Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in gudu wurinki" Murmushi Bahar tayi na manya

"Attatuwa zanga ranar da xaki girma kinji, nidai yanxu wannan maganar sirri ce karki gayawa kowa" Tana murmushi tace

"Bahar na kusa inzo in ganki yaa Hammood yace wai dana kammala exams zamuzo hutu"

"Mezan dafa miki.im zakizo? Tsalle tayi daidai lokacin da hammood yashigo parlon tana rawa tace

"Bahar ina wannan miyan yauk'in dakejin daddawa sosai? Wanda kike dafawa da kanki acikin wannan tukunyar na laka? Bahar tanata dariya tace "Naganeshi Hafsat"
"Yauwa sweety kin ganeshi sosai toshi zakimun da tuwom dawa me santsin nan seki saka a soyamun zabi kuma sannan amin kunun gyada" Bahar tace

"Duk da kaina zan miki ma, ni kinsan ina son shiga kitchen dandai tsufa yaxone amma ko zamanin sarki me rasuwa nice sarauniya acikin matansa amma ninake masa girki ba ruwana"

"Yauwa Ammuna i lobiyu lodi lodi zan sayo miki wannan madarar dakikeso sosai" Nan sukayita hira shikuwa yayi tsaye k'ik'am yana kallonta yama rasa meyake kallo ajikinta, yau da aka tabbatar masa an d'aura masa aure da ita shida yayi auren manufa segashi ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa. Sanda ta ganshi tsaye abayanta turo baki tayi, shikuwa ya tsaya yana k'arewa d'an tsirut d'in bakin da data turo gaba kallo, cin k'unk'uni tace

"Shi mutum kawai baze yi sirri ba se an saka masa ido abinda banaso kenan" Ta antaya da gudu dantasan yaji me take cewa sarai, kuma inya damk'i sumar kannan nata dababu d'an k'wali setayi fitsari, murmushi kawai yayi ya girgiza kansa ya wuce d'akin khairiyya........kallon sa khairi tayi tana mamakin annurin dake d'auke a fuskar sa kafin tace

"Ranka ya dad'e wannan farin cikin dakake yau ya dace muje yawo gaskia, musha iska mu shak'ata" Rungumarta yayi yanajin wani yanayi na musamman dabazece ya tab'a tsintar kansa a irin wannan yanayin ba gaba d'aya rayuwar sa! D'agowa tayi suka kalli juna tace

"Honey muje yawo please" Murmishi yayi tare da gyad'a mata kansa, k'ara rungumeshi tayi "Thank you love" Sannan ya soma shiri sauri sauri. A bangaren hafsa kuwa batada masaniyar cewar an d'aura aurenta da Mood dan haka sun gama shirinsu akan zasuje yawo itada Bilal da k'awarta Cylia dan haka batare da b'ata lokaci ta shirya taje gidansu cylia acen aka cab'a ado na musamman Bilal yazo ya d'aukesu suka daushi hanyar Beach.....
Sunsha wasannin a Beach sunta ciye ciye, sun shiga ruwa sunyi jagab, yayinda shima Hammood da khairii Beach d'in suka je, basu suka had'uba seda kusan yamma sosai lokacin har Hafsat suna shirin zuwa gidan kawai Hammood se hangota tayi suna wasa da ruwan da ita da Bilal,idan ya watsa mata itama ta watsa masa, dake tuni khairi taje hawan lilo acewar ta tana tsoron ruwa sosai, Wani irin yanayi mara dad'i Mood ya tsinci kansa aciki, hafsat wane kalan iskanci take koya awurin Bilal da wannan baturiyar me kamada kazar k'auri ? Yaushe yayi saken da har sukayi sabo da Bilal haka? Yasan Bilal yana zuwa dubata sosai ko sanda batada lafiya amma beyi tsammanin shak'uwar su hartakai suyi sakim jiki haka da juna ba, a fusace yaja khairii suka nufi gida, ita kanta tayi tsananin mamakin sauyawar yanayin sa lokaci d'aya! Amma batace masa komai ba har sukaje gida, bayan ya shiga ya watsa ruwa zuwa yayi bakin gate ya tsaya, yana nan har Bilal ya sauke Hafsat lokacin dare yayi kam dandai sedai hasken fitilun street amma ba komai me kamada haske sam! Tana takowa har lokacin wandon dake jikinta da top a d'ame suke da ita d'am babu inda wata iska zata iya kutsawa kuma yasan duk waccen cylia ke rikitar mata da kai, kamar daga sama yaja hannunta seda ta k'walla k'aramar k'ara kafin ta gane shine, har cikin gidan yajata suka shiga kai tsaye d'akinta yashiga da ita seda ya manna masa key tana tsaye tana kallon sa gaba d'aya ta tsorta da yanayin sa dan kuwa ta gama hango fitina kwance a fuskar sa, Juyowa yae a fusace bayan ya gama yiwa d'akin key sannan ya soma tinkarota a hasale, a hankali ta soma ja dabaya ta fahimci bin shawarar Cylia akan ta dena tambayar fita ba abu bane me sauk'i dan ta tabbatar shine abinda yaa mood kewa wannan ciccikar, har seda suka matse bango sannan ya mata rumfa, goshinsa yakai akan nata nan take ta runtse idon ta, k'irjinta yana tsananin dokawa hannunsa ya kai daidai fatar cikinta agefe kunkurunta yayi mugun matsewa seda tayi k'ara, janye kanshi yayi daga goshinta baze iya hak'ura ba yau seyayiwa wannan sharar magana yace muryarsa cen k'asan mak'oshin sa

