Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin d.p.o yana rawa yace

"Yallab'ai babu yanda xanyi da matsalar Yallab'ai Ubandoma, idan ma banyiba ze b'ullo ne ta wata sigar" Gyaran zama yayi kafin yace

"Daga yanzu duk abinda nace ka gaya masa shi zaka gaya masa, sannan kuma duk abinda ya gaya maka kake gayamun ta hanyar lambar wayar dazan baka b'oyayyiya sabida a wannan suna bibiya ta, na biyun sa kuma wlh idan ka sake wanima yaji nazo nan wurin ko naji hirarrakinku senayi mafarin rufe ganin ka da k'asa" Nan take ya amsa da angama ya rufa masa asiri kodan aikin sa, sun tattauna sosai ya samu sirrikan su kafin ya buk'aci ganawa da Hafsa inda kai tsaye suka gabatar masa da ita har offishin D.P.O


Mik'ewa yayi tsaye ya matso da sauri inda take ya kama hannunta inda atake D.P.O ya basu wuri, hannunta yake murzawa wanda yaga alamun shatin sanda rud'u rud'u ajiki cikin tashin hankali ya kalleta

"Waye ya dakeki a hannu haka? Murmushi tayi ta shafi k'afad'arsa

"Ya raunin hannun ka, harbi da zafi ko? Sannu yaa mood, hankalina yana wurin ku kaida Me matraba da wannan Muhseen d'in" K'ara shafa hannun ta yayi sannan yace

"Cewa nayi waye ya dakeki Hafsah? Murmushi tayi kafin tace

"D.P.O naji kaman suna kiransa ko, so yake ince nice na saka a kasheku, tayaya zan amsa laifin daba nawa ba, kuma tayaya zance nasa akashe mahaifina da mijina? Kuma kaga dukan nan Allah da zafi" kawai seta soma sheshekar kuka ga alama dama kukan takeso tayi tuni amma taurin kai ya hanata tayishi agaban su, iskar bakinsa yasanya yana hure mata hurin da hannunta ya tashi cikin kulawa

"Dame ya dakeki? Tab'e baki tayi irin na yara

"Sanda ne babba baka ganshi ba, niba abinda na masa so suke su kasheni, nace su kasheni amma ni kowa yasanni bana k'arya bakuma zan fara k'aryaba sabida karsu dakeni" Zuciyarsa tazo masa iya wuya yama rasa mezeyi kallon juna sukeyi kowa da abinda yake sak'awa har lokacin kuka take, k'ara kallon ranin yayi farcenta d'aya harya kumbura

"Shidawa yazo? Ya tambaya yana k'ara hura mata iska agun

"Baba Usman ne, shugaban k'ungiyar aci ta duhu da fada"

"Ya akayi kika san shine" Tana me share k'walla da gefen kafad'arta sabida ya rik'e hannayenta tace

"Dama inaso in gaya maka komai kafin su kasheni" Had'e jikin sa yayi da nata

"Kisa wai kike magana, kinada hankali kuwa? Waye ze kasheki? Kukan ta ta k'arawa sauti

"Wannan mutumin da suke kira DPO wanda ya kawoni nan dakuma Baba Usman sune sukace sauramun kwana uku a kasheni" Runtse idansa yayi sanya fahimci sunyi nasarar tsoratar da ita, k'ara matseta yayi da hannun sa me lafiya

"Babu wanda ya isa ya kasheki ina numfashi, k'yalesu kedai duk abinda kika sani ki sanar dani"zare jikinta tayi a nasa sannan tace

"Wani zezo na aminta da aikinsa da gaskiyar sa sunansa Detective Sufyan Data, munyi akan zece dasu zeje dani special investigation centre nasu ya tuhumeni, amma gun matarsa ze kaini, inada manyan shaidu awurin wani dakuma kaina, ze taimakeni yace inna gaya masa komai ze fitar dani lafiya" kallonta yayi

"Nasan Data ai, dama dashi ne naso in had'a yayi mana bincike, zan masa waya yaxo ku tafi, gidansa akwai tsaro ba abinda ze sameki acen, amma kinsan wannan dukan da aka miki sena rama, Allah har Baba usman sena saka ammasa fiye da wannan" Murmushi tayi tana kallon sa

" Laa Babba ne fa? Shima dariya ta bashi yace yana kallon ta

"Hafsah mesa kika sanya rayuwarki a hatsari har haka, mesa baki tab'a yimun bayani akan komai ba, se Uncle Jay ne ya gayamun komai da komai d'azu" tana kallon sa ta shagwab'e fuska

"Kaine kace baka sona ai, kuma ka tsaneni, Bahar kad'ai ke sona se Ummi" Murmushi yayi kome yasa wowtar Hafsah take burgeshi?


