Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tashin hankali tanemi taxare jikinta daga gareshi.
Murmushi yayi yaci gaba da cewa hmm dan ban bu'de miki baki ba shine kike min asarar hawayanki.
'Dagamai kai tayi cikin rikicewa.
Nan take yashafi bakin nata saiko ya bu'de.
Ahankali tajuya da niyar barin gun.... Yayi saurin jawota jikinsa yana cewa kiyi hakuri my baby gayamin menene...
Cikin wani hali Tace nakasa gane meke faruwa dani. Na kasa gane mafarki nakeyi ko idona biyu.
Junior kanasan rikita kwakwalwata. Waye kai. Meyasa kashigo rayuwata......
Dalilai qalilan
Kuma ba da'dewa xanyi bah. Ya katseta da fa'din hakan. Aiko cikin sauri da Sanyin rai takallesa da cewa me kenan...
Qara rungumeta yayi Yace ina sanki Babyna kuma banasan kiqara tada hankalinki akan dukkanin abinda xaki dinga gani.
Baxan cuceki ba babyna daga ke har Maryam data shigo rayuwarmu
Karki qara tambayata akan duk wani abu da xaki ga nayi
Sannan Kisaki ranki kibani farin ciki dan ina buqatar hakan daga gareki
Shuru tayi mai
Jin tayi shurun shiyasa ya fara wasa da ita
Nan jikinta yafara mutuwa Tace dakata malam. Karka qara kuskuran yimin irin na jiya.....
Murmushi yayi Yace ai nalura abuqace kike jiyan. harda wani cewa dan Allah karka barni kasoni ka qaunaceni baxan iya rayuwa ba kai ba.....
Saurin hanka'deshi tayi cikin jin kunya ha'de da mamakinsa Tace hmm zaka sani. Nike fa'din hakan kokai. Ya waro ido ka'dan Yace toh asake aga me fa'da mana. Tace naqi wayan.
Yace saboda kinsan saurin narkewa kike ko.
Tace tare dakai ba...... Tana fa'din hakan tanemi tanufi kitchen. Yayi wani juyi da ita sai ganinsu tayi a bedroom
Ashagwa6e Tace dan Allah mana
Yace me kenan
Tace kabarni
Yace baxan iya bah
Tace kayi hakuri kaje kaji da amarya
Yace hmm kemah ai itace
Tace da bambamci
Yace nafi kowa sanin hakan
Tace Ni bazawarace wacce tahaife ba kamar ita bace budurwa sankaceciya. Kaima rikimarka ce tasaka kwasata.
Kiss yasakar mata cikin shauqin so yana me shafa fuskarta yace ko ayaya kike baxanqi kwasarki bah my baby
Ina miki wani so Wanda yafi qarfin akirashi da MASEEFAR SOO
Kin mallake 'dan uwana nima yanxu kina San mallake ni Allah kika cutar dani baxan yafe miki bah.
Tace hmm aidama anyini ne kawai danku
Karka damu ko'ina cuta baxan iya cutar da kai ba.
Kasanko yanda ayanxu nake jinka araina.
Kasanko yanda yanxu haka xuciyata take bugawa jina ajikinka.
Murmushi yayi dakai hannunsa qirjinta ha'de da lumshe ido natsawan wani lokaci sannan ya bu'de idan ahankali yace naji xuciyar na bugawa da gaske
Sannan tana tabbatarmin da abinda kika ce yanxu
Sannan tana San takasance tare dani har qarshen rayuwata
Sannan baxataso nayi nisa da ita bah.......
Sannan tana tsorata da lamarina
Sannan tana San tafani Farin Ciki Na har qarshen rayuwa
Sannan tana so nadinga jin tausayinta akowane lokaci....,.
Shuru yayi ganin hawayan dake xubuwa daga fuskarta.

Tace wlhi banta6a jin hakan ga RAMADAN ba.
Nasan nasoshi so me tsanani
Amma lokaci 'daya kacanja tunaninah
Nayi mamakin yanda naji hakan agareka.
Ka gayamin kai waye
Nayi imanin kai ba mutum bane
Inkai mutum ne ya akayi kake karantar xuciyar mutum.
Duk abinda kalissafo yanxu duk haka yake
Kaji tausayina
Kadena cutar da ruhina
Kaine mutum na farko daka shigo rayuwata kakesan tarwatsamin ita......