"Idan kina tunanin zan k'yaleki akan abubuwan dakikemun na fili dana b'oye toki dena wannan tunanin danba k'yaleki zanyi ba sam, idan kuma tunani kike kin isa ki fita bada izininaba agidan nan ki kuma gwadawa ki gani, karna k'ara ganinki tare da Bilal, koda gaisuwa ban yadda kukeyi ba bare har kije beach dashi kuna wasan watsawa juna ruwa kinajina ko? Rashin kunyane da Hafsa tak'in k'arawa cikin masifa tacw

"Dankai ubanane? Kodan kai waye awurina da duk kake tunanin zanyi duk wad'annan abubuwan dakake lissafomun" hannunsa dake kan kunkurunta ya sanya ya k'are matsewa sesa ta kai hannunta tana magiya kafin yace ko yanzu k'asa k'asa cikin kunnenta

"Sabida ni mijinki ne, an d'aura mun aure dake tun safe yau, wannan kayan dakike fita dashi sekace chidera jikar inyamurai ma idan na kuma ganinki dashi a waje sena b'abb'alaki" D'agowa yayi suka k'urawa juna ido cikin ido sannan ta kanne tsoron datakeji tace

"Bantab'ajin hikaya mafi ban dariya irin naka ba, ni bebin roba ne? Kokuma a'a ni totuwar rake ce dazakace an d'aura aurena dakai" Bakinta ya matse da hannun sa k'wayar idansa yana yawo acikin nata

"Hafsat kinsan Allah, bazan tab'a ragawa rainin wayon nan naki ba, idan kikace tsiwa zakimun a hankali zanyi maganin tsiwar" k'wallah yana fita a idanta tace bayan ya sake bakinta

"Mugu kawai me k'aryar kurumta" Tana fad'ar haka ta zame ta k'asa daga rumfar daya mata ta fece ta oc d'insa, toilet ta fad'a amma shi sam bebi bayanta ba tsayawa yayi kawai yana tunanin dalilin daya aikeshi yi mata magana!!!

