Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hau titi sosai yanda tunda ya gayar da ita yakeshan mur tace

"Son meye haka? Momynka kake wahalar wa haka, ka bani wahala sosai kwana biyun nan, ina matuk'ar kewarka wlh" bece mata komai ba ta d'auki hanyar kasuwa siyayyar kayan abinci sosai tayi sannan suka shirya juyawa gida, amma amaimakon suje gida seta d'auki hanyar Ni'ima hotel, shidai Bilal besan amfanin zuwan su hotel ba, kuma be kawo komai a ransa ba, ta saya musu lemo ta bashi kuma yasha sabida k'ishiruwar data addabesa

"kazo muje ciki, akwai sak'on dazan karb'a sannan kuma akwai kayan dazaka tayani dubawa" Ba musu suka shiga ciki, har d'akin suka shiga inda yaketa kallonta yana mamakin me suke a d'akin to, waye ze bata sak'on datazo karb'a anan d'in to? zama tayi kusa dashi tana murmushi sannan tace

"Bilal inson yanda kake kulada tsaftarka, shisa ma na saya maka turaruka ka gansu na manyan yara, na saya maka singlet da boxer's d'an mommy" Ta k'arashe maganar hannunta asaman kafad'ar sa" Idansa a lokacin harsun fara sauya launi zuwa ja, jijiyoyin jikinsa sun mik'e asalin tashin balagar dayake ciki se tasawa take, duk wannan abun sakamakon desire tablet data saka masa ne a lemo! bece mata komai ba se lumshe idansa dayake yana zube su akanta, hannunta takai akan wuyan sa ya kama ya rik'e hannun

"Bilal bakada lafiya ne tashi muje gida" Ta mik'e ya rik'e hannun ta, cikin kirsa tace "Muje gida mana, ai ba laifi mun dade" Tsatsareta yayi da ido kafin yace batare daya shirya ba

"Momy bashin kifa saura takwas fa" Girgiza kanta tayi

"Haba Bilal ka manta wa'azin malamin kune, gwanda karka fara wannan abin, aimun tuba ko" Jikinsa yana rawa yace

"Momy idan mukayi d'aya semu tuba" Dawowa tayi ta zauna

"Amma Bilal yanzu kaga kaine kaja abun nan karkazo daga baya kace nice" Allah sarki yaro yana ta kamo tsohuwar mace yace

"Momy so d'ayan nan fa" Haka ta biye masa taketa koyar dashi abubuwa fiye da tunanin me  tunani.

   Mahaifin Bilal bawai zargin yake momy tana zina da d'ansa ba, A'a yana zargin tana shirin b'ata masa yaronsa da kud'i,wanda yasan bame d'orewa bane ba,kar yaron ya lalace masa anan gaba, amma duk sanda yakeso ya nsanta alak'ar momy da Bilal se Baba lami tace shid'in d'an bak'in cikine dan kawai yaga yaranta ze samu alkhairi inba haka ba yanda Hajiya ta d'aukesu ai yafi k'arfin wulak'anci dan dole yake hak'ura dan haka yaso yakai yaran boading school amma k'ememe Baba lami ta hana wannan zancen tafiya boading!!!!

*************
   *Bayan shekaru biyu*

lokacin da Bilal ya zana jarabawar waec ya gama tanturancewa wurin biyewa hajiya, har wani girma ya taso masa jikinsa ya k'ara zama na isashen namiji alokacin yake 19yrs, be samu admn ba dan haka haryayi shekaru 21 yana nan Hajiya tana yawon hotels dashi, farinsa ya samu hutu yayi luwai,  fatar nan se shek'i take ya tara suma irin buzu bak'u wuluk se gyarata ake da mayuka, hajiya dashi da iyayensa ta mayar dasu 'yan uwanta, ga motar hawa ga kudad'e a acc, a haka ya samu admtn awani garin daban wanda ya tilastawa Bilal barin momyn sa kamar yanda yake kiranta ita kuwa take ce dashi son.