Lashe hawayanta yahau yi cikin wani hali. Sanda yagamah lashe mata tas kana yahau kissing din bakinta yana me cewa inajin da'din bakinnan sosai....
Tasan yabasar da xancan nata ne....
Dan haka tayi qoqarin tsaidashi daga kissing din tana cewa kabani amsata manah.....
Kallan kwayar idanta da yayine yasata yin shuru
Dan ganin yanda idansa ya canja ya zama bula wanda tunda take arayuwarta bata ta6a ganin idan mutum ya zama haka ba. innalillahi'wainna'ilaihirraji'un. Shine abinda tace
Yace my baby kika qara tambayata kan wani abu wanda ya shafeni xan hukuntaki
Da tsoro Tace na bari. Saidai kaji wa'yannan bayanan nawa ka'dan.
Yace ina jinka

Tace kadena 6acewa dani dan hakan yana sani tsurewa
Yace angamah. Sai kuma me.
Tace sai kuma kabarni karkaqara kusantata dan kaqara mutuwa xanyi dan bana tunanin wani 'dan Adam yata6a shiga duniyar Dana fa'da ahannunka jiya
Murmushi yayi yace shima angama.
Murmushin itama tasakar mai tace xan dinga baka kiss ako yaushe idan katabbatar min da abubuwan da kace.
Yace toh Amma da wata magana 'daya
Tace ina jinka
Yaci gaba. Ayanxu bama qasar Nigeria muna misra
Waro ido SAILUBAH tayi tace me😳
Yace nasan kinji
Dani ka'dai xaku rayu sannan xamu mutu tare
Baxaku qara ganin wani naku ba
Kun barsu kenan har abada......
Tace tayaya akayi muke misra bayan 'yan uwa da abukan arxiqi sun kawomu wannan gida a daran jiya

Murmushi yayi yace nasan baxaki dena tambayata ba. Amma bakomai xan amsa miki dan kinyi min babbar illah arayuwata.

Lokacin da aka kawoku bayan tafiyar kowa ne nayi amfani da wannan damar dan dama nasa anyimin irin wannan gidan anan misra.
Da wannan damar nayi amfani bayan kowaccanku tayi bacci saina daukeku nadawo daku nan
Dagaku har kayanku ba abinda nabari
Karkiyi mamaki sosai dan lamarina ya wucce nan sosai

Ayanxu baku da hanyar 6ullewa ficcewa awanan gida.
Ba get bare kusan ta inda aka shigo daku
Komai na rayuwa bawanda babu awannan gida.
Na gama baki labarin sai kitashi muje dining muyi breakfast
Tace waye yabaka wannan labarin kuma ta ina kata6a ganin anyi hakan

Qura mata ido yayi batare da yace mata komai ba.
Ganin haka yasa tatashi ta ficce daga 'dakin ixuwa ga dining tana rayawa aranta Lalle Junior ya gama raina mata hankali. Shegen gaye itaji take ma kamar mafarki takeyi. Jitayi aranta koma me xai dingayi yayi can tamatse mishi yaje can ya qarata da Rainin Hankalinsa ita ta gaji wlhi.


Bayan taxauna gakan kujerar sai tashiga bu'de fulasan tana mamakin yaushe aka kawo musu breakfast haka kusan fulas biyar tana ina

Fulas 'din farko farfesun kajine yaji komai na kayan ha'di sai Qamshi yake
Na biyu soyayyan dankaline ha'de da kwai yaji sinadarin tafarnuwa da citta
Na uku indomie ce zallah da kayan lanbu taji bushash shan kifi
Na hu'du dogwan falas ne me 'dauke da ruwan tia Wanda yaji kayan Qamshi me 'daukar hankali
Na biyar nan kuwa farfesun kayan cikine lafiyayya......