Mom Nu'aiym.


*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA*
26.

Sanye ajikinta wata farar rigace shara shara me santsi, ta tufke gashin kanta a tsakiya, ta sanya wata shara sharar hula itama fara akanta, fatarta dake shek'in wani haske tana asalin glowing abar d'aukar hankali takai hannu ta murza gefen fuskarta lokaci d'aya tana lumshe idon ta

"Yaa Sufyan bacci nakeji, tara ya gota fa, kake shirin fita? Hannun sa yakai ya tallafota jikinsa daidai kunkurunta

"Laurah wannan babban al'amari ne daya zamar mun dole senayi fitar dare, a k'aida kowa yasan 8 ana gama sallan isha ina gida, to wannan fitar basaja ne kin gane? Nisawa tayi kafin tace

"Dabadan kayi nasarar tarwatsa gidan madubi ba, da bazan barka kafita ba, amma duba da yanayin sharrin dakafi k'arfin sa na tabbatar kaime bautar Allah ne, da wannan nakeda hak'ik'a akan cewar aduk inda kake Allah mabuwayi yana tare dakai" Sumba yakai mata a agoshi sabida yanayin gajarta irin nata yana dariya yace

"Acikin shekaru hud'u Laurah baki ya bud'e, girma ya kawo kanshi" Zame jikinta tayi tana murmushi sannan tace

"K'waila tasha raino zakace" sarai yasan neman maganar sa take amma bebi ta kanta ba, murmushin sa kawai yake yafita yabar gidan.

Ta k'ofar baya yabi, wata iriyar k'oface ta sirri wacce bazaka tab'a sanin akwaita awurin ba, Likitan yaso shammaz (Littafin Sa'a) shine yabi dare ya gina masa wannan k'ofar ta sirri... yayi tafiyar kusan mintuna goma kafin ya isa wurin wata motar ya bud'e ta ya shiga batare da yayi magana ba, kai tsaye police station ya nufa inda ya tarar D.P.O anata rafka gumi yana bakin kantarsu a tsaye, hannu ya mik'a masa suka gaisa sannan yace

"Detective Data" D.P.O ana muzurai akace

"Na gane sosai sir" hular daya sako wacce ke had'e da riga ya ture taje bayan wuyansa"

"Inaso zanyi magana da suspect tamu" Muryansa yana rawa

"What is the use? Tana tare da prince hammood shisam be yadda akan ita bace take neman ransu" Murmushi Data yayi

"Interesting, haka ma wani babban taimakon ne, because inaso nayi bincike da tushe, and right now am taking the suspect with me" kallon sa cikin tashin hankali

"Wai yallab'ai mesa baka tab'a bari muyi aikin mune? Waya turo ka kuma wannan karon" K'ank'ance idansa yayi

"C.P Mai doki ne ya turoni (ACP mai doki yake magana na littafin gidan madubi, yanzu ya tashi daga ACP ya zama babba shine commissioner.) Sosa k'eya D.P.O yayi kafin yace

'If that is the case, i will like to help" Murmushi yai masa

"Kai D.P.O Maharazu ka san waye ni kuwa? Bana son taimakon ka kamar yanda banason shishigi, wannan aikine na intelligence agency me zaman kansa, ka gayawa masu baka wasu kud'i kana shirin murd'e al'amura suyi hankali da kansu, maza abisa kansu inada tarin dukiya bazasu iya sayana ba, inada tarin gaskia k'aryarsu bazata rikitar dani ba, inada tarin basira datafi k'arfin masharranciyar basirar su, now lead the way? Juyawar dazasuyi sega Hammood a fusace janye da hannun Hafsat kallon A.C.P yayi sannan yace

