Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yace kika mutu ainima binki Xanyi
Taqara harararsa da cewa bawani nan
Kama huta. saikaci gaba daga inda ka tsaya
Yace Wlhi my Luv na rasaki binki xanyi ina miki wani so Wanda yafi qarfin akirashi da MASEEFAR SOO
Tace toh naji gayamin
Yace mefah
Tace gayamin 'yan matanka nawa kuma bayan ni wacece kakeji aranka
Qura mata ido yayi kafin yayi Murmushi dan ya hango kishin natane yau yatashi. Abin takaicin wai dan tagirmeshi shine take neman mishi wayo
Ya qarayin Murmushi aqaro nabiyu
Yace ni bani da 'yan mata yanxu dan tunda nasameki kika shafe Komai na jikin wata bana ganin kyansu sai naki bana jinsu sai jinki bana ganinsu sai ganinki
Tace hmmm toh ita wacce nagunku fah
Yace pls my Luv ki barni haka dan Allah mana
Tunda kika ganmu naji na tsaneta Sam. Kuma nagaya mata bani ba ita
Xatayi magana yayi saurin rufe bakinta da hannunshi Yace sanyi nakeji my Luv dama mun xama masoyan gaskiyan inji 'dumin ko nasamu nutsuwa. Yafa'da da janye hannunsa yana jifanta da wani irin kallo
Aiko nan take jikinta ya mutu dan kallan daya aika mata dashi
Tace hmmm
Yasan dama hmm 'din xatace dan haka ya tashi yana cewa yau kin hanani xuwa skull.
Tace ni.
Yace eh mana. Dan ko naje ba abinda xan 'dauka a kwakwal wata
Tayi Murmushi Tace gobe saimuje tare
Yace tarayo miki kenan
Tace eh
Yace hmm in xaki tsaya kiyi karatu kitsaya kiyi inba haka ba Wlhi na mallakeki ba qaramin mamaki xan baki ba
Tace ko
Yace Sa wasa kiganshi gabanki
Tace Allah ya kaimu lokacin Yace AmEEn my Luv

Ni xan tafi sai Allah ya kaimu anjima ko Auntyna
Tace hmm saura ka fara xuwa gunta......
Yayi Murmushi da ficcewa daga falan yana cewa nidai bance ba kuma ba ruwana.....

'Dankin RAMADAN ya koma
Yana shiga yaga RAMADAN junior da senior da FAWAS
Junior yana yana canjah Kaya dan har Dady ya shigomai da kayansa
Ganin yanda ya qame shi yasa RAMADAN senior ya dafa kafa'dar shi Yace 'dan Uwa nane mu 'yan biyu ne.
KHAMIS Yace bar fa'damin dan Allah
Tunanina nayi gamo ne😳
RAMADAN yayi dariya yana qara mishi haske akan lamarin
Nan hankalin KHAMIS ya kwanta yace Koda Naji. Nayi farin cikin kasan cewarshi garemu dafatan mun xama 'yan uwa
Junior yayi Murmushi Yace Sosai mah
Yace amma kamanninku yayi yawa. Bafah Wanda xai gareku
Junior qara kallansa yayi Yace xaku dinga ganemu mana.
FAWAS Yace ta ina Komai naku 'daya
Yaqara yin murmushi yayi Yace nan gaba ka'dan xakuce na gaya muku
KHAMIS Yace toh kai me sunanka
Yace RAMADAN.....
Suka kallesa dukkansu har senior...
FAWAS Yace RAMADAN kuma
Har sunan naku 'dayane
Yace eh kai
Sai dai shi Senior ne nikuma Junior
KHAMIS Yace Yauwa gwara daka babbance mana
FAWAS ya tashi yana fa'din bara inje office 'din Dady na dawo
KHAMIS Yace nima Momy ta ha'dani da wani aiki wai inje in gaida wata yarinyar qawarta Ameera batajin da'di an sallamora daga asibiti. koni ina ruwana dasai naje gaisheta oho
Senior yayi Murmushi Yace kaje dai kaga matar da sukesan baka
KHAMIS yawaro ido 😳 cikin tsoro Yace what
FAWAS ya shege da dariya Yace wai kai nan baka gane manufar xuwan naka ba.
Yace Wlhi ban gano ba😳
Junior yayi Murmushi Yace ya toh xakayi da Aunty XEE
Duk suka kalleshi atare sukace kasanta ne
Yace na santa mana sanadinku
Suka cika da mamaki dan basusan yasan rahotan kowa a cikinsu ba
KHAMIS Yace na rantse da Allah akarabani da Aunty XEE mutuwa Xanyi
Bansan yaushe Santa yayimin mugun kamu bah
Senior Yace kata addu'a ba abinda xai faru
FAWAS Yace hmm Allah yasa
KHAMIS Yace kai barama naje yanxu dan tabbatar da maganarku