    Zuwa wannan lokacin Baba Lami tasoma fahimtar cewar tabbas akwai wani mara kyau dake shiga tsakanin uwar gijiyarsu da d'ansu amma son abun duniya ya rufe mata ido harta kasa yim magana, kafin zuwa 'yar shara rayuwar su kuwa masu aiki an kori sunkai goma, dan duk suka gani sesun tsegun tawa uwar Bilal amma seta had'asu da hajiyar sabida son duniya, acikin wanda aka kora d'in akwai biyu da Bilal yayiwa ciki, idan hajiya batanan anan yake holewa abunsa dasu sabida ta sabar masa da kanta, ta gama lalata masa rayuwa gaba d'aya hankalin Bilal inba mata ya gani ba baya kwanciya. Ga kud'i da ake zuzuta Bilal dasu har kawo wannan gangarar kuma suna aikata masha'ar su" Cikin tashin hankali Dr. Sunita ta zare glashin idanta, a hautsine take kallon Bintu kafin tace

"Bintu!! Wannan wane irin rashin imani ne, 17yrs fa kikace, yaro yana 25yrs yanzu good 8yrs kina tatse masa ruwan jikinsa, zina kika koyar dashi, harkinsan yanawa 'yan aiki ciki amma seki koresu akan laifin nasune yaya kike tsammanin iyayen su zasuji, Gaskia Bintu am sorry to say bakida hali me kyau, i cant even imagine irin wannan rayuwar akaina, kai not even in my bad dreams, Allah ya kiyaye mana imaninmu amma wlh tallahi its not too late to repent, kiyi maza kiyi taubatun nasuha!!!!!! Nisawa Bintu tayi kafin tace

"Friend say what ever u want to say, call me with any bad name, yea i deserve it i'm a monster, i'm a bad which a big devil friend!!! Sunita cikin jin zafi tace

"What do you really plan with your life now? Tana sosa kunne tace

"I dunno really, but deep down i know i love Bilal, kuma inaso ne ya aureni, abubuwa sunmun yawa Sunita, inajin tsoron rabuwa da Bilal, inajin tsoron in furta masa kalmar aure ya gujeni, Sunita ina sane da cewar Bilal ya samu duniya ta hannu na yanzu, ya gina katafaren gida, yanada shaguna sunkai bakwai a kasuwa, yana shigo da kayan gini na zamani daga waje Bilal duk wannan abubuwan b'oyemun yake, na tabbatar chance kawai yake nema, wasu lokutan ina kallon k'wayar idansa tsanata sosai nake gani manne a idansa, tabbas Bilal yayi wuya ya isa yanke, banida tabbacin ze yarda ya aureni, sunita inaso na tuba, wlh summa tallahi ina nadamar rayuwa ta, nayi danasanin abubuwa da yawa, kinga ada ban gane yarana ana hanasu zuwa guna ba sabida halin danake ciki da Bilal ashe kowa ya sani ni ina kallon na b'oye, shekaruna biyu ban sanya yaran nan a idoba, hawan jinina befi akan Message da Yarona Bilal yamun ba, yace in dena kiransa dan baze tab'a d'aukar wayana ba, yakuma ce dani ai yaga na samu sabon yaro Bilal muna shek'e ayarmu toya bar masa, bayako nigeria fa, ya akayi ya sani" Shiru sukayi na wuccin gadi dukkansu kafin Sunita tace

"Amma kinsan da wahala yaran nan ya aureki ko? shekarunki kusan 50 fa komafi, shi yana tak'ama da kud'i yanzu mezaiyi dake, bayan ma dayake da kwad'ayi da wanine aida tuni yayi ta kansa ya kwahse iyayensa, kuma bari kiji wlh koki yadda ko kada ki yadda bilal yanada target mummuna akanki, koda bansan ko meyeba amma ki shirya wannan" K'wallan idanta ta share

"Dr. Sunita tunda nake kece mutum ta farko dana fayyacewa cikina, sabida kece hankalina ya kwanta dake akan tabbacin zaki d'aurani a madaidaiciyar hanya, dan Allah ki ceceni, banida nutsuwar zuciya koda bazan samu Bilal ba Allah nakeso ya yafemun" Nisawa Sunita tayi, tasan wannan itace mummunar k'addarar da ake cewa mu nemi Allah tsari da ita ta tsakiyar rayuwa shisa taketa bata tausayi

"Ki fara neman yafiyar Allah, ki nemi Bilal shima ki nusar dashi ku tuba, kada kuma kiyi k'asa a gwiwa wurin sanar dashi k'udirinki" Sauke ajiyar zuciya itama tayi

"Zan gwada yin hakan Dr. nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" Harta mik'e takai k'ofa sunita tace

"Fatima" waigowa tayi amma bata amsa taba tace

"When ever u need a shoulder to cry on, just give me a call, lastly ki aikamun number Bilal na wurinki ba wannan farkan naki ba" Murmushin yak'e tayi dukda kalmar farkan ya daketa sannan ta gyad'a mata kai bata iyayin magana ba tafita tabar office d'in!!!

