Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nakeji" Murmushi yayi "Damsel am so sorry for that day, namiki alƙawari gajimare kawai zan riƙa ɗaukar ki muje tunda naga shi akwai daɗi" Rufe fuskar ta taƴi da tafukan hannayen ta

"Yaa Mood bakada kunya" Ta furta har lokacin fuskar ta a rufe, yana dariya yace...

"Suuuuuu yaa mood na gaji da tsayuwa" Tunawa da tayi tabbas ta furta hakan kawai seta ɓare masa baki ta fara kuka seda ya dawo rarrashi, gaba ɗaya Hafsa ta tsani a tsoka ne ta shikuwa Mood yafi tsokana nan gaba kaɗan setayi tekun hawaye indai Mood ne. Seda ta dena kuka loƙacin ys rufe mata jikinta sannan yace bayan ya rufe nasa jikin

"Maza tashi na miki wanka, gwara muje in gayawa Bahar ina tattalinki kuma in gaya mata yau har duniyar gajima re na kaiki, dama inason in ƙara aure, kinga idan taji na iya tattali, ƙawar nan taki Ameena, wannan baiwar ita zats auramun inason fararen mata" Filo ta ɗauka ta wurga masa ta kuma fashewa da kukan daya rasa dalilin sa...

Jama'a na tafi hawan gajimare lollxx...

*Mom Nu'aiym.*


*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA TARA*

          39.
Daƙyar ya yi aikin rarrashi, sannan yau Hafsa ta tabbatar wa kanta wannan rayuwar itace zaɓin ta, meyafi daɗin ayi maka wanka, a san ya maka tufafi bayan an lafce ka da man shafawa.

  *SAFIYA*

Ƙarfe takwas na safiyar rananr agidan tayiwa Bahar, tazo ta tarar Hafsa tana bacci, Mood dake falo ta harara kafin tave tana taɓe baki "Kai ina Jikata kums ƴata" Girgiza kanshi yayi kafin yace "Ohh matata wai? Bacci take meye?  Dundu ta ɗaka masa a baya

"Ja'irin yaro ni zaka gayawa sanabe? Matarka ma kake gayamun, zakamun bayani ko kuwa, yau inaga ka ɓalla mata ƙafa ɗaya ko? Murmushi yaƴi sannan ya gyara zaman sa

"Dama wurinki zanje yanzu, maganar Hafsa. Jiya Momyn ta tamun waya akan maganar mahaifiyar ta, nasha mamaki sosai wannan ya sanya nake cewa zanje nayi ƙwaƙwaran bincike akan hakan, ban gama aminta ba" Kallon sa tayi cikin mamaki sannan tace tana kaiwa zaune

"Meta sanar mata ne? Gaba ɗaya ni bata sanar dani akan komai ba" Murmushi yaƴi sannan yace

"Idan aka motsa kice Jikar ki ƴarki, gashinan dai kinga nafiki matsayi a gunta" kallon takaici tayi masa kafin tace,

"kaga zaka gayan ne ko kuwa?

"Bahar kinsan meta sanar dani? Tsaki taja cikin masifa tace "Dole in sani mana tunda abun saukar wahayi ne" Dafa kanshi yayi yana dariya kafin yace

"Cewa tayi ƴar sarkin fulanin wuro ce taya haka zata kasan ? Magana take akan Masarautar Sarki Me Fura, Malam Arzika Djoro" Shiru Bahar tayi kafin tace "Tunani na bawai akan gaskiya ko ƙaryar abin bane ba, tsananin kamannin Hafsa da kuma Surbajo nake hasashe kamar karka ambaci Sarkim Fulanin Wuro" kallon ta yayi da mamaki "Surbajo kuma da Hafsah? Tayaya? Gyaran zaman ta tayi kafin tace

"Surbajo da kake gani mahaifin ta shine tsohon Sarkin fulanin wuro me rasuwa, a yanzu haka ɗan sa ne akan  mulkin wato Arzika Modibbo Djoron daka faɗa, ita sunan mahaifin ta Modibo Djoro,abin ma daya ƙara kawoni shine akan matsalar ita Surbajon, sam bata maganar gida idan na mata maganar seta saka kuka tamkar dai am mata kurciya" Ɗan kallon Bahar yayi cikin mamaki sannan yace