*************
*Bayan sati biyu*

Har sati biyu ta cika wasan b'uya akeyi tsakanin Hafsat da Hammood tunda ta kira bahar aka tabbatar mata da zancen auren gaba d'aya se hankalinta ya tashi, wata irin damuwa mara misaltuwa ta shige ta, lallai tabbas yau ta tabbata mara gata wannan wane irin aure ne? Ace koda Ummi bazata iya kiranta ta sanar mata ba, rayuwarta gaba d'aya a baud'e take, koda wanda ya tsinci kansa agidan marayu yafita gata ayau, tanada family, na uwa dana uba yaya zata k'are a haka, babu me saurarar ra'ayin ta, bame saurarar uzirinta bameso yaji me take so ita kenan ba kowa bace, da wannan damuwar ta rage walwala sedai tas kudirinta yana nan nason shiga al'amuransa dasuka shige masa duhu.......A b'angaren Hammood kuwa banda damuwa ba abinda yake ciki, yayi imanin cewar yayi katob'arar yin magana ya bud'ewa hafsat sautin muryarsa, besan da wane ido ze kalli Uncle Jay ba, bare kuma Barra datasha gargad'insa aka ko khairiyya kartasan bakinaa yana bud'ewa dan kuwa mata wawaye ne, acewar su kosu haka suke fama da magana dashi irinta wahala ta kurame,dan haka ya zame masa dole ya iya takunsa, mesa bakinsa yake k'aryata zuciyar sa akusa da Hafsat kullum se idan be ganta ba, amma duk suka kasance a tare babu abinda ke hanawa zuciyar sa bugawa dason furta kalamai irin na baki agareta, yaudai yayi kudirin nemanta su fita dan kuwa nanda kwana d'aya zasuje Nigeria yana da kyau ya sanar mata karta kuskura ta gayawa wani wannan sirrin dan haka sak'o ya tura mata akan k'arfe 5 na yamma ta sameshi a mota parking lot zasu fita, dan magabar tafiyar ma baharce ta sanar mata.

Yau d'inma wandone d'amamme ajikinta sedai wannan karon kaftan top ta saka tare da d'aura k'aramin d'ankwali ke zubin hanky akanta, sumarta se yawo take abayanta dan kuwa batayi parking na sumar ba ta zubar dashi abayanta se shek'i take, tana yawan sonyin mu'amala da makeup wannaj ya sanya fuskar nan rad'am take da light makeup wanda gaba d'aya yake shirin turata a jinsin larabawan usul! Kallo d'aya ya mata ya d'auke kanta yauma kamar kullum atare suka zauna a bayan motar driver cikin girmamawa ya gayar da ita sannan suka kama hanya, wani restaurant suka je acen suka jeru domin shiga daga ciki, hannun ta ya kama ya rik'e batare daya kalle taba ita d'inba bata k'wace hannun nataba bata kuma ko kalle saba har suka zauna inda takeda yak'inin an tanadesa ne domin su, lemo aka aka ajiye haka sukai shiru ita ma yau fuskar nan a d'aure tamau, seda yasha lemom ta hanyar zuk'a da straw ya zare gilashin idansa ya ajiye sannan ya shanye idansa anata ya tangale hab'arsa da hannayensa daya dunk'ule sannan yace yana kallon ta

"Kinsan dalilin dayasa muka zo nan" Kallon sa tayi ta yamutsa fuska ya dinga yin abubuwa da izza sekace ajiye mutane yayi cikin takaici tace

"Saukar wahayi ne inaga" D'an had'e fuskar sa yayi "Me kikace ? Kallon sa take har lokacin sannan cikin tsiwa tace "ka manta" Wani gajeran murmushi yayi da gefen bakinsa kafin yace

"Hafsa Abu biyu zan gaya miki, da farko dai wannan shigar dakike kina fita bazan lamunta ba har abada, karki kuskura ki k'ara koda tunanin fita a haka, abu na biyu kuma magana ce akan wannan maganar ta fatar baki damuke nidake, ki sani ko.Ummi na bana magana da ita sabida wani babban dalili damuka barwa kanmu sani, matata zab'ina khairiyya ma dakika gani batasan wannan harshen nawa yana kad'awa ba, inada tarin mak'iya irinki masuso kawai susan sirrin harshena, dan haka ya zame miki dole ki adana wannan sirrin, idan kikayi gangancin zuwa Nigeria koda shadow d'inki kika gayawa mun tab'a magana haka dake wlh sena b'atar dake a doron k'asa, abu na k'arshe dazan gaya miki kuwa shine daga yanxu, karki kuskura kokuma kiyi tunanin zan k'ara miki magana a haka, munyi na farko bisa rashin sani, mukayi na farko bisa kuskure wannan ya zama ma k'arshe kuma munyishine bisa tilas sabida haka anyi farko anyi k'arshe kinaji na ko" sake baki tayi kamar me mamaki seda yakai aya sannan ta tab'e baki tana murmushin kama rainani sannan tace