"Waye acikin ku yakai hannun sa ajikin matana saraki ce fa? Kallon tuhuma duk yaran sukayiwa ogansu sannan wani jikinsa yana rawa yace

"Amun aikin gafara yallab'ai nine na daketa, alokacin anata so tayi magana tak'i tayi" Da mamaki Hafsa ta kalle sa, sannan ta narke fuskarta cikin shagwab'a tace

"Allah sarki me k'arya d'an wutane fa, wancen ogan nasu shine ya samu sandar sa me zafin tsiya, ya d'aura hannayena asaman bench ya dinga rotsamun seda na suma na farfad'o" ta k'arashe maganar tana sauke fuskarta asaman d'aya kafad'ar hammood me lafiya, hannun sa yakai yana patting bayan ta a hankali

"Koma waye wlh sena rama mata, sekunci ubanku a hannuna 'yan sandan kawai, kune kuke b'ata mana k'asa, haka ake bincike inaga ta kanku zan fara" Data ne ya matso ya mik'a masa hannu sukati musabaha sannan yace

"Ranka ya dad'e babban son ya akayi kazo nan bayan raunin dake jikin ka haka? Murmushi yayi cikin girmamawa sanin cewar Babban abokin Uncle Jay kenan ya sanya yace

"Am sorry Uncle Sufyan, hankali na yana kan yarinyar nan, she sacrifice alot for her family, and mak'iya are busy trying to accuse her of something big as this, yarinya da kind soul irin hakan nan ai gobe bazataji dad'in k'ara taimakon kowa ba" Nisawa Data yayi

"Polisawan k'asar nan gaba d'ayan su kaso 75 acikinsu sunada raunin saitin kai, Allah kad'ai ze mana maganin su" Anan suja tattauna kafin su shiga mota subar gidan, gaba d'ayan su gidan Data suka isa ata wannan b'oyayyiyar k'ofar. Da kansa yayi kiran matarsa lokacin 11. Yayi tazo ta gayar da Hammood yana mata murmushi yace

"Ga d'an gidan Jay fa, yaran da ake xuwa aita mana kuka akan sa, kai Jay wlh ya iya shak'iyan ci, shida matar sane, tana buk'atar taimakon ki Anty Laurah matar Data" Murmushi tayi

"Yanzu nice anty dan Allah? Ta furta tana shagwab'a, dariya yayi "Jibi zatayi 18yrs ina ke harkin cinye cake naki na 19, so ke antyn tane ai ko yaya? Murmushin ta ta k'arawa fad'i

"Hakane na zama anty, yanxu ina muka kwana,?" Murmushi yayi

"So nake ki nutsu mu saurari labarin ta" gyaran zaman ta tayi kafin tace "Malama Hafsat Bismillah" Seda tayi gyaran murya sannan tace

"Na tasone a hannun kakata wacce ta haifi ubana, tun sanda na bud'i idona na ganni duniya nake kuma shaida mutane babu abinda nafi sabawa dashi sama da fuskar kakata, bansan waye Babata ba amma tabbas yanayin d'acin harshe na yana tabbatar mun da cewar babu saukar d'and'anon nono uwar haihuwa acikin sa, yanayin yanda gabb'an jikina,zuciya da ruhina suka kwad'aita dason jin dumi irin na mahaifiya ya tabbatar mun dacewar tabbas ban tab'a sanin d'imin jikin uwar haihuwa ta ajikina ba, wacce na bud'i ido da ita itace Baba suwai kakata kenan. Na taso gidan yawa gidan shugaban wani babban gari na fulani me zaman kansa, gaba d'aya ba ruga bace babban garine me d'auke da sassa sassa na fulani acikin ruga iri iri, wanda duk wannan suna k'ark'ashin kulawar Kakana Baba Jere wanda shine limamin garin shine kuma babban me gari na duka yankunan garin da kuma rugagen dake mak'otaka da ahalin garin sa. Acikin gidan namu akwai tarin samari da 'yan mata wanda idan wannan ba uwarku d'aya ba tokuwa d'an qanin uba ko wan uba ne, acikin fulani dana sani gidan Baba jere kad'aine basuda gadon kiwo ko noma sedai k'ira, mak'era ne da suka shahara a wannan fannin sedai irin fulanin nan ne dasam basuda d'igon addini a al'amuran su, gaba d'aya komai nasu yana tafiya ne bisa wata wahaltacciyar al'ada mara tushe,ko kak'i kokaso tilas ne kabi wannan al'adar, koda na tashi bansan sunana Hafsah ba sedaga baya 'yar shara shine sunan danasan yake mallakina, bayaga haka banida wani suna agidan, kyara da tsangwama yanda kukasan a duniya niba mutum bace wata halittace ta daban, inada shekaru shida a duniya akazo neman yara masu son aikatau kawai se Baba suwai ta rok'i alfarmar Baba jere yabarni in tafi burni aikatau nan take kuwa yace dama ya tsani d'aga ido yaga 'yar shara acikin gidan sa, dan haka in tattara in tafi har yau kalaman sa sunamun amsa kuwwa sanda yafito ya kalleni ina musu sallama yace