*****************
Jay abubuwa sun masa yawa akan Mood, bayaso yaron ya koma U.S, kuma yace acen zeje ba UK ba, gabaki d'aya shi bayaso ya masa nisa shishi kad'ai, bakuma yason ya auri macen dabayaso, dazebi shawarar sa daya tsaya sun fahimci juna da yaran, amma wannan tsarine mara kyau ya d'auka, inama ace yanzu haka yana tare da Barra, daya d'ebe takaicin abubuwa da yawa, yana cikin wannan tunani Zulaiha ta shigo d'akin tana wak'a, tasha k'aramin mini skirt da riga iya cibiyarta, kannan cike da attachment tasha makeup tamkar wacce zataje partyn dare, zama tayi kusa dashi tace tana kallon sa

"Jay abincinka yana dining yana jiranka"kallonta yayi yana murmushi yace

"To muje mana" Tab'e baki tayi

"Naci nawa kaje kaci naka kawai" Ba musu ya mik'e yaje yayi serving kanshi ya zauna yanacin abincin, ba laifin tuwon garine da miyar egusi yau ansamu kanta, seda ya k'oshi sosai sannan ya mik'e yaje ya wanko bakinsa yayi wanka sannan yayi shirin kwanciya, Zulaiha se rawar kai akeyi ansha kayan mata fin na dubu hamsin, ansha tsumi, ansha tabaje, ansha gumbar sosa gaye, ansha gumbar ungo kama, ansha ruwan wanke ango ba uban tsiyar da ba'a shaba. Lokacin da Jay ya kula matarsa tana buk'atar sa itama seya kalleta yana murmushi yace

"Zulaiha kinsha kyau, matso maza in baki tukwicin wannan wankan" Kamar an jeho sandar sunuka haka ta tashi ta matso bawani kwarkwasa kamar an ajiye masa icce" Kallonta yayi ya hasaso yanda Barra take masa karairaya ji wannan to meye haka? had'iyar yawu yayi sabida yanason matarsa, shine da kansa ya zab'o abarsa ya auro bayan Barra, fuskarta ya kamo ya manna mata kiss a lips nata sannan yace

"Yau wace tsarabar zan samu ne ehn my baby" Murmushi tayi aladole ita me kyau da diri

"Me kakeso" Ta fad'a a tsatsaye, yana shinshinar jikinta yace

"Haba mana baby, kina magana cen bazaki matso kusa dani ba ehn" Wani juyar dakai tayi gefe batace komai ba, duk yanda yake tab'a jikinta tana nan tak'i tayashi se basarwa take gani take tamkar jay baze rayu ba idan babu ita sabida yanda yake nunar mata so da k'auna, haka Jay ya k'araci kid'ansa da rawarsa amma sam kwata kwata bata tayashi komai ba dan haka babu wata cikakkiyar gamsuwa sabida yanayin ta, duk yanda yaso ya nuna jin dad'in sa haka ya kasa sukayi shiru bayan komai ya lafa"

*Note:*
*Wasu acikin mu zasuyita cewa basason hiran gidan Jay, waye waye, to haka zakubi labarin haka yake akwai alk'awarin wayar wa mata da kai akan matsalolin dasuke fuskanta na aure, nan gaba kad'an zaku fahimci dalili yawan sako maganar Jay da ahalinsa acikin labarin nan, inshaa Allahu duk zamu amfana, dukda yake na sanar daku zamuyita cin karo da maganganu masu nauyi a tafiyar nagode*


*******************
Haka aka shirya Hafsat aka kaita fadar sarauni wurin bahar, inda aka shaida mata acen zata zauna, lafiya lau ta kwana d'aya washe gari tunda asuba Bahar ta tasheta tayi sallan asuba, seta sanya bayi suka wadata gaban yarin yar da abun kari iri iri. Anan tashiga ciki domin shiryawa Kamar an juyar dakan ta sekuma ta soma wasa da abincin irin yanda yara sukeyi, atake ta b'ata wurin ta masa kaca kaca, sagaga Bahar ta sake baki sanda tafito kafin ta kama salati