Atare FAWAS da KHAMIS suka fitta

Senior RAMADAN ya xauna daf da 'dan uwan nasa Yace xanso kaban labarinka
Junior yayi Murmushi Yace ahannun Dady Jibiril nataso
Saidai duk Wasu abubuwana a waje nake yinsu
Senior Yace kana nufin Kaine 'dan uwan da momyna take gayamin yana wajan Dady Jibiril
Junior ya gya'da mishi kai
Yace watoh 'dan Uwa akwai cakwakiya acikin tarihin rayuwarsu
Xakaji Komai Amma lefin nan bara naci abinci muyi Sallah idan na hutta na baka labari ko da dare ne
Senior Yace Owkie



Suna xaune kan dining Suna cin abinci Amma banda Senior RAMADAN
Dan danne dannansa kawai yakeyi awaya
Junior ya kalli kwayar idan Dady Yace ba da'dewa Xanyi ba.
Kwata kwata sati uku ne ya ragemin in koma skull
Senior RAMADAN Yace nayi tunanin kadawo garenine gabaki 'daya
Yace eh haka ne
Dan nabar hannun Dady Jibiril kenan ko Baku
Dady ya ajiye cokalin hannunsa Yace da gaske kakeyi
Yace gaskiyar kenan dad
Tunda nagane akwai wani abu aqasa Wanda kuka da'de da 6oyewa shikenan fah naji banisan qara xama kusa dashi
Cikin sanyi Dady ya kalli Momy alamar ya shiga damuwa
Daidai nan 'din junior ya tashi yana yana goge baki da tishu ya ficce daga falan xuwa part 'din senior RAMADAN

Momy Tace akwai matsala
Dady Yace damuwata kaddai ya gano Komai
Senior RAMADAN Yace Dad kaban haske bai kamata ka6oyemin abubuwa haka ba
Ace inada 'dan Uwa Amma sai yanxu naganshi.
Me yake faruwa ne
Dady yajah numfashi Yace kayi hakuri my son banyi maka hakan daniya bah
Tashi RAMADAN yayi ya bar falan xuwa ga Qanin nasa
Shida da Momy suka bishi da kallo

Momy Tace lokaci yayi daxaku fayyace musu Komai dansu fuskanci rayuwa
Dady ya kalli Momy Yace Wlhi yanda nake san yarannan ko 'ya'yana bana jinsu kamarsu
Momy tayi Murmushi Sam mijin nata bai iya 6oye gaskiyarsa ba
Shiyasa take qara sanshi
Idan abu ya kasance gaskiyar shine baya damuwa da ranta ya sosu ko karya sosu fa'da mata kawai xaiyi
Tace nima ina matuqar sansu Allah ya dubesu ya rayasu
Yace AmEEn


Senior Yace pls 'dan uwana gaya min Komai
Junior ya tashi ya bashi diarys 'dinnan biyu Yace ka karanta nidai hutu nake nema brother
Da sauri senior ya kar6a yana cewa tnx.....