"Kasan Allah wlh sena tona maka asiri, sena gayawa duniya bama masarauta ba duniya setasan kai butulu ne ka butulcewa Allah da Ni'imar bakin daya baka kana living fake life, ur all fake bakada godiyar Allah, sabida haka sena fad'a coward! Kalmar ta ta k'arshe da matuk'ar dakesa a k'irji dukan ya kaiwa table d'in sannan ya tarwatse duk abinda ke table d'in cikin k'araji sannan isa gabanta ya cafki sumar kanta, atake jijiyoyin kansa suka bayyana tsananin b'acin rai ya haddasa masa ganin jiri da kuma harbawar zuciya, take ya sake kanta yayi azamar zaunawa, ya dafe kansa kusan minti biyar be motsa ba, dan haka hankalinta ya tashi da sauri taje ta dafa shoulder's d'insa

"Dan Allah kayi hak'uri" hannun sa ya sanya ya doke hannunta dake kan kafad'arsa da sauri tayi waje kai tsaye taxi ta hau tawuce gida tanata kuka a motar, tayi danasanin abinda ta gaya masa, tarasa dalilin sayasa take yawan fusata akan sha'anin Mood, koda gaje zalinta yakeci shisa.

Basu kuma had'uwaba sesa zasuje airport, nanma dai irin wannan shigar ta kumayi amma wannan khairiyya ce ta mata magana akan bazeyiyu ta doshi masarauta a hakaba ko kallon khairiyya batayiba har suka hau jirgi zuwa Nigeria. K'asar dasuka tsaya transit ma bakinta da nashi be had'uba, anan ta sauya kaya dan sesa suka kwana ta sanya jallabiya cream me adon dutse bak'i tayi matuk'ar yi mata kyau, sannan suka d'auki hanya dukda a k'ule take da Hammood dankuwa wannan karon iya shisa Khairii ne kawai a VIP ita tare da kuyangi sukabi yarima sukasha kid'ansu.

*Nigeria*

Tunda sukazo khairiyya b'angaren hammood sabo acen suka sauka sabida dama yayi gini acikin masarautar me d'auke da part biyu gefe gefe manya da madaidaici a tsakiya, na gefen dama khairiyya anan danginta suka gyare mata wanda dama tanada labarin hakan se hagu da aketa hidima acikinsa na kai kaya k'awata wuri.
Durk'ushe yaukam Ameena take agaban Hafsat tana gaya mata yanda akayi

"Ranki ya dade anmun waya da kuma sak'on inda zamuyi meeting da 'yan k'ungiya a daren yau, tun zuwanmu dama aketa shirin hakan" Murmushi Hafsat tayi kafin tace tana kallon Ameena

"Kai abin yazo a daidai lokacin danake sha'awar faruwar hakan, nice zanje taron ba keba" Da sauri Ameena ta kalleta ita kuwa taba dariya tace

"Karki damu ai kince basa bari wani yaga wani ko, bazan bari asirin mu ya tonu ba, bazan mayi magana ba akwai abinda nakeso najine da kunnena Meena" Jinjina kanta tayi sannan tace

"To babu damuwa ranki ya dad'e, sunce da magrib zasu ajiyemun kayan sakawa a wani wurin zanje na d'auka" Jinjina kai Hafsat tayi kafin tace

"Wannan yayi daidai, zanyi basaja da magrib sena sauka a d'akinki kekuma karki fito harse zuwa safiya" Meena kanta a k'asa tace

"Amma ranki ya dad'e keda kika fini sanin suma inaga ai kyau kema ace sun gayyaceki sunce babban tarone" Murmushi Hafsat tayi aranta tace ba laifi itama wannan yarinyar akwai brain "Idan suka gayyaceni Hammood ze gane kekuwa, kinsan fa ni komai nawa anfiso ya zama sirri" Jinjina kai Ameena tayi "Ea gaskia Ranki ya dad'e hakane" Hafsat gyaran zaman ta tayi sannan tace

"Ina mutumin damukayi zaki had'ani dashi idan mun dawo? Shiru Ameena tayi kafin tace "Na bincikesa ance wlh ya koma ghana" Tsaki kad'an Hafsat tayi sannan tace

"Yadai zamar mun dole in ziyarci tsohuwar secondry school d'ina, uncle computer nake nema, akwai abinda nakeso na tambayeshi ni banda waya ba abinda na iya operating sosai gwanda ma laptop yanzu nad'an iya"

"Ranki ya dad'e me zakiyi dashi to" tab'e baki tayi

"Ba ruwanki kinji, tashi kije" Haka Ameena ta mik'e tana mamakin wayo irinna Hafsat, yarinyar nan seta warwasa ilimin tantiri kai tsaye.....

