Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saki nauyinta akan sumar daya rik'e idanta ya rufe ruf, da sauri ya taro ta, ya sake sumar kan nata yana Jinjjigata, khairii dale fatan Allah yasa Hafsat mutuwa tayi tace

"Honey la gani ko, kasanfa Bahar tace mana ba lafiya ta ishi Hafsat ba akanta, lallab'ata kawai zakayi bawai dukaba, kuma rik'on sumar kai irin haka akwai azaba" cak yayi sama da ita zuwa kan gadon ta, ya bud'e k'aramin fridge dake wurin ya d'akko ruwan sanyi ya b'alle murfin robar ya kwarara mata amma ko gezau! Hankalin sa ne ya tashi sosai, ya kwasheta driver kawai ya kira suka bar gidan, bayan motar ya sakata ya zaune shima a abaya ya d'aura kanta a saman cinyar sa, banda kallonta babu abinda yake, lana ganin yanayin ta kasan cewar she's in deep pain, to meyayi zafi haka? Se danna k'irjinta yake amma ba numfashi, da k'yar yaga sun isa asibitin, aka karb'eta zuwa Emergency. Iyashi da driver suka zo Kuma ko wayarsa bezo da iya ba, kusan 2hours tana jiran gawon shanu Kafin likita yazo kiransa.

A Office likitan ya kalle sa da kyau yace

"Na duba file na patient d'inka, lokacin da akace ku dawo a mata surgery baku dawo ba, Kuma yanzu gashi wani abu ya k'ara dukan kanta kome jinin kan nata ya k'ara yawa, jijiyar dake kula da d'abi'un d'an adam na kanta wani jinin ya Kuma harbawa aciki, na rasa dalilin dayasanya bakwa kulawa da lafiyar yarinyar nan, anya kuwa iyayenta suna tare da ita? Kofa damuwa bamaso tana shiga kaga yanzu da k'yar muka shawo kanta, Zata tashi lafiya lau amma tabbas bazata iyayin komai da babba keyi ba, zakuyita hak'urin behavious nata zuwa wata uku masu zuwa, semuyi aiki mu cire jinin duka, Zara samu lafiya bayan nan, yanzu idan muka tab'a kanta komai ze iya faruwa" Nisawa yayi, mekenan yayi? Kawai sabida zuciyar sa ta rufe seya hauta da zalinci, kallon Dr d'in yayi

"Nagode dr, zuwa yaushe zamuke zuwa check up Kuma yaushe zaku sallame mu?

"Se zuwa gobe gaskia koma jibi, se munga jinin dake fita a hancinta ya dena zuba gaba d'aya" Jinjina kansa yayi sannan yayiw likitan godiya ya karb'i takardar maganin yafita, driver ya tura yaje ya d'akko masa kuyangi biyu inda yafita sayen maganin.

Lokacin da yake magana da nurse d'in akan zancen maganin daya saya,lokacin ne Amina da Barira suka shigo asibitin barre dayasan dasu ba, atare suka kalli juna sannan da sauri suka koma da baya suka lab'e, Amina jikinta had rawa yake sanda ya zaro wayarta da aka Tanada aka bata aka turo mata wani ya kawo mata layi takanas sabida irin wannan aiki, Message ta turawa wata lamba da cewa

"Bayan was biyu ka kirani, akwai labari meban al'ajabi" Seda sula kimtso kansu suna ganin ya nufo kofar barin wurin suka fito, atare sula gaishesa be amsaba ya kaisu d'akin Hafsat suka duba ta, sannan yabarsu anan ya tafi.

*Jiya taro ya tab'an keyboard d'ina gaba d'aya na gagara typing, da k'yar ko yanzu nayi wannan ya sayan keyboard bana gane kansa, zuwa dare zan Baku post d'inku na dare, nisha Allah, koma yamma*

Mom Nu'aiym.