Sosai junior yake bacci hankali kwance yayinda senior yagama karance diarys 'din nan tsaf
Hawaye ne kawai yake sauka afuskarshi
Na Farko abinda ya sashi kuka na mutuwar iyayan nasu dan yasan da mahaifinsu yana nan dole ya bayyana garesu
Toh ya akayi ya mutu kasheshi akayi ko haka kawai ya mutu
Tabbas xaiso yaji wannan

Na biyu kuma yanda Dadyn shi Alhaji Naziru yanunamai qauna fiye da 'ya'yansa
Baya ha'da soyayyar da yake masa da kowa agidan
Tabbas yanuna mishi qauna ta qarshe
Yana nuna mishi SOYAYYAR DA BATA DA QARSHE 😀

Ya maida kallansa ga junior da yake baccinsa hankali kwance.
Sai yaji wata masifaffiyar qaunarsa takamashi
Nan yaci gaba da kukan nasa Sosai.

Awannan yanayin ne junior ya tashi ya gansa
Ya kalli agogo yaga kusan shidda da rabi Yace Ya Allah banyi sallar La'asar ba
Senior yaqi kulashi
Junior yayi Murmushi ya matso kusa dashi
Yace yane brother
Kuka haka
Kamar wanda xai rasa dukkanin farin cikinsa
Kar damu in haka ne kana dani
Ni kadai na isheka
Hmmm nasan xaka fini shiga Baqin ciki idan ka karanta
Soboda koda wasa Dady bai ta6a nuna maka cewa bashine ya haifeka ba.
Saidai nafika shiga baqin ciki ayanxu dan nagano na rayune ahannun Wanda ya kashemin mahaifina
Senior ya kallesa da sauri Yace katabbatar Dady Jibiril ne ya kashe mahaifinmu
Yace ko shakka babu dan bashi da imani
Na sanshi fiye da tunanin me tunani
Allah ya jarrabeshi da sona ne danya nuna mishi qarshansa
Karka damu brother xansan yanda xanyi dashi

Senior yayi saurin cewa aa banasan kayi yunqurin yin Komai idan na isa dakai

Junior yayi murmushi Yace duk abinda kasani Xanyi
haka dukkan abinda ka hanani xanqi yinshi
Yace Yauwa 'dan uwana naji da'din wannan furucin naka
Yace kai ka'dai nake dashi in banyima ladabi ba. baxan ta6a yafema kaina ba.
RAMADAN ya rungumeshi Yace kasoni pls inajin maseefar sanka araina
Junior yayi Murmushi hawaye yaxubo mishi Yace nasoka tun kan ka ganni.....

(Wato shidai "dan uwa da'dine dashi)
bayan sunsami nutsuwa
Toilet senior yashiga yana cewa ai nima banyi sallar ba. Dan haka saina rigaka Alwala
Junior yayi Murmushi Yace idan kada'de Saidai kasameni akan sallaya dan swn yanxu in rigaka......

Bai qarasa furucin nasa ba tashigo kamar an jefuta
SAILUBAH kenan

Junior yayi mata kallo 'daya xuciyarsa na bugawa fat fat fat
Ai bai ankareba yajita kusa dashi. Qamshinta ya bigeshi ya lumshe ido cikin basarwa
Tabishi da kallan shagwa6a ta kama hannunsa Tace Abban nan nawa kamar mai aljanu kaga yacanja tsarin nasa yanxu wai wata biyu yaban nafito da Wanda nake so. Tunda wancan bai 'doramin idda ba.
Nufinshi yajanye wata takwas 'din da Yace kenan
Wai inda nafitoh da Wanda nakeso hankalinshi xaifi kwanciya Koda baxa'ayi bikin nan kusa bah
Pls ka temaken Qanina ya xanyi.
Taqarashe kamar xatayi kuka

Yanda take mishi maganar ba qaramin hargitsa mai kwanya takeyi ba
Dan haka ya xare hannunshi daga nata ya tashi
Tace kaji dani mana
Cikin rashin kunya da raini ya watsa mata harara Yace Karki qara ta6amin hannu malama
Kantayi magana senior ya fitoh daga toilet.
Yace Auntyna😁
Tawaro ido 😳 Tace me nake gani
RAMADAN Yace 'dan uwana ne. Mu 'yan biyu ne. 'Daxu yaxo