********************
Se k'arfe uku da rabi na asuba sannan aka tashi daga wannan taron wanda tsabar tsorata dajin abubuwa Hafsat kasa d'auka kanta tayi, a wannan safiyar kuwa Hammood yana zaune da waya a hannun sa yana duba labarai na wannan safiyar yaci karo da wani heading .

BREAKING NEW'S..*Ashe dama prince Hammood na masarautar Daulatul dinar ba kurma bane?* Da sauri ya mik'e tsaye ya nanata wannan rubutin yakai so goma kafin saitin kansa ya tsaya akan abinda ya gani, k'irjin sane ya doka, tabbas wannan aikin Hafsa ne, dama abinda ya kawota kenan, abinda tazoyi kenan kuma gashi tacika burinta a wurin mak'iya, idan hakane se yarinyar nan ta yabawa aya zak'inta, seya nuna mata iyakarta ayau, setayi danasanin zuwan sa a dumiyar ta me cikeda hazo!!! Wayoyin sane suka hau ruri kusan a tare, nan Uncle Jay ne d'ayar kuma Ummin sane gaba d'aya babu d'aya daga d'aga dankuwa yasan ko zancen me zasu masa!!!


Hafsat dake rik'e da wayarta a wannan lokacin tana karanta New's d'in itama murmushi tasake wanda ita kad'ai tasan ma'anar sa.

MOM NU'AIYM.

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *NA: BILLY GALADANCHI*

*Ohhhh gaskia Reader's kuna bani nishad'i, harga Allah inajin dad'in comment naku dakuma k'aunar dakuke nunawa wannan littafin na tsintar aya, Allah yabar tare..... Wannan shafin gaba d'ayan sa sadaukarwa ne ga duk wata me bibiyar littafin Tsintar Aya, kuyi yanda kukaga dama dashi.*

*SHAFI NA ASHIRIN*

  20.

Gabaki d'aya kanta ba k'aramin d'aurewa yayi ba, tayama za'ayi wannan maganar ta fita? Waye yaje ya buga wannan labarin meke damun wannan gidan jaridar dazasu buga labari kansu tsaye batare da wata hujjar ba? Mik'ewa tayi kawai tabar Fadar sarauniya cikin sassarfa har tana had'a hanya kai daga bisani ma da gudu ta had'a dashi, sedai lungu da sak'o na masarautar mutane sunyi gungu d'aya idan ba wayace a hannunsu  ba to jarida ce, wannan abin ne ya sanya ta k'arawa gudun gudu zuwa na fanfalak'i har zuwa lokacin data iso gidan Hammood, tana haki ta kalli hadiman dasuma jaridar suke kallo tace fuskarta a had'e

"Ina prince mood yake? Kallon ta sukayi sannan d'aya daga cikin su yace

"Ranki ya dade tunda ya dawo daga masallaci be fito daga ciki ba, kai tsaye b'angaren dayake mallakin sa ta nufa a k'ofar parlor sukayi karo yana sauri ze fita, hannun sa ta rik'o batare da b'ata lokaci ba ta juya ciki dashi, shikuwa haka ya dawo tamkar rak'umi da akala be iya hanata ba dukda so yake yaga k'arshen iyashegen ta dan ubanta... A tsakiyar d'akinsa ta sake masa hannu sannan ta waigo gaba d'aya suka fuskanci juna har lokacin huka take na gudun datasha dan haka seda ta d'anja fasali sannan tace