"Kaina ya ƙulle sosai, tayaya haka zata faru? Babu shakka Ubangiji me girma da ɗaukaka ne, idan har ya zamana Hafsa jinina ce to ko tabbas zuwanta a rayuwa ta akwai wani dalilin, ambatar kalmar kamanin da kikayi tanayi da Surbajo seyaja tunani na zuwa ga kawo siffar Surbajo a kusa, tabbas murmushin su kaɗai yana kamancece niya dana juna" Nisawa Bahsr tayi ƙafin tace

"Maza tashi muje wurin.Momyn tata, inason sanin gaskiyar labarin" Miƙewa yayi  ya shiga ciki ya ɗakko key sannan yazo suka bar gidan.

**************
   Lokacin dana koma ƙauyen dana dakko hafsa da sunan zan bata haƙuri akan abinda ya faru senayi rsshin sa'a dajin akasin labarin abinda nake tsammani, gaba ɗaya Bilal ya lalata sunan Hafsa ta dawo mara tarbiƴa a idan dangin ta, haka fito gwiwa a sace sedai me kakarta wacce ta haifi ubanta wato Baba suwai seta janyoni gefe tace dani

"Barira akwai abinda nake so in gaya miki akan Hafsa" Nan take cewa dani,
"Yarona Kabir ya taso yana son kiwo sosai mu kuwa gaba ɗayan mu nan gidan maƙera ne bama noma baku ma kiwo. Yasha wahalar duka da kyare akan yaƙi gadon gidan su awurin mahaifin sa da kuma sauran ƴan uwan sa, amma sam.be saka yaja baya ba, ni kaina nayi dukan nayi faɗa amma a banza, dukda ni bawai na hanashi kiwo bane nace ne ya haɗa da ƙirar amma sam seyace bazeyi ba, nayi rashin sa'a ne Kabir yanada kafiya! Haka girma yazowa Kabeer yace tas matan garin nan bayaso kowa se wata Nufaina ƴsr ƙauyen tsallaken nan wacce gaba ɗaya mahaifinta da Jere me ƙira basa shiri haka yarinya ma ta kafe amma me se kawai suna zuwa da maganar iyaye suka ce basusan zancen ba, shekarar su biyu suna faman neman ysnda za'ayi amma ina kowa mahaufin sa ya dage. Wata rana muka tashi wuni cur ba kabeer! Babu wanda ya damu saini, dik rintsi baya magarib a ko ina sai a nan gidan amma ranar shiru, muna nan sega samari maza daga ƙauyen mijiye sunzo neman wai ƴarsu da makmai akan Kabeer ya sace ta. Nan aka shiga nema da ban baki amma ssti guda ko labarin wanda ya gansu bamu jiba, hankalin kowa ya tashi akayi ta neman har aka haƙura babu labarin wanda ya gansu ma. Watanni suka wuce har wata goma sha ɗaya kullum ba dare ba kuma rana addu'a nake akan dawowar su, katsam rana guda sega su a gidan mu a tare amma tare da jinjira a hannu! Nan take ƙauyen nan ya ɗauka akan sunce sun dawo da shegiya! Sukayita rantse rantse babu wan ya saurare su seni bayan sati biyu na saurari kabeer sabida tausayin yarinyar datake a yashe kullum bame kulawa da ita, dana ɗauketa jere har sakina yayi naƙi in tafi ko ina, haka dai na saurari kabeer ga labarin daya bani.