Tace kut😳
Amma shine Komai naku 'daya
Xama yayi kusa da ita lokacin junior ya shige toilet

Yace kema kin tabbatar ba abinda ya rabamu ko.
Tace eh
Amma wannan bashi da kunya
Yace me yayi miki
Tace sanda nagama mai xuba yawani yimin rashin kunya
RAMADAN yayi Murmushi Yace toh kiyi hakuri
Tace kai dashi Waye Babba Yace nine
Tace toh kaja mishi kunne ni Auntynka CE
Yace toh my Aunty
Tace naga xakayi Sallah bara inje. In ka idar kanemeni ko awaya ne
Yace angama my Auty
Har xata tashi sai kuma taxauna Tace toh meyasa baka ta6a gayamin cewa Ku 'yan biyu bane
Yace kiyi hakuri dama inasan yimiki baxata ne
Kamar yau da kika gansa kika xata nine
Ta 6ata rai Tace karka sake
Yace shi ka'daine nawa kinga sakewa bada niba...

Tace Yauwa baka gayama momy tare muka dawo bane
Yace eh
Tace kamar nasani nafara xuwa gareta anan naga Dady mah
Ta kallan da mamaki da San jin ya taganni
Shine nake gaya mata Komai
Dady Yace aiya mantane bai gaya mata ba Amma sunyi xancan da Abbana da safe.
Yayi min Nasiha Sosai
RAMADAN Yayi Murmushi Cikin wani yanayi ya qare mata kallo Yace kinyi kyau Auntyna
Takalli kanta. Wata rigace dogowa tasa sai qaramin gyane data yane kanta
Tace banyi fah wankan yamma bafah.
Yace aiko bakiyi wanka ba kyau kike

Xatayi magana junior ya fitto bai kallesu ba ya shinfi'da sallaya zai hauyin Sallah senior Tace am 'dan uwa gafah Auntyna ta Kaina inaji da ita over kaso pls dan zanji da'din hakan....
Cikin maseefa SAILUBAH Tace karma yasoni mana

Junior ya kalleta araini Yace gaskiya brother na rainata. Ma'ana baxan sota ba
Dan banga abin San bah
Cikin sauri senior RAMADAN Yace bafah wancan san ba.
Junior yayi Murmushi Yace ai in wancanne tayimin yarinya
Ina nufin baxan sota bane kwata kwata dan bakai nabata kowane irin matsayi na so ba......
Ya qarashe da tada abbara cikin halin ko in kula.
Kut😳 SAILUBAH Tace ta kalli senior. Yayi saurin marairaice murya cikin kunya da nadamar gabatar da ita gareshi
Yace am sorry my Aunty karkiji Komai aranki dan furucinsa Wlhi qarya yakeyi ke abar San kowa ne
Tace Amma wannan akwai 'dan iska mara mutunci shege
Nixai kalla Yace baiga abin so ba
Ni sa'arsace
Shuru senior ya mata dan yasan ta shaqa kuma baisan me xai kuma CE mata bah
Itama shurun tayi tana jiran ya idar ta tsefeshi tamkar senior yasan me take saqawa saiya kama hannuta Yace kanya idar xo in nuna miki wani abu da Dady ya siyamin
Batayi musu ba tabishi har harabar gidan
Yace am sorry my aunty Ki yafe mishi banasan tashin hankalinki
Xan mishi magana Sosai akanki
Yasan girmanki daatsayinki
Tace dama wayo kamin dankar in tsefeshi
Yace aa ni na'isa in miki wayo. Fatana dai Kiyi hakuri dan Allah
Tace toh naji
Wlhi saina mishi rashin mutunci baxan hakura ba
Dafe kai RAMADAN yayi. Yayi shuru dan ya hango rashin hakurin nata axahiri