"Garin da ubanki ya tafi be dawo ba Allah ya sanya dagacen kibi bayanshi 'yar shara" Bansan menene asalin tarihina ba seda na shekara biyu a birni a lokacin ina aiki wani gida na wata malamar makaranta ina mata rainon yarta dan haka dani take zuwa makaranta, aji biyu take d'auka a wancen lokacin nikuwa seya zamana duk karatun da akewa yaran yana nan daram akaina bayako motsi kuma banida wata wasa abakina se karatun nan, ganin haka malama ta sanyani aji d'aya a primary, dukna girmi yan ajinmu dankuwa nafi shekaru shida haka na dage Allah ya sanya inada tsananin k'ok'ari matsala ta d'aya ce inada kafiya, fad'a ga kuma rashin kunya, sam bana lank'wasuwa wanda wannan ya sanya ina aji shida a primary a lokacin ina shekaru sha biyu kawai na rasa aikina agidan malama, ina gama common interance ta mayar dani gida akan wai banajin magana ana fad'a ina fad'a, nan Baba jere yamun duka ya kusa sumar dani, daganan duk inda akazo d'eban yara 'yan aiki sekiga ance nayi girma har Allah ya kawo Hajiya Barira garin ita kuwa ta dawo ne dame mata aiki akan tayi shege bataji kuma ita batason yara, ana haka aka ce gani nan take Baba jere ya hau gaya mata mugwayen halayena, inda tace aid'a na kowa ne, dan haka ita taji ta gani ba akan 'yar aiki bama ta d'aukeni a matsayin 'yar rik'o, zata rik'eni amana dukda halina, haka muka kwaso muna dawowa Burni na nuna mata takardar primary na nace nifa so nake in zama lauya Baba jere zan d'aure, haka na shiga bata baki harta sakani secondry school aji d'aya nake zuwa abuna, na zama yar gidan masu kud'i bana mason ace yau inje k'auyen mu, haka nazo bayan nakai S.S 1 se wani al'amari ya soma faruwa dani mara dad'i, dama cen daga secondry school danake zuwa kullum se an kawowa momy k'arana, nayiwa malami kaza rashin kunya nayiwa malami kaza rashin kunya, wannan ya sanya momy setake sanya D'an me gadin ta wato Yaya Bilal daya xama d'an gida kamar ni yakemun duka wannan ya sanya a duniya banida wanda nake tsoro sama da yaa Bilal, sabida muguntar sa yaga damar ya sanyani tsallen kwad'o idan banyi ba kuma inci duka, hakan ya tilastani rage yiwa malamai na rashin kunya sekuma abun ya dawo kullum se anmun tsakani da wani a class d'inmu danni sam banida hak'uri kona kwabo ni kaina na sani, haka akayita gwagwarmaya dani momy tanata hak'uri har zuwa lokacin da Yaa Billal ya tsiro da wata d'abi'ar banza a kaina" shiru tayi tana kallon su wanda dukkansu ita suke se Hammood ne dake k'arawa matsowa kusa da ita cikin tashin hankali

"Wane irin d'abi'a ne wannan? Meyake miki duka? Share hawayen idanta tayi ta girgiza masa kanta