_"Lokacin damuka bar gida ƙauyen samarin shaho mukaje domin Malam Bargu ya ɗaura mana aure amma semuka yi rashin sa'a malam ya rasu a ranar da muka isa,dan haka bamu ɓata lokaci ba muks ƙara gaba, bamusan ko inaba sedai akwai kuɗi a hannuns dan haka bamusha wahala ba sabida shanu na na sayar! Muka isa wata rugar Fulani se kawai mukace miji da mata ne dan haka aka bamu masauki ɗaki daya, haka muke kwana tare amma wani mummunan al'amari be taɓa shiga tsakanin mu ba dan haka bayan wata tara da kwanaki a garin semuka nemi zuwa wani garin a ɗaura mana aure, anan semu ka isa wata babbar ruga me shirin bunƙasa saboda arzikin su zanma iya cewa rugar ta zama babban garin fulani naga sunada wayewa har karatun boko suke ba irin mu bane ba, anan muka sauka mukayi kusan wata biyu sedaga baya na gayawa Sarkin gaskiya inaso a ɗaura mana aure, nan take ya hau yimun wa'azi akan lallai mu koma gida a mu baiwa iyayen mu haƙuri akan su barmu muyi auren mu idan har muka kuskura muka bari mukayi aure ba slbarkar iyaye har abada zamu tabbata acikin dana sani! Da wannan muka juyo gida munyi nisa a jeji muka haɗu da wata mata ga jina jina ga alama da wuƙa aka yanki gefen cikin ta tana cikin suturu irin na bororin gidan sarautar yamma damu na shaida hakanne danna taɓa ganin su wata rana munje siyan shanu. Tana ɗauke da jinjira ƙarama ɗanyen haihuwa da kuma wata takarda tare da wani abu me kamada ruwan ɗanyen gwal, munso mu ceceta seta ce mu karɓi yarinyar mu gudu mata da ita tanaso ta cikawa mahaifiyar yarinyar alƙawarin tseratar da ran yarinyar datayi, ta bani takardar hannun ta da ruwan wannan ɗanyen gwal tace in adana idan akaƴi shekaru biyar in kaita inda akayi bayani acikin takardar nan, tare da ssyar da wannan ɗanyen gwal in ciyar da ita, tace ƴar mulki ce a bata kulawa! Hadda zoben zinare a hannun jinjirar, muna tsakiya da cewa bazamu karɓi ƴar ba matar nan ta mutu, muna tunanin ya zamuyi da ita kawai muka jiyo muryar ƙarti suna ga layin jini inda ya zuba, ku bita ku kashe ta har jinjirar, da wannan muka yanki jejin a guje bamusan ya sukayi da matar ba. Ya ƙarashe maganar da wlh Baba haka akayi.

Uwar tace "mahaifin sane ya masa tambarin ƙira na fanɗararrun ƴaƴa yaƴi ajalin sa, ta bani takardar da zoben hannun jinjirar da kuma ɗanyen gwal ɗin tace in nemi gaskiyar magansr. Sanda na buɗe takardar sena tarar da bayani kamar haka

"Sarki me adalci, ko bayan raina kasani ƴarka ce wannan dako suna baka raɗa mata ba, na haihu bayan baka nan kayi tafiya, amma Fulani se neman ran ƴar jinjirar takeyi! Na baiwa Adama ita ta gudu mun da ita se bayan shekaru biyar zata dawo da ita, babu tabbacin zan rayu dan haka idan na mutu ta dawo da ita yarinyar tana tsananin kamannu da kai tamkar an tsaga kara, sannan a gefen hancin ta na dama akwai baƙin ƙololo, ayanzu haka inta yamutsa fuskarta kumatunta duka biyu sukan loɓa, zoben daka bayar a sakawa kome aka haifa yana hannun ta. Masarautar sarkin Fulanin wuro, Malam arzika Djoro. Saƙo daga matarka Fulanin Yarima Djoro Hinda".

Sanda na gama karantawa seda nayi ƙwalla, ko wacece Fulani kuma? Kanaji kasan makircin sarauta ne tsagwaran sa, menene daliƙin ta na neman ran jinjira kamar wannan. Driver na ya kaini har garin inda na nemi iso a masarautar da ƙyar, matsalar dana samu ta farko itace awurin Fulani Babba aka kaini, kallon farko naga tanayi mun kallon wulaƙan ci anan na nemi ganin Fulani ƙarama setace ni wacece? Ana haka kawai sega Sarki ban ɓata lokaci wurin sanar masa wa nake nema ba, anan yace a jagoran ceni zuwa gunta har yana faɗa akan lallai idan baƙo yazo ya tabbatar da inda yazo ziyara amasa iso cen, har zan bar wurin sekuma na duƙa na nemi alfarmar ganin su a tare, shida Fulani ƙarama bayan mun zauna sena gabatar da abinda yazo dani tiryan tiryan na miƙa zobe da kuma ɗanyan gwal sannan kuma na haɗa da karanto takardar nan da nan Fulani ƙarama ta rikice akan lallai tanason ganin Hafsa danna gaya mata sunanta, hatta zanin saƙin fulani datazo dashi nannaɗe tana jinjira kai dama kayan jikinta da Babar Kabeer ts bank na nunar mata, haka tayita kukan farin ciki, da ƙyar mukayi akan yau zasu zo kuma tabbas suna kan hanya dan ita da kanta tamun waya akan hakan" Nisawa Bahar Tayi atake ta zube tana godiya wa Allah da irin wannan girman dayafi ƙarfin duniya da abinda ke cikinta, tabbas Allah mabuwayi ne, wato Hafsa Jinin Surbajo ce sannan kuma jinin Hammood ce! Bahar ta ce,