Ita ko ganin shurun da yayi yasata cemai
Meya samu idanka kamar kayi kuka. Tun 'daxo nakesan tambatarka.
Tafa'da dasan kawar da damuwar da tagani a fuskarsa
Yace kuka nayi Auntyna
Tace waya samin kai
Yace nayine dan ganin 'dan uwannan nawa
SAILUBAH tata6e baki da gallamai harara Tace hmm toh karka sake dan ba irinsu akeyima kuka ba......
Kai bakaga idanshi tsaf na marasa kunya bane da tarbi.......
Da sauri senior ya tufe mata baki Yace kibar shi haka mana Aunty baxai qara yimiki rashin kunya ba promise
Tace hmm imma xaiyi ina daidai dashi
Nan dai RAMADAN ya rakata gida yana lallashinta ya dawo


Sanda yayi Sallah ya fuskanci junior Yace 'dan Uwa ka....
Katseshi junior yayi Yace baxan qara yimata Komai ba...
Senior yayi Murmushi Yace Yauwa 'dan Uwa ka lura pls
Yace karka damu......

Wannan dare Sam RAMADAN bai bar qanin nasa ba yana tare dashi yana nuna mishi tsantsar qauna
FAWAS ko sha'awa suka dinga bashi


KHAMIS ko damuwa da tashin hankaline yayi mishi yawa dan ya tabbatar da xancan senior RAMADAN akan Ameeran da Momyn shi Tace yaje dubata
Shegiyar yarinya qiri qiri tafitoh tace tana sanshi

Yanxu haka bayan Isha'ine
xaune yake a 'dakinsa sai saqa yake yana kwancewa
Shidai Aunty XEE ce aransa ba wata mace Sam agabansa........
Momy da Dadyn shi suka shigo 'dakin
Aiko ya 'daure fuska
Dady Yace me yake damunka
Yace haba Dad meyasa mum xatayi min haka
Ni fah nayi qarami a Aure
Yace ko
Yace Wlhi
Yace toh saurareni dakyau kaji Wlhi Aure xan maka da ita Ameeran
Ko kana tunanin bansan me kakeyi bane na futan dare
Kuna yawan xuwa club Kullun dare
Me kukeyi acan iye
Hakanne yasa nagane Aure kakeso dan haka acikin satinnan xancan sadakinka gidansu Ameeran
Ko kanaso ko baka so mutumin banxa kawai.........


Wani ihu KHAMIS ya kwalla🙆🏼 ha'de da wani tsalle ya dire agaban Dadyn nashi Yace Dady kamin rai Wlhi bana santa.
Ina skull Dady pls karkamin haka
Dadyn yayi murmushi irin nasu na manya
Yace Wlhi baxaka jawomin abin kunya ba saina maka Aure tunda kanuna shi kakeso

Yace wayyo Dady ina da wacce nakeso Wlhi.
Momy Tace wacece ita
Da sauri Yace Aunty XEE
Momy da Dady suka waro ido😳 cikin mamaki har Suna ha'da baki wanjan cewa Zainab....
Dan sunsanta Sosai.
Ya 'daga musu kai cikin tsoro Yace Wlhi ita kawai nakeso kuka rabani da ita mutuwa Xanyi
Gauuuuu Momy ta falleshi da mari.....

Atarihin KHAMIS tunda yataso da wayansa bai ta6a ginin ranar da iyayan nasa suka dakesa ba
Amma yau sanadin masoyiyarsa yasha mari agun momynsa

Ya kalli Dadyn nashi cikin sanyin yanayi.
Dadyn ya 6alla mishi harara Yace kamin magana saina qara maka wani Marin
Shashashan yaro kawai
Ina xaka kaita yarinyar data girme maka da shekaru kusan biyar ko shidda
Toh kasani ko xaka mutu baxan Aura maka ita ba
Yana fa'din hakan ya ficce daga 'dakin cikin 6acin rai
Momy Tace Wlhi idan ina raye baxaka ta6a Auranta ba. Sakarai kawai
Ina xaka kaita yaxakayi da ita kana 'dan qaraminka....