SAILUBAH ta lumshe ido ha'de da ha'diye yawo tace wow beautiful

Nan taja plet taxuba abinda ranta yake so. Tana cewa aranta Allah sarki Momy. Nasan wannan girkinta ne. Ba 'yan aiki tasa bah

Sanda tafaraci tatuna da maryam. Nan tata6e baki tace gaskiya xan faraci baxan iya jiranki bah.
Sanda tacika cikinta tace masha Allah.....

Nan tashiga Neman wayarta tanemeta sama da qasa tarasa

Hakan yasa tanemi fittowa waje dan neman junior........



Junior ko bayan ta ficce gun maryam ya nufah wacce tuntuni take harabar gidan xaune tana aikin kuka

Ya xauna daf da ita wannan karan bata tsorata sosai bah

Yace malama maryam Ki sauwaqema kanki wannan kukan muyi magana
Kallansa takeyi tamkar yau tasanshi
Yaci gaba. Nan ba Nigeria bane
Kin shigo wata sabowar rayuwa ce ke da SAILUBAH
Axahiri nafi cutar da SAILUBAH akanki danke kika ganni kikace kina soh
Sannan nasaka araina ayanxu ina sanki ina qaunarki
Ki kwantar da hankalinki mugina kyakkyawar rayuwa......
Cikin sauri ta katseshi da cewa in kwantar da hankalina fah kace
Tayaya xanyi rayuwa da aljani bayan ni nakasance mutum
Wlhi na hakura da sanka ayanxu babu soyayyar araina tsorone fal ha'de da nadama da Allah wadai acikin xuciyata

Wlhi baxan iya rayuwa dakai bah

'Yar kyakkyawa da ita.... Junior yace aransa. Kana yayi Murmushi ya kama fuskarta ya ha'de bakinsa da nata yana aika mata da wani shu'umin kiss Wanda yasa tafara shinewa

Murmushi SAILUBAH tayi dan hakan tafarune dai dai da isowarta gun
Ta ta6e baki tace aranta wanan kiss 'din bala'i ne
Tayaya ni nake iya 'daukarsa. Bare ke nan take xaki narke yarinya....

Bayan hararo wa'yannan bayanan da tayi sai kuma wani zazzafan kishi ya caki xuciyarta

Cikin ranta tace 'yan iska kawai
Wlhi daga yau baxan qara yarda kamin kiss ba. Ka ha'da bakina da nawata. Tab da sake

Ganin da tayi kamar sumar da maryam yake qoqarin sanyi shiyasa yin gyaran murya amatuqar fusata.......

Junior yayi murmushi yace haba my baby kinsan dai baxan 'dauke miki waya ba.
Kiyi hakuri ganina da kikayi awannan lokaci so kawai na afresh shin kwakwalwarta
Kin 'dauki minti uku kina kallanmu ko.
Harara tasakar masa da cewa nasan kai ka'dauka pls kabani wayata kawai
Yace wlhi na barsu a Nigeria taki data maryam.....

Cikin maseefa takatseshi da cewa wai me kake cewane
Kanata wani magana kamar kasha giya a'ina aka ta6a yin hakan

Tashi maryam tayi cikin wani dan jitayi ayanxu bata damu da komai bah

Ji tayi ayanxu bata wani tunanin da takeyi 'daxo nasan komawa gida ha'de da tsoran masoyin nata
Tana ji aranta zata rayu da Junior xakuma tamutu dashi ahaka xatabi umarninsa akan komai.

Taji hakanne saka makwan wannan asirtaccan kiss 'din da yayi mata

Dan haka takalli SAILUBAH idanta na lumshewa tanayi kamar xata fa'di dan ciwan so da Junior ya antaya mata ayanxu fiye da nada
Tace AUNTY SAILUBAH kiduba gidan nan dakyau wlhi ba Wanda aka kawomu jiya bane

Kinsan ni idona abu'de yake lokacin da aka shigo dani jiya
Harabar gidan ta bambamta da wannan.