"Surbajo Mahaifiyar Hammood ƴar sarkin Fulanin wuro ce wato Marigayi Modibbo Djore, nice naje har garin a wancen lokacin na auro wa Tahir ita sabida Jarabar Maryama, sannan kuma dalilin auro masa sedan danganta kar dake tsakanin mahaifiya ta dasu, danni kakar data haifi uwata 'Yace awurin Sarkin Fulanin wuro tun suna ruga, mahaifiya ta ta rasu dan haka na haɗa su aure sabida ƙarfafa zumunci, ni Surbajo ƴar uwatace ta jini, dan kuwa da kakar datafi haifi uwata da kakar datafi kakarta ƴan wa da ƙani ne, wannan shi ake kira TSINTAR AYA, Ayau tas na gama regaye aya ta na tattare tsakuwar na watsar ys tsbbata zuri'ata ta dawo wuri ɗaya, domin bayani a taƙai ce shine ita Hafsa 'ya ce awurin yayan Surbajo babba, kunga taubasan taka ta jini a tsakanin su. Zan iya fassara dalilin neman ran Hafsa, don kuwa ko durbajo anso a kasheta. A ƙabiƙar fulanin wuro akwai al'ada dake ɗaga darajar mace sabida ita bats mulki, sukan baiwa ƴar sarki mace damar yin mulki kafin taje gidan aure, se abinda ta faɗa akeyi idan ko bata auru ba haka zata ringa juya kowa har sanda tayi, wata al'ada ma idan sarki bashida mace to saukeshi ake, a cewar su zeyi baƙin mulki, ita Fulanin a sanina yaranta duka maza ne, na jima sosai banda labarin su basa zuwar mun bana je musu inaga hakan yanada alaƙa da asiri gaskiya danko Surbajo bata maganar su" Shiru kowa yana saƙe saƙen sa har sukaji sallama, me gadi ne ƴace anyi baƙi! Atake aka tarbesu nan aka zauna shaida juna inda Yayan surbajo yaji labarin ta suka rankaya zuwa Fada. Duk wannan budirin Hafsa bata san anayi ba, tanacen tana mita akan shegen yawon Hammood yasan mutane na farautar ransa!

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA* FREE BOOƘ

*BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ARBA'IN*

Gaba ɗaya a fadar Mai Martaba Sarki Tahir suka sauka inda ɗaukacin mutanen fadar suke. Aka kira Hafsa hsr khairiyya ma, Tiryan Tiryan Momy tayi bayani inda Sarkin Fulani ma yayi nashi jawabin,

"Sanda Tafiya aikin hajji ya kamani nabar Fulani ƙarama da juna biyu tsoho ma, amma ashe kuskuren lissafi muka samu, seya zamana tafiƴa ta da sati biyu ta haihu, koda na dawo anata farautar rayuwar ƴar, daga ƙarshe kuma se labarin ɓatar ƴar na samu ita kuma uwar tunda akaga gawar kuyangar ta seta shiga ruɗu, babu inda bamu shiga neman yarinyar ba amma bamu ssme ta, se muka ɗauka sun kashe ƴar dan haka muka haƙura" Kowa se jaddada godiya yake awurin Allah mabuwa yi. Hafsa kuwa kuka tiryan tiryan itada Baba Surbajo, nan Baba surbajo taga yayan ta Arzika aka shiga hirar yaushe gamo sun yada ta, anan takejin sabom labari wai sarki Tahir ya aika takarda me hatimin sa akai cewar Surbajo an kama ta da wani bawan sarki suna zina an kuma kashe ta itada bawan da yaran dats haifa dan haka karma masarautar ta ta kuskura ta ziyarce sa sun bashi mugun iri, wannan ne babban dalilin daya hanawa zuri'ar ta neman ta duk tsawon wannan lokacin akan tayi abun kunya ta mutu a banza, kuma sun aiko takardar ban haƙuri aka mayar musu akan an raba jiha! Baba Surbajo tayi kuka iya kuka da kyar aka rarrashi juna.