*Mutan wattpad sam bakwa kyautawa, Rowan comment, ga rowan votes, da gaske zan dena posting muku.*

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

   *NA:BILLY GALADANCHI*

*Masu tambaya akan yanayin ciwon hafsat, tabbas ana samu, anyi a unguwar su antyna, nasan yarinyar kuma har yanzu datayi aure ta haihu befi idan abun ya tashi mata ba tayi wasan k'asa, idan fatan kun gamsu.*


*SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI*
17.
Seda suka zauna sannan suka kalli juna, gano yanayin cewar Hafsat bata cikin hayyacinta ya sanya Amina tace

"Kinji abinda naji kuwa? Kinga abinda na gani Barira? Kamar fa Prince Mood nagani tsage tsage yana magana da waccen nurse d'in ko" Ita kanda Barara mamaki bawai ya barta bane ba ta kalleta cikin jimami tace

"Amma ke Amina banace ki rabu da shiga shirgin Idan fad'a ba? Banace ki rabu da d'aukar muhimman maganganu kina gaya musu ba, ke yanzu 'yar wannan gulmar damuke a tsakanin mu bata ishemu ba sekin d'auki magana kinkai wa idan fada, kuma kina sane da cewar k'yas kawai suke jira kisa ma zasu iya yi" Turo baki gaba tayi

"Haba Barira ke sam bakya tab'a dubawa ci gabanmu koda wane lokaci ci bayanmu kawai kike kallo, a bauta zamu mutu? Iyaye da kakanninmu haka suka k'are suka auri bayi suka tabbata a bayin su, yanzu mu banbancinmu dasu d'aya shine munsamu mund'anyi makarantar bokon nan, a duk cikin fad'in fada gayamun idan ba idan fada ba wayake ta tamu? Magana idan kikaga sun mana toko tabbas aiki zasu sakamu, da gaske tona masa asiri zanyi kowa ya huta" Rik'o hannunta Barira tayi

"Kada kiyi haka Amina, nifa ina ganin ma kamar bawai magana yake mata ba, koke kinji sautin muryar sa, akan wane dalili ze dawwama da harshe me motsi yana dak'ushe tasirin sa, wane d'an adam ze tabbata kurma har'a wurin matar sa alhali yana magana, nida ina tunanin kawai motsi yake da bakinsa tunda kinga har hannun sama yana motsi, ta yiyu matar batajin yaren kurmanci, kinga dole yayi yanda zata fahimta" Shiru Amina tayi tana kallon yanayin Barira tare da tunanin kumafa hakane? Barira ganin Amina ta d'auki maganar datake gaya mata yasanya tace

"Idan fada ko jininsu basu ragawa ba bare mu, ya dace mu tabbatar dakoma meye kafin mu sanar dasu, bayaga haka yanada kyau sosai mu iya kame bakunan mu mu dena shiga sha'ani irin wannan daya shafi rayuwa da mutuwa, kiyi komai amma ki kiyayi d'aukan hakk'i wannan shine iyakar abinda zan iya gaya miki, idan kunne yaji gangar jiki ya tsira" Nisawa tayi

"Toni dana rigada nakira Baba babba yanzu inya kirawoni mezan gaya masa" shiru Barira tayi kafin tace

"Kice dashi kina tsammanin ciki ajikin amaryar prince" Jinjina kanta tayi alamun gamsuwa "Dama kuma kinsan suna tsammanin baze nemi mace ba"

****************
  Barra dai jiki yak'i dad'i, daga asibiti an kuma dawowa da ita gida, wannan karon da kanta take addu'ar neman mafita daga wurin Allah, tasani wannan wata ayace, watak'il sabida yanda take neman haihuwa ne ido a rufe Allah ya jarabe ta a yanzu kam gwanda mata lafiyar ta akan wannan bak'ar wahalar ga zullumin ganin kamar zata mutu. Sun dawo asibiti da kwana biyu lolacin cikinta yacika wata biyar ta haihu, haihuwar d'an tayi ba'ako gama halittar saba amma kana kallon jinjirin zaka gano cewar mace ce, shida kanshi yasha wahala ainun, kuma anan se jini yak'i d'aukewa baya dai b'ulala kaman da amma tas yak'i ya d'auke se wasa yake mata da hankali, hankalin uwarta ya tashi tashiga damuwa me tsanani akan rayuwar da Barra  take ciki, anan aka duk'ufa wurin karb'o mata magunguna da addu'o'i irin gargajiya tunda asibiti yaki yi.