"Na shiga uku ni Salamatu, yanzu yarinyar nan dan la'ancewa akanki ta fara zaki zauna ki b'atamun wuri haka da girmanki da komai, iskancin da ke nan wannan ai, aikuwa wlh sekin gyara, ba hadimar dazata gyara wurin nan dan babu tambad'adden daze d'auki wannan sakarcin tundasu ba la'anannu bane ba" Kallonta Hafsat tayi yanda taga tanata fad'a seta tsorata irin na yara nan danan seta soma kuka kamar wacce aka daka, cikin mamaki Bahar tace

"Yau naga la'ananniyar yarinyar, ni zaki nunawa tambad'ewa, sangarta, sangarta ya'i, Allah ni zaneki zanyi" Mik'ewa Hafsat tayi ta soma bubbuga k'afa daga baya kawai seta shige cikin jikin Bahar tana kuka" Zareta takeyi ita kuwa se manne mata takeyi, ajiki suka soma zagaye a haka

"Yau nashiga uku ankawomun mayya, ke da hankalinki kuwa, kajimun la'ananniyar yarinya, b'alla ni zakiyi" Cikin wannan halin Mood ya shigo, tsayawa yayi yana kallonsu, gaba d'aya ya shagala da yanayin yarinyar, ita kuwa idanta yana sauka akanshi tace dawa Allah ya had'ata bada shiba, nan take ta rugo ta k'ank'ameshi tace

"Yauwa kaga kaka tanamun fad'a ko, ban mata komai ba" zareta yake k'ok'arin yi ajikinsa amma k'ememe tak'i ta sakeshi, nan Bahar tahau salallami

"Hammude agidan ubanwa ka nemo wannan gayyar mayun, anya ba 'yar iska bace ba kuwa ? ke balagai balagai dake kike wannan sakalcin" sakeshi tayi tasoma bubbuga k'afanta a k'asa se kukan gaske kuma, nan ta zauna tayita yi, Bahar se banbami take, kawai jiri hafsat ta soma gani, da sauri ta dafe kanta daga tsayen datake, cikin seconds kad'an segata ta sulale a sume da sauri ya tareta ta fad'o jikinsa, an sanar dashi matsalarta, ba'aso tana yawan kuka, idan akaga tana abun rarrashi takeso ba fad' ba, zatayita samun suma ne har abinda ake gudu ya faru, kwantar da ita yayi agefe ya kalli bahar, da hannu ya mata nuni da ruwa ruwa, bata ko motsa ba se baiwace ta kawo ya yayyafa mata ta soma sauke gaurayen numfashi hular kanshi ta facecap ya cire yanata mata fita, bahar ta hard'e hannayenta tace

"Sabon salon la'anta, lallai ma kurma ka iya iskanci, rabu da wannan shashashar maza kazo abinda yasa nake nemanka daban" mik'ewa yayi ya soma janyo wayar sa, sak'o ya tura kamar haka

"Anty Barra, kizo fadar sarauni, that witch is sick again,suma ma tayi, kuma kuyiwa bahar bayanin yanayin ta, she's messing off here kuma sarai kinsan halin Bahar" yana aikawa ya kalli inda take kwance, har yanxu bata bud'e idanta ba, baze tafiba se Barra tazo dole, yana tunanin kiranta sega reply nata akan dama gidan zatazo.

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*


JOIN OUR TELEGRAME PAGE TROU THE LINK BELOW.
https://t.me/joinchat/WVNVv7LzJdo-DIjC


*ASSALAMU ALAIKUM, INASO NAYI AMFANI DA WANNAN DAMAR WURIN MEMAN YAFIYAR DUK WANDA WANI ABU YA TAB'A HAD'ANI DASHI A MEDIA, DA WANDA MUKA FADA, WANDA NA ZAGESU A BAYANSU, WANDA NAYI GULMANSU IDAN MA NAYI, WANDA AKACE NAYI GULMANSU KODA BANYIBA,WANDA KE GANIN NA HAD'ASHI FAD'A DA WANI, WANDA KE GANIN RASHIN ADALCHINA, KAI DAMA WANDA KODA SUNANSA NA AMBATA A BAYANSA,DAN ALLAH YA YAFEMUN, ANATA MUTUWA BANNASO IN MUTU DA HAKK'IN KOWA AKAINA, NIMA NA YAFEWA KOWA DA ABINDA KAMUN INA SANE DA WANDA BAN SANIBA DUK NA YAFE, ALLAH YA SANYAYA ZUCIYAR DUK WANDA NA ZALINTA YAJI YA YAFEMIN HAR ZUCIYAR SA AMEEN. SAK'O BILLY GALADANCHI.*