*Bayan wata ɗaya*

Hafsa taje garin su tayi kwana 13 yau ta dawo, taga gata sosai kuma taje hsr wurin su Baba jere da ƙauƴen su budurwar kabeer inda acen sukaji labarin mutuwar ta bayan ta samu labarin mutuwar kabeer. Baba Suwai tasha kyaututtuka 'ƴar Shara ta zama sarauniya.

Sati biyu bayan dawowar ta dannan Mood ya dawo daga tafiyar aiki ta emergency daya je UK gaba ɗaya Hafsa tayi kewar sa, wata iriyar tsananin sha'awa ke damun ta tun bayan satin farko da saduwar su ta biyu. Tana part ɗin bahar tana fama dacin ƙwallon dabino ya shigo, sam bata zata cewar yau ze dawo ba kuma jiya da dare ma sunyi waya yau ne kaɗai bata samu wayar saba data kira. Da dauri ta miƙe ta falla aguje se cikin ƙirjin sa "Ga yaa Mood ga yaa Mood, yaa mood oyoyo" Ta ɗage ƙafafuwanta sama ta ƙanƙameshi. Kunkurunta ya riƙe ya soma juyi da ita yana zaga palon tana dariya, Bahar se murmushi take tana kallon su har ya dire ta, sumbatar ta yayi a goshi sannan yace

"Yar Fara kyakyawa Hafsa, kinyi babban suna Hafsa...." Dariya ita da Bahar sukayi sannan Bahar tace "Wayaga kurma anyi baki har waƙa kake?" Yana dariya ya zauna kusa da ita

"Bahar nayi kewar ki, yaushe wannan ta zo nan" Dariya tayi tace "Tunda safe fa, ka ganta nan muna faɗa da ita, bataci bata sha ƙwallon dabino dakake gani shine abincin ta" Kallon Bahar yayi da mamaki "ƙwallan dabino kuma? Wannan ai bazema ciwu ba ko?" karɓe zancen tayi

"ze ciwu mana, bakaga daɗin dayake mun ba wlh, idan ban shi nake ciba wani tashin zuciya nake, wani bin ma ko ƙamshin abinci banaso amma nikanci tuwon dawa miyar kuɓewa me man shanu da nonon shanu, yanzu ma shi nake jira a gamamun in tafi dashi cen" Da mamaki ya kums mayar da dubansa zuwa gs Bahar "Dawa kuma? Ya furta cikin mamaki da alamar Tambaya Bahar tace "Wannan da kake gani dawowar ta da sati biyu rak yanzu amma naci bone a hannun ta, yau wannan gobe wancen" Murmushi kawai yayi "To Allah ya kyauta" Shiru falon yayi ya ƙureta yanda take gwagwiyar ƙallon dabino harna wani lokaci sannan yace

"Ashe kuma Momy da Abbin Muhseen aure ya ɗauru? Yanxu nakeji shi kuma Bilal Ɓarayi sun shiga gidan sa sun kasheshi" Kallon sa tayi "Ea wlh, Allah gafarta masa, momy anje honey moon" Adaidai lokacin kuna Amina ta shigo falon, zama tayi ta gayar Mood yana fara'a ya amsa sannan yace

"Zanyi tafiya kuma na bada saƙo a baki kin karɓa? Sunne kai tayi a ƙasa "Ea na karɓa Allah ya ƙara ya girma" Gemun sa yaɗan ja "To kuma ina alƙawarin mu?" Rausayar da kanta tayi cike da kunya "Yana nan yariman yarimomi" Hafsa mugun haɗe rai tayi