Aikan tafuta KHAMIS yasa mata kuka fa'di yake mum ina Santa Wlhi kuka rabani da ita mutuwa Xanyi
Tace toh ka mutun mana....
Taficce
Kuka Sosai KHAMIS yasa
Toh yatake ne XEE
👯 matsala kenan👯




Haka yaci kukansa ya share hawayansa
Kuma kamar ance mai karya kira 'daya daga cikin munanan nasa
Sam bai kira kowa acikinsu bah



Toh ga FAWAS ma hakan take
Dan Ashe Dadyn KHAMIS ne yasami Dadyn FAWAS Dana RAMADAN suka tattauna akan matsalar yaran

Toh FAWAS bayan ya rabu da RAMADAN senior da junior gida ya nufu
A falo yaga iyayan nasa
Momyn shi Tace xonan FAWAS yaje cikin ladabi
Dady ya bashi wasu pix hotuna Yace kallesu dukka

Cikin sanyin yanayi FAWAS yafara duba hotunan
Kyawawan mata ne agani na fa'da Su goma cif
FAWAS Yace Dady nagama gani
Yace toh xa6i 'daya acikinsu
Da sauri FAWAS ya kalleshi dan ya gane abinda yake shirin San faruwa
Bakinsa na rawa Yace Dady ba wacce xan iya xa6a aciki
Momyn shi ta harareshi cikin 6acin rai tace kafita daga idona tunkan raina ya6aci dakai kaxa6i 'daya acikinsu
Yace toh momy miye ma'anar hakan
Dadyn nashi ya fusata cikin tsawa yace Aure xan maka tunda kaxama 'dan iska ashe kullun yawan xuwa club kukeyi
So kake kajawomin abin kunya agari ko
Toh baka isa ba Wlhi

Maxa xa6i 'daya acikinsu ko ranka ya 6aci
Turo baki FAWAS yayi Yace ina fah da wacce nakeso fah Dady.....
Gaskiya acikinsu ba wacce tamin. Ni HAMEEDA kawai nakeso
Cikin sanyi Dadyn nasa Yace wacece HAMEEDA
Yace a qauyan takai take ina Santa Sosai......
Cikin fusata momyn nashi Tace HAMEEDA a qauyan takai
Yace eh
Tace kana da hankali kuwa😳
FAWAS ya lalleta cikin sanyi Yace Wlhi ita nakeso kuma tama girmeni da kusan shekara hu'du
Tana sona Sosai kamar yanda nake Santa
Dan Allah Momy Dady karkuyi yunqurin rabani da ita
Gauuuu Momy ta falleshi da mari Tace Lalle Dadynka ya shagwa6aka da yawa
Toh bari kaji kayi gaggawan cireta aranka
Dan Wlhi ba wanda xaije nema maka Aure a qauye
Shashasha mara hankaki
karasa wacce xaka nema sai 'yar qauye wacce ta girmemaka mah. Mara hankalin Yaro kawai

Hawaye ne ya xuboma FAWAS
Ya kalli Dadyn shi yaje ya kwantar da kansa akan cinyarsa cikin muryar rauni Yace dan Allah Dady karka bari momy ta rabani da ita
Wlhi na rasata mutuwa Xanyi
Dadyn da mamakin 'dan nasa ya hanashi motsi shafah kansa yayi Yace karabu da ita my son
Yace ina Santa Dady
Shuru Dadyn yayi
Can Yace toh tashi kaje kayi wanka kaci abinci ka kwanta
Ya 'dago da kansa Yace toh Dady baxaka rabani da itaba ko
Yace sai nayi tunani. Yafa'da da shafa fuskarsa cikin kulawa.......
Wani dogwan tsaki Momy tajah Tace Wlhi baxaka Aureta ba.
FAWAS ya marairaice fuska Yace Dady kajita ko
Dadyn yayi Murmushi Yace jekayi abinda nace ko

Tashi FAWAS yayi yana bin Momy da kallo tana banka mishi harara
Ahaka yayi part 'dinshi
Daqar yayi wankan dan yasan Momyn tashi sarai bata fa'din abinda baya yuhuwa
Gwara dadynshi yana da 'dan sanyi