*SHAFI NA TARA*

Be gama zama a parlon ba ta Barra ta shigo, a hautsine kallon sa tayi

"Meya sameta? K'ureta yayi da ido amma bece mata komai ba, kallon mahaifiyarta tayi

"Ammu Bahar, meya sameta haka? Yatsine fuska tayi

"Daga sama aka jehoki ne? Cikin damuwa tace

"Ammu dan Allah meya faru, koda yamun sak'o ina kan hanyar zuwa nan d'in dama"

"Yarinya sekace mahaukaciya Barratu, iya hege kala kala, abinci anbata ta dagula wuri, se sakalci wai dan an mata fad'a taketa kuka daga k'arshe segata tana fad'awa ajikin Hammude nace wannan wai salon son a la'anceka ne kaga laifin mutane" Nisawa Barra tayi

"To Ammu seme kuma ya faru?" Tab'e baki tayi

"Suma tayi hakanan kawai, shine sarakan tausayi ya rud'e dukya fita hayyacinsa, amma na kula tana numfashu ta dawo hayyacinta kamar baccine ya kwashe ta" Jinjina kai tayi

"Abinda Jay yace nazo na miki bayani kenan akan yarinyar nan Ammu, batada lafiya akanta, anan aka rasa meya fad'ota daga bene ta buga kai, shine ta samu cutar irin ta tab'uwar wani b'ari acikin kanta da wasu lokutan kawai seta sauyin abubuwa irin na yara, amma zaki iya wuni da ita koma kwana biyu abun be tashi mata ba, sabida haka dan Allah Ammu kiyita hak'uri da 222,idan ana hantarar ta inji likita setayita samun attack irin na suman nan, kuma idan har yaci gaba wata rana idan ta suman bazata sake farfadowa ba se mutuwa" Wara ido Bahar tayi

"Yau naji labarin Assha, anan gidan haka ya faru? Nan dai barra ta kwashe komai ta gaya mata har rashin lafiyar Hammude da aketa b'oyeta, anan Bahar ta fahimci tabbas gadar zare ake shiryawa Hammuden ta, sedai ita sam bata zargin yarinyar, duk yanda akayi wasu ne suke bibiyar ta ya ceceta, tinda har aka ganta da wuta me alamar k'arfe da zane ajiki, wama ya sani ko 'yan yankan kaine sukaso su hallaka ta ? Cikin nutsuwa ta kalli Hammood tace

"Hammude nasan kana jina, dalilin dayasa nayi kiranka anan dama shine in gaya maka, tafiya dai dazakayi America k'afata k'afarka, kana cika son sanya damuwa aranka kuma ni dama nagaji da zaman fadar nan, kasan halina batun yauba tun zamanin da banason takurar da akewa matam sarki, inaso inje ind'an sha iska inke d'ebe maka kewa, to amma wannan maganar da Barratu tazomun da ita akan maganar baiwar Allah cen ta sanya na sake shawara, ni dakai dakuma yarinyar nan atare zamuje America, dole semun nema mata lafiya acen d'in, lakurarta a hannunmu ya sameta dan haka ka shirya tafi banda bayi harmu biyun, akwai wasu bayi guda biyu dasuke b'angaren ka mata ina yabawa da kokarin su Barira da Amina dasu za'aje, Hammude banasanjin kamun gaddama munsan halin juna ai" Jinjina kansa yayi sannan da hannu yayi mata alamar aiba matsala, yazone ya gaya mata zeje wurin waccen yarinyar daze aura me martaba yace yaje gobe, to yau zebar garin sabida nisa inyaso ya isa gidan nasu gobe" Rabin rayuwar Hammude yayita ne awurin Bahar, lokacin kawunsa Jay shima hannun Bahar yake duk yanda yake magana ta fi k'owa k'warewa a wannan fannin,batace komai ba se jinjina kanta yaci gaba

"Mezan je dashi? yayi alamar tambaya? Gyaran zaman ta tayi

"Ka tab'a zuwa ka duba wannan wama sunanta" Gyaran zama Barra tayi tace

"Tace dani sunanta Hafsat ana kiranta 'yar shara" Da mamaki Bahar tace

"Yar shara kuma wannan wane irin suna ne na wulakanci?