"Tab'amun jikina yake yana cewa zeyi iskanci dani, kuma idan ban tsayaba ya dinga marina yana cewa seya k'ullamun sharri, koda wane lokaci Allah ze kawo dalilin daze hanashi cimma mugun burinsa akaina, ta wata hanya mafi sauk'o, tsoron abinda yakemun ya sanya duk sanda nadawo saga school kafin momy ta dawo daga gun aiki nake sauri inbar gidan zuwa gun wata bishiyar bayan layin mu indai yana gari, be tab'a sanin inda nake zuwa ba, da haka har wata rana yazo yadinga yagalgalar jikina yana dukana, katsam sega momy ta dawo lokacin dabata saba dawowa ba, ba wannan lokacin na saba jiyo sautukan zantuttukan banza da iface iface marasa kan gado agidan ba tsakanin Momy da Bilal amma tabbas a wannan ranar na gano ihun meye nakeji, hankalina ya tashi akan yanayi mummunar alak'ar dana fahimta akwai tsakanin su, dake banida hankali nima se kawai naje na samu Baba Lami wadda itace uwar Bilal na zayyane mata komai nan naga rashin dattako dan kuwa atake taje ta gayawa momy wai ina mata sharri itada Bilal momy bata fad'i mummunan kalma ko d'aya akaina ba kawai tace bilal ya mayar dani gida, dama kuma yasan k'auyen mu kuma shine yake kaini, akwai lokacin daya soma koyamun mota acewar momy inna iya inyana school koda cefane na rik'a yi mata amma seyazo da iskancin sa seban iya sosai ba na dena zuwa kawai, dama Bilal yana cike da haushi na yanzu kuma gani gashi abanza ance ya kaini k'auyenmu" kuka ta tsaya ta d'anyi wanda da sauri Hmmood ya matso ya rik'e hannun ta, meya miki dayaje kaiki gida? Tab'aki ya kuma yi? Wani abun ya faru ne" tana share k'wallah tace

"Banaji mahaifiyata da akace ta mutu batamun addu'a har wannan lokacin, sabida Bilal bayan ya kaini gida seyace da kakana inji Hajiya Barira wai a mayar dani sabida nayi cikin shege, wannan ya sanya kakana da dama baida imani yace yanda yayida uban haihuwata haka zemun nima, kayan k'ira ya d'akko seda suka d'auli wuta ya mannamun a tafukan k'afana wanda daganan bansan meya faru ba se farkawa nayi na ganni abakin titin garinmu yashe, haka nasha dukan ruwan sama na tuna kafin Bilal ya tafi ya bani kud'i da katin sa waina nemesa a waya danyasan in aka koreni dole naje na bashi kaina, amma duk wad'annan abubuwan ba abinda na tsira dashi face suturun jikina" Da sauri yakai hannu ya d'aga k'afarta ga wannan tabon nan kowacce k'afa wuri biyu, zuface ta keto masa yana jinjinawa rashin imani irinna wadancen mutanen, murmushi tayi sannan taci gaba

"Da k'yar na samu nahau wata mota tayi loding kayan masarufi sukace zan basu hamsin haka na yadda koda mukazo banida ko anini, na hadu da shakiyanci karen motar yace ajikina ze fanshe hamsin dinsa hankalina be kuma tashiba seda wani ya baiwa karen motar dari bakwai yake cewa aini me tsadane ga dari bakwai yabar masa ni, da k'arfin hali da rashin kunyar da ake cewa inada ita a wannan lokacin sesukamun amfani na fatattakesu na baiwa karen motar zoben azurfata nayi tafiyata ayanayin dako tak'a k'afana bana iyayi sabisa rad'ad'i da zabar k'una, a haka nayi yunk'urin komawa gidan momy da k'afa, na yanke shawarar bazan nemi taimakon kowa ba dukda nisan dake ga unguwar sabida naga kowama dan iskane, haka nake tafiya a d'age har dare a tsala cen k'afa ta d'auke sega zauna gari banza suka afka mun sesukayi rashin sa'a ina cikin al'adata, dan haka sumamun duka suka gudu abunsu, bansha wahalar neman taimako ba dan kuwa a wannan lokacin hammood yazo mun, daganan ya d'aukeni har gidan su a lokacin bankosan shi waye ba, zuwa wayewar garin ranar sena fahimci a gidan sarki nake, maganganun da ake akan cewar d'an sarki yamun fyad'e sune abubuwan dana yi karin safiyar ranar dasu! Haka nan wasu mutane suka sameni suka ce na basu labarina ban boye musu komai ba kuwa na zayyane musu labarin abinda ya sameni kamar yanda na baku, senaga suna dariya d'aya daga cikin su yace