Abincinma daqar yaci
Sanda yakira HAMEEDAN tagama mai shirmen soyayyarta yana jin da'di Sannan ya sami nutsuwarshi ka'dan😟


Senior RAMADAN ko sai kusan sha'daya yasami kiran Auntyn tasa
Lokacin junior yana waya da wata wai Shakira yanayin maganar da ita tamkar yana mata ra'da dan sanyin murya

Senior yayi Murmushi Bayan ya fuskanci qanin nasa yayi nisa a tafiya da kalamai
Ya ta6e baki da fa'din nima bari naji da Auntyna aransa

Lokacin SAILUBAH na chat awata sabuwar wayarta da XEE tasiyo mata 'daxu

Tace yane Qanina
Yace qalau my Aunty
Da fatan ba abinda yake damunki kamar yanda nakeji araina yanxu

Tace nifa Komai damuna yakeyi
Ai kasani
Yace toh gayamin menene
Tace ya rage yawan watannin daya ban
Kana tunanin xan iya rasa damuwa ne atare dani

RAMADAN ya waro ido Yace da gaske Aunty ya rage😳
Tace da gaske mana
Yace wayyo toh yanxu ya xamuyi
Tace shine abinda ya kawoni 'daxu kenan mu tattauna
Yace toh mubarma gobe ko
Tace aidole
Yace toh kihuta my Aunty
Tace hmm kaci abinci Yace naci da 'dan uwana
Tajah tsaki Tace kace da 'dan iskannan mara kunya
Shuru RAMADAN yayi
Tace kayi shuru
Yace sai da safe Auntyna kiyi bacci me da'di da mafarkai....
Sai kuma yayi shuru
Tace da mafarkai masu da'di ko
Yace yes my Aunty bye bye. Ya kashe wayan

SAILUBAH tajah numfashi fuskarta cike da annuri ta gyara kwanciya da cigaba da chat 'dinta

RAMADAN mah gyara kwanciyarsa yayi. Yana sauraran junior Wanda har lokacin bai gama wayan nasa bah
Can yagama ya kalli senior Yace brother dawa kayi waya
Yace Auntyna SAILUBAH
Yace naga alama kam
Senior Yace alamar me kagani Yace nalura da farin cikin da nagani a fuskarka ne
Yace Hakkane 'dan Uwa
Idan ina tare da ita ina samun kaina Cikin nutsuwata
Idan kuma ina waya da ita ina tsintar kaina cikin farin ciki
Junior ya ta6e baki Yace kana Santa kenan Yace Sosai mah.
Yace toh Allah yabarku tare😊
AmEEn Senior Yace kana ya'dora da fa'din wacece shakiran da kaketa wani amsa wayarta kamar bakaso
Junior yayi Murmushi Yace kai brother har kariqe sunanta daga furtawa so 'daya
Senior yayi Murmushi Yace sunan nata ne so sweet
Junior Yace tnx
Sunanta kenan
Ban ta6a Santa bah
Saidai ina more rayuwa da ita Sosai
Dan tasan darajata
Karuwace ada
Amma ayanxu tawace ni 'daya
Tana xama a Dubai balarabiyace ta gaske gata 'yar babba haka
Dan ayanxu xata kai 26 years
Senior yajah numfashi Yace idan na fahimceka kana harkar xinah kenan......

Junior ya katseshi da fa'din no no no no brother.
ba Hakka bane .banayi da kowa sai da ita
Kuma ban 'dauki hakan atsayin xina bah
Tunda da ita kawai nake harka....
Senior ya katseshi da cewa xinah kake aikatawa 'dan uwana
Dan duk mutumin da xaiyi harka da mace irin yanta ma'aurata sukeyi. Batare daya mallake ba. Ma'ana ya Aureta ba. Toh ba shakka xina yake aikatawa daga shi har ita
Barama kaji 'dan akwai xinar ido ta kallo
Akwai ta hanci ta wajan shaqar qamshi
Akwai ta baki tawajan kalamai
Xinar ido itace wacce........
junior yayi saurin katseshi da cewa karka damu brother
Nasan xakamin wa'axinnan ne dan indena toh nadena
shikenan😊

Senior yayi Murmushi Yace kamarko kasani shikenan kuwa


Da tsakar dare junior na kallan senior RAMADAN yanata Sallah
Abin yadinga bashi mamaki da sha'awa
Harya kasa hakuri Santa ya tambayeshi da safe
Yace brother
Senior Yace na'am
Yace kuma kullun kake tashi yin Sallah cikin dare
Yace eh Sosai mah
Yace Amma kana qoqari .