"Labarin dake yawo gaba d'aya a masarautar nan na tabbatar kaima ka ganshi, zuwa kawai nayi in baka shawara k'waya biyu, na farko idan ka fita waje pretend as if nothing happened, i mean bakaga komai ba zakayi kamar bakasan da wannan labarin ba, na biyu kuma karka k'aryata 'yan jarida, am only telling you this because i care in kayi sab'anin abinda na fad'a zaka wargaza komai, zaka basu lasisin ci gaba dayin barazana da rayuwar ka, bance dole sekayi abinda nace ba bankuma ce dole seka yarda daniba wata rana zaka fahimci inda na dosa" Tana kaiwa nan ta juya zata bar d'akin ya damk'o hannunta ya wulwulo da ita ta fad'a jikin sa suka tsaya kallon juna a hankali yace

"U really are a drama queen, so kike ki mayar dani sakarai ko? Aikinki yana kyau sosai, abu d'aya zan.....hannu takai ta rufe bakinsa sannan tace shhhhhhhhhh

"No where is safe in this palace, please no matter how angry you are karka kuma furta koda kalmar A ne a palace d'in nan" Tana kaiwa nan ta k'wace jikinta ta ruga gaba d'aya tabar cikin gida, amma me tana zuwa waje sega dandazon 'yan jarida sunkai su goma sha kowa yazo ne yin magana da Hammood, shi d'inma bayanta ya nufo tun daga bak'in k'ofa daya hangosu seyayi tsaye kawai ya jingina da k'ofar ya hard'e hannayensa a k'irjinsa yana murmushin dake d'auke d'auke da ma'anoni daban daban....., tamkar wacce k'wai ya fashe a ciki haka ta dinga takawa harta isa gabansu,waigawa tayi ta kalle sa yanda yake murmushi ya matukar kashe mata jiki T bataso ya b'ata mata shirinta taga alamar zarginsa akanta me yawane baze tab'a saurararta ba. Kallon su tayi tace

"Waye ya bud'e muku main gate, kuma waye ya baku izinin zuwa nan ku tashi prince hammood daga baccin sa? Speakers suka kawo kusa da ita da masu waya kowa dai da abinda yake amfani wurin yim recording

"Ranki ya dad'e me zakice game da gaskiyar wannan al'amarin daya faru gameda jita jitan da aketa yad'awa akan k'aryata kurumtar Prince Mood da mutane sukayi? Bataso kulasuba amma bari ta ari action tayi acting kamar actrees ta indian film!!!

"Akan meyasa ku kuna aiki amma kwata kwata bakusan aikin kuba, ita kanta jaridara data buga wannan labarin k'aryar semunje kotu dasu, dan wannan labarine mara tushe? Idan tushensa ? Kuntab'a gani meji yana magana yayi kurumtar k'arya? Akan me sarki me jiran gado zeyi putting up wannan act d'in? Wannan labari ne ya samo tushene daga mak'aryata mak'iyan prince, kunsan duk inda mutum me babban matsayi irin prince yake dole seya samu mak'iya, sabida haka nake baku tabbacin wannan labarin k'aryane, kuma ni matar prince ce, sabida haka kunji daga bakina, koyazo bashida bakin baku amsa koda akwai wanda ya iya maganar kurame ne anan nakirashi seya muku bayani da kanshi? Wanine daga cikin 'yan jaridar yace

"Amma Ranki ya dad'e majiya me tushe ta tabbatar ance yanayin magana da zab'abb'un mutane ne kawai akan wani babban dalilin daya barwa kansa sani, mezakice game da wannan" Murmushi tayi

"Mekakeso nace maka to? Idan har akwai zab'abb'un mutane a rayuwar sa tokuwa koda banzo ta farko ba zanzo ata uku, kuma ni kaina dazanji sautin muryar mijina danafi kowa farin ciki, inama ace Allah  ya amshi bakunansu yanda ya bud'e masa jinsa harshensa ma ya soma motsi aida munyi farin ciki, banaji idanda ace prince Allah ya bashi damar magana zamu b'oye wannan baiwar, dan kuwa har gobe bamu dena nema masa magani akan hakan ba" Wani daga gefe yace

"To Ranki ya dad'e ke a haka kina magana kika yarda kika aureshi matsayin sa na kurma wanda baya magana" Yanxu kam hawayene suka wanke fuskarta cikin fad'a tace