Kinga fah☺ ba hanyar ficcewa....
Rungumota Junior yayi ganin saura qiris ta fa'di tsabar layi yace dats good my luv gaya mata ashe xaman da kikayi 'daxo bana kuka ka'dai bane Ashe kina qarema in kike kallo ne
Murmushi tayi tana me neman bakinsa cikin buqata. Ganin haka yasa SAILUBAH fara waige waigen gidan hankalinta amasefar tashe tahau xaga gidan

Ba Hanyar 6ullewa da gaske ne
Kuma gashi katanga me tsawo ko ganin gidan makwaftansu ba gani take bah
Gani SAILUBAH tayi kamar suna wata duniyar ce

Afurgice takai ganinta ga inda Junior da maryam suke......
Nan taga wayam
Nanko take cikinta ya mur'da alamar tasamu hargitsewar cikin

Tunda uwarta ta haifeta bata ta6a ganin tashin hankali irin nayau ba......
Bata ankare bah taganshi gabanta
Baiyi wata wata bah ya rungumeta yana mai cewa nakai maryam dining ne tana break. Yana fa'din hakan ya ha'de bakinsa da nata yana aika mata da wannan asirtaccan kiss 'dinnan daya ba Maryam

Nan take taji kamar angoge mata wani tunani acikin kwakwalwarta
Taji tamanta komai sai So da qaunarsa ne acikin xuciyarta

Junior kenan
Yaje ya shinfi'deta akan gadanta ganin tariga da ta tafi. yayi wani shu'umin Murmushi yace aiba nine nafaro SAMAREEN BANAH bah.



Momy ko tashirya ma direba breakfast lafiyayye dan ya kaima su SAILUBAH.
Saidai yana zuwa gidan da harda shi axuwa jiya ya tarar da Filin Allah kawai.
Yanda yaxubama Filin ido yana tuna anya nan ne kowa. Hakan illahirin wasu tsirarran Mutanan unguwar suka xubama falin ido da mamakin ya haka






Yayi duban duniyar nan Amma tunaninsa ya tabbatar mai da nanne gidan
Toh me yafaru a daran jiya
Haka ya kuma gida gun Momy ya gaya mata abinda idansa ya gani
Lokacin dad nanan yace wannan irin xancan banxa ne kakeyi
Direba Yace Allah dady abinda nagani kenan
Dama breakfast Dady

jin hakan yasa yace suje
Momy tace muje tare. PH air at dake jinsu tace xan rakaku Momy
KHAULAT DA KHAULEET suma ganin Khairat xata yasa suka miqe
Momy tace kuxo muje dakka

Ikwan Allah. Aikuwa suma ganin Filin Allah
Duk suncika da mamaki wannan abin Al'ajabi

Momy tasa kuka tana cewa nashiga uku mefe shirin faruwa ne
Dady yace koma miye ai ya faru yanxu kam dan haka mukomah musan abinyi
Tace aa mutambayi me gidan nan na kusa dasu
Dady baiyi musu bah dan yafita shiga tashin hankali
Tunda RAMADAN yabar duniya baya da wani abinso kamar junior
Bayasan yayi nisa dashi
Wai meyake faruwa ne.

Yanda makwafcin jikin gidan nasu yake qaremah filin kallo hakan kadai ya Isa ya tabbatar musu baida sani akan komai dan fuskarsa qarara tanuna mamakinsa da Al'ajabi
Yaudai baifito sallar asuba bah bare yasan ya akayi
Ya kalli Dady yace wato tunda nake aduniya ban ta6a ganin abin mamaki haka bah
Wannan kamar aikin aljanu ne.......
Momy tadafe qirfe tace shikenan yanxu suntafi min da junior da SAILUBAH komai kake nufi bawan Allah😳
Yace bawai ina nufin hakan har tafaro bane
Saidai abinne ya xarce hankalin mutum
Tayaya kana ganin gida lokaci 'daya kanemeshi karasa
Wannan ai ba aikin bil'adama bane
Gaskiya na tsorata da lamarin xani bar anguwar nan yau da iyanina

Dake mutumin ba qaramin tsorata yayi da lamarin ba. Dad nayi mishi magana Sam baiji shi bah
Damuwarsa ya isa ga iyaninsa kawai subar wannan unguwa