Senior ya kallesa da kyau Yace kai bakayi ne
Yace ko sau 'daya ban ta6ayi ba
Amma ina lura da farillata Sosai. Bani barin ta wucce lokacinta
Yace da kyau
Amma Saidai da xaka daure kadinga yi xaiyi kyau Sosai
Dan nafula tana tsare mutum daga dukkan kowane sharri
Tanasa mutum ya samu kwarjini
Tanasa mutum ya kasance Cikin nutsuwa.
Tana hana baqin ciki yin tasiri a xuciyar mutum
Tana 'daukaka darajar mutum
Ata'kaice dai 'dan uwa yana dakyau mutum ya gyara lahirarsa kada yabari duniya ta ru'desa
Inaso kaxamo 'daya daga cikin masu leman lahirarsu
Junior yayi shiru
Can Yace toh Allah yabani iko
Kallansa kawai senior yayi
Yace yau inada lectures qarfe tara Amma baxan jeba dan inasan baka lokacina
Junior yayi Murmushi Yace bana wasa da karatu my brother ko ka'dan
Idan lokacina yayi tafiya xanyi in Barka
Inada wani aboki Abbas wanda mukaxo hutu tare
Kanaji 'daxo da mukayi waya dashi yake gayamin yana Cikin garin nan a Nasarawa J:R:A. Kaji dai xaixo ya 'daukeni
Banaso kayi missing wani abu daga karatunka
Senior yayi Murmushi Yace toh Amma kace mishi yalura min dakai da kyau
Junior yayi Murmushi Yace toh. Da kallan agogo Yace kaga taran ta kusa

sukayi falan gidan
Anan Momy taha'da musu breakfast bayan sun gaishesu
Dady ya kalli senior Yace my son
Yace yes Dady
Yace inaso in maka Aure acikin shekarar nan.......
Cikin sauri senior ya furxar da tia 'din da yake bakinsa
Ya waro ido Yace Aure Dady
Murmushi Dadyn yayi Yace eh. Naga kana so ne
Yace Wlhi Dady bankai Aure ba
Yace shine kuke yawan xuwa club
Yace Wlhi ba abinda muka ta6ayi narantsema
Yace hmm naji
Amma baxan canja wannan tsarin nawa ba
Adalci 'daya nayi maka shine kakawo min wacce kakeso acikin watannin nan

Yace Dady😳
Yace my son
Shiru senior yayi
Can yatashi ba tare daya gaba breakfast 'dinba xai fita
Momy tariqe hannunsa Tace katemaken kayi break 'dinnan. Kafah dena wasa da cikinka
Yace hmm xanje gun Auntyna naci ne
Tace toh me Aunty daga can xaka wucce ne
Ya turo baki dacewa eh
Tasaki hannunshi ya fitta....
Junior ya bishi da kallo da 'Yar dariya ka'dan
Dady Yace kaima ina xuwa gareka
Shuru junior yayi
Can Yace Nagano Dady Jibiril ne ya kashe mana mahaifinmu.......
Waro ido Dady yayi Cikin shaqewa Yace bashi bane my son
Junior yayi Murmushi Yace Wlhi shine
Ni naji da kunnena yana gayama wani
Shuru Dady yayi
Can Yace banasan kace xakayi wani abu akai
Yace naso kasheshi nadai fasa dan bansan abinda Allah yake nufi ba da har yabari narayu ahannunsa ya kuma tusa masa qaunata
Momy Tace kayi kyan tunani
Allah yayi muku albarka
Yace Amiien
Dady Yace toh yanxu xansa

Please Login or Register in order to submit comment