"Ke daga yau daga yanxu ma duk abinda zakiji kibarshi a haka ma'ana karkiyi musu, za'azo ana cewa yarima hammood ya miki fyad'e ki tafi ahakan, indai kinason wanda ya taimakeki.ya rayu, indai kinason karmu kasheshi tokuwa ki mana biyayya inba haka ba nan bakida kowa kasheki kawai zamuyi mu kashe banza" wannan maganganun sune suja tilasta bakin gaza motsawa dukda kuwa inaso ya motsa akan fad'ar gaskiya, haka na tabbata a zillimi bana iya cin komai, har maganar aurena dashi tazo kunnena, wata ziyara da Ummin sa ta kawomun baki ta bud'e ta gayamun gaskiyar ita ba kurma bace in sanar da ita gaskiya kuma na gaya mata gaskia, daga baya ne labari ya sameni cewar tayimun magana dan kawai ta tabbatar turoni mak'iya sukayi setaji shiru har gobe babu tashin zancen, a gurguje abubuwa da dama sun faru, mutane da dama sun zo akan ran Hammood sa hannuna sukeso, wasu na amsa musu da to wasu na bisu da dabara wasu kuma na zagesu dama kamar yanda na fad'a na iya tsiwa. Bayan munbar k'asar sena fahimci hankalin fada gaba d'aya yana kanmu, acikin kuyangi da bayi ma akwai wanda takanas ko motsin me yayi sesun fad'a, sena shige acikin su, hatta Kuyangin Khairiyya akwai wanda sukeda aiki akan Mood kawai, bayan na fahimci komai da kowa nasan kowa abinda yake ka sa senayiwa Bahar tiryan tiryan daganan tayi waya da ummi inda atake muka had'e kai da Uncle Jay da kuma Barra acikin taimakon kai da kai gani mun tsamoshi a hannun mak'iya, kuskuren farko da Hammood yayi shine rashin yarda dani, na biyu kuma ya barwa kansa tunanin cewar inya bayyana kansa mak'iya zasu kashesa, ni kuwa nake tunzurashi da kalamaina masu zafi dan kawai nasanya ya dena shakka yafito yayiwa kansa fighting, uncle jay bayaso yayi magana amma ni inaso, da wannan na gayawa 'yan jarida tabbacin yana magana har akayi caa akansa dama haka nakeso, k'ungiyar danake da tabbacin akwai sena shiga acikin ta a b'oye...... tabasu labarin duk abinda ya faru sannan tace

"Wani dare a k'ungiyar munkai ziyara nida Hammood a tare inda aka tashi kamamu shinema ya ceceni, amma seyayi canjiya da uncle Jay shi uncle jay seya koma yana gaya musu be ganni ba, Uncle Jay tsohon d'an kungiyar Ne wanda yake nuna musu atare amma ina zargin sa akan bayason Hammood ya gaji wannan sarautar sabida dalilai masu yawa, ban yanke masa hukuncin komai ba senaga yanda ta yiyu, se iya yiyuwa hujjar dayakeda ita me k'arfi ce. Na fahimci cewar khairiyya 'yace awurin tsohuwar marik'iyata wato Hajiya Barira, na fahimci anaso ayi amfani da ita a cutar da hammood abinda ya sanya nayi gangancin fita kenan wanda hammood keta bibiyata kuma nasan da hakan, nayi sanasar tattare muhimman sirrikan Idan fada, sedai kuma sun murd'e abin ta hanyar daban zata ba, inada shaidu sosai, inada hujjoji inada sautikan muryoyin su a ajiye suna maganganun cutarwa agaremu baki daya, ganin na kamasu a saukake shine sukamun wannan sharrin" kallon nutsuwa Data ya mata