    Tunda aka sallamo Hafsat asibiti abubuwan datake sunfi k'arfin tunani, gabaki d'aya be wuce ta zauna tayita gwab'e abinci a wuri ba kokuma, tayita surutai irin na yara, ko irin tabi'un yara, kuka ba komai bane akan tanason abu idan ba'ayi mata ba, ga Mood se b'oye b'oye yakewa Bahar bayaso tasan halin da ake ciki, kusan sati hudu kenan yana fama da Hafsat ga tsananin tausayin datake bashi, bahar naso tayi waya da Hafsat amma wayar hafsat d'inma tana hannunsa ya kashe ko school ta dena zuwa sabida yanayin ta. Yauma kamar ko yaushe yana zaune yana aiki a laptop dake gabansa, wani kamfani suka bashi aikin zanen tiles yake so ya kammala yaje yanzu takai musu yanada presentation ba, zama tazo tayi kusa dashi shiru kamar me nazarin wani abu,se cen kuma ta sanya rigarta abakinta tana tsotsawa, kallonta yayi rigar ma gaba d'aya be dace ta sanya shiba, ya gayawa Barira kuma take kula da ita tadena barinta tana sanya gajerun kaya tunda ba hankali bane akanta, yanzu ta yane rigar zuwa bakinta duk ga pant d'inta nan afili, kawar da kanshi yayi sannan ya mik'e daga wurin zuwa d'akin sa batare daya d'auki komai na aikin saba,ganin ya tashi a wurin ya sanya ta saka hannunta tayita dandanna lambobi gaba d'aya seda tayi erasing aikin dayasha wahalar yi wuni d'aya, koda ya dawo da sauri wurinta yazo ya karb'i laptop d'insa yana duba, a zuciyar sa ya soma ambaton Allah sannan ya juyo ya wanka mata mari, so yake ya taushi zuciyar sa akan karya ci gaba da dukanta amma seda ya shureta, da gudu ta nufi d'akin ta tanata zuba kuka me k'ara sekace ta goye, haka yabar gidan ransa a b'ace a dole ya lalubo zanen farko daya gama yace be masa ba ya nuna musu, ga mamakin sa se murna suke suka karb'a hadda k'arin kud'in aiki, yayi godiya sosai sannan ya wuce presentation shima na zane nez sedai wannan bedding company ne ke neman zanen sa yaje ya nuna musu tasa k'warewa danshi be tab'a zanen gado wa kampanin ba, bashi ya dawo gida ba se after 9, inda ya tarar da hafsat still tana kuka. Kuyangin ya tara shiba sabawa yayi da magana dasu ba, yarasa dalilin dayasa tunda hafsa tashigo rayuwar sa yake yawan son yayi magana, yanzu da wanne bakin ze tambayesu dalilin kukan hafsat gashi khairiyya tayi bacci, wayarsa ya zaro ya rubuta

"Ina hafsat? Kallon Ameena yayi ita yagani da waya rannan ya haska mata wayarsa karancewa tayi a hanzarce tace tana duk'ar dakanta

'Ai ranka ya dad'e gaba d'aya tunda ka fita take kuka, ga jikin nan nata ya d'auki zafi, se jijjiga takeyi, mun rasa gane kanta, nayi rarrsshin duniyar nan tak'i, kowama ya rarrasheta don ganin yanayinta amma sam tak'i ta saurare mu, daga baya Princess tace mu barta tunda tak'i tayi shiru ta kashe kanta, yanzu kuma danaje gunta bayan marib sena tarar har yanzu kukan take ga jikin nan rau" Dafe kanshi yayi, bashida zab'in daya wuce lallai ya gayawa Bahar matsalar nan, bayaso ta dinga fad'ane ta tashi hankalin ta ga abinda ya faru da Barra amma ya zeyi, ta soma  shinshino gaskia dan bayan magrib ba rigimar da bata saka masa ba akan tanason magana da Hafsan, shiga yayi d'akin datake ya zauna a bakin gado, kai hannun sa yayi ya shafi wuyanta nan take yaji zafi rau, nisawa yayi  ya dafe kansa, ya kwaso gajiya ga kuma wata gajiyar nan akan sa,  magungunan ta ya duba ya d'akko yazo ya tsaya kawai yana sauraren sautin kukan ta tana bashi mugun tausayi, yama zeyi ya bata maganin, juyawa yayi yaje ya yafito wata kuyanga dabhannu ta biyo bayansa har d'akin, nuna mata magani yayi da ruwa nan take ta gano me yake nufi,tasan yasha yi musu  fad'a akan irin wannan sakacin da maganin ta. Tashinta zaune tayi amma tayi tayi tasha maganin tak'i, kallon ta Mood yayi ya mik'a mata hannu ta zuba masa maganin ta ajiye ruwan, shine da kansa ya tallafeta ya bata maganin kuma ba musu ta karb'a tasha, tea ya had'a da kanshi ya tilasta masa shanshi..... Be zauna cikin gidan ba mota ya hau yafita seda ya samu wuri me sirri sannan ya kira Uncle Jay, bayan sun gaisa Jay yace