Bayanda Momy da Dady suka iya haka suka koma gida hankalinsu a bala'in tashe. Khairat ko kuka kawai takeyi


** ** **
Dady momy Kakah innah FAWAS KHAMIS HAMEEDAH XEE Dadyn Maryam da mom 'dinta duk sun hallara a falan Dady kowannansu hankalinsa a matuqar tashe
XEE kuka takeyi da gaske dan bata ta6a ganin wannan abin Al'ajabi ba
FAWAS da KHAMIS sunyi shuru sun rasa wane tunani xasuyi. Musamman idan suka hango filin da aka kira da nan ne gidan Junior wanda suka rabu dashi jiya hankalinsu ba qaramin qara tashi yake bah.

Su Dad ko tun suna tattauna lamarin har sun gaji sunyi shuru

Dadyn maryam ya bada shawara atara malamai suyi Addu'a ko Allah xaisa agano wani

Toh... kowa yayi na'am da batunsa
Dan dama abin daya dacene ayi.....

KHAULAT DA KHAULEET sun lafe jikin momy abin tausayi ganin da sukayi tana kuka sunsan ba lafiya ba musamman idan suka kalli yanda fuskokin kowa yake.


KHAMIS ya rungumi matarsa XEE bayan komawarsu gida yace narasa gane wannan wane irin lamarine my luv. Banta6a ganin hakan a xahiri bah
Sai gashi yaxo gareni axahirin
Ina yin wani tunani
Da sauri XEE ta kalli fuskarsa tace me kake tunani
kai hannunsa yayi ga fuskarta yahau goge mata fuskar yana cewa share kawai banda tabbacin hakan
Ki kwatar da hankalinki Ki saki ranki komai xaixo da Sauqi
Murmushi tayi Tace Aunty LUUVAH ce bah
Lumshe idansa yayi Yace nasani ai
Kinga kukan xai haifar miki da ciwo Amma idan Addu'a kike musu fah.....
Shuru tayi mai
Ganin hakan yasa ya qara rungumeta yana cigaba da cewa Ki sakar min kanki kinyi Aunty XEE


HAMEEDAH ko bayan subewarsu a kujera lafewa tayi jikin FAWAS tana numfashi Ahankali Ahankali. Tace naga wani al'amari ni HAMEEDAH meke faruwa dasu oho
Wai dama anayin hakan ne.
Murmushin yaqe FAWAS yayi yace ban ta6a ji bah
Tace nima dai kam
Amma bakayin tunanin wani abu
Yace konayi bashi da amfani
Tace toh tashi muyi musu sallah Allah ya baiyana koma miye

Jamata hanci yayi yace kina lafe jikina kina mutashi
Tashin tayi tana cewa jikin naka ne É—ami habibi
Murmushi yayi Yace ke kuma naki laushi bah








*** *** *** ***

Wata 'daya da fara rayuwarsu agunsa
Sun manta da komai sai soyayyar mujinsu ce aransu ha'de da 'dan kishin junansu

Sam sundena damuwa da 6acewar da junior yake musu
Sunsa aransu xaixo musu ako wane lokaci

Ba abinda sukeyi naci da Sha dan komai ganinsa suke sai wanda mah ransu keso sukeci

Sunyi 6ul6ul dasu gwanin ban Sha'awa basu da damuwar komai

Ko waccensu xatayi kallanta a 'dakinta idan tagaji tafito gun shaqatawan gidan tayi kalle kallanta idan nanma tagaji taje gun 'yar uwarta susha hira

Kuma karkuce hirar gida suka ko ka'dan hirar duniya kawai suke.
Dan maryam ta manta tana da iyaye. Bare tayi wani tunaninsu
Haka SAILUBAH sam tamanta komai daga ciki ko har da 'ya'yanta

Dukkansu abu 'daya ne aransu wato soyayyar mujinsu



Abinda yake damun SAILUBAH 'daya ne yanda Junior yake kusantarta Cikin mafarkinta. Idan baya 'dakinta
Sam bata ta nutsuwa dashi koran daba ran girkinta ba

Tayi mai qorafin yaqi denawa dan yanxu lamarin nashi ya dena tsoratar dasu bare mamaki sun rigada sun saba ayanxu.