"Mesa kika gayawa 'yan jarida yana magana" Tana kallon cikin idansa tace

"Sabida yana magana, akan me ze rayu a kurumce akan wasu banzayen mutane, akan me yana namiji ze zama wani irin mace ma ta fishi, akanme ze rik'a rayuwa ta rashin 'yanci alhali shi saraki ne, koni nan danake mace aka d'aura aurena da d'an sarki inajin izza tana fizgana akan me yarima ze mayar da kansa sakarai? Danme yasa Uncle Jay ze tilasta masa datse harshen sa? Akan me ? Nisawa Hammood yayi kafin yace

"Akan me kika sadaukar da rayuwarki akan tawa ? Mesa zaki taimaki wawa kamar ni? Murmushi tayi

"Wawane ya fara taimako na dole in biya bashi, bayaga haka kai yayana ne ka manta? Above all kuma akwai k'auna" Murmushi Data yayi kafin yayi gyaran murya yace

"Kin d'auki hanya me kyau sosai sedai kuma hanyace mafi hatsari agareki, sedai dabadan keba bansan yanda za'ayi abubuwa su warware acikin sauk'i haka ba, yanxu da kikayi nasarar gano komai da kowa menene taimakon gaggawa dakika shirya bamu sabida bamuda lokaci, bamu kad'ai muke shiri ba harsu nasan sunacen suna shirin yak'i babba damu" Kallon sosai tayiwa Hammood kafin tace

"Dabadan mahaifiyar khairiyya ba dabazan kawo wannan lokacin a wannan garin ba harna samu wayewa, da k'arfin dukiyar ta nayi nasarar samun ilimi na addini dana zamani, itace take ciyar dani banda so dakuma k'auna babu abin ta nunamun, har lokacin danayi yunk'urin tozartar da ita in tona mata asiri ko bak'ar magana bata gayamun ba, tayi zaman amana dani, ta d'aga darajata har kawo wannan lokacin tayaya zanyi kishi da 'yarta data rayu batare dajin dad'in uwartaba har zuwa aurenta, ni abokiyar zaman khairiyya ace nasan sirrin mahaifiyar ta mafi muni, nakuma san nata mafi muni duk a matsayinta na kishiyata anya anmata adalci kuwa? Tayaya zata rayu a farin cikin sanin cewar abokiyar zamanta tasan labari mafi muni akan mahaifiyarta da wani b'angare anata, da wannan nakeso kafin na bayar duk wasu hujjoji da kuma shaidu dana tara in sanya sharad'i na" kallon ta sosai Hammood keyi lokaci d'aya zuciyar sa ta shiga luguden tashin hankali, me yarinyar nan take nufi, Data dake nazarin ta yace

"Toohh wannan wane irin sharad'ine haka? Gyaran zaman ta tayi sannan tace

"Tun daga kan sarki da sarauniya har duk wani wanda baya cikin k'ungiyar aci duhu ta idan fada rayuwar su tana cikin hatsari, ya rage na Hammood ya cecesu ta hanyar rubutamun saki har k'waya uku in bashi duk wani abu daze tarwatsa mutanen fadar sa danakedasu a hannu, kokuma yak'i ya sakeni in adanae hujjoji da shaidun danake dasu al'ummar dasuke iyayensa, da talakawan sa su mutu a banza akan sonkan sa, banaji wannan aikine me wahala agaresa yasha gayamu ya tsanani, bashida wata alak'a dani na mata da miji tun bayan auren mu bare yace mun saba, dan haka yanxu dabara ta ragewa me shiga rijiya" Yanayin sa kad'ai zaka kalla ka tabbatar wa kanka cewar wani sabon tashin hankali ya ziyar cesa, gaba d'aya ya gid'ime wata iriyar zuface ta keto masa ya kalli Data cikin tashin hankali yace

"Uncle Sufyan kanajin wani zance kuma na mata, wannan wane irin magana ne" Shiru Data yayi na wani lokaci sannan ya kalli Hafsa, seda ya had'a rai sannan

Please Login or Register in order to submit comment