"Son mesa zaka alk'awarin daka d'aukarmun? Kafasan koni nan baso nake muke magana dakai ba koda a wayane kuwa, meye yasa kaketa nacin kira amaimakon message? Nisawa yayi

"Amma U Jay bana kok'ari, abun nan yana damuna, ga abu ina kallo inaso nayi magana ba hali ka barsu su kasheni mana, ni wlh nagaji" Cikin tausayin sanyace

"Mahaifiyar ka fa baka tunanin ta? Kuma nifa baka tunani na ehn Hammood?  Yana share k'wallah yace

"Its really hard for me to leave like this Uncle, matar aurena bazanyi magana da itaba, wannan yarinyar Hafsat batada lafiya sosai, abubuwan sunyi yawa yanzu yamafi yawa she's always behaving childish, kuma ni setake mammak'ale mun tamkar mi ubanta ne, abinci ma seta ce sena bata, kuma sosai take shiga jikina, bayan haka tayita saka suturu irin kamar tana tsirara uncle kasan be dace nake ganin ta a haka ba, uncle tayita nanuk'emun inaso na saka hadimai su mata abu banida bakin magana, ko magani se idan ina nan zatasha, ga b'arna kamar yar shekaru uku, wannan abubuwan kuma sunata haddasa fitina a tsakanina da khairiyya ta matsa akan na mayar da ita gida nikuwa abinda nake dubawa aikin ta saura sati shida, yazan maidata gida a haka" Nisawa Jay yayi kafin yace

"Duk na fahimci matsalolinka amma wannan bashi bane ze sanya kayi magana koda danine kuwa, a U.S kasan bana hanaka magana, amma yanzu bakai kad'ai bane, idone da yawa akanka kamar me, kowa motsi kad'an yake jira" Shiru yayi kafin yace

"Yanzu gaba d'aya Uncle so kake na tabbata a haka, so kake inci gaba da zama a wannan rayuwar ta rashin 'yanci, magana yana cina abin nan yanamun zafi yana dagulan lissafi" Cikin tsawa yace

"To Umminka mutuwa tayi? Waikai mesa wani zubin sam ba'a gaya maia magana kaji ne? Ya kakeso nayi, Barira ma gatanan bata tsira ba, idan suka mayarda hari a kanka tun yanzu zaka iya dasu ne, na gaya maka lokaci beyi ba, ba yanzu zakayi magana kowa ya sani ba, kuma daga yanzu karka kuma mun wannan maganar" Sauke wayar yayi daga kunnensa,guntun hawayen dake mak'ale a idansa ya dauko, mesa aka haifeshi a cikin wannan gida me duhun gaske, mutane suna masa kallon d'an baiwa danshi ubansa sarki ne, amma shi irin rayuwar su itace take burgeshi, itace yake muradin samu, rayuwa me cikeda kwamciyar hankali......Jay dafe kansa yayi lokacin dayake gudun yazo yazo masa da sauri, ga Barran sa babu lafiya itace tunaninta yake da amfani a irin wannan gab'ar, yaya zee tinkareta da wannan maganar alhali tana fama da kanta!