**
Tana kwance kan kujera tana kallan wani film ita da Maryam yaxo ya rufe mata ido ta baya...
Murmushi tayi tace yau kuma da wasan yara kaxo
Murmushi yayi yazauna kusa da ita yace baki da damuwa ko
tace sai taka my baby
Yace toh gayamin menene
Tace cikina yana min wani iri hak dai
Yace kodai nayi ajiya ne
Murmushi tayi tace ba mamaki
Yace gyara kwanciyarki nagayi
Gyarawa tayi yahau shafah cikin idansa arufe Yace hmmmm baby girl zaki qara bayarwa
Tace nata6a bayarwa ne
```Xuba mata ido yayi na 'dan wani lokaci yana tuna ashefa ya shafe tunaninta.```..…….…

Kayi shuru….. Ta katseshi
Yace mantuwa nayi
Tace kodai miye ina buqatar caka lalla6a.....
Rufe idansa yayi na'dan wani lokaci kamar minti uku sai ya bu'de
Yace rufe idanki.....
Rufewa tayi
Yace toh bu'de...
Ahankali tabu'de. Sai ganin cakalalla6ar tayi ahannunsa cikin wata tsohuwar roba irin ta yaran nan
Da murmushi takar6a
Tana cewa a ina kasamo
Yace can wani qauyan takai naga wata yarinya nayi tatara yara kowa nasan siya
Shine na'dauko wanda tasoyan da ajiye mata ku'dinta
Atare Maryam da SAILUBAH suka sake dariya
Maryam Tace xanso naga idan yarinyar rikicewar da xatayi
SAILUBAH tace konima xanso ganin hakan

Aiko Junior yace toh Ku kalla nan.....
Nan suka maida kallansu inda yace

Muraran sukaga wata yarinya bata wucce shekara goma ba. Da kaskwan suyanta na cakalalla6an nata
Tatara yara sa'o'inta suna tayata hira damasu siyan da marasa siyan
Tajuya na kaskwan tana San sakawa a robarta taga ba robah
Dan ba wanda yaga 6acewar robar tata duk cikinsu
Ganin hakan da tayi shiyasa tahau dubawa qawayan nata na tayata

Gasu suna duban duniya basuga roba bah
Nan yarinyar ta cukume wata qawarta tana fa'din wlhi saikin fitomin da robata 6arauniya
Niyi lissafi sarai na sittin da niyar na soya
Nan fa'da ya kaure ita wacce aka lanqayama satar tace ita bata 'dau robah ba
Abinka da yara nan suka fara fa'dan doke doke har aka nemi xubar da kwullin cakalalla6ar
Wata acikinsu idanta yakai kan ku'din da Junior ya ajiye musu tace kinga ku'dinki sittin da biyar 'din Rabi Amma ba robar
Jin hakan da ganin ku'din da gaske shiga tsaida fa'dan nan kuma akashiga neman roba abin yara ba tunanin waye ya siya


Ganin hakan yasa SAILUBAH da Maryam sheqewa da dariya.
Maryam tace bara na 'dauko abu kijuye sai a mayar musu da robarsu
Kanta tatashi har junior ya aiwatar da abinda tace
Ganin hakan yasa takuma taxauna.
SAILUBAH tace tayaya xaka mayar musu da robar
Yace bari kigani. Jefa robar yayi a qeyar wata daga cikinsu
Saiko nan suka hau ihu suna masu cewa wayan jefo robar
Rabi tace mah manu ne yasiye shine yajefo kinsan shi dasan cakalalla6an
Da yawansu sukace kuma hakane
Wacce ko aka lanqayama sata tafiyarta tayi



Haka rayuwarsu take ayanxu
Shin xata 'daure kuwa



Rokwan Allah sosai su dady sukasa agaba

Wannan ba abu bane wanda yake buqatar fitowa duniya kowa yaji
Suna addu'ar suna masu sawa ayi

Lamarinfah ya damu zuciyoyinsu
Takai har daqar suke iya cin abinci