"Kurma ba mutum bane? Ko gani kake kafishi? Acikinku babu wanda ya baiwa kansa ilimin ji gani ko magana, kyauta ce Allah ya baiwa wanda yaso sabida haka ni koda gurgune yafiyemun mutane marasa nagarta irin masu yad'a labarin k'arya, dik wanda ya kumanbuga labari mara tushe akan prince da ahalinsa wlh kotuce zata rabamu, ku barshi yaji da abinda ya dameshi, kokuma nayi sanadin da gaba d'aya gidajen jaridunku da gidajen radio ku dama na tv zasu dena aiki har abada" Nan sukaci gaba d'a wurgo mata tambayoyin su amma bata kula kowa ba tasanya kaintabar wurin tana sharar k'walla, abun ya mata ciwo ainun mesa mutanen nan basuda adalcine akan komai? Meya tsare musu bata ganinsa da hayaniyar komai, baya shiga shirgin mutane, wayarta ta janyo ta duba acc nata taga ruwan dala aciki kud'ad'en da aka ware mata musamman dan biyan buk'atunta na yau da kullum, kawai daga zuwa Fadar sarauni wanka tayi ta shirya ta kira waya aka shirya mata driver sannan ta fita, bata tsaya ko inaba se tsohuwar makarantar datayi secondry school anan garin, batasha wahalar ganin malamin nasu ba, yasha mamakin ganin ta sosai kafin suka keb'e tana murmushi tace

"Sir taimakonka nake nema dan Allah" kallonta yayi sannan yace

"Bakida matsala Miss arrogant, ina saurarenki"

"Sir nasan ban isa na samu ilimi akan computer ba tunda dacen ma baso nake ba, as u know dai sam banason karatu, amma a ire iren kallon american films danake naga idan sunason su gano abu suna amfani da abubuwan dasuka shafi computers wurin gano abubuwa da dama kaman su trackers dinnan, CCTV camer'as irin wanda basa buk'atar dogon wiaring na wutar lantarki da dai sauran abubuwa, to ban saniba ko kanada ilimi akan hakan" kallon mamakinya sakar mata

"Ke kuwa Miss Arrogant meya kaiki? Me zakiyi da wannan abubuwan? Mirmushi tayi

"Malam dik wanda ya taimakeni akan wannan aikin nawa zan bashi dala dubu d'aya"  Kallon ta Malam yayi

"Hafsat a nufinki dubu d'ari biyar da goma sha biyu? Ke ina kikaga wannan kud'in? Wani murmushi tayi

"Malam idan ka had'ani da wanda ze taimakeni zan baka dala d'ari biyar, albashinka na wata nawa kenan a kwana d'aya" Mik'ewa yayi tsaye

"Idan dai zaki bani  wannan kud'in muje na had'aki da Zubairu mass com danshi k'arshene sosai  a wannan b'angaren" Tana murmushi tace

"Muna zuwa zan bakasu bawai se anjima ba Sir" Yana washe yace

"To Miss Arrogant muje" Haka suka fita ya shiga gaban motar dogarawa ya zauna ita kuwa tashi k'atotuwar jeep baka k'irar land cruiser prada akaja suka tafi.

Basu wani sha wahalar neman Zubairu Masscom ba, anan dai bata b'atawa uncle nasu lokaci ba ta sallameshi ya tashi yana godiya tare da mamakin yaushe 'yar shara ta samu duniya har haka take yawo tare da dogarawa cikin manyan motoci na alfarma?




Hammood kai kawo yake da jaridar yamma a hannunsa yana nanata karatun maganganun da Hafsat ta fad'a, wato tsakani da Allah dai Yarinyar nan so takeyi tayi wasa da hankalin sa, ta gama fallasa asirinsa kuma sannan yanzu takeso tayi amfani da hikima da dabara wurin kawar da tunanin sa akan cewar itace ta fad'a, yaya ze aminta da wannan? Banko k'ofar d'akin da akayine yaja hankalin sa ya juya yana kallon Khairiyya da gaba d'aya wunin ranar be sanyata a ido ba, a hankali ta tako zuwa inda yake fuskarta gaba d'aya tashin hankali ya bayyana tace

"Me kakeso ka mayar danine wai Hammood? Anya baka baiwa Hafsa dama da yawa ba kuwa? Tafita a media tana yayata

Please Login or Register in order to submit comment