Yana shigowa gidan da Barira yayi karo, da sauri zube ta gayar dashi beko kalleta yau halin ya motsa, ganin haka da sauri tace

"Ranka ya dad'e Princess Hafsat fa sam jiki ya hanata sukuni, tun fitarka take ta amai, ga kuma jini dataketa fitarwa daga hancinta" Da sauri ya kalleta, cikin jimami yayi d'akin datake acen ta sameta wahale, yanzun ma aman take kwad'awa, rik'ota yayi yana mata kallon tausayi tamkar shima zeyi kukan, seda ta gama sannan da kanshi ya goge mata baki ya tafi da ita gaba d'aya jikin sa, jinin hancintane ya kuma b'allewa idanta se lumsashewa yake, yanzu kam yama rasa me zeyi, zuciyar sa tana bugawa sauri da sauri, hannun sa ta rik'o tace

"Ka kaini wurin Baba jere in gaya masa sharri Bilal yamun ya yafemun su barni in zauna awurin su, dukana kakeyi kaina yanamun ciwo, so kake ka kasheni nikuwa banaso in mutu yanzu, Bilal ne ya rabani da dangina gwara intafi wurin su sumun azaba da wutar k'arfe akan wannan ciwon kan, kaina ze tsage gida biyu, nagaji da dukan nan da kakemun, kayi hak'uri ka dena dukana ban maka komai ba" kallonta kawai yake amma bece mata komai ba hartakai k'arshen maganarta, wani azababben yaji ya tokare masa mak'ogwaron sa,me kenan hafsat ta samu sauk'i ne kome? Yana tsakiya da tunanin yaji ta sake kamo hannunsa

"Wurin Baba jere zanje, da kakata me sona, kaina yanamun ciwo sosai" Khairiyya ce ta shigo d'akin kamar zata tashi sama, tana yatsine tace tana kallon su

"Haba Hammood, wannan wane irin salon tambad'ewa ne? Yaya zaka tasa baliga a gaba kana mulkar jikinta? Bayi da kuyangin wurin yabi da ido kafin 1 sec duk sun b'acewa ganin sa, mayar da idanshi yayi akan khairiyya ita kanta bata tab'a ganin irin yanayin data gani a fuskarsa ba, dukda sabida ta fusata hannu takai ta figi Hafsat ta wurgar da ita a k'asa tana haki

"Shegiya karuwa, ki mik'e daga aikin ciwon k'aryar dakike kibar nan wurin, haba jama'a yaya za'ayi ka ringa biyeta kaima naga alamun tsohon d'an iskan n.....kafin ta rufe bakinta taji saukar lafiyayyen mari, da d'an yatsan sa ya mata alama akan cewa karta kuskura tayi tunanin alak'an tashi da wannan kalmar, tana hauka ne! Da kanshi ya d'auki Hafsat bashida zab'in daya wuce ya kaita asibiti, ya zame masa dole yasan meke sanyata wannan hab'on ga alama ma ta dena abubuwan k'urciyar dasuke neman addabar tunanin sa, Allah ya bata lafiya.

Bayan dogon Bincike likita ya tabbatar betab'a ganin jinin daya haura acikin kai ya sauka da kansa ba se yau, dan haka yake congratulating Mood akan ba'a buk'atar wani surgery sedai a yanda ya kula jinin yabar tabo ajikinta, duk abinda yake ba damuwa ko hayani ya tashiga kanta zeke rik'a sara mata, kuma jinin hancinta kowane lokaci ze iya fallewa ya dinga zuba, se se'a kiyaye faruwar abubuwan, allurar bacci aka mata sannan aka bata jonin ruwa, yayi addu'a yayi hamdala so dubu, danshi harga Allah ya gaji da wannan Hafsatun, tunda tazo rayuwar sa yau wannan gobe wancen hartakai yanzu ace ya d'aga hannu akan khairin sa abinda koda wasa be tab'a tsammanin ze tab'a yiwa matar auren saba, turai nurses ne suke kulawa da patient sedai relatives suzo dubiya amma banda kwana wannan ne ya tilasta masa barinta ita kad'ai ya komai aikin rarrashin matar sa.