"ke tashI Bar nan wajen" kallon mamaki Amina tayi mata "Zaki tashi ko dai na kakkarya ki" Sumsum ta miƙe, itama kuma Hafsa ta miƙe zatabar wurin! Fuuu, bayanta ysbi yanata kira bata saurare shiba har suka isa cikin gidan su. Kai tsaye ɗakinta ta wuce yabi ta hsr ciki zata shiga toilet ya riƙo hannun ta, juyo da ita yayi ta fuskance sa yace yana kallon ta "Damsel dirowa na ina zanzari zan ganki seki fara halinki? Hawaye ne shaa a idanta "Kaine kake cewa zaka suri Amina, kanata mata murmushin soyayya agaba na, imma soyayya zakuyi ku bari kuyi auren tukunna"Murmushi yayi "Blood kinfi ƙarfin amiki kishiya da baiwa, Muhseen zata aura dashi na haɗasu shine saƙon danake cewa ta karɓa, kuma tamun alƙawarin ta amince shine alƙawarin danake magana akai" Bayan hannu ta saka ta share hawayen ta sekuma ta rungume shi

"Dama jiya a waya baka saurare ni ba kace zakayi bacci abu nakeso in gaya maka" kallon ta ya ɗago yayi

"Menene kikeso ki gayamun" Shagwaɓe fuska tayi "Dabinon Uk nakeso ka saya mun inji ya ɗanɗanon ƙwallan sa yake" Wara idanshi yaƴi aƙamar mamaki "Damsel wai yaushe zaki girma ne? Kefa sarauni ya ce ta masarautu guda biyu, wowta kika mayar sutura" Turo baki tayi "Nadai gano kai kaɗai ne baka yaba mun, komai nayi s gunka wowta ne" Murmushi yayi

"To na dena yi haƙuri, inna koma zan saya miki" Bata yi magana ba se cura kanta a ƙirjin sa da tayi tana lumshe ido, da mamaki ya tsaya yana kallon ta sunkai 2 minute a haka kafin ta ɗago kanta taja numfashi me tsayi "Naƴi kewar ƙamshin jikin ka, wata ɗaya fa ban ganka ba kai bammaga alamar ka damu dani ba" Murmushi yayi "Damsel wlh nayi kewar ki, Allah ranar dana tunaki kawai kuka na saka, gaba ɗaya yanzu idan bama tare hsr wani zazzafan zazzaɓi nakeji" kallon ƙuri taƴi masa sannan ta juya masa baya

"Dazaka tafi ai Anty Khairiyya ka ɗauka kuka barni nini kaɗai, kunacen kunacin soyayyar k.. Dakatawa tayi ta kalle sa "Yaa mood mema kuke tayi wai duk tsawon sati biyu a Uk? Kafin yayi magana wayar sa tayi ringing da sauri ya zaro ta, sega hoton sa da khairiyya yana yawo an rubuta wa sunan ta My Princess tana zaune akan cinyar sa sun haɗa kai, wani wahalallen yawu ta haɗiya data rasa na meye sannan ta dube sa ya zare jikin sa daga nata juya sannan ya ɗauki kiran

"Riyyah dear how far? Ya furta yana ɗaga kiran daga ɓangaren ta tace "Abinci nake jira kazo muci kace zakaje ka dawo am really hungry" Ɗan waigawa yayi ya kalli Hafsa ds wutdiyar idon sa sannan yace,
"On my way, yanzu zan zo" Batace komai ba ta ajiye kiran ya waigo gaba ɗaya ya kalli Hafsa

"Am mun dawo a gajiye sosai, nazo kawai danna ganki bara naje naci abinci na kwanta na huta sena dawo anjima" Kawai se taji ba daɗi a ɗage tace,

"Allah ys huta gajiya" Ya juya shima yana tunanin anya hakan daidai ne kuwa? Wayar ta ta ɗakko ta kira Barratu tana ɗagawa suka gaisa tace

"Anty Barra dama tambayarki zanyi, nace da aka ɗaura aurenku da Yaa Sufyan satin dakukayi tafiya a tare kuna dawowa shekaranjiya a ina ya sauka? Murmushi Barra tayi "Kin dena fushin dani kenan, na aure mijin ƙawar ki? Ɗan Murmushi tayi "Anty ba fushi bane ba, kunyar Laurah nske wlh matuƙa" Tana murmushi tace