Abin tausayi KHAULEET KHAULAT sai ambatar mahaifiyarsu suke SAILUBAH
Da xaran hakan tafaru Momy fashewa take da kuka ita dasu Kakah

XEE tasaka damuwar rashin aminiyar tata aranta
Xanso kuga yanda tarame ta ficce daga hayyacinta

Duk da yanda FAWAS da KHAMIS suke qoqarin 6oye damuwarsu abin ayanxu yafi qarfin 'daukar xuciyarsu
Dan basu da wani tunani sai nasu AUNTY LUUVAN SU

Wasu malaman sun tabbatar da cewa suna tunanin mijin nasu aljanine
Dady yayi ma malaman tsawa akan 'danshi mutum ne

Hakan yajawo hankalin mahaifin maryam har shima yafara tunanin kidai Gaskiya ne

Momy dasu Kakah hankalinsu ya qara tashi tunaninsu ta'ina kuma Junior ya zama aljani

FAWAS da KHAMIS xuciyoyinsu sunshiga ru'du sosai
Inda suka tuna ranar rabuwarsu da junior daran angwancinsa da abinda ya tabbatar musu akan matan nasu
Saidai sunqi kar6ar hakan amatsayin hujjah.........................,






Suna zaune suna hira Maryam tace Aunty inaso yau mufita waje kinga tunda muke gidan nan bamu ta6a Fita munga yanda wajan take bah
SAILUBAH tace toh maryam idan zamu fitan ta'ina xamu fara
Kinga ba qofa bane da gidan......

Toh kushirya muje mana
Junior ya katsesu da fa'din hakan
Murmushi sukayi atare suna me kar6ar hijabikan daya miqa musu
Bayan sunsa
Ya kalli maryam yace anya matar nan baxata haihuba yau
Tace ba mamaki dan naga kamar cikin yayi qasa yau....
Katsesu SAILUBAH tayi da cewa kuci gaba da gwulmata dakyau

Dariya maryam tayi tace magana muke akan qila yau Ki haihu
Tace oho kemah saura wata nawa ne Ki harfe

Tace 'dan mutum ko 'dan aljan xamu Haife oho
Murmushi SAILUBAH tayi tace dake mu ya tabbatar mana da cewa mu Mutane ne qila su 'debo ruwa biyu.

Sa dinga al'amuran aljanu dana mutane

Maryam tace qilama dan hakan ne xamukai wata tara tara
Dan kamar nata6ajin ance wai aljani yanxu xai miki ciki awanni uku nayi xaiki haife idan ya kasance babu miss da jinin bil'adama

SAILUBAH tace a'ina kikaji

Dafe kanta maryam tayi tace inaji a jikina kamar na ta6ayin wata rayuwa da 'yan uwana bil'adama
SAILUBAH tata6e baki tace niko banta6a jin hakan bah
Tace nima kawai na fa'di hakan dan yana zuwa min lokaci lokaci ne a kwanyana

Murmushi Junior yayi. kunga kun isheni da surutu ke kalli hotannan kinsan ko suwaye
Yafa'di hakan da kallan SAILUBAH

Kallan hotan take da kyau RAMADAN ne dasu KHAULEET ha'de dasu kaka da Momy XEE da HAMEEDAH FAWAS KHAMIS.....

Saurin girgixa kai tayi tace bansansu ba ban ta6a ganinsu ba. Kaima kasani kai ka'dai nasani meyasaka nuna min su......

Murmushi yayi da jawo wani hotan daban daga aljihunsa ya nunama maryam yace ke fa kinsan wa'yannan....

Mahaifinta ne da mahaifiyarta ajikin hotan
Shuru tayi na wani lokaci kana tace kamar idan ina bacci ina ganinsu
Amma ban sansu bah ko ka'dan
Ka sani Kaine wanda muka sani meyasa Kanuna mana wa'yannan hotonan ne.

Murmushi yayi yace bakomai muje

Tashi yayi dasu sama yace Ku kalli qasanku....
Kallan qasan sukayi aiko sai sukaga babu gida ko 'daya ajikin nasu