"Haka dai tace sunan da ake kiranta Bahar"

"Karnaji wannan sunan agidan nan, akirata da Hafsat d'in nan, inba tsinancewa da lalacewa ba meye kiran sunan mutum had'e da kalmar shara fisabilillah, kai ina jinka nace itafa ka kai mata kyauta kaje kun gaisa? K'urawa Bahar ido kurin yayi aranshi yace wannan bak'ar munafukar zewa wannan akan me? ganin yayi shiru yace tace masa

"Nice uwarta Hammude, idan ka dawo daga Masarautaul Baihatul Mulk wurin amaryarka Lallai a kawowa uwargida Gaisuwa ta musamman tare da kyautar ban girma, ka girmi millions ina sane da hakan, kanada kud'i sosai dan haka kyautar gaske zaka shiryawa kowaccen su daidai" Barra ce tace

"Amma waccen ai saraki ce Ammu, yaya xa'ayi mata kyauta daidai da wannan tsintsacciyar magen sabamuda tabbas akanta ma" Harara ta wurgawa Barra

"Nice uwarta kuma nice ubanta, itama saraki ce dan kuwa itama 'yace awurin uwar sarki, sarki yayanta ne kuma d'an sarki zata aura, ku bakuda tunani tayaya za'ayi su shirya masa gadar zare da yarinyar kuma har yabi layi har haka, Allah shine yasan dalilin had'asu da Hammude amma ni wannan yarinyar dakuke gani koda ku yarda ko kada ku yarda nasan batada laifi batada masaniya, in har zata dauki komai banda azabar wuta, shidai ya taka sawun b'arawo su kuma sunyi amfani da wannan damar sunso su murd'e abubuwan su saka har ita, likitan dasukace yace ammata fyad'e ma k'arya suke, duk shirine shi Yayanki Tahir mugun gab'o ne sarautar ma da mace nayi ke zan bawa, yana kallo da sanya hannunsa ake cutar da nasa sekace besan halin fada ba da masarauta" Mik'ewa Hammood yayi ze fita ta rik'o hannunsa

"Banda iya shege mun gama da kaine? gidan wa zakaje da sanaben tsiya" kallon mamaki ta wurga mata sannan da hannu yace

"Duk abinda kikeso bahar ba musu zan miki zanyishi, kawai banda zuwa zance wurin waccen mayyar" Harara ta wurga masa a karo na barkatai

"Iya shegen banza, kaji yaro da kafid'inin tsiya, ban haifi mayya ba, duk wanda yace da Hafsat Mayya tokuwa tabbas niya cewa, zuwa gaisuwa kuma sekaje uwar saraki ma bare sarakin aikin banza aikin wofi, duk abinda ze la'anceku shi kukeyi dan shashancin wofi" Nisawa yayi Barra ta masa alama da ido akan yace to ya kalli Bahar ya mata nuni da cewa tayi hak'uri zeyi. Anan tace

"Lau dadai inga karshen fi'ili, yarinyar nan ina kallonta naji ta kwantamun arai, dan haka dole kowa ya sota, zanje in gayawa me martaban dakuke tak'ama dashi lallai abata matsayin gimbiya, ya mayar da ita halastacciyar 'yarsa niko tazama jikata, Tazama 'yar Sarauniya Maryama inga k'arshen wulak'anta ta, yarinya ko lafiya batada na tabbatar labarin ta seyayi abun tausayi" Nisawa yayi danyasan duk abubuwan nan data fad'a tabbas zatayi su, yana murmushi yace

"Nizan tafi" da hannu yayi alamar tace tana d'auke kanta

"Yadai fi mutum ya tsaya nemawa kansa la'anta, kuma ka tsaya kuduba yarimyar nan idan bataji sauk'i ba asibiti zamuje" Beyi musu sukaje kanta anan aka tasheta daga baccin daya sureta, tana farkawa ta takure wuri d'aya da sauri ganin Hammood, gayar da su tayi duk suka amsa banda hammood tace da Barra