"Itama ta fahimci ƙaɗɗara ne, ba yanda zamuyi ne Hafsa, babu wanka a tsakanina da Jay ya sskeni kafin mutuwar sa na kammala idda ta da wuri kinsan yanda nake al'adata yace ze surenk danna rage damuwa ya zanyi Hafsa? Tana murnushin yaƙe tace "Haka Allah yaso ya tsara ba damuwa" Nisawa Barratu tayi

"Ya tsara mana kwana bibbiyu, to muna dirowa a gidan ta muka sauka mukaci abinci dake tasan zamu dawo, daga nan semuka rabu, zeyi mata kwanakin ta biyu yau ze dawomun" Jinjina kai Hafsa tayi "Haka ya tsara ko haka musulunci ys tsara? Barra ta gano akwai matsala tanada labarin dawowar Mood cikin damuwa tace "Hafsa wani abinne? Haka tsarin yake a musulun ce" Wani gauron Numfashi Hafsa taje "Dama shine kawai zan tambaya, ba wata damuwa na tambaya ne kawai" Haka sukaƴi sallama Hafsa ta kwanta kanta asama tana tunanin irin son datasan Mood yana yiwa Khsiriyya tun farkon ganin sa da ita, dama tasan bazatayi fada ba, amma ba komai bazata tilasta masa komai ba. Haka gaba ɗaya ranar ta wuni baci ba sha, ko ƙwallayen dabinon tarasa dalili ɗaci suke mata, shi kuwa gaba ɗaya be kuma waiwayar ta ba.

Mom Nu'aiym.


*TSINTAR AYA*  FREE BOOƘ

    *BILLY GALADANCHI*

        41.

Gaba ɗaya a wannan daren Hafsa kasa bacci ta yi, haka nan ko madarar  shanun dake bata kuzari bata nema ba, tuwon Dawar ma batako bi ta kansa ba, daga ɓangaren Bahar aka kawo mata kuwa. Wayewar gari seta tashi da azababben ciwon kai, da ƙyar ta yi sallan asubahi anan ta kwanta wani nannauyan bacci ya kwashe ta.

   Gaba ɗaya daga kammala cin abinsa baƙi yaƴi a part ɗinsa, bashi ya samu zama ba se bayan isha, ya gincira a saman sopa ɗinsa take agun bacci me nauyi yayi awon gaba dashi, bashi ya farka ba se 7 na ssfe, a gaggauce yayi sallah sannan yayi wanka da jallabiya ya buɗa a guje dama gudu ba wani wahala yake masa ba, kai tsaye part ɗin Hafsa ya nufa. Zazzafan kishi dabatama san tana dashi ba ya haddasa mata zazzafan zazzaɓi, shigar sa ɗakin da sallamar sa be tsaya komai ba inda take kwance akan carpet ya nufs ya ɗago kafaɗun ta sabida tun daga ƙofa kana jiyo sautin numfashin ta sannan se rawar ɗari takeyi, jin jikinta da zafi sosai ya sanya da hanzari ya rabata da hijab ya shiga jere mata sannu, amma se baccin wahala take da yunwar masifa data addabe ta, kan gado ya kaita sannan da sauri ya fita wurin hadiman ɓan gare, kitchen ya nufa dan acen yake tsammaninn ganin su. Yana isa suka zube suna kwasar gaisuwa, be amsa su ba yace,

"Tun Yaushe ne Hafsa batada lafiya kuma me tace yana damun ta? Kallon juna sukayi sannan da ƙyar ɗayar tace, "Sanda kuka shigo a tare jiya shine ƙarshen ganinmu da ita, tuwon ma da aka saka mata bata fito taci bs har yau, dabinon ma mun ɓare ƙwallayen amma bats fito ba" Cakuɗa fuskar sa yayi tamau cikin masifa yace

"Ita Sarauniya Hafsa, itace kuke jiran ta setazo tace ga abinda takeso? Rabon daku ganta tun jiya wuraren la'asar and baku neme ta ba, gayamun ma kuke cewar bats nemi tuwo ba kuma ku kun kammala amma baku kai mata ba. Yaushe gidan sarauta ya zama haka? Hafsa saraki ce fa! Jikinsu ne ya ɗauki rawa yayinda shi gaba jikinsa yafi nasu rawa tsabar ɓacin rai "ku fita daga part ɗin nan kuje waje ku jirani, badai da yunwa kuka barmun itaba ba wata kulawa,

Please Login or Register in order to submit comment