Gabaki 'daya ma gidan nasu a tsakiyar wani babban ruwa suke
Atsorace SAILUBAH tace ina jin jiri...
Maryam tace dama acikin ruwa muke
Murmushi yayi yace ga xahiri kurufe idanku...
Ruf suka rufe. Can yace su bu'de suna bu'dewa suka gansu a wata qasa ga Mutane sai harkar gabansu suke. Kyawawa dasu duk dogayan riguna ne dasu alamar qasar musulmai ne. saidai dukkanin qafafunsu irin na akuyane. Sai sukaga na Junior ma ya koma irin nasu
Da ganin junior Sai suka fara zuwa gaishe shi da nuna girmamawa a gareshi da alama yana da wani babban matsayi agaresu

Sannan sukan kalli SAILUBAH da maryam su sunkuya ka'dan a gabansu suna me nuna Farin Cikinsu da ganinsu sannan su wucce

Maryam tariqe hannun SAILUBAH tace kinga wasunsu na 6acewa kamar na Junior
SAILUBAH tace kika sani ko 'yan uwansa aljanunne. Kin ta6a ganin kyawawan mutane irin wa'yannan ne kallesu fah☺
Kallansu sosai maryam takeyi tace toh ai xarginsa muke bamu tabbatar da cewa shi'din aljani bane
Ta6e baki SAILUBAH tayi takama hannunsa tace kai tabbatar mata da cewa kai ba kamarmu kake ba kai aljanine
Murmushi yayi Yace kunfiya surutu komai kika gani saikun tattauna akai. Nan garin iyayena ne kunga wancan gidan shine gidan iyayen nawa.....
Har suna ha'da baki wajan cewa toh muje mana dan kowaccansu so take suqara iri ace su uku kwallin kwal suke rayuwa ba wanda suka sani.....

Ganinsu Cikin gidan shiyasa su tsorewa
Dan ba qaramin ha'duwa gidan yayi ba
Kamar mah gidan sarauta ne. Dan yanayin tambarin gidan ne ya tabbatar musu da hakan
Ga ma'aikatan gidan sai xubewa suke gabansu suna me meqa gaisuwarsu
Gashi dukkaninsu kyawawa ne naqarshe

Sudai tsintar kansu sukayi acikin wani babban falo Wanda ya tara komai na jin da'din Junior

Wata mata suka gani wacce kyanta yaso furgitasu
Ta sakar musu murmushi tare da cewa lale marhaban da sirikaina
Saiyau yaga damar kawo min Ku
Shuru suka mata
Dan basu ta6a jin murya me xaqi irin tata bah

Junior ya saukar da kansa qasa yace amin afuwa mama nayi kuskure......

Wata dariya takaure da ita sannan ta kallesa rai 6ace tare da tashi daga shigingi'dan da take ta har'de qafarta cikin isa da jin mulki. tace Dama nabaka kwana biyu ne naga xakaxo....
Qara sunkuyar da kansa qasa yayi yace natuba Ki yafemin ya ummi

Kawai da fuskarta tayi Tace yanxu nakeso kaje ka tada *Yaran mutane gada baccin daka sashiyi*
Ka rikita tunaninsa kan wani uxiri naka
Ka hanashi ibada na tsawan kwana uku dan tsabar mugunta
Yaushe kacanja hali dahar kabari she'dan yayi maka ganga aka

Kajefah 'yan uwansa cikin tashin hankali
Tunani fah suka shiga akan wane irin lamari ne irin wannan
Likitocinsu basu ta6a ganin wannan ya kwanta bacci na tsawan kwana uku ba. Ba kwaya yasha ba. Haka ba kayan maye yasha bah.
Kawai kasashi agaba kana nuna mishi rayuwar da bata da amfani.

Duk abinda kake nufi wannan damuwarka ne ni damuwata tsayar dashi da kayi daga ibadarsa

Gashi ka hana yuhuwar aure tsakanin Fatima SAILUBAH da

Please Login or Register in order to submit comment