Tunda Bahar taga Barra ta warware se hankalinta ya kwanta, jinin daine yak'i ya d'aga k'afa seyayi kamar ya tafi sekuma ya kuma dawowa sedai wannan karon bame yawa bane ba, dan haka suka d'auketa suka mayar da ita gidan mijinta dayake ta sintiri kaman zariyan dillali. Da kanta tai ayyukan ta gaba d'aya har girki ta tsala ado kamar ko yaushe ta zauna a parlor tana jiran shigowar mijinta, lokacin daya zo kallo d'aya zaka masa ka tabbatar cewar yana cike da farin ciki, mik'ewa tayi suka rungume juna lokaci d'aya suka soma hawaye atare, tallafo kanta yayi yana murmushi kafin yace

"Barratu 'yar aljanna, nayi kewarki sosai, Barra na duk kin gama ramewa narasa meke damunki haka" kallon sa itama takeyi

"Kewarka kad'ai ta isa tayi arangama da nutsuwar dazata bani damar cika k'ugu, banida nutsuwar ciyar da kaina ban saba hakan ba, haka kuma banida kwanciyar hankalin dazan kwantar da hankalina tunda bana tare dakai, nayi kewarka sosai mijina, banida tamkar ka a duk fad'in duniyar nan, bana fatan yau ace baka duniya ni ina cikinta, gwanda na tafi sabida idan baka raye banga amfanin rayuw....rufe bakinsa yayi anata lokaci d'aya suka fara saukar da numfarfashin missing juna dasukayi, yanda yake rik'e da bayan k'eyarta haka itama take rik'e da kunkurun sa shawagi take akan iskar gajimaren dad'in ma'auratan dake d'ebanta ya d'aura tafukan k'afafunta asaman nasa k'afafun sabida ya daidaita tsawon su, hakan ya sanya ya d'age dukaduginsa yana mata lilo, tun a parlor ya zuge zib d'in rigar ta, sannan ya sanya hannayensa duka biyu ya raba jikinta da bra d'inta yana me sake mata sambatu, ita d'inma hannayenta duka biyu suna cikin rigar k'ananin kayan dake jikinsa tana shashafshi cikin fita hayyacin ta da tsananin shauk'in yanayin dasuke ciki, lokacin daya rabata da skirt d'in ta cak ya d'agata zuwa bed room nasu, inda tuni zaliha ta lab'e tana sauraren holewar da suke.......

*Bayan sati uku*

Yauma kamar kullum Hafsat dabaran zama tayi acikin k'awayen ta wato Barira da kuma Ameena,wanda ta shigewa cikin jiki take nunawa so da kuma kyautata musu a tsakankanin nan, chocolate dake hannunta ta kaiwa cizo kafin tace tana kallon Ameena

"Gaba d'aya agidan nan babu wacce ta rainani irin khairiyya, itafa bata ganin girman mutame, nida ta tawa za'abi da tuni na koma wurin Bahar abuna, karatun nan ba sansa nake ba" Murmushi Ameena tayi, tana k'ask'antar dakai tace

"Ranki ya dad'e nifa laifin duk akanki nake d'aura su, sabida kin bata dama da yawa ne yasa take miki izgilanci, banda haka ina kema zaman auren nan yinsa zakiyi da prince d'in" kallon ta tayi tana murmushi

"To ai yanzu dan taga tashiga gabana ne ki rabu da ita, garin zan bar mata" Murmushin yak'e Amina tayi

"To Ranki ya dad'e ba gwamma zamanki atare da khairiyya ba, duk hatsabiban cinta ai batakai idan fada ba ko? Kuma su indai za'ace yau kai Hammood nashine kai tokuwa yaseen sesunga bayanka" Zabura tayi irin da mamakin nan

"Bayanka kuma? Kamara yaya? Kina nufin wai akwai wasu mugwaye sama da khairiyya a fada, amma ni ai bansan dasuba" Murmushi Ameena tayi

"Tayaya zaki sansu? Ai idan fada baka isa ka sansu ba, sedai kuyi waya komai kaiwarka k'arshe a naci bazaka tab'a sanin su waye idan fada ba, sedai idan kana musu aiki to a san nan ne fa, zakaga iya yin waya dasu duk masifar ka sedai kaji muryar su" Jinjina kai tayi sannan ta sunkuyo cikin rad'a tace da Meenan

"Nifa inaga sune sukayo hayata inzo in kashe musu hammood, dan kuwa ban tab'a ganin suba, kawai mahaifina ne bashida lafiya sukace zasu kaishi asibiti sun had'u damu akan hanya, sukace indai mun yarda zasu taimakemu amma da sharad'i, inzo awa prince sharrin yamun fyad'e daga nan sunsan aura masani za'ayi naci riba biyu" kallon Meena tayi ta d'aka mata duka