"Anty Barra yaushe kikazo? Murmushi ta sakar mata kafin tace

"Kinata aikin bacci yaushe zakisan nazo" Murmushi tayi sannan tace

"Anty Barra dan Allah kije da Ammu Bahar take barina ina aiki, Allah banajin dad'in komai amun, nasaba da aikatau sosai, jikina baya karb'ar zaman nan" Murmushi Barra tayi tace

"Kinsan lafiya be isheki ba, ban b'oye miki komai ba akan Lalaurarki Hafsat, idan kikazo kina yawan aiki se abubuwa su iya taso miki"

"Anty na fahimci idan nacika zama ni kad'ai kaina seyayita ciwo daganan se inta bacci, gwara ina aikin sena dena tunanin komai" Shiru ta d'anyi kafin tace

"Zan soma tambayar likitanki idan zaki iya ayyuka Hafsat idan har babu matsala, amma idanda matsala sedai ki hak'ura gaskia".

******************


Tunda wannan maganar ta shiga tsakanin khairiyya da Bilal seya zamana kullum kwannan duniya suna mak'ale a waya, harma yau yayi nasarar shawo kanta akan ze kawo mata ziyara palace, da wannan ta tanadi kayan ciye ciye iri iri a babban masaukin bak'i na wannan b'angarin domin sa kawai. Bilal yayi kyau sosai cikin shigar manyan kaya, dukda yake d'inkin big man ne daya kameshi a sama amma rigar iya cinya yadin kalan maroon color ba karamin karb'ar fatar bilal yayi ba, asaman kansa bak'ar hula ya saka, agogon sa bak'i tare da bak'ak'en takalmi, yasha turaruka duk a ciki black sudanese Oud me k'amshine yafi tashi, sumar kansa dayake tarawa tasha gyara matuk'a bayaga haka kuma gabaki d'aya gashin gaban girar sa ya had'e da wanda ya zago ta goshinsa, sajen fuskarsa ya zaga har zuwa gefen kunnensa ya had'e da gashin kansa, fari ne fat,me sirkin ja aciki, Leb'en bak'insa me duhu ne irinna jan buzu, hakance ta k'arawa asalin jar fatarsa yi masa kyau, Bilal irin mutanen nan ne da zakiga Allah ya haliccesu da kwallin su a ido, farin idan sa fari fat, bak'in idan nasa kuma tsakiya Ash ne zagaye da cikin bak'in shine bak'i, Eye lashe's d'insa zara zara, jikin sane kawai bana buzu ba, sabida yanada cikar haiba ba k'aramin jiki bane ba yanada murjewar sa damuke tsammani hutu ne ya haifar da ita, sabida yawan k'wallon da Bilal yakeyi da exercise ya tara 6 paks ga jikinsa yanata murd'ewa alamar yanaji da sabon jini ajiki....Seda Khairiyya ta gama k'are masa kallo sannan tayi murnushi ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa, dama k'waya biyu ne masu samfurin coffee chairs da table a tsakiya, Murmishin sa ya fad'ad'a kafin yace

"Lil sis wannan kallon fa? Murmushin ta ta fad'a kafin tace

"Yaa Bilal Allah kyau kamun kamar me, harna manta ina tsaye ina kallon kama" Murmushi yayi

"Shisa acikin k'awayenki zaki samomun kyakyawa iri na, dan bazan auri mummuna ba" Tab'e baki tayi tawani kallesa,sannan tace

"Wai nikam when did the table turn ne? daga friends zuwa brother and sister? Dariya siriri yayi

"Kinaso ne ake cewa ke k'anwar handsome Bilal d'in nan na enginearing kawai se kima manne mun, yana iya dole nabi da lil sis, koba komai kina kamada larabawa ur royan higghness" Dariya itama tayi sannan daga bisani ta langwab'e kai irin shagwab'abb'in yara

"Yaa Bilal alk'awarin mufa? murmushi yayi

"Kinaso kije kiga momy ko? da sauri ta gyad'a kai, yana murmushi yace

"Then u need kiss me first anan" ya fad'a yana nuna gefen kuncensa, Dariya tayi

"Dan wannan me sauk'i ma, haka Momyna kome zata maka setace seka mata kiss a kunci, haka yaa Bilal ma yanxu kaima haka kake ko? Dariya ya d'anyi tunawan dayayi awurin mahaifiyarta ya d'auki wannan d'abi'an sannan yace

"To when zaki dad'e a school ne zan kaiki har garin datake kuma zan dawo

Please Login or Register in order to submit comment