, sam harshen ka baya motsi" Yi yayi tammar beji taba, dankuwa ko motsawa beyiba harta k'araci maganganun ta na rainin wayau aganin shi..........Motar yana parkawa da sauri ta fito ta zari jakarta, kanta yana mata ciwo sosai akan rik'on sumarta da yayi, tarasa metayiwa wannan man d'in yakeji da kansa sosai, mugu kawai. A k'ofar shiga parlor tayi karo da khairiyya zata fito ita da muk'araban ta, kallon juna sosai sukayi sannan da k'yar Hafsat tace

"Sannu da gida khairiyya" Dama khairiyya ta shak'a ganin Hammood ya d'akko Hafsat daga school sekace ba Bus take dawowa dashi ba, rigarta ta janyo tayi dragging nata gabanta dan ita hartayi gaba abunta

"Ban hanaki kiran sunana ba gatsai, ni sa'ankice gimbiya khairiyya zakice jahila kawai" yamutsa fuska hafsat tayi har seda duka gefen chicks nata suka lob'a, tana kallon cikin idon khairiyya tace

"Koda wane lokaci ina mamaki idan akace waike gimbiya ce haihuwar babbar masarauta irin ta Baiha, gabaki d'aya yanayin magana kike irinta 'ya'yan buje, wannan dalilin ne ya sanya bazan tab'a jinginka ainahin sunanki da wata kalmar gimbiya ko princes ba, ki bari tukunna randa duk kika zama me irin kalaman tushenki, ni matsa ki bani wuri danla" Cikin d'aga murya khairiyya tace "Kutmar uban cen kai ni kike gayawa magana a baud'e, hannu ta d'aga zata kaiwa Hafsat mari Hafsa ta tare hannun ta cillar dashi

"Idan kika sake kai hannunki jikina karyaki zanyi wlh, sannan kuma dakiketa izgilin cewar ke sarauniya ce kije masarautar Daulatul Dinar kiji wacece ni, nima haka ake kirana Princess Hafsat, kuma nima gimbiyar ce, mijin dakike tak'ama dashi soon enough zamu fara sharing nashi dake, ya kamata kisan me kike ciki danna kula sam bakida wannan ilimin, idan kinaso inke kiranki da suba Princess Riyya kema daga yanzu kike kirana da suna princess Hafsah ina fatan kin gane, laslas karki k'ara tareni a hanya kinamun hayaniya sam banason irin wannan wuce gona da iri" Tana kaiwa nan tayi gaba abinta tabar Riyya sororo baki a bud'e tana mamakin wannan rashin mutunci.


Da yamma Mood yana zaune a garden Uncle jay ya masa text message

"Gaba d'aya a fada komai ya cab'e, zasu d'aura maka aure sa wannan yarinyar gobe amma sunce se idan ka amince zaku dawo Nigeria koda na 4month ne, acewarsu zasuyita fitinane matan" Nisawa yayi yana tunanin mezaice shi bawai danze kwanta da ita koyana wani santa ze auretaba kawai close mark yakeso ya bata ta hanyar dazesan duk abinda take shiryawa akansa, layintama bawai k'yalewa xeyi ba dole seya ringa sanin dawa take waya kuma a wane lokaci, suna kammala aikin dake gabansu ze tattarasu har ita har yan iskan dake sanyata subar masarautar, kansa yayi zafi besan mezaice

"Hakan yayi zamu dawo nanda sati biyu su d'aura a goben inyaso bazan gayawa dukkansu ba semun dawo se Bahar ta gaya musu har amaryar" Nisawa Jay yayi, ya tabbatar Hammood is up to something bayason gaya masa ne kawai dan yasan ze iya hanashi yin koma menene, amma bari ya bashi dama tukunna, lolaci yayi daze gwada nashi ilimin ya gani ko zasu dace.....

*****************
Sarki be b'ata lokaci ba Bahar kawai ya gayawa daganan aka d'aura auren dan ita dama burinta kenan, wayarta ta d'aga ta kira Hafsat da zumud'i Hafsa ta d'auka tana murnar ganin kiran kakarta me sonta

"Ammu na oyoyo" Dariya me sauti bahar tayi kafin tace

"Amarsu ta ango, amarya ansha lalli" Da mamaki hafsa tace "Amarya kuma Bahar a ina amaryar take" murmushi irin na manya Bahar tayi ta gano kenan Hammood be sanarwa Hafsat ba setace

"Ji nayi ance za'a d'aura muku aure da Hammude ne ai" B'ata fuska tayi

"Mejan gashi zakice Bahar mugun zan aura tab Allah ya kiyaye nisai me kirki" Dariya Bahar tayi

"Kiyi hak'uri Attatuna kinsan fa alk'awarin dakikamun ko wannan damace da samemu, dan Allah karkiyi musu akan D'an kurma yana neman taimakon ki" Nisawa tayi

"To kaka Bahar i lobiyu, zanyi maneji dashi, shid'inma dandai yana yanayi da larabawa ne da badan ba ruwana dashi, kuma Allah ki kirasa a waya ki gaya mar ya dena cin zalina inba hakaba zan rotsa masa waya aka

Please Login or Register in order to submit comment