"Koda yake be dace ina gaya miki sirri naba, ban gama yarda dakuba, nasani ko kuma idan fadan ne" Barira cikin hanzari tace

"Ban shiga k'ungiyar ba amma Meena ta shiga" rik'e baki Hafsat tayi

"Mesa bazaki shiga ba? Ki shiga hanyace dake b'ullewa, dan kin ganni nan, se inda k'arfina ya k'are akan nemawa mahaifina lafiya kuma fa gwala gwalai duk sekin saka idan kikayi aikin dasuke so" Murmushi Barira tayi

"Allah ranki ya dad'e ni sone banayi a cutar dawani ata sanadiya na" Murmushi itama tayi

"Nidai dan Allah ku rik'emun sirrina, banason wani abu makaman cin tonon asiri, ku bakusan idan fadaba amma ni nasan su, kuma anan garin zamansu nakeyi, abinda ya b'atawa aikina gudu d'aya ne shine wannan rashin lafiyar kuma yanzu na warke, sabida haka aiki tuk'uru yanzu ma na fara, kuzo mu had'e kai dukkan mu 'ya'yan talakawa ne, kowafa kansa ya sani muyi aikin mu atare kowa da aikin dazatayi, ku dubi kanku karku dubi wanin ku" Barira yanzu kam tafara hawa kan netwrk yanda ya kamata tace tana gyaran zaman ta

"Wane irin aiki zamu miki Ranki ya dad'e" Murmushi Hafsat tayi kafin tace

"D'aya daga cikinku dole zata koma Nigeria, itace zata zama idanmu acen, kunga yanzu idan nace da Bahar auren nan nakeso ayi wlh ko sati baza'ayiba se an d'aura kunga munsan sirrin juna ku kwantar da hankalin ku duk zan taimakeku, ke Barira kinfi Amina wayo ita kuwa tafiki iya munafurci" kallon juna sukayi tace taba dariya

"Mamaki na baku ko? Nifa da aljanu nake aikina? Dan kar wata acikinku tayi tsammanin zata iya cutar dani, bara na baku misali

"Sanda aka kaini masarauta bakwa k'aunar ganina, ke Amina kina sani kika jefoni daga sama, kuma idan fada ne suka sakaki alokacin suna tsoro in tona musu asiri! Da sauri ta kalleta, murmushin cin Nasara hafsat tayi ta k'udurta aranta seta binciko ainahin tarihin masarautar Daulatul Dinar ta tonawa Idan fada asiri

"Karkiyi mamaki idan na gaya miki cewan nasan cewa kinso kiran waya ki sanar akan wai Hammood yana magana" Atare suka kalli juna Barira tace

"Ranki ya dad'e kodai kinji sanda muke maganar ne mun zata bacci kike lokacin? Murmushi tayi kafin tace

"To itama gulmar dakukaje kukayi wa khairiyya akan niba kowa bace ba ina bacci awurin kukayi? Ke Amina kece bakinki a sama se bayan kun fito Barira ke tattareki" Sautin cikin Meena ne ya bada k'uuuuuu, Hafsat tana murmushi taci gaba

"Ko idan fada a tafin hannuna suke, dan uban dasuke takamar sun hadu dani atare dashi duk shirin boka nane banko sanshi ba, sannan kuma ke dan tsaurin ido wai hammood kikeso" Fitsari ne kawai batayi a wando ba amma seda ya d'an d'igo, Hafsat ta tab'e baki taci gaba

"Har number wayarki inada ta k'asar nan kuma kodai kumun biyayya kona had'aku da Hammood a k'asar nan seya sanya a kashe yarinya tazama tarihi kamar ba'ayi taba, duk abinda kuke fad'a inajin ku boka yana gayamun, duk zagin dakukewa hammood inadashi tas a akaina, na gaya muku wannan ne sabida karku d'aukeni da sauk'i, Hammood da gaske kurma ne sabida haka kar inji kinje kin fad'i akasin hakan, ke kuma Barira ya zame miki dole kimun aiki, idan ba haka ba wallahi abinda

Please Login or Register in order to submit comment